You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" AMEEN".

sannan suka shiga gaisawa tare da jajanta 'kaddarar da ta fa'dowa yaran su. Jikin Hajiya a sanyaye yake sosai, tunda abin nan ya faru take son zuwa, amma kunya da nauyi sun hanata, sai yau ta yi shahadar zuwa, ha'kuri ta bayar yafi cikin kwando, karbar da ta samu daga iyayen Sa'a yasa ta sake jin nauyinsu ainun, karamci a jininsu yake, tabbas Mukhtar ya yi asarar irin zuri'a me yakana da alheri.

Ganin Baffah ya fita ya Sanya Sa'a dauko Hijabinta ta saka ta shiga falo Jawad na binta tamkar jela.

Daga gefe ta tsugunna, ta gaida Hajiya kanta a 'kasa.

Hajiya ta hau fa'din taho ki zauna kusa da ni Sa'a.

Da rarrafe ta karasa kusa da Hajiyan, amma kanta a 'kasa tana Jin kunyar Hajiya na kamata irin wadda bata ta'ba ji ba.

Sosai Hajiya ke kallon yadda ta lalace ta yi ba'ki sosai, 'kwalla ta cika idonta a sanyaye ta ru'ko ta jkinta, hawaye ya gocewa Sa'a ba tare da ta shirya ba, tana yiwa kanta jajen rashin suruka irin Hajiya! Ta tabbatar samun uwar miji irinta a Yau zai yi matu'kar wahala.

Itama Hajiyar kukan take yi, tausayin Sa'a da Mukhtar da tilon dansu na matu'kar sa ta zubar da hawaye. Wacce irin ba'kar 'kaddara ce ta afka musu haka?

Mussaman yanzu da taga irin bibiyar da Jawad ke yi wa uwarsa, duk inda tasa 'kafa nan yake mayarwa, duk irin gatan da take masa, duk yadda ubansa yake masa siye-siyen kayan wasa da na ciye-ciye kala kala, bai hana ya yi kukan neman uwarsa ba, yanzu da ya ganta kuma ita ka'dai yake bibiya duk kuwa da yasan ubansa na 'kofar gida a zaune.

Duk dabarar Hajiya dan Sa'a ta fa'di musabbabin rabuwar ta su ta 'ki!kuka kawai ta ke yi mai tada hankali, Jawad kuma na ta goge mata kamar yadda ya saba yi mata idan tana kuka.

Tausayinta ya sake cika zuciyar Hajiya, ta dinga rarrashinta da kalmomi masu da'di.

Da zasu tafi Hajiya ta kalli Jawad taga ya ri'ke Sa'a sosai, sai ta yi nufin tsokanar sa ta ce "to zo mu tafi Jawad".

Ai kuwa nan da nan yasa kuka yana nuna dukkan yatsun hannuwansa yana cewa "Malam fa ya ce kwana haka zan yi?"

Hajiya ta yi gaba tana cewa "yi shiru da bakinka wasa nake maka".

Har zaure ta yi wa Hajiya rakiya, Mk na bakin kofar gidan a jingine yana waya, take zuciya ta ayyana wa Sa'adah da Farida yake waya a kofar gidansu.

Hawaye ya sake kwace mata, Hajiya da ta zaci ganinsa yasa ta kuka ta hauta da fa'da sosai tana cewa "wanne irin sakarci ne wannan Sa'a? Kina bada ni, banda bayar da kai menene ba zaki warware ki saki ranki ba, kina kallon kanki a madubi kina ganin irin lalacewar da kika yi?"

Ita dai Sa'a kuka kawai take yi 'kasa 'kasa, Hajiya ta nisa ta cigaba da cewa "ki kwantar da hankalin ki, kin ji!komai zai wuce kamar ba ayi ba, so nake nan da wata daya na ga kin dawo Sa'adatun nan mai birge yara da manya, Allah ya shiga lamarin ki, ya baki miji nagari, da zai wanke miki dukkan ba'kin cikin da kika kwankwa'da".

