You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya mamaye zuciyarta, ta dinga jin tamkar ta mutu ta huta.

Da sauri ya janyota jikinsa ya rungume sosai, ya dinga fa'din sorry a hankali, wannan rarrashin ya sanya kukan ya kwace sosai, ta dinga yi, shikuma yana saka tissue yana goge mata. Ta jima a hakan, sannan ya ce "Ya isa haka, Yi shiru ki fada mini menene ya kidima ko haka".

Cikin kuka ta ce "Tsoro nake ji kar na rasaka, tsoro nake ji kar juya mini baya, tsoro nake ji kar ka kasa yin adalci ka halaka".

Cikin rarrashi sosai ya ce "Na ta'ba fa'da miki ba macen da zata sa na rabu da ke saboda ita, sai idan tamu ce ta hado mu, ba yadda za'ayi na juya miki baya Farida! Ina mamakin har yanzu da muka yi shekaru uku baki fahimci iri son da nake miki ba zai tan'kwabu bisa 'karamin dalili marar tushe ba.
Ba zan miki 'karya ba, da gaske an jarrabeni akan Sa'a! Amma ki taimake ni ki fa'da mini shin ina miki wani abu da kika kasa gamsuwa son da nake mata, ba zai hana na so ki ba"

Ta yi shiru tana ajiyar zuciya! Ta sani bai ta'ba mata wani abu da zata ce baya sonta, ko ya tauye ta ba, amma da ace zata iya da ta ce so take ya fi sonta akan Gogel, sai dai ba zata iya ba, shima kuma bata jin zai iya hakan, tunda ta san ubangiji ne yake cusa soyayya a zukatan bayi.

Ya sake rungumeta tsantsan ya ce "fa'da mini mana ke nake sauraro"

Ta girgiza kai ta ce "Babu"
Ya ce "Zan fa'da miki gaskiyar magana! Wallahi ina sonki, Ina tsananin sonki, hakuri da kawaicin ki ya 'kara miki 'kima a idona da zuciyata, kar ki bari kishi ya kwace miki wadannan halayyar, domin kina jan hankalina da su, ina jin kunyar bata miki. Sannan zan ro'ke ki arziki! Ki bani hadin kai ta yadda zan yi muku adalcin da zaki gamsu, idan na kuskure dan Allah ki mini uzziri wallahi ba zanyi abin da muzanta ki da gangan ba".

Ta saki ajiyar zuciya taare da cewa "To".

Ya dinga yi mata maganganu masu da'di, Wanda wasu ta tabbatar ya fa'da ne dan hankalinta ya kwanta amma dai ta ji da'di kwarai da gaske, ta samu sau'kin daurewar da kirjinta ya yi.

Ya kalli agogo ya ga har sha'dayan dare ta gota ya mike da ita cak tamkar yar jinjira ya shige daki da ita ya dire kan gado ya ce"Ashe ma fafaloloce ba nauyi"

Ta dan murmusa kadan ba tare da ta ce komai ba.
A haka ya dinga hilatarta sai da ya raya daren da ita cikin wata irin soyayya mai tsayawa a zuciyar mace.

Har ranar daurin aure ta zo ba wani jituwa tsakanin Mk da Sa'adah.

Ranar juma'ah 15/7 aka sake daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel akaro na biyu akan sadaki Mai darajah.

Sai yamma suka baro Gogel, duk yadda Mahmoud ya so suje gun amarya Amma Mk ya ce ba inda za shi.

Dr 'Karfi ya kalli Dr Mk da ya yi kicin kicin da fuska ya ja tsaki ya ce "aikin kawai duk wani cin magananinka na 'karya ne, wato yanzu ka sami kwanciyar hankali shine zaka hau wani fiffika, to dan ma dai tsiyar Sa'adah ta fi taka, yanzun nan zata sumar da kai, farfadowa sai a gadon asibiti".

