You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manta da
batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar
da kansa yana rufe idanu ya ce. "A...a...au au aure kuma A a Abba?" "E, Aure mana
Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi
aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi" Sheikh zai magana
Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
"Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin
lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada
kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m zai isa komai na lefen" Sheikh ya ware idanu
jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya
sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta "2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa
fa?" Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan
gane da rayuwar mace.

"Meke sani Sheikh Aliyu? Kasan kayan mata da tsada, ko kai Alkyabbar nawa kake
siya? Duk Alkyabbar ka tafi nawa kuɗi sosai, kuma a arziƙin da Ubangiji ya yi maka
dan an taɓa 2.5m har wani abu ne?" Shafa gemunsa zuwa sajansa kawai Sheikh ya yi
bai damu da auren ba, amma yaji daɗin yadda Abba Hakimi ke nuna kulawarsa ga duk
abin da ya shafe shi.
Abba Hakimi bai nunawa Sheikh ya san komai ga Bankunan da yake shirin buɗewa ba,
dan haka sai ya ce "Ka tashi kaje can gidan, kuɗi kuma daman hakƙina ne na aurar da
kai daga nan har sadaki" jin Sheikh yaƙi cewa komai ya sanya Abba Hakimi ɗago kansa
ganin Sheikh ɗin ya yi zaune jingine jikin kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu
zufa na yanko masa tsakanin gashinsa jikinsa na rawa kaɗan kaɗan.
Girgiza kai kawai Abba Hakimi ya yi tare da jawo rubutun da ya yi da safe ya
tsiyaya a cup ya zuba zuma a ciki ya juya kaɗan tare da ajjiyeta gefe guda zuwa
lokacin da Sheikh ɗin zai daidai a hankali shi kuma yaci gaba da duba wani littafin
Tafsir.

Mother na zaune tana girgiza ƙafa cikin damuwa take kallon tilin kayan lefen dake
parlourn, da sunan kayan lefen yarinyar da Sheikh zai aura. Yaya Halima ta ce.
"Na daɗe banga kayan lefe mai yawan haka ba, shi Sheikh ɗin har nawa ya bada?"
Motar ba ta ce komai ba sai Dr A'isha data kalli kayan da kyau ta ce. "Kalli fa
Yaya iya gold guda biyar ne, Wallahi sai na ɗaukar wa su Maimoon kowa ɗaya abar
shegiya da ɗaya kawai" Mother ta kalli Dr A'isha ta ce. "Tsinke na kayan nan babu
mai ajjiye mini cikin gidan nan, balle su Maimoon su saka ba su rasa komai ba, a
barwa wacce aka siyawa". Dr A'isha ta ce "Amma Barrister kalli kayan fa? Ni dai sai
na ɗauka dukiya ai ba hauka bane" cikin faɗa Mother ta ce "Wai meke damunki haka
A'isha akwai abin da kika rasa ne balle kayan nan su dameki idan su kike let me
know I'll buy it for you" a sanyaye Dr A'isha ta cewa yayat tata "Am sorry Yaya"...
"Sai haƙuri Barrister" cewar Yaya Halima wacce take babba a cikinsu. Miƙewa kawai
Mother tai tana faɗin "Idan ban yi haƙuri ba kashe kai na zan? Ina nan dai wlh sai
na aurawa Sheikh wata macan ya haɗa mata biyu" Dr A'isha ta ce "Wai ya kaga Sheikh
da mata biyu" Dr A'isha ta kalli Yaya Halima ta ce "Nifa ina da shawara Yaya
Halima, mai zai hana mu kai kayan lefen nan da kanmu zamu ƙara ganin ita Zahran da
ake faɗa sai mu ganu tarbiyyar ta" Yaya Halima ta ce "Gulma zamu kenan? Maza ke
kaiwa a bari su kai kawai?" Dr A'isha ta ce "Please mana Yaya Please" da ƙyar Yaya
Halima ta amince ta ce zata nemi Engineer domin tasan yadda Mother ta ɗauki
Al'amarin ba lallai tai magana ba.
