You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haife ki ba, da tuni ki ba'kanta ni a idon duniya".

Kunyar da Sa'a take ciki ta sake nunkuwa, dan haka ta sake 'kara sautin kukanta dan ta kawar da su daga sake kunyata ta.

Aikuwa dai Baffah ya ce "To ai a hankali zaki bita, ni na gasgata Iyah ba zata kunyatamu ba, ba ta yi shashanci a 'karancin shekarunta ba bare a yanzu da ta yi hankali, na kuma shaida Mutari ba zai ha'ince ni ba".

Wani irin farin-ciki ya kama Sa'adah tana gasgata Mk da ya ce Baffah Babansa ne ba nata ba.

Innah bata gasgata ta ba, amma Baffah ya shaideta ba zata yi Zina ba, haka ya shaidi Mukhtar ba zai lalata masa 'yah ba.
Kuma hasashen Baffah shine gaskiya.
Kawai Innah mafarkin da ta yi ne, yake sata wasiwasi.

Ya sassauta murya ya ce "Yi shiru ki mini bayani"
Ta kasa cewa komai saboda tsananin kunyar da ta tsinci kanta a ciki.

Ya juya ya fita yana cewa yanzu nan na hango shi ya zo unguwar bari na ji daga bakinsa.

Ganin Baffah ya fita! Ya saka Inna cigaba da sababinta, "munafukar banza, kika dinga cika bakin ba kya sonsa, kika yaudarar da ni da cewa ba zaki tare babu kayan daki ba, ashe kina zagayewa kuna abin da ranku ya so, saboda tsananin fitina da rashin kunya"

Daga ganin yadda kika aune, ansan ciki ya kwana biyu a jikinki, yo ina ganin HALIN YAU ni Salamatu!".

Sa'a ba baki sai kuka.

Baffah kuwa shagonsa ya 'kira Mk.
Cikin nutsuwa sosai ya ce "Mutari ka ce mini jibi juma'a Iya zata tare?"

Kai tsaye ya ce "Eh Baffah".

Ya numfasa ya ce "yanzu na shiga gidan na ji wani irin al'amari da ban fahimice shi ba, na tarar da Iyah da gyatumarsu a halin 'bacin rai saboda ta fahimci tana da juna biyu".

Mk ya mi'ke da sauri , zuciyar Baffa ta buga a tunaninsa kaduwa ya yi da jin maganar saboda ba shi da alaka da cikin.

Da azama Baffah ya ce "Ina zaka? Nutsu ka saurare ni, baka da alaka da cikin da yake jikinta ne?"

Ya koma ya zauna ba kunya ya ce"Haba Baffah! Ni fa zaburar da na yi, zuwa zan yi na fahimtar da Innah ta daina yi mata fa'da, Ni zata yiwa, tunda nine Babba! Domin na san kai zaka shedi ne ba zan yi lalata da jininka ba! Amma sai na ji kana tambayar ko bani da alaqa da al'amarin.
Kawai ayi ha'kuri Baffah! Abin da za a kallah a samu nutsuwa matatace, na kuma shaida akan ka'ida komai ya faru".

Hankali Baffah ya kwanta sosai ya ce "To Allah ya rufa asiri".

Mk ya mi'ke yana cewa "Yau ba doguwar hira Baffah na ji kunya ba ka'dan ba".

Murmushi Baffah ya yi tare da cewa "ja'iri da kana jin kunya da baka yi abin da ka yi ba".

Ya rufe shago ya koma gidan ya tarar har lokacin Innah na zubawa Sa'a sababi da gorin ta ji kunya, ta yi ciki a gida. Ita kuma sai kuka take yi tana jin takaicin abin da Mk ya janyo mata.


Baffah ya ce "Mayar da wukar ki Salamatu! Bata hanyar banza suka same shi ba, ni dama ina da kyakkawan Ya'kini a ziciyata baza suyi hakan ba".

Takaici ya kama Inna ta shige daki ta barshi da Iyah, tana Jin irin rarrashinta da yake yi, tamkar ba abin ayi mata kashedi ta yi ba.

Ranar juma'ah Mk da kansa ya zo ya dauki Sa'adah! A mota sai kuka take yi.

