You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata.
Ta nisa ta ce "Har gaban abada ba zan ri'ke waya ba, ba zan sake mu'amala da su Halima ba, sai abin da kake da dama shi zaka yi mini Dan Allah kar ka tafi ka barni a haka".


Ya nisa yana jin wani irin abu ya shake shi, ya ce "Sa'adatu ki barwa Allah ya mana zabi kin ji, ina son ki har yau, idan 'kaddarar zaman bata 'kare ba ubangiji zai sake hada mu, amma ni yanzu fatana ki cire damuwa a ranki, ki fuskanci karatun ki, shi zai taimake ki a ko ina zaki samu kanki, duk abin da ya taso miki ki fada mini kai tsaye ki ji tamkar Nima Sumayya ne a gurin ki".

Ta kasa yin magana sai goge fuskar ta take duk ta bata Hijabin nata, haka ya shiga mota suka tafi Jawad ya yi lakwas, ya zama marar kuzari adalilin Halin da ya ga uwarsa a ciki.

A hanya ya dinga fa'din"Malam sai yaushe Mami zata zo ta dauke ni, mu koma gidan mu, me yasa kullum sai ta yi kuka? ko abinci bata ci sai Inna ta zauna kusa da ita, me take yi anan din?"

Ya 'kasa bude Baki ya amsa masa, ganin da Jawad ya yi bai kula shi, yasa shima ya yi shiru dan yasan idan ya dame shi zai mammake shi ne.

A kofar gidan Hajiya ya ajiye shi, ya juya karban wani sakon, sukuku Hajiya ta ga Jawad ya shigo Mata, ta dinga tambayar me ya same shi a Ina kuma ya Da'de ?.

Ai kuwa ya marairaice ya ce "Mami ce take ta kuka".

"A ina ka ga Mamin?"

"Malam ne ya kai mu, tana wani waje babba har da masallaci, tana ta kuka, tana ce masa ya mayar da mu gidan mu".

Jikin Hajiya ya mutu ta ayyana idan Mukhtar bai yi taka tsan tsan ba zai jefa 'kinsa a zuciyar 'dansa.

Wacce irin zuciya ne da shi haka mai tauri bata sani ba, kana son mace kana bibiyar ta amma ka kasa yafe mata ko dan kaima hankalin ka ya kwanta?.

Haka da ya zo ta dinga masa fa'da akan lalle ya mayar da Sa'a, amma ya kafe akan ta cigaba da addu'a abarwa Allah, ta yi shiru ta fara wasiwasi ko jifansu aka yi, ko aljana ce ta shige shi, tunda matsalar kin auren a gunsa take.

Haka ya tafi kasar ingila ya bar Jawad a hannun Hajiya.

Kuka ba irin wadda Sa'a bata yi ba dan kuwa tafiyar sai ta sake dagula mata lissafi, sati guda bata zuwa ko makaranta, har ta kai tausayinta sosai Inna ke yi, saboda ta gane sosai Iyah ta yi nadama, amma Mukhtar ya rufe 'kofar sulhu, duk da har a lokacin bata kullace shi ba.

Zainab Ma'aji da ta kammala karatunta tana bautar 'kasa ita take ta jelan zuwa tana jinya ha'di da ban baki har ta fara samun sukin jiki da na zuciya.

A wannan lokacin Sa'adah ta gane Bata da 'kawa ta amana irin Zainab domin ta nuna mata kauna ta gaskiya, ta tsaya mata a sadda ta shiga taskun rayuwa, yayin da su Halima da Safina har yanzu da ta shafe watanni masu yawa a gida basu waiwaye ta ba.

Haka nan ko a group din su na old girls basu ta'ba jajenta ba, dan tana yawan tambayar Zainab ko ta ga sun neme ta, amsar dai itace basu yi ba.

Ganin Mk ya bar kasa yasa Baffa amincewa da shawarar Sumayya da ta bayar na asiyar da kayan furniture's din Sa'a, a waccan lokacin kin amincewa ya yi, yana tunanin ko Allah zaisa su daidaita kansu, sannan kuma ai ba su suka yi kayan ba.

Tv da freezer kawai suka bari sai set din gado daya da katifarsa, aka hada kan kudi akaje can kauyen Alu gaban unguuwa uku aka sai filaye a jere guda biyu, bayan ta siyar ta zobenta daya aka cika kudin, tunda ba kamar yanzu bane da komai ya yi tsada.


