You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaji sai take fama da alawowi ko cingum, ko kuma kaninfari.
Matu'kar kuwa ba komai a bakinta to kuwa miyau zai cika mata shi.

Ga 'dan karen barci. Da kanta ta yiwa kanta alkalanci tabbas ciki ne da ita, domin tana iya hakaito haka cikin Jawad ya yi mata.

Duk da yadda ta gamsu tana da ciki sai da ta yiwa kanta gwaji da P.T strip, sakamakon kuwa ya kasance positive.

Wani irin tashin hankali ya dinga ziyaryarta, ita kuwa da wanne ido zata kalli Innah da kuma Anty Sumayya?.

Da wanne irin harshen zata musu bayanin da zasu gamsu, sau 'daya tak wani abu ya gitta a tsakanin ta da Mk, shima kuma ba da sonta da yardarta ba, fin karfi ya gwada mata.

Mk ya shammaceta kwarai da gaske, gashi yanzu ya dawo da asalin halayyarsa ta bagarar da ita da lamarinta.

Ta nisa tana tunanin hanyar da zata bi ta boyewa Innah halin da take ciki. Ta shafa cikin tana Jin wata irin zazzafar soyyaarsa na huda dukkan sassan jikinta.
Cikin Jawad ta same shi cikin kuruciya, da kuma sa Rai za'a samu tunda tana ganin da anyi aure ake samun ciki a haihu.

Cikin kanwarsa kuma bai zo mata a sadda take so ba, asalima unwanted pregnancy ne, sai dai bayan ta haifeta ta dora ido akanta aka dora mata sonta fiye da tsammani, a yanzu da hankali ya shigeta ta tabbata tana jin son cikin jikinta kwatankwacin yadda take jin son Jawad. Shine kuma cikin da ta yi 'mararin samuwarsa duk da bai zo a lokacin da ya kamata ba.

Washagari ta nufi asibiti, aka yi mata gwaji na sosai, sakamakon dai 'dayane da wadda ta yi da kanta. Ta dawo gida tana ayyana lissafin zuwanta Sokoto, lissafin cikinta wanda yana shirin shiga sati na biyar.

A yanzu ba abin da take so irin ta tare tun kafin a ankara da halin da take ciki.

Ta dinga tunanin yadda zata sanarwa Mk tana son tariya da wuri, ta tuna ranar da ya sameta gidan Sumayya kafin ya yi tafiyar, da muradinsa na son su tafi tare, Amma ta kekasa kasa ta 'ki. Ta nisa tana sake tuno sadda suke yiwa juna gatse, inda ita ta ce a bari sai nan da shekara guda.
Zuciyarta ta harba idan kuwa hakane har sai ta haihu, da kusan wata hudu.

"Tirkashi" ta furta a fili, tun yanzu kunyar Innah take ji, gashi dai a gabansu ta yi ciki, sa'ar da aka yi, ba cikin gaba da fatiha bane kamar yadda Inna ta gani a mafarkinta.

Kwanaki uku da zuwan Sa'a asibiti ta kasa daurewa saboda yadda kullum take Samun sababbin alamomin da Za'a fahimci halin da take ciki.

Da daddare tana kwance a dakinta, ta kalli agogo, ta ga lokaci ya fara ja, amma hakan ta kasa hakuri ta 'kira layin Mk.

Ringing biyu ya dauka, Yana ayyana zuciyarsa da ta Sa'aadah tare suke bugawa, domin kwnaciyar da ya yi ba abin da yake tunani sai ita, yana mamaki yadda bata neme shi ba, gashi har ya doshi kwanaki ashirin, amma ko ta 'Kira ta ji ko ya Isa lafiya.

Ya dauka! Amma ta yi shiru, ya nisa tare da cewa "Ina Jin ki, ta jima tana zumbure zumburen baki tamkar Yana gabanta.

Da kyar ta ce "Ina yini?"
Ya amsa da cewa "lafiya kuwa?"

Ta 'kulu amma ta daure ta ce "sai ba lafiya zan neme ka?"

