You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son kukan nawa, yanzu sau nawa za ki ga ina kuka amma ko ki nuna kin gani bare ki rarrashe ni?"

Murmushi ta yi ta ajiye ledar da take hannunta ta zuba mata ido sannan ta ce "Iya bawai kukan naki bai dame ni ba ne. Ni kadai na san yadda zuciyata ke zafi idan na gan ki cikin rashin sukuni, halayen da nake gani a tare da ke ne ba su mini ba, ina matu'kar kaduwa da yadda kike kokarin jefa kanki a rayuwar da ba za ta bulle da ke ba"

Sa'adah da jikinta ya yi laushi amma sai ta yi karfin halin cewa, "Don Allah Inna wai mene ne nake yi wadda bai miki ba?".

Muskutawa ta yi sannan ta ce "Iyah kin san dai ke din nan ba 'yar kowa ba ce, mu iyayenki ba wasu ba ne illa masu neman abin da asirinmu zai rufu, amma ke kina daukar ra'ayin ya'yan masu wadata, ba kya duba idan ba yawan gashinku daya ba, yawan kitson ku ba zai daidaita ba! Watanni kadan ya rage ki kammala makarantarki, kin san kuma aure za a miki amma duk saurayin da zai zo gidan nan da maganar aure za ki yi tsalle ki ce bai miki ba, amma kina son abin hannunsu saboda kawai kin 'dorawa kanki sai kin daura abin da kike gani a jikin yaran da 'karfin iyayenku ba 'daya ba"

Ta nisa tana jiran ko Sa'adah za ta yi magana sai taji sabanin hakan, duk da dai ta lura jikinta ya sake yin laushi fiye da 'dazu, don haka sai ta sake cewa, "Ki ajiye wannan dabi'ar, sannu a hankali idan kina da rabon yin arzikin za ki yi shi ne. Yanzu dai babban misalin da zan miki da yayarki ne, duk da cewa lokacin da aka aurar da ita ba ki da wayon da za ki gane komai, mijinta ko mashin din da kika raina mai hawansa ba shi da shi, amma a yau mene ne bai mallaka ba? A saninki 'kasashe nawa ya debi iyalinsa suka fita? Wace irin hidima da karamci ne ba ya mana ke ma shaida ce tunda dai ko wannan makarantar da kike yi ba don shi ba, da ba ki yi ta ba, da ace farko ta raina matsayinsa da yanzu ta cim ma wannan jin dadin da kowa ke mata kallon tana ciki? Tsakanin ki da Allah ba don ta sau'ka'ka buri ba ta kai wannan matsayin?"

Kai Sa'adah ta girgiza wa mahaifiyarta don kuwa harshenta ya mata nauyi, amma a ranta tana raya in dai akan zaben miji ne an wuce wannan babin, zuciyarta ta riga da ta aminta da MK Bichi kuma shi ma ai talaka ne tunda ko mota ba shi da ita. Jin da'di da son kayan 'kawa kuwa ba mahalukin da ba ya so sai idan bai samu ba, ita a jininta ne son gayu ba wai fariya ko 'karya ta sa a ranta ba. 😀 Don haka ba ta dauki maganar ajiye dogon buri da aka mata nasiha da wani muhimmanci ba.

"Kullum addu'a ta Allah ya ba ki miji nagari wanda zai kula da ke da amana, ke ma irin adduar da za ki rike ke nan. Dauki abinci maza ki ci kar ya gama hucewa, Allah ya miki albarka."

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amin na gode?" Sannan ta ja abincin ta hau ci, danwaken fulawa ne da yaji mai da'din gaske, tana ci tana yaba yadda Innarsu ta iya sarrafa abincin gargajiya masu da'di, kawai dai abincin zamani ne ba ta yin su ko kuma don za su ja kudi ne?

Sai ta tsinci kanta da cewa "Allah Inna na kusa daina cin abinci mai nauyi."

Cike da mamaki ta ce "Me za ki dinga ci to?"

Murmushi ta yi, ta ce "Chips, chicken, sai dangin su pizza, da indomie da kwai, sai na bi bayansu da ababen ruwa irin su juices da yougurt ko hadadden shayi hadin kauri."

