You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai nima na jira shi, ka riga kasa masa rai, sai kuma ya ga shiru, Ni bama zan iya zama da kai babu shi a tsakanin mu ba, ni ka'dai nasan yadda nake jin yaron nan a zuciyata".

Dadin kalaman ta suka kama Mk ya ce "wato saboda Jawad sai ki barni ni ka'dai, baki damu da halin da zan shiga adalilin rashin ki kusa ba?"

"To idan hakane sai ka yi kokari mu samu visa tare da shi".

Sosai suka sha hira mai cike da 'doki.
A ranar ta nuna masa yatsun kafarta guda biyu da suke a tankware , dan kar sai daga baya ya gano ya ji an yaudare shi, sosai ya sake jin tausayin ta, bai san me yasa yake jin tausayin ta ba tun fil'azal, ya yi ammana wannan tausayin ba zai barshi ya zalunce ta ba.

Har wajen harabar Adana motoci ta rako shi, anan ma sun sake bata lokaci suna hira.


Sai da ya koma gida ya kwanta tunanin ciwon Farida ya zo masa menene (Arthritis?).

Da tunanin ciwon barci ya yi awon gaba da shi, yana karyawa kuwa bai zame ko ina ba sai asibitin kwararru na Murtala, ya samu Dr Babangida Bojuwa abokin kaninsa ne Akil, suka gaisa sannan ya nemi alfarmar ya masa bayanin menene ainihin ciwon Arthritics da hanyar da za'a bi a kula da mai fama da wannan ciwon.

Dr Bojuwa ya yi murmushi sannan ya cire gilashin idonsa wadda yake taimaka masa wurin gani sosai sabanin da mutane suke kallon tamkar na ado ne.

Cike da girmama yayan abokinsa Dr Bojuwa ya ce "Zan maka bayanin da harshen Hausa tunda kai Baban turanci ne, gara na adana turancina da bai fi cikin cokali ba".

Da murmushi a fuskar Mk ya ce " kowa a fanninsa gwani ne 'kanina, baka ga takakkiya na yi domin ka sanar da ni abin da ban sani ba?"

"Hakane yayan mu".

Dr Bojuwa ya ce "A likitance an fassara Arthritics (Ga'ba) da mahadar kasusuwa biyu zuwa sama. Ba iya 'Kashi ke bada abin da ake kira ga'ba ba!
Muna da ga'bo'bi da yawa a jikin 'Dan Adam amma anraba su zuwa manya biyu mafi shara wato masu motsi da marasa motsi".

Dai-dai lokacin Dr ya nisa sannan ya zarce da fadin "(osteoarthritis) wannan nau'in shine yafi yawa yana farawa adalilin kokewar shimfidar kawunan kasusuwan(articular cartilage) wacce take hana kasusuwa gogar juna yayin motsi, daga karshe hakan na janyo sidewar kawunan kasusuwan da kuma curewar su zuwa 'Kashi guda daya.
Wannan nau'in na faruwa adalilin jin rauni a ga'ba ko shigar kwayoyin cututtuka".

"Na'aam" Mk ya furta cike da gamsuwa.

Dr ya cigaba da cewa "sai kuma na biyun (Rhematoid arthritis) mai farawa da kumburin shingen gabobi, wannan nau'in yana farawa da kumburin da ya zagaye gabobi wanda ya ke samar da ruwan gabobi. Daga baya kuma ya cigaba har ga kokewar shimfidar kawunan kasusuwan. Wannan nau'in na faruwa ne sammakon rikicewar Garkuwan jiki har ta kai suna yaki tare da lalata shingen da ya zagaye gabobi wato(synovial membrane).

Cikin nutsuwa Mk ya fahimci Farida na fama da ciwon Arthritics nau'i na biyu wato (Rhematoid arthritis). Dan haka ya ce "Na gode sosai Dr! Na gamsu da bayanin ka, amma me yake kawo wannan ciwon?"

Cikin rashin gazawa Babangida ya ce "zuwa yanzu dai an tabbatar tasirin wannan ciwon ya hada da
GADO- ana iya gadar wannan ciwon idan an samu wani a ciki dangi yana da wannan ciwon ma'ana yana bin jini.
SHEKARU- yawan shekaru na tasiri sosai wurin samuwar wannan ciwo.
MATA-Jinsin mata sunfi kamuwa da ciwon Rhematoid arthritis yayin da jinsin maza suka fi kamuwa da (Gouty arthritis).

