You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni wata azabar take yi, bata daukan wayata, jiya kuma 'kaddarar zan yi gamo da ba'kin ciki ta kawo ni shago, kawai sai ganinta na yi da wani dan guntun halitta sun zo tare a motarsa, a gaban motarsa fa ba mayafi sai wannan rigar da hular lauyoyin da basu rufe kwalliyarta ba, gaban rigar bai rufe komai ba".

Ya fada yana dukan sitiyari, Mahmud shima ya ji kishin yaron ya kama shi, amma ya daure ya ce
"Kai ka bada kofar da zata yi hakan da ka mayar da ita tuntuni da bata zo tana sake shayar da mu wannan ba'kin cikin ba".



'Karfi ya shanye dukkan yadda zuciyarsa take bugawa ya ce "Mk tsakani fa da Allah tsananin rabo ne zaisa yarinyar nan ta saurare ka, ka yi mata zunubin da 'ya'ya mata basa yin sassauci a cikinsa, ka tsaurara kwarai da gaske. Ka yi tsam da ranka wallahi ko Baffah kawai dan zuciyar sa irin ta mutanan da Allah ya zaba ya musu alheri da ha'kuri ne. Banda hakan da tuni gaba ne a tsakanin gidanjenku, amma ko ni din nan Baffah ya na mutuntata ni adalilin ka! Barah gaf da zaka dawo ranar juma'ah ya mini waya akan idan ba damuwa na zo washagari asabar dan Allah. Na taho cikin wasi-wasin menene ya faru, ina zuwa sai ce mini ya yi Daurin aure zamu je Bichi, za'a yi auren cousin dinka, baka nan bai kamata bamu halarta ba, muje mu wakilce ka, a hanyarmu ta dawowa ya ce mini ya ji dadin tafiyar mu domin na debe masa kewar ka kwarai da gaske. Wlh da na dawo gida sai da na yi hawayen tausayin bawan Allahn nan, sonka yake irin son da babu algus, gefe daya kuma na dinga jin kunyar matakin da ka dauka akan jininsa, matu'kar da gaske son Sa'adah kake yi sai ka na'de kafar wandon jure dukkan borenta har mu samu ta zo hannu".

'Karfi ya zarce da fadin "Ka gama da ita, ka sha da ita, ba abin da zata yi maka ta huce tarin takaicin da ka cusa mata".


Jikin Mk ya yi sanyi yana ayyana ina ma zai iya fitowa ya fa'di irin abin da ta yi masa da ya tabbatar an gane shi din adali ne na gaske, domin aure ba adadi ya mutu a irin wannan matsalar sannan kuma zubewar mutunci shi ya biyo baya, tunda duk macen da aka saka adalilin tana mu'amala da wani namiji komin kankatar muaamalar kuwa mutane da yawa zasu mata hukuncin babbar mu'amalar take yi.

Basu zame ko ina ba sai gaban Hajiyar Bichi suka fa'da mata abin da Alh Isa ya ce.

Ta yi jugum ta ce "Ashe kuwa Allah ne ya so ni domin wlh ni kaina kunya ce ta sa nake ta jan kafar zuwa gidansu Sa'a, yanzu kuwa na fasa ba zan iya ba, maganganun Babanku akan turba suke, yanzu ne kake so mu shige maka gaba alhalin a farko ka nuna musu baka da iyaye".

Hankalin Mk ya yi tashin gauron zabi.

A hankali ya ce " Amma Hajiya da bakin ki kika ce zaki rarrasar mana ita".

Ta ce " eh na fa'da amma yanzu na gane bai kamata na shiga ba, domin a lokacin da yarinyar nan take cikin tasku ai baka yarda na yi iko irin na uwa da kai ba, ka ga kuwa bai kamata ace yanzu ita na yi mata karfa-karfa ba, tunda na san da dukkan zuciyarta tana sona tana girmama ni, ku je Mahmoud ya taya ka, zan biku da addu'ar dacewa ubangiji ya huci zuciyarta, amma ni kaina ban jin zan iya yafe irin abin da ka yi mata idan aka yi mini irinsa".


Idonsa ya ka'da ya ce "wai har me na yi ne haka Hajiya? Saboda na zabi na bar abin da ta mini a zuciyata shine kuma sai aga ni na zalunceta, na san dai laifin bai wuce kawai dan na yi aure ba".