Salatin da Inna ta 'dauka ne ya sa ta dakatawa tare da tunanin ta yi subutar baki.

"Ashe duk togaciyar da na gama yi miki bai shiga kunnenki ba? A gidan uwarki kika san wadannan kayan, wadda ba ta alfahari da abin da ta bude ido ta gani a gidansu, sai hangen kayan wani da ba ya rufa maka asiri!
Nasan kina nufin idan kin je gidan miji ne kike tunanin wannan rayuwar za ki yi"

Ta kafe ta da ido tana mata kallo mai tsanani sannan ta ci gaba da cewa, "To saurare ni da kyau aure ya wuce wasa tun wuri ki cire wannan tunanin a ranki, gabadaya aure ibada ne, duk abin da akace ibada ne, to ba son ranka za ka yi ko zaka gani ba, sannan ba abin da ke ri'ke da aure gabadaya sai ha'kuri don haka ki cire wannan tunanin a ranki. ki yi fatan Allah ya ba ki miji nagari, da hankalinki zai kwanta, domin komai za ki samu idan ba kwanciyar hankali ina tabbatar miki ba za ki ji dadinsa ba Allah ya shirye ki, adduar da zan dinga miki ke nan."

Ta fada da iyakacin gaskiyarta, domin ta lura addu'a ce kawai za ta canja mata Iyah ba hantara ko nuna fishi ba.

***

MK yana isa gida ya tarar da Hajiyar Bichi ta zo, a falo ya tarar da su ita da Hajiya Babba suna cin makani wanda ba ya tantamar daga Bichi ta taho da shi, da murna ya hau fadin,
"Hajiya ashe da gaske kike da wuri za ki dawo?"

Dariya ta yi ta ce "Allah Ya yarda ban dade ba".

Suka ci gaba da hirarsu har su Abbas da Ahamad suka dawo aka ci gaba da hirar da su, Maghriba ce ta dakatar da su.

Bayan sallar Isha MK ya tarar da Hajiya Babba a dakinta, ya gama kame-kame da soshe-soshen 'keya, sannan ya ce "Hajiya so nake aje a tambayar mini izinin magana da wata yarinya a wajen mahaifinta."

Dadi ya kama ta, ta shiga fadin "Alhamdulillah! Allah Ya sa abokiyar arziki ce, ina ne gidan nasu?"

Sake kasa ya yi da kansa da kyar ya ce "A babban layin Unguwa Uku suke mahaifinta mai karamin karfi ne amma mutumin kirki ne, na san shi tun kafin nasan yarinyar."

Farin ciki ya bayyana a fuskar Hajiiya Babba ta ce, "Yanzun nan za mu tattauna da Hajiyar Bichi tunda Allah ya sa ta zo garin, gobe In Sha Allah zan je har gidan Babanku Alhaji Isa (Aminin mahaifinsu ne) na shaida masa. Sai ya je ya tambayar maka, tunda ka kammala karatun kuma ka iya harkar kasuwanci ba za mu ji tsoron aurenka ba, bare da ikon Allah da wuri za ka sami aikin yi ka ci gaba da rike mu gabadaya."

Koda ta sami Hajiyar Bichi da maganar fatan alheri kawai ta yi tare da cewa, "Hajiya Babba ai ke ce uwarsa, ni 'yar addua ce!"

Wannan biyayyar da tun fil'azal Hajiyar Bichi ke yi wa Hajiya Babba ta taimaka kwarai wurin samun zaman lafiya a tsakaninsu, tare da saukaka kishin junansu matu'ka da gaske.

A satin aka tambayo masa izinin magana da Sa'adah, a take kuma Baffa ya ce ya bashi damar ya nemi yardarta ba don yana jin tsoron halin dan yau ba, da a take zai ce ya ba shi ita, to tsoron kar ta ce ba ta sonsa ta kunya ta shi yasa ya ce idan har sun daidai ta kansu to ya ba shi, aka yi murna aka rabu ana addu'ar Allah Ya sa hadin Allah ne.

