You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wadda Mk har cikin zuciyar sa yake jin kukan, ya yi shiru yana sauraron kukan, sai ya dinga jin ashe har da kukanta cikin abubuwan da yake kewar su a tare da ita.

Tana rerewa yana tuna sadda take tisa shi a gaba tana masa kukan iyashege ko na shagwaba.

Tsawon mintina biyar kafin ya yi karfin halin cewa "Kinga idan iyakacin maganar kenan tashi ki tafi tunda kuka kika zo yi mini".

Ta shiga goge fuskar ta kafin ta yi 'karfin halin hadiye kukan ta ce "Kai ka ce duk sadda na shirya fa'da maka gaskiya, zaka saurare Ni fa".

Ya zakudo yace "eh na fa'di haka, amma ai ke yanzu bansan gaskiyar ki ba, sau nawa kina canja mini baki, da me zan dogara har na gamsu?"

Ta zube a gabansa kan guiwowinyata ta ce "Billahillazi iyakar gaskiyar kenan ubangiji shine shaidata".

Ya yi shiru! Bai ce komai ba illah fama da yake da zafin zuciya.

Cikin rawar murya ta ce "Ina ha'da ka da girman Allah da Ma'aiki ka yafe mini, ka mayar da auren mu, gobe kafin ka 'daura da wata jibi, na yarda na amince, ka yi auren har ma ka tafi da ita, Ni ka barni anan zan jiraka, na cigaba da amsa sunan matarka shine kwanciyar hankali na! Wallahi tunda ga ranar da ka sake ni Malam har yau ban sake barci da Ido biyu ba, me yasa ba zaka gasgata ni ba?".

"Sa'a ta ya ya zan gaskata ki alhalin ke baki gaskata kan ki ba?
Ke ce kika janyo komai, ke kika cusa mini rashin aminci game da lamarin ki".

Murya na rawa ta ce baka aminta da Ni ba fa ka ce?"

Kai tsaye ya amsa "kwarai da gaske Sa'adatu, menene alakar ki da Khalil da zai baki Agogon gold? kin tattauna da kawayen ki na kasa siya miki wayar da kike so, ke kika san tsiyar da kuka yi , ya mallaka miki kayayyaki masu daraja tamkar ke din yantacciyar mace ce".

Ta rushe masa da kuka tare da ru'ko kafarsa ya kwace da sauri.

"Kar ka zarge ni da abin da baka da tabbaci, kar 'bacin rai yasa ka daukarwa kanka zunubin da ba zaka iya daukarsa ba".

Ya mike da sauri, a fusace ya nuna ta da dan yatsa ya ce "ke kika haskaa mini kofofin zargin ai, akan wanne dalili zai baki Agogon gold?"
Da waya mai tsadar gaske?"

Murya a dakushe saboda da kuka ta ce "English gold ne Malam! Bai kai darajar Dubai gold ko Saudi ba"

"Amma dai me daraja ne? tunda a lokacin ai ba zan iya siya miki ba. Bayan haka me ya hana ki bu'de mini wayar? Me kuke yi da ba kya so na gani, ha'inta ta kawai kike yi Sa'adatu, dama ance yanzu mata ta waya ma suna tura tsaraicin su ga shedanun mazan da basu san darajar mace da kuma aure ba, bare wannan 'Dan iskan yaron da bani da tabbacin aure ne ya kawo shi duniya".

Ya yi shiru saboda yadda kirjinsa ke masa ciwo.

Ido Sa'a ta zuba masa, ta jima tana kallon shi, tana jin wata irin jarumta na shigarta, ido cikin ido tace "wannan dalilin ne yasa ka kasa mini afuwa, ka kasa kallon nadamata, ka kasa yi mini alfarmar cigaba da zama matarka da kuma rayuwa tare da Jawad?"

Ba ja in ja ya sake cewa "kwarai da gaske ai dama na ta'ba fa'da miki, ba zan sake miki uzziri akan dan'iskan yaron nan ba, ashe a lokacin ma abin na ku da tsabta".

Ya zarce da fa'din "dama yanzu ai anfi lalata da matan aure saboda kome aka kwaso kai-tsaye za'a likawa mijinta ya yi ta wahala da abin da ba nasa bane, ko ayi ta masa sharing matarsa hankali kwance, tunda darajar aure ya bata dukkan kariya daga jifan da zai ta'ba mutuncinta dana ahalinta".