Daga 'Karfi har Hajiya suka hada baki wurin cewa " Ai kuwa ya fi karfin ace kawai, kai yanzu ka barta ta auri wani mana indai kawai ne".

"Bana son haka 'Karfi bana son wannan kwatancen"

"A a ba da Mahmoud kake ba, da ni kake, ni kuwa ba yadda zaka yi da ni, domin ko yanzu Sa'a za ta yi wani auren da kaina zan jagorancin kaita dakin mijinta".

"Dan ka ji irin ciwon da ta ji alokacin da ka tura ubanta ya nemo maka aure".

Da rawar murya ya ce "Haba Hajiya! Haba mana! ni ban tura Baffa ba, kawai na fa'da masa zan yi aure, shikuma saboda yana mini kallon Ni 'da ne a gunsa ya shiga cikin harkar tsundum, amma menene laifi na anan?"


Hajiya ta ce "Baka da laifi ko kadan, yanzu na gane kawai sanin ya kamatansa ne ya yi yawa. Bai kamata kuma ka ji haushi dan nima zan nuna irin nawa ya kamatan ba".

Tashin hankalin da Dr 'Karfi ya lura ya fara bayyana a jikin Mk yasa shi cewa "Ha'kuri dai zaki yi Hajiya, dole a samu Babban da zai taya mu nema da rarrashi"

Hajiya ta ce "To sai kuje ku laluba a wani gurin ko za'a dace, sai ku tafi Bichi ko 'Karfi ku samo ai hidimar dan dangi bata lami".

Daga haka ta ce "Na sallame ku sallar walaha zan yi".

Kwanaki biyar Mk ya na fama da matsanancin kishi da damuwa domin ya kasa ganin Iyah sannan idan zai kwana yana kira ba zata dauka ba, ya lura idan bata ganinsa ta fi jarumta sabanin idan idanuwansu suka sarke da na juna zuciyarta take kasa boye sonsa da yake cikinta.


Har gidan Sumayya ya je amma bai Samu ganinta ba adalilin ta cewa mai gadin ya ce bata nan, tunda ta san ba su yi da Alh Mamman ko Anwar wani zai zo ba.

Ranar juma'ah bayan masallaci ya samu Baffa a shagonsa a kuma ranar ya dawo daga Gogel.

Da sakakkiyar fuska Baffah ya ce "Ina fatan zuwa yanzu ka shawo kan mutumiyar taka ta daina fishin kun shirya kanku?"

A raunane Mk ya ce "Ai sam ta'ki saurarona Baffah, jiya har Bichi na je wurin su Baba umaru akan su zo, su bawa Baba Isa hakuri, sai kuma su zo wajenka, amma kowa ya ce shi ba zai zo mini ba, kunyar abin da na yi maka suke ji".

A filin gurin Mk ya durkushe kan guiwowinsa ya ce "Ina sake bada ha'kuri Baffa! Ba zan ta'ba gajiya wajen neman afuwa da alfarmar kar ka kullace ni ba, kaddarar mu ce a hakan amma ba da gangan na yi hakan ba".


Baffa ya dago ya ce" Tashi ka zauna kada ka 'bata rigar ka"

Sai da ya nisa ya ce "kullum ka yi mini irin wannan rokon Mutari ina jaddada maka ba auren Iyah bane ya hadamu, ba kuma zai zama silar rabuwarmu ba! Yanzu kana tunanin har sai ka sake turo mini iyayen ka da na baka aure? Kawai wadda zai karbar maka ne zaisa na jira sai anzo tunda dai dole iyayenka da jini ya hada ku, sune a hakku akan ka, indai ba ina son na shiga al'amarin zumunci ba ne, ka kwantar da hankalinka ni sai na je na same su da kaina, a ko ina ni mai Nemo maka aure ne, ni so nake ka shawo kanta ko yaya ne, kasan tana yarinyarta ma cewa na yi ka nemi yardarta, to yanzu ma nemi yardarta ko ya ya ne idan ya so sai naga ta yadda zan bullo mata".


Mk ya dinga godiaya yana cewa "Baffa gaskiya idan ba taya ni ka yi ba, ba saurarona zata yi ba".

Farin-cikin Baffa ya kasa 'boyuwa saboda yanzu ya gamsu idan Iyah ta koma hannun Mutari zata yi daraja sabanin shekarun baya da ta koma din sai dai ta yi zaman hakuri da taka tsantsan.


