You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ayman 'din Sumayya, duk da Ayman din ya bashi shekaru biyu, amma abota suke yi sosai.

Inna ta tashi ta dauko hijabin ta da ke rataye a bakin 'kofa ta saka tana tambayar Jawad wa ya kawoka?
Yace "Malam ne", ba ta zauna ba ta dauko tabarma ta shimfida a inda ta saba shimfida masa, tana ayyana
tasan zai shigo, aikuwa kafin ta dago ta ji sallamarsa.

Ganin Sumayya lullube ta ke da mayafi, Sa'adah ce kawai a zaune ba mayafi daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda wuyan ya mata yawa tsabar rama, kanta ba dankwali asalima tsifa take yi, ga tulin gashinta a gefen ta wadda ya ke zuba tamkar wutar daji.


Inna ta amsa masa tare da bashi iznin shigowa, Sa'adah da tun jin sallamarsa ta daskare a zaune, ta rasa me za ta yi duk kuwa da yadda Jawad ya saki Ayman ya zo ya haye cinyarta yana taba wuyanta, alamun ramar da ta yi shima ta bashi mamaki.

A hakan Mk ya shigo, idonsa ya fada cikin na Sa'adah, gabansu ya buga a tare da azama ya dauke idanuwan sa, ya isa ga tabarmar da yasan dan shi aka shimfida, a ransa ya dinga godewa ubangiji da 'kaddare shi ya shigo, da ya kunyata Inna.
Suka gaisa cike da kunya da girmamawa tamkar komai bai faru ba, haka suka gaisa da Sumayya.

Da Sa'a ta gaishe shi ya amsa mata ba yabo ba fallasa, amma yanayin da ya ganta ya matu'kar bashi mamaki da tausayi, mussaman da ya ga Jawad ya lafe a jikinta.

Ba ta ji kunyar Inna ba,
bare Sumayya, ta ajiye Jawad ta mike ta dauki hijab ta bi Mk hanyar waje, a zaure suka tsaya, ya zuba mata ido, bai ji so ko tausayin yadda ta lalace ba, domin tare suke shan bakin cikin, kawai dai shi Namiji ne, namiji kuwa da juriya aka san shi.

Ya daure ya ce "har yau ba ki fara cin abinci bane? kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa?"

Hawaye ya 'balle mata ta ce " Ka yi hakuri , na 'kira Jawad ka tafi da mu, ka mayar da ni gidanka, ba sai ka kulani ba, zama tare da kai 'karkashin inuwar aure ya gamsar da Ni".

Ya yi murmushin da babu nisha'di ko kadan yace " ba kya yawan addu'a, ki nemi zabin Allah a tsakanin mu, ba son rai ba, sau da yawa mukan so abu 'kololuwar so, sai abin ya zama sharri ne a garemu, hakan nan muna 'kin abu iyakacin 'ki, sai ya zama alheri a garemu".

"Kar ka kwatanta ni da sharri Malam, ina hadaka da girman Allah ka yi hakuri ka yafe mini".
Ta tsugunna guiwa biyu a 'kasa

Ta cigaba da cewa "saura 'kiris na kammala idda, ka taimake ni, ka ji 'kaina."
Daidai lokacin Baffa ya shigo zauren ya kewaye su ya wuce ba tare da yace uffan ba.

Jikin Mk ya yi mugun sanyi, bai so Baffa ya gansu a haka ba, ya dubeta ya ce " ki koyi karban rayuwa a yadda ta zo miki, ki kuma daina wasa da damar da rayuwar za ta baki, na so ki, iyakacin so, amma menene amfanin son da babu kwanciyar hankali ko aminci a cikinsa?"

Da haka ya juya da sauri yana fadin "ki yi murna kin zama 'yantacciyar macen da ki ke fata".

Ta jima tana kukan zuci da na fili, sannan ta shiga gidan, ba ta tsaya a tsakar gidan ba ta shige daki ta kwanta tana cigaba da rizgar kukan da ba ya amfana mata komai.

Ganin wulgawar Jawad ya dan rage mata kewa, ga Sumayya da take tausarta.