Fuska a daure Mk ya ce 'Tunda ba a lahira zan ji ni ba, ai da sau'ki, ka takura ni fa ".

Da dariya 'Karfi ya ce wallahi ka bini a hankali ka san ina da dorinar da idan na zuba maka sau uku, amarcin da kake rawar jikin zaka sabunta shi ba zai yiwu ba".

Dariya ta kwace musu dukkansu Mk ya guntse ya ce "Na rantse kuwa da ba zan yarda ba".

Har suka rabu caccaka Mk yake sha a wurin Mahmoud.

Washagari da hantsi Mk ya yiwa Sa'adah siyayyar komai na amfani, karon farko da shi a karan kansa ya siya ba wai Jawad ya saka shi akan dole ba, ya tuno sadda take cewa idan ya sake yi mata wani abu na alheri ba zai gama da Hajiya lafiya ba.

Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya yana ayyana banda zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta ai bai kamata zuciyar tasa ta zarme akan soyayyarta haka ba.

Ya nisa a fili ya ce "Albarka cin Baffah na yafe wannan maganar".

Amma haushin ganinta da Khalil da kuma tariyar da ta ce ba zata yi yanzu ba, ya matu'kar bata masa rai, shiyasa kullum ya yi sallah sai ya roki ya samu dalilin da itace zata nemi ta tare da bakinta.

Ya cika mota da kayayyakin ya nufi gidan su Sa'adah.
Domin ya kai mata ,tunda yanzu ta rataya a wuyansa, duk da ita bata da niyyar sauke nasa hakkin da ya rataya a wuyanta.





Surayya Dahiru
โœ๏ธโœ๏ธ.


๐ŸŒบ *HALIN YAU*! ๐ŸŒบ

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ยฎ_* โœ๏ธ
โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ษ—amfare da bin ฦ™a'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ
____________(โœช)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/


*GAISUWA GA*.
*Haj Zulaihatu Sani Kagara*
*Haj Maimuna Beli*.
*Hassana 'Danlarabawa*.
*Ku Dade, ku yi 'karko irin na Dabino*.



*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

107-108.


Sannu a hankali yake yin tuki, har ya isa gidansu Sa'a.

A zauren kofar gidan, ya tsaya, ya fito da wayarsa, ya dinga 'kiran layin Sa'adah amma tana gani ta yi mirisisi, yana tsaye Baffah ya shigo, suka gaisa ya ce "Ya ka tsaya shigo mana".

Tare suka shiga cikin gidan, Inna ce a Zaune tana kwadon zogale.

Mk ya zauna a gefen tabarmar da Baffah yake kai, ya gaida Inna! ta amsa ba yabo ba fallasa.

Cikin nutsuwa Mk ya ce "Inna ina neman afuwarki, na sani ni mai laifi ne, amma tunda ubangiji ya sake hadamu ina rokon ayi mini hakuri, bana jin da'din yadda kuke mini ke da Hajiyar Bichi".

Kunya ta matu'kar kamata, ta dinga jin wani iri, da kyar ta yi kundubalar cewa "Ni ba fishi nake yi ba, Allah ya kiyaye gaba, yasa albarka a aurenku".

Da'di ya yi matu'kar kama Mk, ya yi ta godiya.

Baffah ya ce "Idan ka zo, ka dinga shigowa, ai yanzu ba maganar tsayawa a zaure, Ina fatan ku kammala shirin ku da sauri ta tare hankalin kowa ya kwanta".

Innah da ta gama 'kwadon ta zubawa Mk, ta kai na Baffa dakinsa sai ta yi shigewarta daki, yayin da Baffah shima ya fita yana cewa Mk "shiga tana ciki, bakam ta yi".

Ya shiga dakin ya sameta a zaune cikin kwalliya tamkar ya yi mata waya zai zo, ta yi masa kwalliyar.