"Ya labarin Jawad kuwa?"
Baffah ya tambaya.
"Rana ita yau ne hutun su in Sha Allah".
Murmushi sosai ya bayyana a fuskar Baffah har ransa yake jin kaunar Jawad fiye da ta su Khalifan Sumayya, wata'kila soyayyar uwarsa ce ta shafe shi. Ko da yake ai Mk ma na daban ne a wurinsa.


Kamar da rada Baffa ya ce"tana cikin gidan dazun nan ta zo mini barka da zuwa, je ka ku gaisa mana".

A kunyace Mk ya ce "Bata daukan 'kirana, har gidan Aunty Sumayya na je amma bata fito ba"

Jeka dai yanzun! Ina hango ka shiga zaure zan mata waya ta fito kamar zata karbi sako".

Mk ya rasa mai zai ce a duniya idan aka cire iyayensa biyu ba wadda yake sonsa yake karrama shi irin Baffan Sa'adah.

A matu'kar kunyace ya ce "Baffah na gode sosai Ubangiji ya fini yabawa, in sha Allah komai Iyah zata mini zan yi ha'kuri da ita muddin rai, ina maka al'kawarin zan ri'ke ta fiye da ri'kon farko, ka bimu da addu'a".

Da sakakkiyar murya Baffa ya ce " Bana jinka Mutari! Amma yau zan fa'da maka wani abu da ba wadda ya sani sai ni da ubangijin zuciyata.
Iyah itace abu mafi soyuwa a gare ni, ban taba mallakar wani abu da ya fita a gurina ba, ko mutuwa na yi idan kana ayyana ina ma ina nan da ka mini kaza. Na ro'ke ka duk abin da ka raya a zuciyar ka zaka mini na kyautatawa to ka yiwa Iyah shi. Basu da 'dan'uwa namiji ka taimake ni ka zame mata miji kuma 'danuwa, ta wahala akan ka, ta yi kukan rashin ka, na ro'ke ka kar ka bari ta yi kukan ita ubanta talaka ne, amanarta nake baka".

Hawayen tausayin Baffah ya kwacewa Mk ba tare da ya shirya ba, amma yasa dukkan karfin zuciya ya ce "Na karbi amana, na karba da dukkan zuciyata, zan taya ka sonta, zan jiyar da ita da'di, sai dai yau da gobe dole za'a samu sabani, mussaman da yake ita din Yar daru ce sosai. Wata'kila sai kana mata rubutun rage daru Baffah".


Murmushi sosai ya yi "ya ce zungurar ta kake yi Mutari, amma yanzu ai ta girma ta yi hankali wani abin ba zata yi su ba! Jeka kar lokacin maghrib ya karaso baku gaisa saosai ba".

Yana isa bai fi da minti biyu ba, ya fara jiwo takun dogayen takalmanta mai tsinin gaske, kamshin ta ya riga ta isowa. Kwalliyarta na cikin abubuwan da ba zata iya dainawa ba.

Ta karaso cikin taku 'dai'dai tamkar wata hamshakiya sanye cikin Riga da skirt na atamfa kalar ruwan hoda da fari.

Dinkin ya zauna tamkar a jikinta aka yi su.

Farin mayafi ta sanya dan haka takalmin kafarta ma fari ne mai tsananin tsada, da Mk ya lura zai gane wanda Jawad ya sa shi siya dole ne, wadda fa'dan kudinsa a lissafin naira sai aga tamkar fariya ce zata sanya a zuba wannan ma'kudan kudin a siyi takalmi kafa daya.

Sosai ta yi kyau domin ta zubawa fuskarta kwalliya, hakanan sabon kitsonta na shuku ya taimaka wurin kawata daurin dan kwalinta.
A ransa ya dinga yabon kyaun halittarta. Ya dinga tasbihi da hamdalar yadda aka jefa soyayyarsa a zuciyar wannan halittar da take tsananin daukan hankalinsa, duk tsawon shekarun da ya shafe a duniyarsa bai ga wadda ta zarta Sa'a iya tsara kwalliya ba.

Bai ga wadda take zuba ado iya ado ba tare da fita zata yi ba, ya fahimci tana samun farin ciki a cikin kwalliya, bata ta'ba bashi matsalar wai bai yabi kwalliyarta ba, yi take domin ta zame mata jinin jiki.