NAUYI- nauyi fiye da kima na jagorantar kamuwa da wannan ciwon, da kuma buguwa a gabobi".

Kafin Mk ya yi magana Dr Babangida ya sake cewa "kalubalen da masu wannan ciwon suke fuskanta bayana rad'ad'in azabar ciwon, sun hada da Tankwarewar yatsu, hannu ko kafa, ciwo yayin motsa gaba, kumburi sosai a gabobi, dama daina aikin gabobin gaba'daya".


Mk ya ce "Madallah da hazikin Dr! shin wanne shawarwari zaka bani don kulawa da mai fama da irin wannan ciwon?".

"To shawarar da zan baka kasancewar wannan lalura kusan ta dindince, ma'ana za'a tabbata ne ana s!han magani. Mafi soyuwa a inganta abincin marar lafiya, a yawaita masa cin kifi, a karanta masa cin nama mussaman Jan nama.
Da kuma yawan motsa jiki da shan maganin da likita ya 'dora mai lalurar akan ka'ida, sai kuma rage kiba ga masu ita".

Mk ya mika masa hannu tare da cewa"likita na gode sosai da lokacin ka da ka bani tare da mini cikakken bayanin da na gamsu, ina rokon ubangiji ya yiwa rayuwar ka albarka, ya kara maka ilimi mai albarka, ya sa sunanka ya yi fice a cikin 'kasa da waje".

Babangida ya amsa da cewa "Amin Nima na ji 'Da'din yadda ka nemi bayanin likita, baka tafi kanka tsaye siyan maganin rage rad'ad'in ciwo ko kumburi ba, domin yawan shan irin waddanan magagunan na janyo ciwon ulsa da ma gazawar 'koda bagatatan, ubangiji ya bamu lafiya gaba'daya".

Har wajen ofis din Dr Bojuwa ya rako Mk dan karramawa ga yayan abokinsa Akil, Mk yana ta masa fatan alheri da samun mace ta gari, tare da jinjina fasahar Babangida, yana hakaito sadda yake biyowa Akil makaranta, oh rayuwa gaibu ce, ba wadda yasan me gobe zata zo da shi.

Yana tafe yana tunin bashi da matsalar gwajin rukunin jini, tunda tuni yasan Farida A.s ce yayin da ya kasance A.A basu da matsala, kawai fargabar sa daya ciwon da ta ke faama da shi ance ana iya gadarsa kenan akwai yiyuwar ta haifa masa mai irin ciwonta.
Alatilas zai yi auren nan, ko dan ya nuna mata martanin soyayyar da ta wanzu tana masa ba gajiyawa amma a zahirin gaskiya kaso mai yawa na zuciyar sa da gangar jikinsa gaba'daya Sa'adah suke so, da ita suke son su rayu muddin rai, shi da kansa yasan hukunta kansa yake yi da rashinta.

Yana tu'ki yana ayyano cikakken dirin jikinta bata da rama kamar Farida, duk da a yanzu ta tsiyaye, amma ya yi imani da zarar ta dawo hannunsa komai da ta rasa zai dawo mata tunda zata sami nutsuwa, ga iya girkin gargajiya tamkar Innarta, ga ga gayu, kullum tamkar mai Shirin shigaa gasar kyawawa saboda kwalliya. uwa uba ta kasance mace mai lafiya, A.A ce sannan O positive duk wadda ya san darajar lafiya ya san wadda ubangiji ya hada musu wannan nau'ikan ba karamin ni'imomin ubangiji suke ciki ba.

Kalamanta na karshe ya fado masa wai idan ya sake tura mata kudi ba zai gama da uwarsa lafiya ba! Bai taba ganin inda abin arziki ya zama sharri ba sai a gurin Sa'adatu.

Ba 'karamin bata masa rai wannan kalmar ta yi ba, bayan tasan ita mai laifi ce, ya tsani kaifin harshe, umm

Kusan Wannan bacin ran da ta haddasa masa ya rage masa fargabar auren Farida da yake ji.

Washagari asabar dai dai da 17/09 aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi, da Farida Nasir Torondi.
Daurin auren da ya samu halarta manyan mutanen na Nijer da Nigeria.

Sosai aka yi hidima ta bangaren amarya, duk yadda Farida ta so ya halarci Dinner da zata yi a harabar gidansu ha'kuri ya bata, bai je ba, yana ji a ransa tunda bai yi irin wannan sha'anin a bikin Iyah ba, to yanzu ma ba zai yi ba da yake da shekaru talatin har da tara.

