You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsiri fishi! Ya tattara ya watsa da ita, ya shareta, dake bame yawan fishin bace da kanta kuma ta dawo hanya.

Haka rayuwar take gudana yau fari gobe tsumma kowa ha'kuri yake yi da abin da rayuwa ta zaba masa.

A haka Allah ya sauki Sa'adah lafiya! Ta haifi danta lafiyayye mai kama da Jawad sak, kenan Mk shima ya biyo.

Kwananta'daya a asibiti aka sallamota bayan an tabbatar da lafiyarta da ta jariri.

Tana zaune a dakinta ta tsurawa jaririn ido tana ayyana abubuwa masu yawa, bai zo da wuri ba a lokacin da Mk ya matsu ta haihu, haka bai yarda ya fito a jikin Farida ba, bai kuma fito a jikin wani namijin ba, tabbas kudurar Ubangiji yawa ne da ita, duk tsawon shekarun nan sai da ya jira ya fito ta tsatsonsu a lokacin da ba a yi zato ba, Wannan ka'dai ya isa aya ga mai hankali.

Dai dai lokacin Mk da Farida suka shigo. Dukkansu suka isa gareta cike da kulawa suna yi mata sannu.

Farida ta rungume yaron da tun jiya da ta 'dora ido akansa ta ji son yaron ya shigeta tamkar ta sace shi ta gudu.

Sosai ta rungume shi, karon farko das tausayinta ya kama Sa'adah!

Mk ya dinga tambayarta ko abin da take so ko bu'kata?

Ta ce "Ba komai so dai nake yi na je gida ko kwana goma ne! Ka ga Umman Fanshekara bata jin da'di ba iya zama mini zata yi ba".

Ya girgiza kai da sauri ya ce "ba zai yiwu ba, abar maganar".

Ta yi shiru tana cewa "An barta".
Mamamki ya kama Farida ada kallon mijin ta ce take yi masa indai akan Sa'adah ne, ashe ba ita ka'dai yake hana yin wasu abubuwa ba har da tauraruwar tasa.

Tsawon lokaci sannan Farida ta mike da nufin basu guri ta ce "Tamkar na tafi da shi, tamkar na dawma ina kallonsa".

"Tafi da shi mana Farida ai d'anki ne".
Sa'a ta fàdi hakan a tausashe sannan ta mike da kyar tana janyo akawatin kayan yaron, Mk ya ce karfa ki fa'di".


Ta dire a gaban Farida ta ce "Ki tafi da shi, ki dauwama kina kallonsa,ya dauma a 'danki, ina miki al'kawari ni dai a bakina wani mai rai ba zai ji ni na haife shi ba, ke din masaniyar magaganganuwa ce, kin san wadda zaki sha ya taimaka ruwan nono ya zo miki, na shayar miki da shi na kwana 'daya da yini, ubangiji ya taya ki tarbiya da juriyar raino, ina kuma yi miki fatan ki samar masa 'kanne ta tsastonko masu yawa".

Mk ya mike da sauri ya rungume Sa'a yana jin sonta yana sake tumbatsa.
Da rawar murya ya ce"Tunda kika yi sa'a Baffah na ya haife ki, na sani zaki yi abin da yafi haka na karamci! Na gode miki sosai Ina tabbatar miki har yau din nan ke ta dabance a cikin duniyata. Allah ya miki albarka! Idan har aljannarki tana 'damfare da yardata ne, wallahi daga yau na yarje miki, daga yau din nan Ubangiji ka shaida komai Sa'adatu zata mini na kuskure, har zuwa karshen zaman mu na yafe mata, na yarda da ita, Ubangiji ka yarda da ita".

Farida tana tsaye tana kallonsu tana Jin inama itace Sa'adah! Ta matsa kusa da ita ta kalleta cikin ido ta ce "Wallahi Sa'adah kin fini kirki, kin fini hakuri, na tabbatar a yanzu da nake jin 'kaunar yaron nan ba zaan iya yin kyauta da 'da ba, koda na haifi guda goma.
Ba abin da zance miki, sai fatan alheri, Ubangiji ya fini yabawa".