Wani irin abu mai tsananin nauyi ya tokare a wuya da zuciyar Sa'a, hawaye mai zafi ya balle mata, ta mike tsaye, ta sake zuba masa ido ta ce "Na gode da dukkan dawainiyar da ka yi da ni har ya zuwa yau, ina maka fatan alheri a sabon aurenka, Ina fatan ko wacece ta kasance abokiyar arzikinka ce".

Kuka ya nemi subuce mata, amma ta sa dukkan dauriya ta danne shi, ta yi shiru, na dan sakwanni goma, sannan ta dora da cewa

"A yau na tabbatar komawa gareka ba alheri bane, domin cikin shekaru hudu ba yan waattani kullum a cikin sallar dare nake, ba abin da nake ro'kar ubangiji sai ya 'kaddara ka mayar da auren mu, duk satin duniya sai na yi azumi biyu, idan na zo buda baki ba abin da nake ro'ka irin na koma dakin ka".

Anan kuma sai kukan ya gwada mata fin karfi ya kwace ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kukan sosai, a zuciya kuma sai ambaton*Hasbunallahu wa Ni'imal wakil* take yi! Ai kuwa ta sami sau'ki sosai .

Yana tsaye yana kallonta yana jin tamkar yasa ruwa da omo ya goge tsatsar da ta yiwa zuciyarsa, Amma ya kasa, ya tabbatar kishi ne ya rufe masa ido, fasa wayar nan da ta yi means a lot to Him.

Kanta na kasan ta bude murya ta ce "Na yarda da kalaman ka na cewa mu kan so abu alhalin sharri ne, haka nan muna kin abu alhalin alheri ne, na gamsu sosai tunda har Kai da ka tabbatar kaine mutum na farko da ya fara taka ta, amma ka kasa kubutar da ni daga sake saken zuciya da na shaidan.

Idonta a soye ta ce "shin ka gamsu Jawad 'danka ne ko kuwa kana tantamar li'ka maka na yi kake ta wahala da shi alhalin ba jinin ka bane?"

Da rawar jiki ya dunfare ta ba zato ta ji ya faskawa bakinta mari mai zafin gaske har sai da jini ya fara fitowa tabbacin ya fasa mata shi.

Cikin gajiyawa da neman sulhu ta ce "wannan shine kawaicin da zan maka na karshe akan 'daga mini hannu da kake yi, kuma dole na tambaye ka, idan shima a Ballagazancin da ha'incin na samo shi, sai ka dawo mini da 'dana ni zan cike masa gurbin uba, tunda dama ai mutum baya rasa uwa sai dai uba, to ka bani shi kawai, domin ba 'danka bane! nawa ne".

Kallonta kawai ya ke da tsananin mamaki, can ya nisa ya ce " Ashe kaifin harshen ki yana nan, ashe rashin arzikin ki na nan fal a zuciyar ki? No wonder na kasa yarda da gaske kin canja, yanzu na tabbatar da na mayar da ke din ma kina wartsakewa zaki 'dora da dibar albarkar da kika saba".

Yana rufe baki ta ce "Ni Iyah Basiru Ado Gogel idan ka mayar da ni ban yafe maka ba, ko da gwal aka yi ka na barka, ai da tun farko nasan kallon fasi'ka kake mini, da ka yi tsararo na bika, wallahi Mukhtar ko zaman mota bana fatan ya sake hadamu balle zaman aure! Idan har ni diyar Malam Basiru da Malama Salamatu ce na barka. Koda kai ne autan maza, idan kuma ban aikiata abin da ka jefe ni da shi ba, to na yafe maka, idan kuma na aikata ubangiji ya bayyana ni, na kunyata na kuma tozarta a idon duniya".

Ta juya ta tafi sai da taje ba'kin kofar barin falon ta juyo, suka hada ido tunda kallonta kawai yake yi, ta ce "ka manta ka sanni domin kuwa daga yau nima na rufe shafinka, sannan hidimar da kake yi da ni ta makaranta ka dakatar bana so, ban bu'katar komai daga gareka, idan kuma har na ji alert din kudi zan mayar wa da Mahmoud, turowar kuma na nufin in sha Allah baza ka rabu da Hajiya lafiya ba".

Ta juya da saurin gaske ta fita, ta bar shi a tsaye cikin mugun mamakin kalaman da ta jefa masa, mafi tayar da hankalin a ciki shine alakanta Jawad da datti, ko makaho ya shafa ya san Jawad jininsa ne, domin komai na jikin Jawad nasa ne, hatta tawadar Allah da Mk yake da ita akan lebansa Jawad na da ita.
Bugu da kari da ta masa fatan mugun alkaba'i na rashin gamawa da duniya lafiya, to ai mahaifiyar ka itace duniyar ka.