A ranar Baffa ya zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta ya ce, "Bakin da suka bakunce ni a yammacin yau, zuwan Iyah ne. Yaron nan Mutari ne ya turo a ba shi iznin neman amincewarki, ni kuma na ba shi dama ya nemi yardarki ba don Ina jin tsoron kada ki yi mini *HALIN YAU* ba, da kai tsaye zan ce na ba shi su zo ayi maganar aure. Saboda yaron nutsatstse ne , ya san mutuncin manya mai kokarin neman na kansa ne, kullum ya zo shagon askinsa sai ya zo ya gaishe ni, ban kuma taba jin hayaniyarsa da wani ba, kiga dai yadda shagon yake cika dam da matasa amma ban taba jin an ce ana fada da shi ba.
Da shi muke sallar Magariba da Isha kullum yana sahun gaba, ba zan miki dole ba amma da a ce zan miki zabi ki karba, to da ba zan tsallake shi ba. Idan kuma kin kafe shi ma bai miki to lallai ki tsayar da wanda ya miki da zarar kin kammala makaranta zan aurar da ke, ki ri'ke wannan!"




Alkalamin
SURAYYA GWARAM
✍️✍️.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*TALLAH* *TALLAH*!
*KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN*

*⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️*
_NA_
*Jameey yar'mutan kankia*.


*Promo* *Promo* *Promo*


_Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_.

*#300-sau biyu a rana*
*#500 -sau ukku a rana*
*#700 -sau hudu a rana*


_Kiyi ma wanann number magana danjin yanda zaki biya 08160508316_.



*MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU KOFA A BUDE TAKE*
_TUNTUBI_
08032773332.



*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



34-35.



Baffa na rufe baki, Inna ta yi caraf ta ce "Gara ka jaddada mata don ni a halin da nake ciki da ita, ban ki ka kawar mini da ita a cikin wannan watan ba."

'Dan murmushi ya yi mai sauti tare da cewa, "Anya Salamatu ba gaskiyar Iyah ba ne da take cewa kin fi nan nan da Sumayya?"

Da sauri ta ce "Hmm Ni yaushe ma na ga yayar tata bare har na nuna son kan da take korafi? Mafi yawa ai karamin 'da ya fi shiga rai, sai idan halinsa ne marar kyau ko ba ya jin magana".

Ya sake fadada fara'arsa ya ce "Ato ni ma dai na ce ban taba ganin wacce ba ta ririta autarta ba sai ke".

Da sauri Sa'adah ta ce, "Ai ni Baffa Inna ba ta dauke ni a auta ba, ALLAH ne ya mayar mata da ni auta akan dole."

"To ki dinga jin maganar da ake fada miki, ki rage dogon buri, sannan ina sake jan hankalinki akan yaron nan kar ki bari ya kubuce miki."

Ta yi kasa da kanta, nuna alamun kunya, a ranta fadi take "Son sa nake sosai Baffa daina jan hankalina" 😀
Sa'ade ke nan.

Daga haka ya sallame ta ta mike tana fadin "Sai da safe."

Tana zuwa, ta zube kan katifa tana jin wani irin nisha'di na tsirga mata, idonta a rufe wani irin shauki yana mamayar ta.

Can kuma ta fara tunanin maganar Baffa in da ya ce, "Shagon aski! Kar dai The Boss barbing shop?" Duk titin ba katon shago irinsa, shago ne da ya samu karbuwa wurin samari yan kwalisa da kullum suke dafifin zuwa gyaran suma ko yin aski. Ashe shi yasa kwanaki ta gan shi agun? A fili ta ce, "Hadadden guy dan boko da yin aski?"

A take wani sashi na zuciyarta ya ce mata ai ya huce takaicin bani-bani a wurin iyaye da dangi, ya kuma kere sa'a a tsakanin abokai masu jiran gwamnati ta ba su abin yi.

Maimakon ta ji abin alfahari ya yi, ta yabawa kokarinsa na dogaro da kafafunsa, sai ta ji tana jin kunyar ace saurayinta wanzami ne 😁.

Washegari da wurwuri ta shirya ta biya wa Zainab Ma'aji, a hanya ta ba ta labarin yadda ta kaya tsakaninta da MK, murna sosai Zainab ta yi tare da cewa "To ki kiyaye abin da ya ce baya so, sannan ki kama bakinki."

