You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azabtar da su take yi, shi da yayarsa makaranta nan da suke zuwa ne kawai bata yi nasarar rabasu da ita ba, hatta magana da mahaifinsu sai a sace suke yi da shi domin shima tsoronta yake ji.


A hankali Jawad ya fara janyewa Farida idan ana son aga damuwar sa to weekend ne ace zai tafi gadon kaya. Ba irin rarrashin da Farida bata yi masa amma ya kame daga yawan yi mata hira, idan kuwa yaje gidan a takure zai zauna tamkar bai santa ba, abin ya damu Farida sosai hatta Mk ya damu, ya tabbatar kuma ba zaluntarsa take yi ba tsiya ce kawai irin ta 'Dan Yau.

Har aka kai jallin da kuka yake zuwa gidan, idan Hajiyar Bichi ta ce da Mk ya barshi tunda baya son zuwa, ya kafe sai yaje.

Rannan dai da abin ya ishe Mk a gaban Hajiya ya dinga fa'din "ko zai shide sai ya je gidan, da suka rayu shekaru biyu tana masa wahala bai 'ki ta ba, sai yanzu saboda ya samu shashar uwa tana kitsa masa maganganun iyashege to kanta zata cuta ta kuma cuci 'danta.

Ya kalli Jawad da yake bayan Hajiya yana kuka da hawaye ya zare masa ido ya ce "idan na kuma jin kace mini zaka unguwa uku sai jikinka ya fa'da maka ai can ba gidanku bane, kana kin gidan ubanka kana kwadayin gidan wasu, zo ka shige girma da arziki tun ban tashi ba, kuma nan din ma ba zaka dawo ba can din da baka so a can zaka zauna".

Jawad ya rushe da kuka yana cewa "Hajiya ki ce ya dawo da Ni dan Allah".

Aikuwa haka ya tafi da shi yana kuka , sai dai kaya kala biyu Hajiyan ta bashi tabbacin zai dawo kenan.
Shiyasa ya rage sautin kukan nasa.

Wannan matsalar gaba'daya Mk Sa'adah ya jinginawa ita ya dinga tunanin hanyar da zai magance ta.

Ana haka Jawad ya dinga wani irin zazzabi, karshe farankama(chicken fox) ta feso masa a jiki.

Hajiyar Bichi da kanta ta bugawa Inna waya ta sanar musu, Inna bata yi kasa a guiwa ba ta zo ta duba shi har da tsarabar kayan dubiya, ba yadda bata yi da Sa'adah akan su tafi tare su dubo Jawad amma ta ki.

Da kyar Inna ta shawo kanta bayan taje da kwana biyu, Suka shirya Suka je da Zainab Ma'aji wacce a lokacin wattannin ta biyar da aure, da kuma cikin wata hudu a jikinta. Ma'aikaciya ce a hukumar kidaya ta kasa reshen jahar Kano.

Cikin kwalliya sosai Sa'adah take, ta dawo wata irin mace da gayu da ilimi suka ratsata mussaman da Alhaji Mamman ya sake dawowa cikin rayuwar ta, ba karamin kudi yake sakar Mata ba, ita kuma bata kwangen yin sutura ta daukar hankali.

Komai nata daukar ido yake yi, ado take a yanzu irin wadda bata yi zaton zata yi irinsa ba, amma kuma cike da hankali da nutsuwa. A wannan lokacin ta kammala karatunta tana makarantar horar da lauyoyi ta Bagauda(call to Bar).

A motar mijin Zainab Suka je bayan sun tsaya a hanya sun masa siyayya ta sosai, kai tsaye suka shiga gidan ba wani nauyi domin dai Sa'a ta kan zo gaida Hajiyar duk da ba kasafai ba.

A falon Hajiyar suka tarar da Mk yana shafawa Jawad calamine lotion a jikinsa ko ina jikin Jawad din maganin ne adalilin duka jikinsa ta feso masa har fuska, farin maganin ya maida Jawad wani iri.

