You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tafi, Jawad na kukan zai bishi.

A tunanin ta kwana daya zai yi ko biyu, amma sai da ya shafe kwanaki biyar ba shi ba alamun sa, a kwana na shida ne, idonta ya fara raina fata, mussaman da ta tabbatar da Mahmoud suka yi tafiyar, Amma shi ya dawo kwana biyu kawai ya yi.

Kuka ta dinga yi, tamkar shine mafita, ga rashin waya dake addabar ta, ga rashin sa.

Sai da yayi sati guda ya dawo, kallo daya ya mata yasan ta ji jiki, sakonsa ya daketa sosai, amma saboda Halinta na taurin rai, ko kallo bai isheta ba.

Washagari da ya fita, sai da ya kai 11pm kafin ya dawo, domin ya jarrabata ya gani. A bangaren ta tana son rufe masa gida amma ta kasa, kwanakin da ya yi baya gida, sune mafi tsauri a dukkan rayuwar ta, tunda suka yi aure bai ta'ba yin tafiyar da ya kwana ba tare da ita ba. tasan rufe masa gidan da ta yi ne, yasa yayi tafiya mai tsayi ba tare da ita ba, ba magana mai dadi, ko na zai yi missing dinta.

Ya dawo ya tarar da gida a bude, ya yi murmushi, yauma 'dakinsa ya zarce, wannan abin ya dameta, amma bata ji zata bashi ha'kuri ba, tunda ai ita ya zalunta.

Washagari yana shirin fita, ta fito ta tsaya a tsakar gida, sai da ya fito sannan tace " Ina son zanje gida".

Ba tare da ya kalleta ba, yace " Ba za ki je ba".

Ya sa kai zai fita, taja tsakin da yasa shi juyowa da sauri, kafin yayi magana tace "dama idan mutum na cin amanar matarsa, sai ya yi ta boyeta a cikin gida, mai za'a yi da auren likitan mata, da mai koyarwa a Jami'a, aiki ne na yan iskan maza, masu juyawa matansu baya idan sun sami biyan bu'katar su"

Ya zuba mata ido yana jin wani iri Abu mai kama da tsanar ta na son yiwa zuciyar sa dirar mikiya.

Ya nuna kansa da yatsansa, yace "Ni ki ka zaga?"

Idonsa ya kada ya yi jawur, ya rasa inda zaisa ransa ya sami sau'kin zafin da zuciyar sa ke yi.

Ya girgiza kai yace " Na gode, amma U will pay for it Sa'adatu".ya juya ya fice da sauri.

Ganin yanayinsa yasa ta jin nadama na dan shigarta mussaman yadda ya nuna kansa yana tambayar shi ta zaga? tasan bai taba zaton zata iya zaginsa ba, ita kuma ba'kin cikinsa ne yake neman kashe ta a tsaye, sannan ma a ina ta zage shi?

Fishi ya dauka sosai, sun kai sati a haka, abin ya fara fin 'karfin ta, rama take yi a tsaye, ko uffan baya cemata, Idan yana gida Jawad na manne da shi yana bashi labarin yaci abu kaza da iri kaza, ko yace su Anty Safina sun kawo masa abu kaza.

Hankalin ta bai tashi sosai ba, sai da yayi shopping, taga iya abin da ya zama dole ya siyo, wadda ya saba siya na kyautatawa duk bai siyo ba, duk wani tarkacen kayan kwa'dayi babu a siyayyar nan, hatta kayan miya da yake zuwa janguza ya lodo musu, wannan karan ko guda daya bai siyo ba.

Sannan a drower yake ajiye kudinsa baya mata iyaka, ya zara , ta zara, har su 'kare a haka, a wannan lokacin sai ya zauna ya yi 'kiyasin 200 zai isheta kullum da sunan kudin cefane, dan haka sai ya adana kudinsa yake bata wannan darin biyun, Jawad yake bawa ya kai mata.