Ranar lahadi suna zaune, Sumayya na mata kitso bayan Ahamad 'kanin Mk ya zo ya tafi da Jawad, kawai suka ga ana ta shigo da kaya, kallon su kawai Sa'adah ta yi ta fahimci kayan ta ne Mk ya Aiko musu, tunda ya ga an'ki zuwa a debo.

Abin mamaki sai ba ta ji kuka ya zo mata ba, ko dan ta yi kukan har ta gaji ne?
Tsakar gidan sai da ya cika da kaya, domin duka gadajen nan uku ya Aiko mata haka nan kujerun falo da tv plasma hatta freezer da bai 'dade da siya ba, ya ha'da ankawo mata.

Ga wasu bakko guda uku sha'ke da kaya, Sumayya ta bude biyu duka kayan Sa'adah ne, ya yin da 'dayar labulaye ne da zannuwan gado a wanke a goge, sai lokacin 'kwallah ta zowa Sa'a, wato ya da'de yana shirya mata kaya, tunda ga labulayen da suke dakunanta ma ya cire su anwanke su. Haka akwatunanta duka kayanta ne a ciki, ba kayan da ba' a wanke an goge ba, a cikin fishi ma Mk ya iya alheri, ta ayyana a ranta.

Gwala gwalan ta ne kawai ba ta gani ba, indai ba a tsakiyar kayan ya 'boye su ba. Ilai kuwa cikin katon akwatin ta ya saka mat su a tsakanin kaya.

Dukkansu jikin su ya yi sanyi da ganin kayan, hatta Baffa da yake nuna mata bai damu ba, ganin wannan kayan ya tayar da hankalinsa, balle Inna da take ta faman goge hawaye a fuskarta.

Ganin hakan Sumayya ta roki Baffan su, za ta tafi da Sa'adah Gombe, ta kwana biyu, idan ta 'dan warware sai ta dawo.

Ya kalli Sumayya, a sanyaye ya ce "kin manta ba ta kammala iddarta ba? har yanzu a matsayin matar Mutari ta ke, bani da ikon da zan turata wani guri alhalin ba hakki na bane yin hakan".

"Baffa dan Allah ka bari mu tafi, mutumin nan, ba mayar da ita zai yi ba, gaba'daya ya fita a kaina wallahi".

Murmushi ya yi ya ce " Ban sanki da son zuciya ba, Sumayya! Kar son 'kanwar ki ya mayar da ke mai son kai, kinsan me ta shuka masa ne? Ruwa ba ya tsami banza, har yau ya 'ki fadan me ta yi masa, maimakon haka sai ya 'dorawa kansa laifi, Ina rantse miki da Allah! Iyah ce ta yi wani abu marar 'dadi, ko shekaranjiya na ganta durkushe a gabansa, Ni na fara tsoro da wasiwasi akan lamarin ta, Allah dai ya sa ba wani mugun abu ta yi ba"

Sumayya ta kasa magana, tausayin Iyah na ratsa ta.

Ko da shiga dakin a zaune ta sameta, ta tsurawa gefe 'daya ido, idonta a soye, sai da Sumayya ta kirata sau uku sannan ta amsa a firgice.

"Ki fa rage dogon tunani Iyah Ina jiye miki ciwon farat 'daya.

Ta dago ta dubi 'yar'uwarta ta ce "Dama na mutu Aunti".

Da sauri Sumayya ta ajiye Anis ta 'karasa kusa da ita ta rungumeta ta ce " idan ki ka mutu, ki barni da wa Iyah? ke ka'dai gare ni bayan Innah, ko da na haifi mace ba zata cike min gurbin ki ba, bare ban haifa ba, me yasa ba za ki duba wadda farin cikinsu na 'damfare da ke ba? Yanzu Mukhtar din da ba ki san shi ba sai da kika mallaki hankalin ki ne, zai sa ki yi fatan mutuwa ki bar Baffah, ki bar Inna, ki bar Jawad, ki bar Ni?"

Sai lokacin kuka mai ciwo ya gocewa Sa'a.