Sai da suka zo kofar famfo ya ce "Fisabidillahi kukan nan na menene? Na ro'ki karki bata mini Rai".

Tara saura suka isa, taga irin daular da aka shirya mata, ta rungumo shi tana ta fa'din thank you Malam"!.
Ya ce "ki yi hakuri ban samu damar yi miki lefe ba wannan karon ma, ki bini bashi, idan komai ya dai-daita zan yi Miki"

Kwana suka yi cikin farin-ciki mai yawa ha'din kai da soyayyar da Sa'a ta nunawa Mk yasa ya dinga hawaye ba tare da ya san yana yi ba.

Da sassafe ta tashi ta shirya masa irin kunun gyadan da tasan yana so tare da wainar rogo mai dadin gaske.

Ya tashi ya ganta ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shaddar da ta karbeta, cikin jikinta ya' kara mata kyau da yarinta.

Ya dinga kallonta, a zuciyarsa sai faman godiya ga ubangiji yake yi.

Ta ce "wannan kallon fa? Ka tashi ka yi wanka ka zo mu karya ni wallahi yunwa nake ji".

Ya diro daga gadon yana cewa "zo muje ki tayani wankan".

"Ni na riga dana shirya dan Allah ka yi sauri ka fito".
Ya wuce toilet din yana cewa to 'Ranki ya da'de".

Cikin kwanaki ukun da ya yi a gidanta wadda shari'a ta bashi, ba karamin soyayya ya nuna mata ba, ba irin rawar jikin da bai mata, shekarun bakwai din da suka shafe cikin tashin hankali da ba'kin ciki sai da ya wanke musu a cikin kwanakin, har Sa'adah take mamakin maganar Innah da tace idan ta yarda da shi kafin ta tare, ba zai yi 'dokinta ba.

Ga mamakin Mk ranar da zai koma wurin Farida yini ya yi cikin zullumin kada Sa'a ta botsare, amma har 'karfe shida na yammaci ta biye shi suna ta harkar arziki.

Da zai tafi, ya rungumeta ya ce" idan na yi sallah zan wuce gidan Hajiya, zan kaita unguwa wata'kila kafin na dawo kin yi barci".

Ta ce "ba damuwa ma hadu da safe".

Da'di ya kama shi, ya dinga kissing 'dinta.

Suka rabu 'kalau, yana murnar addu'ar da yake yi mata na samun sau'kin kishi ya fara ganin tasirinta.

Yayin da ita kuma tana sallah tana kuka, tana ro'kon ubangiji ya sassauta mata kishi, ya bata jarumta da ha'kurin danne shi.

Kwananta hudu wata babbar motar daukan kaya ta zo shake da kayyaki, yini guda aka yi a bagaren Farida har washagari suna fama.

Ranar da juma'a kuwa wadda yayi dai-dai da satin Sa'a daya a gidan Mk ya dauko Farida da kansa.

Kai tsaye bangaren Sa'adah suka yada zango, cikin 'karfin hali ta karbe su, ta gabatar musu da ruwa da lemo har da abinci.
Cikin son K'ulla alaka a tsakanin su, Mk ya ce " kin zuba mana abinci tare, ke kuma kin koma gefe, dauko cokali kawai muci tare".

Ta daure ta ce "Na riga da na ci tun
'dazu".
Kallonta kawaya yi ya gane bata ci ba, sannan kokawa kawai take yi da zuciyarta.
Dan haka sai ya mike ya dauko mata spoon din da kansa.
Ta karba suka ci dukkansu uku a plate 'daya.

Ba magana sai karo a tsakanin cokula da plate.
Sai da suka kammala ya yi musu addu'a! Sannan ya roke su arzikin su zauna lafiya da juna, bayan ya tabbatar musu zai yi iyayinsa ya yi adalci a tsakaninsu, ya tabbatar musu dukkansu yana sonsu dan haka ba wadda zai musgunawa da gangan, ranar da aka samu akasi ya 'batawa wata, to ta yi masa uzziri yau da gobe ne, sannan dole idan ana tare dole a fuskanci matsaloli, sai dai kar a bari matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba.