Wani irin kishi da Mk bai yi zaton zai sake ji akan Sa'adah ba, ya kama shi, takaici yasa shi barin bakin 'kofar ya nufi mota ya shiga yana ta a'uziya, saboda yadda ya ji takaicin Hajiya ya kama shi matu'ka da gaske.

Yana tuki amma zuciyarsa tamkar ta fashe, a gabansa Hajiya ke wannan fatan. ita kuma da ta lura da yadda yake ta 'dacin rai, tunda ta shigo motar ta gane kishi ne ya turnike shi, dan ayiwa matar da ya saka, ya ki mayar da ita fatan samun wani mijin.

Ta dinga kallon yadda ya fusata tamkar kububuwa, Hajiya ta tsinci kanta da mamakin kishin maza, ka saki mace, kace ba za ka dawo da ita ba. Sannan baka son kowa ya aureta alhalin tana cikin shekarun da take bu'katar auren.

Itama haushinsa ya kamata da ya kasance cikin masu son kansu, sannan har ita zai yi wa wannan fishin?.

Dan haka Yana shan kwanar layin 'Dan Hassan da shine layinsu amma a ciki suke sosai, sai an hau abin hawa.

Murya a dake ta ce samu wuri ka tsaya! Bai yi musu ba, ya gangara ya yi parking.

Ba jinkiri Hajiya ta fito cikin sa'a kuwa ta tsayar da dan adaidaita da zai shiga ciki, ba 'bata lokaci ta shiga suka tafi.


Ba'kin ciki ya sake kama Mk idonsa ya yi jawur, ji yake tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, Hajiya da Sa'a su huta da ganinsa.

Yasan Jawad kawai ke da asarar rashin mahaifi, amma ita Hajiya tana da Ahamad, haka nan Sa'adah zata auri wani ya iya mantar da shi a ranta, amma Jawad fa?
Duk yadda yake da tabbacin Abbas da Ahamad har ma da 'Karfi baza su bar tilon 'dansa ya yi kukan maraici ba, ya tabbatar Jawad ba zai rasa uba ba, amma tabbas zai yi asarar rashin mahaifi da ba a samun biyu.

A hankali ya ja motar yabi bayan su Hajiya. Tsawon lokaci yana gurfane gabanta, ita kuma ta yi 'diban karan mahaukaciya da shi.
"Hajiya Dan Allah ki gafarce ni, ban san me na yi miki ba, fishin ki dafi ne a rayuwata, ki mini ha'kuri dan Allah". Karo na hudu kenan yana maimaita wannnan kalamin, ta kalle shi ta ga duk ya sake firgicewa, da gaske tasan yana tsananin gudun zuciyar ta, amma dole ta nuna masa ita ba UWA bace irin Agwagwa ba, yaranta a gaba ita tana binsu a baya. Ita kaza ce da ta ke gaba 'ya'yanta na bayanta, sannan idan ta ga 'da ya yi rashin 'da'a ta take shi ba dan bata sonsa ba sai dan ya zama nagari abin so da kwatance a ckin alumma.


A raunane ta ce "Kai ne da ha'kuri da na yi laifin da zaka iya mini fishi, har yaushe ka yi motar? da zaka dauko ni ka hade mini fuska tamkar wadda ka mini alfarma, ka sani ai ni ba bakuwar mota bace, idan ana sako wadda suka fara mallakar mota a Bichi da kewaye sai ansako gidanmu. sannan tun kafin a haifeka duk inda zani a mota ake kaini, bude ido ka yi ka ga mota a gidannan bare ka mini wani iyashege".

A matu'kar gajiye Mk yake fa'din "Na yi kuskure, ki yi hakuri abin ne yafi 'karfi na, ki mini uzziri Hajiya, ki sake dagewa wurin yi mini addu'a".