Sumayya ta cigaba da cewa ki fauwalawa Allah lamarin ki, ina tabbatar miki zai kawo miki mafita, ki ha'kura da Mukhtar yadda ya ha'kura da ke, ba sai da shi za ki rayu ba, ba sai da shi za ki yi farin ciki ba, ki dube mu, ruwa da iska ba zamu canja ki ba, shi kuwa ko gobe kina iya jin ya auri madadin ki, ya shayar da ita soyayya irin ko ma ta zarta wadda ya miki, fatana dai ki 'dauki darasi, kar ki sake maimata irin kuskuren da ki ka yi idan kin samu wata damar".

Ganin maganganun na shigar Sa'adah sosai, Sumayya ta zarce da fadin "gaba'daya aure ha'kuri ne da kawar da kai, duk macen duniya da ki ka ga ta tsufa a 'dakinta ta shiga 'kalubale kala kala, amma idan aka yi ha'kuri aka danne sai a cimmma babban matsayi, ki cire buri, da son 'kyale 'kyale ki rabu da 'kawayen banza na tabbatar wadannan abubuwan sun taka muhimmiyar rawa wurin mutuwar aurenki".

Sosai ta ke kuka a 'kirjin Sumayya karon farko tun bayan rabuwar su da ta samu ake rarrashinta cikin tausayawa.

Haka suka shafa lokaci mai yawa Sumayya na lallashinta, tare da 'karfafa guiwarta.

Kwanaki goma Sumayya za ta yi tare da yaranta, adalilin Yaran suna hutun zangon karatu na uku, sannan kuma mijinta na cikin tawagar da aka zaba zuwa New York din 'kasar Amurka akan sanin dabarun inganta bankunan 'kasashen Africa.

Zaman Sumayya ya taimaka wa Sa'a sosai, tare suke cin abinci, sannan sai da ta sa Inna ta sauko da ga fushin da take yi da ita, Baffa kuwa cewa ta yi tasan duk dauriya yake yi, amma ai shi da Iyah sai Allah.

Ya yi dariya ya ce "wato ta tabbata kema zargina kike akan na fi sonta, kamar yadda itama ta ke 'kalubalantar gyatumarku ta fi son ki".

Sumayya ta yi dariya ta ce "Ni bana kalubalantar ka Baffa, ai ita 'karama ce, sannan sunan iyakar ka ce".

"Allah ya miki Albarka Sumayya, yau kusan shekaru sha bakwai da auren ki, ba ki taba janyo mini bacin rai ko jin kunya ba, ina fatan ki dore da hakan, ina matu'kar jin dadi, Ina alfahari da kasancewa ta uba a gare ki, Àllah ya miki shirya miki zuri'a, ya faranta miki, ya buda miki kofofin alheri".

Cikin kukan farin ciki ta ke fadin "Ameen Baffa!ni ma Ina alfaharin da ka kasance uba mai kare mutunci da martabar yaransa a gidajen aurensu madallah da uba irin Baffah na".

Sa'adah da ke 'daki tamkar mujiya ta ji wani 'kullutun ba'kin ciki ya mamayeta tun farko dama tana kishin taga iyayen ta suna nunawa Sumayya soyayya sama da ita, duk da Inna ta fi wannan abin dan ta cusa mata takaici, amma Baffah kowa yasan itace 'Yar gaban goshinsa, amma wai yau ita ya ke yiwa zambo, yana nunawa Sumayya ce mutum, yana ta 'kwararo mata addu'a ita ka'dai.

Hawaye na zuba 'kasa 'kasa ta ce "Ni da na yi shekaru bakwai aka sako ni, sai a kore ni ko a tsine mini na bi titi ina tsince tsince".

Da sauri ta tura hular kanta a baki tana cewa " Astagafirillah Ubangiji ba da Baffah na ke ba da kaina na ke, Allah na tuba, ka yafe min, ka mini albarka, ka saukaka mini lamarina, ka mayar da ni 'dakina".







*SURAYYA DAHIRU*
✍️


🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU GWARAM*.