Ya nisa ya kalli Sa'adah da kanta yake 'kasa ya sassauta murya ya ce" Sa'adah ta dago ta kalle shi sannan ta ce "Na'am"!

"Ku fa'da mini tsarin da ya muku wurin rabon kwana"

A sanyaye ta ce "Farida fa'di yadda zai yi".

Cikin nutsuwa Farida ta ce "Majority anfi yin kwana biyu, mu barshi a hakan mu ma".

Ya sake kallon Sa'a ya ce "Hakan ya yi miki?"

Ta amsa da "eh" a hankali.

Ya sake yi musu nasiha tare da shawartarsu su sanyawa ransu zaman ibada zasu yi, yin ibada tsabtatacciya kuwa sai mai hakuri mai kuma Imani na gaske.

Ya mi'ke yana cewa Sa'aadah "muje ki yi mata rakiya".

Ta bisu ba dan tana so ba, sai dan kar ya ga gardarmarta.
Da gaske ta dauki aniyar canji.

Suka isa bangaren Farida da ya 'kawatu da kaya na garari.

Duk yadda Sa'adah ta yaba haduwar bangarenta, da ta ga yadda aka narka dukiya a wurin Farida sai da ta girgiza matu'ka da gaske.

Jikinta ya sake mutuwa, bata fi mintina biyar ba ta mike tare da cewa"Allah ya sanya alkhairi".

Itama Faridan ta mike tana cewa "zo mu shiga mu ga gidan sosai mana".

Akan dole Sa'a ta bita, ta ga 'dakunan da suke falon wanda 'daya tsarinsa ya tabbatar mata Jawad aka shiryawa dakin.

Akwatuna da ta gani guda uku set, masu tsadar gaske, ya tabbatar mata kayan fa'dar kishiya Mk ya yi mata, Amma ita ko akwati 'daya bata samu ba.
Sai dai take ta tuno milyoyin da ya kashe mata, sai ta yarda ta kuma gane ba laifi ya yi ba.
Ta riga ta gamsu Mk bai kai 'karfin da zai zuba irin wannan kayan ba, ta kuma yarda idan har yana da ku'din yin hakan to ita zai fara siyawa.

Suka gama da dakunan suka yi kicin da yake shake da na'urorin zamanin da ba zasu lissafu ba.

Sa'a taki yarda da shiga dakunan su na cikin corridor wadda ta tabbatar sai ya ninka na falon 'kawatuwa.
Tunda dakunan Farida da Mk ne.

Har bakin kofar Farida ta rakota sannan ta juya ganin Mk na waje, ta sani rakiya zai yi mata, tunda wurinta yake ma'ana Faridan ce mai girki.

Sa'adah tana ganin Mk ta wuce shi fuu tamkar bata ganshi ba, ganin haka ya bita yana 'kiranta amma bata tsaya ba.

Har suka isa bangarenta, ta zauna a falo ta fashe da kuka, jikinsa na rawa ya ru'kota, ai kuwa ta dinga dukansa ta ko ina, ganin dukan ba mai illah bane, sai ya sunkuya mata sosai ta yadda zata ji da'din dukan nasa.

Sai data gaji dan kanta sannan ta barshi, shikuma ya janyota ya rungume.

Ya dinga karfafa mata guiwa, tare da zugata, har ya samu ya zagwanyar da rikicin da ya taso mata.

Sai da ya kaita har 'dakin barcinta, ya jira ta yi wanka, ta kwanta ya lulluba mata bargo.

Sai a lokacin ta ce "Malam" !

Ya amsa Mata da cewa "Na'am my dear Iyah"!

Cikin rauni ta ce "Amana dai itace amana! Haka cika alakawari sai mai Amana, kar ka bari a kwace mini kai, kar kuma ka saba al'kawarin ni zan jagoranci zuciyarka".

Ya kamu da tausayinta! Ya sani irin kayan alatun data gani an zubawa Farida shi ya sanya ta karaya.

Ya matsa jikin gadon ya ru'ko hannuta ya ce "shekaru uku na yi da aure amma ba a kwace miki ni ba, sai yanzu da muke tare?"
Ki daina shakku Malam 'din kine har yanzu, har kuma gobe".

Hawaye ya zubo mata ta ce "Na gode sosai! Sai da safe".