Suka gaisa da Hajiya cike da girmamawa, suka tambayi mai jiki.

Zainab ce ta gaida Mk cikin mutunci, har tana cewa "Uncle rabon da na ganka har na mance".


Ya yi murmushi yana cewa "kina cikin daliban da nake cikiyarsu Zainab! Ya mijinki da Yara?"


Ta 'kasa kuma kallon Sa'a kawai ya ke yi zuciyarsa na wani irin tsalle, yayin da ita ta yi tamkar bata ganshi ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, ko Jawad da yake kusa da shi, sau daya ta masa sannu ta maida hankalinta wurin Hajiya.


Rashin gaisawar da basu yi ba, ya ta'ba Hajiya kwarai da gaske, yayin da Mk ya dinga fargabar wayewar da cigaban da ya gani a tare da ita, kwarai da gaske ta banbanta da Waccan Sa'adan da ya rayu da ita.


Zainab sai zungurar ta take yi akan ta gaishe shi, amma ta yi mirsisi.


Suna zaune Ahamad ya shigo ya ganta yana cewa "yau wa nake gani kamar Antina"

Da murmushi sosai ta ce "Nice me zan Samu?"
Ya mi'ka mata 'datar da yake ci, aikuwa ta karba ta hau ci, hakan kawai sai da Mk ya ji haushi dan me zata ci ragowan yawun Ahamad?

Ta mi'ka masa mukallin mota tana cewa "daure ka debowa 'danka kayan dubiya da mamarsa Zainab ta kawo masa".

Da azama ya karba, ya dinga shigo da kayayyaki har Hajiya ta ce " wanne irin hidima kuka yi haka Sa'a? Sai kace wadda zai bude shago?".

Ran Mk ya baci saboda yadda yaga uban kayayyakin ciye ciye masu tsada sai kawaia zuciyarsa ta kisima masa Bazawarinta ne ya yi wannan siyayyar.


Ya dinga huci karshe ya fice bai ko sake kallon kayan ba, da kyar ya ce da Zainab ta gaida gida.


Jawad ya warware ya koma zuwa School amma rashin son zuwa gidan Farida na sake ruruwa a ransa kullum da kuka yake isa gidan, sannan har yaje ya dawo sai ta 'kure da ya yi mata magana har zane shi Mk ya yi amma bai canja ba.

Kan dole Mk ya samo masa makarantar kwana ba tare da ya yi shawara da kowa ba, da kyar aka samo makarantar saboda anci karfin zangon karatu na biyu.

Sai da komai ya kammala na makaranta ya fa'dawa Hajiya dan kar ta hana, Kan dole ya dauki Jawad ya kai shi makarantar gwamnatin tarayya ta Kiyawa, a kokarinsa na nisanta shi da masu hure masa kunne da masu son cusa masa muguwar dabi'a.

A dai dai wannan lokacin aka dawo da Mijin Sumayya aiki Kano, da Karin girma sosai.

Tuni dama sunyi gininsu a gandun albasa layin kwankwaso, da farin ciki Suka tattaro Suka dawo kano cikin gidansu na alfarma.

Zainab ta haihu ta sami Musa sunan uban mijinta ne, Sa'adah ce ta yi masa inkiya da Walid.

Farida ce dai shiru har yanzu da suke cikin shekaru uku da aure, Mk na iyakacin kokarinsa wurin kwantar mata da hankali ya na tabbatar mata zai cigaba da sonta ko bata haihu ba.

Amma deep inside his heart ba abin da yake so irin yaga an masa haihuwa, ya matsu ya samarwa Jawad gishirin duniya.


Watan Mk uku da dawowa Jami'ar ta yi bikin karrama shi, tare da bashi mukamin Dr! Sannan ya zama shine H.O.D na English department. Wanda shine mafi karancin shekarun da ya taba zama Head of Department.