Ya zauna yana shakar kamshin turarenta, ya kalleta, ya na tuna sadda ta zo wankan haihuwar Jawad irin soyayyar da suke fakar idon Innah suke yi a dakin, amma yanzu ba wani farin-ciki a tare da ita, asalima tunda ta amsa sallamarsa bata sake yin magana ba.

Ya daure ya hadiye komai ya ce "Barka da lokaci"
A hankali ta ce "Barkan mu dai".

Ya nisa ya ce"Tsakanin ki da Allah ya kamata ace anan kika wayi gari? Komai mutum zai yi ya auna abin nan a mizanin hankali da sharia, saboda kawai ki kuntata mini kika cewa Baban Na'ibawa sai kin shirya zaki tare dan Allah ba ki ji kunya ba?"

Ta yi masa banza, abin da ta san ba ya so.
Bai yi fishi ba, ya sake cewa wanne shirin zaki yi? Ki tashi kawai mu yi tafiyar mu, ke kanki nake so ba wani shiri ko kwaskwarima ba, har yau ina kallon ki a little Sa'adah dalibar FGC Kano".

Ta tura baki gaba amma ba ta tanka ba.

Ya sake yin kasa da murya, ya ce " Kin amince na kira Baban Na'ibawa a waya ki fa'da masa kin yarda zaki tare yau? kawai sai mu yi tafiyar mu da waccar katifar da kike ta ajiye da ita. Zan dai siyo miki wata, tunda naga har yau din nan tana cikin abubuwanki masu daraja".

Ta hango katifar da take saman wadirof a 'daure wadda ya siyo mata ne tun shigar ta FGC a lokacin ma basu san juna ba, amma ta ki yarda a bayar da ita, ta kafe tana son abarta.

Ya taya ta kallon katifar da ba abin da ta yi, tunda ta da ce mai aminci.

Ya ce "ya kamata mu tafi da ita, ko akanta ubangiji zai sai a samowa Jawad kani ko kanwa".

Ta dauke idonta daga kallon katifar ba tare da ta ce 'kala ba.

Ya matsa kusa da ita ya ce "pls Sa'a zuge mini zip din rigar nan, ina son ganin kirjin ki, just gani zan yi, I won't touch it" .

Ta mike ta koma kan wata kujera da take dakin, ta juya masa ba, tabbacin ba zata yi ba kenan, zuciyarta sai hango mata take Allah 'dai ya san me ya yi da wata matar kafin ya zo nan, yana mata maganganu na rainin wayo da dasa ciwo a zuciya.

Ya nisa ya ce da alama, dukkan hardship din nan da muka yi going through bai zame miki iznah ba. saboda kawai kina da masu daure miki gindi ana dannata, abin da baki sani ba, indai har kika ce zaki cigaba da yi mini taurin kai wallahi zan yi dealing din ki with iron hand".

Ta ce "Ai daman na san ba abinda da zan kwasa a hannunka sai ba'kin ciki, na ce bana sonka, bani da burin aurenka amma an matsa mini".

Kuka ya kwace sosai.

Cikin kuka sosai ta ce"Idan ina sha'awar auren mai mata Allah ya tsine mini. Amma saboda ka fini a wurin Baffah ya mini fin 'karfi, ni an cuce ni, gaskiya angama da ni".

Jikinsa ya yi mugun sanyi, amma ya waske da cewa "Da gaske ba kya sona? To Ki yi hakuri son da nake miki ya isa ya ri'ke mana auranmu".

Bata tanka ba, haka bata daina kukan da take yi ba.

Ya ce zo muje ki raka ni unguwa, daga nan mu biya, mu yi lunch a restaurant din Royal Tropicana, mu tuno moment din mu na baya".

Ta 'kara sautin kukanta ta ce "sai dai ka je ka dauki Farida kuje Tahir sai ka fi shaukin tuna bayan. Ni kuwa me zaka yi mini na ga haskenka? ai babu shi, iya tozarci ba wadda ba ka mini ba, ina cikin bala'i amma ka iya daukar wata macen ka tare da ita a hotel, sannan har ka iya ce mini wai sai ka tuno ni kake gamsuwa".