Da kyar ya ja kafarsa ya isa kan kujera ya fadi yaraf yana jin tamkar kansa ba a jikinsa yake ba tsabar nauyin da ya masa.

Zuciyarsa ta kuntata sosai, gumi ya dinga karyo masa, fargabar auren da zai yi gobe ta sake nunkuwa, fishin da ya gani a tare da Sa'adah ya sake kassara shi, Anya haka kawai Sa'a ta bar shi kuwa, wanne irin so yake mata haka? Ya dinga tambayar kansa, a cikin wannan yanayin 'Karfi ya dawo ya tarar da shi.

Cike da tausayawa ya ce "Bichi ka dawo da Sa'a itace matsalar ka, Ina jin fargaba kar hawan jininka ya sababa maka ciwon zuciya".

A shake sosai Mk ya ce "Dan Allah 'Karfi ya zanyi ne, ban son auren nan da zan yi, ka taimake ni ka 'boye Ni".

Ido kawai 'KARRFI ya zuba masa amma zuciyarsa sai harbawa take fiye da 'kima saboda yadda maganar Mk take nuni da rashin nutsuwar da mai yin ta yake ciki. Amma ya san ganin Sa'adatu ne ya gigitashi haka, da kansa Mahmoud ya dinga jinjinawa kansa, ya tabbatar Mk na mutuwar son Sa'a amma ya tabbatar bai fi shi sonta ba, kawai girman aminci ke hakurkurtar da shi, sau tari zuciyarsa da tunaninsa na fa'da masa ba haramun bane, ya gwada Sa'arsa kawai, amma da ya tuna girman Mk da tarin sadaukarwar da ya masa a baya, sai ya ji a ransa ana barin halak dan kunya!
A fili Mahmoud ya ce " Ashe dai ni jarumi ne na gaske, Allah ka samu a cikin masu yin soyayya da abota saboda Kai".

Mk da yake fama da zafin da Sa'a ta hada masa, bai fahimci 'Karfi ba bare ya nemi fashin ba'ki kan kalamansa.

Hannuwan Mk ya ru'ko ya ce "ka yi hakuri nasan yadda kake ji, auren Nan na cikin kaddarar ka, ka karbe shi da zuciya daya, ubangiji zai buda maka kirjinka in sha Allah! Fatana dai ka dawo da Ummu Jawad, ka sau'ka'ka muku wannan dambarwar tura ta fara kaiwa bango, bana son a kai matakin da zata janye nadamarta tunda ka ki bata damar da zata gyara kuskuren ta, wallahi yarinyar nan ta gane kurenta, komin sharrin zuciya da mahassadi ansan dai ta nutsu ta fahimci rayuwa yanzu".

Ido jawur Mk ya ce "mumunar karyace baka ga Tijarar da ta mini ba yanzu, sosai ta wulakanta ni tare da yi mini mugun fata, ashe so yana zama tsiya?"

Mahmoud ya fahimci Mk yana cikin tension sosai sai ya kyale shi, ya rasa gane wannan masifar ta Mk, Yana son abu yana cutar kansa, yana cutar Yar mutane, haushin yadda Mk yake wulakanta Iyah yana neman samun muhalli a zuciyarsa.

****
Ikon Allah kawai ya kaita gida lafiya, domin daga gidan Mahmoud ba tasan ya aka yi ta isa titi ba. Haka nan tunda ta hau abin hawa, bata sake sanin inda take ba, sai da Mai adaidaita ya ce "Malama mun iso fa, ta daga kai ta ganta jikin shagon da suke kwatance da shi, a sukwane ta fice yana ta Kiran ta tsaya ta karbi canjinta amma ina, ba ta tsaya din ba, ta dai samu sukunin daga masa hannu alamun ta bar masa.

Tamkar an jefota haka Inna ta ganta ta fa'do, ta shige dakinta ta kwanta ta dinga gunjin kuka mai dafa zuciyar Dan Adam, kuka take yi na kaicon yadda rayuwa bata zuwa mata a yadda ta zace ta, kuka take yi akan kalaman Mk da suke nuni karara kallon mai cin amanar aure yake mata, wanne irin zalunci ne wannan?