Bangaren Iyah kuwa sai da aka daura auren ta gane Farida ya aura.
Duk yadda ta so yin jarumtar boye yadda auren Farida ya bugeta kasawa ta yi, ta fito daga dakinta, daidai lokacin Baffanta ya dawo daga wurin daurin auren ya ci sabon dinki tamkar yarsa yake aurar wa.

Tana tsaye tana kallonsa , sai kuma ta fara ganinsa bibbiyu, basu ankaraba suka ji tim ta zube a kasa.

Dukkansu suka kai mata dauki, tsawon lokaci ana kanta har sai da aka kira Maman Ema wata kwararriyar nurse ce har ta kai mukamin metron, ita ta dinga dawainiya da ita har ta farfado, tana fa'da musu jininta ne ya yi kasa sosai adalilin rashin samun barci da kuma damuwa da ta sanya a ranta.
Kwana biyun da suka biyo baya ba karamin tsauri suka yiwa Sa'adah da iyayenta ba, domin ba karamin wahala ta sha ba, har zabura take ta kwasa da gudu, gaba'daya ta gigice ta fita a hankalin ta, ba kuma komai ke damunta ba illah matsananciyar damuwa wato (Desperation).

Yadda take zabura da suratai ya matu'kar tada hankalin ahalinta mussaman Inna da ta ke uwa, ansan kuwa raunin uwa akan danta.
Bayan maganin asibiti har rubutu Baffa yake zama da kansa ya ke mata wadda na dangana ne da samun sukunin zuciya.

A wannan lokacin Inna ta kudiri aniyar Mukhtar ko shine namiji tilo a duniya da ya hallata Iyah ta yi zaman aure da shi, to kuwa ita ta Haramta mata shi, wannan abin da ya yiwa Iyah ta tabbatar ya yi tsauri da yawa ya wuce laifinta, ta yi imanin 'yarta ba zata yi zina ko sata ko wani mugun kaba'irar da zai kasa yi mata afuwa ba, ta lura so yake ya susuta mata yarinya ya sa zuciyarta ta buga, tunda shi bashi da asara ya angwance da 'diyar masu kambun susa.

Asalima Inna sai take ganin tamkar so yake ya shafawa Sa'adah kashin kaji. kuma raina arzikinsu ya yi.


Kwanaki biyu suka ragewa Mk ya wuce, ya dauki Farida da hantsi suka je ta gaida Hajiyar Bichi, duk yadda Hajiya take jin dama Sa'a ya dawo da ita, ta karbi Farida da sakakkiyar fuska, yayin da Jawad ya ke ta murnar Malam ya ce zasu bishi Ingila a jirgi da wannan balabiyar Auntin. Dai dai lokacin shekarun Jawad goma.


Kunyar Farida da sanyin ta yasa Hajiya ta dan rage 'kin data ke yiwa auren na su.

A hanyar su ta komawa gida ta ga ya sauka daga kan titin da zai bi ta unguwar su, ya hau wani daban.

Bata ce kala ba, ta zuba masa ido kawai.
Bai tsaya ko ina ba sai a harabar hotel din Tahir.

Jikin Farida ya yi sanyi sosai, ta shiga cikin rudani da fargaba, amma haka ta bishi, har dakin da ya riga da ya kama a safiyar yau, domin taga a aljihunsa ya fito da mukallin daki mai lamba 008.

A dadare ta shiga ta zauna, shikuma ya juya ya fita, ba'a jima ba ya dawo da leda mai dauke da yougurt da gasasshen kifi, sai lemuka masu sanyi hadi da ruwa.

Ka'dan ta dan ta'ba adalilin matsawar da ya mata, shi kuwa da dama yunwa yake ji sosai ya ci, sannan ya shiga ya yo wanka, ya fito daure da tawul iya kugunsa.

Mk da kansa ya dinga mamakin kansa bai yi zaton zai ji sha'awar wata macen bayan Sa'a ba, bai yi zaton zai yi rawar jiki har ya kasa ha'kuri su isa Uk kafin ya tare da amaryarsa ba, amma abin mamaki jiya kwana ya yi yana juyi, rabon da ya shiga irin wannan yanayin ya manta, bai sani ba ko dan yasan bai da wadda ta halatta a gare shi ne.

Ganin abin na neman kassara shi, shiyasa ya murje kunya ya je har gidansu ya daukota da zummar zai kaita ta gaida mahaifiyarsa sannan sisters dinsa na son ganinta sosai.