Ya Dora hannunsa daidai setin zuciyar sa ya ce, "zuciyata ciwo take mini sosai, tana mini zafi, wataran har numfashi bana iya yi, dan Allah ki yafe mini kar mutuwa ta zo mini kina fishi da ni, zan roke ki, komai na miki, da wadda zan miki nan gaba ki dubi Allah ki yafe mini, Ina rayuwa ne kawai amma wani lokacin bana sanin me nake ciki".

Tausayinsa ya kama Hajiya sosai, ta zuba masa ido tana nazarinsa.ta sassauta murya tace kana son ka warke daga ciwon da keke 'dan'dana, kana son nutsuwa ta zo maka, ka dinga sanin halin da kake ciki, kana son nutsuwar da ta yi maka tutsu ta dawo maka?

Ya ri'ke hannun ta muryar sa na rawa ya hau cewa 'ina so Hajiya, bana iya barci fa, ko abinci da na fara ci sai na ji ya tokare mini a wuya shikenan sai na kasa ci, kuma ina jin yunwar".

Hajiya tace "fada mini laifin da Sa'a ta maka na san shine yake neman kassara ka, rashinta kusa da kai ne yasa kake rasa gane halin da kake ciki domin kana sonta, farincikinka na 'damfare da ita ne".

Bai musawa Hajiya ba domin kuwa yasan gaskiya ta fada, amma sai ya saukar da kansa 'kasa ya ce 'kaddara ce ta rabamu Hajiya".

Cikin rarrashi ta ce "Ni uwarka ce, duk wadda zai ri'ke maka sirrinka a bayana yake, me yasa kake gudun abin da ka ke so da gangan?"

Sai lokacin bacin rai ya sake taso masa cikin fitar hayyaci ya ke firzar da maganganu " Ina sonta sosai, Ina son na rayu da ita, komai Ina yi mata, har da wadda ya fi 'karfina yi mata nake yi, amma kullum cikin zullumi nake zaune da ita, fa'da mini Hajiya me na gaza da ban cancanci na sami kwanciyar hankali da ita ba?".

"Ba ka gaza ta ko Ina ba, itama ai kullum cikin damuwar take tunda kishin rashin hankali ta 'dorawa kanta".

"Yanzu fa'da mini abin da ya kawo musabbabin rabuwar dan nasan irin hukuncin da zanyi, na kuma daina zarginka da manta alheri, da kuma rashin ha'kuri".

"BA KOMAI QADDARAR MU CE".

Ta zuba masa ido ta ce "Ko dai Ni ta zaga ko mahaifinku ko Hajiya Babba?".

A hankali ya girgiza kansa ya ce "Haba dai, ai komin tsiyarta ba ta isa ta mini hakan akan idona, na barta haka salin alin ba, sannan fa Hajiya yadda kike sonta haka take son ki, Ina mata shaida ko giyar wake ta sha ba abin da zan yi mata ta zage ku".

Ta kalle shi tana tuna fa'dar gaskiyarsa tun yana Yaro yana cikin abin da ya janyo masa soyayya a zuciyar mahaifinsa.

"To Ni dai indai ba wannan laifin ba, banga me zata yi ka 'ki yafe mata har haka ba".

Zuciyar Hajiya ta kasa daurewa tace "ko dai kama ta ka yi da wani?"

A zabure ya mi'ke yana fa'din subhanllah! haba dai Hajiya me yasa za ki yi wannan hasashen, har abada Sa'a ba zata yi hakan ba, in sha Allah ba zata yi hakan ba duk lalacewar *HALIN YAU* SA'ADATU ba zata yi hakan ba".







*SURAYYA DEE*
✍🏼✍🏼.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*Fatan alheri ga*
*UMM ASGHAR NOVELS*.
*NOVEL ONLY GROUP*.
*Da dukkan grops din da ake tura wannan labarin ake sharhi tare da fatan alheri, ina ji ina kuma godiya da fatan Allah ya bamu damina mai albarka*.