*Shekaru uku a gaba*


Zuwa wannan lokacin kome ya lafawa Sa'a, sai dai damuwar zuci wadda karfin imani ke sawa ayi harka sosai har aga kamar mutum ba shi da damuwa
Sau daya Mk ya zo yayi sati uku ya koma

Ta kammala karatunta na diploma, ta yi jarrabawar D.E. don 'dorawa da karatun digiri a Jami'ar Bayero, duk da Baffah bai sani ba jira suke a samu admission din sai asan yadda za'a bullo masa, har yanzu kuma Mk ke dawainiya da ita duk da ba kasafai ma suke waya ba, Dan har yanzu ta'ki rike waya sam, amma duk karshen wata zata ji alart na kudi a wayar Inna tunda da layin ta bude ko mantawa ba ya yi, hakanan duk karshen wata Hajiya ke kawo mata Jawad da kanta yayi kwana biyu, idan kuwa aka yi hutu gaba'daya a gun uwarsa yake yinsa.

Ba wata wahala ta sami admission a B u.k kasancewar ta dage ta fito da sakamako me kyau a diplomarta hakanan jamb dinta ta yi kyau.

Wannan karon Sam Baffa Bai tirje ba saboda ya yadda iya a nutse take, sannan idan ba makaranta ba ko kofar gida bata fita, haka nan idan antashi bata tsaya ko Ina gida take Yi, hanyar ta daya tamkar tururuwa.

Sai dai a ranar da zata fara zuwa Jami'ar Bayero, a tsakar gida a gaban Innah Baffah ya ce "Iyah kina karatun nan ba dan ina so ba, na so ace daga gidan mijin ki, kike wannan karatun amma na yarda ki yi, domin na gamsu alfaninisa yawa ne a rayuwar ki da dukkan wanda ya shafe ki, ina fatan yaddda na barki kike karatun ki ba dan ina so ba, sai dan rayuwar ki ta inganta, Nima wataran zaki mini abin da nake so ko da bakya so, sai dan kin san ba zan miki sanadin shiga wahalar rayuwa ba".


Kai tsaye ta ce "In Sha Allah Baffah, bana fatan na fifita son raina akan na ka, bana fatan ranar da zaka ce na yi wani abu na bijire maka".

Ya dinga mata addu'ar samun Nasara a dukkan al'amarin ta.


Ba abin da ke gabanta sai karatunta, bata saurarar kowa, haka nan bata da kawa saboda ta ga illar kawance, tsakanin ta da abokan karatunta, gaisuwa da tattauna inda ba'a fahimta ba, amma ba kawance ba, ta riga ta fita harkar 'kawance duk da dai tana da kawar arzikin wato Zainab, sai dai bata san wacece zata sake zame mata kamar Zainab din ba,wadda a da raina Zainab din take yi, tana mata kallon bagidajiya, ashe itace Bagidajiyar bata fahimta ba sai da komai ya kubuce mata.


Ta fara karatunta daga aji biyu a Jami'ar Bayero duk dai a fannin Sharia, dan haka a old side take lectures din ta.


Second semester a year three dinta Mk ya kammala karatunsa, sai dai Jami'ar Bhirmingham din ta ri'ke shi tsawon shekaru biyu inda zai koyarwa masu degree na farko.

Ya dawo gida, ya yi hutun wata guda tunda sau 'daya ya zo Nigeria. Zuwa wannan lokacin Mk ya murje, ya goge fatarsa ta goge farinsa ya sake fitowa, gaba'daya ya canja, ilimi da gayu sun sake kama shi, Yan mata sai kai masa caffa suke, tunda ga dalibai har abokan karatunsa, bakake da fararen ingila.

Haka anan gida Nigeria ma bai huta da Yan mata masu ui masa kutse cikin shafukan sa na yanar gizo ba.


Al'amarin mata ya tsorata shi, wadda ya so, son da baisan iyacinsa ba tasa tsoron mata yake yi, gaba'daya, wahalar da ya sha a soyayya tafi da'din ta yawa shiyasa ya juyawa soyayyar baya, tsawon shekaru hudu haka yake gudanar da rayuwar sa, sai soyayyar Sa'adah da ke makale a kasan ransa.

Da Farida kawai yake dan gaisawa sama sama saboda nauyinta da yake yi, wadda yanzu ta kammala karatunta tana aiki da asibitin Nasarawa.

Har gida ya zo ya gaida Baffa tare da tsarabar yadi da turare da liptons masu yawa na Ahamad tea.

Sosai suka yi hira, haka nan ya shiga ya gaida Inna itama da tata tsarabar.