A wannan lokacin da ya rikice mata, ya canja sosai, sai ta gane ashe dai da kirkinsa har yawa ya yi.

Ta fara neman hanyan sulhu, amma ta rasa yadda zata yi, yaki ya bata dama ko kadan, ko ta kai masa abinci baya ta'bawa haka take daukan abinta, ta fara daukan wanka da kwalliya, shikuma sai yake runtse idanuwansa daga kallonta.

Ta rasa mai kuma zata yi, sai ta dawo da gyara masa dakinsa, kullum idan ya fita, zata shiga ta gyara, gyara na mussaman, ranar da ta fara, da ya dawo ya gani, a ransa yace zaki san ba ke ka'dai kika iya neman masifa da tashin hankali ba.

Ganin ta debi kwanaki tana bin hanyoyin neman sulhu, amma ya yi biris da ita, sai ta canja salo.

Rannan da daddare ya dawo, ta kai masa abinci da tea din da ya zame masa ka'idar sha duk dare, tana ajiyewa yace " fita da su na gode".

Ta yi shiru tana kallon sa shikuma yana zaune, yana nazari a waya, amma yana jin kallon ta a jikinsa.

"Dan Allah Malam ka sha shayin nan na roke'ka".

Ya girgiza kai yace "Na koshi ne, ki ajiye zan sha da safe".
Da murna tace "Na gode".

Ta mayar kicin ta adana abincin a fridge, a gurguje ta yi wanka, ta bi dukkan jikinta ta shafa Arabians perfume masu kamshi sosai.

Ta dauko rigar barci ruwan madara, mai santsi ce kuma very transparent, ta gyara gashin kanta ta shafe shi da man gashi na Kuza. ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, tabbas ko ita ta burge kanta, ta tsinci bakinta da yin tasbihi da godiya gurin ubangiji,hakika an kyautata halittar ta.

Har taje falo kuma sai ta dawo, tana bin cinyoyinta da kallo, iyakacin Rigar rabin cinyarta ne, ko kusa da guiwata bata zo ba, bugu da kari, bata sa komai a kasan rigar ba.

Shaidan da zuciya suka fara wasan kura da hankalinta, suna kitsa mata idan taje a haka, ta yarda itace mai laifi, bayan duk irin yadda ya nuna mata ita da babu basu da maraba.

Ta tuna yadda ya shafe sama da sati biyu bai nemeta ba, shaidan ya sake tunzuro ta, yana jaddada mata irin zalamarsa akanta, idan ba wata ya samu a waje ba, yaushe zai iya jure tsawon kwanaki bai rabeta ba, tabbas mata yake bi na banza.
''
Ta koma ta kwanta a gadonta, tana Jin hawaye na bin fuskarta.

Sai juyi take yi, tana kallon yadda Jawad yake barcinsa cikin nutsuwa, tana jin inama itace shi, da bashi da wata matsala a duniyar sa, indai zai ci abinci, a masa wanka, a bashi sweet shikenan baisan komai na bacin Rai ba.

Ta kasa barci ta zabura ta sauko daga gadon, tana jin dolensa ya fada mata mai yake nufi da ita, ya kuntata mata, ya kuma fita fishi🤔

Ta kunna fitilar dakin, ta fice ba tare da ta kashe ba, saboda Jawad .

A zaune ta same shi, yana marking din exams din 'dalibai.
Ya amsa sallamarta, hankalinsa na kan takardar da ke gabansa.
Ganin bai 'dago ba, yasa tace "Ina son magana da kai".

Yana cigaba da marking yace "Amma dai kinga aikin da ke gabana ko? Sai ki jira na kammala, ko ki tari lokacina na gaba".