Sanin mijinta ne yasa ba a nemi ba'asi ko fargabar fitar su tare ba, asalima kyakkawan shiri aka mata, domin turaren da mahaifiyarta ta dinga bin duk wata ga'ba tana shafa mata na alfarma ne, takanas ake yiwa manyan matan da suka amsa sunansu a sanin duniyar kamshi.
Sannan ta bata wani irin tsumi da tunda aka fara aurenta kullum sai ancika mata ciki da shi, akan Dole Farida ke Sha, saboda kasancewarta masaniyar magaganuwa bata yarda da Shan kowanne irin abu da sunan magani ba.

Wannan kamshin ya sake rikita Mk yana jin tamkar wani maganadisu ke jansa ga Farida, shi ka'dai yasan yaddda ya kosa su kadaice.

Duk yadda Farida ta ke da kunya ta yi iyakcin bakin kokarinta ta bashi hadin kai, duk da yadda ta ke cin kwakwa a hannunsa kasancewar ita din cikakkiyar budurwa ce ta daure ya samu nutsuwa sosai.

Koda ya kammala kifa ta ya yi akan cikinsa fatar jikinsu na manne, yana jin nisha'di sosai ya dinga mata addu'a, yana gode ma ubangiji na yadda duk shine ya fara bude matan da ya aura, ya tsare kansa bai taba Zina ba, ubangijinsa kuma sai ya mutuntata shi ta hanyar bashi katangaggun mata.

Zuciyarsa ta buga da ya tuno Sa'a yasan sharrin zuciya ne da yake jin tamkar tana ha'intarsa ne, amma shi da kansa yasan zai yi wahalar gaske ta aikata wannan al'amarin.

Jikinsa ya dinga bari har Farida ta dinga jin barin, saboda yadda ya ke jin wani iri abu da baisan dalilinsa ba, yau gashi da Farida a cikin yanayin da Sa'adah kawai ya ta'ba tsintar kansa a ciki, ko ya take ji a dalilin aurensa yasan idan itace ta yi aure tabbas sai ya kwanta a gadon likita.

A sanyaye Farida ta ce "baka da lafiya ne? jikinka na rawa fa".

Murya a dashe ya ce" farin cikin yadda na same ki ne, duk son ki ne yake kidima Ni"

A ransa kuma fa'di yaushe zan iya fa'da miki abin da ya kidima ni ai ya zama tamkar cin fusaka ne, gangar jikinmu a hade amma tunanina da zuciyata na wani waje daban.

Ita kuma zuciyarta ta yi fari kal har tana ganin sannu a hankali zata iya mantar da shi Gogel kamar yadda Gogel din tasa ya manta da lamarinta a baya.

Yini zur Mk ya yi da Farida bai yarda ya mayar da ita ba sai bayan Isha, wadda sai da ta yi kuka, domin kuwa da murje idonsa zai yi ya kwana da amaryarsa, kafin su tafi ta fahimci mabukaci ne na gaske, domin sai da ya sake yin second round ,sannan yana daukar lokaci yana abu 'daya tabbacin yana da lafiya yana kuma kula da lafiyarsa.

A iya wannan awannin da suka yi sai da Farida ta dinga yiwa Iyah jajen rashin mijin da iya sarrafa mace, lalle Gogel jaruma ce da ta iya shafe wannan lokaci babu zumar da ya 'dade yana lasa mata, ita yau kadai da suka kasance da shi addu'a take yi, da neman tsarin abin da zai rabata da Mk.
Fata take ta kasance da shi muddin rai, zata yi dukkan ladabi da biyayyar da zata dauwamar da ita a zuciyarsa, zata yi ha'kuri da duk wani abin da baya so koda ita tana so, matu'kar zasu samu zaman lafiya , ta kuma rayu da shi, idan har zai iya rabuwa da Gogel tsawon lokaci bai waiwaye ta ba, to ta tabbatar ita idan ta yi kuskuren da suka rabu shafeta zai yi gaba'daya.

Suna tafe yana tuki yana ta mata hira da suke nuni da kololuwar jin dadin yadda ya sameta, ita kuma tana ta murmusawa alamun tana Jin dadin yabawar ta shi, a ranta tana fa'din karatu a Jami'a baya sa mace ta lalace sai idan dama lalatacciya ce.




***

Har Mk ya tafi ba su hadu da Sa'adah ba, domin ko da yaje gidan ana gobe zai tafi, ya fadawa Baffah zai tafi amma nan da sati biyu su Jawad za su bishi, cikin karfin hali Baffa ya yi masa addu'a tare da fatan alheri.

