You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi, tunda Ni na zartar da nawa hukuncin, ba kuma zan canja ba, sai na tabbatar da gaske kin daina mini wulakanci".

Da rawar murya ta ce "Ai yanzu ma na yarda! Ba zan sake tureka ba".

Da'di ya yi matu'kar kamashi, dama abin da yake so kenan.
Da rawar jiki ya isa ya rungumeta.

Ya dinga jifa da Hijabinta da komai ma, haka ya dauki lokaci yana abin da ya ga dama da ita.
Yayin da itakuma ta ke share hawaye.

Har ya yi wanka ya fito bata bar kuka irin na sharbe ba.

Ya waske ya yi kamar bai gani ba.
Suna tafe a mota da rawar murya ta ce "Yanzu yaushe ne tariyar?"

A gajarce ya ce "sai kin daina mini kukan da babu dalili, sai na gamsu da gaske idan kin tare din zaki barni na dinga samu nutsuwa da ke".

Da kuka ta ce "kawai na gane yawo kake mini da hankali! Dan kasan ka gama da ni, inace yanzun ba abin da baka yi da ni ba, amma yanzu kana wata magana".

"Tabbas na yi, amma mai na tsinta ban da bacin rai, dame kika taimake ni? inace zama kika yi tamkar ruwa, sannan kina ta Kuka".

A matu'kar gajiye ta ce "To ai ba zan sake yi maka kukan ba".

"To zame mini tamkar gawa fa?"

Da sauri ta ce "Na daina".


"To ki bari sai na tabbatar da gaske kin daina din har zuciyarki".

Cikin kwantar da murya ta ce "yaushe to zaka tabbatar din?"

Ya dauke kai ya ce mu barshi nan da wata daya, idan yanayin biyayyar da kike mini ya gamsar da ni, shikenan sai ki tare abin ki".

Da rawar murya ta ce "idan na kara wata Innah zata gane halin da nake ciki".

"To wai ke wannan boye boyen da kike yi na menene? Abin kunya ne, Inace an daura auren?"

"Ni dai bana so a sani ne kawai".

Ya murmusa ya ce "ai dole ki ji kunya, kin gama fadin ba kya sona a gabansu, sai gashi daga dan ta'ba ki ka'dan, kin yi ciki, ai dole ki ji kunya, ina kika kai 'kiyayyar?"

Ta kasa bashi amsa.

To mu barshi sati biyu nan gaba, amma sai na tabbatar fah".

Tunda ga wannan ranar Mk ya mayar da Sa'a tamkar ya tare da ita ne, domin kullum sai ya fita da ita, ya yi abin da zai yi sannan su dawo.

Har satin biyun ta cika amma baice komai ba, a lokacin cikinta yana shirin shiga wata na uku.

Rannan suna gidan da suke yini, zuwansu kenan, ta kalle shi, ta ce na gane so kake dai sai na kunyata dole. Banda haka menene bana yi maka Kullum sai ka fita da ni, amma ka dage akan bana yi maka yadda kake so?
Fa'da mini me zan yi maka kuma?"


Cikin rashin damuwa ya ce "ba Kya mayar mini da martani kamar da can, sannan kullum na kusance ki da kuka ake karewa, ke yarinyace? Sannan ba har zuciyarki kike amincewa ba, kina yarda ne akan dole, sai dan kina son ki tare kar agane kina da ciki.
Abin da baki gane ba, ni ba abin kunya na yi ba, tunda na yi hakuri sai da aka 'daura aure, ke kika ce ba zaki tare ba da bakin ki. Babana ya goya miki baya, yanzu kuma sai ki dame ni da maganar tariya alhalin kin san inda zaki fa'di kin matsu ki tare, asa ni dole, ko bana so".

Ya nisa ya ce "ki kira Baba da bakinki kice zaki tare".

Idonta ya ciko da kwalla ta ce "Kaine zaka kira ka ce ka shawo kaina na amince, idan ya nemi jin ta bakina sai na yi shiru alamun kunya, shikenan sai ya gane ina bu'katar tarewar da gaske".