Ta saba 'danta ta fice da shi, sai lokacin Sa'a ta fashe da kuka, tana jin girman 'karfin halin da ta yi.

Ya dinga rarrashinta.

Ta ce "shikenan Farida ta haihu, ta sami 'da Kamar Jawad! Sai ka daina takura shi sai ya je wajenta ya kwana, sai ka daina wannan tausayinta da yake neman zame mini barazana".

Ya sake rungumeta tsantsan yana gasgata dinbin sonsa take yi, ya sani ba macen da take sonsa a doron 'kasa irin Sa'adah, idan aka cire Hajiya.

Ya sani saboda tausayin Farida da yake yawan yi ne, ya sanya ta bada abin da yasan ba kowacce mace ce zata iya yin hakan ba.

A fili ya dinga "cewa Madallah da ke Sa'adatu, a yau na sake ganewa ke din jarumace, mai kuma 'kaunata ce, zan sake maimata miki abin da na ce ba zan sake fa'da ba.
Wallahi ban taba son wani abu a duniyata kamar ke da 'Yay'anki ba, Wallahi kune farin-cikina, kune duniyata, har na daina numfashi kece jagorar zuciyata.


Ya rasa mai zai yi mata, sai ya ce ki shirya Gobe na kai ki gida, ki yi sati uku Inna ta sake gyara mini ke, kafin ba'di ina fatan ki haifo na ki wadda zaki ri'ke a hannun ki, a dakinki".

*Wattanni shida a gaba*

Zuwa lokacin Sa'a na dauke da wani cikin na wata biyar, yayin da yaron Farida mai sunan Mahaifinta Nasir(Amir) ta yi masa alkunya, yake wattanni shida.
Yaron ya yi wani irin girma gashi fari kwal saboda farin Mk ya yi, sannan yana shan nonon farar mace, sai ya sake zama tamkar dan larabawa, irin ku'din da Farida take narkawa akan yaron abin tamkar a littafi, albashinta akan yaron yake karewa, haka Mahaifanta duk fitar da zasu yi sai anyi masa akwati guda, hatta Sa'a dalleliyar mota mahaifin Farida ya aiko mata a matsayin tukuicin sanya farin-ciki a zuciyar diyarsa.


Shayarwa ba karamin karabar Farida ya yi ba, idan Sa'a tana ganin status din Farida da 'danta wani lokacin har kusan shidewa take yi tsabar kishin yadda suke daukar ido, domin komai designer take masa amfani da shi, yaron ya zama one in town.
Haka fita goma shiga goma zata ganshi a kafadar Mk.

Idan ya shigo da shi ta mika masa hannu sai ya ki, 'kiwa yake yi mata ba Yar kadan ba, tunda ko wurin aiki da shi Farida take tafiya da mai rainonsa.


A wannan lokacin Mk ya kalallame Sa'a ta ajiye aikinta, ta zama lauya mai zaman kanta, a lokacin kuma tafiya zuwa kasar Amurka ta taso masa inda zai yi kwas na wattanni shida.

Ya tisa Sa'adah ya tafi da ita.

A can ta haihu still dai boy, ta saka rai girl zata samu sai dai Ubangiji ba hakan ya so ba.

Sun more sosai a a zamansu na wattanni shida a U.S. Ta dawo da d'anta mai kama da ita wadda Baffah(Bashir) aka yiwa takwara Jawad ya ce *Jadid* za'a dinga ce masa.

*Shekaru biyu a gaba*.

Hankali kowa ya kwanta arziki da cigaba sai sauka yake yi a gidan Mk! Mussaman da ba'a yi masa tashin hankali, duk da kuma basa shiri.

Dan hatta Amir har yau bai wani sake da Sa'a ba, idan Mk ya zo da shi baya yarda ya ajiye shi, ya dinga kuka yana cewa "Malam dauke ni"
Ba zai yi shiru ba sai ya dauke shi, ko ya mayar da shi wurin uwarsa.
A lokacin Sa'a ta yaye Jadid ta haifi mai sunan Mahmoud, da suke 'Kira da Junior, ta Kuma je asibiti ta sanya loop da amincewar Mk, tana addu'ar ta yi auta kenan, duk da tana tsananin son Baby girl, mussaman da ta lura Mk ma ya matsu ta haifi yar budurwa, amma itakam ta gaji ta fahimci ita da Sumayya basu da rabon haihuwar girls har gara ma Sumayya ta samu Khairat itama kuma sai a karshe domin itace ta biyar kuma autarta.