"To na ga tunda na yi tafiyar nan ko Kirana ki ji yana isa baki yi ba. Ni kuma na kira ki ba adadi kin ki picking, saboda kawai ki nuna mini da gaske kike ba kya sona, ba kuma wani abu na alheri a tsakaninmu da cin arzikinsa"

Ya fa'da a dan tunzure ka'dan.

Ta yi shiru tsananin sonsa na ratsata mussaman cikin jikinta idan ta tuna bai yi gaggawar kaita auren wani ba, sai ta tsatson Mk ya fito sai ta ji kawai tana ambaton Alhamdulillah!

Babbar matsalarta kishin auren Farida , ta tabbatar da wata ya aura ma zata ji kishin amma ba kamar na Farida ba, domin shi ka'dai me dalilin da yake sawa ta ji tsanarsa da tsanar cigaba da kasancewar a doron 'kasa.

Hawaye ya cika idonta sosai, ta daure ta kuma cije bata bari kukan ya kwace ba, da rawar murya ta ce "yaushe zaka dawo?"

"Inace na fa'da miki sai na cinye kwanakin wata?"

Ta yi shiru!
Ya nisa ya ce "fa'da mini menene tunda na san haka kawai ba zaki nemi ni ba tunda kin ringa kin jefa ni sahun Marasa adalci da daraja a duniyar ki".

"Ni ni bani da lafiya ne".

Ta fa'da a rarrabe kuma a shagwabe.

"Me ya same ki?"

Ta yi shiru, ta kasa cewa komai.

"Na san dai ba kewata kike yi ba, tunda tuni kin cire ni a masoyinki".

"Dama zan fa'da maka ne, Anty Sumayya da Umman Fanshekara suna son zuwa su ga gidan da zan zauna".

Ya murmusa ya ce "Na san ki tamkar tafin hannuna, fa'da mini dai gaskiyar magana. Kawai ki ce kin fasa yin rabin shekarar kina son tarewa dan kar abin da kike boyewa ya bayyana a gaban su Baffah".

Zuciyarta ta tsinke, da sauri ta ce "me nake boyewa?"

Ya waske da cewa "Tarin Sona mana na zuciyar ki, bayan bakinki yana ta jifana da kiyayya".

Ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ni ai dama ban ta'ba cewa bana sonka ba, sai dai na ce da aure ne bana yi, saboda kaima ai ba ni kake so ba".

"Fahimtar ki ce hakan, kuma Wallahi ina taya ki jin kunyar ace kin rayu da ni shekaru bakwai, amma baki ki san wannene Mukhtar ba".

Ta katse shi ta hanyar cewa
"Ni yanzu me zance wa masu son zuwa ganin gidan?"

Kai-tsaye ya ce "ki ce ban kammala gyran gidan ba, sai nan da wattanni shida lokacin ya yi dai dai da kammaluwar na ki Shirin".

A mugun shagwabe ta ce "Bana son haka, bana so, ka daina daukar hakkina haka Nan".

Wani irin farin-ciki ya mamaye Mk ya ce "fa'da mini me na yi miki na daukar hakki?"

"Ni kawai ka fa'da mini gaskiyar abin da zan fa'da musu".

"Ki fa'da musu saboda kin ce sai kin gama shiryawa, ya sanya nima na shiririce. Da gaske ban tanadi inda zaki zauna ba".

Hakan da ya fa'da ya sa ta fashe masa da kuka sosai.

Ya matse dariyar da ta so subuce masa ya ce "Share hawayen ki kin ji my dear, ki bari idan na dawo sai mu yi maganar a nutse, ki fa'da musu bana gari, Amma da zarar na dawo, zamu tattauna".

Da yake son tariyar take yi a kwanakin nan yasa ta biye masa, suka rabu kalau.

Yana ajiye wayar ya dinga dariya yana fa'din Ubangiji ka kaddara addu'ar da nake yi ne ka karba, ubangiji ka kaddara hasashena ya zama gaskiya.

Ya yi shiru yana murmushi a zuciyarsa sai fa'dawa Ubangijinsa yake yi idan har ya tabbata ciki ne da ita azumi uku zai yi na godiya ga Allah, abin da ya da'de yana son ayi masa kenan haihuwa! yana son ya ga Jawad ya na da mahadi, yana son 'kananun yara.