Ya matu'kar firgita da kalamanta, ashe. duk motsinsa ta sani? Ya kalleta a kidime ya ce "waya fa'da miki wannan maganar?"

A hassale sosai ta ce "wadanda suka ganku, masu son na kalli yadda ka tattara ka yi wurgi da ni da dukkan al'amarina. Masu son na cireka a raina, na daina ganin idan babu kai ba zan iya rayuwa ba, domin kana can kana more rayuwarka da wata macen, ahalin ni ina shirin zaucewa adalilin ka".

Ta yi shiru tana shesshekar kuka mai ha'de da gunji mai cin rai.

Tausayinta ya maye gurbin takaicinta da yake ji, ya dinga jin komai ya narke na laifukanta a zuciyarsa, ya sani ita din mai tsanani kishi ce akansa, tamkar yadda yake tsananin kishinta.

Ya sani kishin Farida ne yake yagalgalata mussaman da bata samu damar amayarwa a lokacin auren ba, ta bar abin a zuciyarta yana cinta.

Ya numfasa yana jin sonta da ya makale a kasan zuciyar sa yana ta tunkubowa yana mamaye kowanne gurbi da sako na cikinta, sai shine yake ta kokawa cikin jarumta kar son nata ya mamaye har inda Farida take makale.

Ya sassauta ya ce "mu yafewa juna hakanan, zukatan mu sun wahala, gangar jikinmu sun yi kewa ba ka'dan ba, pls My dear Sa'adah let gone be by gone".

Har ranta ta ji da'di, dan haka ta sassauta kukan ta sa hannu ta dauko, tissue ta fara goge fuskar ta.

Ganin ta rage kukan, ya nisa ya ce "muje ki yi shopping din kayan kwalliya".

Ta girgiza kai tare da cewa "ina da su".

"To muje ki raka ni, na gaida Aunti Sumayya, na bata ha'kuri ta daina watsi da al'amarina, tunda mun shirya ta yafe mini".

"Ba zani gidanta ba, sai ta neme ni".

Ya yi shiru, amma jikinsa wani irin bari yake yi, ba abin da yake so irin ya jita a jikinsa, so yake ya samu dalilin da zai rungumeta, ya yi kissing dinta, ya yi sucking harshenta da yake jin zakinsa har cikin kwanyarsa.

Sannan yadda ta yi masa magana cikin kwanciyar hankali ya sake sa shi nisha'di ya dinga kallonta yana jin tamkar ya tabbata a hakan.

Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Sa'adah"
Bata amsa ba, haka nan bata dago ta kalle shi.

"Sa'adah! Sa'adah! Sa'adah! Sa'adah".

Haka ya dinga kiran sunan ba adadi, tun bata jin komai, har abin ya dinga ratsa jikinta , ya na saukar mata da dukkan kasala, yana kuma tuno mata al'amura masu yawa da suka shude.

Ta sani idan yana mata irin wannan Kiran cikin laushin murya, to ya kai kololuwar gajiya da son ta daina fishi da shi ne, hakanan ya kai ma'kuran wurin son su shirya, sannan a matu'kar matse yake da ita.

Ta sake zurfafa tunani, tana tuno idan yana mata irin haka, ita kuma sai ta yi bakam, har sai kiran ya huda dukkan sassan jikinta, ya saukar mata da matsanancin begensa, kawai sai dai ta tsinci kanta da yi masa kukan shagwaba, tana dirza kafafuwanta.

Yayin da shi kuma ya ga hakan ya san ya riga da ya gama kunnata shikenan, sai ya sa dukkan karfinsa ya ru'ko ta, ya bita da kisses da maganganu masu nauyi, tun tana zillewa har sai ya gwada mata, bada ha'kurinsa ba dai macen bil'adama ta tankwabar da shi ba, saboda tsananin dadinsa da shauki mai makalewa a kwanya da zuciya.