Ta dawo makaranta sanye cikin Hijabinta kamar kullum, suka yi kicibus da shi ya fito a gidansu, Jawad ya kawo, tunda ya zo basu hadu ba adalilin kullum tana makaranta, yana son ganin ta amma ya rasa yadda zai yi tunda har ya zuwa wannan lokacin ta ki ri'ke waya.

A zaure suka gaisa ya lura da yadda ta samu cigaba a nutsuwar ta, haka nan da alamun ilimi ya fara bin komai nata, kawai yadda ta kankace ta sake zama Yar karama ne ya bashi mamaki, ba alamun kwalliya a tare da ita amma fes take ba ta da makusa.

Ta kalle shi ta ce "Malam ka canja, ka sake girma, idan ka shiga cikin turawan sajewa kuke yi da su ko?"

Ya yi dariya baice komai ba, ya sake kallon ta ya ce "ke kuma kin zama Yar karama tamkar ba ke ce uwar Jawad ba".

Ta yi kasa da kanta bata ce komai ba, amma a ranta tasan rashin sa shine dalilin tunda kullum zuciyar ta ba Da'di

**

"Ba fa za ka koma wannan kasar da sunan aiki ba, ka yi ta zama ba aure kenan, muma nan kasar ai ana bu'katar irin ku"
Hajiya keta wannan fa'dan yayin da Mk ya yi shiru, ita kuma so take ya mayar da matarsa ko sati guda suyi tare sai ya yi tafiyar sa tunda ba zai yiwu ta bar karatunta ba.

Amma tana fara maganar ya hade fuska iya fuska, jikinta yayi sanyi, daga karshe ma sai ga Alh Isa ya zo mata da maganar ai ya samu yarinyar da zai aura, za'a daura auren kafin ya tafi, daga baya zata bishi idan Jawad ya samu visa.

Girman Alh Isa ya hana Hajiya cewa komai saboda kawaicin kar ta nuna masa iyaka akan Dan amininsa, wadda tunda maigidan nasu ya kwanta dama , Alh Isa Bai taba juya musu baya ba, yana tsaye akan almarinsu dana 'yayansu.

Ba'kin ciki a zuciyar Hajiya tamkar ta fashe kan dole Alh Isa ya hakurkurtar da ita tare da nuna mata aure kaddara da rabo ne, shi kansa Mukhtar din har ya dira a kasar bai san zai yi aure ba.

Al'amarin ya faru ne, da ya samu labarin rashin lafiyar Farida a bakin aminyar ta Rukayya Mustapha.

Bai yi kasa a guiwa ba ya je asibitjn data ke kwance da niyyan dubata, ai kuwa mahaifin ta yana asbitin suka gaisa, Farida ta gabatar da shi tare da cewa "Dadi yau ga Uncle Mukhtar a gabanka".

Ai kuwa budar bakin Dadi sai cewa yayi "madallah da Mukhtar ganin ka yau na ji ka shiga Raina Kamar yadda ka shiga ka kwanta a zuciyar 'diyata, na gode da alherin ka, ka turo mini waliyyan ka, na baka auren Farida ba tare da neman komai daga gurinka ba".

Daga Farida har Mk abin ya zo musu tamkar saukar aradu, barin Mk da yaji tamkar mummunar kaddarace ta kawo shi asibitin, ba dan ba ya son Farida ba, sai don bai shirya aure a yanzu ba, bai shirya aurenta ba, a yanzu da ya gama sanin kansa ya fahimci mata masu duhu sunfi burge shi fiye da farare 'Kal, yana jin tsoron kar ya kasa yi mata adalci, tunda yasan ba karamin so take masa ba.


Cikin hikima irin ta manya Alh Nasir ya tisa Mk a gaba ya bashi lambar Alh Isa a matsayin Babansa dan su Baba umaru sama sama suke da shi adalilin sakin da ya yiwa Sa'a sun kuma lashi takobin matu'kar ba Sa'a zai dawo da ita ba, ba za su sake neman masa aure ya kunya ta su ba.

Cikin cire girman kai mahaifin Farida ya gaisa da Alh Isa ya zarce da cewa "yaron ka na bawa matar aure amma na ga tsoron tunkarar ku da maganar ya ke yi, shiyasa Ni na gabatar maka da maganar, na fada maka cewar nutsuwar danka ta sa na bashi kyautar 'yata mafi soyuwa da fatan zaka karbar masa".

Matu'kar mutum yasan daddako wa za'a yiwa haka ya ce ba zai karba ba?

