You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Kai waccan baby an zuba mata halitta Billahillazi da ina da kudi da na yi kerwa da ita."

Tun tsayuwar motar MK ya ji zuciyarsa ta tsinke musamman da ya ga mace a gaban motar ta kare fuskarta, haka kawai ya dinga fatan kar ta kasance Sa'adah ce, ya san zai yi wahalar gaske ta zama ita ce, amma sai ya kasa nutsuwa, a lokacin da ya ga Khalil ya fito da gadara sai ya tabbatar Sa'adatu ce, take ya ji wani irin matsanancin kishi ya kama shi, irin kishin da yake danne soyayya.

Maganar da wannan saurayin ya yi na yabon surar ta sai ya sake ninka bacin ransa wanda bai taba Jin irin sa a tsawon rayuwarsa ba.

Zuciyarsa ta yi zafi, take ya ji yawun bakinsa ya kafe makogaronsa ya bushe, kansa ya sara da wani irin ciwo mai tsananin gaske.

Ashe Sa'adah da Khalil ta fita, ashe shi yasa ta kashe wayarta, don ta nuna masa tana tare da wanda ya fi shi, ta kuma yarda ya kawo ta har titin da take da tabbacin zai iya ganin su a tare, karo na farko da ya ji ya yi kuskuren barin Farida saboda Sa'adah.

Ya tabbatar ta fi ta son sa kawai dai shi Sa'adah ce ta fi shiga zuciyarsa, kuma ta fi daukar hankalinsa.

Ko ta kan gyaran mashin din bai tsaya ba, ya tari abin hawa ya nufi gidansu, kafin ya isa wani irin zazzabi da azababben ciwon kai sun masa mugun kamu.




Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.


*TALLAH*.

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._







45-46



Tana shiga zauren gidan ta fito da hijab ta sanya, sukuku ta shiga gidan. A tsakar gidan ta sami iyayenta. Tsoron da ke cikin zuciyarta ya sake bayyana a fuskarta da jikinta.

Baffa ne kawai ya amsa sallamar, da 'kyar ta tsugunna ta gaishe shi, ya amsa ba sakin fuska, ya kalle ta fuska ba wasa ya ce, "Daga ina ki ke?"

Cikin rawar murya irin ta rashin gaskiya ta ce, "Zainab na raka gidan yayarta kuma sai da na tambayi Inna."

A kufule Inna ta ce, "Tabbas kin tambaye ni amma ce mini kika yi ba za ku dade ba, don haka na gode miki da cika al'kawari."

Ganin yadda ran Inna ya baci sosai sai shi kuma ya sassauta, ya mata nasiha tare da cewa, "yarinyar kirki in dai ta san kanta, killace kanta take yi a gida, bai kamata dare ya riske ta a waje ba."

Har ya sallame ta sai kuma ya ce, "Yawwa dama zan fada miki, aurenki bayan sallah za a yi, nan da wata uku kenan.
Bayan haka kuma na sanar da iyayen yaron cewar kar ya yi lefe, ni ma kuma ba zan wahalar da kaina wurin saya masa kayan daki ba, ke zan ba shi ina kuma da yakinin na miki tarbiyar da zai sami nutsuwa da ke. Uwarki kuma ta koya miki yadda zai yi alfahari da ke a matsayin uwar yayansa. Haka na yi wa Sumayya har yau din nan da ta kai shekaru goma a dakinta ban taba jin ance mini ga wani abu na kaico daga gare ta ba, mijinta kullum kara girmama mu yake yi, Ina fatan ki yi koyi da ita, Tashi ki je."

Ta mike ta wuce dakinta cikin wani irin yanayi, tana zuwa ta fadi kasa ta fara kuka kasa-kasa, tana jin karshen tozarci an yi mata.

Ta ya ya za a dinga hada Sumayya da ita, ai ba lokacin su daya ba, sannan ba iyayen mijinsu daya ba, a wannan zamanin ma an kai yarinya da kayan daki idan ba na alfarma ba ne, dangin miji suna yi wa yarinyar izgili da habaici, to ina kuma ita da za a kai ta tsurarta? Wanne irin raini da kaskanci za a janyo mata? Ba'kin cikinta ya ninku ta rasa inda za ta tsoma ranta.