Ta wuce shi tamkar bata ganshi ba, ta fita kofar gidan, ta shafe minti biyu a tsaye, yayin da zuciyar Mk take wani irin bugu, mayafin jikinta iyaka cinsa kafadarta wadda tunda ga kanta ta na'de shi, gata a tsaye skirt dinta ya matu'kar fito da zahirin surarta, ba namijin da zai kalleta ya tsaya a iya kallon sharia guda daya, dole sai ya sake yin kallon bawa ido hakkinsa.

Mk ya dinga jin wani irin tashin hankalin yadda take tsaye a tiiti a hakan, anya akwai wadda ya saki matarsa a duniya amma yake dandana kudarsa kamarsa?

Can ya juyo ta tana cewa"
Baffa na dade da fitowa banga kowa ba"

Ta juyo da nufin shigewa ta bar shi fuskar nan daure tamkar hadarin da ya gama tunbatsa.

"Zo mana Dawisu sarkin ado, ni ne mai baki sakon ai".

Ta yi kamar ba ta ji ba, ta doshi hanyar shigewa da azama ya sha gabanta, ya ce "kwanakin baya fa a gabana Baffa ya ce miki ko rago ya kawo ya kamata ya shiga rigarsa".

Ta turo baki ta ce " Ai son rai ne yasa shi fa'din hakan, ya san komai yake so ina taya shi son abin ina kuma girmama shi. Amma kai Baffa ne yake sonka ya daukaka lamarinka ya girmamaka. Yayin da kai baka sonsa kana amfani da shi ne dan cikar burinka da zarar ka samu, zaka iya ture komai ka kunyata shi, ka cusa masa takaicin da yake fakar idon mutane yana goge hawayen ba'kin cikin ka".

Idonta ya ciko da hawaye, ta shanye ta zarce da fadin " wannan karon wallahi har Baffan na shirya shayar da shi mamaki tunda baya kishina. Matu'kar Sharia ta damka mini zabin mijin aure a hannuna to ina tabbatar maka zan yi iyakacin yi na na dora hukuncin Sharia akan hukuncin Baffah. Ka rabu da ni, ka daina zuwa wurin ubana, kai ba 'dan-uwanmu bane, bamu da alakar komai da kai, akan me zaka zo ka dinga yi mini katsalandan a tsakanina da ubana, alhalin lokacin da ya kamata na shiga rigar uban nawa nuna mini ka yi bai isa ba, amma yanzu kana mini karfa karfar dole ka shiga rigarsa".

Jikin Mk ya yi sanyi kwarai da gaske ya ce "Allah dai ya so ba daga sama na fado ba Sa'adatu, kina yawan yi mini gorin bamu hada komai ba, na yarda bamu hada komai ba, amma Jawad ya hadamu, Baffa ai kakansa ne wannan hadin ai ya wuce ace na zama bare".

Ta kufulo ta ce "oh saboda Jawad kake mini wannan bibiyar, kake neman hada ni ya'ki da tsohona, to albishirinka, duk duniya uwace kawai ta san ainihin uban danta".

Wannan karon bai kai hannu jikinta da niyyar duka ba, amma ya yi matu'kar kidima, wani irin tashin hankali ya bayyana a fuskarsa da jikinsa, sai ta ganshi tamkar ranar da ya saketa.

Ya jingina da bango yana fa'din"Ya Hayyu ya QAYYUM bi Rahamatika astagisu".

Abin mamaki tausayinsa ya shigeta soasai, amma ta daure ta hadiye shi.

Ido jawur ya kalleta ya ce "Ki yiwa Allah da Ma'aiki ki fa'da mini mai zan yi ki daina jifana da irin wadannan kazaman kalaman da suke nufin tarwatsewata".

Yana rufe baki ta ce "ka daina shiga tsakanina da ubana saboda kai Baffa ya mini abin da har na mutu ba zan daina takaici ba, ba zan daina zubar da hawaye ba, ba dan darajar sa ta zarta komai a gurina ba, wallahi da ba zan yafe ba domin iyakacin cin fuska anyi mini, ba kuma dan komai ba sai dan ya faranta maka".

Ya tausasa murya ya ce " Fada mini abin da ya miki saboda ni, na miki al'kawarin idan na ji kina da hujja ba zan sake zuwa wajensa akan maganar ki ba, ke kawai zan tunkara, ke kuma ai sai kin amince".

Murya na rawa ta ce "kasan dai ai kusan sadakata Baffah ya baka, Nima nasan haka aka kai ni ba wata hidima, amma dai naje da gadona da kayayyakin amafanin da suka fi zama Dole. Na so a mini kayan daki da lefe kamar yadda ake yi a al'ada amma na yi hakuri na bi ra'ayinsa, dan samun albarka.