Jikin Alh Isa ya mutu ya ce "kyuatar dan mutum ba mahalu'kin da za'a bawa ya tankwabar mun gode zan zo in sha Allah da kaina zan zo na karbar masa na kuma yi godiya.

Washagari Alh Isa da Mk suka tarar da Baffan Sa'a suka masa bayanin Halin da ake ciki, idan ya ce bai ji rashin da'di ba ya yi 'karya, idan ya ce bai so Iyah ce zata koma 'dakinta ba yayi karya, hakan nan idan ya ce mahaifin Farida yasan ciwon kansaa Nan ma bai yi karya ba.

Amma ko dan ya ramawa Mk kadan cikin alherin da tunda yasan shi yake masa ba gajiya har yau yasa shi cewa "madallah jibin idan za ku tafi ku biyo ku dauke ni da ni za'a je neman aure tare da godiya ina fatan alheri tare da fatan ta kasance abokiyar arzikin ka ce".

Kafin jibin kuwa sai da Baffa ya siyar guda cikin filayen nan wadda kudin daya ya zarta kudin duka biyun sadda aka siya, sosai gurin ya yi daraja adalilin anata gine gine. Dubu 'dari uku da talatin aka siyar.

Da daddare ya Kira Mk ya danka masa dubu dari biyu akan ya bawa Alh Isa dan akai gidan su Farida.

Kunya ta kama Mk ya ki karba, ai kuwa Baffa ya rantse sai ya karba sai idan ya raina me ko yana ganin bashi da arzikin da zai masa alheri.

Da sauri Mk ya sa duka hannunsa ya karba yana cewa "Haba Baffa, mahaifana ne kawai suka mini alheri sama da kai, har yau kuma banga dattijon arziki sama da aki a idona ba gani na yi na doara maka nauyi mai yawa Baffa! Ina rokon na raba biyu na dauki rabi".

"Duka na baka Mutari sadaki ne haka nake so ka bayar dan su san iyayen ka sun san alheri, ko da sunce basu bu'katar komai daga garemu dole ka bada sadaki, burina ace na biya maka fiye da haka, ban son Alh Isa ya gane ni na bada kudin shiyasa na baka a hannunka da sai munje zan bayar, sannan shine wakilinka dole shine mai bayarwa".

Zuciyar Mk ta karye ya yi kasa da kansa yana jin hawaye na Shirin zubowa.

Haka kuwa! Da Baffah aka kai kudin auren Mk akasa 'daurin aure sati mai zuwa, tunda ba tarewa zata yi ba, sai sun dawo, can ingila zasu tafi.



Har zuciyar Alh Isa yake jin rashin da'di, har jinyar kwana biyu ya yi adalilin kunyar Malam Basiru da takaicin Mukhtar.

Haka kuma Mk da yake jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige dan tsananin kunyar Baffah.









*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺


Na


*SURAYYA DAHIRU GWARAM*.


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*Comments din ku na sani nisha'di kwarai da gaske! Na gode muku ubangiji ya bamu damuna mai albarka*.


*Gaisuwa da fatan alheri ga dukkan yan KUNGIYAR LAFAZEE WRITERS*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*



85-86.


Murna wurin Farida tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta godewa Allah, ta godewa mahaifinta Ashe da gaske yake da ya ce sai inda karfinsa ya kare wurin nemo mata farin cikinta. Ta tuno sadda Mk ya auri Sa'a irin kukan da ta yi a kirjin mahaifin ta, yana lallashinta da kalmomi masu da'di, tare da al'kawarin matu'kar yana raye sai ta auri wadda ya fi Mukhtar, ko kuma shi Mukhtar din kansa. A wanccan lokacin bata gasgata ba, kawai ta dauka saboda ya kwantar Mata da hankali ne.
"Wa yake da uba irin nawa?" ta furta a fili, hawaye na zirarowa wadda ta tabbatar sune na karshe akan rashin Masoyi.

Sa'a kuwa ba tasan me yake faruwa ba, har sai da auren ya rage kwanaki uku, Zainab ta gano musu a group, da farko bata gasgata ba, amma da yake Rukayya Mustapha aminyar Faridan suna dan gaisawa da Zainab sama sama tunda duk class mate ne, anan ta tabbatar jibi Uncle Mk Bichi zai angwance da Farida Torondi.

Hankalin Zainab ya kasa kwanciya, a gigice ta tafi gidan su Sa'a amma da ta lura Sa'adah bata san mai yake going ba, sai ta fasa fa'da dan kuwa be kamata ace a bakinta aminiyarta zata ji wannan ba'kin labarin ba.