A wannan lokacin kuma mahaifin Farida ya bashi dan'kareren guda a Rijiyar Zaki, a matsayin kyautar karramawarsa ya taya shi murnar kammala karatunsa. Gida ne mai kyau, mai dauke da bangare biyu, matu'ka da gaske gidan Flat ne amma ya tsaru kwarai da gaske.


Har Jawad ya shekara Sa'adah bata ta'ba zuwa masa ziyara ranar visiting din ba adalilin tana gujewa haduwarta da Mukhtar. Sai dai Sumaayya da Inna su je, haka Farida da Mk da Hajiya duk suna zuwa.

Sai visiting din karshe wadda suka hadu da Mk har zuwa ranar da Mahmoud ya je gurinta da neman sulhu da irin bijirewar da Innah ta yi akan maganarta da Mk.



*'karshen labarin abin da ya faru a Rayuwar Sa'adah da take fatan matan da suke cikin waccan rayuwar da ta yi a baya su hankalta kafin komai ya kubuce musu*.









*Surayya Dee*
✍️
🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_


*Assalama Alaikum*!


*Tsokaci*

*Ina jinjina da godiya ga dimbin masu bibiyar wannan labari na *HALIN YAU* ina kuma jin dadin yadda kuke sharhi akan labarin, Allah Ya bar zumunci*.

*Bayan haka zan so na yi dan tsokaci game da wata sa'dara a cikin labarin, a shafin baya da na saki. Watau daidai wajen da MK ya tare da Farida a hotel din Tahir na yini daya. Wasu daga cikin masu kokarin bibiyar littafin kullum, sun yi sharhi akan cewa don me MK ba zai bari har sai sun tafi UK ba kamar yadda aka tsara? Me yasa bai yi hakurin ya nuna zumudinsa wanda hakan tamkar cin fuska da tozarci ne ga Sa'adah?*

*To abin da nake son na ja hankalin masu bibiyar labarin shi ne, a dabi'a ta namiji wannan ba komai ba ne. Idan har namiji na bukatar abu idonsa rufewa yake ya manta da komai, musamman ma bukatar kwanciyar aure. Abin a halittar maza yake, don haka shi MK bai yi haka da nufin muzantawa ga Sa'adah ba ko kuma jin cewa Farida ta fita. Sai dan a fahimci kaso casa'in da tara da digo Tara na mazan Yau haka suke, domin zasu iya kwanciya da macen da bama sonta suke ba, kawai dan su biya bukatar su ne sabanin da yaje wahalar gaske mace ta sallamawa wadda bata so kanta Akan tana so sai alatilas.*

*Watakila tsawon lokacin da ya dauka ne yasa shi gaza hakurin jurewa har sai sun tafi UK din*.

*Ina fatan masoya Iyah za su fahimci MK kuma su yi masa uzuri.*


*Wasalam*.



*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.


91-92.


*Barkan mu da Dawowa*
*Asalin labarin*.


Kwana Sa'a ta yi tana juyi, Abu goma da ashirin sun cakude mata, na farko idan ta ce bata son Mk ta yi karya, duk yadda take jin haushin sa, da jin bacin rai akan lamarinsa, bai hana ta ji wani irin murna da farin-cikin dawowarsa ba. na biyu kuma bata jin a karan kanta zata saurare shi har sai ya janye kalamansa, sannan kishin auren Farida da ya yi yana matu'kar kassara tunaninta, yana gushe dukkan farin cikin da take ciki, haka nan yana sanya mata jin haushinsa marar misaltuwa, sannan ya sababa mata jarumtar da zata iya yin fito na fito da shi. Sai kuma fargabar yadda Inna ta zafafa lamarin ta da shi.

Haka gari ya waye ta tashi da idanuwanta a kumbure ga ciwon kai tabbacin babu isasshen barci a tare da ita.

Tana tsakar gida tana brush ta dinga jiyo sautin wayarta, bata wani damu ba tana raya koma waye ya sake kira.