Bayan mun rabu na tattara komai da nake ganin kamaar lefe na ne, har da gold dina sai da ya nutse na sayi filaye da zummar idan hidimar iyayena ko aure ya zo mini a siyar ayi hidima, kawai Baffa ya je ya siyar mini ya baka kudin ka yi aure kana jin dadinka ni kuma ko na mutu ko na yi rai ko oho".

Wani irin kuka ya kwace mata, fiye da wadda ta yi a ranar rabuwarsu a mota, sosai take yinsa saboda yadda abin yake dafata.

Kukan da take yi ya wanke bacin ran da ta jefa shi a farko.

Tausayinta ya maye gurbin takaicin maganar da ta caba masa ya ce "Tabbas ba a miki adalci ba Sa'adatu, amma ki yi hakuri, na yarda kuma Baffah ya na sona, amma ko daya cikin goman son da yake miki ban samu ba. Da ciwo sosai, da gaske kuma na taya ki jin takaici, amma bari na tuna miki wasu abubuwa, Ni dai na da'de ban ga mai sa'a irinki ba, tabbas kin ci sunan ki na Sa'a".

Ya nisa ya ce da" kin san irin soyayyar da Baffah yake Miki da kin ji kunyar takaicin ya siyar da abinki ya bani na yi aure."

"Da kin san yadda Jawad yake son ki, yake fatana ya girma ya yi ku'di dan ya jiyar da ke da'di, da ba abin da sai sake damun ki na dai wani abu da ku'di zai iya siyansa."

"Da kin san yadda nake son ki, nake kwana nake tashi da ke, nake jin kin fi duniya da abin da yake cikinta da baki yi kishin auren Farida ba".

"Bari yau na fa'da miki gaskiyar magana ba dan ki yarda ki karbi soyayyata ba, sai dan ki gamsu iyakacin gaskiyar kenan, ina da yakinin ban ta'ba yi miki karyar da ban cancanci ki 'ki gasgata ni ba".

"Farida na cikin jerin matan da ubangiji ya kaddara mini zan aura. Rabuwarmu ta zama tilas Sa'adah domin itama kaddarata ce. Kin sani idan ina tare da ke wallahi duk yadda nake zage 'kwanjina akan ki, zai yi wahalar gaske na iya aure, bani da wannan 'kwarin guiwar saboda tsananin son da nake miki. To fa'da mini ta yaya zan auri Farida alhalin hakan ya zama dole, na farko mutuwa na iya kauda ke, na biyu kaddara ta rabamu, kinga da ki mutu ki barmu, ai gwara kadarar rabuwar tunda idan da rai ai da rabo".

Sannan Dan Allah bai isheki daraja ba ace ke ce kika biya sadakin kishiyarki, ke kuwa ni zan biya na ki, na tabbatar abin da Jawad yake yi miki a shekarunsa ya isa ki gane ubangiji yana tare da ke".

Jikinta ya yi sanyi ta san kalamansa duka ba karya, illah wadda ya ce ta fi duniya, da hakane ai da sai ya bari kaddarar ta kasheta in yaso shima ya zauna jiran wa'adinsa babu aure har ya mutu, su hadu a aljannah su sake rayuwar da babu bacin rai, amma yanzu ya gama curarta ya bari wannan makirar da take boye ainihin kalarta, ta san komai nasa, ta mallake shi, shine zai zo ya mata da'din bakin wai ta zarce duniya? kai namiji Hankaka ne tabbas.

Ganin ta yi lakwas sai ya ce "kin gamsu kin yarda?"

Ai kuwa tamkar wadda ya mareta har huci take yi ta ce "Wallahi ko shiga kunnuwana wai kana sona fiye da duniya bata yi ba, na dai yarda Baffah da Jawad na zarce komai a gunsu".

Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "shikenan ba sai kin yarda ba. Ko ba kya sona mu komawa aurenmu, son da nake Miki, da wadda Jawad yake miki ya isa yasa ki rayu cikin farin-ciki".

Ta goge kwalla ta ce "har abada ba zan yi farin ciki a hannun ka ba, ka rufe idonka ka ce mini ina ha'intarka, ka rufe ido ka ce mini ana maka sharing dina"

Muryarta ta fara rawa tabbacin tsumin bacin rai ya taso, ta nisa ta ce "ka rufe idonka ka barni ka dauki wadda kasan na tsaneta saboda munafuncinta, ta faki idon mutane ta tsokane ni, amma sai ta layance a kuma bata gaskiya. Allah ne ya rufawa al'umma asiri ba karatun lauyanci ta yi ba, dan anga kwarewa wurin bada kariya ga karya".