A hanzarce Inna ta bita dakin ya zauna kusa da ita, ta dauki kanta ta dora a cinyarta, a tausashe ta ce "Iyah ki daina bibiyar Muutar, ba zai mayar da ke ba, ki fita harkar sa idan ba kina son ni na fita a harkar ki bane, ki fuskanci rayuwar ki, ki bawa wasu dama kafin ya dawo kasar kema ki yi aurenki".

Kuka kawai Sa'a ta ke yi na fitar hankali har da shidewa, sosai hankalin Inna ya tashi mussaman da taga yadda lebunan bakin yarta suka kubura tabbacin an musu dukan zalunci.

Kwalla ta cika idonta ta ce Muutar ne ya dake ki haka? Me kika mayar da kanki ne Iyah? To saurare ni da kyau, kinsan daukan kafafuwan da kike yi kina binsa ba komai bane face Ballagazanci, duk shashancin namiji kuwa bai son Ballagazar mace! Wallahi ba zai saurare ki a cikin wannan halin ba, ki fita a harkar sa, ki manta da shi, ki tattara shi ki watsar, ba shi kadai bane namijin kirki ba, Ina tabbatar miki Sa'adatu akwai wadda suke son ki kwatankwacin son da Muutar ya miki, ki kwantar da hankalin ki, zaki Sha mamaki".

Idonta dauke da hawaye ta kalli Inna da mamakin jin ta ambaci zahirin sunanta, Bata taba jin ta fa'di hakan ba, saboda riko da al'adar ba a fadar sunan uwar miji.

"So nake na manta shi Inna, amma na kasa! fada min me zanyi na huta da azabar da nake ji ta rashin sa"

Ta fa'da cikin rushewa da kuka sosai.

"Ki ji a ranki yanzu ba kece a gabansa ba, da yana sonki, da ya hadaku ku biyu ya aura, hakan ma wani nau'i ne na ladabtarwa tunda komai nasa zai raba muku biyu ne maimakon da, da bashi da komai a gabansa sai ke da 'dan ki, na sani ke kika jawowa kanki komai ya miki, amma ai ya ladabtar da ke, sannan kin yi nadama kin sauke girman Kai kin bada ha'kuri, ya kamata ya yi ha'kuri shekaru hudu yana jan ki a kasa, yanzu kuma zai yi aure tabbacin ya riga da ya sallama ki".

Zuciyar Sa'adatu ta dinga budewa tana fahimtar maganganun mahaifiyar ta, tana gasgata dukkan kalmomin ta, matsanancin kishi da miyagun kalmomin da Mk ya jefata da su sun taimaka wurin narkar da zazzafar soyayya da take masa, sun dakusar da kulafacin ta na son sake zama da shi by fire by force.

Inna ta Kai hannun ta kan leben Sa'a tana jin wani bacin rai na taso mata fiye da kowanne lokaci, akan me zai dukar mata 'ya alhalin ya ce ba ya yi da ita, dan mugunta har ya ya nemi canja mata fasali, sai dai ya makaro domin tana da yakinin ko hakori ya cire mata, ta zama mai wawulo ba zata rasa wadda zasu sota ba, da yawa ma kuwa.

Da karfin zuciya ta ce "In sha Allah Inna na miki al'kawarin bazan sake bibiyarsa ba, ba zan sake rokon ya zauna da ni akan dole ba, ba zan sake masa kallon idan ba shi rayuwa ta bata da amfani ba, na jingine shi, ki taga ni da addu'a Allah ya taimake ni"

Ta fa'da hawaye na gangarowa, da sauri Inna ta ce "da ikon Allah idan kika yi haka ba zaki wofinta ba".


Har dare Mk na murdadawa da bacin ran mugun fatan da Sa'a ta masa, da kyar ya lallaba ya isa gidan su Farida adalilin kiran da mahaifin ta ya masa.

A katafaren mahaifin Farida Mk zaune kan lallausan karfet na alfarma, kamshi na mussaman da sanyin AC ya sake maida falon aljannar duniya, duk juyin da Alh Nasir ya yi da Mk ya hau kujera ya 'ki hawa, hakan ya sake karawa Mk kima a idon dattijon.

Cikin 'kankanin lokaci aka baibaye gaban Mukhtar da nu'ikan abinci da na sha kala kala.

Cikin hikima yake jan Mk da hira har ya zo kan maganar da za su tattauna.