Ashe shi yasa MK yake mata gadara da isa, saboda an nuna masa sadaka za a ba shi an dauke masa lefe? Shima kuma kar ya sa rai za a je a yi masa jere. Ba ta san lokacin da ta bude murya ta dinga zunduma ihu ba.

Daga Inna har Baffa a kidime suka mike suna rige-rigen isa dakinta a tuninsu wani abin tsoro ne a dakin, ko maciji ko kunama ta harbeta.

Sai dai ganin ta ras illah kukan da ta bare baki tana yin sa tamkar yarinya yar karama yasa suka yi cirko-cirko! Baffa ne ya ce, "Mene ne ya saki wannan ihun sai ka ce wacce ba ta zuwa Islamiyya, ba za ki ambaci Allah ba! Sai ki cika mana kunne da kuka har da ihu?"

Cikin kuka sosai ta ce, "Ka taimake ni Baffa! kar ka kai ni ba kayan daki wallahi gori za a yi mini, ko a yi ta zunden sadaka ta ka bayar." Ta karasa cikin gunjin kuka.

A zuciye Inna ta ce, "Watau ke ba za ki bi shi ba, sai shi ne zai bi ra'ayinki, ke kullum sai an yi artabu da ke? Kin taba ganin wanda ya bi iyayensa bai ci ribar rayuwarsa ba? Ashe ba za ki koyi da yayar ki ba?"

Ta sake kara sautin kukan ta ce, "Ai samun irin mijinta da yan'uwansa sai an tona a wannan lokacin, sannan kuma ni da ita akwai banbanci."

Takaicin ta ya kama Inna ta ce, "Banbanci kuwa a bayyane, ita ta yarda duk talaucinmu, mu ne iyayenta, za mu yi iko a kanta ba tare da ta ga gidadancinmu ba, sannan karatu kadan ta yi amma mai cike da ladabi da biyayya, in sha Allah Ubangiji ba zai kunyata ta ba."

Tana fadin hakan ta fita ta bar su da Baffa.

"Iyah!" Ya kira ta da muryar da bai saba mata irin ta ba, tunda shi kullum a cikin lallashi da tausasawa yake mata magana.

"Na riga da na zartar da maganar nan a gaban Mutari da iyayensa, ba zan koma na ce na fasa ba. Ko a fuska kika nunawa yaron nan tsarina bai miki ba, ki tabbatar kin nuna ban isa da ke ba, ba kuma zan sake yin iko akan ki ba."

Ya na rufe baki ya juya shi ma ya fice abinsa, sai ji ta yi kukan ya tsaya mata cak!

Amma wani irin ba'kin ciki take ji ya shake mata wuya da zuciya. Da 'kyar ta fita ta yi alwala ta yi sallar Maghrib da Isha wanda ba nutsuwa a cikinsu.

Da rarrafe ta isa kan shimfidarta, hawaye na bin fuskarta, ta ya ya za a mata irin wannan auren sai ka ce mutanen da? Ai ko shi Baffan da zai auri Innarsu, ya mata hidima, ita ma kuma da kayan dakinta aka kawo masa ita har yanzu gadonta na aure ne a dakin, duk kuwa da auren zumunci aka musu, shekaru kusan talatin. Amma sai ita a wannan lokacin za a mata irin wannan auren, kuka ya sake balle mata.😭

Tsawon lokaci tana kuka har kanta ya fara ciwo, a ranar dai ba ta yi wani cikakken barci ba, ba ta tuna matsalarta da MK ba sai da Asuba.

Tana idar da sallah ta ciro wayarta a caji ta lalubo lambar MK ta kira, har ta katse bai dauka ba, ta kira ya fi sau biyar amma bai amsa ba. ta ja wani dogon tsaki tana furta "Sai ka yi ta yi."

Ta kwanta ta yi shiru, amma sai ta kasa hakuri, ta sake kiran sa, nan ma bai dauka ba, ta yi ta kira har ta gaji, takaici ya sa ta yi jifa da wayar.


