You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini.

Har gida Mai girma Sanata ya aiko mata da dankareriyar mota kirar Toyota Camry new modern.

Direbansa da wasu yaransa ne suka kawo, suka danka a hannun Baffah. Bayan sun yi godiya a madadin Sanata.

Washagari asabar Khalil ya mata wayar zai zo ya mata godiya tare da ban gajiya.

Saboda jidalin Mk ta masa kwatancen gidan Sumayya dan kar ya zo shago ya hango ta da Khalil, duk da a gidansu ta kwana. Sai bayan azahar ta tafi gidan Sumayyan tunda ya ce sai bayan la'asar zai zo.

Aikuwa ana idar da Sallar la'asar ba jimawa ya iso, sosai suka sha Hira, wani lokacin kuma suyi ta jifan junansu da kallon kauna sai kuma a waske da murmushi, tabbas soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa.

Amma Sa'a ta 'kudire ba zata auri Khalil ba, domin ta san komai na iya faruwa da Mk a sanadin hakan.

Da zai tafi ya ajie mata envelope mai dauke da dalar amurka, wanda idan a kiyasin naira zasu iya kaiwa dubu dari biyar.

Ya yi ta mata godiya tare da cewa "Na so kwarai ace na aure ki, sai dai jiya Mum 'dina ta tabbatar mini Yar kanwarta ta zaba mini, bijirewa ta kuma na nufin lalacewar al'amurana, na sani har na mutu ba zan daina son ki ba, sannan tsayiwar ki, kadai kan mahaifina ya tabbatar mini da cewa tabbas baki manta ba, duk irin kaini 'kasa da Mk yake ko wa, da ya yi"

Tana dariyar wai ya manta sunan Mk ta rako shi har wajen da ya ajiye motarsa, Suka sake tsayuwa a wajen adalilin ya ce zai shiga gidan Madugu wurin abokin karatunsa a Egypt.

Suna tsaye motar Mahmoud ta tunkaro su, zuciyar Sa'a ta buga, kafafuwanta suka dinga barazanar kada ita. Mk dake gaban motar ya ji tamkar ya sume, mussaman da ya tabbatar Khalil ne wannan zabgegen saurayin ya girma sosai.

Suka hada ido amma Khalil sai ya dauke kai bayan ya galla masa kallon raini tamkar shekarun baya. Har zuwa yau bai ji zai iya kallon Mk a matsayin malamin sa ba, sai dai a matsayin dan fashi a soyayya.

Wannan kallon ya sake rikita Mk, domin yasan na rainine tsantsa. Yayin da Sa'a bugun zuciyarta ya tsananta, tana raya ina ma motar Mahmoud ce mai tint?

Mai gadi ya bude musu gate Mahmoud ya ja suka shiga, ya juya ya ga Mk yana wani irin numfarfashi, tamkar ya samu attack na asthma.


A farko 'karfi ya dauka abin Wasa ne sai da ya ga Mk ya sume sai kawai ya ja motar a kidime zuwa asibiti.














SURAYYA DAHIRU.
✍️✍️


*HALIN YAU*!

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.


*Lafazee writers*

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*

*GAISUWA GA DUKKAN MAMBOBIN*
*HALIN YAU FANS*
*_Na gode sosai da yabawar ku, comments din ku na matu'kar sa ni Nisha'di, Allah ya bar zumunci_*.


102-103.

Suna tsaye suka ga mai gadi ya bude musu kofa, Mahamud ya fito a guje kana ganin tukin da yake yi kasan babu sukuni a tare da shi.

Hankalin Sa'a idan ya yi dubu ya tashi, Khalil ya kula da yanayinta ya ce, ina son ki sosai, ke kuma kina son wanccan wicked man din.

Ya'ke kawai ta yi, ba tare da ta ce komai ba.

Ya juya ya fara tafiya yana cewa" sai wani lokaci, muna godiya, kwarai da gaske".