Da 'kyar ya ce na janye kalamina, wallahi tashin hankali ne da kishinki, Amma nasan ha'inta dai babbar ha'inta ba zaki yi ba, na san ni ka'dai ne na muaamalance ki, na tabbatar da hakan har zuciyata".

Wani abu mai nauyi da ya danne kirjin Sa'adah shekaru uku ya fa'da mata sai dan saura.

Ta ce "to shikenan na yafe maka. Amma ka sani gaskiya ban da buri ko sha'awar auren mai mata kishi kashe ni zai yi, kawai ka barni na auri wadda zan sami nutsuwa, ka bar ni nima na dandana wani namijin kamar yadda ka ke dandana Balarabiyar Yemen".

A sanyaye ya ce "Sa'a ina jiye miki tsoron kar ki zama ajalina, domin kuwa banda lafiya, duk sadda na ganki sai kin yi mini fami a akan jinyar da nake yi".

Kai tsaye ta ce" Tunda bakin cikin ka bai mayar da ni gawa ba, na tabbatar kaima ba zaka zama ba".

Cikin gajiyawa ya ce "Next week Jawad zasu yi hutu, gaba'daya zai yi hutunsa a gurinki".

Maimakon ta ji dadi saboda ta san dan ya faranta mata ne yasa ya yanke wannan hukuncin, sai ta yi nufin gwasale shi.

Ta ce "bana bu'katar ganinsa ma bare ya mini hutu, inace saboda kar ya zo na zuga shi yasa ka kai shi makarantar kwana? Saboda kana son sai ya so Farida sama da ni yasa ka hana ya kwana a gidan nan sai dai ya zo ya yini? To shima na barka maka shi ban bu'katarsa, Ni kuwa a duniya me zaka mini na huce, ka zalunce ni iyaka".

Kafin ya yi magana sai ganin Innah suka yi, a ladabce Mk ya sunkuya ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, daga gaisuwar bata ko tambayi Hajiyarsa ba bare matarsa, ta juya tana cewa "kin dora girki kin barshi zai kone, daga cewa zaki karbo sako?".


Wannan shagulatin bangaro da Inna ta yi masa ya matu'kar dukan zuciyar sa, yana ganin rashin nasarar sa a fili, Bai ga laifinta ba ko kadan, domin ya fahimci tana kan fahimtar su Baba Isa da Hajiyar Bichi ne. Wato Baffah ne kawai hoope dinsa.

Akwai gumurzu kenan dan kuwa sai inda karfinsa ya kare, yanzu ne zai yi dambar jefa alkalamin sa cikin Tawada. Domin ya ga maneman nata dukkansu basu da makusa, shine ma mai tarin kalubalen rashin samun goyan baya a wurin iyaye da Sa'adatu sa'ar Mata.





Surayya Dee
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



*GAISUWA GA*
*HAUWA BELLO GANDI*.
*MUM KHADY*.

98-99.


Har sati ya zagayo Mk bai da nutsuwa, Farida kanta bata da sukuni adalilin halin da take ganin Mk a ciki, duk yadda take jin kishin Sa'adah sai take yin jarumtar boyewa.
Take ta hadiye sauyin da take gani a tare da shi, gefe daya ma sai take hilatar sa da bashi labarin fa'dansu da Iyah a FGC, idan kuwa ta yi hakan sosai ta ke samun walwalarsa ya yi ta dariya, hirar kuma ta yi tsayi.


Ranar dauko Jawad da wurwuri Mk ya tashi yana ta saurin tafiya, wani irin zumudin dawowarsa yake yi domin shine tsani na biyu da zai taimaka wurin shawo kan Sa'adah. Ya tuna yadda Jawad ya matsa mata ta gaishe shi ranar visiting. Ya sake tuna rokon da ya mata akan ta yarda su taho Kano tare, dalilin da ya zama sanadin da ta doke shi.

Ya dinga murmushi yana jin kwarin guiwa na shigarsa.

Tun jiya kuma Farida take ta faman hada masa snacks din barka da zuwa.
Domin a harkar Baking ta yi zarrah, abinci wahalar sarrafawa yake yi mata amma

Please Login or Register in order to submit comment