Har rana ta fito tana kwance ta ki fita, fishi sosai take yi, ga idanuwanta sun kunbura saboda tsabar kuka.

Inna kuwa ko ta kanta ba ta bi ba, ta yi dukkan ayyukanta, ta yi abin karin kumallo suka karya da Baffa amma ba ta nemi Iyah ba bare ta ba ta.

Sai da Baffa zai fita ne ya tsaya bakin kofar dakinta ya kira ta. Ta fito sanye da hijabi duk fuskar ta a kumbure, ta tsugunna ta gaishe shi, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Iyata yau ban ji motsin ki ba ga shi har zan fita, kin san idan ban gan ki ba yini zan yi ba kuzari".

Ta sake yin kasa da kanta hawaye na cika mata ido, "maza fito ki yi wanka, ki sami abinci ki ci idan zan dawo zan taho miki da indomie har da Sadine na gwangwani, da ma kwanaki kin ce mini indominki ta 'kare, yau zan sayo miki ki ajiye a dakinki har da madara."

Cikin kuka ta ce, "Na gode"

Ya tafi yana jin kukan ta har cikin ransa, ya na raya yadda Sumayya ta zarta ta biyayya da gudun zuciya amma Iyah tafi shiga ransa matu'ka da gaske.

Ko da ta koma dakin sai ta sake dasa sabon kuka mai cike da kururuwa, yin sa take iya karfinta, fishin da MK ya dauka ya sake dagula mata lissafi.

Tun Inna na danne bacin ran ihun da Sa'adah ta cika mata kunne da shi, har ta kasa jurewa.

Don haka ta shiga 'daki ta samo wani danko mai kauri ta nada a hannunta, ta nufi dakinta, tana shiga kuwa ba bata lokaci ta shiga zabga matata ko ina, da iyakacin karfinta, da kyar Sa'adah ta kwace ta fice a guje, ta nufi hanyar zaure ta tsaya tana kuka sosai.

Ta dade kafin ta dawo gidan, tana rabe-rabe, Inna ta kalle ta rai a bace ta ce, " Idan kin san za ki ta sani a gaba kina mini kukan iyashege ki juya ki tafi duk inda za ki shiga, watau ni kika raina? Kin ga Baffanku ya fita shine za ki 'bude mini wannan ja'irin bakin naki da bai iya komai ba sai 'kulla karya da munafunci kina mini ihu. Wai har kin yi wayon da yafi nawa, ni za ki yiwa karyar Zainab za ki raka unguwa? Ashe da wannan shedanun kawayen naki masu yi wa Babba kallon raini kuka fita, har kin yi lalacewar da za ki shiga gaban motar namiji ya kawo ki har kofar gidanku, ki fito akan idon jama'a, oh ni Salamatu wacce irin yarinya nake tare da ita ne haka?"

Ta Fadi hakan tare da tafa hannu tana salati.

"Wai kuma don ki bata ni a gunsa shi ne zaki ce nasan zaki fita, to don uwarki daga yau kika kuskura kika ce mini za ki fita da sunan zuwa unguwa wallahi sai jikin ki ya fa'da miki. Na daina raga miki tunda ke rarrashi baya bi da ke, kafin nan kafin ki bar gidan nan sai na miki tabbuna ba ma tabo ba. Tunda nake da Baffanku bai taba ganin kasawa ta ba sai akan ki, jiya da daddare ba abin da bai fada mini ba, bayan an tabbatar masa a mota aka kawo ki."

Jikin Sa'adah ya yi sanyi kalau, ta yi shiru amma hawaye bai daina zubo mata ba, tana jin tsanar Khalil sosai a ranta duk shi ya janyo mata wannan tashin hankalin, da ya ajiye ta a hanya ai da ba wanda ya ganta, ga fushin Uncle MK, ga fishin Baffa duk da dai shi mai yawan yi mata afuwa ne. Amma yau har zane ta Inna ta yi, ba za ta iya tuna yaushe rabon da Inna ta dake ta irin haka ba.