Hawaye ta ji na neman kwace mata, da ta tuna kafin su fara takun saka, baya iya yin aiki sosai matu'kar suna tare, ya fi kauri wurin tsokanarta, ta hanyar dumbulan kirjinta, ko ya biyeta su yi ta shiririta, tana bashi labarin ai tana yawan mafarki ta zama Hajiya, ta zama big madam, shikuma ya yi kudi, ya zama Alhaji, ya gina musu katon mansion.
sai yace Ina fatan dai ba kiga na 'kara aure ba? Wani lokacin tace bata gani ba cikin da'din Rai, wani lokacin tace abin da yake ransa ne, sai ta hau bori, shikuma ya lalace wurin rarrashin ta, a haka har su cinye lokaci mai yawa basu farga ba.

Amma a yau, gata a gabansa yana nuna mata bashi da lokacin saurarenta, aikin da yake yi ya fita muhimmanci kenan?.

Da gaske ita da Babu 'daya ne a gurinsa? sai kawai ta fashe masa da kuka irin wadda ta tabbatar yana gigita shi.








Surayya Dahiru
✍️✍️.
30/03.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*Surayya Dahiru*.

Lafazee writers.


*Doka mai lamba ta 68 ta nina cewa satar fasaha babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*.

*A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.



*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*




67-70.



Ya yi shiru yana jin kukan da take masa, yana ayyana rashin mutuncin ta kullum kara gaba yake yi. ransa ya baci iyaka, mussaman yadda ta ware murya tana masa kuka tamkar wadda ya ke mata dukan kawo wu'ka.

Ya kasa cewa komai, domin zuciyarsa sai fada masa take, ya daketa kawai, ko ya huce kadan cikin takaicin da take guma masa, itama kuma sai ta yi kukan mai dalili.
Tsawon lokaci tana kukanta, jikinta ya yi sanyi tubus, a dalilin halin ko in kula daya ya mata, da gaske dai Malam ya gaji da ita, hakan ya sake sa ta fashe da sabon kuka fiye da wadda take yi.

A harzuke ya nuna ta da yatsa yana cewa " tashi ki koma dakin ki, kici gaba da kukan a can. Idan kuma ba ki gama min tuya a gurin makwabta ba, sai ki kara himma har su shigo su ceceki."

Jin hakan yasa ta rage sautin kukanta, shikuma ya cigaba da aikinsa amma bashi da sukuni ko kadan, ya kuma yi al'kawarin ba zai ce ta daina kukan da take yi ba.

Aikuwa kusan raba dare ta yi, tana masa gunjin kukan da babu shagwaba, sai zallar bacin rai, irin kukan da me yinsa yake son a rarrashe shi, lura da hakan da yayi shikuma ya yi biris da ita, dan kuwa bai ga dalilin kukanta ba, shi ta musganawa, ta masa rashin kunya, bata bashi hakuri ba, shine take sa ran shi ya risina mata, lokaci ya yi da zai daina biyewa son zuciyar sa akan lamarin ta.
A inda take zaune barci ya sureta, sai sakin ajiyar take yi.

Sai da ya gama aikinsa, ya kammala komai, ya dauko Jawad ya kwantar da shi, ya dauko bargo ya lulluba mata, sannan ya kashe fitila ya kwanta bayan ya rungumo Jawad a jikinsa.

Da asuba ta tashi ta ganta lullube da bargo, ta ji dadi, sai dai rashin tashinta ta yi sallah ya dakushe waccan jin dadin, ta kalleshi har ya dawo daga masallaci, ta zuba masa idon da ya kumbura saboda kuka, murya a dashe tace "Malam abin har ya gagareka tashina na yi sallah?"

Ya yi mata shiru tamkar ba da shi take yi ba.

Takaicinsa ya sake kumeta, tace "Ma'aiki dai yace Allah ya jikan mijin da ya tashi cikin dare ya kuma tashi iyalinsa suka yi sallar nafila, to ina kuma ga wadda ya tashi, ya kuma tashi iyalinsa dan sallar Farillah? ka rasa wannan ladan, ba nice da asara ba".