Ya tuna lokacin da ya matsu Sa'a ta sake haihuwa amma kawayenta suka zugata wai zata tsufa da wuri.

Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai, a fili Kuma sai ya ce "Na yafe komai, na manta komai".


Sati biyu Mk ya dawo, zuwa wannan lokacin cikin yana shiga sati na bakwai, ta fara wani irin fari, sai kuma ya canja salon ba komai zata ci ba, asalima bata isa ta sha tsurar ruwa ba.

Sai dai ta sirka ya dai canja launi.
Ga miyau bai tafi ba.
Kullum cikin Hijabi take da safa, saboda yadda kafafuwanta suka yi fari, suka yi fresh, da zarar Baffah ya tafi Gogel zata tafi gidan Sumayya, saboda kada Innnah ta ganota.

Washagarin dawowar Mk ya iso wajen Sa'a da tarin tsarabar manja da kuma kwakar manja.

Da rawar jiki ta kai ta zubo a bowl ta dawo ta hau ci tamkar nama.

Ya zuba mata ido yana ganin sauyuka a tare da ita karara.

Zuciyarsa ya gama gasgata zatonsa. Ya dinga Hamdala a ransa.

Lafiya Lau suka gaisa, ba bacin rai.
Ganin Bai sako maganar da ya ce sai ya zo ba, ya sa ta kawar da fuskarta gede ta ce " Ya maganar da na yi maka?"

"Wacce?".


Ta tura baki gaba ta ce "su Anty sun matsa mini akan zasu je su ga yanayin windows da kofofi saboda maganar labule".

Ya cije ya ce "idan dan wannan ne ba matsala na riga na tanade su".

"Kar ku damu".

Ta juyo ta ce "Na damu ni na gama shiryawa ranar juma'ah zan tare".

Dariya ta kwace masa sosai, yayin da itakuma ta hau kuka marar sauti.

Ya kalleta sosai sai fahimci kuka take tunda ga zuciyarta ba wai na shagwaba bane.

Ya hadiye dariyarsa ya ce "menene kuma amma dai kinsan ban son irin wannan kukan ko?"

Ta kasa magana. Sai da ya dinga rarrashinta ya samu ta daina kukan.

A hankali ta ce "Akan me zaka mini dariya bayan abin da ka janyo mini?"

Da sauri ya ce "me na yi miki?

"Abin da ka yi mini a Sokoto mana".

"Oh sorry Sa'adah! na dauka abin ya wuce ai".

"Ina ya wuce tunda kullum yini nake da yawu a bakina, ga idan Innah na girki sai dai na rufe daki, na yi ta amai ban son ta gane mai nake ciki."

"Ya waske, da cewa to ana boye ciwo ne? Tashi muje ki ga likita".

Ya kalleta gaba'daya ta yi laushi, ya san laushin da ta yi dan ta samu yadda take so ne.

"Ni ba inda zani".

Ya kuwa mike da sauri ya ce "shikenan na fita hakkin ki, mu yini lafiya".

Tana daga zaune tasa hannu ta ru'ko rigar farar shaddar jikinsa.

Ya juyo suka ha'da ido suka dinga kallon juna, suna jin wani irin tsumin soyayya yana tsuma su.

Sa'adah ce ta yi saurin dauke kai.
A hankali ta ce "da gaske na gama".

Ya juyo ga'ba daya ya ce " Sa'a ba zai yiwu na tare da ke a hakan ba, kina musguna mini, ban isa ki mini yadda nake so ba, ban isa na ce ga yaddda zaki yi, ki ce to ba, haka kawai fa kika ce ba zaki tare ba, sanin kanki maganar ba a hannuna take ba, tunda Baba Kika fadawa, shine kuma ya bani umarnin na lamince miki ki kammala shirin ki, yanzu kuma cewa zai yi na nuna bai isa da ni a karo na biyu ba".

Ta tura baki gaba ta ce "Amma ai da ka ro'ke ni akan ka kira shi , na fa'da masa zan tare da bakina".

"Eh na fa'da amma sai na ga bai kamata na matsa miki ba, shekaru bakwai na yi ina kuakan rashin ki, Kinga kuwa duk dadewar da zaki yi kina shirin ba zaki kai irin wannan lokacin ba. Ki Bari ko wata uku ne, nan gaba sai mu san yadda za'a tunkare shi.