Ya ce ai ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba".

Ta kuwa murmusa sosai, ya sunkuya ya yi pecking dinta yasa hannu ya shafa cikinta.
Ya ce Good night and stay blessed".
Ya kashe mata fitila ya fita.

Ta dinga shafa daidai inda ya shafa cikin, tana Jin kaunarsa na ratsata.
Ta nisa tana hakaito kayan da Mk ya siya ya zuba mata ta tabbatar duk yadda Ma'aikatar shari'a take da albashi mai tsoka, sai ta shafe shekaru uku zuwa hudu kafin iya tara kudin siyan irinsu, ta tabbatar Farida kuwa iyayenta suka yi mata.

Ta share hawayenta tana Jin tabbacin ko a birnin Abuja ba za'a raina mata nata kayan ba.

Satin da ya zagayo aka yiwa su Jawad hutu.
A hanyar su ta dawowa ya ce "Malam".

Mk ya amsa da cewa"Jawad".

"Dama wannan hutun ma ka ce mini ina nake son yin hutuna?"

Dariya ta kama Mk ya ce "Dama ka bari muje gida tukun".

Suka wuce Gadon 'kaya Jawad ya ce "Malam zamu biya wani waje ne? Na ga mun wuce hanyar gida".

Ya ce "Na manta wani file a office ne, shine zamu je na dauko".

"Ok" Jawad ya fa'da a gajarce.

Suka iso mai-gadi ya bude musu.
Jawad ya kasa hakuri, ya ce Malam ko kun yi parking zuwa wannan gidan ne?"

"Mun dawo last two weeks"
Mk ya amsa masa.

Farida tana wurin aiki.

Kai tsaye bangaren Sa'adah ya nufa da shi, bata falo, Jawad ya fa'da kan kujera ko sandal dinsa bai cire ba.

Ya ce "Wow falon nan so mashallah! Ya 'dago a zabure ya ce Malam amma ka san me nake ji?"

Kafin Mk ya yi magana ya zarce da cewa!

"Ina jin irin 'kamshin gidan Maman Gombe (Sumayya) sannan ina jiyo 'kamshin Mamina! Aunty ta canja turare ne ko kuwa kewar Mami da nake yi ne?".

Mk ya zuba masa ido yana gasgata kaifin kwakwalwar yaron.
Kafin ya bashi amsa Sa'a ta fito cikin tattausar yadin material doguwar riga bubu, ta yi kyau sosai.

Jawad ya daskare a zaune, ya murtsuka idanuwansa yana son ya tabbatar ba Farida ce take yi masa gizo ba.

Ya budesu sosai ya tabbatar itace mussaman da kamshinta ya sake cika gurin.

Ya kuwa fasa ihu ya kwasa a guje zai wawurota.

Mk ya yi hanzarin ru'ko shi ya ce "Wallahi ba zaka ka kayar da ita ba, tana fama da kanta.

Da Jawad ya rasa yadda zai yi, sai kawai ya yi tsalle ya 'dane Babansa.
Yana fa'din thank you world best Father!
Ka cika promise, na dawo na tarar da Mami a gidanmu, thank u very much Malam".

Ya sauko ya nufi uwarsa cikin nutsuwa ya rungumeta, haka kawai sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka.

Itama ta dinga hawaye. Mk ya kallesu da tarin 'kauna ya ce "To kukan kuma na menene, ban da dai kin 'bata shi da kukan shagwaba, maimakon ki hana shi sai ki taya shi kuma?"

Bata kula shi ba, ta ja hannun Jawad ta zauna akan kujera shi kuma ta dora shi a cinyarta tamkar 'dan shekaru biyar.

Da azama Mk ya mayar da shi kan kujera ya ce "Ban son haka! sai ya buge ki? Ai kinsan ba lafiya ne da ke ba, da zaki sun'kuma wannan 'katon yaron a cinya, garama a samo masa 'kanne da yawa, ko ke da shi kwa yarda ya girma".

Tissue ta dauko tana goge fuskarsa tana fa'din "is ok, ya Isa haka".
Sun dade kafin su samu kansa ya daina kuka.
Sai da ya yi wanka a dakinsa da aka shirya masa da kayan katako irin na 'kasar Turkey

Ya fito falon yana cewa "Dakin nan nawa ya birge ni, ya mini kyau".