Maimakon ta shiga dakinta, dakin Innarta ta shige ta sameta ta idar da sallar walaha.

Ta sake gaisheta tunda sun riga sun gaisa tun asuba.

Ta zuba mata ido ta ce "Iyah wani Mafarki na yi da ya tayar mini da hankali, amma zan bishi da sadaka da kuma addu'a domin ba abin da sadaka bata wanke shi, kema ki tsananta addu'a ki kuma fita harkar Muutar tun baku sake jefa mana ba'kin cikin da ya zarta wadda muka shiga a baya ba".

A sanyaye Sa'adah ta ce "wani abin kika gani ne marar Da'di Innah?"

Da sauri Inna ta ce "ai idan akace marar da'di da sauki, abin da na gani muninsa ya zarce hankali, abin a nemi tsari ne, ba a kanmu kawai ba, akan kowanne musulmi ma, Malamin islamiyarmu ya ce ba kyu fa'dar Mafarki marar kyau domin duk yadda aka fassara maka shi haka zai zo maka, dan haka zan kame bakina , na bishi da istigifari da sadaka, ina sake jan kunnenki ki sake nesanta kan ki da Muutar".


A tsorace Sa'a ta ce "To Inna zan kiyaye in sha Allah, ashana zaki bani, ta kicin din na jefata a ruwa ban lura ba".

Ta karba ta fita, tana Kissimmee kissimmen mafarkin Inna da dukkan alama ita da Mk ya shafa.


Haka ta yini sukuku har yamma, Innar ma haka take ba kuzari adalilin mafarkin da ya mata tsaye a zuci, domin ta san da wahalar gaske ta yi Mafarki amma idan ta yi, ta kuma tashi da abin a kanta ma'ana bata manta ba, to kuwa lah shakka sai abin ya faru ko da ba kwabo da kwabo ba. Amma kaso sittin sai ya zama reality.

Mafarki ta yi wai Muutar na ta bin Sa'a da gudu, suna ta tseren, so yake ya kamota amma tana ta zille masa ga wani abu Abu a nade a hannunsa, sun ci gudu, har Sa'a ta gajiya ta zube a kasa tana haki ya karaso, da gudu ya jefa mata abin da yake ta faman kankame shi, tamkar 'kwai.

Da kuka Sa'adah ta bude ashe jariri ne, maimakon ta ga Sa'adah ta mayar masa da abinsa, sai kawai ta ga ta hau shayar da shi, cikin zafin nama ta nufi Sa'a, tana zuwa tasa hannu da nufin fisge yaron sai kawai ji ta yi an tureta da wani irin karfin da ya zarta na bil'adama, ta sake yun'kurin sake kwace yaron, aka sake turata cikin wani irin rami. Da wata irin murya ta ji ance "Zaki iya mutuwa akan wannan yaron, domin 'dansu ne, ke ce shamakin zuwansa duniya, to kuwa zai zo, idan baki yi Sa'a bama a dakinki zasu yi cikin su haifar miki shi a matsayin shege".

Da kyar Inna ta fito a cikin ramin nan bayan ta kukkuje kafafuwanta, dai dai lokacin Kuma ta farka adalilin Kiran assalatu da ta ji Anayi a masallaci.

Ta tashi duk jikinta a jike tsabar fargaba da rudu, ta mike a hankali tana neman tsari da samun shege a cikin zuri'arta.

Yammaci sosai kafin Sa'a ta shirya ta fito da Shirin tafiya gidan Sumayya.

A tsakar gidan ta sami Inna, ta ce "Inna zan tafi".

Ta daga ido ta kalleta ta ce "Ince sai wani satin kike da zama a kotu?"

"A a Gobe ne Innah".

"To ki gaishe da Yayar ta ki, sannan ki fa'da mata lalle ta sake taya mu da addu'a".