A darare ta shigo ta shige dakinta, ta fito da shirin wanka, sai da ta fito ta shirya, sannan ta je ta tambayi abincinta, ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ban yi dake ba tabbatacciya! Kina kwance na tashi na yi komai saboda zuciyarki ba imani balle tausayi, amma har ki iya cewa ina abincinki? Saboda ga baiwa kin ajiye, to ga tuwo can da kika raina sai ki hada wuta ki 'dumama, idan kuma kin fi nan sai ki zo ki dora abincin rana idan kin gama sai ki ci."
Tana kaiwa aya ta ja bakinta ta tsuke.

Cikin rawar murya ta ce, "Me zan dora?"

Kamar ba za ta kula ta ba sai kuma ta ce, " Dambu!"

Hawayen da ta ke matsewa ya balle tasa gefen dan'kwalinta ta goge, sannan ta ce, "To!"

Haka ta hau aikin sarrafa dambu tana goge hawayen da ya'ki yankewa ta san dan a musguna mata yasa aka 'kir'kiri yin abincin da zata jima bai kammala ba. Ba ta sami kanta a hannun Inna ba sai wajen karfe uku, saboda yadda ta'ki sa mata hannu, ada idan za su yi dambu kusan Inna ke jagorantar yi, kawai sai dai Sa'adah ta sa ido tana lura tare da gyara gyada ko zogale.

Amma na yau komai sakar mata ta yi, ta kuma kara yawansa a cewar ta za ta aika wa makwabta, ita dai Sa'a ba bakin musu saboda a tsorace take da ita don ba karamin duka ta mata ba.

Faranti guda ta cika da danbun ta debi ruwa a randa mai sanyi ta sami inuwar bishiyar dake tsakar gidan, ta fara ci hannu baka hannu kwarya tamkar ba Sa'adah mai cin abincin a gayance ba.😁

Inna na kallon ta a ranta ta ce, "Ja'ira yau kin gane yunwa ba kanwar uwa ba ce."

Sai da ta share abincin nan tas ta yi gyatsa gumi ya karyo mata, ta yi Hamdala. Ta jima a zaune a gun, sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan ta cika bokiti da ruwa, ta jira Inna ta fito a bandakin sannan ta shiga wanka.

Sai da ta yi sallah sannan ta shirya, kana kallon ta kasan zuciyarta ba walwala, tana zaune waya a hannu tana ta kiran MK amma ya ki dauka, lamarin da ya sake dugunzuma damuwar da take ciki, a fili ta ce, "Me yasa nake son mutumin nan ne?" Ta sunkuyar da kai tana tunano adadin yadda take shiga damuwa saboda shi.

Haka ta ci gaba da kira ba kakkautawa har ta gaji. Sai kuma ta koma tura text din ban hakuri da maganganun soyayya masu taushi. Amma ko sau daya ba ta ga amsa ba duk kuwa da sun nuna mata sun yi delivered, (Watau sun je).

Wasa-wasa sai da aka shafe sati biyu ba ta ji daga MK ba idan kuma za ta yini tana kira ba zai dauka ba.

Abin ya yi matu'kar tayar mata da hankali tun tana boyewa har abin ya fara fin karfinta, ta zama wata iri, ko abinci ba kasafai take iya ci ba. Ga Inna ba sakar mata fuska take yi ba, abin ya hade mata biyu, ta fara ramewa a tsaye.


***

Bangaren Mk kuwa ba karamin zafi ya dauka da Sa'adah ba, kwana biyu ya yi a kwance yana fama da ciwon kai da wani irin zafi a cikin kirjinsa. Idan ya tuna yadda Sa'adah ta fito a gaban motar Khalil jikinta a dame sai ya ji tamkar ya shide, haushin ta yake ji ba ka'dan ba, gara ya gan ta da Alhaji Mamman akan wannan dan iskan yaron, so yake ya hakura da Sa'adah amma kunyar mahaifinta yake ji musamman yadda ya girmama lamarinsa.

Sannan ya san ko giyar wake yake sha bai isa ya tunkari iyayensa maza da maganar ya fasa auren ta ba, ya rasa inda zai tsoma ransa. Yana ganin yadda kiran ta yake shigowa wayarsa ba adadi. To me za ta ce masa? Ta je su karata da wanda ta zaba.