Ya zuba mata ido yana kallon ta, Yana jin sabon tashin hankali na shigarsa, tabbas ta kerewa tunaninsa, an mata famfo fiye da duk yadda yake zato.

Haka ta gama sakin magaganu sannan ta fita zuwa dakinta, don yin sallah.

Kan Mk ya kulle, ya rasa mai zai mata, ya yi fushin, ya bagarar da ita, Amma duk a banza, wai ya zai mata ne? kawai sai ya tsinci kansa da daga hannunsa sama yana cewa "Allah kasan irin son da nake yiwa Sa'adah, Allah ka shirya min ita, ka bude kirjinta ta gane gaskiya, ta fahimci bani da nufin zaluntarta, ka zaunar da mu lafiya, Allah ka kara min ha'kurin zama da ita cikin adalci".

Ya kishingida yana tunano kafin shigowar su Halima cikin rayuwar aurensu, ko ya ya taga ya canja mata, ta dinga tambayar me ya same shi, ko itace ta masa laifi? Ta dinga bashi hakuri kenan, ko yace bata masa komai ba, kawai yanayi ne, ko baya jin dadi ne, duk da haka hankalin ta baya kwanciya sai ya dawo da walwalarsa, amma a yanzu kusan sati uku suna dauki ba dadi, amma kullum da abin da zata yi da zai sake bakanta masa Rai, karon farko da ya fara zargin Anya kuwa dama Sa'adah da gaske tana sonsa?

Ya dinga hasaso yadda yake gudun zuciyarta, har wasu da yawa suna ganin tsoronta yake ji, alhalin ba haka bane, kawai tsananin sonta da yake yi ne, yasa baya shiri da duk abin da zaisa ta koka, mussaman na rashin wani abu, zai ha'kura da dukkan bukatun kansa, matu'kar ita zata wadatu. Amma duk su Safina sun lalata mata tunani, sun jefa mata shubuha, wai yan mata ne da shi na banza! Tabbas suna neman raba shi da ita ne.

A fili ya furta " Allah kana ganin masu son shiga tsakanin aure, Allah ka min maganinsu".

Sai da ya isa makaranta! Ya na cikin motarsa ya ciro wayarsa, ya lalubo lambar Anty Sumayya, cike da girmamawa ya gaisheta, sai kuma ya yi shiru ya na jin nauyin zartar da kudiransa. Jin yanayinsa yasa ta tambayarsa ko akwai matsala ne?

Cikin jin nauyi ainun yace " So nake ki yiwa Sa'adah magana, mun dade cikin rashin nutsuwa, na yi iyakacin kokarina dan mu fahimci juna abin yaci tura, bana son na tayarwa da su Baffah hankali".

Hakuri Sumayya ta dinga bashi, tare da al'kawarin yanzun nan zata kirata.

Kai tsaye yace "ba waya a hannun ta".

Jikin Sumayya ya sake mutuwa, shiyasa kwana da kwanaki tana gwada layin Iyah baya shiga, ta damu kwarai da rashin jinta, sai da Inna tace mata, lafiya ce take buya, Ni kaina an kwana biyu bamu gaisa ba, da kuma wata matsalar ce ai da mun ji, tunda mijinta kusan kullum sai yazo unguwar, kowacce juma'ah kuma zai shigo ya gaishe ni, ya bar Jawad sai zai tafi ya zo ya dauke shi, na fahimci Iyah! indai naji ta shiru haka, to cikine da ita.


"Yanzu kana gida ne?"

Ya girgiza kansa tamkar tana ganinsa "Ina makaranta, sai da yamma zan koma".

Ai kuwa da yamma yan isa gida ba jimawa, Kiran Sumayya ya fado wayarsa, bai dauka ba, ya bawa Jawad wayar tare da cewa" sauri ka kai mata, Maman Gombe ce" dake tuni sun bar Jos tun shekaru biyu da suka wuce.