Da azama ta juya itama tana jin tamkar ta yi ta zunduma ihu, ya ya zata yi ne?

Ta san ganin Khalil tare da ita means alot a wurin Mk.


* **
Suna isa Asibiti aka shiga da shi dakin agajin gaggawa wato (emergency). Likitoci suka rufu akansa ana kokarin shawo kan matsalar, tsawon lokaci kafin a samu numfashin sa ya dawo, sai dai ba dai dai ba, Dan haka dole aka saka masa na'urar sau'ka'ka zukar numfashi (oxygen).

Sai dare 'karfi ya sanar da Farida da Abbas halin da ake ciki.


Dukkansu sun yi jigum jigum a asibiti suna kallon Mk a kwance bai san wanda yake kansa ba.

Farida sai fama take da tissue tana goge hawayen da ya kasa tsayuwa a idonta, ta dade da sanin mijinta bashi da lafiya, ta Dade tana jiye masa shiga irin wannan halin, adalilin kullum yana cikin rashin sukuni, ta dinga jin haushin Sa'adah na kamata, ta tabbatar ita take son kaishi barzaku dan kawai ta musu biyu babu.

Hajiya kuwa sai da gari ya waye aka sanar mata, ta isa asibitin cikin tashin hankali, ta kalli yadda ya ke shimfide akan gadon asibiti, ya zabge sosai, dama ya dade a rame Amma yanzu ramar ta bayyana karara.

Haka suka tasa shi a gaba masu addu'a na yi, masu share hawaye na yi.

Sai da aka kwana biyu Baffa ya samu labarin ciwon Mk adalilin Bai ganshi ba, bai ga Mahmoud ba, haka Abbas, har shagon su ya je, anan ya samu labarin ai yana asibiti an kwantar da shi.

Akeel ne ya raka shi asibitin, ba karamin damuwa ya shiga da ganin Halin da Mk ya ke ciki ya yi ba.

Ya dinga yi masa addu'a yana tofa masa.

Har ya gama zamansa Mk bai farka ba, ya isa gida ya tarar da Innah a tsakar gida tana yanke farce, ta masa sannu, ya amsa, ya samu gefe ya zauna.

Ya nisa ya ce "Mutari ne bai da lafiya rabona da shi yau kwanaki uku kenan, dazu na je shagonsa jin ba'asi sai ake fa'da mini bai ji da'di ba, na je na gano shi, Amma ban ji da'din ganin sa ba, domin gaba'daya yana kwance tamkar gawa.

A sanyaye Inna ta ce "Assha Ubangiji yasa zakkar jiki ce".

"Ameen dai! Amm an tabbatar mini jininsa ne ya hau fiye da 'kima, na san baya rasa nasaba da bijirewar ku, Ayyah Salamatu ba zaku yiwa yaron nan sassauci ba, ko bai ci arzikin kowa ba, ya ci na tilon 'dansa mana".

A sanyaye ta ce "Àllah zai bashi lafiya, Iyah har karamin hauka ta yi, amma da aka yi hakuri ai gashi nan ta mike, har ya zama tamkar ba a yi ba, shima zai tashi ne".

Ran Baffa ya fara 'baci da lamarin ta sosai, Amma sai ya mike ya fice domin ya san cigaba da zamansa a cikin gidan yana nufin rikici mai tsanani a tsakanin su, abin da ba zai iya tuna ko sau nawa suka yi a tsayin rayuwar aurensu ba.

Sa'a da ke daki take jiyo su, hankalin ta yayi tashin gauron zabi, ta da'de tana wasi-wasin fishi su Dr 'Karfi suka yi, ko kuwa jikin Mk ne har yanzu domin yadda ta ganshi kwance a gaban mota da irin gudun da Mahmoud ya yi ta tsorata.

Gashi kwana biyu bata sake jin su ko a waya ba.

Hawaye ya 'balle mata, ta tuno sadda yake ce mata, yana jiye mata fargar jaji, yana jiye mata kar 'danta ya zama maraya.