*Gaisuwa ga*

*Fati Eshaik(Ummu Asghar)*
*Zalhatu Umar(Yayar mu)*
*Hauwa Umar(Mrs Nasir)*
*Zainab Abdullahi(Beneficial group)*.
*Fatima (Maman Aslam)*
*Aunty Ai'nau*
*Hauwa'u Umar Gwaram*
*Balki Sani*.
*Rahma Shu'aibu Kankara*.
*Kulsum Baffah Azare*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



83-84.



Sosai Hajiya ke nazarinsa, sannan ta sami nutsuwa da ya kasance ba abin da shaidan ke kissima mata bane. Dan haka sai ta ce "idan kuwa hakane banga menene mai zafi da ba zaka yafe mata ba, wallahi ta gane kuskuren ta, ka bata wata damar Ina tabbatar maka lafiya lau za ku zauna".

A hankali ya ce "Dan Allah Hajiya na ro'ke ki, ki bar wannan maganar, ki mini afuwa, ki kuma yi mini alfarmar daina yin wannan maganar, kawai fatana ki mini addua".

"To shikenan Allah ya yi zabin alheri".
Ta fa'da jikinta a sanyaye.

Ta bangaren Sa'a kuwa, har lokacin tana yawan 'kiransa a waya ta bashi ha'kuri, ko ta yi text, har ta kai har makaranta ta bishi, ta tsugunna a gaban sa cikin cire girman kai, tana bashi ha'kuri, a irin haka Farida ta fa'do ofis 'din ta tarar da su a hakan, ta juya da mugun sauri tana fa'din "Sorry excuse me"

Ganin da Farida da ta yi mata gurfane a gabansa ya matu'kar dukan zuciyar Sa'a, da muryar kuka ta kalle shi tace "yanzu ita ka ke so shiyasa ka rufe mini 'kofar afuwa ko?"

Kai tsaye ya ce "kinsan ba haka bane ,amma idan haka zuciyar ki ta rinjayar miki to bazan 'karyatata ba! Kar ki kuma zuwa mini nan, idan kina son magana da ni ki kira Ni a waya, Ni Kuma zan zo!amma wannan ya zama shine zuwan ki na karshe if not, zan fa'dawa Baffah".

Da kuka sosai ta isa gida, ta wuce Inna, ta fa'da dakinta, ta kwanta tana rusar kuka mai tada hankali.

Ada Inna ta 'kudiri aniyar duka zata mata, tunda ta fita bata sani ba, to kuwa zata nuna mata dan ta yi aure ta haihu ba ta fi karfin ta ba, bata wuce ta zaneta ba.😀

Amma ganin yadda ta shigo a kidime ga kuka tana yi na fitar hankali sai wanccan alwashin ya bi iska, ta ajiye lagwanin rishon da ta ke gyarawa, ta bita dakin.


Ta shiga! ta zauna kusa da ita, ta sassauta murya ta ce "Iyah Ina son ki gane gaskiya, ki gane sunnar rayuwa, ba komai ne kake samunsa a lokacin da kake so ba, mata da yawa basu sami nasarar auren wanda suke so ba, amma sun yi ha'kuri da wanda 'kaddara ta za'ba musu, suna cigaba da rayuwar su tamkar basu da damuwa.
Sa'banin ke da kin samu cikar burinki, sai dai *HALIN YAU* yasa kin tankwabar da dukkan daukakar da minjin ki ya miki, Ni na haife ki, ko Baffanki bai fini sonki ba Iyah".

Wannan maganganun na Inna ya sake karyar da zuciyar Sa'a, ta kasa daina kuka.

Yayin da Inna ta cigaba da cewa "Sai dai duk soyayyar da nake miki ba zan 'ki fadar gaskiya ba! Na tabbatar ke kika 'kullawa kanki wannan salalar tsiyar, ke Kika biyewa'kawar zuciya da shedanun 'kawaye suka jefa ki a kogin nadama, na shaida Muuutar mutum ne har da rabin mutum!