Ya tsura mata ido ya murmusa ya ce "Sannu Sa'adah! Ke idan kina son abu, kin iya shirya zance".

Daga haka ya janyota jikinsa yana kissing dinta.

Sai dai yau yana kammalawa ta dinga kelaya amai tana kuka.

Sosai ta yi, sai da ta kammala ta koma gefe ta cigaba da kukanta.
Haka Mk ya kwashe Aman nan, ya sa tissue ya goge.

Ya kalleta ya ce "je ki yi wanka".

Bata Musa ba ta mike ta shiga toilet.

Ta fito ta same shi ya yi tagumi da hannuwa biyu.

Ta zauna a sanyaye.


Ya kalleta ya ce "Anya kuwa Sa'adatu kina jin tsoron ubangiji? Anya kuwa baki kafirta ba?"

Da saurinta ta dago ya ce "kwarai kuwa! Na sani kishi ne yake son halaka ki! Amma ki sani ubangiji ne ya halasta, sannan shine ya bada umarnin a auri bibbiyu ko uku ko hudu. Aaya ce sukutum cikin al'kura'ani mai girma.
'Kin amincewa da hukuncin Allah kuwa tamkar ka kafirta ne".

Ya yi shiru yana nazarinta.
Ya nisa ya cigaba da cewa "ina jiye miki kada ki halaka kanki, ki halaka ni, Ina jiye miki tsoron kada na samu aljannah adalilin ba'kin cikin da kike ta 'kunsa mini, ke kuma ki tsince kanki a wuta.
Annabi ya ce akwai mazan da suke rabauta da aljannah adalilin hakuri da taurin kan matayensu da kaifin harshensu.
Ina jiye miki na shiga aljannah, na hadu da Farida ba da ke ba".

Dai-dai nan ta rushe da wani irin kuka, fiye da kukan da ta yi ranar da ya saketa.

Da sauri ya matso ya rungumeta, domin ya tabbatar wannan kukan ba na shagwaba ko iyashege bane, na tsantsar damuwa ne.

Bai hanata ba, ya barta ta yi, iya yinta, ganin yana neman wuce ka'ida ya sanya ya fara lallashinta da gwalagwalan kalmomin da suke nuna kololuwar matsayinta a zuciyarsa.

Cikin kukan ta ce "Me yasa sai ita zaka aura? Me yasa na shafe shekaru hudu, Ina binka ka mini afuwa ka 'ki, karshe sai ka hukunta ni da auren wadda na tsana, Dan Allah baka ji a zuciyarka ka tozartani ba?"

Da sauri ya ce " Ni ban tozarta ki ba, domin 'auren da na yi 'kaddarata ne, wadda ko muna tare ba zan iya tsallakewa ba.

Ta ture shi ta ce "Ai kuwa zamu rayu a haka cikin damuwa, domin zuciyata ba zata huce ba, har sai ka yarda ka wulakantani, ka mini hukuncin da ya wuce laifina".

Ya sake rungumeta tsantsan tamkar zai mayar da ita cikinsa ya ce "Anya mutum yana tozarta zuciyarsa da rayuwarsa? Amma tunda shine abin da zaisa ki yafe mini, shine abinda zanyi ki dawo mini da nutsuwata, to na yarda na wulakanta ki, amma wallahi ba intentionally na yi hakan ba, ki yafewa masoyinki, kamar yadda na yafe miki, ko na tuna abubuwan da kika yi mini, a take nake jaddada cewar Ubangiji ya zama shaidar na yafe miki, ya kuma hane ni tunowa".

Da rawar murya ta ce "Ai ni ko ina son na manta din ba zai yiwu ba, a da kai din nawane ni ka'dai, kome zan yi maka na san ba inda zaka je ka kwana zaka dawo gare ni ne, amma yanzu fa? Zan dinga rabaka ne da wata muddin rai".

Ta karasa cikin kuka na sosai.