Ta kasa fitowa waje dan idan Inna ta ga tana kuka akan Mk to kuwa ta kade har ganyen ta.

Ta rasa inda zata tsoma ranta.

Washagarin ranar sai ga Baba Isa sun zo har da su Baba umaru, daga asibiti suke, ganin Halin da Mk ya ke ciki, yasa suka ji tausayi, suka saka Mahmoud ya kawo su, su zo ko Allah zai sa a samu yarinya ta huce .


Amma wani abu da Sa'adah ta kasa gane menene ya daure mata baki da zuciyarta, ba abin da take hange sai Mk da Farida cikin mayafi guda, duk tambayar da suke yi mata ta kasa amsawa sai kuka take yi, tana satar kallon mahaifiyarsu.

Hade ran da Inna ta yi, yasa ta ce "Na yafe masa, amma ni bana sonsa da aure".

Jikin su Baba Isa ya mutu kwarai da gaske, dan haka suka ha'kura domin dai sun san yarinyar ta hadiyi ba'kin ciki kala kala.

Ran Baffah bai ta'ba baci irin na yau ba, gaba'daya ya ji Sa'adah da mahaifiyarta sun kunyata shi, sun tozarta shi.

A daddafe ya sallame su, ya dawo gida, ya dinga surfawa Inna sababi, yana fa'din "Ban san ladabin karya kika yi mini ba, a tsawon shekarun da muka kwashe ba sai yanzu".

Ya nisa ya ce "wallahi Salamatu kin yi 'karko irin na kifi ace wai ke kika raba mini gida zuwa jami'iya biyu, kin hana yarinya zabin zuciyarta, saboda son rai irin naki.
Yanzu haka yaro yana gadon asibiti rai a hannun Allah! Tabbas idan ya mutu, ke ce sila, kin bada muhimmiyar gudunmawa wurin kisan rai"

Ta fara kuka ta na cewa "Eh ai da yake shi ka damu da lafiyarsa, shiyasa kake akilon samo masa mafita, amma sadda ta dinga zabura tana surutai ai duk ka manta. Ina nan akan bakana bana son Muutar da Iyah".


Ya hassalo ya ce "to kuwa ba zan iya zama da ke da wannan bakar zuciyar ta ki ba, har kina iya buda baki kina ce wa wanii mai ru'ko da 'Kullaci, to ke ai zuciyar ki tafi ta kafiran farko ma tauri".

Da kuka sosai ta shige 'daki ta fara tattara kayanta tana fa'din "akan Iyah ta komawa Muutar gara na ha'kura da zaman tunda ka ce ba zaka iya zama da ni ba".

Sa'adah da take tsaye tana kukan bacin ran yau akanta iyayenta da bata ta'ba ganin sunyi ko da musu ba, suke wannan tashin hankalin.

Ta bi Inna daki tana bata hakuri amma ko kallonta ba ta yi ba, sai hawaye take yi, tana cigaba da hada kayanta.


Baffa ya shigo ya ce "daina ha'da kayan ki, yau shekaru arbain har da uku da auren mu, kike tunanin dan na rabu da ke zan tura ki gidanku? Ai ni ba azzalumi bane, ba zan karar miki da karfinki da kuruciyarki sannan na sallama ki ba".

Ya nisa sosai ya ce "mahaifiyata ita ta sha nono ta barwa mahaifin ki, kenan a ko ina ni mai tsaya miki ne, ba me tozarta ki ba.
Ni ne zan fita na barki miki gida, ki yi yadda kike so da yaranki, tunda ni ban isa na yi iko da su ba, kin riga kin zama 'Yar birni, son ya'ya kawai shine a gabanki ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba".

Ya sake cewa "ki yi zamanki, ko ban aure ki ba, aike kanwata ce da zan baki 'daki a gidana, bare kuma nine na karar miki da komai".