Da gudu kuwa Jawad ya fita sai dai kafin ya isa inda take ya danna ok, ya fara yiwa Sumayya surutu, ita kuma ta biye shi, duk da ba komai take fahimta a hirar tasa ba.

Fada sosai Sumayya ta yiwa Sa'adah, ta yi shiru tamkar tana jinta, sai da ta gama ta saka mata kuka tana fadin
"Yana zaune da yan'uwansa kalau, amma ni yana ba'kin ciki da hadin kan dake tsakanina da ke, Ina zaune da shi ne kawai, amma ba irin wulakancin da baya mini, ya fifita farin cikin yan matansa akaina, ya koyo wata dabiar da ba tasa ba, ko kukan jini zai ga inayi ba ruwansa, shine har ya kawo karata?".

Mamaki ya kama Sumayya tace "Ni kike fadawa wadannan maganganun? Eh na tabbatar Mijinki ba karamin ha'kuri yake da kaifin harshen ki ba, amma ki saurare ni da kyau, wlh idan baki canja ba, za ki jefa kanki a nadama mai yawa, wato ke har yanzu baza ki yi hankali ba? Kowacce mace da akwai inda take ha'kuri, ance miki auren wasa ne, ke naki ma wallahi ba matsala bace, kawai dorawa kanki kika yi, Ina ruwan ki da yanmatansa, ko aure yace zai kara Ina ruwan ki? Tun zuwan ku Jos na lura sai kin koya masa bagarar da lamarin ki".

"Dan ke mijinki ba mai hayaniya bane, ba mai kule kulen mata bane shiyasa kike ganin bani da matsala" Sa'adah ta fada a tunzure.

Cikin bacin rai sosai Sumayya ta ce "shikenan ki yi duk abin da kike so, ya dauka ina da wata kima a wurin ki! shiyasa yake ganin zan iya muku sulhu basai iyayen mu ba, amma tunda ban isa ba shikenan! Rayuwarki ce, kina da ikon yin duk yadda kika so, sai dai ki sani wadda bai ji bari ba, ba zai ki ganin hoho ba". daga haka ta kashe wayar ta, ta bar Sa'adah ri'ke da waya tana kunshekin kuka.

Jikinta ya yi sanyi, tana Jin Aunty Sumayya uwace ta wuce ta yi misayar yawu da ita! Dan haka sai ta sake kira, Sumayya ta daga tana cewa "menene?" Cikin kuka Sa'adah tace
"Na ji! kiyi ha'kuri".

Sumayya da bata da zafi, tace "yauwa Iyata, ni nasan indai a cikin Innarmu kika fito ba zaki 'ki jin abin da na fa'da miki ba, saboda kinsan nan duniya bani da kamar ki, mu kenan iyayen mu suka haifa, ki daina duk abubuwan da mijinki baya so, ki kara hakuri, idan ma ke yake zalunta ki yafe masa, ki yawaita addu'a sai kiga Ubangiji ya warware miki komai, fiye da yadda kike zato! Yanzu abin da nake so da ke, ki bashi ha'kuri, kar kuma a sake tada maganar koma wacce iri ce".

Sai da Sa'adah ta ja majina murya na rawa tace "Anty shine fa yake fishi da ni, yake ta share ni, ba abin da banyi dan mu shirya ba, ya ki bani fuska, kuma sai ya kawo karata?"

Cikin rarrashi Sumayya ta ce "bafa kararki ya kawo mini ba, nasan dai kuna zaune kalau ba zai barki ba waya ba, nice dai na tambaye shi Kuna lafiya kuwa, yace na miki magana baya son ya shigo da Baffa cikin matsalar, iya haka ya fada min wallahi".

"To Anti na ji fa'danki, amma shima ki fa'da masa idan ina kuka, ya daina cemin na dame shi da kukan banza, ko na iyashege, ya bar komai ya rarrashe ni".

Sumayya ta 'kunshe dariyarta tace "Zan fada masa, amma ki bashi ha'kuri first, nasan kafin ki yi tuba sai tura ta kai bango, kullum ina fada miki hakan sifface ta girman kai.