Kwanaki na ta shudewa, damuwar da Sa'adah ke ciki na sake karfafa, tsawon kwanaki ashirin ke nan MK bai dauki kiranta ba, balle kuma shi ya kira.

Ranar wata Laraba da daddare suna zaune da Inna a tsakar gida amma kowa na gefensa, Yan NEPA suka kawo wuta, daidai inda Sa'adah ke zaune hasken ya fi karfi, Inna ta zuba mata ido tana kallon yadda ta lalace ta birkice. Nan da nan tausayin ta ya kama ta, sai dai ba ta nuna mata ba, amma ta kudiri aniyar yi mata sassauci.

Washegari kuwa da walwala ta amsa gaisuwar Sa'adah, ta daina daure mata fuska, idan ta mata magana cikin dadin rai take amsa mata, sab'anin lokutan baya da hantara ce a tsakaninsu.
Afuwar da Inna ta yi mata yasa ta samu sau'kin halin da take ciki, amma har yanzu ba ta da kuzari da walwala, Inna da kanta ta ce mata, "Idan ban manta ba na kai wata ban ji Muutar ya zo ba."

Sunkuyar da kai kawai Sa'adah ta yi ta kasa cewa komai! Amma idanuwan ta sun kawo 'kwalla.

Ganin yanayinta ya tabbatar mata akwai matsala a tsakaninsu ta ce, "Hala kin sallame shi saboda ba zai miki lefe ba?"

Da sauri ta ce, "Haba Inna! Ni wallahi ban sake tayar da maganar ba."

Cikin takaici sosai Inna ta ce, "To labarin abin da kika aikata ya same shi."

Ganin hawaye ya kwace ma Sa'adah ya sa ta hadiye fa'dan da za ta fara yi mata, sai ta bige da fadin, "Kadan ke nan a cikin sakamakon da mai yin 'karya ya ke fuskanta."

A ranta kuma tana raya dole su yi magana da Baffa akan rashin zuwan MK shirun ya yi yawa.

Washegari Zainab ta kawo mata ziyara, suna zaune kan katifarta, "Sa'adah me yake damun ki haka?" Zainab ta fada cike da mamakin ramar da ta ga Sa'adah ta yi.

Bata boye mata halin da take ciki ba, ta zayyane mata komai.

Cikin takaici Zainab ta ce, "Ai indai kina biye su Safina sai sun kai ki sun baro, ka'dan ke nan."

Tana kuka ta ce, "Ni yanzu ki nemo mini mafita don Allah!"

"E ai yanzu da yake ta kwabe miki za ki neme ni, amma lokacin da kika bi su ai ban sani ba."

Waya ta mi'ka wa Sa'adah tana fadin, "Saka lambar Uncle Mukhtar din mu kira shi da layina." Jikinta na rawa ta karba ta hau jera zababbun lambobinsa, tana fatan Allah ya sa ya dauka tunda har layinta da bai san da shi ba ta sha 'kiran ba ya 'dagawa.

Cikin Sa'a kuwa ya dauka! Zainab ta gaishe shi, ya tambayi wacece?
Ta amsa da gabatar da kanta, sai ta shiga ba shi ha'kuri a madadin Sa'adah, ya yi shiru har ta gama.

Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce, "Ba dan ina ganin hankalinki ba da ba zan saurare ki ba. Ki yi hakuri, ki cire kanki a cikin wannan maganar, ba zan iya da halin yarinyar nan ba, duk yadda nake zaton ta ta wuce nan". Yana fadin haka ya katse wayarsa.

Bugun da zuciyarta take yi ya sake tsananta, a rikice ta ce "Zainab mai yake nufi? Ya fasa yi da ni ke nan?"

Cikin son ta kwantar mata da hankali ta ce, "Ba fasawa zai yi da ke ba In Sha Allah! Kawai ya yi fishi ne sosai, ai kema kin san ba ki kyauta masa ba."