"Ka saurare ni da kyau Mukhtar! Na baka auren Farida ba dan ka nuna sha'awar ka ba, sai dan yadda ka ke da matsayi a wurinta, sannan nima da na ganka na gane tabbas kai din mutumin kirki ne! Amma na yi wani kuskure guda daya, da tun farko ban fa'da maka cewa ita din bata da koshin lafiya sosai ba, duk da lalurar bata hanata komai, amma dai tana tashi akai akai sannan hakkin ka ne a fa'da maka tunda dawainiya mai yawa ce zata sake hawa kanka".


Ya nisa ya cigaba da cewa "Farida tana fama da ciwon gabbai(Arthritis)!
Wanda hakan ke sababa mata kumburar yatsu, da guiwa dama kafafuwanta, daga lokaci zuwa lokaci, an tabbatar mana ba zata warke ba, ma'ana zata dauwama akan shan magani ne, idan har zaka yi shahadar karban aurenta, Ni kuma ba zan gaza da 'dawainiyar maganin ta ba".

Ya nisa yana sauraron Mk amma ganin ko kwakkwaran motsi bai yi ba, ya ce "Ka je ka yi nazari idan kaga da damuwa ko zaka takura, ka yiwa Allah da Ma'aiki ka fa'di gaskiyar ka, sai na maida auren kan 'Dan uwanta da ya 'dade yana sonta tana ki!
Hakan zai fi mini sau'ki da na baka aurenta ta kasa samun kwanciyar hankali da nutsuwa a tare da kai".

Harshen Mk ya yi nauyi ainun, shashen zuciyarsa da ba son auren Farida yake yi ba, ya dinga tsalle yana jin ga dama ta samu, da zai zillema auren cikin kwanciyar hankali.






*SURAYYA DEE.*
✍️✍️

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

Na

*SURAYYA DAHIRU*


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*Gaisuwa da fatan alheri ga* *kanwata*
*Fatima Isiyaku (Baby)*
*Mrs*
*Nasir Auwal Gwaram*
*Na gode da nuna yabar ki kan rubutuna*



*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.




87-88


Mugun fatan da Sa'a ta masa na ba zai gama da Hajiya lafiya ba, ya Fado masa, ya hassalo sosai.

Cike da ladabi ya ce "Ciwonta ba matsala ba ce ina sonta a haka, zan kuma kula da ita da iyakacin iyawata".

Da'di ya cika zuciyar Alhaji ya ce "Ubangiji ya maka albarka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya zaunar da ku lafiya"

"Iyayenta mata suna son zuwa yin jere na dakatar da su, akan sai mun tattauna, nasan baka shirya komai na auren ba, dan haka na gyara maka wani karamin gidana da ke LAMIDO crescent"
Ya ajiye mukulli tare da takardun gidan kusa da Mk.

A nutse Mk ya ce " Na gode sosai Alhaji amma ba zan karba ba, domin zan dinga jin tamkar Ina gidan mace ne, ina fatan kalamina ba zai zama laifi ba".

Sosai Alh Nasir ke nazarin Mk, yana jinjina masa, domin samun irin su da zuciyar su bata zarme ba, zai yi wahalar gaske, saboda yau muna cikin wani irin zamani da ake auren jari.

Da murmushi a fuskarsa ya ce "Mukhtar ina da tabbacin ko a gaban Farida na baka wannan gidan ba zai zame maka na'kasu ba, ba a shaidar 'dan Yau amma na shaidi Farida. Balle ma ni a satin nan na siye shi, ba kuma wadda yasan na siya, da sunanka na siye shi, Dan haka mallaka maka na yi ba aro ba".


"Na gode sosai, Allah ya kara arziki, amma ba zan karba ba, abawa masu son zuwa jere ha'kuri, ba zata tare ba, zamu tafi Uk ne, idan ubangiji ya kaddara mun dawo lafiya, Ina da 'karamin gida a gadon kaya sai ayi komai".

Ganin da mahaifin Farida ya yi da gaske Mk yake yi ba zai karba ba, sai ya bar maganar gida yana 'kudire dole ya masa wani abu na alheri komin dadewa.

Ya ce "idan nace ina son na dauki nauyin tafiyar iyalin naka fa, ko shima baka so?"

Kunya ta kama Mk ya sake yin kasa da kansa domin ya gaji da yin musu ya ce "Na gode sosai, Allah ya kara arziki".


Alh Nasir ya mike yana ta musu addu'a da fatan alheri, tare da cewa "Bari na turo maka ita".