Kuka ta fara tana cewa" ba wannan maganar, wallahi ba zan yarda Innah ta fahimci Ina da ciki ba, tunda ba za su gane da bada son raina hakan ya faru ba".

Ya zauana ya fuskanceta sosai, sai kuma ya tafi ya yi sujjud shukur, ya dago yana cewa "Alhamdulillah, ubangiji ya raba ku lafiya, na dade ban ji farin-ciki irin na yau ba".

"Tashi muje ki siyi abin da kike so a matsayin tukuici".

"Ni ba inda zani".

Ido kawai ya zuba mata, jikinta ya yi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa.

Ta mi'ke tsaye, tana tura baki gaba, irin wadda take yi masa a shekarun baya, mai ha'de da wani irin ta'bara da shi kawai take yiwa irinsa.

Nan da nan jikinsa ya hau tsuma da sauri, ya matsa kusa da ita, ya rungumeta sosai, dukkansu sun shiga wani irin yanayi mai tsuma jiki da gangar jiki gaba'daya.

A kidime Mk ya saketa ya shiga waiwayen inda zai ga hijabinta, can ya hango wani a ninke akan akwati.

Da kansa ya ware ya fara kicinyar saka Mata. Tmda taimkonta hijabin ya daidaita.

Ya kalleta sosai ya ce "Bari na fita, sai ki fito muje asibitin a duba ki, daga Nan sai ki raka ni unguwa".

Ta kasa yi masa musu, tana tsaye tana jin yana yiwa Inna sallama, ya fice ya barta tana faman tauna maganar da zata fa'dawa Innah.


Haka ta fito rataye da yar 'karamar Jakarta, ta kalli Inna da take kofar kicin a tsaye, ta ce "Inna zanje asibiti, daga nan kuma zan wuce gidan Maman Khalifa".

Ido Innah ta bita da shi tabbas tana ganin kasala a tare da ita, kuma ba kasafai take cin abinci ba.

Ta ce "wanne asibitin zaki je?"
"Ban san wadda zai kai ni ba, Ni ba dan ya dage bama, da ba wani asibitin da zani, na san zazzabin cizon sauro ne".

"To sai kin dawo, amma kar ki kwana gidan su Khalifa, Baffan ku baya gari, gara ki dawo mu kwana tare".

Sa'adah ta amsa da cewa "To Innah".

Innah ta sake cewa "ki kula da kanki, ki lalla'ba shi, kar ki yi abin da zai ja hankalinsa akan ki, har sai anyi tariya. Ni ba gaskiya ba zaki mini wata uku a gidan nan da auren ki ba, wanan watan da wani watan ya isa, koma kudin bai isa ba, kina dakinki sai ki dinga siyan abin da kike so, tunda dai ai ansan mu masu karamin karfi ne".

A sanyaye Sa'a ta ce "Hakane Innah! Ni idan kin ce ma a wannan watan na tare zan yi biyayya ba dan Ina so ba, sai dan na nuna miki na fi girmama ra'ayin ki akan nawa".

Sosai Innah ta zuba mata ido tana son ta gasgata maganar Iyah, amma bata san meyasa take ganin tamkar akwai wani abu da yasa ta sauko haka da wuri akan tariyar ba.

Ta tafi, Inna ta bita da addu'ar dawowa lafiya.

Suna tafe yana ta yawo da su akan titi, shi kansa tunanin inda zai kaita yake yi.

Can ya kalleta ya ce "wanne asibitin kike zuwa yanzu?"

A hankali ta ce "Ni fa na je asibitin an duba ni, ta butde jakarta ta fito da magungunan da aka bata tana nuna masa.

Ya ce "To sannu My Sa'adah".

"Yanzu bari ki raka ni unguwa"

Basu zame ko ina ba sai gidansa na rijiyar zaki.



*Ina ta shan korafi daga makaranta cewar yanzu yanga nake yi, ko kadan ba wannan maganar, a farkon fara posting Ina da pages masu yawa a 'kasa, a yanzu kuma babu, sai na yi typing kafin na turo, kowa ya san akwai hidimomi irin na yau da gobe akan kowanne bawa.*

*Ni Kuma har da ciwon idon da yake sani rauni a typing din, Ina fatan za'a yi hakuri, saura kiris ma mu kammala, ban yi tsammani labarin zai yi tsayi haka ba*

*Zan sanar da cewa ba kullum zaku ga update ba, amma ba zai dinga daukan lokaci ba*
*Na gode sosai da yabawar ku kan rubutuna*.







Surayya Dahiru
✍️✍️.




*HALIN YAU*!

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/


*TAIMIYYAH*❤️

Ina kuke ne masoya kuma makaranta littafan Hausa,me kuke jira baku afka cikin wannan tafiya ba? ko kuna da labarin cewa shahararriyar marubuciyan wato Ayshat Ɗansabo Lemu,marubuciyan👇🏻

*LAIFIN ƁOYE*
*HAMAL*
*HURAYYAH*
*BURIN ZUCIYA*
*ƘALUBALE*
*NAILAH*
*INA DA HUJJA*

ta sake yinƙurawa domin tazo muku da zazzafan labarin ta me suna asama,domin faɗakar da ku da kuma nishaɗantar da ku,haɗi da koyar da ku dibarun girkunan zamani da gwangwaje ku da salon soyayya me tsayawa a zuci,duk acikin wannan shahararran labarin nata me suna *TAIMIYYAH!* Labarin da yazo da wani irin salo me cike da ban tausayi do motsa zuciyan me karatu,duka wannan zai zo muku akan farashi me sauƙi,da kuɗin ki 500 kacal zaki mallaki naki don gujewa shiga hakkin marubuciyan,zaku biya kuɗinku ta wannan asusun kamar haka👇🏻

*0504192664 Aisha Ibrahim Dansabo GTbank.Sai ku aiko da shaidan biyanku ta wannan layin 08167768704.*

*Masu turo katin waya zaku turo katin MTN ta wannan line ɗin 08167768704.*

Kada ku bari abaku labari domin wannan karan salon na daban ne,tuna da sunan *TAIMIYYAH!* sai ku garzayo don ji wacece TAIMIYYAN ya rayuwanta zai kasance alhali ta kasance gurguwa!


Masu buƙatan a tallata muku jahar ku a wannan daddaɗan labari zaku tuntuɓi marubuciyan ta wannan layin 08167768704.


Share it ga wanda taci karo da wannan tallan,tayi sharing ɗinsa fisabilillah! 👏🏻

THANK U ❤️


*GAISUWAR GIRMA GA*
*IYAYENA! KUMA MANYA MATA!*
*HAJ HAMZIYA ALI(MRS BELLO BAFFAH MAITAMA)*
*AUNTY ZAHRAH IBRAHIM*
*AUNTY KHADIJA ABDULLAHI(MRS IBRAHIM BABA)*
*HAJIYA MAIJIDDA TA GWARAM(MRS ALI BUKAR MAKO'DA)*
*AUNTY AISHA HAMISU KANO(MRS ABDULAZIZ SHEHU)*
*AUNTY AISHA SANI GWARAM*
*AUNTY SA'ADATU SANI GWARAM*
*AUNTY SHEMA'U SANI GWARAM*
*AUNTY AMINA SANI GWARAM*
*AUNTY ZARA'U BILYAMINU USMAN HADEJIA*
*AUNTY A'I GARBA*
*AUNTY SHAMSIYYA USAINI*
*AUNTY ZAINAB SIBA*
*AUNTY FIDDAUSI 'DAYYABU TAURA*
*AUNTY WASILA MUHAMMAD* *(AMINYAR AUNTINA TA KAINA RABI SANI)*
*FATAN ALHERI ALLAH YA KARA MUKU LAFIYA DA NISAN KWANA MAI ALBARKA*.


*FATAN ALHERI GA AISHA JOS MARUBUCIYAR TA CUCE NI*.
*ALLAH YA 'KARA BASIRA*


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*


111-112.


Katon gida ne mai dauke da babbar haraba, ga wasu irin gini flat guda biyu, a tsakiyar filin.

Sai daga can kusa da karshe kuma wani flat din mai kama da boys quarters.