Har Sa'adah ta kusa kaiwa zaure Inna ta dawo da ita, ta zaunar da ita ta fa'da mata komai na mafarkin da ta yi, ta rufe da cewa "Dan haka ki nisanci Muutar.

Kunya ta kama Sa'adah amma ta daure ta ce "in Sha Allah hakan ba zata faru ba ubangiji ba zai kunyata ku ba Inna".

Sa'adah na aiki da (supreme Court) ta court road. Watan jiya Alh Mamman ya kawo mata (upper) takardar samun aiki har gida, wadda wannan na cikin abin da ya sake dagulawa Mk lissafi, domin kuwa a bakin Ahamad yà ji Sa'a ta samu aiki, duk da tafi zaman gidan Sumayya adalilin daga gandu zuwa court road ba nisa. Ya fi mata sau'kin zuwa.

A bincikensa ya gano Alh Mamman ne ya samo aikin, ya dinga jin takaici yana kallon Alh Mamman a matsayin a karambana, da ga fitowarta a makaranta sai ka nemo mata aiki? Tamkar ance masa ana bu'katar hakan, kai dattijan mazan nan wuyar sha'anine da su idan suna son Yar yarinya. Ko kunya ba ya ji, zai dage yana son Sa'adah alhalin yana da 'dan da yake sa'anta ne.

A fili Mk ya ja tsaki ya ce "zanga yadda za'ayi ka mallaketa shekaru da yawa ka kasa rabuwa da ita, tamkar ita ka'daice yarinyar mace bayan ga yanmata nan masu shekaru irin na ta".

Ya sake jan dogon tsaki yana cewa "Halima tana nan har yau a kasa ta ke da gudu zata soka, amma wannan kam a yanzu ma ba samunta zaka yi ba". sai dai a zuciyar sa ya tabbatar son gaskiya Alh Mamman ya ke yi mata, wani irin abu mai nauyi ya danne shi a zuciya, wadda shi ya damalmala masa lissafi har ya ji ba zai sami nutsuwa ba, idan ba shiryawa ya yi da ita ba, ya lura ba zai ta'ba iya jarumtar wani ya aureta alhalin yana da rai ba.



A zaure ta tarar da Baffa da Mk da kuma Mahmoud a zaune kan tabarma suna tattaunawa, sai da zuciyarta ta buga tunda ta ganshi da Mahmoud lah shakka maganar kome ya zo yi, a ranta ta dinga jinjina rashin ta ido a gurin namiji, yanzu da yake son komen ya na'de kafar wando zai nemi komenta duk yadda ya jingineta shekaru bakwai, Anya kuwa Mk yana da adalci a yanzu?

A ladabce ta ce "Baffa sannu da yammaci, zan tafi, sai wani satin Kuma".

Da wani irin farin ciki ya amsa mata da fa'din "To ki gaishe su, ki kula da kanki, Allah ya tsare".

Ta amsa da cewa "Ameen".

Ta kalli 'Karfi ta ce " Baban Dadi barka da yamma ya iyali?"

Ya amsa ta saka kai ta fice bata ko kalli inda Mk yake ba, bare ta gaishe shi ko da gaisuwar da zai raina ne.

Ran Baffa ba karamin baci ya yi da abin da ta yi ba, ta ganshi da ba'ki, ta gaishe da 'daya, ta wulakanta 'daya, idan dai da gaske bata son Mutari a yanzu menene zaisa ba zata gaishe shi ba?

"Iyah"
Baffah yasa baki ya kirata da karfi, ta dawo tana cewa "Ga ni Baffah"!

"Me yasa kika gaishe ni, Me yasa baki wuce kanki tsaye ba? Ai na yi zaton ko da rago Ki ka ganni zaki tsaya ki tambayi lafiyarsa saboda ya shiga rigata, akan idona ki yiwa Mutari wannan wulakancin? Amma ba komai ai ni kika yiwa ba shi ba, Na gode miki je ki, yi tafiyar ki".

