You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________________



Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji
sallamarsa ta karade tsakar gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da
sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar yazo yi,ko kuma akwai abinda ya
hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da halayyarsa,macce daya ce
cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan maganinsa,ta
kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta kulashi ba anji
muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta.

Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce
uwar dakin ta yadda ba zata tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan
nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin mutanen nan ne dai basa shiga
abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata da magana sam
sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma
yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu
su kansu basu da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji
ai sun gama bayyana a fili a game da ita.

Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda
bibbiyu,sai dressing mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma
dakin neat yake,komansa akan tsari,ga kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman
dai yadda falon yake.

Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar
shimfida da tattausan blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta
keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga
gefan pillow dinta.

Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da
wayar da kuma me wayar gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu

*_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da
wani emotion. Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran

"Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana
tuna yadda al'amura suka tafi mata successful kaman yadda aka saba.

Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya
shafeshi cikin wayar,bata bar hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar
alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta sake bin wayar ta tabbatar komai ya
koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi wata number ta kira
ta kara wayar a kunnenta.
Bugu biyu aka daga ana sallama cikin zaquwa da zumudi

"Ina fatan saqon ya riskeki?" Tayi tambaya zuwa ga daya sashen

"Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me
baki haquri kuma akan sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko
sunanki ma ban sani ba"

"Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata
ba......abinda na baki kiyi qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin
mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan yadda zaki sanya masa
tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce ba,na
barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan
fada masu yawa da take dasu take kuma son gaya matan.

Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin
lambobin dake akwatin katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani
irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce number da bata yarjewa bace take iya
samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda take da muradi ra'ayi
ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani.

Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata.
Batason takura sam,sai taja tsaki tana kallon fuskar wayar.

Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun
akwak enough kudi a hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin
ta fada zuwa wani agenda din.

"Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting
kiran shima sannan ta kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta
qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe
zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana qoqarin daure
gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta.

Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin
farin hijab cikin jerin hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata
shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta
tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan fuskar tata. Towels
dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta
can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando
kaman kwandon kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana
fita a dakin tare da sake gauke fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take
duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk da dama ita din ba matum
bace data cika fara'a.

Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar
gidan ba zasu wuce mutum biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa
da nata shekarun idan ka dauke mutum daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman
kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take qoqarin kunnawa hayaqinta
yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata.

Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar
yadda itama kusan haka take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta
kaman yadda a wasu lokutan yake kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya
sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu.

Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da
tsafta da kulawa,ta xare towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta
nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye daga gidan mahaifansa zuwa gidan
kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen gwaggo mace ta
biyu a wajen mahaifinsu.

Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama
ta motsa bakinta tana maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a
zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar
sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato murmushi kowacce safiya a tsakar
gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar mahaifiyarta.

Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga
qarshe,dole ta kauda kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan.

Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu
qananun mitoci da qorafi duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami
da ci gaba da yasar da maganganun da tayi imanin da biyu suke yinsu kamar yadda
suka saba.

Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa
da dakinsu toilet. Daya daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing
toilet.

Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a
bandaki qwaya daya tal!. Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta.

Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na
daura alwala a nan bakin famfo sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a
sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin bishiyar.

Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun
kalleta sun kuma dauke idanu kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan

"Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi
koda yunqurin tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa
kowacce cikin su ukun ba muddin zasu hadu a farfajiyar gidan.

Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta
da wannan kallon dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu.
sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*



PAGE 15



A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta
guda daya sauke qafarta da dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa
data zamewa kowanne motsi na rayuwarta lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin
gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin numfashi wato MAHAIFIYA.
Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara
yin tsaho da nesanta bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka
shude amma ya gaza yin nasara a kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin
rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin tata......jajirtacciyar uwa data zamewa
maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana musu kuka akan rashin
mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya
ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta
tare wannan shingen maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne
musu numfashi har ya zuwa lahirar duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata
tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da rayuwarta......ya kuma bude mata
qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi yawan
lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana
zuciyarta don cimma burikanta.

Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen
dolen ta sauya akalar rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar
kamawa cikin ruwan da take ninqaya. Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala a
duk sanda taso hakan,ta bace ta kuma saje da duk yanayi ko launin da takeso ko kuma
taga dama.

Tana da tarin sunaye masu yawa da a duniya a yanzun bayan ainihin
sunanta na yanka SABREEN. Sunayen da ba'a yiwa yanka ba don tabbatuwar samuwarsu a
kanta.

Akwai idanuwa bakuna da hankula masu zafi da batasan adadinsu ba a
kanta. Kowanne kuma da irin nashi kallon.....hasashen da furucinsa dangane da ita.

Karon farko ta sakarwa fuskar nan tata murmurshi data fito tawai bisa
fuskar madubin dame gabanta duk kuwa sa siririyar qwallar dake kwance cikin
qwayoyin idanunta masu sheqi kaman an diga ruwan zaiba. Karaya da kuma qwarin gwiwa
na karakaina tsakanin qirjin nata,saidai ko sau daya bata aminta ta dauki FADUWA
TSORO ko kuma ja da baya ba.

K'aramin towel da yafi kama da handkerchief ta sanya ta tsane qwalla
don kada ta bata daman fitowa,ta miqa hannu ta jawo stool ta zauna a kai tana saka
hannunta tana kokawar daure sassalkan gashinta dake qoqarin kwancewa daga daurin
farko datayi masa.

A nutse ta jawo set na kayan shafarta da take amfani dasu. Skin care
product ne da suke mahadi da shower gel cream da sauran tarkace,wanda kudinsu duka
zai tasamma dubu arba'in.

Kudi ne me nauyi da ciwo a wajen me qaramin qarfi,to saidai ta
wajenta amfani dasu sun zame mata jiki kaman yadda suka zame mata wajibi. Tana son
ado,tana qaunar tsafta da qamshi,wanda da a baya bata basu muhimmanci ba,saidai
daga bisani ta gama karantunta tsaf......ta fahimci kowanne taku a rayuwa akwai
abokin yinsa.....akwai sauyawar yanayi da ta zamewa jiki da rayuwa dole......dole
sai an aiwatar da wasu abubuwa ake samun wasu abubuwan,dole sai an gusa koda da
taki daya ne sannan ake samun wasu sabbin damarmakin suke shigowa rayuwar dan adam.

Gayunta na daya daga cikin abinda ya sake sama mata MUMMUNAR SHAIDA da
kuma mummunan zato daga bakunan mutane da dama. Zaton daya kamata ya qona mata
rai.....ya sanyata fidda qwalla masu zafi.....a maimakon hakan saidai kawai ta
murmusa,ta kuma motsa ta barka a wajen da salon abun nan dake nuni da BANI DA
LOKACINKI/KA.

Tsaf ta duk wani shafe shafe nata,ta kuma gyars gashinnan me tsanani
yauqi sheqi da tsaho,ta dameshi cikin ribbon me dan girma,abinda ya sake bawa
ainihin kamanninta fita ras kenan.

Koda ta bude ma'ajiyar kayanta tsaiwa tayi tana tunanin suturar da
zata dace da jikinta a wannan lokaci. Shaqe take tafff da tarin suturu na
alfarma,masu tsadar da koda ba'a gaya maka ba kai kanka ka sani. Suturun da a
tashin farko xakasan sunfi qarfin wanzuwa cikin wannan wardrobe din.....kaman sunfi
qarfin ma ace akwai wani cikin gidan daya mallaki masu darajarsu.

Juya zagayyayun idanunta tayi tana dan lumshesu kadan zuwa bangaren
abaya. Sai data gama nazarinta sannan ta jawo daya daga ciki. Egyptian abaya ce me
asalin daraja da kuma kyau wadda kudinta ya tasamman dubu arba'in da 'ya'ya. Sam
sutura me tsada ba damuwarta bace,tana iya mallakarta a duk sanda tayi marmari ko
kuma muradin hakan.

Da sanyinta dinnan da yake cikin halittarta take daura belt din da
abayan yazo dashi bayan ta saka ta farko ta kuma dora alkyabbar da abayar tazo da
ita. Siririn mayafi ta zaba daya dace da rigar tayi rolling me kyau da ma'ana,take
zagayyar fuskarta ta fito cif tsakiyar veil din,sai ta kuma duba handbags dinta
dake rataye sama da goma sha biyar kowacce da takalminta mahadi a qasanta.