"Anty sanin da, kika mini, wlh na bashi hakuri, ta hanyoyi da dama, ai ba sai na fada da baki ba, shi da kansa yasan na bashi hakuri, kawai dai ya runtse idanuwansa ne".

"To yanzu ki fada da bakin ki yasan Ina da mutunci a gurinki, idan na fada miki zaki ji! Idan kuma kin ki, shikenan, kin wula'kanta Ni, kin wula'kanta kanki".

Da haka Sumayya ta risinar da Sa'adah, sun dade suna magana har sai da kudin wayoyin ya kare tas, sannan suka ha'kura.

Da kanta ta kai masa wayar, duk da Jawad na cewa ta bashi ya kaiwa Malam! ta bashi wayar ta zauna gefen gadon Sannan tace " Malam ka yi hakuri dan Allah".

Idonsa a rufe, bai bude su ba yace "Ni dama barcin da kike hanani yi da daddare ne, bana so, hakuri na zai iya :kwacewa, idan zaki yi kukan ki ban hana ki ba, amma pls stay away from me, na riga na gane ban da mutunci ko ka'dan a gurinki, zaki iya zagina kan ki tsaye, zaki iya fada min duk maganar da ta zo bakin ki, na zuba miki ido ki yi duk abin da kika ga dama, amma ki jira sakamakon zagin da kika min, na rantse miki! ba zai tafi a banza ba".
Ya karasa da rawar murya saboda 'bacin rai.

Hankali Sa'adah ya yi mugun tashi, mussaman yadda ya yi maganar da dukkan zuciyarsa, ta zuba masa ido tana ganin yadda yake numfarfashi tamkar wadda ya yi gudun fanfalaki, dan tsananin bacin rai.

Ta zame ta durkusa a jikin gadon ta ru'ko hannunsa "ka yi hakuri, ba zan sake ba".

Ya bude ido da suka yi jah yace "wallahi za ki sake, ba dai kin bada kofar da wasu suka shigo cikin rayuwar aurenmu ba? ba kin fi gaskata maganganunsu, sama da nawa ba, nace ban son su zo min gida, kin nuna ban isa ba, saboda kina jin isar gidan na ki ne, na sha jan kunnen ki akan kaifin harshen ki, amma kullum sake koyon dabarun ba'kaken magana kike yi, ki rubuta ki ajiye wañnan *HALIN YAU* din da suke cusa miki, kina dauka babu nazari bare tsinkaye, ba inda zai kai ki sai nadama, na fara gajiya da halin ki, hakuri na ya fara kaiwa geji gaskiya, Menene bana miki da kike wulakanta ni haka?"

Jikin Sa'adah ya yi wani irin nauyi, zufa sai karyo mata take yi ta ko Ina, ta kasa bude baki ta yi magana, dan hatta harshen ya mata nauyi ainun, hawaye kuma tamkar an bude famfo, Jawad da yake tsaye yana kallon su, ya karaso ya fara goge mata hawayen, Yana cewa "biskit za ki ci? ko Malam ne ya doke ki?"

Ta kasa magana kamar yadda hawayen ya ki yankewa,ya zuba musu ido yana ganin yadda Jawad ke goge mata hawayen,yana kuma fa'din ta yi shiru, zai goyeta a kekensa, wani irin abu mai kama da tausayi ya tsirga masa yana ayyana karfin soyayyar da ke tsakanin uwa da 'da.

Murya a dashe Mk yace "ki ci gaba da kukan, so kike ya 'kullace ni, ya zaci kamar Ina gallaza miki ne, idan girma ya cimmmani ya'ki jin 'kaina"

Da sauri ta dago manyan idanuwanta ta zuba masa, a fili akan idonsa tace " Malam plz ba kai bane, ka dawo wancan Malamin nawa! mai yawan yi min afuwa, mai tausasa mini".