To a yauma hakan ta tsinci kanta, tunda ya 'kira sunan ta ana goma shi takwas, shikenan ta ji wata irin kewarsa na yi wa gangar jikinta wani irin kutse mai karfin gaske, ta fara mutsu mutsu.

Yana kallonta, Yana jin da'din yadda ya fara samun lagonta dan haka ya sake lankwashe murya ya cigaba da 'kiran ba kakkautawa.

Zuciyarta ta yi laushi tubus, ta sami sau'kin nauyin da ta yi adilin kishi, domin ta gasgata shi da ya ce har yanzu shine bai canja ba, ba kuma abin da ya ragu na soyayyarta a zuciyarsa.

Cikin muryar tabarah ta zallan shagwaba ta ce "Haba Mana, Inna ta na cikin gidan nan fa! Ni dai ka daina, na amsa Na'am, Na'am Na'am".

Ya zuba mata idanuwansa da suka kada tamkar ya tashi daga barci ne.

Murya ba amo ya ce "Ba zan boye miki ba, sha'awar ki nake ji sosai, tunda muka rabu nake fama da matsanancin ciwon kai da mara, sosai na sha wahala a farkon shekaru uku da rabuwarmu, a lokacin da nake Uk, na sha zarya a gaban manyan likitoci, suka tabbatar mini rashin mace a kusa da ni ne dalili.
Da na yi aure na samu sassauci, baya tashi sosai, ko ya tashin ma baya takura ni sosai, amma wallahi Sa'adah, tun ranar da muka kai ki gidan Anty Sumayya nake Jin alamun ciwon na neman takura ni, jiya ko runtsawa ban yi ba, adalilin yadda nake jin ciwon da marata take yi, ga gangar jikina taki sarrafuwa domin ba abin da take so ya rabeta sai ke".

Ya bu'de dukkan hannuwansa yadda yakee mata tun fil azal, da rawar murya ya ke fadin "come closer to me my dear"!


Kishin yadda ya tabbatar mata, bayan ya yi aure ya samu sau'kin ciwonsa, ya sake sawa ta hargitse.

A tunzure ta ce "ka gaggauta tafiya ka rungumi wadda ta kwantar maka da ciwon rashin mace da ka yi fama da shi a baya! Wai kwana ka yi baka yi barci ba, kwana ka yi dai kana rarrashinta, kana kasheta da soyayya amma saboda ka mayar da ni bitacan shine ka karkace baki kana fa'din min tatsuniyar da ko Jawad yasan 'karya ne tsagwaronta, 'karya kawai".

Jikinsa ya yi sanyi, tabbas gaskiyar Baffah ne akwai abubuwa da yawa da Sa'a ba zata canja ba, domin a jininta ne, gashi dai a zahiri hankali ya shigeta, ilimi ya ratsata, Amma kishi yasa agabansa ta karyata shi, ba shayi ko shakka.

Wanda shi kuma ba zai ta'ba yarda ya sake daukan kaifin harshenta ba, a yanzu da take shekaru talatin da biyu.

Ya mike ya ce "Ni ne mai fa'dar tatsuniyar karya? Ni Kika karyata, nine makaryaci?"


Ta saci kallonsa, ta ga yadda ya bata rai sosai, ta yi shiru tana jin guiltiness na kamata, amma ta kasa bu'de baki ta ce masa sorry.

Ya kada kai ya ce "Tabdi jam ashe kuwa da sauran ki".

Dai dai lokacin Inna ta fito tsakar gida taga zogalen da ta ajiye wa Mk, yana gurin dan haka ta bude baki ta ce "Iyah zo ki daukar masa zogalen nan mana, nasan shi da son zogale".

Farin ciki ya mamaye Mk! Ba dan komai ba, sai dan sassaucin da yake gani tare da Innah.