Ta kasa tafiya, ta yi sukuri tana jin takaici na kamata, hawaye ya balle mata, Mk yana kallonta ta gefen ido, yana ganin yadda ta turo baki gaba, sai ya dinga jin wani irin tsumi na tsumashi, abubuwa masu yawa akanta suka dinga bijiro masa, ya dinga jin wani irin abu na taso masa.

A hankali, kuma cikin bacin rai ta ce "
Mutarin Baffah ina yini?"

Dariya ta kwacewa Mahmoud ya dinga kyaykatawa Baffa kuwa ya gintse tasa dariyar ya dubi Mk da ya hade girar sama da ta kasa kuma bai amsa ba, hakan da ya yi ya sake hassalo da Sa'a.

Baffah ya cije ya ce "Yanzu kuma laifinka ne ta gaisheka baka amsa ba, tunda hakane sai ka tashi ka kaita, ai bazai yiwu ka sace mata iska a banza ba, dole ka hutar da ita tsayuwar jiran mai adaidaita sahu dama kuma garin hadarine sossai".

Mahmoud ya yi maza ya ce "To Baffa bari mu kaita mu dawo, mun gode Allah ya kara girma".

Baffah ya shige gida ya barsu a zauren Sa'a ta na jin tamkar ta yi ta zunduma ihu.

Hawaye ya dinga tsere a idonta, wannan irin bada ita da Baffa ya yi? Duk wula'kancin da Mk ya mata wato Baffah bai ga laifinsa ba, daga zuwa da magana zaice ta shiga motarsa ya kaita a matsayinsa nawa din ta?
Zauciyarta ta kuntata sosai tana jin gara ta tafi da kafa a kan ta shiga motar Mk.

Har suka fita kofar gida kuka take marar sauti, Mahmoud ya bude mata gaban motar, ta cije, a hankali ya ce "a titi muke fa, sannan umarnin Baffa zaki bi, ba son ranki ba" .
"Akan me za'a tilas ni shiga motarsa,?"

Ta fa'da cikin rishin kuka.
"Yi ha'kuri ai dukkan mu umarnin Baffa zamu yi wa biyayya akan kunnen ki dai ya hukunta Mk ta hanyar mayar da shi dureban ki, adalilin amsa gaisuwar ki da bai yi ba. Kina kallon bai yi musu ba sai ke?"

Hawaye ya zubo mata ta ce "Ni na yafe masa zan tafi da kaina".

Mahmoud ya ce "Ai tunda Kika bari Baffa ya shige cikin gida dolen Mukhtar ya miki direba kar ki yadda ki sab'awa mahaifin ki adalilin wani Mukhtar".

Take Sa'adah ta gane gaskiyar Mahmoud ne, tunda rashin gaisuwar da bata yi bane ya janyo mata wannan hukuncin mai kama da saukar aradu.

Maimakon ta shiga gaba inda Mahmoud ya bude mata sai kawai ta bude baya ta shiga.

Da azama Mahmoud ya isa setin direba Mk ya juya musu baya tamkar baya wurin hakan da ya yi ya sake tunzura Sa'a tun fil'azal ta tsani a nuna mata rashin kulawa.

Mukullin hannun Mk Mahmoud ya karba, a hankali ya ce "shiga baya mu je".

Ba musu Mk ya bude bayan motar ya zauna, Yana rufewa Mahmoud ya ja motar.

Zuciyar Iyah tamkar ta fa'do kasa dan tsananin ba'kin ciki mussaman da ta tuno irin addu'ar da dinga yi, tun bayan da ya auri Farida na kar Allah ya sake ha'data ko da zaman mota ne da Mukhtar balle kuma zaman aure, sai gashi karon farko da zaman motar aka sake ha'dasu, zuciyar ta dinga bugawa fiye da kima tana fargabar menene zai biyo bayan wannan zaman?