Ya juya ya fice zuwa dakinsa ya dinga ha'da kayansa. Sa'a ce ta ankara da yadda yake ta fito da kayayyakinsa tsakar gida.

Ta fito da sauri, cikin kuka sosai ta zube tana cewa "Na ro'ke ka Baffah ka yi hakuri, kar ka bar mu ina zaka tafi ka barmu?

Muryarsa na rawa ya ce "ko ina ma zan shiga menene matsalar ku, ina ce yanzu kun yi wayewar da zaku iya rike kanku, ku zartar da hukuncin da ni ne zan yi muku biyayya, ba kune zaku mini ba, saboda kuna gamsar da kanku da uwarku, kyale-kyalen duniya fiye da yadda zan yi muku. Dan haka gara na nesanta kaina da ku, tunda ban isa na ce ga yadda za'ayi a gidana ace mini to ba".

Inna da take bakin kofar daki hawayenta ya kasa tsayawa, da sauri ta tsugunna tana cewa "Ka mini hakuri, na yarda na yi kuskure, na yi laifi, ka gafarce Ni, na amince Muutar kaddarar Iya ne, ina fatan ubangiji ya sa karshen bacin ran mu kenan. Ka yi hakuri na ce to, na amince, ka yi yadda kake so da 'yarka".

Dadi ya mamaye zuciyar Baffa ya ce "Na gode miki Salamatu! Ubangiji ya kore shaidanun da suke son tarwatsa mana kyakkawan zaman mu".

Ya kalli Iyah ya ce "A lokacin da na barki ki yi karatun ki, na tabbatar miki bana so, amma na amince miki dan na yarda alfanu ne a gare mu baki'daya. A lokacin na ro'ke ki duk sadda nima zan zo miki da wata bukata ki daure ki mini biyayya ko da ba kya so, sai dan kin san ba zan dora ki akan abu marar alfanu ko cutarwa a gare ki ba".

Kafin ta amsa masa, ya sake zarcewa da fa'din "To yau ina son na roke ki, ki koma dakin ki, burina a duniya bai wuce ace kina dakin mijinki a zaune kin nutsu ba. Mutari shi nake so ya zame miki miji a karo na biyu".

Da rawar murya ta ce "To Baffah! Na ji, na kuma amince zan yi maka biyayya, zan yi ha'kuri na zauna lafiya da shi komai runtsi".

Da murna Baffa ya ke cewa "Na gode miki in sha Allah ba zaki yi nadama ba, ubangiji ya miki Albarka, ya zaunar da ku lafiya, ya baku zuri'a mai albarka".

Ya nisa ya ce " ku shirya gobe zamu je Gogel ki fa'dawa Yaya Ayuba kin amince ba dole na yi miki ba,
Sannan ku samu lokaci ku gano Mutari domin yana jin jiki"

Da sauri lya mike yana cewa "Bari na bi su Alhaji na fa'da musu wannan labarin mai da'di".

Inna ta bi bayansa da ido har ya fice daga gidan, tana ayyana girman soyayyar da yake yiwa Mukhtar.

Kai tsaye gidan Alh Isa ya dosa, a kofar gidan ys tarar da Dr 'Karfi zai shiga mota, ai kuwa ya ce "Mahmouda zo mu shiga, ba tafiya zaka yi ba".

Baffa da murna yake fa'da musu "ai yanzun nan yarinya ta tabbatar masa ta amince, dan haka ku zama cikin shirin zuwa Gogel, a satin nan. Domin a son raina ku tafi da sadaki, a ranar da kuka je a daura auren a huta, kafin ta sake botsarewa saboda na lura kishin banza ta bari yake rinjayar ta".

Daga Baba umaru har Baba Isa kowa ya yi shiru amma suma jinjina alherin bawan Allahn nan suke yi, da karfin son da yake yiwa 'dansu.