Da azama ta amsa, ta kuma mike ta fita duk a kokarinta na kar Inna ta zargi wani abu.
Ta dauko ta ajiye masa a inda yake tsaye, kamshinta ya cika masa hanci, da ta sunkuya ajiye masa zogalen, ya ga yadda siket din jikinta ya matu'kar fito da taswirar mazaunanta, sai ya matu'kar kidima, ya dinga kokawa da zuciyarsa domin kuwa, ba zai sake kulata ba, har sai ta bashi ha'kuri.

A kausashe ya ce "juye mini a leda sai naje gida zan ci".

Ta sake juyawa ta fita! Tana jin tamkar ta bashi ha'kuri ya fasa tafiyar, ta sani badan maganar da ta fa'da ba, da sai anyi kiran sallar azahar da ya tafi, haka Kuma zai ta zama yana rarrashinta da son ya jagwalgwalata.

Amma yanzu zai tafi gurin matarsa, ya barta da kewa da bacin ran zuciya.

Ta hango shi ya zaunar da Farida a cinyarsa yana bata zogalen a baki, tunda ta san shi da son dora mace a kan cinyarsa.

Tana juye masa a ledar ta ri'ke, ta kasa bashi, kawai ta saka masa kuka.

Ya yi sakare yana kallonta, yana ayyana ko sai yaushe zata daina kukan banza marar dalili, ya sani tafiya gida da ya ce zai yi ne ya mata ciwo.
Tabbas kishinta ba zai bari su yi amarci mai da'di ba, ba zai bari su rayu cikin farin-ciki ba.

Shikuma ya riga ya kudire duk runtsi ba zai rabu da FARIDA ba, zai yi kuma dukkan kokarinsa ya ga bai tashi a sahun masu shanyewar barin jiki ranar gobe ba.

Wahala ne dai zasu dandana shi da ita tunda idan ranta ya baci, ko idan ya ganta cikin rashin nutsuwa shima hakan zai zama marar nutsuwar. Domin ya tabbatar itace jagorar farin-cikinsa.

Ya daure ya kore raunin da yake neman sawa ya fasa tafiyar, ya kalleta sosai ya ce "Zaki san kin ce mini makaryaci, na rantse miki sai na miki abin da gaba idan zaki mini magana, sai kin tauna harshen ki sosai. Godร i godร i da ke amma lafazinki na yara 'kananu, ko Farida ai ba ta mini irin wannan iyashegen".

Ai kuwa ta fร di kan shimfidarta ta fashe da kuka, tana cewa "Na gode da cin fuska, kullum sai ka mini gorin na tsufa, saboda kawai na haifar maka Jawad! to wadda kake yiwa kallon 'kuruciya saboda Ubangiji ya jinkirta mata haihuwar ta girme ni da shekara guda, domin ina Sha bakwai na kammala sakandire, ita kuwa Sha takwas cif. Amma saboda son sai ka nuna itace mai daraja shiyasa kake bata kuruciya, ni ka maida ni tsohuwar mace, to koma menene dai, kai ka zuke mini komai, sannan daga kai har ita dukkanku kun girme mini".

Ya Galla mata harara tare da cewa "Sokuwa marar wayo kawai, wacce ba abin da ta iya sai kaifin harshe da kukan banza".

Ya juya ya fice, bayan ya dauki wayarsa a inda ya tashi, ya barta tana kukan banza nata.

Sai da ya yiwa Innah sallamah, sannan ya fita.

Ya fito ya bu'de but din, ya samu almajirai biyu, ya dinga basu kayan suna shiga da shi. Sai da suka kammala ya basu dari biyar ya ja motar sa ya yi gidan Hajiyar Bichi.

Ya isa ya tarar da Hajiya cikin Shirin fita unguwa, ya zauna ya gaisheta, ta amsa da murmushin da ya jima bai ga ta yi masa irinsa ba.