Tasan da tana da waya da ta ji.

Baffah da kansa ya fa'da wa Innah da Iyah auren Mk, ba Sa'a kawai ba hatta Inna kuka ta fashe da shi mussaman da ya tabbatar musu ya siyar da fili daya cikin filayen Sa'a ya biyawa Mk sadakin auren.
Sosai suka tayar masa da hankalin sa domin irin kukan da suke tamkar ance Sumayya ta yi mutuwar fuju'a ne.

Har cikin ran Inna take jin wani irin azabben kishi na ratsa ta, bata
san kishi ba sai a ranar tunda ta wanzu ita kadai ne a wurin mijinta
A kuma ranar ta fara jin tsanar Mk irin wadda bata yi zaton zata yi masa ba.

Kuka na fitar hankali Sa'adah take yi 'karshe ta dinga kelaya amai ta hanci da baka. Hankalin Inna da Baffah ya yi tashin gauron zabi.

Ranar Inna a wurin Sa'adah ta kwana karon farko da ta bar mijinta shi ka'dai alhalin suna gida 'daya.

Sosai Inna ta ke jin takaicin Baffah a ranta, idan ba zai yi kishin 'yarsa ba, menene zai siyar mata da kadararta ya bawa tsohon mijinta kudin dan yayi aure, babbar damuwar ba wai Rashi ne yasa akayi hakan ba, kawai dan ya nunawa duniya har da shi a cikin masu musgunawa farin-cikin Iyah.

Washagari da rashin kuzari ainun Iyah ta tashi, babban damuwarta ta ga Mk, ganin Inna ta shiga wanka yasa ta dauko wayarta ta 'kira layinsa, tana ta wasi-wasi ko an rufe layin?.

Ai kuwa bugu 'daya ya shiga, da sauri ya 'daga zuciyar sa tana bugawa.

"Malam ina son ganinka, ya za'a yi?"

Yadda ya ji muryar ta, da yadda ta yi maganar ya san zancen aurensa ya sameta.

"Ki saurare ni zan zo nan da awa guda".

"Ni dai mu ha'du gidan 'KARFI".

"Ok yanzu haka Ina gidan sai kin iso, ina jiran ki".

Yana ajiye wayar Mahmoud na fitowa daga kicin 'dauke da ruwan roba da tumblers guda biyu, ya dire wa Mk yana ta faman cin magani, ko abincin da suka gama ci, haka suka ci tamkar kurame adalilin fishin da Mahmoud yake yi da auren da Mk zai yi nan da kwanaki biyu.


Mk ya kalli Mahmod ya ce "Karfi ka daina wannan tunbatsar! kwanaki 'kalilan suka rage mini, na bar maka 'kasar ka huta da ganina".

Da rauni ya yi maganar hakan yasa Mahmoud sassautawa ya ce "Mk tunda ka amince zaka auri yarinyar nan, to ka hada su da Sa'adah, wallahi kai take jira, ko mai ta yi maka ai ka hukunta ta, shekaru hudu ba wata hudu bane, ba kuma sati hudu bane, Ni kaina na taya ka jin kunyar Baffah, wallahi tallahi karfin hali kawai yake yi akan lamarin ku, shi ya haifi Sa'adah, alkunyar da yake yi fa ta kai geji".

Kallo 'daya zaka yi wa Mk ka gane kalamin Mahmod sun sanyaya masa jiki kwarai da gaske, amma baya jin zai iya yin wannan al'amarin, ya kalle shi ya ce.

"Mahmoud na 'dade da gane ban da kirki, Ni da kaina zaluntar kaina nake yi, saboda wallahi har ya zuwa yau ban huta da kewarta ba, ban daina jin cewar na tafka asarar rashinta ba, ina son na rayu da ita, amma tsoron ta nake ji, ko ayyanawa na yi a zuciyata ya kamata na bata wata damar, sai na shiga ru'du da tashin hankali".

Ya yi shiru yana sakin ajiyar zuciya! Ya 'dora da cewa "wata'kila wannan na cikin 'kaddarata, na rayu a duniya ba da wadda nake so ba, alhalin tana raye".

Mahmoud ya rasa abin cewa, tausayin Sa'a yake ji, amma yanzu har Mukhtar 'din tausayi ya bashi, ya tabbatar a matu'kar takure yake da 'kadddarar da ta fado masa na auren Farida ba'katatan

Suna cikin haka! Yayan Mahmoud ya kira shi a waya, da sauri ya mi'ke yana cewa " yau tawa ta same ni wurin Auwal, sai da ya yi ta gargadi kar na bar shi yana jirah na.