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A kiyaye ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din*
*M HAUSA NOVEL*
*MAMAN YUSUF FANS*.
*ASMA BAFFAH FANS*.
*MAMAN MAMAH NOVELS*.
*HUGUMA CONVERSATION*.
*THE SPARKLE*.
*DUNIYAR NOVEL*.
*UMMU ILHAM HAUSA NOVEL*.
*MARUBUTA*
*BENEFICIAL WRITERS*
*ZAUREN KARATUN HAUSA*.
*FAR JEED-DAH HAUSA NOVEL*
*BAKANDAMIYA HIKAYA*.
*QIYAS HAYAT HAUSA NOVELS

*_Dukkan ku madallah na gode da yabawa*_.



*Fatan alheri ga Aminyata*
*SHAFA'ATU ALHASSAN BAUCHI*
*Na gode sosai da yabawar ki kan rubutuna ubangiji ya dorar da zumuncin mu, Sa'adah ta ce ki rokar mata Mk*😁

*_JAN HANKALI_*
*BABU MAHALUKIN DA YAKE SO A TABA MASA ABIN DA YA SHA WAHALA KAFIN YA SAMAR DA SHI BA TARE DA IZININSA BA! SABODA HAKA A CIKIN MAFI YAWAN SHAFUKAN NA KAN YI GARGADI AKAN LAIFI NE TA'BA WANNAN LABARIN TA KOWACCE IRIN SIGA BA TARE DA IZININ MAI HAKKIN MALLAKA BA. A YAU NA CI KARO DA HALIN YAU DOCUMENT WADDA AKA YI BAN SANI BA, NA ROKE KU KAR A KUMA, NASAN SOYAYYAR LABARIN CE TA KAWO HAKAN, AMMA NI KO KUNGIYAR DA NAKE CIKI NE KA'DAI KE DA IKON YIN HAKAN, INA FATAN ZA'A FAHIMCE NI, DOMIN RASHIN KIYAYEWA KA IYA ZAMA DALILIN KATSEWAR LABARIN GABA'DAYA. UBANGIJI YA BAMU DAMINA MAI ALBARKA!_*


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.




81_82.


Zaman Sumayya ya taimaka 'kwarai wurin ragewa Sa'a damuwa, haka nan basu koma Gombe ba sai da suka kwashe kwanaki sha biyar a maimakon goma da za su yi.

Ranar da suka tafi ba 'karamin filin'dakin Sa'adah ta gani ba, tana jin tamkar sun tafi da wani sashe na jikinta.


*SATI BIYU*
Ranar da ta ga period 'dinta na uku, hankalin ta ba 'karamin tashi ya yi ba, damuwarta ta dawo sabuwa fil.

Cikin dare ta kasa barci ta rasa inda zata tsoma ranta, ga fanka na ka'dawa a sama, amma zufa ke damunta ji take tamkar ana hura mata wuta, tana zaune banda tunani iri iri ba abin da ta ke yi.

Tsawon lokaci tana zaune, kafin ta tashi da 'kyar ta fita zuwa ban'daki, dan watsa ruwa.

Ta fito, har za ta shiga 'daki idonta ya hango mata wayar Inna a cikin bahon kayan sana'ar ta, da mugun sauri ta juya ta 'dauko ta shige 'dakinta, dan Inna bata bari ta 'daukar mata waya.

Sai da ta kintsa kanta sosai gudun staining. Sannan ta 'dauko wayar ta shiga lalubo lambar Mk! Zuciyarta na bugawa da 'karfi, cikin sa'a kuwa bai kashe wayar ba, abin mamaki kuma bugun farko ya 'dauka, ta daburce ta rasa me za tace, sanin halinta da ya yi wadda masu azancin magana suka ce yafi sanin kama.
Yasa yace "me ya hana ki barci?"
Cikin rawar murya tace " Malam!" Sai kuma ta kasa magana kawai ta saka masa kuka sosai.