'Yar qarama ta dauko qirar kamfanin D&G da takalminsa,ta natsa gaban
madubi ta dauki turarenta ta bintike kan ta feshe jikinta dashi,sannan ta zari
wayarta ta jefa a jaka tana duba agogon dake daure a tsintsar hannunta ta doso
falon.

Jakar ta ajjiye tana jawo tea flask dinsu tana qoqarin budewa. Bata
fiya son cin abinci da wurwuri da safe ba,to amma kuma tana tunanin zaiyi wahala
idan ta fita din ta iya tsaiwa taci komai tasan halin kanta da kanta sarai.

A tsaitsaye take kurba kyawawan idanunta zube fes saman qaramar waya
me keypad data dora saman cinyarta tanata qoqarin kiran wata number.

Bugu biyu aka dauka,muryarsa ta bayyana cikin wayar da wani irin
shauqi da doki

"Da wacce irin saa yay na wayi gari ne?,ya Allah" Ya fadi yana zama gefan gadon
bedroom dinsa.

Taqaitaccen murmushi me qaramin sauti ta sake tana kai cup din
bakinta,can qasan ranta wani abu yana yawo gami da kai kawo a ciki. Gaba daya ta
manta da rayuwarsa,taso kuma ta gogeshi a babin rayuwar tata gaba daya,to amma data
tuna wani abu,sai take ganin ya kamata ko yaya shima a bashi darasi.

"Ina kika shiga don Allah,ina kika boye hanan?"

"Dukka wadannan tambayoyin basu kamaceka ba,tunda dai gani din na kuma kira ai sai
ka ajjiyesu ko?"

"Haka ne ranki ya dade" Ya amsata da sauri ba tare daya damu da yadda matarshi ke
tsaye saman kanshi tana dubansa cike da qunar zuciya da kuma takaici ba.

"Zaka iya samuna nan da mintuna goma a gaban flavours na gadon qaya?" Ta jefa masa
tambayar tana ajiye cup din hannunta,daidai sanda yaron ya daga labulen falon bayan
ya turo.qofar ya shigo. Washe mata baki yaron yayi,abinda ya sanyata murmusawa tana
miqa masa hannunta dake daure da agogon fatan daya kwanta a jikinta sosai,gefe guda
kuma tana sauraron amsarsa

"Ko mintuna biyar kika ce zanyi qoqarin kawo kaina"
"Yayi,saika qaraso" Ta amsa masa tana dan kauda wayar ba tare data kashe kiran ba.

"Wace tayi kiranka?,ina zaka je?,wallahi baka isa ka fita a gidan nan ba" Sautin
muryar matar ya ratso ta cikin wayar. Lafiyayyen zagin da taji ya fita a bakinsa ya
sanyata datse kiran ba tare data shiryawa hakan ba,ta lumshe ido tana jin yadda
qirjinta yake quntata

"Har yanzu yana nan a yadda yake......har yanzu babu wani abu daya sauyashi"
Kalaman dake karakaina a kwanyarta kenan

"Am sorry.....am sorry" Ta fada murya can qasa tana motsa labbanta.

Sanyin hannun yaron daya taba nata hannun ya sakata bude idanunta.
Har ya qaraso inda take ba tare data ankara ba

"Antyn huda" Ya kira ta da sunan daya saba kiran nata

"Kaci abincin safe?" Ta tambayeshi tana dubansa. Girgiza kai yayi da sauri,sauta
juya gefanta tana masa nuni da doguwar yatsarta

"Dauko wancan plate din ka cinye duk abinda yake ciki na barmaka" Da zumudinsa ya
juya din yana nufar wajen. Zama yayi sosai bayan ya bude yaga abinda ke
cikin,soyayyen chips da ragowar soyayyen qwai,ya fara kaiwa bakinsa yana murmurshin
jin dadin garabasar daya samu.

Qananun surutai da muryarsu tun kafin sukai ga isowa falon shine yaja
hankalinta. Ta kafe qofar falon da kallo har zuwa sanda suka yaye labulen suka
bayyana,yana gaba tana binsa a baya......