Abin da nake so ki fahimta 'daya ne, A yanzu dai bae zai mayar da ke ba, na tabbatar da zai mayar da ke da sauri haka, da ya ha'diye abin da kika shuka masa ko dan mahaifin ki!
Ki fuskanci rayuwar ki ta gaba, kin rayu a duniya shekaru goma sha shida zuwa Sha bakwai babu Muutar a cikinta, yanzu ma kuwa dole ki rayu babu shi, idan mutuwa yayi ai dole ki ha'kura bare yana raye, kuna sha'kar numfashi a duniya 'daya".

Cikin rarrashi Inna ta sake cewa"Zan fa'da miki wani abu ki ri'ke shi da kyau, Wannan bibiyar da kike masa ita take sake sawa Yana nesanta da ke, kin yi laifi, kin bashi ha'kuri tamkar yawun baki zai 'kafe, kin yi nadama, nadama ta gaskiya, to ki barwa Allah lamarinki ya miki za'bi, zabin Allah kuwa gaba yake da son ranmu, idan Kika ha'kura kika yarda da kaddarar da ta afkoiki, kika gamsu idan kin samu wata damar baza ki sake maimata kuskuren ki na baya ba, kika gane darasin da rayuwa ta koya miki, ina tabbatar miki Allah ba zai barki haka ba, ko dai ya dawo miki da Muutar da kansa ta yadda zaki fi 'kima da daraja, ko kuma ya baki wani mafi alherin".

Da sauri ta fada jkin Inna tana cewa "na gode Inna dan Allah ki dinga mini addua, ki mini adduar dangana ji nake zan mutu, Ina cikin kunci da ba'kin ciki mai yawa".

A tausashe Inna ta ce kin bar Allah ne, shiyasa ya bar ki, ki yawaita addu'a, ki lazimci istigifari, duk tsaurin damuwa istigifari na wanketa. ki daure zuciyarki,ki daina rokon Muutar akan ya zauna da ke a dole, fadawa Allah damuwar ki yana jin ki".

Da kuka sosai ta ce " To Inna".
sai kuma ta dinga fadin Astagafirillah da karfin gaske hadi da salatin Annabi.

"A hankali za ki yi Iyah, ko a zuci kike yi Ubangijinki ya ji ki"

Bata daina ba, haka bata rage ba, ganin da Inna ta yi tamkar ba a cikin hayyacinta take ba yasa ta fita ta 'kyaleta, tun tana jinta har ta daina ji, ta leka ta ga barci ne ya mata shigar sauri, a fili Inna ta ce Allah ka dawo wa da yarinyar nan nutsuwar ta, Allah ka tausaya mata".

Kwana biyu kullum Inna ke tausarta, hakan kuma ya taimaka gurin rage kaso mai yawa na damuwar ta, dama kuma ganin da Farida ta mata, tana tsugunne gaban Mk ne ya susuta ta, sannan ta sa a ranta soyayya yake da ita.

A 'ko'karin Inna na son ta 'kara nesanta Iyah daga tunanin Mk yasa ta roki Baffa akan ya barta ta tafi Gombe ta yi ko wata 'daya ne, ko hankalin ta ya 'dan kwanta idan tana tare da yar'uwarta.

Ai kuwa Baffa na bude baki yace "Eh ita ta'ki zaman aure sai kuma taje ta zauna gidan SUMAYYA, arasa gane wacece matar gidan a tsakanin su, wata'kila kuma idan ba sa'a aka yi ba, ta koyawa Sumayyan iyashege tunda tana ganin ita wayayyiya ce kuma me ilimi ce, sa'banin Sumayya da tasa Allah da Ma'aiki a gabanta! Ba inda za ta je nan ne dolenta, ba gidan Sumayya ba".

Da 'kyar Sumayya ta roki Baffah ya amince Iyah ta je Gombe amma da sharadin sati biyu zata yi.

Zuwan ta Gombe ya sake sa mata hakurin rashin Jawad da Babansa, duk da dai kullum dare sai ta ji'ka filonta da hawayen takaici da kewa mai yawa.

Daga sati biyu sai da ta shafe wata uku a Gombe, wadda yayi dai-dai da wattanni bakwai da mutuwar aurenta.