Kukanta da yake ji ya taimaka wurin sake jefa shi ru'danin da yake ciki, tun rana yake cikin fargaba da yaga kwanan wata a wayarsa. take ya tuno a irin wannan kwanan watan Sa'adah ke fara ala'adarta kenan tana gaf da fita daga matarsa, tun lokacin, ya rasa kwanciyar hankalinsa.

Ya tabbatar itama dalilin da yasa take kokawa kenan. Ya rasa me zai ce mata.

Tsawon lokaci suna haka, tana rera masa kuka, shi kuma yana ri'ke da wayar a kunnensa yana sauraronta, sai kuma ya ji 'kiran ya katse.

Ya duba sai ya ga ashe ita ta 'kira, wata'kila kudin wayar ne ya 'kare.

Bai yi jinkiri ba, ya bi bayanta, ta 'dauka ta na cigaba da kuka tamkar matar sabon mamaci.

A hankali ya ce "ki daina irin wannan kukan za fa ki ha'du da ciwon farat 'daya".

Cikin kukan sosai ta ce "ina fatan ciwon ya shige ni da 'karfi irin 'karfin guguwar iska, idan na yi sa'a ya dangana ni da kusheweta, wata'kila na huta da azabar da nake 'dan'dana da raina a cikin wannan duniyar".

Kuka sosai take yi, wadda ya matu'kar dukan zuciyarsa sosai.

Ya nisa ya ce "Zan tambaye ki, kinsan na san ki tamkar tafin hannu na, kar ki mini 'karya dan kuwa zan gane ki".

Ta tsagaita da kukan, kafin ta bashi amsa ya ce "wa ya baki waya da agogo da kayayyaki a Jawad?".

Zuciyarta ta buga ta 'barke da kuka tana cewa "Dan Allah ka fahimce ni, ba fa yadda ka ke zato bane".

Ya busar da iskar 'bacin rai ya ce " ok to fahimtar da Ni! ina sauraron ki, warware mini".

Da rawar murya ta ce "Tsakani na da Allah! Saurayin Safina ya siyo mata, ita kuma already tana da ita, shine ta bani, akan na bata rabin ku'din ".

Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ina jin ki! A ina kika samo ku'din?"

"Zobena 'daya na gold na bata, a hankali kuma zan cika mata sauran ku'din da suka rage tunda ba yawa".

Ya yi shiru yana nazarin anya Sa'a za ta shiryu, yanzun nan ta tsara labari tamkar a wasan kwaikwayo ko a littafi?

A kausashe ya ce "kuma ya aka yi naga ba sunanta bane akan rasit din siyan wayar?".

"Malam! baka lura bane domin kuwa SB aka saka ma'ana Safina Bunkure".

"Hmmmm" ya furta kawai ya yi shiru.

"Gaskiya na fa'da maka Malam".

Yace " idan kina ganin na gamsu ba Sa'adatu Bashir ake nufi ba. to ki fa'da mini, ta ina kika mallaki agogo mai daraja haka tunda English gold ne".

Duka na Safina ne, kayan da ka gani kuma siyawa Jawad ta yi tunda Alheri ta samu ba ka'dan ba".


Ya ce "alheri irin na 'yantattun Mata?"
Jikinta ya hau ' bari ita kam tam ta shige su, kalma 'daya tak da ta fa'da ta wanke ta a zuciyar Mk! ta janyo Mata tashin hankali mai yawa, ta yi amanna har da wannan kalamin suka 'kara fusata shi, ya yi irin fushin da bata ta'ba hararowa zai yi ba, hakanan kalaman sun janyo ya kasa gasgata ta. A daren ta gane tuntu'ben harshe yafi zafi fiye da wadda za'a yi da 'kafa ta fashe.

Jin ta yi shiru ya ce "Sa'adatu har yanzu ba ki shirya fa'da mini gaskiyar magana ba, bare na auna naga zan iya miki afuwa ko bazan iya yafe miki ba! Abin da nake son ki fahimta shine, ki daina yaudarar kanki cewar wannan laifin zai wanku a gurina da kwaskwarimar 'karya. matu'kar kin san ba zaki fa'da mini gaskiyar lamari ba to ki daina tunanin maganar zata bi ruwa da sau'ki."