Mukallin mota ya 'dauka da sauri akan center table din da ke tsakiyar falon.

Ya kalli Mk da ke kishingide bai da niyyar tashi, ya ce "ko na je na dawo?"

Kai kawai Mk ya iya 'dagawa a dalilin mutuwar jiki, saboda yadda al'amarin Sa'adah ke damunsa.

A hanzarce Mahmoud ya fita ya na fadin "saboda gidan ba kowa yasa ka yarda ka zauna".
Da yake matar Mahmoud din sunje Kaduna bikin cousin sister dinta sai jibi zasu dawo.


Mahmoud na fita 'kofar gidan inda ya ajiye motarsa, bai shiga da ita cikin gidan ba, saboda yasan ba wani jimawa zasu yi ba, kawai sai ganin Sa'adatu ya yi tana bawa mai adaidaitanm sahun da ya kawota, ku'dinsa.

Da sauri ya karasa kusa da ita yana mata barka da zuwa, yana jin wani irin yanayin da ya ganta a ciki, alamun rashin lafiya da rasnin kwanciyar hankali baro baro a jikinta.

Ba dan 'karfin dangantakar sa da Mk ba, da ya aure yarinyar nan ko ya huta da motsawar da zuciyarsa ke yi a duk sadda zai ganta, kai so masifa ne, Madallah da mutanan da suke sadaukar da soyayyar su dan halacci, aminci, ko
masalaha.

Suka gaisa, ta tambayi iyalinsa, Har zaice matarsa bata gidan, sai kuma ya yi shiru, ya ce "ki shiga, zan je na dawo". Ya dinga addua da fatan sulhu a tsakaninta da Mk.

Tana shiga, kai-tsaye bangaren matar gidan ta dosa, ta dinga knocking, jim ka'dan Mk ya leko daga bangaren maigidan yana cewa "iso nan, bata nan matar gidan".

Ta shiga falon da sallama, ta gaishe shi, sai kuma ta kasa magana, sun Jima a zaune suna ta sake-sake a zuci.

Mk ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "ina jin ki, kin ce zamu yi magana".

"Malam da gaske ne wai aure zaka yi?"

Zuciyarsa ta buga, mamaki ya kama shi na yadda ya ji fargaba ta kama shi, saboda yadda ta yi tambayar muryarta na rawa. Ya kasa koda motsi, hakan ya tabbatar mata da gaske auren zai yi".

Hawaye ya balle mata, ta ce " Na shirya fa'da maka gaskiya".

Ya ce "Ina sauraron ki, waya baki kayayyaki nan?"

Cikin kuka mai yawa ta ce Khalil ne! ya bani agogo da rigunan Jawad tsarabar Egypt, shine ita kuma Halima ta ce da ya bar agogon ya siya mini waya! sai kuma ya hado har da wayar".

Ransa ya matu'kar baci tamkar yanzu abin ya faru, ya fesar da iskar bacin rai, ya ce "Ta hannun wa sa'kon ya same ki?"

Da kukan ta ce "wallahi Safina da Halima ne suka kawo mini! wannan itace gaskiyar magana ban munafunce ka ba".

Idonsa ya ka'da ya yi jawur dan tsananin kishi, ya ce "Munafunci kuma na nawa Sa'a! Ni dai kafin ki yi hakan wallahi ban ta'ba tunanin zaki mini wannan Munafuncin da aurena akan ki ba".

Kukan Sa'adah ya 'karu ta ce "Tsautsayi ne, ban ta'ba yin haka ba, wallahi a lokacin da kayan suka zo sai da na ce tsoron kar gani nake yi ba zan karba ba".

Ransa ya sake ri'banya baci a tunzure ya ce "Amma da suka fa'da miki Ni 'din banza! sai kika karba, mussaman da suka nuna miki idan ma na rabu da ke ga wadda ya fini 'kuriciya da kudi yana son ki ko?"

Ganin yanayinsa ya sake tada hankalin Iyah, saboda rikici ne zallah cikin idanuwan sa irin wadda bata ta'ba gani a tare da shi ba.

Da sauri ta ce "Wallahi Malam.."
Ta yi shiru sakamakon harar da ya watsa mata ya ce "Idan kika 'karyata ni wallahi zan miki duka, ki kiyaye ni".

Ta yi shiru sai kuka kawai ta ke yi

Please Login or Register in order to submit comment