Baba Isa ne ya yi karfin halin cewa "Malam Basiru ka dai matsa mata ta amince, gashi muma zamu sake yin son rai, mu amince da abin da ka zartar domin a samu lafiyar yaron nan ta dai-daita, bamu da bakin godiya, abin da zamu ce maka daya ne, da ikon Allah mu kabawa amanar yarinyar nan, mune iyayensa abin da ya faru a farko ba zai sake maimaituwa ba da ikon ubangiji.
Kira mini yarinyar a waya"

Baffa da ya san bashi da fargaba da azama ya fito da wayarsa.

Bugu 'daya ta dauka, ya ce " Baban ku na Na'ibawa ne zai yi magana da ke".

Kalaman kwantar da hankali tare da yabo da kuma girman mai hakuri Alh Isa ya dinga yi Mata, ya sake jaddada mata kar ta sake yin shiru har sai abu ya girmama, komai ya taso matu'kar yafi karfinta to ta sanar da shi zai magance mata da ikon Allah.

Ya rufe maganar da cewa ko kina da korafi domin mun tsayar da kwanaki biyar masu zuwa na daurin auren ku".

Zuciyarta ta buga sosai, cikin rishin kuka ta ce "Ba ni da matsala Baba! Amma zan ro'ke ka dan Allah a bari sai na kintsa sannan ayi tariya".

Da sauri ya ce "Na miki Wannan laminin ki shirya a nutse, ai na san tutsiye Malam Basiru ya Miki ko na ce karfa-karfa, dan haka daga wata daya zuwa wattanni shida ki yi shirinki a hankali, bu'katar mu dama a daura auren hankalin kowa ya kwanta".

A yammacin ranar suka je asibiti ita da Inna har da Sumayya.

Har suka gama zamansu barci yake yi, wannan barcin shike daga hankalin kowa, ya rame kwarai da gaske.


Har waje Hajiyar Bichi ta rako su, tana ta faman godiya, yayin da tausayin Hajiya ya lullube Sa'a, kallonta kawai take yi saboda yadda ta zabge ta yi zuru zuru tabbacin tare suke yin jinyar ita da Mk.

Cike da rauni ta ce musu "Idan har zuwa gobe bai samu sassauci ba, zan tura Ahamad ya dauko Jawad ya zo ya ga ubansa don".. sai kuka ya kwace ta kasa karasawa.

Jikin Inna ya mutu kwarai da gaske, ta dinga bata ha'kuri tare nuna cewa cuta ai ba mutuwa ba ce.

Har suka isa gida ba mai cewa komai saboda ba su zaci haka jikin Mk ya yi tsanani ba.

Washagari cikin ikon ubangiji jikin Mk ya yi sau'ki domin har cire masa oxygen aka yi, sannan ya yini idonsa biyu.

Akan idonsa Inna da Sumayya suka iso, sosai ya ji da'din zuwan su tunda ya lura, sune kanwa uwar gamin wurin tunzura Iyah, sune suka hau dokin na ki, da tallafin su ta sami kwarin guiwar yi masa bore.

Amma da ya tuna wai Sa'adah ya gani da Khalil sai ya ji wani irin kunci ya mamaye zuciyarsa! Tabbas ya yarda a duniyarsa bashi da wani kalubale irin Yaron nan, sannan yadda Khalil ya zama tsalelen saurayi na kerewa Sa'a ya sake tayar masa da hankali kwarai da gaske, domin kowacce mace ta ganshi zata so mallakarsa a matsayin miji.

Ba komai ke nukurkusar Mk ba irin kishin Khalil, a sanadinsa ya rasa aurensa da matar da yake so fiye da kansa, gashi har yanzu basu rabu ba, ya tabbatar Khalil ne ke da nasara akansa, wani irin karfin zuciya ya shige shi, ya dinga kalubalantar kansa meyasa ya kasa mantar da shi a zuciyar Sa'a tamkar yadda ta mantar da shi soyayyar Farida a lokacin da suke tare.