"Gaskiya na fa'da maka Malam! ka zafafa ne, ya kamata ace kasan abin da zan iya da wadda ba zan iya ba! ko ban tsira da komai ba, ka gaskata ni mana".

"Ki mini adalci! wacce maganar zan 'dauka na gasgata ki akanta, alhalin tunda abin nan ya faru, kike ta canja magana, kin ce Sumayya ta baki, kin ce ta Halimace, kin ce ta Safinace shin wacce zan 'dauka na gasgata ki akanta?".

Shiru ya ratsa amma zukatansu sai bugawa suke yi tamkar ana lugude, ya nisa ya ce "ki kwantar da hankalin ki, duk sadda kika yi nufin fa'da mini gaskiya, Ni kuma na miki al'kawarin zan saurare ki, nasan kuma zan sami nutsuwa a zuciyata tunda gaskiya a bayyane take bata bu'katar ado".

"Malam na kusa kammala iddah fa, dan Allah " sai ta fashe da kuka fiye da na farko.

Yace "Na sani! yau kika fara period 'din ki na uku, me kike jin tsoro?"

Ta kasa yin magana, ya ce "Ni ya kamata na yi fargaba, Ni ya kamata na koka, domin zan rasa damata, sai dai na shiga sahun zawarawa, ke kuwa ai baki da damuwa idan har kina sona ai za'bin a hannun ki aka dam'ka shi".

Cikin kukan ta ce "Ban son muje ga haka, Ni ka zo ka dauke ni mu koma gidan mu, na yarda kar ka ci abinci na, kar ka kula ni har sai ka gamsu kamin abin da ka huce".

Ya ce "matu'kar muna tare kin san ba zan iya wannan jarumtar ba".

Ya sassauta ya ce "ki dinga addu'a sannan ki bar komai a hannun Ubangiji. Abin da nake so ki fahimta, wallahi na fiki shiga damuwa da tasku, kawai ni jarumta na fiki saboda kasancewata Namiji! Sannan ba zan ta'ba sauya hukuncin da na yi mana ba, har sai kin fa'da mini gaskiya koda hakan na nufin rushewar farin-ciki na gaba'daya, duk lokacin da kika shirya fa'da mini gaskiyar magana, ki mini magana".
Da haka ya kashe wayar gaba'daya.

Ta yi sororo da waya a kunnen ta, tana kallon agogo da ya nuna uku da rabi da minti biyu.
'
Har aka fara 'kiraye 'kirayen sallah barci bai iya surarta ba, tana ta tufka da warwara, ta yaya zata iya fa'da masa Khalil ne ya bata wadannan kayan? To akan wanne dalilin zai mata kyautar su ta karba? zuciyarta ta shiga harbawa, bare da ta tuno waccan kato'barar maganar da ta yi.

Ta yi amanna har da wancan laifin ya sake girmama wannan laifin a zuciyar Mk, sai ta yi kamar ta fa'da masa gaskiya sai ta tsorata, a yadda tasan ya tsani Khalil zai iya 'kararsa ko dan ya ci mutuncin gidansu tunda mahaifin Khalil fittacen 'dan siyasa ne, ita kuma ta hadu da zubewar mutunci a idon dangi dama duniya gaba'daya tunda tasan suna chatting da shi, ha'kika Sa'a na cikin hali irin na canka ca kare.

A fili ta dinga fa'din "Allah na tuba! na cuci kaina, son zuciya ya janyo mini 'bacin rai da damalmalewar lamura! Na keta alfarmar shari'a shiyasa na ke 'dan'danar 'bacin rai mai azabtarwa".

Tamkar mahaukaciya take surutai, tana sake cewa "Na yi al'kawari idan har na koma 'dakina bazan sake yin wani abu na rashin gaskiya ta kowacce fuska ba, sai da nace wa su Halima ina jin tsoron abin da zai biyo baya ta mini ingiza mai kantu, na biyewa 'kawar zuciyata na gasgata su, waiyo waiyo! Lah ilah ha illah anta subhanaka inni kuntu minan zalimin".