Ranar wata lahadi Mk da Mahmoud suka je wurin Baffa, suka gabatar masa da takardar admission din da Mk ya samowa Sa'adah A Aminu Kano college of legal studies (LEGAL KANO). Inda zata yi diploma a fannin Sharia tsawon shekaru biyu.

Kai tsaye Baffah ya ce "Mutari ba zai yiwu ba, ka sani tun tana 'karamarta ban barta ta tafi babbar makaranta ba, aurar da ita na yi, sannan kaima tsawon shekaru bakwai ba ka'dan da ta yi a hannun ka, ba ka sata a makaranta ba sai yanzu?"
Ya girgiza kansa alamun bai amince ba.

Mk ya yi kasa da kai ya ce "Allah shine shaida tuntuni na so ta fara, to makarantar da take so bata samu ba, sai na mata sha'awar F.C.E KANO. Ashe mun makara sai muka bari sai bana, to ga yadda banan ta zo mana ba yadda muke zato ba. Dan Allah Baffah ka mini wannan alfarmar, ka barta taje ta yi ilimi ai yanzu ta yi hankali ba kamar da bane da kake jin tsoro".

"Mutari ka bar wannan maganar dan kuwa bata shiga kunne ba, ba kuma zata shiga ba".

Sai lokacin Mahmoud ya ce " Hakuri zaka yi Baffah! Idan ka gamsu da gaske Mukhtar bai rabu da Sa'a da nufin tozarci ba, to ka bashi dama ta shiga makarantar nan, yadda ya dauke ka, wallahi ko aure bai gitta a tsakanin su ba, shi me yin alheri ne ga ahalinka.

Sosai su Mk suka matsawa Baffa da roko har suka shawo kansa ya amince, zata yi karatun amma da zarar mijin da ya cacanta ya fito neman aurenta to zai katse karatun, domin kuwa yafi bu'katar auren akan karatun. Jikin Mk ya yi sanyi tubus adalilin kalaman Baffah, na farko da Baffa yace ya fi bu'katar auren sai ya ji tamkar gugar zana ya masa, sai kuma kishin da ya ce idan ta sami miji zai yi aurenta.


A satin ta dawo kasancewar har fara karatu a makarantar, ba ta yi wani murna ba, amma dai ta gamsu ta fara karatun shine yafi mata alheri, zuwa wannan lokacin ta fara ha'kura da Mk! duk da zuciyar ta tafi son ta koma masa, ha'kurin na dole ne mussaman yadda Inna da Sumayya suke ta yi mata nasihar hakuri da karbar kaddara.

Ana jibi zai tafi Uk, inda ya samu gurbi a Jami'ar Bhirmingham zai yi digirin digir gir (P H.D). duk akan harshen turanci.

Baya so ya tafi bai yi sallama da Sa'a ba, haka kawai zuciyar sa ke ta azalzalar sai ya mata sallama, kunyar zuwa gidansu yake yi, ta yaya ya saketa, bai mayar da ita ba kuma ya je nemanta, me iyayenta za su dauke shi?.

Dabara ta fa'do masa, dan haka lokacin tashin Jawad a makaranta na yi ya bar koami ya 'dauko shi da kansa bai zame ko Ina ba sai legal. gefe ya samu kusa da masallaci a jikin wata bishiyar darbejiya ya yi fakin.

Ya jima a zaune a mota cikin rashin abin yi, tunda yanzu bata da waya, ko ta Inna ma bata sha'awar ri'kewa dama shi take nacin kira, zuwa yanzu kuma ta yi matu'kar rage 'kiran nasa, duk da dai idan abin ya juyo mata tana kiransa ko text me dauke da kalaman fatan alheri, da tuni akan girman ladan da me yin ha'kuri ke samu.


Ya yi zurfi, cikin tunani ya ji Jawad na cewa "Mami" da 'karfin gaske.

Ya zabura ai kuwa itace ta fito a masallaci sanye take cikin dogon hijab har kasa kalar albasa, ya sha guga, fuskarta dauke da farin glass, ba kwalliya ko ka'dan a fuskarta, sannan zuciyar ta ba sukuni amma sai ta yiwa Mk kyau.