Da daddare duk suna zaune a parlour Mother, Yaya Halima, Dr A'isha dasu Maimoon da
auta Fattoumah. Motar Sheikh tai parking a gidan da gudu Fattoumah ta miƙe yana
faɗin "Yaa Lee Mother ta Yaa Lee nan" murmushin jin daɗi Mother ta yi ba tare da ta
ce komai ba. A hankali ya fito da ƙafafuwansa waje kasancewar shi kaɗai ne da kansa
ya yi driving hakan ya sanya gajiya ta saukar masa, yana fitowa Fattoumah na zuwa
wajansa da gudu ta ce "Wlcm Yaa Lee" lumshe idanunsa ya yi tare da buɗewa, ganinta
ƙarama kuma autarsu ya sanya ya sassauta fuskarsa tare da sunkuyawa ya ɗauke ta da
hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya rufe motar. Gemunsa taja ta ce "Yaa Lee ina kake
zuwa muna ta missing naka" ya ware idanu bai ce komai ba sai hancinta da yaja
kaɗan.
Da idanu suka bisa yana sanye da shadda ruwan madara babbar riga da jamper bai saka
hula ba sai hirami daya rufe kansa da shi fuskar shi mai ɗauke sanje zuwa gemu ta
bayyana ta cikin hiramin daya gewaye fuskar. Ƙamshin Roja tuni ya mamaye parlourn
da ƙamshi, Maimoon da Zeefa duk suka miƙe tsaye suna sakin murmushi a tare suka ce
"Sannu da zuwa Yaa Lee" bai kalle su ba ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga
Fattoumah dake masa surutu, bayan ya zauna saman kujera ya daidaita nutsuwarsa da
kyau cikin ƙasa da murya ya ce. "Barka" ya faɗa kai tsaye ba tare da In-ina ba, Dr
A'isha da Yaya Halima suka kalli juna. "Dani ka ke ko Yaya Halima?" Bai kula Dr
A'isha ba ko kallonta bai ba domin yasan nemen magana ce. Tai dry ta ce "Ka gama
kame fuska duk girmata da kayi dole ace da mijin iya baba, ko yanzu goma ta faɗi
tafi biyar albarka dole na amsa sunan uwa a gare ka" miƙewa yai da Fattoumah ganin
Dr A'isha na neman fasa masa kai da surutu. Kai tsaye Upstairs ya nufa ɓangaren
father domin amsa kira. Yaya Halima tabi bayan shi da kallo ta ce "Sannu Dr da
tsaurin ido, lallai karanki ya kai tsako Sheikh kike faɗawa haka? Sai da Barrister
Maryam ta yi aure ta haifi Sheikh da shekaru huɗu ba aka haifeki?" Dr A'isha tai
dry ta ce "Wallahi yaya ƙarfin hali ne kawai, amma ba ƙaramin kwarjini ya yi mini
ba, gashi ko inuwata bata samu albarkar kallo balle Ni" dry gaba ɗaya sukai. a
zaune Sheikh ya samu Father hannunsa riƙe da jarida idan kaga Sheikh da Father ba
zaka taɓa cewa Sheikh ne ɗa ba, domin yafi cika idanu da jiki tsayi faɗi uwa uba
fuskar Sheikh data samu sumar ƙwarai ta ƙara fidda asalin shi. A kan carpet ya
zauna yana sauke numfashi kansa a ƙasa bakinsa na rawar gaida Father ya yi saurin
ɗaga masa hannu ya ce. "Bani da lokacin jin faa kakkkkka yayyyya, na kiraka domin
ka shirya zuwa Yola wajan Zahrah kafin akai lefe jibi, umarni na baka Aliyu ba
shawararka nake nema ba" Jinjina kai kawai Sheikh ya yi bai ce komai ba. "Tashi
kaje idan ka zauna ba zaka amfane ni da komai ba, zan bawa Saif-wazir address ɗin"
miƙewa tsaye Sheikh ya yi sai da yaje bakin ƙofa Father ya ce "Ka kwana a nan, ban
amince ka koma gidan Hakimi ba daga nan har ɗaurin aure" Sheikh ya juya da sauri ya
kalli Father wato ya fahimci duk abin da yake masa baya damunsa shi yasa ya sanya
Abbansa cikin al'amarin. Juyawa ya yi kamar yadda ya ce ya nufi Part ɗin nasa yana
tattare babbar rigarsa.