Ya saki ajiyar zuciya yana jin ciwo mai yawa a kirjinsa mafi girma a ciki haushin Sa'adah yake ji kwarai da gaske, a gaban kowa take fa'din bata sonsa, amma dan lalacewa tana soyayya da yaro sa'anta.

Su Innah na zaune Farida ta iso dauke da kwandon zuba abinci. Tana kallon Sumayya ta gane sister din Gogel ce, duk kuwa da Sumayya fara ce tas. Har kasa ta tsugunna ta gaishe su.

Hajiyar Bichi ta ce mata "Kakar Jawad ce da Yayar Mamansa"

Da girmamawa ta sake gaishe su, a ranta sai take ganin Gogel da yayarta dan sun yi kyau ba zai zama abin mamaki ba, domin ko a yanzu da Inna take cikin shekarun tsufa, tana nan da kyaunta, mai kyakkawan jiki ce da yake boye tsufa. Wata'kila haka mahaifin su yake, dan ta lura ba kammanin Inna a tare da Gogel, Sumayya ta fi kama da ita, wanda hakan na alamta cewa mahaifinsu ma ba baya bane.


Sumayya ta 'karewa Farida kallo tsab, takaicin Iyah na kamata da ta dinga kukan Mk ya auri Farida dan ta fita kyau ne, a yau da taga zahairin Farida ba hoto iya fuska ba, sai take ganin ba karamin kerewa Iyah ta yi mata ba. Kawai fararen mutane suna da kwarjini ne ta yadda ake ganin kyaunsu ko da kuwa masu 'karancin kyau ne.


Farida bata dade da isowa ba, su Inna suka yi sallama suka tafi.

Suna isa gida suka tarar da Sa'adah cikin kwalliya ta birgewa, amma tana kwance a falo tana kallo.

Inna ko zama ba ta yi ba, ta hau ta da fa'da "Iyah cewa ki ka yi zaku tarad da mu a asibitin tare da Zainab, ashe karya kika yi mini?"

Cikin rashin damuwa ta ce "na shirya jiranta nake yi".

Kafin Inna ta sake magana Zainab ta kira wayarta, sannan suna jiyo horn dinta tabbacin ta fita, ba shigowa zata yi ba.

Ta mike tana fa'din "gata nan ma, sai mun dawo".

Sumayya ta ce Yanzu irin wannan kwalliya tamkar kin manta asibiti zaki ba gidan biki ba?".

Dake Yan darun akusa suke ta ce "Anty ke kika manta cewa ni wannan ban dauketa kwalliya ba, domin ko a gida haka nake".

Da sauri Sumayya ta ce "gaskiya ce sai na fa'da miki, Hajiyar Bichi na gurin, duka danginsa suna gurin, ki je dubiya cikin irin wannan kwalliyar tamkar me shirin shiga gasar miss Beauty. Ba nadama ba komai a al'amuranki".

Inna ta ce "ta shi ki wanke fuskarki sai ki dauko Hijabin ki dora, ai kinsan yadda hijabi ma yake karbar ki".

Ta mike tana kunkuni wadda yake nuna Sumayya ta fitineta da yawa, dan yanzu ta fi zaman gidanta, to wannan satin ma ba komawa zata yi ba, har sai ta nemeta da kanta.

Yayin da Sumayya ta ce "Ai yanzu kin tabbatar zaki samu burin ranki dole ki tattaro dukkan iyashege ki dawo da shi".

Ai kuwa Sa'aadah ta fasa uban ihun kuka. dai dai lokacin Baffah ya shigo, ya dinga tambayar ba'asin kukan da take yi mai daukar hankali.

Ai kuwa ta fito cikin kuka ta ce "Baffah shata mini layi da Maman Khalifa, ta takura ni, ta matsa mini, saboda ta san duk abin da ta yi mini Inna ba zata ce ta yi laifi ba".