Da sauri ta 'karaso yayin da Jawad ya balle motar ya fice ya nufeta da gudu, ta tsugunna ta bu'de masa dukkan hannuwanta ya fa'da, sakwanni goma suna haka sannan ta dago shi, ta ce "Halan biyo Malam ka yi akan dole, Na ganka da uniform?"

"A a dauko ni ya yi daga school ko gida bai kai ni ba! Ya zarce da cewa "Mami me yasa ba kya daga Ni sama irin yadda Malam ya ke mini?"

Da murmushi a fuskarta ta ce "saboda bani da 'karfi Jawad".

Maimakon ya yi shiru sai ya sake cewa "yau kin rungume ni, amma a gidan Inna ba kya yi mini haka".

"Oh Jawad! to kunya nake ji kar Inna ta ce ban da kunya".

Ya kalleta badan ya gane manufar ta ba.

Mk da ke jinsu ya bude motar ya fito, suka kalli juna, a nutse Sa'a ta gaishe shi.

Ya amsa yana cewa " ya karatun dai ?"
Ta amsa da fa'din Alhamdulillah".

Kai tsaye ta ce "wani abu zaka yi ne anan?"

kai ya girgiza ya ce "sallama na zo yi miki duk yadda nake cikin bacin rai ba zan iya tafiya ban miki sallama ba, jibi idan ubangiji ya nuna mana zan tafi ingilah, Ina fatan za ki yi karatun ki da kyau, Ina miki fatan dukkan alheri a rayuwar ki"
Da ga jin yadda ya ke magana kasan cikin rauni yake yinta.

Ita kuma tuni hawaye ya goce mata, ta yi 'kasa da kanta ta kasa furta ko da kalma guda.

Takaici ke cinta ta ko'ina, tafiyar da ya dinga cin burin dai ita da Jawad zai tafi, har ta yi karatu ta kuma haihu acan sai gashi tafiya ta zo amma ba ita. Kusan kullum sai ta ci karo da abin da ta rasa a dalilin rashin Mk.

Ya nisa ya ce " duk hidimar ki ta makaranta tana hannun Mahmoud, zaki bude account, fatana kar ki tambayi Baffah kome, ke kanwata ce, ko ba ma tare zan miki komai Dan rayuwar ki ta inganta, ina miki fatan alheri a rayuwar ki ta gaba, na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, fatan nima zaki yafe mini inda na musguna miki".


Ta 'dago idanuwanta cike taf da 'kwalla ta ce "Baka mini komai ba sai alheri, ban san wani abi da kai mini ba face mutunci da karramawa, nima ina maka fatan alheri, Allah ya bada sa'a ya tsareka a duk inda zaka samu kanka".

Sai kuma kuka sosai ya 'kwace mata, bai yi yun'kurin hanata ba, domin shi kansa da yake namiji ji yake tamkar ya yi ta zunduma ihu ko a fahimci Halin da yake ciki.
Idanuwansa sun yi jawur tabbacin yana cikin damuwa mai yawa.

Tsawon lokaci tana kuka kafin ya ce "it's okay ya isa haka zuwa yanzu ai kin dan samu relief, kukan ya isa haka share fuskar ki Jawad na kallon ki fa".

Ta dago ta sake kallonsa ta ce "Da gaske ka yafe mini Malam".

Da sauri ya'daga kansa yana fa'din har zuciyata".

Murmushi mai ha'de da hawaye ya subuce mata ta ce " zan yarda ka yafe mini ne, idan har ka mayar da Ni, zan gamsu da gaske ni 'kanwarka ce idan ka mini adalci irin yadda yaya zai yiwa 'kanwarsa na duk girman laifinta ba zai janye jinin da ya hada su ba. Ka mayar da ni zan jiraka ko da baza mu bika".

Ta yi shiru tana shanye kukan da yake son kwace

Please Login or Register in order to submit comment