*_TURQASHI_*

*_BIGI SAI BIGI_*

*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*

*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*

*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*

*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*

*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*

*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*

*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray

*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*

08032119803

Ko ki lalubeta ta nanπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ

*Instagram handle_incense by kabo daughter*

*Facebook_kabo daughter*

*Twitter_kabo daughter*


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*
PAGE 16
___________________________

*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*

*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*

*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________________




Idanunshi a kanta sanda yake shigowa zuwa cikin ainihin falon da yake
da banbamci da sauran faluka dake gidan. Itama shi take kalla,kaman yadda suma
bambanta a kamanni da mahaifinta haka suka bambanta a halaye da kuma dabi'u.

"Kai....kai,ubanka.....cireshi daga bakinka......tashi!" Matar dake biye dashi a
baya ta furta a zabure bayan shigowarta dakin,idanunta kuma suka fada akansa sanda
yake cin Chip's din hankalinsa kwance. Debe idanunta tayi daga kansu ta maida kan
yaron da ya tsorata sosai saboda yasan halinta,ba shiri ya miqe tsaye har farantin
chips din dake saman cinyarsa ya fadi,tsirarun dankalin ciki da yayi saura ya
tarwatse a wajen.

Gewayesu yayi da gudu gudu zai fice yana matsawa daga wajenta amma duk
da haka bai tsira ba,bayan uwar harara da take narka masa sai data bishi da
ranqwashi tana cewa

"Bansan inda ka dauko kwadayi ba don ubanka,saidai daga can bangaren uban naka,don
mu nan ba makwadaita bane,masu kwadayin ma addu'ar shiriya muke musu.....ba zaka
jazamin masifa ba......cin abincin da aka da kudin haram?,ina zamana lafiya?,to
muddin zaka ci gaba da shigowa dakin nan kuwa sawuna a likkafa zan maidaka gidan
naka uban" Tayi maganar tana daga tsaye tana kallon qofar da tuni ya riga ya fice
daga ita.

Dauke dubanta tayi daga kanta,don gugar zana irin wannan tash ba
kasafai ta fiya damunta ba. Idan d sabo ta jima da sabawa da ita din,ta kuma zame
mata jinin jiki.

"Ni zan fara gaidaki ko kece zaki fara gaidani?" Muryarsa ta dawo da hankalinta
daga duniyar tunanin data fara nausawa. Fararen idanunta ta aza a kansa,mutumin
dake a mazaunin mahaifi a gareta.....wanda ya kamata a ce a yanxun basu da
tamkarshi,koda baiyi ya mahaifin nasu ba.....amma ya zamana ya toshe wani babban
kaso cikin gibi da rayuwarsu zata samu.

Qaramin bakinta ta motsa wanda sauri yakan kira da shegen bakin rashin
d'a da rashin mutunci,da wannan muryartata da sautinta ke cike da sanyi da nutsuwa
tace

"Ina kwana kawu?"

"Lafiya qalau na kwana,sai uban baqinciki da takaicinki dake shirin hallakarmin da
rayuwa" Ya furta cikin hargagi tamkar dama yana jiran ta gaidashinne.
Har yantsu dogon yatsanta yana saman labbanta,yayin data kafe mutumin
data kira a dazu da kawun nata da idanunta,tana dan motsa yatsan nata saman lebenta
tana kuma nazarin fuskarsa furucinsa dama motsinsa.

Ko sau daya bata taba ganin mutunci kima da martabarsa ba......daidai
da misqala zarratin bata taba daukarshi da wani babban matsayi ba......abu daya ta
sani,komai lalacewar fura tafi kashin shanu......komai kashinsa da zabgewa gami da
lalacewar martabarsa a idanunta sunanshi kawunta kuma qani ga mahaifinta.

Maida idanunta tayi ta lumshe kawai kaman yadda ta saba masa a
yawancin lokuta......tasan me ya sanyashi wannan zuwan,wani boyayyen buqatarsa ne
dake a qasan rai da bai samu biyanta ba. Ta tuna haduwarsu ta qarshe dashi a wancan
satin daya wuce. Dama ta sani ba

Please Login or Register in order to submit comment