Ya mayar da idonsa ya rufe yace "shikenan ya wuce, dauki "danki ku tafi gurinki barci zan yi".

"Ka yafe mini?"

"Nace ya wuce" ya fada a gajarce.
Taja hannun Jawad! amma yaron ya coge alamun ba zai bita ba, ta tsaya tana kallon sa ya hau gadon ya kwanta jikin Babansa, Mk ya rungume shi yana ji a ransa shima fa Jawad na sonsa sosai😀Mk manya.

Kwana biyu, Sa'adah ta sauko, tana komai yadda ya kamata, ta bangaren Mk shima yana iyakar kokarinsa na bai sake yin wata maganar ba, zai ci abincinta, idan ta masa magana, yana amsawa kadaran kadahan, kawai a shimfida ne ba ya kulata, ta gama shure shurenta, ya yi biris, duk da shima fama yake da shan lemon tsami.

Tana zaune tana tunanin mai zata masa ya ta'ba ta, hawaye na siraro mata, saboda yadda abin ya dagula mata lissafi, mussaman yadda ta san shi da rashin ha'kuri a wannan harkar, idan ta hasaso ko a waje yake samu sai ta ji tamkar ta sume, ta sake ramewa ta yi zuruzuru, kamar ance kunna radio, aikuwa nan ta ji sanarwa a gobe litinin hukumar zartarwa ta kwalejin tarayya ta kano (F.C.E.) zata rufe yin registration.dan haka duk dalibin da bai yi ba ya hanzarta kafin a rufe.

Ta yi shiru, ta tabbatar Malam yasan ranar da aka bude dan farawa, dan kuwa yana da aboki da yake aiki a gurin, duk da ba lakcara bane.(Non academic staff)ne.wani sashi na zuciyar ta yace kika sani ko ya biya miki ne? Da haka ta samu sukuni kadan.

A ranar bai dawo da wuri ba, dan haka ta danne komai ta barshi ya gama komai cikin nutsuwa, sai da suka kwanta ta bijiro da maganar da ta ji a radio.

Tsawon lokaci ya mata shiru, zuciyarta ta sosu da wulakancin nan da ya tsira, ashe haka yake jin rashin dadi idan ya mata magana ta share? ta daure tace "kana tare da ni kuwa?".

"Ina jin ki, na sani, har na biya miki, yasa hannun ya ja drowar gefen gadon ya fiddo da teller ya nuna mata, farin ciki ya mamayeta, kafin ta yi magana sai taji yana maganar da ta kasa gane manufarsa.

"Na gama miki komai illah wurin da yake bu'katar signed dinki!amma a yanzu na fasa, matu'kar da aurena akan ki! wallahi ba za kije makarantar nan ba".

Cikin rudu tace "Ban gane ba fa?"
Ya tashi ya kunna fitila, sannan ya zauna! ya zuba mata ido yace
"Ina nufin idan har sai da yardata zaki yi karatu, to baza kiyi ba, idan kuma ya zama dole sai kin yi, sai dai kije a matsayin single amma ba matata ba".

Hawaye ya balle mata, ta ru'ko hannuwansa cikin rawar murya tace
"Na roke ka kar min haka! dan Allah kar bari na gasgata masu fadin ba zaka taba barina na yi ilimi ba".

Ido cikin ido yace "gara ki gasgata su Sa'adatu, ada kam na kudiri aniyar ilimi sai kince ya isheki! amma Billahillazi yanzu na fasa, ba ki fara karatun ba, kina iya zagina, bare kuma na baki damar da kullum sai kin fita, kin yi cudanya da mutane daban daban, tunda na gane kawaye zasu iya rinjayar ki, zasu iya canja miki dabi'a, zasu iya ruguza mana kyakkawan zaman mu, daga lokacin na gane barinki karatu mai zurfi ha'dari ne, ilimin sakandiren da kika samu, yasa kina jin kina

Please Login or Register in order to submit comment