Ta dade tana kwantar mata da hankali, kafin ta mata sallama ta tafi da al'kawarin za ta sake tuntunbar sa.

Kwanaki biyu da zuwan Zainab, Anty Sumayya ta yi waya Sa'adah ta je ta karbo mata sa'ko a karkasara gidan kawarta.

Akan dole Inna ta barta ta fita bayan ta sha jan kunne da nasiha iri-iri akan kar ta biya ko ina, har kunya ta kama Sa'adah ta na jin ita ta janyo wa kanta rashin yarda a idon iyayenta.

Tana karbo sakon ta juyo, duk da yadda Anty Walida ta yi nacin ta zauna ta karasa yi mata yinin, ita kuma ganin biyu da rabi ta yi yasa ta gaggauta fitowa dan ta zartar da kudirinta na son ganin Mk a yau.

Kai tsaye FGC Kano ta sauka, sai dai ba makarantar ta shiga ba, gangare can gefe ta tsaya inda suka ta'ba tsayawa da shi, ta san kullum ta nan ya ke bi. Cikin sa'a kuwa ba ta dade tana jira ba ta hango shi, yana doso inda take, a kafa yake tafiya. Ta ce, "Ko ina ya baro dan mashin 'din?"

Sanye ya ke cikin 'kananun kaya yana rataye da jakar da yake zuba takardun shi, ya mata kyau sosai duk da ta ga ya dan zube kadan.

Sai da ya wuce ta sannan ta bi bayansa, jin ana ta bin bayansa yasa shi jiyowa, ba zato idanunsu suka sarke, ya hade girar sama da ta kasa tamkar bai ta'ba dariya ba, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa tamkar bai gan ta ba.

Sai lokacin ta yi magana "Uncle na yi kewar ka, idona sun yi kukan rashin ka!"

Ya ji ta sarai, bacin ransa ya dawo sabo, ya rasa wane matakin zai ajiye Sa'adah, duk inda ya ke ajiye ta, yau ya tabbatar masa ta kere gurin!har ta san ta bi saurayi gun aikinsa?

Ita kuma ganin bai kula ta ba har sun fara hango titi sai ta fara masa kukan da babu hawaye tana kuma fadin "Zuciyata ba za ta iya daukar fishinka ba, ka kalle ni ka ga yadda fishinka ya ramar da ni, ba na iya barci, ba na iya cin abinci, kamin afuwa, don Allah ba don halina ba!"

Ta fada cikin wani irin yanayi mai motsa ZUCIYA.

Ya juyo ya zuba mata ido tabbas ta rame, ta birkice amma hakan bai yi tasiri a zuciyarsa ba, musamman da ya tuno kallon rainin da Khalil ya yi masa, ya sake hango yadda ta fito a gaban motarsa, sai kawai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya ce mata uffan ba.

A kidime ta ru'ko hannun jakarsa murya na rawa ta ce, "Na san na yi ba daidai ba, na ba ka ha'kuri, ka yi hakuri mana!"

Bacin rai sosai a fuskarsa ya dube ta sannan ya ce, "Ke ba na son ballagazanci, a titi za ki ri'ke ni?"

Ba'kin ciki ya kama ta ta fara kukan gaske ta ce, "Ni ka kira da ballagaza?"

Kishi ya rufe mai ido sosai, ba wani ja-in-ja ya ce, "E, idan akwai sunan da ya fi haka muni ma ki hada da ballagazar, don kuwa sunayenki ne, dabi'un da kike yi irin nasu ne. Yanzu kuma kin nuna mini kin saba cu'danya sosai da maza, har kike ganin za ki iya cakuma ta a titi."

Ba'kin ciki ya turnuke ta, ba a taba yi mata tozarci a rayuwarta irin na yau ba, kuka sosai take yi wanda ya matu'kar taba shi, kawai waskewa ya yi. ba tare da ta sake fadin komai ba, ta yi gaba da sauri ba ta ko sanin inda take jefa kafarta saboda tsananin 'bacin rai.





Al'kalamin
*Surayya Dee*
✍🏼✍🏼✍🏼


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ

Please Login or Register in order to submit comment