Shi kansa da ya tuna bala'in da ya shiga da ya ganta da Khalil ya gamsu ita din jarumace, domin shi akanta ba zai iya shanye abin da ita ta shanye ba, ya dinga ji har zuciyarsa yana taya ta Jin ciwon kaddarar nan da ta kutso musu.

Ya Dora bakinsa daidai kunnenta ya ce "Daga yau din nan ba zan sake maimata miki wannan kalmar ba! Ki ri'keta ta zame miki jagora a zaman da ubangiji ya kaddara zamu yi".

Ya nisa ya ce "Wallahi ban taba son wata halitta a doron 'kasa irin ki ba, Hajiya ce kawai ta fiki darajah a duniyata.
Ke nake yiwa so na 'kauna, so na sha'awa, so na burgewa, wani irin so nake miki da a kullum ina tuna ki sama da sau sabain a rana, ke kadaice nake tuna abin takaicin ki, amma sai na tsinci kaina da yin murmushi.
Ke kadaice kike mini iyashege ya burge ni.
Ke kadaice macen da idan na kalla sai na tsinci kaina da yawan ambaton Alhamdulillah!
Ke ka'daice macen da idan na ta'ba ki, ba ki mayar mini da marta ni ba, nake Jin bacin rai da tashin hankali.
Haka nan ke ce macen da nake fatan idan na tsinci kaina a aljannah na fara tozali da ita cikin jerin matayen da ubangiji zai bani.
Wallahi idan kika cire Hajiya ba wadda nake jin sonsu a raina da zuciyata irin ke da d'anki."

Ya nisa ya cigaba da cewa
"Ba zan miki karyar bana son Farida ba, ba zan miki karyar bata da wata daraja a idona ba, hakanan ba zance miki bana jin da'din zama da ita ba.
Sai dai idan har gaskiya zan fa'da miki! Ina jiye miki a wayi gari Farida ta yi kunnen doki da ke a zuciyata, koma ta zarta ki, domin ita din mai hakuri ce, mai kawaici ce, ta sani na fi sonki, amma bata ta'ba tayar mini da hankali akan hakan ba.
Zuciya a kirjina take kawai, amma bani nake sarrafa ta ba, ubangiji ne, Annabi kuma ya ce an gina zuciya da kaunar wadda yake kyautata masa".


Jikinta ya laushi irin tubus din nan, tana gasgata dukkan furucinsa, ta kuma gasgata tana da kafiya da kaifin harshe.
Tun ranar da ya auri Farida bata sake jin nutsuwa a zuciyarta akansa ba, sai yanzu.

Ta nisa ta ce "Shikenan! Ka yi ha'kuri zan gyara, zan kuma kiyaye, amma dai ka dinga mini uzziri, ni akan ka, bana iya sarrafa kishina, ka taya ni addu'a, ka kuma kara ha'kuri da ni, kar kuma ka bu'de kofar da wata macen zata kamo ni a zuciyarka".

Ta fa'da hawaye na zubowa.
Da sauri ya matsa ya rungumeta, yana jin tamkar an yaye masa wata katuwar masifa a rayuwarsa, yana jin wata irin salama tana mamaye dukkan zuciyarsa.
Ashe wannan 'daaurin da 'kirjinsa ya yi, ashe wannan fargabar da yake tsintar kansa a ciki, duk saboda rashin samun aminci ne daga wajen Sa'a?

A yanzu da ta yarda zasu zauna lafiya sai ya ji tamkar anyi masa bushara da gidan aljannah ne.

A fili ya dinga fa'din "Alhamdulillah! Allah kasa karshen tashin hankalin da zamu fuskanta kenan, Allah ka sanya wannan shine karshen jarrabawar mu".

Sau uku tana yun'kurin yin magana sai ta kasa, da ya lura da hakan sai ya ce "fill free, fa'da mini abin da ke ranki".

Ta tura baki gaba ta ce "Amma dai ka yi mini al'kawarin ba zaka ha'da ni zama da wata matarka ba, kuma yanzu na tabbatar waccan part din na Amaryarka ne".

Ya sake ru'ko ta sosai ya ce "Ban manta al'kawarin ba, amma sai nake ganin a waccan gidan da kika tsara yadda za'a gina shi, na miki wannan al'kawarin, yanzu kuma ai bashi bane".

Da rawar murya ta ce"kar ka hadani zama da ita, kar ka bari na dinga ganin mua'amalarku, zaka iya rasa ni a dalilin ciwon zuciya ko hawan jinin farat 'daya".

"Ina son ki koyi jarumta Sa'adah! Ina son hankali na ya tsaya a wuri daya, a yanzu da nake matu'kar mararinki, idan na rabaku zan halaka ne, Ina tabbatar miki zan tare ne a inda zuciyata tafi so, shi kuma adalci wajibi ne ka yiwa kowa.
Addinin musulunci! Addinin adalci ne, ubangiji ya sani namiji ba zai iya raba soyayyar matansa ta zama daidai a zuciyarsa ba, sai akace an masa uzziri anan, ma'ana bai yi laifi ba dan ya so wata sama da wata ba.
Har ilah yau Sharia bata ce dole abin da ka yi da wannan, idan ka koma wajen wannan ma sai ka yi mata irin wannan ba, domin ansan ba zamu iya ba.
Amma duk da hakan sai da Annabi ya yi ta wasiyyar kar mu jingine mace, mu ratayeta ita ba sakakkiyar mace ba, ita ba matar aure ba, dole a rabon kwana, muhalli, abinci da sutura ya zama daidai (eqaul).
Shari'ar musulunci ta yiwa mata gata da adalci, ta yadda ko ba ke aka fi so ba, to kuwa indai ana kan tsarin sharia din ba za'a ki wulakanta ba".

Ya numfasa sannan ya ce "ki min hakuri zaki koma wanccan gidan amma ba yanzu ba, ki bari nima na koyi jarumtar da zan kiyaye ka'idojin shari'a".

A hankali ta ce"To" ba dan tana so ba, sai dan kar ta cigaba da yi masa gardama yana ganin Farida ce mai biyayya kawai.

Ya tsura mata ido yana kallonta, sonta sai huda dukkan sassan jikinsa yake yi, cikin kasalalliyar murya ya ce "har yanzu baki huce da ni ba, har yau baki yafe mini ba?"

Murya ba amo ta ce "me yasa ka ce haka?"

"Har yanzu ban ji kin kira suna na ba, Na sani kuwa idan kina fishi ne kike gatsa sunana dan ki nuna mini iyakata. Idan kuma ba kya son shiga shirgina sai ki yi maganar ki ba tare da kin kama sunan ba"

Ta zuba masa wani irin kallon da yake kidima shi, tana murmushin da wurshiryarta ta bayyana, hawaye kuma ya zubo mata Ta ce "Malam".

Farin-ciki ya dirar masa fiye da wadda yake ciki, rabon da ya ji ta ambaci Malam a bakinta, tun ranar da suka hadu a gidan 'Karfi kafin komai ya tabarbare musu.

Ya sa baki yana lashe dukkan hawayenta da yake zubowa.

Ya yi gyaran murya ya ce "nan da kwanaki shida zaki tare, Ranar juma'ah mai zuwa.
Yanzu mu je ki za'bi funtures din da kike so, masu harkar 'kawata gida, za su zo su shirya miki".

A hankali ta ce "Na gode sosai! Amma ka barsu, domin yanzu ina da kishiya idan ta gane haka na zo, zata samu dama akaina".