A lokacin Ubangiji ya sua'kar da ayarsa Farida ta samu juna biyu, murnar da mk ya yi ba yar kadan bace, sosai yake tattalin ta har Ubangiji ya sa ta haihu lafiya duk da dai c.s aka yi mata, yarinyarta mace mai kama da su Jawad kwabo da kwabo mai tsananin gashi irin nata.

Bidirin da akayi ba kadan bane, tun akan Amir farida ta gane jama'a na sonta na tausayinta, haka a wannan ma aka sake nuna mata kauna.

Sosai Mk yake ji da yarinyar nan. Aka sanya mata sunan Hajiya Babba! Wato Aisha, Farida ta sanya mata Amira.

Mafi yawa Mk ya fi yawo da Amir da Amira tun Sa'a na jin wani iri har ta hakura ta gane ba dan komai bane illah ya samu Amir ne bayan ya dauki lokaci babu haihuwa, ita kuma Amira only girl ce.

Jawad ya kammala karatunsa na sakandire, ya wuce kasar Canada yana digiri dinsa akan engineering.

Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin nasarori da kuma kalubale kala-kala.

A yanzu haka Mk ya samu appointment ya zama minister ilimi na kasa, yayin da ya nada Mahmoud mai magana da yawunsa.

Yana Abuja tare da Farida a dalilin itama ta samu transfer a wurin aikinta zuwa Abuja.

Sa'adah kuma tana kano tana cigaba da zurfafa iliminta, a yanzu haka digiri na uku take duk a fannin shari'a.
Duk week end din duniya sai ya biyo jirgi ya zo, sai dai idan baya ' kasar.

Ta da'de da tarewa a gidan Jawad, haka nan Mk yana kan yi musu gini da ya zarta wadda take ciki.

Ta dauko Hajiyar Bichi suna zaune tare cikin girmamawa.

A yanzu da shekarun hankali da girma ya zo mata sai ta gane ba abu mai Dadi a rayuwar mace irin samun miji na gari mai adalci, ita da kanta idan ta tuno ta'barar da ta yi a baya sai ta ji kunya ta kamata, ta kuma godewa Mk domin ba abin da bai mata ba, ta kuma gasgata shi da ya ce shi din tamkar Sumayya ne a wajenta ba wai miji kawai ba, ba abin da bai yi mata, yana kuma tsaye akan dukkan bu'katunta, sannan yana hakuri idan borinta ya tashi.

Haka nan ta gasgata shi da ya ce Baffanta Babansa ne ba nata ba, domin ba abin da bai yi musu ba, ya rushe gidansu ya zamanantar da shi, ya kai iyayenta sun sauke farali.

Itama ta je, ta koma Umrah, duk da bata aiki kuwa.

Ranar juma'ah ta yi ferfesun naman rago ta kaiwa Hajiyar Bichi dakinta, sannan ta ce "Hajiya zan je na gaida su Baffah".

Da murmushi Hajiya ta ce "Ki gaishe su Sa'a, Ubangiji ya yiwa kokarinki albarka, yasa kema naki 'Ya'yan suji 'kanki.

Ta isa gidansu ta tarar da iyayen nata zaune a falo sun yi shar da su tamkar tsufa bai cimma musu ba, ta zauna tana cewa "wayyo Baffahna".

Da wata irin 'Kauna ya ce"sarkin hakuri, giwar mata, mowar 'ya'ya".

Ta murmusa ta ajiye masa kwanon naman a gabansa.

Inna ta ce "Danma dai uwa mafi uba ko da uban sarki ne".

Cikin tsokana ta ce"Ai ni Baffah kam ya wuce ki Inna, sai dai ki yi 'hakuri kawai".

Ta mike ta shiga kicin din da yanzu yana cikin falon ta debe bowls ta zuba musu, suna ci, suna saka mata albarka.

Ta hada kan kayansu kananu ta wanke su tas.

