You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ba?".

Halima da tafi Safina ginshira ta ce " Akan mai zamu neme ki, inace kin dauke mu kin watsar a shara, shiyasa muma muka manta da ke, kin ri'ke miji kin manta da kowa! zuwan ma yanzu da muka yi ba naki bane, na 'Dan mu ne ko kin fada mana kin haihu?"

Dariya sosai Sa'adah ta yi, tana fadin "shikenan yana godiya"
tare da cire nono a bakin sa, a kafada ta saba shi, sai da ya yi gyatsa sannan ta nade shi a shawul da ke canja masa riga aka yi, ta mi'ka ma Safina da tafi makwaftaka da ita.

Ido ta zuba tana yaba kyaun jaririn, ta ke ta ji sha'awar ta samu nata, ta jima tana ri'ke da shi, har sai da Halima tace " Ba za ki bani na ganshi bane?"

Sannan ta mi'ka mata tana fadin "Babyn ne so mashallah". Halima na zuba ido akansa taga kamannin Uncle Mukhtar sak a fuskar yaron.

A fili ta furta "Allah dai yasa kar ka kwaso mana halinsa".

Da sauri Sa'adah tace "Uncle din kike cewa kar ayi halinsa? ai kuwa zan fada masa".
Ta no'ke kafada, alamun ko ya ji Ina ruwanta.

Har kusan maghrib sannan suka tafi, suka ajiye mata leda mai dauke da rigunan yaro masu tsada guda uku da Pampers mai 48, ta musu godiya. Zainab tana daga falo tace ku gaida gida! da kyar ta basu ledar da ta ke rabawa mai dauke da sunan jaririn!cikin kuma memo ne mai hoton Jawad.

Kwana uku da suna dan kishiyar Umma ya rasu, daga ciwon ciki kawai sai mutuwa, dole ta tafi, ta taya yar uwarta zama da juyayi! mutuwar matashi akwai gigitarwa.

Kwanaki biyu a jere Inna ke zuwa da safe ta mata wanka da sauran hidima, sai ta mata wankan yamma sannan ta tafi.

Ganin zirga zirgar zata mata yawa kullum, yasa ta roki Baffa ya bari Sa'adah ta zo gida ko sati biyu ne, ta kula ta ita, ita kadai tasan me ta gani, da dukkan alama daki daya suke kwana da mijin ta, tunda Umma ta bar gidan.

Bai tsananta ba, ya amince amma da sharadin idan mijinta bai amince ba, baza'a matsa masa ba.

Tace "Ni ai da iyayensa zan yi magana, idan ka bani dama a daren nan zanje gunsu".

Bai hana ba, itakuma bata yi sanya ba, tana idar da magariba ta tafi gidansu Mk, a falo duk ta same su har Hajiyan Bichi, bata bata lokaci gurin fayyace bu'katar ta ba.

Dukkansu sun yi shiru!sai Hajiya Babba ce ta yi kundunbalar cewa "tunda har kika zo ba za'a hanaki ba, sai dai ki yi hakuri da kaina zan kawo miki ita, idan aka shirya".

Godiya sosai Inna ta yi ,har kofar gida suka rakota suna ta yiwa juna godiya.

Har ta isa gida tana mamaki! ko kishiyoyi nawa ne suka dace da kyakkawan zama irin na iyayen Mk? ko
Ana samun adalar uwargida irin Hajiya Babba, mai hade kan ahalin gida babu banbanci, ko kai sukar wani ga wani, da sauran gutsiritsoma irin na tsofaffin mata masu kitsa munafunci da sunan kishi? Ko
Ana samun amare masu kawaici da biyayya da sanin mutunci da alherin uwayen gida irin Hajiyan Bichi? sha'awar zamansu ya kamata tana jin inama, itama tana da abokiyar zama, ba yabon kai ba, da zata yi koyi da Hajiya Babba.


Da murna ta bawa Baffa labarin yadda suka yi, shi da kansa sai ya zaku Iyah ta dawo kusa da shi duk da dai bai furta ba.

Suna komawa gida, Hajiya Babba ta Kira Mk a waya, ta sanar da shi bu'katar mahaifiyar Sa'adah! ya yi shiru ya rasa mai zaice, jin shirunsa ya tabbatar mata da bai ji dadin maganarta ba, bashi kuma da niyyan amincewa.

Dan haka sai ta kwantar da murya cikin hikima tace " Da na yi karambanin amincewa, har naci alwashin da kaina zan kai musu ita, amma ba zai zama komai ba, idan banyi daidai ba, sai na koma na lashe amai na".

Cikin takaici iri iri yace "Ni bance ba, tunda kin amsa shikenan! amma dai sati daya za ta yi".

"Akan mai zaka 'kayyadewa iyayen ta kwanakin da zata yi a gaban su, ba ka ga mutunci irin nasu ba? neman alfarma suka zo yi gaban iyayenka, saboda girmama hakkin aure. ba dan basa sonta, ko dan sun gaji da ita suka dauketa suka baka ba, yau kusan shekara guda. me zai sa ka shata musu layi dan su nemi su kula da lafiyar yarsu?"

Ya yi shiru yana jin maganar na shigarsa sosai, ya nisa yace "Shikenan Hajiya duk yadda kika yi dai-dai ne"

Dadi ya kamata! ta shiga jero masa addu'ar albarkar ubangiji a dukkan kasafin sa.

"Tunda ka yarda da hukuncin da nayi, duk da ba ka so! Ni kuma zan fada musu sati uku za ta yi maimakon wata guda".

Takaici ya sha'ke masa wuya, wai har sati uku, shi ya dauka anyi wuta ta yi sati biyu, to da fiye da wata ake nufi zata yi ko me?

Sa'adah na zaune a daki tana shayar da Jawad, shi yana falo yana musu guga, ya tattara kayan ya kulle ya kashe iron din saboda yadda jikinsa ya mutu da 'bacin rai.
'
Jiki a mace ya shiga 'dakin bai kalleta ba, ya wuce ya hau gado yana jin zazzabi na namen kama shi.

A gigice ta dinga tambayar sa lafiya kuwa, me ya same shi?

Jinsa shiru yasa ta shimfi'de Jawad! ta isa kusa da shi tana ta'ba jikinsa ta ji ko zazzabi ne yake san'darsa.

Ras ta ji jikinsa, sai rashin kuzari, ta shiga tambayar sa, ya kasa bu'de baki ya mata bayani, amma ganin zata masa kuka, ya fisgota jikinsa ya kankameta, yana sakin ajiyar zuciya.

Tsawon lokaci suna haka, cikin rashin kuzari yace "Tun yanzu na fara kewar ku"

Gabanta ya fadi ta kalleshi ido a bude "Tafiya zaka yi ka barmu?"

Sai kawai ta fara hawaye, ya kalleta yana jin sonta na sake daskarewa a zuciyarsa, shagwabarta, rauninta, soyayyarta na sake gigita shi.

Ya sake kankameta sosai yace " Kune dai za ku tafi ku barni, yanzun nan wayar da kika ji inayi!Hajiya Babba ce, wai na shirya miki tafiya gida, ki yi wankan acan".

Da'di ya cika 'kalbinta! ta ji tamkar ta tashi ta taka rawa, sai kuma ta ga yadda ya shiga damuwa akan tafiyar ta, idan har ta nuna murna! Tamkar ta baro bacin rai a tsakaninsu, dan haka sai ta hadiye dukkan murnar ta!
Ta tattaro dukkan damuwa ta yaba akan fuskarta da jikinta.

Cikin shagwabe fuska har da sake matso hawaye ta hau fadin
" Ni dai ba zan je ba, ai kaima kana kula da mu sosai".

Idan yace bai ji dadin kalamin ta ba yayi karya, ya shiga kissing dinta ba kakkautawa, ganin zai wuce iyaka, yasa ta katse shi, ta lura ya manta da halin da ta ke ciki na rashin tsarki.

Idonsa sunyi ja, sun kankance saboda fitina, ya zuba mata su,ya ce "Hajiya Babba da Innah ne suka zartar da hukuncin nan, hakuri zamu yi, mu yi yadda suke so".

Wani irin farin ciki ya sake kamata, amma a iya zuciyarta ya tsaya, tana jin zumudin sake zama da mahaifanta na taso mata.

Haka suka kwana yana jaddada mata irin kewarta da zai yi, tamkar wadda kasar za ta bari.

Kwanaki biyu a tsakani ta koma gida tare da dukkan abin da za'a bukata, Hajiya Babba ce kuma ta kaita kamar yadda ta yi al'kawari.

Sosai Inna ta ke kula da Sa'adah, wankan rumfu take mata ba tausayi, ga duren kunu, da tuwo, duk ranar da zata mata gardama kuwa cewa take yi " Na lura dakinki kike son komawa, zan 'kira Hajiya ta zo ta mayar da ke, tunda ina tattalinki, kina 'ki! idan kika kufu'de na ga yadda za kiyi rawar jiki akan mijin, ko shi ya yi rawar kai akan ki".

Shiru ta ke yi, kan dole kuma sai ta yi yadda Innar take so.

Jawad ya sami kyakkawan kulawa, kullum safe aka masa wanka ya sha nono, Inna take goya shi, haka zai yini a baya sai anyi azahar yake tashi, cikin 'kan'kanin lokaci ya bundume, kammaninsa da Mk suka bayyana 'karara.

A yini Mk na kiran Sa'adah kamar sau uku koma fiye, koyaushe cikin tambayar lafiyar su, ko yace Babana na kukan dare har yanzu, ko ya tambayi me take so, menene bata da shi, kar fa tace zata dinga 'dorawa Baffa nauyi.

Ire iren tambayar kenan a kullum, itakuma cewa take, komai akwai Uncle. Duka-duka ma yaushe muka zo ne?

Ranar da suka yi kwana biyar, ya je musu.

Ana idar da sallar la'asar ya Isa gidan, a zaure ya tsaya, yana faman kiran wayarta, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, ya jingina da bango, yana ri'ke da wayar.

Baffah da yake faman jijjiga Jawad, saboda wankan da Inna ta ke yiwa Sa'adah, kullum ana idar da Sallar la'asar yake dawowa gidan dan ya ri'ke musu shi, su yi wankan, saboda riko da al'adar ba a barin jariri shi ka'dai.😁

Yau sai koke koke yake yi a dalilin cikinsa ya kumburaba a ankara ba, yana sa'be da shi a kafada ya doshi zauren, kwatsam yaga Mukhtar a tsaye.

Cike da girmamawa ya tsugunna ya gaida shi, Baffa sai fadin "ya ka tsaya anan? da ga yau ka dinga shiga kanka tsaye".

Baffah da kansa ya masa jagora har 'dakin Sa'adah yana cewa "wanka suke yi, zauna ka saurare su kadan".

Ya mika masa Jawad tare da fadin "dama so na ke na fita ana jirana za mu je dubiya asibitin Malam".

Cike da kunya ya karbe shi, yana masa godiya.

Baffah na shirin fita Inna ta fito duk ta hada zufa, ta kalle shi, ta ce "kwantar da abokin naka ka yi?"

"A a Babansa ne ya zo, yana gunsa, na shigo da shi, yana dakin Iyah ni fita zanyi, za mu je asibiti mu sake dubo Malam lado".

"Adawo lafiya, shikuma Allah ya bashi lafiya".

Ya fita, yana fadin "Ameen ameen".

Sai da ta sako hijabi sannan ta shiga suka gaisa da Mk, da yake ta fama da Jawad.

Ta karbe shi tana fa'din "Bari a masa wanka kar sanyin yamma ya sauka, ko idan ya ji ruwan dumi zai daina wannan koke koken".


Murmushi kawai ya yi, kansa a kasa, ya bata shi, a zuciyar sa tana jinjina kunyarsa, ko Idris din Sumayya bai kai shi kunya ba.

Yana zaune yana jin kukan wanka da Jawad ya ke tsalawa, jikinsa sai tsuma yake yi, yana jin tamkar ya leko yaronsa ko sabulu ne ya shigar masa ido, amma kawaici ya danne shi.


Ana cikin haka Sa'adah ta shigo da daurin kirji, ta yi mayafi da faffadan tawul.

Mamakin ganinsa a zaune ya daskarar da ita a tsaye.

Da azama tace " Uncle yaushe ka zo?"

"Tun dazu, dan Allah hanzarta ki dubo yaron nan , ki ji har shidewa ya ke yi?"

Ri'ke baki ta yi tare da cewa"oh oh wato Innah tace mini bani da kunya ko?"

"Haka yake da kukan wanka, da angama kuma ya yi ta barci, sai dare zai ishi Inna da kuka".

"Oh barinta ki ke da shi?"

Eh to, shi sai yace ba zai kwanta ba, sai dai a baya! itace kuma mai jure goyon, tace na kwanta na yi barci na huta".

"Amma kuwa dai ba ki da tausayi ko da ya ke, Auta ce ai".

Dariya suka yi a tare, ts shirya cikin doguwar rigar atamfa, irin dinkin masu shayarwa.

Ta zauna tana shafa mai tare da turare, ta yi cas, ta masa kyau, da gaske ta huce din, duk wani kumburi ya sace, fuskar nan da ta aune, duk ta sabe, ta dawo masa Sa'adatun nan mai burge masu kallon ta.

Yace "kin huce din fa Iyah, kin zama so mashallah".

Ta tura baki gaba, tace "ai so na yi na zauna kar na huce din, naga yadda zaka yi".

"Hmm ke dadina da ke misunderstanding dina kike yi sometimes".


"Iyah Iyah"

Ta mike da sauri tana amsawa ta fice gurin Innah da take 'Kiran.

" Zo ki dauke shi ki bashi ya sha, ashe cikinsa ne ya kumbura shiyasa kukan yau yafi na kullum, yanzu Ina bashi wannan maganin ya hau gyatsa, sai kuma ga tutu, dole sai canja masa Pampers din na yi"

Ta karbe shi tana fadin"Ayyah, sannu da kokari Innah".

Ta dawo dakin ta zauna ta fara shayar da shi, Mk da ya zuba musu ido yana jin duk wani bugun da zuciyar sa ke yi da kaunar su ta ke bugawa.

Sai da ya 'koshi, sannan ta mi'ka masa, ya karba yana mai masa kallon kurillah, yana ganin hoton fuskar sa, akan ta yaron.

Ya dago ya kalleta, ya yi kasa da murya sosai, sannan ya furta "Duk yadda kika yi ta makale min, ashe ba wani abin da kike tabukawa? dubi! ba wani abu, na ki a jikinsa".

Kunya ta kamata, ta kasa cewa komai sai ta buge da murmushi.


Haka suka sha hirarsu, ta na shan yoghurt din L&Z da ya taho mata da shi.

Kwana ashirin da haihuwar, Sumayya ta zo ganin Baby, tare da kayan uwa da jariri kala kala,sun zo juma'ah suka juya lahadi saboda makarantar Yara.


Ranar da ta cika sati uku ta koma dakinta, rawar jiki ba irin wadda Mk bai mata ba. Sun tabbatar sunyi missing juna, irin wadda ba su taba yi ba! haka suka cigaba da rainon dansu cikin tattali, da kulawa mai yawa.





Surayya Dahiru
✍🏼✍🏼✍🏼
19/03.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.








59-60


Irin kulawar da MK yake yi wa Sa'adah da danta, yasa take mamakin da ake cewa da zarar mace ta haihu sai namiji ya canja mata, ita kam ba ta ci karo da wannan matsalar ba, ta dinga tunanin ko don ta sami kyakkawan gyara ne a wurin Innarta da Sumayya, ko kuma dabi'ar wasu mazan ce haka?

Lafiya Lau suke zaune, har yanzu a cikin marararinta yake tamkar amarya, hakan ba karamin faranta ranta ya ke ba.

Ya wadata su da komai daidai gwargwado, sannan da ya fahimci, ta fishi saurin fishi, sai ya ke kaffa-kaffa da abin da zai bakanta ranta, shi yasa zamansu lafiya, sai yan kananun sabani na yau da kullum da ba za a iya kauce masa ba. Kuma ba sa bari fishinsu ya wuce na yini daya.

Watan Jawad uku, Sa'adah ta kasa gane kanta, yau zazzabi, gobe mura, jibi jiri, kullum da abin da za ta tashi da shi.

Zazzabin hakori da rashin kuzarin Sa'adah, sai suka yi wa Jawad rubdugu, duk sun yi laushi.

Ganin yadda suke yamushewa ya sa MK ya kai su asibiti, gwajin farko ya nuna ciki ne a jikinta, na tsawon sati hudu.

Dankari! tun a asibitin take kuka, bakin ciki ya turnuke ta, da danyen goyo za ta sami wani cikin? kuka take yi sosai tana fadin sai dai a san yadda za'a yi, amma ita ba ta shirya sake haihuwa yanzu ba. Tun MK na rarrashin ta bari suje gida, har ya gaji ya kama bakinsa ya zuba mata ido.

Suna shiga gidan ko zama ba ta bari sun yi ba, ta ce
"To mun zo gidan fada mini yadda za'a yi".

Ya kalle ta da tausayawa ya ce "Zauna ki nutsu, ki huta sai mu yi maganar, ba inda zani yau, ina tare da ke".

Ba tavce komai ba, ta zauna tana huci, tana jin duniyar ta mata kunci.

Shi kuma ya shige cikin daki ya shimfide Jawad da ya yi barci.

Yana fitowa kicin ya wuce, ya zauna ya dafa musu indomie, ya juye a plate, ya kai gabanta ya ajiye, ya koma ya hado tea Sai da ya zauna sannan ya kalle ta ya ce, "Bismillah sauko mu ci."
Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tare da fadin "Na koshi".

Ya kafe ta da ido, ya nisa ya ce "Me kika ci?"

Ta kasa ba shi amsa, tunda dai ba su karya ba, suka yi sammakon fita.

Ya sake kallon ta, sai goge hawaye take yi, har ransa shi ma bai so samuwar cikin nan a yanzu ba, amma tunda ya riga ya shiga, to ba zai ba ta kofar da za ta yi abin da take so ba.

"Idan har na gama cin abincin nan ba ki ci ba, fita zan yi, ba zan yi maganar da zamu yi a yau ba kuma".

Kan dole ta wanko hannu, ta fara ci, turawa kawai take yi, saboda gabadaya ba ta jin dadi, ga kuma bakin ciki da ya cika mata zuciya.

Sai da ya hada mata tea, ta sha, ya ba ta magani, ya dauke plate da cups din ya kai kicin ya dawo! ya zauna kusa da ita sosai.

Ya sassauta murya cikin lallashi ya ce, "Fada mini matsalar ki akan cikin nan, da kike ta wannan koke-koke da bacin rai".

Cikin kukan ta ce "Har sai na furta matsala, sannan za ka fahimci matsalolin da suka dabaibaye ni?"

"E fada mini mana wata'kila sai na fahimta a yanzu".

Ta goge fuskarta da ta yi kozai-kozai, sannan ta ce "Ba ka ga Jawad har yanzu jariri ba ne? sannan wannan cikin ba irin waccan ba ne, yau kusan sati uku ban da cikakkiyar lafiya".
Ta yi shiru tana jan hanci.

Sai da ya ji shirun ya yi yawa sai ya ce "shike nan matsalolin?"

"Ba shike nan ba, yanzu fa wannan lalacewar da Jawad ya fara yi, yana ta tsinkewa, cikin da yake sha ne, kuma bai isa yaye ba".

Da azama ya ce "Duk na fahimce ki Sa'adah, har zuciyata kuma tausayinku nake ji musamman Jawad, amma tunda Ubangiji ne ya ba mu ya za mu yi? Sai mu raini abin mu cikin farinciki da godiyar Allah".

Kukanta ya dan kara yawa ta ce "Yaye Jawad din za'a yi ke nan?"

"Wane irin yaye kuma ba dadin ji? Ai kin ji bayanin likita, ga magunguna nan ya rubuto muku, ba abin da zai same shi".

Maganganunsa suka haska mata sai ta haifi cikin nan dole, don haka ta dage ta dinga zunduma masa ihun kuka da ya yi sanadin tashin Jawad a gigice, shi ma ya cika dakin da kuka.

MK ya rasa wanda zai lallaba a cikinsu, dole ya wuce daki ya dauko yaron ya fara jijjiga shi.
Sai da ya yi shiru sannan ya kalli Sa'adah da take kuka irin na mutuwar Jahiliyya ya ce "Wane irin abu ne haka kike yi?"

Ba ta kula shi ba ta ci gaba da yin kukanta hannuwa aka.

Kan dole ya zauna kusa da ita yana cewa "Ki ga fa yadda kika sa Jawad kuka, don Allah ki yi hakuri, ke baki san baiwa ce Ubangiji ya yi mana ba?"

"Ni ba na so!" Ta fada da karfi.

"Shike nan na ji ba kya so, ni Ina so". Ya fada da alamun ya ji haushin maganarta.

"Karbe shi, ki ba shi ya sha".

Banda kuka ba abin da take yi, ko kallon sa, ba ta yi ba bare ta karbi yaron.

"Kin ji".

Ta kalle shi cikin ido ta ce "Na yaye shi".

Ganin yadda ta rikice neman tashin hankali take yi da gaske, ya ce "To ba shi ya sha yanzu, kafin a jima na siyo masa abin da zai dinga sha".

Nan ma a zafafe ta ce "Ba zan bayar ba".

Kyale ta ya yi, ya ajiye shi ya hado masa shayi mai dan dumi, ya dauko sabuwar feeder ya wanke ta da ruwan zafi, ya zuba shayin a ciki, sai ya zauna sannan ya dauke shi, ya fara ba shi, cikin ikon Allah ya shanye har da gyatsa.

Ya hada ruwa ya masa wanka, ya shirya shi tsaf, yana ta yi masa wasa, shi kuma yana ta dariya har barci ya sake awon gaba da shi, bai kwantar da shi a dakin Sa'adah ba, ya fita ya kai shi dakinsa don kar kukan uwarsa ya sake farkar da shi, ya rage masa karfin fanka sannan ya fita zuwa wurin Sa'adah, da har yanzu take yin kuka.

A kasan da take zaune, shi ma ya zauna ya ru'ko hannun ta, ya kira sunanta, ta ki amsawa, ya sake tausasa murya ya ce "Yi hakuri tashi muje na taimaka miki ki yi wanka, ki ji dadin jikin ki. Yi hakuri kin ji my sweetheart".

Da kyar ya shawo kanta ta yi wanka, bayan ta ce ba ta son taimakon nasa.

Mai kawai ta shafa ta zura doguwar riga cotton marar nauyi, ta kwanta, tana ta ajiyar zuciya ba jimawa barci ya wuce da ita.

Kwanaki uku ban da tashin hankali ba abin da Sa'adah take yi gaba'daya ta burkice, ban da kuka ba ta komai, ko wanka ba taki yi, bare aje ga hidimar gida, Jawad kuwa da tashin hankali take bashi nono sau biyu a rana duk kukan da zai yi kuwa.

MK ganin ba irin ha'kuri da rarrashi da bai yi mata ba, yasa ya zuba mata ido, shi yake yin komai na gidan har girki, ya ki yarda ya biye mata, ya tabbatar tana cikin halin da za a tausaya mata, duk da abin nata har da rashin mutunci, amma da zarar ya tuna abubuwanta na alheri sai ya mata uziri, babban abin da ya dame shi, rashin shayar da Jawad musamman da yake ana ba shi supplement na yara mai sa su kuzari da saurin girma, akai-akai yake jin yunwa, don ma yana shan madara da fricso cream.

Washegari da yamma ya dawo da ga wurin aiki tun daga waje yake jin kukan Jawad, a sukwane ya shigo cikin gidan, ya tarar da ita, tana zaune a falo tana ganin sa, amma ba ta dauke shi ba.

Bai taba jin haushin ta irin na yau ba, ya jima yana tsaye ya zuba mata ido, yana kallon ta, yana jin tamkar ya rufe ta da duka.

Kwafa ya yi, ya dauki yaron ya hada masa abincinsa, ya ba shi ruwa sannan ya kwantar da shi, yana ta shure-shuren 'kafa, tamkar ba shi ne mai kukan nan ba, da ma shi ba mai fitina ba ne, indai ka ji kukansa to dayan biyu ne, ko yunwa ko rashin lafiya, tunda ya yi kuka kafin su yi arbain shike nan ya daina kukan banza.

Wanka ya yi, ya fito ya zauna a falo, ya dube ta ya ce "Na gaji fa da abubuwan da kike mini, na yi iya hakurin da zan iya, na ga abin naki babu mutunci ko kadan".

Kai tsaye ta ce "Da ma ai so nake ka gajin, matu'kar kana son zaman lafiya, sai dai ka zabi daya cikin biyu, ko dai a yaye Jawad gaba'daya, ko a cire cikin nan".

Ransa ya yi matu'kar baci ya kalle ta ya ce "Ni ban san inda ake cire ciki ba, ke da kika sani sai ki je, ai don kin ga na damu da ke shivyasa kike mini wannan iyashegen, mafi yawa idan mace ta samu ciki da wuri irin haka, daga wurin mijin take fuskantar kalubale, amma ke don samun guri ni kike yiwa wulakanci".

Ya nisa sannan ya ce "Ba zan kai kararki ba, amma daga yau ba zan sake rarrashin ki akan wannan matsalar ba, idan kin ga dama ki bar cikin nan, idan kin ga hagu ki zubar a rariya, Jawad kuma In sha Allah yau an yaye shi, Ubangiji zai raya mini shi, ina ce idan mutuwa kika yi ma ba zai fasa rayuwa ba?"

Daga haka bai kara cewa komai ba, ya tashi ya shiga kicin ya hada cornflakes ya shige dakinsa, bai dawo falon ba, yana kudire ba zai sake dafa abinci ba.

Bai wani jima ba ya shigo, ya tashi Jawad ya canja masa riga, ya samo leda mai kyau ya zuba tarkacen da Jawad zai bu'kata, ya nade shi a shawul, ya saba shi a kafada ya fice, ba tare da ya kalli gefen da takep a zaune ba, bare ya yi mata sallama.

Kawai sai ta ji kuka ya zo mata, bakin cikinta daya yadda bai dafa musu abinci ba, kuma yunwa take ji, ta kalli agogo biyar da kwata 5:15pm, kan dole ta shiga kicin din ta hada tea ta dauko biscuit din super2 ta hau ci.

Gidan Samira da yake Dan'agundi ya tsaya ya ba wa yaro ya kai mata Jawad,

Please Login or Register in order to submit comment