Duk sa idon su Halima ba su iya gano soyayyar da ke tsakaninta da Malamin nasu ba, saboda yadda suka rufe kofar da za a gane akwai wata alaka a tsakaninsu da ta wuce Malami da dalibarsa.
Khalil ne kawai ya kasa gamsuwa musamman yadda ya lura Sa'adah ta yi matu'kar sauya masa, sannan ta toshe duk kofar da suke samu su yi hira, zai mata letter sau goma bai fi ta ba shi amsa daya ba a dukunle. Wannan sauyin da yake gani a tare da ita yasa ya sake kullatar MK yana ganin tun zuwansa makarantar ya canja masa Sa'arsa. Saboda haka ya sake daukar samfurin nuna rashin da'a a gaban Uncle MK, duk lokacin da ya zo ajin sai Khalil ya yi abin da zai harzuka zuciyarsa, wanda hakan ya janyo kiyayya mai tsananin gaske a tsakaninsu, wata rana an fita break ya samu ya yi magana da ita a dalilin ya sa Halima ta tsayar masa da ita, duk tambayar da ya mata idan laifi ya mata ta yafe masa.

Ta ba shi amsa da cewa, "Khalil ba ka mini komai ba, kawai ganin jarrabawarmu ta gabato akwai bukatar mu fuskanci karatunmu ne."

Kai tsaye ya ce, "Zan so wannan dalilin ya zama shi ne gaskiyar magana, amma na san idan na rantse ba zan yi kaffara ba, cewar akwai wani dalilin ba wannan ba. Ni koma mene ne zan yi ha'kurinsa amma idan wannan mugun Malamin is behind your changes, to ba zan yafe masa ba!" Ya fada cike da 'bacin rai.

A tunanin Sa'adah tunda ya turo a ba shi iznin neman amincewarta, an kuma bashi ai zai dinga zuwa zance, sai ta ga an kwashe kwanaki kusan goma bai zo ba, bai kuma sake waiwayar ta ba ko a makaranta, wannan abu na ci mata tuwo a kwarya musamman da a safiyar yau 'yan ajin nasu suka yi laifin da gaba'daya ya zane su, amma da ya zo kanta sai ta ga ya dage iya karfinsa ya zabga mata bulala har hudu maimakon bibiyu da ya yi wa kowa.

Abin ya tsaya mata a rai sosai, sai kawai ta tsiri fishi da shi, ya lura da fishin da take yi amma sai ya share, tun ranar da ya gan ta tana hira da Khalil ya ji gabadaya ya rasa inda zai sa ransa shi yasa da ya samu damar dukan yan class din ya ninka nata dukan!

Ranar wata Juma'a da yamma Sa'adah na zaune a tsakar gida tana yanke farce ta yi kwalliya da daguwar riga ta shadda purple (Mai ruwan Shanshanbale) a lokacin surfani aikin sama ake ya yi, dinkin ya yi kyau sosai!
Innarta sai mita take yi, akan har yau Muutar bai zo ba, ganin Sa'adah ta yi shiru ba tare da ta ce komai ba, sai ya harzuka ta, ta zuba mata ido ta ce, "Iyah ba magana nake yi ba ne kika mini kunnen uwar shegu?"

Tura baki ta yi da ya zame mata jiki cikin yanayin tabara ta ce, "Ayya Inna ni ma ban sani ba fa!"

A tunzure ta ce, "Kin sani Iyah kawai dai kin nuna masa halin naki ne"

"To ni a ina zan nuna masa halin nawa tunda ko a makaranta ma ba kula ni yake yi ba, ni wallahi na fara tantamar shi ya aiko yana so na? Shekaranjiya ba ki ga dukan da ya mini ba."

Jikin Inna ya yi sanyi ta fara wasiwasi tana fatan Allah ya sa lafiya, amma sai ta ce, "Allah ya sa dai ba wani abin ba ne."

Tana rufe baki yaro ya yi sallama ya ce, "Wai ana sallama da Sa'adatu" Da sauri Innar ta ce, "Je ka ce Wai waye?"

Ba a jima ba ya dawo ya ce, "Wai Mukhtar ne." Dadi ya kamata da sauri ta ce, "Je ka ce ta na zuwa."

Ta juya ta ga hakimar ko motsawa ba ta yi ba tana ci gaba da yankan farcenta, kamar za ta yi magana sai kuma ta shanye, tana mai son ganin iya gudun ruwanta.