Inna kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar sa, tare da yi masa fatan alheri a aurensa.

Ya jima a zaune bai ji Inna ta hau Kiran Iyah ba, dama ita ce take yin hakan a kokarinta na su dinga gaisawa har a samu ayi sulhu, amma wannan karon bai ji hakan ba, illah shigewa daki da Inna ta yi ta bar shi da Baffah akan tabarma.

Yayin da ita kuma Sa'a tana kwance akan gado tana fama da zugin zuciya duk da dai Alhamdulillah ansamu cigaba kwarai da gaske akan kwanakin ukun da suka shude.

Tana jinsa Amma sai ta ji a duniya ba halittar da bata son gani kamar Mk, tabbas ya wulakanta ta, ya tozarta mafi munin tozarci, hawaye ya dinga silalowa ta gefen kunnenta, ta dinga hasashen me ya Mata na alheri ne, me ya mata na kyautatawa wadda bai cancanci ta ji wannan tsanar da take ji akansa ba, ta gama duk lissafinta ta yi alkalanci, ta yarda a zamansu bai zalunce ta ba, ta kuma gamsu ya kyautata mata, ta kuma gasgata itace ta janyo komai.

Amma kuma hukuncin da ya dauka akanta ya yi tsauri matu'ka da gaske, zargin da ya jefeta da shi ya ketare iyaka, haka nan kin mayar da ita, kafin ya sake aure tozarci ne Babba ya mata, kishi ya daure mata kirji, duk irin alheri da dawainiyar da ya mata har bayan ya rabu da ita a yanzu duk sai ya tashi a banza a idonta, tana jin ba wani alherinsa data sani da zai lullube cin mutuncin da ya mata, a kuma wannan lokacin ta yanke duk wata mu'amala da shi, tana jin idan har ta sake yiwa Mk kallon masoyi, ko kallon Rahma tabbas ta zama asararriya.

Kunya sosai ta hana Mk tambayar Baffah Sa'a! Sai ya buge da sake bawa Baffah hakuri, tare da neman afuwa.

Duk da a ran Baffa ba ya jin da'din yadda yake ganin Iyah adalilin Mukhtar, sai ya ce " Ba komai Mutari, har yau kuma ban kullace ka ba, kawai dai ina son ka ka daina mini kallon wannan matsalar zata lalata amincin da ke tsakanina da Kai, kallon uba kake mini, Nima kallon 'da nake yi maka, har abada mun hadu ga Jawad nan a tsakanin mu".

Jikin Mk ya sake yin sanyi tunda a da cewa yake yi, idan da saura zama a tsakanin ka da Iyah da kanku zaku shirya kanku, bana ji a jikina an rabu kenaan ba, sai kuma yau ya ce ga Jawad a tsakani, kenan Baffah ya karaya ya daina jin zasu sake zama ma'aurata a tsakaninsa da Iyah.

Ya dade zaune Baffa na ta yi masa nasihar ya kula da amanar yarinyar da aka bashi tunda zai dauketa ne ya kaita wata duniyar da ba ta san kowa ba sai shi, sannan ya sa ido sosai akan Jawad kar ya bari ya koyo dabi'un yahudu wal Nasar😀


Da kyar ya mike ya na kallon dakin Sa'adah da fitila a kunne tabbacin idonta biyu, ya tuna idan ya zo gidan ta dinga sintiri tsakanin dakinta da tsakar gida, ta dinga bare bare kenan, ba ita ba hatta mahaifiyarta rawar jiki take yi, ta dinga fa'din Iyah kaza, zo ki kawo masa kaza mana, amma yau duk sun yi likimo tabbacin sun watsa shi a kwandon shara.p

A sanyaye sosai ya bar gidan.

Washagari kuwa ya bi jirgin Mangal air zuwa Lagos daga can ya shiga jirgin arik air zuwa kasar Birtaniya.

Haka Sa'adah ta cigaba da jinyar zuciyarta, tana samun karfin guiwa wurin mahaifanta da Sumayya, domin Baffah da ya ga sun hade masa kai a gidan dole ya ajiye powaer sa ta maigida ya lallashe su da kalmomi masu laushi, da kuma sanin muhimmancin hakuri.

Ya sake fa'da musu ba su fi shi takaicin auren Mukhtar ba, amma tunda shari'a bata hana shi ba, akan me shi zai kullace shi?