Ya kalleta ido cikin ido tsawon lokaci sannan ya ce "Na ta'ba rokon ki a shekarun baya ina so ki ji a ranki nima tamkar Sumayya nake a wurin ki, ashe baki dauke ni hakan ba?"
Ta kasa bashi amsa.
Ya ce "Wallahi Sa'adah ko wani kika aura ni zan miki komai da uba yake yiwa yarsa domin Baffah zan yiwa, lokaci ya yi da zai huta, a yanzu abin da nake ji game da shi ba wai kallon mahaifinki nake masa ba, kallon nawa uban nake masa, domin ya mini abin da na tabbatar uba ne kawai zai yi wa 'dansa.
Na yarda da maganar da ake cewa ko baka haihu ba, idan ka yi alheri ga marayu da masu rauni, ka zauna da mutane lafiya, ka yi hakuri da cutarwarsu, to ubangiji sai ya turo maka wadda zai yi maka abin da ko 'danka ba zai maka ba, haka nan idan kana da zuri'a ubangiji zai baka wadda zai jibanci lamarinsu ko da baka numfashi".
Baffah uba na ne, da ubangiji ya bashi, komai zan yiwa jinisa a duniya ban biya shi ba, dan haka ki yarda da ni, ko ba aure a tsakaninmu Ni din mai yi miki komai ne, mai kuma tsaya miki ne a ko Ina".

Ya yi shiru! Sai kuma ya cigaba da cewa "wanccan gidan da kike magana akai tun ranar da kika ce mini filin ki Baffah ya siyar ya bani ku'di, zuciyata take ta bugu akan na baki shi kyauta, sai dai bani da halin bawa Farida irinsa, dan haka na bawa Jawad shi, na je an canja takardun, sunan Jawad ne akai.
Idan na gamsu sosai zan iya ware miki gida, shikenan sai ki koma gidan d'anki kafin na samu damar da zan sake yi muku wasu gidajen a jere amma ko haraba ba zan ha'da ku ba".


Karon farko da tasa hannu da kanta ta rungume shi tana kuka 'kasa-'kasa. Ta tabbatar da gaske Malam din nata ne har yau.

Ta ce" na gode sosai ubangiji ya fini yabawa.
Zan iya kokarina ban tayar da hankalinka ba, ba zan cuci matarka ta hanyar asiri, ko sharri ko zagon kasa ba, lafiyarta da mutuncinta har ma da dukiyarta amanace a gare ni, na yi maka al'kawarin ba zan tsokaneta ba, ba zan taba mutuncinta ba, ba zan yi shirka dan na farraqa tsakaninku ba, na yarda 'kaddararka ce itama.
Amma abin da nake so ka yi mini dalci a ciki shine ni ban iya munafunci ba, am straight forward, ka ja mata kunne akan tsokanar da take fakar idon mutane tana yi mini, ba zan yi gaba da ita ba, amma kuma babu aminci a tsakaninmu da zamu zama so close, kowa ta yi harkar gabanta".

Jiki na rawa ya dinga fa'din"thank you! Thank you so much my love".

Saboda ba 'karamin nutsuwa ya samu na saukowar ta botsarar tasa ba,๐Ÿ˜… ya dinga neman tsari da abin da zaisa ta sake mur'dewa. Ya tabbatar har zuciyarsa tsoron fishinta yake yi, tsoron ta birkice yake yi, 'karfin hali kawai yake gwada mata, idan yana bagarar da ita ko yana nuna mata iyakarta.

Bai nemi ya sake ta'ba ta ba, duk da yana bu'katar hakan. A waya ta zabi furniture's din da take so, amma Mk ya canja mata da masu tsadar gaske, ta dinga jin tausayinsa, shikuma so yake ya wanke mata zuciya, ya sani dan ta kwantar masa da hankali ne, da kuma son ya fahimci ita yanzu ba luxury life a gabanta yasa ta zabi masu sau'kin kudi, shikuma sai ya daure ya siya mata masu daraja sosai tunda ya yi 'karfi yanzu, business dinsa yana garawa 'kwarai da gaske.

Ya mayar da ita gida, suka rabu cikin shau'ki tamkar wani abin bai ta'ba gittawa a tsakaninsu ba.

Kai-tsaye gida ya wuce tunda biyar ta yi, ya samu Farida a falo ta yi kwalliya ta sha kyau, ga abinci a dining, yana jiransa, ya dinga jin kunyar me zai ce mata kuma yau?
Tunda yake fita da Sa'a baya cin abincin rana a gida, saboda tare yake ci da Sa'adah.

Ya daure ya bita zuwa dinning din, ta zuba masa brown sphagetti da ta ji kayan lambu, sai papper fish a gefe.

Ya dan ci ka'dan ya ture domin ya riga ya shafa'a ya ci a waje.

Takaici ya 'kume Farida, idonta ya ciko da 'kwalla.

Ya kalleta ya ce "menene yake damunki?"

Da rawar murya ta ce "yau kusan kwanaki goma baka cin abinci na, jiyan nan ka gama yi mini al'kawarin yau zaka dawo mu yini tare, kai ka ce na yi maka wannan nau'in abincin, na yi kuma ka bar mini abina".

"Yi ha'kuri my ferial! ba haka bane, ai dai kinsan duk safiyar duniya da abincin ki nake karin kumallo, idan na yi aiki na gaji ne, yunwa ta kamani sai na kasa daurewa na je capteria na ci, amma yi hakuri zan dinga jurewa".

Yana rufe baki ta ce duk zamana da kai ban san kana zuwa capetaria kullum ba, sai yanzu dai da ka yi Kome!
Na san abin da nake yi, Ina sawa abin da nake so ido fiye da kaina, kullum ka cire kayanka scent din Gogel nake ji, ban yi magana bane saboda na sani matarkace kuma cike kake da 'dokin sake dawowar ku abu guda, amma kuma shikenan sai abin ya zama ba waiwaye tun yanzu kake son sai dukkan rauni na ya bayyana? Ka yini a wajenta, ka dawo mini gida a gajiye da ka kwanta sai barci".
Ta fa'da muryar ta na rawa.

Sanin da ya yi ita din ba mai 'korafi ba ce, sai ya gano lallai bango ya nemi kaita, ya sani kuma da gaske ne ya watsar da ita a wannan tsukun.

Dan haka ya sassauta murya ya ce "very sorry my dear! Ko ka'dan ba abin da kike nufi bane, amma tunda na bata miki, ki yi hakuri ki sake yi mini afuwa da uzziri. Ubangiji ya miki albarka, ke mai hakuri ce, mai kuma fahimta ce."

Da haka ya lallaba ya jata bedroom, second round din da bai yi da Sa'a ba, ita ya yi da ita.

Sai daf da magariba suka samu kansu, a gurguje ya yi wanka ya wuce masallaci, yana jinjinawa duk Namiji da yake da mace sama da guda, yake kuma tsaye dan ya yi adalci.

Sai da ya dawo ya fa'da mata Sa'adah zata tare ranar juma'ah mai zuwa, ita kuma zata tare juma'a ta sama.

A ranta ta ji ita ya kamata ta fara tarewa, tunda itace suke tare, bai kamata ace ita zata je ta tarar da Sa'adah ba, shikuma ya yi hakan ne dan ya tabbatar da Sa'a ce uwargida ba dan wani abin ba.
Amma sai ta ce "Allah ya Sanya alkhairi".

Ranar laraba aka gama shirya komai na bangaren Sa'adah! duk inda tsari da haduwa wurinta ya kai, a ko ina kuwa, ba kananun kuda'de aka fitar ba.

A ranar dai ta laraba Sa'a na zaune a tsakar gidansu ba hijabi a jikinta adalilin Inna ta je unguwa, ba zato ta ji sallamar Innar a tsakar gidan.

Gabanta ya yanke ya fa'di, ta hau dube duben Hijabinta ashe a 'daki ta barshi.

Zabura da waige-waigen da take yi ne ya ja hankalin Innah ta tsura mata ido, take ta gano abubuwa masu yawa da suka sauya a tare da Iyah.
Kirjinta ya matu'kar cika, sannan ta yi fari ta 'dashe tamkar mai shafa man bleaching, sanin da Innah ta yi duk kwalliyar Sa'a bata yarda ta canja launin fatarta ba.
Ta kalli fuskarta tana ganin yadda ta 'danyace, alamun dai mai shigar ciki 'karara.

Dabas Innah ta zauna tana hirji.

Ta jima tana kokawa da numfashi, sannan ta ce "mafarkina ne zai tabbata Iyah, ko kuwa yanzun ma mafarkin nake yi?"








SURAYYA DAHIRU




โœ๏ธโœ๏ธ.



๐ŸŒบ *HALIN YAU*! ๐ŸŒบ

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ยฎ_* โœ๏ธ
โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ษ—amfare da bin ฦ™a'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ
____________(โœช)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/




113-114.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*PROLOGUE*.


*Masoyan FARIDA*!
*Team FARIDA na so na ambato sunanku, sai na gane yawanku ba zai bari ba, Farida tana sonku, tana yaba muku, Ta ce na ce muku son so Fisabidillahi*.๐Ÿฅฐ

*MARUBUTA*

*Hajiya Saliha A.A Zaria*
*Hajiya Hafsat Sodangi*.
*Hajiya Maimuna Beli*
*Aunty Sumayya Takori*.
*Hajiya Zulaihatu Sani Kagara*
*SADIK ABUBAKAR*.
*Fadila lami'do*.
*Binta Abbale*.
*Hassana 'Danlarabawa*
*Maman Mama*.
*Ayusha Muhd*
*Kulsum Baffah Azare*
*Umm Azghar*.
*Gidan Iko*
*Asiyah(asi beauty)*
*Aisha jos*
*Hafsat Bature*
*Rabi'atu Shitu*
*Aysha Dansabo*.
*Da dukkan yan kungiyar lafazi writers da ma sauran marubuta gaba'daya*
*Ina godiya sosai tare da fatan alheri.* *Allah ya 'kara Basira.*



*Da* matu'kar kunya Sa'a ta ce "wanne irin mafarki kike magana Innah?"

"Kul kika yi mini iya-shege Iyah! Ai kin san dai mai nake nufi, mike tsaye na ganki soasai".

Ta 'ki mikewa sai 'boye jikinta da take yi.

Salati sosai Inna take tana cewa Ni dama na da'de ina mamakin yadda aka yi kika sauko har kina nuna zakuwar ki akan ki tare, dan munafunci har kina cemin wai saboda ra'ayina zaki ha'kura ki tare ko ba kayan daki, ashe ke kin tare ma kawai ankara ne ban yi ba.
To yanzu sai ki fa'da mini lokacin da kuka kunsa cikin dan asan ko auren na ku bai yiwu ba."

Da rawar murya Sa'a ta ce haba Innah yanzu sai ki yi tunanin zan iya yin wannan ta'asar?".

"To ina zan sani tunda daga ke har Muutar din ba mutunci ne da ku ba , bare kunya.
Wato shiyasa kullum sai kin san yadda Kika 'kirkiro fita, ko dai da sunan zuwa gurin aiki, ko wani uzzirin da ba za'a hana ki fita ba? Oh ina zaune anmayar da ni garmaho, ko a dakin nan kuka yi abin da kuka yi?"

Kuka Sa'adah ta saka, tana jin wata irin kunya tamkar ta tsaga kasa ta shige.
Ta kasa magana, tana jin haushin Mk da ya janyo mata wannan muzantar a idon uwarta.

Ana cikin hakan Baffah ya shigo ya ce "me ya samu uwata take kuka har da hawaye ne?"

"Kukan iskanci take yi, ba dama ta yi ba dai-dai ba, ayi magana sai ta bare ja'irin bakinta ta yi kuka tamkar yarinya kankanuwa."

"Me ta yi da ba zaki iya hakuri zuwa jibi ta tafi dakinta, itama hankalinta ya kwanta ba?"

"Hmmm! ciki ne da ita, daga na tambayeta yaushe suka yi cikin dan asan matsayin aurensu shine take wannan gunshekin kukan tamkar na daketa ne, ke kam wallahi kin ji kunya, ba dan ni na

Please Login or Register in order to submit comment