Fiye da shudewar mintina goma tana zaune ta gama yankewar. Amma sai ta tsiri kankarewa, zuciyar Inna ta hau ba tare da Iyah ta ankaraba, kawai ta ji saukar duka da mafici a zabure ta mike tana dire-diren shagwaba tana cewa, "Me na yi kuma na duka Inna?"

Dakuwa ta mata da hannunta na dama tare da cewa, "Za ki wuce ki dauko mayafinki ko kuwa?"

Ta shige dakinta tana cewa "Daga zuwansa zan debi jiki na fita, ba jan aji ba komai, salon ya ga arhata."

Mahaifiyarta bin ta yi da kallo, jiki a sanyaye ta rasa bakin magana, ta shiga dakinta ta fito da lemon kwalba guda biyu, da Swan roba biyu, da tuni Baffa ya tanada saboda zuwansa, ta zuba mata a kan faranti mai kyau ta ajiye.

Kan dole ta bi ta dakin a zaune ta same ta ta sake gyara fuskar ta yi kyau sosai ga mayafin da ya dace da zaren surfanin dake jikin rigar, kamshin tsadadden turaren Escada sai tashi yake a dukkan dakin! Sassautawa ta yi ta ce, "Yanzu zama ki ka sake yi Iyah? ko ba komai ai malaminki ne, malami kuwa ai kamar uba ne, ki duba fa tsawon lokacin da kika shanya shi yana faman jiran ki?"

Bata ce komai ba ta mi'ke ta fice ta dauki tabarma, ganin ruwa da lemo a kusa da tabarmar yasa ta ganewar iyayenta sun fi ta kambama lamarin MK.

Tabarma kawai ta dauka ta nufi zauren, a tsaye ya jigina da bango ta same shi. Sanye yake da farar shadda kal (Bankole style) ya dora hula ba'ka, kafarsa dauke da bakaken cover shoe. Sallama ta yi tare da shimfida tabarma sai da ya zauna sannan ta zauna ta gaishe shi. Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamshin turarensa na Versace da wanda ta yi amfani da shi Escada suka cakude suka cika zauren da wani irin lafiyayyen kamshi mai nutsar da zuciya.

Tsawon mintina suna zaune shiru, ita kanta a kasa yake tana ta wasa da yatsun hannunta da ta musu kwalliya da zobuna (fashion).

Shi kuma kawai kallon ta yake yi, yana nazarin yadda ta iya tsara simple kwalliya ta burgewa tamkar wacce take karantar fashion and design.

Gani ya yi ta mik'e tana cewa, Ina zuwa." Ba ta jima ba ta dawo dauke da faranti a hannunta ta ajiye a gabansa. Ta koma in da tashi ta zauna.

Can ya nisa ya ce, "Wai fishin ne har yanzu?"

Takaicin sa ya makure mata wuya, tunda ya zo ban da kallon ta bai ce komai ba, sai gaisuwar da ya amsa mata ba karsashi, shi ne yanzu zai ce wai fishi take yi, so yake ta saki baki ta masa hira bayan shi ya kame bakinsa ya tsuke, saboda yana jin isa?

Don haka sai kawai ta daure fuska sosai, sannan ta juyar da kanta gefe ba tare da ta ce ko mai ba.

Dariya ta kamashi ya murmusa, sannan ya ce, "Ke kullum a cikin fishi kike? Da kin san yadda murmushi yake sake kawata miki fuska da kullum kin kasance a cikinsa"

Ba ta ce komai ba, ya yi shiru yana nazarin mai zai ce da zai sa ta kula shi. Ya nisa ya ce, "Babana ya yaba da karbar da Baffa ya masa, ya yi murna sosai har cewa ya yi na iya zaben suruki, yana fatan a ce ke ma ki yo halin karamci irin na gidanku "

Ba ta ce komai ba amma ta sassauta daurewar fishin, yana kula da ita, don haka sai ya sake cewa, "Kin san kafin na zo raina a bace yake da ke amma kina fitowa na ga wannan kwallliyar da aka cancanda mini sai na ji na manta komai! Ke kawai nake gani kin cika ko ina fiye da duniyar gaba'daya!"