Washegari tunda ya yi sallar asuba bai koma ba, sbd wani irin mafarki da ya yi,
abin ya tsaya masa yana son neman fassarar mafarkin wajan Abba Hakimi amma ya kasa,
baya son mafarkin ya dangancin wani jinsi wanda ba nashi ba. Ƙarfe 7 daidai ya
shirya cikin Milk ɗin shadda gezner bai saka babbar riga ba, sai golden ɗin
Alkyabba daya sanya ya ɗora golden ɗin hirami, da ƙyar ya yi breakfast ɗin da
Mother ta kawo masa shi ma sai da ta zauna ya gama jan ajinsa yaci kana ta fita
ganin ko ƙala bai ce mata ba. Yana gamawa shirya wa Saif-wazir ya jashi zuwa garin
Yola da taimakon Map. Sai da sukai nisa sosai sun ma bar Commission Quarter's ɗin
sun nufi wani waje kamar daga Sama Saif-wazir yaji Sheikh yai gyaran murya kaɗan
alamar ya tsaya. Waje ya nema ya yi parking gurin kamar jeji kamar ƙauye kuma.
Cikin nutsuwa ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa, a hankali ya fara bin
wata hanya hannunsa goye a bayansa. Sai da ya yi nisa sosai kana yaja ya tsaya.
Kwance ya ganta kanta kife a ƙasa jini na zuba kaɗan a goshinta sai ƙwaryar
kindirmon dake gefe guda hannunta guda riƙe da cikinta, da sauri ya zame idanunsa
daga gare ta sbd kansa da yaji ya sara yana ƙoƙarin barin wajan wasu ƴan Fulani
riƙe da Sanduna suka gewaye shi ɗaya ya ce "Aradu mun kama masu fyaɗen yara" Sheikh
ya ware idanu amma bai nuna komai ba, wani ya ce "Wannan kamar kidnama waye kai?"
nan ma shiru ya yi bai ce komai ba, Labo da yafi su iskanci ya kalli inda take
kwance ganin jini a kanta ya ce "Aradu fyaɗe ya yi mata, kuma tunda kayi mata fyaɗe
dole doka ta hau kanka" Sheikh trying to explain amma harshe ya sarƙe. "Kai ku
saurara" Saif-wazir wanda hankalinsa bai kwanta da yadda Sheikh yabar motar ba, ya
faɗa yana nufu wajan. Ƴan Fulanin suka tsaya ya kalle su sosai ya ce "Kuna hauka
wanne irin fyaɗe mai yasa baku da tunani ne, yayi muku kama da wanda zai aikata
haka?" Labo ya ce "Alkur'an sai na raɗeka da wannan sandan, ga jini nan muna gani
ya kwantar da ita, dole kawai ya amshi hukunci" Saif-wazir ya ce "Wanne irin
hukunci kuma?" Labo ya ce "Kai maza kira mana Giɗaɗo" abu kamar wasa kafin kace
wani abu kusan gaba ɗaya ƴan Fulanin Rugar Bello suka zagaye Sheikh. Giɗaɗo ya
kalli Sheikh kana ya kalli Labo ya ce "Zaro mana zoben hannunsa daka gani mai
tsaida ne" Labo ya kama hannun SHEIKH tare da zare zoben, kusan mutuwar tsaye
Sheikh ya yi yama rasa me zai ce, sai gumi dake yanko masa ya shigo ne domin
tsinkar wani ganyen magani kalli yadda tsautsayi ya rutsa da shi. Kamar daga sama
yaji Giɗaɗo na faɗin "Allhamdulillah mun riƙe wannan zoben matsayin sadaki" Saif-
wazir ya ce "What sadakin me?" Giɗaɗo ya ce "Ai yanzu muka aura Wannan Balaraban
aure da yarinyar nan, ni ne waliyin yarinyar Labo kuma waliyin Balaraban hakan shi
ne hukuncin duk wanda ya yi wa wata fyaɗe a Rugar Bello, yanzu da shi da ita mata
da miji ne halak ɗin sa ce....


Free pages yana gab da ƙare wa biya kuɗin ka domin shiga Paid book tuni sun yi nisa
da karatu😂 .... Biya 500 ta Wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu
Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616. Ƴan nijar sun yi mini magana.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Nimcyluv sarauta*_

15....
Saif ya ce "Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?" Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na
yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi
baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce "Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya
isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello"
cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce "Saurara fillo kake kowa, an
faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana
da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku
warware auren yanzu nan" Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga
sanda sama tare da zagaye su Sheikh "ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza
Alqur'anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi
lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello" Saif-wazir zai magana Sheikh
yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi
musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he
doesn't want that to happen. "But Sheikh....," Sheikh ya ware idanu wanda suke
ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda
aka ɗauke wa In-inar ya ce. "Saif-wazir" kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin
mamaki.
Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin "Waye zai ɗaukar maka
matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa Rugar Bello" a fili
Saif-wazir ya ce "Tab..." Domin yasan that's the first thing da Sheikh can't do it
ba zai taɓa ɗaukan ta ba. A hankali Saif-wazir ya sunkuya zuwa inda take kwance
zuciyarsa ta buga da ƙarfi lokacin da idanun shi ya sauka akanta. A ruɗe ya juya ya
kalli Sheikh Aliyu haydar Aliyu wanda ya tattare Alkyabbar jikinsa idanun shi rufe
lokaci guda jijiyoyin kansa suka fito hakan kuma tabbaci ne na zuciyar shi na kusa,
tashin hankalin da Saif-wazir ya shiga lokacin da idanun shi ya sauka akan fuskar
Halisa Danejo Rome yafi ƙarfin tashin hankalin da Sheikh Aliyu haydar Aliyu yaji
akan batun auren nashi da suke ƙoƙarin ƙaƙaba mishi. Saif-wazir ya daidaita
nutsuwarsa wani kuzari na zuwar masa mmkin abin da idanun shi ke nuna masa ya cika
masa zuciya. Ɗaukan ta ya yi daidai lokacin da Sheikh ya runtse idanunsa yana juya
baya da ɗan sauri bakinsa ɗauke da sunan Allah. Saif-wazir na gaba ɗauke da Danejo
Sheikh Aliyu haydar Aliyu na binsa cikin nutsuwa da daddako haɗi da kamala yanayin
yadda ya kame kansa yake tafiya zaka ɗauka sarki ko Hakimi ne. Gaba ɗaya ƴan
Fulanin suka mara musu baya har zuwa Rugar Bello lokacin tuni saƙo ya isa wajan
Arɗo gaba ɗaya sun fito tare da yin shimfiɗa a gaban wata bukka wacce ta cika da
yalwar inuwa, tun daga nesa Arɗo ke kallon Sheikh Aliyu har cikin ransa bai na'am
cewa zai aikata abin da Giɗaɗo ya faɗa ba, amma ya kasa fahimtar mene ya sanya yaji
auren shi ne mafita a gare shi dama su baki ɗaya?. Saif-wazir na zuwa ya kwantar da
Danejo wacce har lokacin bata farka daga suman da take ba, jini kuma bai daina zuba
daga goshinta ba. Arɗo ya kalli Sheikh cikin mutumtaka ya ce "Ka zauna mana?" Ko
inda yake Sheikh bai kalla ba balle ya ama shi, sai ma tsaiwa daya gyara yana ɗan
duba time fuskar shi tai jajir. Arɗo ya jinjina kai yana ƙara samun ƙarfin gwiwar
abin da zuciyar shi ke ayyana mishi. Cikin nutsuwa ya ce "Sannunku, an kawo ƙarar
an kama wancan yana ƙoƙarin aikata abin da Rugar Bello ta hana, wasu sunce ya
aikata ga yarinyar nan kwance, bisa doka duk wanda ya yi hakan muna ɗaura masa aure
da ɗiyar wannan ya sanya zamu aura masa yarinyar nan a yanzu ba tare da ɓata lokaci
ba" Sheikh dai jin abin yake kamar ta tsuniyar yara ko damuwa bai ba, auren Zahrah
ba bai taɓa damunsa ba balle na wannan ƴar tayin yarinyar. Saif-wazir ya ce "Amma
wannan kuskure ne, idan mutum baya so ba, kuma ai ba haka ake ɗaukan doka ba,
shigowarmu garin kenan fa suka fara ihun ya yi me ne kamar wasu marasa ilimi?"
Giɗaɗo ya ɗaga sanda zai makawa Saif-wazir Arɗo ya yi saurin cewa "A'a Giɗaɗo, ko
ma dai yaya ne kuyi haƙuri aure babu fashi" Modibbo da tun ɗazo bai magana ba ya ce
"Sai a karɓi sadaki wajansa ai babu lokaci" Labo ya ce "Ga wannan a wajansa muka
amsa" ya miƙawa Modibbo zoben gold ɗin da suka amsa wajan Sheikh. Sai a lokacin
Saif-wazir ya ƙara cewa "Ga kuɗi a bada zoben, yana da tsada sosai kuma yana da
muhimmanci ga mai shi" Modibbo ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Daman abu mai daraja
muke buƙata ai" abu kamar wasa akan idanun Saif-wazir da kunan Sheikh aka ɗaurawa
Sheikh Aliyu haydar Aliyu aure da Halisa Danejo Rome akan sadakin zoben gold.
Modibbo ya zama waliyin Danejo Arɗo ya zama waliyin Sheikh. Mutane kusan ashirin
suka shaida daga ciki harda Saif-wazir.
Shiru wajan ya ɗauka Saif-wazir ya rasa ta ya ya zai kalli idanun Sheikh ya ce da
gaske Danejo matarsa ce? Zai amince da auren ne ko ya ya? Kamar gilmawar walƙiya
haka Sheikh ya juya yana gyara Alkyabbar jikinsa kai tsaye baki n titi kuma ya
nufa,ganin haka ya sanya Saif-wazir miƙewa da sauri Arɗo ya ce "Ina zaka baka ɗauki
yarinyar ba?" Saif ya juya ya kalleta rauni ya bayyana a fuskar shi har baya son
kallon yarinyar gani yake kamar idanunsa ke masa gizau da abin da yake gani ɗin. Da
sauri ya ɗauke ta ya marawa Sheikh baya yana zuwa titi ya samu Sheikh zaune acikin
mota ya dafe kansa da hannu bibbiyu hayaniyar duk ta sauya masa lissafi baki ɗaya,
Saif na shirin saka Danejo cikin motar Sheikh ya ce "N...n.. No!!!!" Ya faɗa cikin
tsawa da faɗa idanunsa na fitowa waje sosai da kyau, a tsorace ya ce "Jini na zuba
a jikinta kada ta samu ƙarewar jini kuma ba zamu je da ita gida haka ba sai mun
fara zuwa asibiti" kallon da Sheikh ya yi masa ya sanya Saif yin shiru yana ƙasa da
ƙansa. "Please Yaa Lee Matarka...." Kafin Saif ya ƙarasa Sheikh ya yi wa motar key
cikin wani irin azababban gudu ya juya kan motar tare da cillata titi ya nufi
hanyar da zata mayar da shi Kano ba tare daya ƙarawa wajan Zahrah ba..