Mk ya tuna kayan da Farida ta siya ta zuba masa a dakinsa na gidan gadon Kaya, masu tsananin tsada, amma bai ta'ba nuna sha'awarsa ba, bare ya yaba.

Ya sake hakaito a yanzu haka dakinsa na bangaren Farida ya ninka wannan 'kawatuwa, amma ya san halin Jawad sai ya fi son wannan saboda shine na side din uwarsa.

Yamma liss Farida ta dawo, a ranar Sa'adah ta karbi girki.
Da ke Jawad a Farin ciki yake da sauri ya je ya yi mata barka da zuwa.

Sai da dare ya yi Mk ya rufe ido ya ce Jawad ya tafi dakinsa na bangaren Farida ya kwana a can.
Akan dole ya tafi, Sa'a ta bishi da Ido.


Washagari tun sanyin safiya ya dawo side din uwarsa haka kullum yake yi.

Rannan Mk ya balbale Sa'a da fa'dan itace bata nuna masa ya dinga zama a wurin Farida.
Murya na rawa ta ce "Kullum ina yi masa fa'da, ji ne ba ya yi".

Yana fita ta kalli Jawad da yake rakube a gefe ta ce "Ka ji da'di, da ka janyo mini bacin rai".

"Ni wallahi Mami na gaji! A U.k. ba ayin haka, kowanne yaro ana barinsa ya rayu a inda yake so, bare ni da nake so na zauna tare da uwata".
Ya fa'da da bacin rai.

Mk da ba nisa ya yi ba, ya juyo daukan wayarsa.

Ya ji Sa'adah tana cewa "Ai shikenan tunda ba zaka dinga jin maganar da nake fa'da maka ba, idan wani hutun ka dawo kaga ba nan din na koma gidan Baffah, ai ka zauna dole a inda ya ce maka".

A sanyaye ya jiyo Jawad ya ce "sorry Mami na daina, zan dinga zama, har sai na yi wanka na karya.

Ya hango ta mika masa yatsa tana cewa "promise".
Wato ya miko nasa yatsar su K'ulla al'kawari.

Sai suka tuno masa da rayuwarsu ta baya.

Wannan hutun ba inda Jawad ya je ya kwana, ko gidan Hajiyar Bichi yanzu ya'ki kwana ta dinga yi masa gorin tunda yana ganin uwarsa, shiyasa yanzu baya nemanta tamkar ba shine yake kuka idan ance ba zai kwana a wurinta ba.

Haka hutunsa na sati uku ya qare, Farida da Mk suka mayar da shi.

Sa'adah har ta shirya Mk ya murje idonsa ya ce ta zauna a gida ba zata je ba da Farida zasu tafi.

Har sun shiga mota ya kasa tafiya ya kalli Farida ya ce a minutes please.

Ya nufi side din Sa'a ya tarar da ita zaune a falo ko mayafin bata cire ba.

Ya ru'ko hannuta ya ce "Na kasa tafiya sabaoda baki mana addu'a ba".

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Ku dawo lafiya".

Ya kirata a tausashe, ta dago suka zubawa juna ido.
"Fishi ki ka yi ko?"

Ta kasa cewa komai.

"Ki yi hakuri! Na sani kina son zuwa, amma tunda da ita muka saba kai shi da zuwa visiting bai kamata yanzu na canja ba, zata dinga jin damuwar rashin haihuwarta, sannan kema wahala zaki yi, tausayin ki nake ji".

Ba walwala a fuskarta ta ce "Na fahimta, sai kun dawo".

Ya yi sukuri ya numfasa ya ce "Then smile".
Ta tura masa baki gaba tabbacin ba maganar murmushi.
Ya dara ka'dan ya ce "Akan 'dan fari kike wannan fishin, ke ko alkunya baki iya ba?"

Ai kuwa nan da nan tasa hannunta ta rufe fuskarta tana fa'din"Bana so Malam " a shagwabe.

Yasa hannu ya bude fusakr sai ta runtse idanuwanta tana murmushi murmurshi, kunya, kunya.