Dadi ya kamata ta murmusa kadan, amma ba ta ce uffan ba.

Ya dade yana rarrashi kafin ta ware su yi hirarsu, cikin dabara ya tabbatar mata ai ya gan ta da Khalil suna hira a class shi ne kuma dalilin da ya hana shi zuwa, don Allah ta kiyaye.

Ba ta musa ba, cike da dariya ta ce, "Shi ne dalilin da ya sa ka ninka dukan da ka mini?"

"E, saboda ki ji dan kadan cikin takaicin da nake kwana ina tashi a cikinsa."

Bai tafi ba sai da aka fara kiran sallar maghrib, ya mike yana cewa kawo mini buta na yi alwala.

Tana tsaye har ya yi alwalarsa ya mayar da agogon da ya cire ya zura hannu ya ciro sabbin yan dari-dari da suka sha turare guda ashirin ya mika mata da 'kyar ta karba wanda sai da ya rantse akan sai ta karba, sannan ta sa hannu biyu ta karba, ita kanta a ranta addu'a take Allah ya sa kar ya mayar da kudinsa! Ta ga samu ta ga rashi 😁 a wancan shekarun dubu biyu tana da daraja ba kamar yanzu ba.

Ta kalle shi a kunyace ta ce, "Ka tsaya sai ka rasa sahun gaba, Baffa yana ta cewa kullum a sahun gaba kake sallah."

Dadi ya kama shi tare da cewa, "Ashe har kamfen Baffa yake mini a gunki, lallai ki ce na kwantar da hankalina, na same ki na gama! Amma yanzu ba na iya zuwa wurin da yake yin sallah, kunyarsa nake ji."

"Ta yi dariya sosai ta ce, "To kuma a ina kake yi?"

Ya kalleta yana jin wani irin abu na tsirga masa da sauri ya fice yana cewa, Nan Masallacin bayan layi nake zuwa."
Ya tabbatar sai ya sake alwala saboda yadda ya tsinci kansa cikin yanayi na sha'awa sosai.

Bata lura da yanayinsa ba ta dauka kawai gaggawa yake yi tunda an tayar da sallah, shi yasa bai bari sun yi sallama ba.

Sai da ta yi sallah sannan ta je falo gun Inna ta mika mata kudin da ya ba ta, za ta fita ta ce "Zo ki zauna."

Kusa da ita ta zauna, a hankali ta ce, "Ina fatan dai ba shi da matsala ko Iyah!"
Dariya ta kama Sa'adah ta cije ba ta yi ba, amma sai ta yi nufin tsokanar Innar, don haka sai ta ce
"Ba shi da matsalar komai Inna amma gaskiya ni wanzancin da yake yi ne bai mini ba!" Ta fada a dake tamkar gaske.

Salati sosai Inna take yi tana karawa, amma sai ta taushi zuciyarta cikin lallashi ta ce, "Iyah mene ne laifin sana'arsa saboda Allah? Ai abin alfaharinmu ne duka ace matasanmu sun daina zaman banza, sun daina zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, ke yanzu raina wanzancin kika yi? To bari ki ji tun a lokacin ma'aiki akwai wanzamai, sannan duk inda wanzamai suke mutane ne masu amana masu kuma tsananin zumunci, bare kawai don yana da shagon aski sai ki mayar da shi wanzami?"

Dariyar da take dannewa ta kubuce ganin yadda Inna ta kwantar da murya tana lallaba ta, tana cewa a ranta Inna ta koma lallashi.
A fili kuma ta ce
"To shikenan ki cigaba da addu'a Allah ya sa na ji ina son sa tunda na lura duk ya kwanta muku a rai"

"Ai ni tunda na ji Baffanku ya yabe shi na ji ya kwanta mini a rai, kinsan mijin yayarki ma shi ne ya zaba mata, halayensa da nagartarsa kawai ya auna, shi yasa kema nake so ki masa biyayya kar ki yarda ya kubuce miki".


Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*




*KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN*!

*⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️*
NA
*Jameey yar'mutan kankia*.


*Promo* *Promo* *Promo*


_Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_.

*#300-sau biyu a rana*
*#500 -sau ukku

Please Login or Register in order to submit comment