Ya rufe da cewa "kuna ganin laifina dan ban roki Mutari ya zauna da ke akan dole ba, alakawari na yi ba zan bada auren 'yata ba sai a inda nasan za ta yi daraja, a farko da yake so ai na bashi, idan kum zaki fadi gaskiya ai ya ri'ke ki da daraja! a yanzu kuma, da baya so, bashi da abin da zan kalla da zan nemi ya zauna da ke akan tilas, hakuri wuya ne da shi, idan aka daure sannu a hankali za'a cimma buri".

Ya nisa ya sake 'daure su da cewa "A zatona Salamatu, da ke da yaran da kika haifa mini da kuma duk abin da kuka mallaka zan yi iko da ku kai tsaye, ba tare da jin shakku ko fargaba ba, amma tunda laifine dan na yi ikon da abin da yake mallakin Iyah ne to ku mini afuwa, Iyah ta bini bashi in sha Allah zan biya a hankali"

Kunyar kalamansa suka kama su mussaman Innah da ta bari hankalinta ya kwace akan wannan lamarin. A ranta ta dinga fa'din babbar jarrabawar da aka yiwa mata kishi ne, domin da yawa Mata sun halaka adalilin kishi, da yawa sun rasa Imani, ubangiji ka tsare mu ka sau'ka'ka mana.

Hakuri suka bashi, Innah ta ce "Ba siyar da filin bane ya ta'ba ni ba, yadda ka shiga cikin lamarin auren ka yi kane kane ne ya kidima ni, amma ka mini afuwa wallahi ban taba jin bin da ya dama mini lissafi irin halin da na ga Iyah a ciki ba, amma Alhamdulillah komai ai ya wuce ina rokon kar Allah ya sake maimata mana wannan wakiar".

Sa'adah ta nisa ta ce " Dayan filin ma na barka maka Baffa tsakani da Allah bana so, tunda na mallakesu ne adalilin Mukhtar. Kawai so nake ka daina nunawa ya fini a gurin ka, sannan ka mini afuwa akan komai ka daina fushi da ni, domin a yanzu Ni Mukhtar ya zalunta".

Ya yi murmushi ya ce " ko Sumayya ba ta fiki ba Iyata, amma ina son ki gane gaskiya ko kuna tare da Mutari ba zan 'ki shiga hidimar auren sa ba, domin ya mini alkairori daban daban da bazan mance su ba, duk girman kuskure kuwa bai kamata Dan adam ya shafawa idonsa toka ya mance alheri ba, nasani hukuncin da ya dauka akan ki ya yi tsauri da yawa, adalcin da nake yi masa shine ban san mai kika yi masa ba, sannan auren da yayi ba zaluntarki ya yi ba, domin kuwa ko kuna tare zai yi aure shari'a ta bashi dama, idan yana so kuma zai iya adalci. Fatana ki kwantar da hankalin, ki yi hakuri in sha Allah komai zai daidaita miki, Na da'de da ya yafe miki Iyah, fatana ki bu'de zuciyarki ki fuskanci goben ki, sai kinyi nazari hadi da tsinkaye masu zurfi sannan gobenki zata inganta, na yarda da nutsuwar ki a yanzu, na kuma gamsu a kame kike dan haka bana fargabar zamanki!

Amma ba ina nufin kita zama a hakan bane, ki bawa masu sonki kofar da za su tunkare ki, domin a hakan kika samu Mutari, yanzu kuma da kika barwa Allah ya miki zabi, ina da yakinin ba zai barki haka ba".


Jikinsu ya sake yin sanyi, suna gasgata maganganunsa, mussaman Sa'adah da take jin karfin zuciya na dirar mata, tana hango ya kamata ta budewa kanta kofofin farin-ciki, zata dawo da kwalliyar da ta da'de da daina yi, sannan zata sake dagewa a makaranta domin a yanzu da Mukhtar ya auri Farida sai take ganin tamkar ya raina arzikinsu ne.










*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.
16/06.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji ta'ba wannan LABARIN ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*Gaisuwa da fatan alheri ga*
*HADIZA TINAU*.
*Ki yi yadda kike so da wannan shafin, farar mai farar zuciya, ubangiji ya yi mana abin da bamu yi zati ba na alheri*


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



89- 90.

Maganganun Baffah sun sake 'karawa Sa'a kwarin guiwar gina sabuwar rayuwar da babu Mk a cikinta.

Tana kwance har tsakiyar dare tana nazarin yadda zata koma sabuwar Sa'adah da bata san Mk ba, ta nisa tana hakaito abubawan da zata nema, bata da bu'katar sutura domin

Please Login or Register in order to submit comment