Da haka ya lallaba ya tafi suka rabu k'alau.

Zuwa yanzu hankalin iyaye, da dangin ma'auratan ya kwanta.
Haka Mk yana iyakacin kokarinsa na kamatan adalci na gaskiya a gidansa.
Amma idan ya kebe da Sa'a baya iya mallakar kansa.

Ta bangaren matan nasa sun gamsu Mijjinsu ba munafikin namiji bane, sai dai kowacce tana ganin yana fifita yar'uwarta.

Farida har zuciyarta ta gamsu yana yi mata adalci, amma ta san yafi son Sa'adah, Dan haka take zargin yafi walwala da kuzari ranar girkin Sa'a.

Sa'adah kuwa gani take yi, Mk tsoron Farida yake yi, mussaman yadda yake tirsasa Jawad sai ya zauna a wurinta, sannan yafi fita unguwa da Farida akanta.
Kawai hakuri take ta yi, dan kar ace itace babba sannan itace mai yawan korafi.

A haka rannan sun je gaida Hajiyar Bichi da bata jin da'di, da kyar Mk ya shawo kan Iyah ta yarda su tafi tare, dan kuwa da tace ya tafi da Faridan ita zata je daga baya.

Zuwa wannan lokacin cikinta wata bakwai, ta yi wani irin girma, fuskarta ta fara aunewa, haka baki da hanci tabbacin yadda cikin Jawad ya mayar da ita haka ma wannan zai yi mata.

Farida ta yi matu'kar mamakin yadda ta ga Sa'adah da tsohon ciki, tunda ba kasafai suke haduwa ba.

Wani irin kishi ya shaketa, amma sai ta yi ta addu'a tana namen tsari da yin jayayya a hukuncin Ubangiji.

Kai tsaye Sa'a bayan mota ta shiga, matu'kar zasu fita tare dukkansu, ta sallamawa Farida gaban mota, wanda hakan na matu'kar yiwa Mk da'di.

Duk yadda take boyen cikin sai da Hajiya ta gane Sa'a ta kusa sauka tabbacin da ciki ta tare, tunda basu cika wata hudu da tariyar ba.


Sun dawo gida, maimakon Farida tabi Mk zuwa side dinta, sai kawai ta bi Sa'adah akan ta baata dambun da ta yi, tunda ta ga ta kaiwa Hajiya.

Suka shiga, kamshin wurin yana matu'kar birge Farida amma ba zata iya tambayar wanne irin spices ne mai bada wannan kamshin mai kamawa ba, ga turaren wuta sai kamshin ya hadu ya ba da wani irin kamshi mai kwantar da zuciya.
Duk da cewa side din Farida shima kamshi na mussaman yake yi, amma kamshin wurin Sa'a yafi kwanta mata a rai ko dan kishi ne oho.

Sa'adah ta zauna tana haki, ta ce shiga ki dauko muku ya nan a cikin warmer.

Ta shiga kicin din tana kallon komai, kayan tsilla tsilla amma kuma unique.
Ta fito ta ce "Na gode sosai Gogel".

Takaici ya kama Sa'adah wato Farida ba zata daina yi mata izgili cikin dabara ba.

Ta tuna sunan garin su Farida Torondi, Amma bata ta'ba kiranta da hakan ba, ta tuna yadda yan set dinsu suke ce mata Taller saboda tsayinta, amma ita bata fa'da mata hakan ba.

Ta sake tuna yadda ko Farida bata fa'da a gaban Jawad sai dai Anti! Amma shine ita zata dinga ce mata Gogel, ta tuno har a asibiti ta yi mata kashedi, amma saboda tsokana sai ta sake fa'da.
Ta yi tsaki tana tunanin abin da zata yi mata idan ta sake.

Ai kuwa washagari zata fita wurin aiki ta leko ta kawo mata dish dinta.

Suka gaisa lafiya Lau ta kai kicin ta ajiye mata.

Zata fita ta kalli yadda Sa'a ta zama gari guda.

Ta ce "Gogel indai ba twins bane a cikinki, gaskiya kin kusa sauka, sai dai kuma na ga sai yanzu ne muke shirin four months a gidan nan".