Baki Saif ya saka cike da mmkin zafin zuciya irin ta Sheikh Aliyu da alama za a sha
fama kafin Sheikh ɗin ya amince da batun auren Danejo ɗin. Mota ya tsayar ya ce
masa asibiti mafi kusa don Allah. Kai tsaye aka kai shi Specialist Yola dake
Jimeta. Yana shiga reception yaci karo da wata cikin sauri ya ce "Oh sorry it was a
mistake.." Tsaki ta ja ta ce "mistake ko rashin hankali Malam? Kana tafiya kai a
sama" kallonta kawai ya yi shi bashi da lokacin ta ma, Saurayina ta ce "Banza
kawai" Zahrah da hankalinta ya yi gida sbd zuwan wanda yake shirin zama mijinta ta
ce "Wai Surayyerh har lokacin cacar baki gareki ne? Tunda muka zo asibitin nan ki
ke neman faɗa" Surayyerh ta ɗaga hannu ta ce "Saurara Zahrah ke tunda kika samu
cikin nan kike ji da masifa, daidai nake da ko wanne ɗan iska Wallahi" Saif-wazir
ya kalli Zahrah da kyau kaya ne wanda suka kama jikinta sosai hannunta duk farce
taci gashin doki, juyawa ya yi ya kalli Surayyerh ba tare ce komai ba ya juya zuwa
cikin emergency. Kai tsaye aka bawa Danejo gado Dr ya kalli Saif-wazir ya ce
"Suna?" Saif ya shafa kansa sbd sam bai sani ba sai kawai ya wayance da faɗin "Dr
ka fara yi mata taimakon gaggawa, sai mu yi magana" Dr ya ce "Dole a buɗe mata file
ai" "I knw, amma kulawa da ita ba zai hana buɗe file ba, a duba ta first buɗe file
second" Dr ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakin da suka kwantar da Danejo abun mamaki
ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito sukaci karo da Saif-wazir ya ce "Yarinyar
nan ta gudu bata cikin room ɗin?" Saif ya ce "What?" Da sauri ya juya zuwa waje
amma neman duniya babu Halisa Danejo Rome babu ko inuwarta "Innalillahi yau na
shiga uku ko dai aljana ce yarinyar nan? Amma babban asibitin irin wannan ina
zata?" Ganin bashi da wata mafita ya nemi abin hawa wanda zai dawo da shi Kano
domin ba zai iya komawa Rugar Bello ba yace bai ga yarinyar ba, haka kurum su kashe
sa a banza.

Ɓangaren Halisa ana kwantar da ita a saman gado A.c ta fara ratsa ta, ta farka da
sauri tana dabe kanta, tsoro ya kamata tana mamakin yaushe tazo. Ita dai ta fito
tallan Kindirmo ta ce bari ta biya ta Rugar Bello a hanya yunwa da jiri suka yarda
ita, kanta ya daki wani dutse bata ƙara sanin inda take ba. Miƙewa tsaye tayi
jikinta na rawa ta ce "Hande en boni gidan cire kai aka kawo ni wayyo Allah Dadata
na lalashe, lalashewa ta sameni" kuka take sosai har da majina fuskarta tai jaa.
Leƙewa tayi ta window taga ashe bayan asibitin ne, da sauri ta kama tagar ta dira
baya duk da zafin da kanta ke mata amma haka ta dinga gudu kamar barewa a haka ta
isa Rugar Rome. Shiri sosai Zahrah tayi ta tarbar Sheikh amma har dare babu
labarinsa baƙin cikin duniya duk ya kamata ga ƙawayenta duk ta tara zata nuna musu
haɗaɗɗan mijin da zata aura amma ya kwafsa mata.

Misalin 10:23 Abba Hakimi na zaune a Main parlour dashi da Momi kamar daga sama su
kaga Sheikh ya shigo hannunsa guda ɗaya dafe da kansa, Momi zatai magana Abba
Hakimi ya Girgiza mata kai alamar tai shiru,babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa
dake gidan, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan jikinsa abin da bai taɓa
yi ba shi ne, amfani da ruwan sanyi ya tsaya a shower na sauka akansa sanyi na
ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa dan kansa ya kashe shower ɗin
ya naɗe jikinsa a cikin wata bathroom mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd
azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke sa.

"Lafiyar Sheikh ɗaya kuwa?" Abba Hakimi ya ce "Kinga alamar bai da lafiya ne?" Momi
ta ce "A'a, kawai yadda na shigo gidan ne" Apple ɗin hannunta da take miƙa masa ya
amsa ya ce "Kada ki damu, duk sanda ya yi haka alheri ne ke bibiyarsa" tattaunawa
sukai akan gobe za a kai kayan lefen na Sheikh ita ma zata a hankali ya ce "Allah
ya kaimu" sai kusan 12 na dare Sannan Saif-wazir ya shigo ganin dare ya yi kai
tsaye ya nufi part ɗinsa, motar Sheikh da ya gani ya bashi tabbacin ya dawo gida.