Duk akan kunnen Inna take wannan koke koken, da suratai duk da bata fahimci me take fa'da ba, da farko tsorata ta yi, ta 'dauka gwaiguna ne, sai daga baya ta fahimci daga 'dakin Iyah ne, a hankali ta fito, kasancewar Baffah yana Gogel.
Har ta isa bakin 'kofar dakin, sai kuma ta fasa, ta juya a zuciyar ta kuma tausayin'diyarta ya fara kamata, ta dinga mata addu'ar samun sassauci a zuciya.

Haka kwanaki suke ta shudewa, fargabar Sa'a na sake girmama, ba ta sake tuntunbar Mk ba, sai ana gobe za ta kammala iddarta, duk yadda ta kada billenta ta dinga ro'kon kar ya bari ta fita a matarsa bai ji ba, ya nan akan bakansa sai ta fadi gaskiyar lamari.

Washagari ta tashi da zazzabi ga kuka ya ki yanke mata. Inna ta kasa jurewa yanayin da ta ganta a ciki, har 'dakinta ta shiga ta zauna kusa da ita, ta ta'ba jikinta.
Zafi zau ta ji, ruwa ta samo da tawul ta dinga goge mata jiki. ta taimaka mata ta canja Riga, ta zubo mata kunu a kofi ta matsa mata ta shanye, sai dai tana gama shan ta amayar da shi tas.

Haka Inna ta sake gyara mata jiki, da kuma wurin, tana fatan inama ace ciki ne da ita wata'kila hakan yasa mijinta ya mayar da ita.

Baffah da bai fita ba, shi ya nemo Usaini mai chemist ya duba ta, ya kawo mata magungunan da zata Sha.

Tafi kwana uku tana mukurkususu, kafin ta fara warewa, saboda yanzu Inna ta sassauta mata, damuwar ta dan yi sauki.

Sati biyu da kammala Iddarta, tana tsakar gida tana wankin kayansu dana Inna sai ganin Jawad suka yi ya shigo a guje kamar yadda ya Saba.

Kai tsaye ya nufi uwarsa ya rungume ta, ita kuma idon Inna ya hana ta rungume shi, sai ta bige da fa'din wa ya kawo ka?

Yana jikinta yace " Malam ne, kullum sai na yi kukan gurin ki zan zo shine yau Hajiyar Bichi tace sai ya kawo ni, tunda jiya anyi hutun boko".

Inna da ta ke zaune tana fere doya tace "wato Jawad ba ka ganni ba ko, Anya kuwa za ka yi al'kawari?"

Kafin ya yi magana sallamar Hajiyar Bichi ta cika kunnuwansu tare suka shigo da Baffa, Inna ta mike da azama tana fa'din lale da Hajiyar Jawad, ashe tare ku ke tafe?"

Falo suka shiga! Inna ta gabatar mata da ruwa ta zauna Don gaisawa, sai taga Hajiyan na share hawaye Baffa na cewa "to ya za'a yi, sai ha'kuri, komai rubutacce ne, idan rabo bai 'kare ba za su koma, idan kuma ya 'kare sai duk mu yi ha'kuri, mu bisu da addu'ar fatan alheri! fatana dai ki cire damuwa a ranki.
Wallahi bamu 'kullace ku ba, Ni ko Mutari har yau ban ga laifinsa ba, Allah shine shaidata, kawai dai zan so ace sun shirya kansu ko dan rayuwar 'dansu ta inganta".

Murya a dakushe Hajiyar ta ce " Nima abin da nake ta hango musu kenan ban da dole yaushe za'a raba yaro da uwarsa! kome za'a masa ba zai gamsu ba idan ba uwarsa yake gani ba. Haka nan ba kowacce mace bace zata ri'ke'dan da ba nata cikin adalci da kyautatawa ba, akwai su amma sun yi 'karanci 'kwarai da gaske".

"Allah ya musu za'bi mafi alheri" Baffa ya fa'da yana barin falon.
Hajiya da Innah suka ha'da baki wurin cewa

Please Login or Register in order to submit comment