Kafin ta rufe baki Sa'a ta yun'kura ta ce "Idan zaki iya tuna kwanakin da kika yi ba kya ganinsa da rana, ba ya cin abincin ki da rana, to sune kwanakin da aka samu cikin, shi ya yi abinsa bayan an shafa fatiha ba wai shege bane".

Nan da nan Farida ta muzanta ta ce "me ya kawo wannan maganar kuma Gogel?"

Ai kuwa Sa'a ta ce "Tsugudidinki da tsokanarki, ta nunata da yatsa ta ce "Taller ki fita a idona tun muna shaida juna".


Ga mamakin Farida sai ta ji Sunan da Sa'adah ta kirata da shi na Taller ya yi mata zafi ba ka'dan ba.

Idonta ya ciko da 'kwallah ta ce "Sa'adah daga wasa?"

Daidai lokacin Mk ya shigo!
Sa'adah ta ce "ke Kika san wannan, to bana son wasan indai irin wannan ne".

Ai kuwa Farida ta hau hawaye.

Sa'a tana kallonta bata yi mamakin hawayen data fara dan ta ga mijinta ba, da'din abin dai bata isa tasa ya daketa ba.

Ai kuwa Mk ya nemi jin ba'asin kukanta, ta ce Ba komai".


Ta juya ta fita, shima ya bi bayanta, bai yarda ta fita da damuwa ba, sai da yaga ta saki ranta, da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, ya rankwafa ta windo yana cewa "drive with care please".

Yayin da zuciyar Sa'a tamkar ta fashe saboda duk tana hangensu ta windo.

Sai da Farida ta tafi sannan ya koma wurin Sa'a ya sameta, ya dinga yi mata sababi akan ta zo wurinta ne zata wulakantata har ta sakata kuka, har yana fa'din ke baki san halin Farida da son raha ba, ki dinga jin tausayinta mana".

Ba'kin cikinsa yana neman kassarata.
Ta hadiye kukan ta ce "Ai yanzu na gama ganeka, ita bata laifi, komai ta yi daidai ne, kome take so haka zaka yi mata, saboda ita din Babanta zai siya mata kowanne irin miji".

Ai kuwa ya hassalo yana fa'din "wulakanci ki ya tashi ba? Ni kika fa'dawa wannan maganar?"

Ta kasa magana saboda a yanzu shakkarsa take ji sosai, ba kamar da ba, hawaye ya balle mata.

"Ta ce ta zo har 'dakina ta tsokane ni, bayan ka san har fa'da maka na yi akan ka yi mata togaciya, amma ba bincike ba komai, ka bi bayanta, ka rarrasheta, ni kuma ka zo kana mini jidali".

"Jikinsa ya yi sanyi, fishinsa ya sauka, ya isa gareta da nufin rungumeta, ta goce ta ce "Tun bamu je ko ina ba kana son sai na gaza".

Ya sassauta murya ya ce "Tausayinta nake ji, bata da lafiya sosai, bata samu haihuwa ba, sannan na fi son wata akanta, fa'da mini dan Allah bata cancanci a ririta farin-cikinta ba?"

Ta zuba masa ido ta ce "Ban son wannan tausayin da ka tsananta akanta, ina jin fargabar abin da nake gani a idanuwanka akan lamarinta".

"Ni meyasa baka jin tausayi na irin haka?"

Ba ja in ja ya ce "Ina tsananin sonki Ubangiji ne shaida, kina da cikakkiyar lafiya, Ubangiji ya hore miki, kina haihuwa Ubangiji ya arzurtaki, Ubangiji ya arzurtaki da mahaifin da ba kowanne 'da ne yake samun irinsa ba.
Fa'da mini ta inda baki kereta ba".

Ya ru'ko ta, tana cigaba da kuka tana cewa "Allah ka bawa Farida haihuwa ko wannan tausayin da yake neman zame mini barazana ya yi sau'ki".

Haka ya lallabata.

Haka da Farida ta dawo, ya ja kunnanta da cewa "da bakin ki, kin ta'ba cemin kina fakar idon mutane kina tsokanarta, to ki bari tunda bata so, Nima bana so, ki kiyaye bana son muna samun sabani".

Ta

Please Login or Register in order to submit comment