Ta yiwa Innah ganeral sanitation duk kuwa da ta daukar mata Yar aikin da take zuwa ta yi mata shara da wanke wanke.
Amma duk da hakan duk karshen wata sai ta zo ta yi mata gyara na mussaman.

Baffah ya tsura mata ido yana godiya ga Ubangiji, da ya arzuta shi da samun 'Yaya mata, ya tarbiyaantar da su har ya aurar da su, yanzu gashi sun zame masa gata, sun janyo masa mazajensu suna ta hidima da shi, ya yi Imani ko yana da 'yaya maza ba lallai su yi masa abin da Mukhtar d Idris din Sumayya suke yi masa ba.

Gashi kuma ya'yan nasa sun haifa masa 'Ya'ya takwas maza, domin nassin al'kura'ani ya nuna jikanka danka ne.

Madallah da iyayen da basa zaben jinsin da suke son su Haifa, suke godiya ubangiji ta hanyar tarbiyaantar da ya'yansu mata cikin adalci da tausayi.


Sa'a ta koma gidanta, iyayenta suna saka mata albarka da nemawa zuri'arta tsari daga rudin *HALIN YAU*

Mk ya cigaba da kula da iyalinsa cikin adalci da tausayi.

'Ya'yansa biyar Sa'a na da uku
Jawad, Jadid da Junior.

Yayin da Farida take da biyu
Amir da Amira.

Wani week end ya zo Kano, suna zaune a falo ya kalleta ya ce "sai nake tuna shekarun baya da kike ce mini kin yi mafarki, kin zama big Madam, na zama Alaji, na 'kera mana mansion".


Itama ta ce "Na tuna amsar da ka ke bani cewar banga ka 'kara Aure ba?"

Ya fashe da dariya tare da janyota Yana cewa 'dukkan mafarkin ki Allah ya tabbatar miki su, kin zama big Madam, abin alfaharin kowanne miji, tashi muje mu yi nafila mu sake godewa Ubangiji da ya cika mana ni'imominsa.
Wani watan Ina son dukkan ku mini rakiya na gano 'Dan-iyah a Canada har da kannesa zamu tafi".

Ta ce "Jawad bai zama 'dan Malam ba Sai D'an Iyah?"

Da murmushi ya ce "shi ya ce mini sunan da zai sanyawa jirginsa kenan 'Dan-iyah Airlines.
Yana kuma fatan ya samu sarautar 'Dan-iyan Bichi.
Zan fadawa Baban Khairat zamu tafi da ita, ta gano mutumin nata, wata'kila dai zumuncin Jawad da Khairat nan gaba ya bada mamaki".

A zuciyar Sa'a sai fata take Allah ya tabbatar da wannan hadin.



ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH.

*NA GODEWA ALLAH DA YA NUNA MINI WANNAN RANAR TA 27-7. DA NA KAMMALA RUBUTA WANNAN 'DAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA A SAMA*.

*INA MIKA GODIYATA GA DUKKAN WANDA YA KARANTA LABARIN*.
*INA SAKE GODEWA MASU KIRANA, DA MASU YIN MAGANA TA WHATSAPP DAN SU YABA MINI, NA GODE MUKU SAOSAI, UBANGIJI YA FINI YABAWA*

*INA ADDU'AR ALLAH YA KAWO MANA ZAMAN LAFIYA A KASARMU TA NIGERIA, YA KUMA BAMU DAMINA MAI ALBARKA*.

*AUNTY RABI SANI GODIYA MAI YAWA, TABBAS KARFAFA GUIWAR DA KIKE YI MINI YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA WURIN INGANTUWAR LABARIN NA GODE UBANGIJI YA FINI YABAWA*.


*INA ADDU'AR ALLAH YA JIQAN MAHAIFANA DA DUKKAN WADDA SUKA RIGAYE MU*.

*UBANGIJI YA SAKE HADA MU CIKIN WANI LABARIN, DA NAKE FATAN KU KAR'BE SHI TAMKAR HALIN YAU.*


*INA RO'KONKU KAR A HA'DA MINI DOCUMENT, BANA SO, DAN ALLAH A KIYAYE.*

*ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU*🤝




*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
✍️✍️

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment