You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zo akan mashin.

Ya kafe mashin din ya fito da wayarsa Jim kadan ya Kara a kunne, ya ce "na iso".

Ba jimawa ya ga Sa'adah ta fito cikin dogon hijab har kasa, ta karbi ledar ta mi'ka masa kudi, kafin ta juyo Mk ya yi wuf ya mi'ke ya isa kofar zauren nasu, tana juyawa ta ganshi, zuciyarta ta buga ta rasa gane wanne irin abu ne duk sadda zata ganshi sai ta ji wannan bugun zuciyar. Kai tsaye zata shige ba tare da ta nuna ta ganshi ba, ya jah Hijabinta tare da cewa " kina nufin Baki ganni bane?"

Ranta ya baci sosai ta fincike, cikin gatsali ta ce " Mukhtar bana son wula'kanci ko da nake bin maza nake Ballagazaci, ai ba cikin gidan da ubana ya samar da ni nake yinsa ba, kar kuma ta'ba ni, iskancin da nake yi ba da irin ka bane, da yara ne sa'anina wato matasa irin Ahamad dinka".

Ya kai mata wani irin bahagon mari, ta yi maza ta goce ta bar shi da marin iska, a kufule ta daga ido ta zuba masa nata, ta tsorata da yaddda ta ga idonsa ya yi jawur, zuciyarta ta sake bugawa Amma duk da hakan sai da ta yi jarumtar cewa "A da ne ka dake ni ka kwana kalau Mukhtar amma a yau ina rantse maka da Allah da ka mare ni da ka ga 'kwanjina domin kuwa sai na gurfanar da kai gaban Human Right".

Ya juya tamkar tafiya zai yi, sai kuwa ya juyo ya kaiwa bakinta damka ya murde da iyakacin karfinsa, yana fa'din ai tunda kin riga kin tsufa ba zai yiwu ki dinga mini kaifin harshe ba, jikin ki ne zai fa'da miki. Cikin kishi mai yawa ya ce "ki je ki kai ni court of appeal, ko kuma ki sakaye ni a gidan gyaran hali na muddin Rai karshe dai na san ba komai ya saki hakan ba sai kishin na auri first love Dina".


Hawaye ya goce mata ta ce "Me zan yi wa kishin, ina abin kishin ya ke?"

Ya make kafada ya ce "kin fi kowa sanin inda abin kishin ya ke? wato har kin yi ilimin da za ki kai ni Human Right ko? Ina rantse miki da Allah sai na raba ki da wannan damar".

Ta yi tsaki ta ce "Bismillah".

Gaba'daya ya damkota ya jijigata idonsa ya ka'da da wani irin karfi saboda yadda taga idonsa ya juye nan kuwa wani irin tsumin kishi ke huda masa zuciya.

Ya ce " Ni Kika yiwa tsaki? ta yi kasa da kanta ta kasa magana saboda yadda ta razana, ta san baya son tsaki.

Ganin da ya yi ta dan risina sai ya saketa ya ce "Wa ye wannan da ya kawo ki a mota? Anya Sa'adatu ba zaki bar zuciyata ta huta ba? Na fa'da miki ban son na gan ki da kowa shine kika dauko wani gajeran yaro kika zo da shi, kuma kin san zan iya ganin ku?"

Nan ma shiru ta masa tana jin haushin yadda ta kasa tafiya ta barshi, zuciyarta tana bada ita da yawa.

Zuciyarsa ta dinga zogi tamkar ya curo ta, ya daure ya ce "Baffah na dawowa zance a daura auren nan tun ban janye komen da zan yi da ke ba, na san dai sadaki kawai za'a ce na kawo, ko yanzu na ruga shago zan hado dubu ashirin dan baki wuce hakan ba".

Hawaye ya balle mata ta ce "Dan Allah ka janye komen dan kuwa ba sonka nake yi ba, maganar ban wuce dubu ashirin ba kuma, idan ka so ka ce sadaka ce ta dace da Ni, ina ce kai kana da wadda ta cancanci kudade masu nauyi?"

Ya saki murmushin da Babu nisha'di ya ce "kwarai kuwa, kin san dai fari da tsayin amaryata kadai ya isa namiji ya biya kowanne irin farashi domin irin sune na shiga gaban mota, idan kuma kana gida a maka kwalliya da gashi yala yala kana jin ka tamkar kana tare da balarabiyar Yemen".

Hawaye ya balle mata, har da shesshekar kukanta, shi kuma ya dinga jin dadi, domin ya san har abada shi da Sa'a suna son juna dan haka dole su ji kishin junansu, akan dole yake yin hakan dan sai yafi samun lagonta a maimakon ya yi ta rarrashi tunda ya san bata biyuwa ta da'din rai.

Kafin ya yi magana ta ce "idan ma Balarabiyar Saudiya ce ina ruwana, sai dai kuma na san banbancin jikinta da zagarniyar dabino kawai numfashi ne, ta fa'da hawaye ya na sake zuba".

Jikinsa ya yi sanyi ya ce "very sorry my sweet Sa'adah".

Haka kawai ya fa'da kukan ya zo mata gaba'daya ta dinga yinsa saboda yadda ta ji kishin maganganun da ya yaba mata

"Yi hakuri mana tunda na bata miki Rai ki yi ha'kuri, shiga ki dauko mani abin zama, zance na zo, ai ba maganar kuka tunda dai kin san nafi son ina kamo halittu suna cika mini hannu, zangarniyar dabino ai kawai ta fashion ce".

Ta goge fuskarta ta ce "da wa zaka yi zancen?".

Kai tsaye ya ce "Sa'ade".
Ta ce "bani da muradin ka, je ka dauwama da ta shiga mota, ni ma ubangiji ya bani rabona".

Da sauri ya ce " zuciyata ta gama yarda tunda kika shafe wannan lokacin wani bai yi mini shigar sauri ba, to kuwa tabbas ni ka'dai ne zai mallake ki, ada na kudire idan na dawo na tarar kin yi aure zan nemo Safina na aureta, amma tunda kin cigaba da jirana to na fasa da Safina, dan haka ki ajiye duk wani borin da kike da nufin yi mini yanzu da sunan jana a kasa, ki adana idan an shafa fatiha sai ki ta yin su ni kuma zan ta lallashinki da allurorin kauna kala kala".

Kawai sai ganin ta ya yi ta zube a kasa tana kuka sosai tana tirza kafa ya dinga kallon ta yana murmushin ashe dai har yanzu bata girma ba, zai mata komai ta shanye amma idan ya jingina kansa da wasu matan sai yaga gazawarta da rauninta, bata iya jan aji akan kishinsa, ya yi amanna ba macen da take son sa kamar Sa'adah.

Da wata irin murya da sai suna cikin mayafi guda daya yake yinta ya ce " Yi shirun ki Ummu Jawad ai na fasa, kuma ma wasa nake miki ai na san karatu kika tsaya yi, ba Mukhtar kike jirah ba".

Ya sake cewa duk girman laifin da kika mini ai dai bana kin daukar wayar ki, na ro'ke ki ki dinga amsa kirana, idan kuma kin ki jin rokona Ina tabbatar miki zamu je lokacin da zaki ta kira na cikin tsananin son na dauka ba kuma zan saurare ki ba Nima".

Da kuka sosai ta ce ka auro har da Halima Mutari, menene hadina da kai da zan damu ne, kuma Wallahi ba zan yarda da wannan abin da kake mini ba, Baffah na dawowa Zan fada masa ya bawa 'Karfi kyautar aurena shi nake so, dan kuwa birge ni yake saboda sanin ya kamatansa".

Jinsa ya yi shiru na dan lokaci ya sa ta dago ta ga idanuwan nan sun sake kadawa tamkar garwashi, wani irin tsoro ya cika zuciyar ta amma bata ce komai ba.

Cikin murya ba amo ya ce "sonsa kike yi da gaske ko kuwa ramawa Kika yi dan na ce zan auri Safina? Ai bance ina sonta ba ni, akan me zaki nemi hada ni da aminina, ke dai burin ki a duniya bai wuce ki tayar mini da hankali, ki kassara zaman lafiyar zuciya ta ba ko? to Billahillazi zaki san kin fa'da min wannan mummunar kalmar wai yana birge ki. Na rantse miki U will pay for it"

Ganin yadda ya fusata ya sanya ta shamace shi ta mike ta shige cikin gidan da saurin gaske tamkar gudu gudu.

Sai da ta tsaya ta gyara fuskarta, tana raya yadda zuciyar ta take fatali da hudubobin Innah da Anti Sumayya akan kar ta bari ta dinga kula Mk, batavsan dalilin ba, bata iya wannan jarumtar.

Ya jima a zauren kafin ya tafi, ya roki Akeel ya tuka shi zuwa gidansa domin ba zai iya tuki ba.

Kwana ya yi cikin wani irin matsanancin kishi, bai yi barci ba duk juyin da zai yi Sa'a yake gani da wani namijin cikin shigar farin taufafi, sai kuma da ta ce Mahmoud na birgeta. Tabbas idan bai tashi tsaye ba, ba zai samu Sa'adah ba, domin sosai ya hango wani irin fishi mai danne soyayya duk karfinta kuwa a tare da ita.


Washagari daga fitowar Mk daga masallaci ya dauki mota bai zame ko ina ba, sai gidan Alh Isa.

A falonsa na waje ya tarar da shi bisa al'adar sa na zama ya gana da iyali, baya tashi sai 8 sai ya shiga ya kwanta zuwa goma sai ya tashi ya karya.

Ganin da Alh yayi Mk na bu'katar yin magana da shi ya sa ya sallami iyalinshi, ya ce su basu wuri.

Bayan sun sake gaisuwa. Mk ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Dama zuwa na yi, na fa'da maka, ina son kaje wurin Baffah ka tambayar mini auren Sa'adatu".

Alh Isa ya yi shiru, yana jin wani irin bacin rai na taso masa.

Mk ya sake yin kasa da kansa yana sauraronsa, amma tsawon lokaci bai ji Baban ya yi magana ba.

Ya dago sai ya ga Alh yana goge hawaye a idonsa.

A sanyaye Mk ya ce "lafiya kuwa Baba? Subhanllah! Ban san a cikin damuwa kake ba dana bari har ka samu nutsuwa".

Sai lokacin Alh ya nisa cikin rawar murya ya ce "Takaicin yadda wannan ranar ta riske ni ne, Ni ka'dai babu mahaifinka, domin da yana da rai da bulala zansa na zane maka jiki don in tabbatar maka har yau din nan ina maka kallon yaro dan karami da bai kai yaronka Kabiru ba! na kuma ganar da kai irin isar da na yi da kai, don na lura ka manta.
Amma tunda bashi da rai ai dole na yi ta ha'kuri da duk cin kashin da kuke mini tunda na san idan shine na mutu na barshi ba zai fita a cikin sha'anin ahalina ba".

Hankalin Mk ya tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa ya rarrafa jikin dattijon da girma ya sake kama shi ainun. Ya ce " Dan Allah Baba yanzu ma doke ni indai zaka huce! Ai komin girman da zanyi har gobe Ni yaro ne a gabanka dole na jira abin da zaka zartar".

Hawaye ya sake zubowa Alh ya ce "Ai yanzu idan na dake ka kana iya daina zuwa wurina dan ka nuna mini abota ce kawai ta hada ni da ubanku ba jini ba, yau shekaru bakwai ina kwankwa'dar bacin ran jingine yarinyar dattijon arziki irin Malam Basiru, Ina fama da kunya da nauyinsa iri iri. Amma saboda Ubangiji ya zuba alheri mai yawa a zuciyarsa tunda nake jinyar nan da bana iya fita sosai duk juma'ah sai ya zo ya gaishe ni, ba tare da tunanin ina da halin da zan mayar masa da yarinyarsa dakin miji amma banyi ba. Ni kuma na san isane kawai ban yi ba, ka zo yin aure ka saka ni a maganar tsundum tare kuma da uban 'yar da ka saketa. Dan ya gane zan iya nemo maka sabon aure, na yarinyarsa ne ba zan gyara ba, Abin da baka sani ba na shiga lamarin aurenka ne dan kar na ji kunyar kushewa ne kawai! Sai yanzu kuma ka zo ka ce wai naje na nemar maka auranta, saboda kawai ka nuna mini amfanina a gurinka sai sadda ka so Abu akaran kanka, idan baka so ba kuwa da ni da wadda baka sani ba duk daya".

Maganganun Dattijon ba karamin rikita Mk suka yi ba, ba karamin tayar masa da hankali suka yi ba. Ya kasa bude baki ya masa magana, sai ya hado kalmomi sai ya ga sun yi kadan su wakilci ba da nufin hakan ya yi ba, tsawon lokaci yana gurfane yana ta goge zufar da take yanko masa.

Ya ciro wayarsa ya dinga lalubo lambar'karfi amma ya kasa saboda yadda kalaman Baba suka kassara shi, da kyar ya tsaida hankalinsa, ya samo lambar, Mahmoud! Ya na dagawa ya fara masa sababi ya dauka akan Sa'adah ne zai kira shi da sassfe, har yana cewa " Lokacin da ka rabu da ita menene ba'a fa'da maka ba akan ka yi hakuri amma baka ji ba".

Murya a dusashe ya ce " Ina cikin masifa 'Karfi taimake ni ka zo ka same ni a gidan Baban Na'ibawa".

A sukwane 'Karfi ya ce menene, ko jikinsa ne ya tashi?"

A sanyaye sosai Mk ya ce"ka bar komai ka zo yanzu Dan Allah" sannan ya kashe wayar yana ta faman fadin innalillahi.

Mintina biyar Mk ya kasa ha'kuri ya ce "Ka dubi girman Allah ka yafe mini Baba wallahi ba haka bane a Raina, amma na gamsu na yi laifi ban kyauta ba! ka mini afuwa fishin ka dafi ne. Baba abota babban al'amarine da ya wuce a kira shi da kawai, domin sai da Annabi ya jaddada mana mu ri'ke Aminan iyayen mu, mu sadar da ZUMUNTA da su domin ya nuna mana suma suna da Hakki akan mu, ina ba'kin cikin cewar da ka yi baka isa da ni ba".

Alh baice komai ba, illah ajiyar zuciya alamun ya dade da abin yana cinsa a zuciya.

Ya nisa ya ce "Idan ban yi hakuri ba yaya zan yi Muhammadu?"

Dai-dai lokacin Mahmoud ya iso cikin tashin hankali, ya gaida Baba cikin girmamawa.

Mk ya ce 'karfi laifi na yiwa Baba tsawon shekaru bakwai yake ta kallona da abin, Amma ya ce " takaicinsa daya da Baban Samira baya raye domin da a gabansa zai zane ni tamkar yadda za'a zane Jawad, shine nake so ka kawo masa dorinirka ta cikin motarka ka zane masa ni domin yanzu shi ko ya dake ni ma sai ya ji a jikinsa, tunda lafiyar lallabata ake yi, ka cire tausayi ka zane ni har sai ya ce ya isa haka".

Da sauri 'Karfi ya juya mota ya dauko wata irin sharbebiyar dorina ta dukan dokinsa ce da ya mutu, shine yake ta ajiye da dorinar yana yiwa yaransa barazana da ita.

Daga shigowarsa, yasa iyakacin karfinsa ya shammaci Alhaji ya zamba'dawa Mk dorinar nan, a kidime Mk ya zabura domin kuwa ba karamin kidima shi bulalar nan ta yi ba
Ba dan tsananin jarumtar da ya saka a zuciyar sa ba, ba abin da zai hana ya zunduma ihun neman agaji.

Alhaji ya ce "Ashha Mahmuda ai ba umarninsa zaka bi ba, ni zaka jira na baka damar yin hakan, maida bulalar ka dawo ka ji mai zance muku".

'Karfi ya fita, sai da ya ci dariyarsa mai isarsa ko banza ya rage zafin dukan da Mk ya yi wa zuciyar sa tunda amincin da ke tsakanin su ne ya haramta masa samun abin da yake so, da ya zurfafa tunani sai ya gane abotarsu ta yi karfin da zabin zuciyoyinsu ya zama iri daya. Duk da idan anbashi gida da mota akan a bashi Farida ba zai karba ba, kyan fuskarta da farinta bai zama abin burgewa a gunsa ba.

Da alhini a fuskar sa ya koma falo ya gurfana a gaban Baba yana cewa "Ina rokawa Abokina afuwarka Baba, ni shaida ne akan yadda Mukhtar ya ke girmama lamarin ka".

Dattijon ya miskuta ya ce " aminci na da mahaifin wannan yaron ya zarta karfin naku zumuncin domin ku da hankalin ku, kuka hadu amma ga shi nan kun zama tamkar cikinku guda!
Ni kuwa tsakanin mu abota ne tun bamu wuce shekaru bakwai ba, da aka kaimu gabas almajiranci har zuwa yau din nan".

Ya yi tari ya cigaba da cewa "saboda giraman abotarmu iyayen mu sai da suka zama tamkar shakikai ne duk da ba garinmu daya ba,shi daga Bichi, Ni kuma daga Wudil. A lokacin da Kabiru zai auro uwarka Rabi, mahaifina ne ya zo ya karbar masa, duk da ga kannen mahaifinsa nan hakan ya faru ne bisa amincewar mahaifin nasa da yan'uwansa. Ka san dai kaine dansa namiji na farko amma baisa sunan mahaifinsa ba, sai ya saka sunan yayana da ya fa'da a ruwa ya rasu a shekarar".

Ya yi shiru yana goge hawayen da ya kasa maida su, dukkan jikin Mk da 'Karfi ya yi sanyi, da kyar 'Karfi ya ce "Sannu Baba sai a ha'kuri!"

Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi fiye da ta farko ya zarce da cewa "A bayan mun yi aure har mun haife ku na samu matsala da Zuwaira na yi fishin zuciya na saketa, na yi rantsuwar na gama zama da ita.
Bana mantawa dawowar mahaifinka daga Bichi ya samu labarin rabuwarmu a bakin yara, da ya juya Ashe Wudil ya tafi a yammacin, wajen karfe takwas na dare sai gashi ya dawo da ita. Washagari na tashi da azumin kaffara domin bazan iya kunyata Kabiru ba, ko na nuna masa bai isa ya yi hukunci a gidana ba.
Har yau din nan ban sake tada maganar ba sai yanzu da nake baku labarin, amma kai sai ka nuna mu iyayenka bamu isa ka mana alfarmar cigaba da zaama da matarka bare kuma wannan abokin naka".

Ya ja hankici ya goge fuskar sa ya ce "Har Kabiru ya kwanta dama bashi da aljihun kansa, haka nima bani da nawa, koman mu daya ne, Ina da ikon zartar da hukunci a gidansa haka nima yake da cikakken iko, shiyasa na tsorata ainun hankalina yake tashi idan na kalli al'amarin da ka yi mini, na baka umarni, ka kafe ka kasa yi mini alfarma, sai nake ganin da mahaifinka yana da rai da ka ga 'kwanjina. Amma tunda ni ka'dai na saura muku sai na biku da yadda kuke so tunda ubangiji ya nuna mini wannan zamanin da ya zama iyaye sun koma agwagi."

Mk ya ce "Ka yi hakuri, ka kara hakuri Baba"

Ya nisa ya ce "na ha'kura amma ka sani ni ba zan iya zuwa wajen Malam Basiru ba, bani da wannan kwarin guiwar, domin har yau din nan girmama ni yake tamkar shakikin yayansa ba kuma dan kowa yake mini hakan ba, illah dan kai domin ni ban san shi ba, sai adalilinka"

Hankalin Mk ya sake tashi ya ce " Duk cikin Kano bani da wadda ya fika Baba! Idan kuwa ka ha'kura to kaine mai karba mini aure a ko ina".

Alhaji ya ce " ka fadi Gaskiya! sai dai na san daddako irin na Malam Basiru da irin yadda ya girmama lamarinka zai iya tirsasa yarinyar nan ko bata so ya dawo maka da ita dan soyayyar da yake yi maka. Ni kuma na ta'ba fa'da muku kai da ita daya kuke a gurina nine alkalinku, alkalanci na gaskiya zanyi a tsakanin ku.
Zan je na nemar maka aurenta kadai, idan na ji a bakin yarinyar da amincewarta zan nema maka aurenta".

Da sanyin muryar ya ce "fishi take yi da ni Baba! Amma da zarar anyi auren zamu dai-dai ta, tana sona wallahi"

"Ashe dai ta san ciwon kanta, domin kuwa ka yi mata laifin da duk wadda ba ya jin tsoron zuciyarka zai fa'da maka cewa "komin girman laifin da ta yi maka, hukuncin da ka dauka akanta ya yi tsauri, ya wuce makadi da rawa, ko kadan babu a ragayya cikinsa".

Jikin Mk ya dinga bari sosai, shi da kansa ya san kunyar Baffah ya jita irin wadda bai yi zaton anan kusa akwai wadda ya ta'ba jin irin wannan kunyar ba.

Amma ya tabbatar da ya fito ya fa'di laifin da ta yi masa na cigaba da mu'amala da tsohon saurayinta, da ba wadda zai dora masa irin wannan laifin na bai yi adalci ba, domin munin abin ya baci, ba ta da hurumin yin hakan ta kowacce fuska tunda ba muharraminta bane bata da alaka da shi ta kowacce fuska, sai tsohuwar soyayya.

Amma son da yake mata ba zai bari ya fadi wannan al'amarin ba, domin da yawa wasu zasu zargeta, zasu kyamaceta, tunda idan ya ce tana tare da wani ne musabbmabbin rabuwar kowa da abin da zai raya a ransa, ba a kuma isa ace sai kowa ya yarda ba barna suke aikatawa ba, shi yasa ya zabi ya boye a ransa shi ka'dai, amma kuma dole su nisanta da juna tunda ba abin da shaidan ba zai dinga raya masa ba, zai dinga zarginta ne ko da kuwa ba hakan bane a zahiri kasancewar sa dan Adam mai rauni ba a ma'asumi ba".



*UZZIRI*
*Duba da muna cikin kwanakin nan masu tarin falala da albarka, sai nake ganin ya kamata mu jingine Wannan labarin dan samun damar ribatar kwanakin da ubangiji ya rantse da su, ba lallai mu riski na wata shekarar ba*. *Dan haka zamu tafi hutu sai bayan sallah idan muna cikin rayayyu zamu zo mu karasa abin da ya yi saura in sha Allah. Dafatan ubangiji ya karbi ibadunmu ya sa mu yi hidimar sallah lafiya, kar mu manta da yiwa KASARMU addu'a.*
*Ubangiji ya bamu damuna mai albarka*.

*Na gode muku sosai da yabawar ku kan rubutuna*.



*Surayya Dahiru*

✍️✍️





Surayya Dahiru.
✍️✍️.





🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai dai da satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_



*Barkan mu da ibada! Barkan mu da bikin farin-ciki. Ina fatan ubangiji ya karba mana kyawawan aiyukanmu, ya shafe mana kurakurai. Ina yi mana Barka da bikin Babbar sallah, ubangiji ya dawo mana da Alhazanmu lafiya, ya kuma zaunar mana da kasar mu lafiya.*
*Allah ya maimata mana*.


96-97.


A tunaninsa space din da ya bayar a tsakanin su, dan ya samu zuciyar sa ta nutsu ne, ta daina wasiwasi akan ta, ashe laifine tunda ba kowa ne yasan azabar da yake dandana adalilin hakan ba.

A sanyaye ya ce "shikenan Baba na yarda da hukuncinka zan kuma yi biyayya akansa in sha Allah".


Tari ya sarke shi sai da ya lafa masa, ya ce " duk Ranar da kuka dai-dai ta da ita ka zo ka dauke ni, ka kaini gabanta, tunda nema muke yi".

Suka yi godiya sosai suka Mike bayan sun ajiye masa kudi.

A mota Mk ya ce "Karfi ka ji dadi da dake Ni, duk yadda aka yi dama kana son ka samu damar da zaka dakenin shine yau da Ubangiji ya ara maka dama, ka cire tausayi ka tafka mini bulalar da sai da na ji tamkar na saki fitsari a wurin".

Cikin dariya sosai 'Karfi ya ce "Ashe baka iya tsiya ba, da ka saki fitsarin ai kaga dole na yi bi'kin wurin da ka bata, dole kuma na ruga wajen Farida na karbo maka wasu kayan ai ko banza ka wahalar da ni".

Mahmud da ya ga yadda bulalar ta kwanta a kafada zuwa gadon bayan Mk ta tashi sosai wani wuri har ya yi baki tabbacin ya fara fashewa jini ya kume a ciki.

Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskar sa yana faman fadin "sannu Bichi ashe haka ta shige ka wlh mancewa na yi ta dukan doki ce ba bil'adama ba"

Mk ya ce "idan ban yi hakuri ba na Yi Yaya da kai?"

Ya nisa ya ce "Ya zan yi ne 'Karfi? da gaske yarinyar nan so take sai dukkan rauni na ya bayyana, ga dai idanuwanta cike suke da soyayyata amma bakinta sai ambaton kiyayya yake, bayan na san abin da nake gani a idonta akwai ninki ba ninki a zuciyarta, Ni kuma ba zan bata damar da zata ja ni a kasa ba, wahalar da na sha akanta bana jin nan kusa akwai namijin da ya shata, ko da na ki dawowa da ita na tabbatar na fita shiga tagayyara akan rabuwarmu!
Yanzu kuma naga Shirin shayar da

Please Login or Register in order to submit comment