Ya murtsike kunya ya ce "Hajiya ki yiwa 'yarki magana, tana nemana da jidali, ta fa'dawa Baban Na'ibawa ba yanzu, zata tare ba, saboda Allah wanne shiri zata yi? Tunda tana jin maganar ki, ki mata magana, wannan ai tsokanar shari'a ne, an daura aure mace ta cigaba da zaman a gidansu".

Hajiya ta daure fuska sosai! Ta zuba masa ido na tsawon lokaci, shikuma ya sunkuyar da kansa kasa, ba dan ya yarda ya yi laifin da take masa kallon tuhuma akansa ba.

Ta nisa ta Nuna kanta ta ce " Ni ka zo kana fa'dawa wannan maganar? Shi Babanku kana jin nauyinsa, kana ganin mutuncinsa shiyasa ka kasa cewa komai a gabansa, sai ni da ka raina zaka zo ka yiwa rashin ta ido?"

Ya kuwa maze ya ce "To ni ya zanyi ne? ni wallahi ki yi magana, bana so a kaini bango, ban so na fusata, dan kuwa komai yana iya faruwa".

Mamaki ya kamata, ko da yake a halittar maza ne, idan suna son abu idonsu rufewa yake, ta yadda zasu iya murje kunya su yi abin da za'a dauki shekaru ana Jin nauyin abin da suka yi din".

Ta rasa inda zata sa ranta don kunya, domin kuwa ta gama gane tsananin zakuwar da ya yi ya kebe da Sa'a.

Amma sai ta ce "To tashi ka fitar mini, ai kaga fita zan yi".

"Kwanciya zan yi, na huta, ki je ki dawo, bana Jin da'di ne da na Kai ki, ko ki zauna na Kira Abbas ya kai ki".

"Wallahi ba zaka kwanta mini a gado ka mini sake sake ba, ko kunya ba ka ji, ko Jawad idan yana kwance wataran takura nake yi, bare kai, baka tashi zuwa mini sai ka yiwa yarinyar arziki rashin kyautatawa. Dan kawai kasa na ga bekenta, to nikam har yau banga laifin Sa'a ba, sai nauyinta da nake ji".

Ya mata shiru ya dauki ledar zogalensa ya fice, tunda ta riga ta rantse ba zai kwanta ba.

Ya fita yana fa'din "Na tafi Hajiya, Sa'a ta ri'ke ki gam, ta tattare komai a gunki, ai shikenan, nima sai na hada kai da Farida baiwar Allah".

"Komai zaka fa'da, ka fa'da ni Farida bana ganin laifinta, bata mini komai na laifi ba, Nima kuma na sani bata kuka da Ni, sai dai kuma ko kai wallahi baka fi mini Sa'a ba".

Ya fita yana cewa "ai shikenan sai ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta nema ta samu fitinanniyar yarinya kawai".

****

Sai da ta aka yi sallar la'asar sannan suka bude kayayyakin da Mk ya jido Mata, wadda kayan shayi, da sabualan wanka mai tsananin gyara fata na *OLAY* *(quench)* ya hado mata setin su har da bath gel dinsa, da mayukansu.
Sai kayan ciye ciye na gwangwani kala kala tamkar zata bude kanti.
Indomie da kwai suma ga su nan birjik.

Inna ta yi galala ta ce " ban gane wannan siyayyar ba, kuna nufin haka zaku zauna, ba za ki tare ba? Dan na ga wannan kayayyakin yana nuna cewa ba yanzu zaki tare ba".

"Eh Innah ni na ce ba yanzu ba, domin ai ban shirya komai ba".

Ta nisa ta ce " Kika yanke hukunci babu shawarata, ko ta Yayarki saboda kawai kin zama uwar kanki! Ki sani to ba dabara kika yi ba, tunda an riga an daura aure, ai ba abin da shari'a bata bashi dmaa ba, bijirewar umarninsa kuwa ai kin san yana nufin

Please Login or Register in order to submit comment