Shuke shuken fulawowiyi sun 'kawata harabar, sosai gidan ya burgeta, saboda tsarin gini ne na kasashen ketare inda zaka samu yalwar iska(ventilation).

A jere suke da juna, sai dai akwai Yar tazara a tsakanin gidajen.

Kai tsaye ya nufi wadda yafi kusa da 'bangaren dama.

Ya fito da mukalli a aljihunsa ya bu'de babbar kofar, tunda akwai karamar kofa wadda 'karamin falo ne da toilet a ciki saboda zama da abokansa ko ba'kinsa maza. katon falo ne a farko mai dauke da wurin cin abinci da kicin sito, akwai kofar a kicin din da zaka iya shigowa daga waje. Sai ta gefe kuma dakunan barci ne suma manya guda biyu kowanne da bandakinsa a ciki.

Har ilah yau daga can karshe akwai wata kofa idan ka bu'de dogon corridor zaka ga ni mai dauke da wasu 'dakuna guda biyu, da bandakinsu.

Ta jikin wannan koridon akawai kofar da zaka iya fita waje ba sai ka shigo falon ba.

Sosai tsarin ya burge Sa'a marbles din da aka shimfida a ko ina, da kuma girman falon da dakunan ya sake sawa ginin ya zama na mussaman.

Sannan ko ina ansaka labule masu tsadar gaske.

Cikin dakin guda da suka yada zango har da madaidaicin karfet a shimfide.

Suka a zuana akan karfet din.
Ya ce" ina fatan ya yi miki?"

A hankali ta ce "ko gidan da muka fara rayuwa ka kai ni, ya yi mini sosai, bare wannan".

Ya tsura mata ido yana gasgata ta domin yanzu babu dogon buri a tare da ita, amma da yake tana samun hanyoyin samun ku'di bata yiwa kanta kwangen sutura da kayan kwalliya na alfarma. Son ta yi gayu a jininta ne ba wai 'karya ko fariya ba ne.

Ya matsa sosai kusa da ita, yana shakar 'kamshinta, ya na kuma yi mata wani irin kallo mai tsanani.

Ta sunkuyar da kanta 'kasa tana Jin kallon har a zuciyarta.

Ya nisa ya ce "yunwa kike ji ko?"

Da sauri ta 'daga masa kai.

"Shine kuma ba zaki fa'da mini ba? Ai da na tsaya a hanya na siyo miki".

Bata ce komai ba.

"To me zaki ci?".

A hankali ta ce gasheshshen nama da yourgt mai sanyi".

A zuciyarsa sai ayyana irin haka ta yi a cikin Jawad, ba rashin lafiya, sai kasala da rashin cin abinci sai kayan kwadayi, da barci.

Ya mike da sauri ya ce "zamu je mu siyo, ko na je na dawo?"

"Je ka dawo! na gaji".

Bai 'dauki lokaci mai yawa ba, ya dawo da dukkan abin da take bu'kata, ya tarar da ita, tana sharar barci hankali kwance.

Bai tashe ta ba, ya ajiye ledojin ya shiga bayi ya 'doro alwallah ganin 12:45 pm ta yi, yanzu za'a fara 'kiran sallah.

Ai kuwa yana fitowa ya jiyo Kiran sallah, sai da ya yi nafila, sannan ya fice zuwa masallaci.

'Karar rufe kofar ya tasheta, a hankali ta yun'kura ta zauna da salati a bakinta.
Kamshin nama ya bugeta, da sauri ta mike ta wanko bakinta ta dawo ta fara cin naman nan a hanzarce saboda yadda ta tara yunwa. Bata son cin abinci, sannan bata iya siyan abin da take so dan kar ta janyo hankalin Innah. Ko a gidan Sumayya bata iya cewa ga abin da take sha'awa shiyasa take zaman yunwa, sai ta ga zata galabaita ne take zuwa gidan Zainab, ko ta siya ta samu inda zata buya ta ci.

Duk yawan nama da gurasar da suke na'de a poil paper 'dan ka'dan ta rage, ta bude dadda'dan yougurt ta fara sha tana jin sanyinsa har cikinta.

Sai da ta huta, sannan ta yi gyatsa ta mike ta 'doro alwallah.