Da batun Auren Sheikh ya kwana yana tunanin ya faɗawa Abba Hakimi ko ya yi shiru?
Har barci ya ɗauke shi ba samu mafita ba.

Washegari da yamma wajan 5. Dr A'isha ta zabga tagumi Yaya Halima ta ce "Dr wai
lafiya tun da muka dawo kike wata kala?" Dr A'isha ta ce "Wallahi Yaya tausayin
Sheikh nake, ina zai kai wannan uwar matar? Na girgiza ban san rashin tarbiyyar ta
ya kai haka ba, kalli da ita aka amshi kayan lefen fa?" Yaya Halima ta kalli Dr
A'isha tana mmkin rashin control na bakinta da bata iya riƙe zance. "Kowa da
tsarinsa fa Dr Allah dai ya sanya albarka" daga bakin ƙofa akace "Ba Amin ba, mugun
ji da mugun gani ruɓaɓɓan baki ya kau daga kan Gadanga, yau ko ni ko uban Gadanga
ya zaɓa" gaba ɗaya suka kalli bakin ƙofa, tana tsaye taci lace ɗauri har gaban
goshi ta lafta uban Glasses a fuska wanda ya cinye rabin fuska. Cikin farin ciki
Mother ta miƙe tsaye tana faɗin "Jadda" haɗe fuska tayi ta nemi waje ta zauna,
Uncle Haroon ya shigo hannunsa riƙe da torelly ɗin Jadda ya zauna kusa da ita.
Cikin farin ciki Mother ta ƙara cewa "Sannu da hanya Jadda ashe kina tafe" Jadda ta
ɗauke kai sai da Mother tabar wajan, ta juya ta kalli Uncle Haroon murya can ƙasa
ta ce. "Munafuka Algunguma duk masifa da yaƙin da ake a gidan fa bata sanar dani
ba, shi ya sa na haɗe mata fuska na kame kai na, ba kaga jikinta ya yi sanyi ba, ai
wlh yau sai sun bala'i ya sauka" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi ta haɗe rai tana
ƙanƙantar da idanu ta ce "Kaji masifa ko? Ba murmushi za kai ba cewa zakai nayi
daidai" ya ƙara murmushi ya ce "Jadda duk abin da ki kai ai daidai ne" cikin
ƙaramin lokaci Mother ta cika gaban Jadda da kaya kala-kala, Yaya Halima da Dr
A'isha suka gaidata ta amsa a ciki. "Kinga ba kwaɗayi ya kawo ni ba, maza kira mini
mijin naki" Mother ta haura sama yana zaune yana duba Invitation ɗin bikin Sheikh
dana Zahrah Mother ta shiga a hankali ya ce "Barrister ya dai?" Kai tsaye ta ce
"Jadda na kira" tana faɗin hakan ta juya, yabi bayanta da kallo da sauri kuma ya
miƙe shima. A hankali yake sakkowa daga benen yana sakin fuska bayan ya zauna ya ce
"Sannu da zuwa Jadda" banza Jadda tayi masa, ta zare Glasses ɗin idanunta ta miƙawa
Uncle Haroon, ta cire mayafi shima ta miƙawa Uncle Haroon, fuskar Father cike da
tsoro ya ce "Jadda lafiya me kike shirin yi haka?" Bata kula shi ba, ta buɗe
rigarta tana nunawa father ta ce "mene wannan?" Kansa a ƙasa ya kasa cewa komai ta
ce "Idan ba zaka iya ba, ai Ubangiji ya tsaga mini bakin magana nonon dana shayar
da kai ne, kasan Allah tun nonon yana kwance ka lalata batun auren Gadanga da
wannan gantalalliyar yarinyar, idan ba haka ba zan ɗaga maka nonon sama ka lalace
kaje duk inda zaka...


*Not edited*
Masu tambayar yadda zasu biya kuɗin IDAN BA KE. Book 1, 2 ne. Mutum zai biya ₦500
har a gama littafin baki ɗaya. 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity

Please Login or Register in order to submit comment