Ta dinga jin takaicin kin shiga gaban motar, da ta shiga ai tasan shine dole zai ja motar, Kuma dolensa ya zauna iya kujerarsa sannan ya kula da tukinsa.

Amma yanzu ya babbake har gefen jikinsu na gogar juna, gilashin motar irin na munafunci ne wato tint, ya matseta sosai tamkar su hudu ne a bayan motar.

Ba'kin ciki ya isheta sai kawai ta fashe da matsanancin kuka mai sauti sosai, Mk ya yi tamkar bai ji ba, yayin da Mahmoud ya juyo da sauri tunda a tsaye suke traffic ya tsayar da su.

"Menene kike yi haka Sa'adatu?"
Zuciyarsa ta buga ganin yadda Rabin jikin Mk na jikinta, wani irin abu ya tsayawa Mahmoud da bai yi zaton zai ji ba, ya juya da sauri ya dauke fuskarsa yana ambaton innalillahi.

Kukanta ya dinga tsuma Mk ya dinga jin tamkar ya danneta ko ya samu sau'kin halin da yake ciki.

Ya lura fishi na fitar hankali take yi da shi, idan ya ce zai lalla'ba ta to ya kai shekara yana fama adalilin taurin kai irin nata.

Ba zato Sa'a ta ji Mk ya ja uban tsaki mai tsayi, sai kuma ta ji yana cewa "Mahmoud saka mini wa'kar Auren Dole ta Ali jita".

Dariya Mahmoud ya yi ya ce "bansan jita yayi wakar auren dole ba, ta aure mai da'di nasan ya yi"

A gajarce Mk ya ce "to lalubo mini wadda zata dace da halin takurar da nake ciki, banda Hajiya da Baffa sun matsa mini, ina zan zo gurin wannan shugabar masu wula'kancin da niyyar wata magana, ai tun wulakantani da ta yi a ziyarar Jawad na gane idan ka shekara dubu baka mutum ba, kar ka tambaye shi komai binciki halinsa".

Ya nisa ya sake jan tsaki ya ce " Ta tisa ni tana kukan gulma da iskanci, alhalin kasan ranta murna da farin-ciki ne fal, dan kuwa ban tsammaci zata iya barci ba, mafi yawa butulcin mace ke kaita wuta, abin da aka jima ana rokon ya tabbata ne, ya zo kuma sai a bude shafin iyashege, har da kuka kala kala tamkar wata yar yarinya alhalin gyara da kwalliya ne kawai domin ana kallon Jawad za'a gane ta tsufa".

Wani irin daskarewa Sa'adah ta yi, wato Mk da rashin mutunci ya zo, ta tabbatar da hakan tunda a gaban Baffa ma ya yi mata diban karan mahaukaciya, amma ba laifinsa bane, Baffa ne ya bada ita, dama kuma ance naka ne yake bada kai.

Duk yadda ta so shanye maganar Mk kasawa ta yi, ta yi jarumtar shanye kukan ta ce "duk tsufana dai ka girme ni, kuma ina rokonka ka koma ka fadawa wadda suka yi maka dolen aurena! na ce bana sonka, bana sha'awar zama da kai, domin wadda ya soni ina budurwa, yanzuma da na tsufa son nawa ya nan a tare da shi saboda ba sha'awata yake yi ba, idan kuma na so ma saurayi zan aura wadda ni zan cire masa samartakarsa fiye da yadda na ta'ba cirewa wasu".

Ai bata karasa ba, ya shammaceta ya wawurota ya kama bakinta ya murde da karfin gaske, dan kansa ya saketa bayan ya tabbatar ta ji a jikinta. Jikinsa na rawa ya ce "wallahi idan baki kiyaye harshen ki a gabana ba, zaki sha wahala ai yanzu ke ba yarinya karama bace da zaki dinga mini kaifin harshe".

Mahmoud kuwa da ya lura da abin da Mk yake yi

Please Login or Register in order to submit comment