Ya murmusa ya ce "Uwata an taba shiga tsakanin hanta da jini ne, inace da dukkan uku hade mini kai kuka yi.
Yanzu kuma sai kice na shata miki kayi da ita? Ni bana haka, ya kalli Sumayya ya ce ke kuma ki ri'ke girmanki ai dai yanzu kin wuce kisa ta kuka irin haka".


Murmushi sosai Sumayya ta yi, cikin sanyin muryarta ta ce "Baffa daga na ce bai kamata ta je dubiya da kwalliyar da ta yi bane shikenan fa laifin nawa, kuma gani na yi tunda ba zance zata je ba, dubiya ne ai sai ta rage zumudi".

Dariya ta kwace wa Baffah ya shige dakinsa. Ba tare da ya yi magana ba.

Yayin da Sa'adah ta cigaba da kuka sosai, har Zainab ta gaji ta shigo gidan a fusace.

Ganin kukan da take yi, ya tayar mata da hankali ta yi zaton ko Mk ya amsa Kiran mahallicinsa ne.

Amma da ta ji ba'asin kukan sai itama ta hau dariya har tana fadin "Yo dama Ni nasan ba wani bata sonsa, idan akwai abin da na gasgata a duniyata, to kuwa son da take yiwa Uncle na cikin su".

Ai kuwa ta mi'ke a fusace ta ce "Wallahi Zainab har yau din nan ina jin karfi a tare da ni, ya ishe ki".

Zainab ta watsa mata harara ta ce "Da shekarun nan naki, da ilimin lauyancin na ki, da Jawad duk basu sa kin ji cewar kin girma ba? Amma kuwa dai kin ji kunya, kuma na gasgata Anty Sumayya lallai murnar zaki komawa muradin zuciyarki yasa ki wannan fallin, gara ma ki 'dore da kyawawan dabi'un da Kika dauka a shekaru bakwai din nan domin dai kin san yanzu ke Uwargidace kina da amarya mai tsananin wayo da kissa".

Ba'kin cikin maganar Zainab ya sake sawa ta fashe da sabon kuka tana fa'din " Asibitin ma ba zani ba".

Baffah ya fito ya dubi Zainab ya ce "Ni na fi ku fahimtar Iyah tuni Mutari ya fita a ranta, biyayya kawai zata mini, zuwa duba shi ma ai dole na yi mata, ta kuma yarda zata mini biyayya, dan haka ku daina cewa tana sonsa, ko dan shi ta yi kwalliya domin kuwa dukkan mu shaida ne akan Iyah dangin Dawisu ce".

Jin hakan ya sa ta yi shiru.

Yayin da Zainab ta ce "To Baffa ka fa'da mata a biyayyar da zata yi maka ta hada har da sanin ta girma, kar ta koma ta zama ta bizaro a gidan Uncle domin yanzu ba ita ka'dai bace, tana da kishiya mai fi'ilin tsiya".

Baffah ya murmusa ya ce "ke kam Zainab sai a gaishe ki, dukkan mace ai da inda take da tasiri, Ni kuwa na san ko mata uku ne da Mutari ban jin Iyah zata kasa samun kansa, ai duk wannan shagwabar da take yi na gata ne".


Daga haka ya fice ya na fadin "lallai ki fito ku je dubiyar nan Iyah, kinga ba lalle Zainab ta sake samun sukunin fitowa a gobe ba".

Ta fito cikin bakar doguwar riga mai kyau. Tana rataye da Yar karamar jaka, kafarta sanye da flat din talkalmi wadda mahadin jakar ne, powder ce kawai a fuskarta.

Zainab ta mike ta na cewa "Inna sai mun dawo".


Har suka isa asibitin Sa'adah bata ce kala ba, duk da Zainab na janta da hira.

A wajen asibitin Zainab ta samu jikin bishiya ta yi fakin. Suka fito suka taka ciki da kafafuwansu.

Da Abbas suka fara yin tozali, yana zaman jiran Farida ta fito ya mayar da ita gida, dan haka ya mike

Please Login or Register in order to submit comment