Ba a dauki lokaci ba, ta iso cikin tsadaddiyar abaya baka sai walainiya take yi daga hannun rigar an masa ado da shudin duwatsu, dan haka ta yi anfani da shudin mayafi a maimakon na abayar, ba kwalliya a fuskarta tunda ita ba ma'abociyar adon fuska bace, kawai powder ta shafa sai wet lips sai tsadadden turaren ta na amour amour.

Soasai ta masa yi kyau, sai ya dinga tuno sadda yake zuwa zance wurin Iyah yana ce mata ta yi kyau tamkar balabiyar Habasha.

Ya zuba mata idon da suka yi jah tamkar mai fama da ciwon afolo, alhalin bacin ran da Sa'a ta jefa shi ne yake neman kassara shi.

A hankali cikin sanyin muryar ta gaishe shi ya amsa da karsashi.

Ya zuba mata ido sosai, kanta a kasa tana jin yadda kallon ke ratsata.

A hankali ya ce "ya jikin ki? Ko da yake kin warware, irin wannan kyau da kika 'kara yi tamkar balabiyar Yemen"

Kanta na 'kasan ta murmusa tana jin kunyar sa sosai.

Ya dinga janta da hira, har ta dan sake da shi.

"Na fadawa Dadi ba zaki tare ba, Ni Kinga nan da kwanaki biyar zan wuce, ke kuma da zarar visar ki ta fito, sai ki bini, abar maganar jere tukun yanzu".

"Allah ya nuna mana"
Ta fada a hankali.

Suka yi shiru. Na dan gajeran lokaci, Farida ce ta katse shirun ta hanyar cewa "Dadi ya baka aure ba tare da ka ce kana so ba anya ba'a takura ka ba?".

Tausayinta ya sake shiga jikinsa sosai! a hankali ya kira sunanta ta dago suka zubawa juna ido tsawon sakwanni, Farida ce ta yi karfin halin janye idanuwan ta saboda yadda take jin sonsa na sake dafa duk ilahirin jikinta, yadda idanuwansa suke a jirkice da kuma yadda suka yi ja sun sake jefata cikin matsanancin so.

Murya ba amo sosai ya ce "Na yi mamakin da kika yi tunanin aurenki zai zamo mini takura!
Tun yaushe muke soyayya da zaki ce na takura?"

Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "kafin shigowar Gogel cikin rayuwar ka nasan muna soyayya, amma bayan ta shigo sai ta kashe tawa soyayyar".
Ta fa'da cike da rauni sosai.

Idan gaskiya zai fa'da yasan ba 'karya ta yi ba, amma dan ya faranta mata sai ya ce "Ba mutuwa ta yi ba dogon suma kawai ta yi, saboda ina ganin bani da halin da zan zo neman aure wannan gidan, Amma da yake ubangiji yasan yadda na ke sonki sai ya 'kaddara mini samun ki a lokacin da na cire rai, idan kinsan farin-cikin da nake ciki da baki yi wannan tunanin ba".

Ya nisa ya ce "tunda da bakinki kika sako maganar Sa'adah bari na fa'da miki wani Abu, kin san yanzu bama tare, amma idan ubangiji bai karar da zaman mu ba, zan dawo da ita, kar hakan ta faru a gaba ki ji a ranki kin gaza ne, sosai nake sonki Farida, sannan ba zan boye miki ba itama ina sonta, kaddara ce ta rabamu, Ina fatan wannan ya zama na karshe da za ki sako mini maganarta mussaman akan ina sonta ko saboda ita na rabu da ke a farko, an 'kadddara mini sai na fara aurenta ne kawai".

Sosai ta fahimice shi ta kuma gasgata shi, duk da ta ji fargabar da ya ce zai dawo da ita, ba dan ba ta so ba, sai dan kishin da kowacce mace ke da shi akan abin da take so, dan ma ta yi sa'ar na ta kishin mai sauki ne saosai.

Ta katse maganar da cewa
"Ya Hajiya da Jawad?"

My 11 amsa mata suna lafiya.

Ta sake fa'din"kun je anyi masa passport din?"

"Anyi masa sai dai da alamu visar ki zata riga tasa samuwa, kawai idan ta ki ta zaama ready, zaki taho ne, shikuma Mahmoud zai taho da shi nan da wattanni uku".

Yana rufewa ta ce "wallahi ba zan iya ba, kafata, kafarsa, sai

Please Login or Register in order to submit comment