Ta kusa idarwa ya shigo. Ya zauna yana jan ledar gabansa dan shima ya ci, mamaki ya matu'kar kama shi, saboda ganin wanda ta rage.

Ya karasa cinyewa ya bude yoghurt ya sha.

Bata yi masa magana ba, ta sa hannu ta dauko robar ruwa ta bude ta kai bakinta.

Sai da ya kammala ya matsa kusa da ita sosai, ya ru'ko ta. Yana cewa "zo ki ji wata magana, na sani ba iya yunwar nama kike ji ba".

Ta fara ture shi tana cewa "Ni wallahi iyakacin yunwar kenan, kuma na koshi sosai".

"To ai ni ban koshi ba, tunda dai baki rage mini na kirki ba".

Ta 'ki tsayawa, shi kuma ya'ki sakinta, ganin da ya yi da gaske ba amincewar zata yi da shi cikin kwanciyar hankali ba, sai ya saketa.

Ya koma gefe ya na jin bacin rai sosai.
Jikinta ya yi sanyi, amma bata san me yasa take jin tsananin bacin rai idan ya nemi kusantarta ba.

Tsawon lokaci suna zaune ba um, ba um um, a tsakanin su.

Ta saci kallonsa ta ga yadda yake cikin fishi sosai, ta hadiye maganar da take son amayarwa.

Ya mike yana cewa "Tashi mu tafi"!

Ta 'ki yin ko da motsi, balle ta tashi.

Dan jim ka'dan! Ya nufi hanyar barin dakin yana cewa "ki same ni a mota".

Ta daga murya ta ce "Ba ka ce mini komai ba akan maganar da na yi maka 'dazu, kuma ka ce mu tafi?"

Ya dawo ya tsaya akanta fuska ba walwala ya ce "wacce magana ce? Tuna mini, dan ni na manta".

Takaici ya shaketa, amma hakanan sai ta daure ta ce "Tariyar Mana".

Kai-tsaye ya ce "Ban kammala shiri na ba, ba kuma ku'di a hannu na".

Ta fara kuka tana cewa "Ni ko ba ku'din zan tare, kar ka mini haka, so kake na kunyata?"

"To ki ta kunyata mana! Ina ruwana? idan kuma kina da yadda zaki yi da cikin dan ki tsallake kunyatar sai ki yi".

Ta dago a razane dan ta ga shine yake wannan maganar ko kuwa?. Ai kuwa suka ha'da ido, fuskarsa a matu'kar 'daure.

Ta Sanyaya murya, hawaye na zubo mata, ta ce "Haka ka ce mini?"

Take ya ji tausayinta! Ya zauna ya ce "Haka na fa'da miki Sa'adatu. Hakan kuma shine gaskiyar magana, ba zai yiwu kina wulakanta ni tun yanzu ba, sannan ki yi tunanin zan miki abin da kike so, bakya yarda da ni, na sani ko tariyar aka yi haka zaki cigaba da yi mini, dan haka ki zauna ki haihu a gida. Zuwa lokacin idan kin ji a ranki, kin shirya zama da ni bisa tsarin sharia sai na saka ranar tariyar".

Hawaye ya dinga zubo mata ba kakkautawa, a hankali ta ce "kar ka mini haka dan Allah".

Nan da nan ko ya ci laya da cewa "Wallahi ba zan yi abin da kike so alhalin har yau din nan bani da mutunci a idonki ba, inace dai jikina ne ba kya so ya rabe ki? To ba zan sake ba, zan ta siyo miki nama da yogurt da duk abin da kike son ci, nima kuma in sha Allah ba zaki ji, ko ki ga na mutu ba adalilin ba kya yarda da ni".

Ta dinga kuka sosai, ya dinga jin wani iri, ya sassauta ya ce "daina kukan haka! Ta shi mu tafi"

"Ni ba inda zani sai an tsayar da maganar nan".

"To ai na gama, sai dai tunda ni zan biki dole, sai ki tsara na ki, ki kuma sa ni biyayyar dole".

Ta goge hawayen ta ce "Na yarda ni zan bika".

Ya mi'ke ya ce "To tashi mu

Please Login or Register in order to submit comment