You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah" domin gabaɗaya ya manta
Zahrah na bayan motar, ya zame Halisa daga jikinsa tare da duba yadda ya yaga mata
riga sai duk kunyar Zahrah ta kama shi domin kamar cin fuska ne, ya ɗan buɗe ido
irin Kinga abinda ki ka ja ko? A zahiri kuma ya kame fuska yana riƙe kan shi, yadda
Halisa ke jin rikici da rigima yasa sam bai tankata ba, sai kuka take mara sauti.
Tana nan jikinsa yana ƙare shigar da ita jikinsa da hannuna ya yiwa motar key tare
da nufar gate, wanda tuni gatekeeper ya buɗe masa, ya cilla motar kan titi kai
tsaye ya nufi unguwar da haɗaɗɗan gidansa yake.
Cikin nutsuwa da ƙwarewa haɗi da tsantsar kamala Yaa Sheikh yake driving motar
idanunsa akan titi, yadda hawayenta ke jiƙa masa shaddar jikinsa da ƙirjinsa yasa
time to time kawai yake girgiza kai tare da fesar da Iska.
He don't know how sad she's, bai kyauta ba, bai kyauta ba, ko wacce nada burin
tasan halin da mijinta ke ciki, tana son ta zama guda ɗaya tilo daga ita sai
yaranta wajan mijinta, ya sani ya yi kuskure irin babba ɗin nan, Ita ɗin yarinya ce
amma a karo na farko ya rasa kalmomin da zai mata bayani dan gane da kishiyar da
akai mata rana tsaka.
Zahrah tunda tayi ƙasa da kanta bata ɗago ba, sbd abinda ya zo ya tsaya mata a
maƙoshi yaƙi tafiya, ƙirjinta ya yi nauyi, suna mota ɗaya ace har Yaa Sheikh ya
mance da ita? Ko da ba matarsa bace ita, yana da kyau ya yi mata kara ya daina nuna
maitar buƙatar matarsa akan Idanunta me hakan ke nufi? Wata zuciyar ta ce
"Alfarma akai miki Zahrah, kada ki zaƙe" ta girgiza kai ɗayar zuciyar ta ce mata
"To Amma yanzu ai ke ɗin matarsa ce, kina da hakƙi akan shi ba zaki iya zuba idanu
ba, dole ki tashi tsaye"
Baya san sun ƙarasu gidan ba, sai taji ya yi parking a parking lot na gidan shi,
tare da danna horn Sannan ta dawo daga hayyacinta.
Ta buɗe idanu tana kallon mazaunin da yake kai riƙe da Matar Malam, ta buɗe ƙofa
tare da fitowa tazo daidai Glasses ɗin tare da yin knocking, slowly ya sauke
Glasses ɗin motar, ganinsa tayi jingine da kujerar motar ya ɗan lumshe idanunsa
kamar mai jin barci.
Ya ware idanun tare da zuba mata su kaɗan alamar "Ya akai?"
Ta ce "Am looking for my sister, naga kamar tayi barci ma" Ya jinjina mata kai,
nauyinta ya kama shi sbd Halisa dake kwance a ƙirjinsa, ji ya yi tayi shiru hakan
yasa ya kalleta, hannunsa dake cikin rigar Halisa take bi da kallo, ya kame fuska
yana janye hannunsa daga ƙirjin na Halisa.
Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Is she okay?"
Ya dai yi mata shiru yana kallon yadda haske ya ƙawata harabar gidan nasa tamkar
rana, ji ya yi tana kiran sunan Halisa tare da ɗan bubbuga hannunta. "Wake up
Sister, we're at home"
"Kije, zan tashe ta"
Ya faɗa not looking at her, tayi kamar bai dameta ba ta ce
"Ok Sweetheart, catch your life" tana faɗin haka ta nufi ƙofar da zata kaita asalin
cikin gidan wanda yake ɗauke da Main parlour.
Halisa daman akwai gajiya tare da ita, ga zafin da zuciyarta ke mata, ga kewar
mijinta da gangar Jikinta take, suna fara tafiya kuma Yaa Sheikh ya fara hura mata
iska a fuska da kunne, tare da zura hannunsa cikin rigarta yana shafa cikinta wanda
yake jinsa har zuciyarsa, daga nan kuma ya haura da hannun dama wannan dalilin yasa
tun kafin su yi nisa barci ya ɗauketa.
Ya zareta daga jikinsa yana kallon yadda ta ɓata fuska ko a cikin barci, ya faɗaɗa
fuskarsa yana ƙara jinjinawa rigimarta, fitowa ya yi da ita a jininsa bayan ya rufe
ƙofar ya nufi cikin gidan, suna zuwa bakin ƙofar parlour Halisa ta ce
"Sauke ni" daman ba barci take ba she was pretend kamar barci take ko mene, bai ja
batun da tsayi ba ya sauketa, ta ce "Ina ne part ɗina?" Tayi maganar ko inda Yaa
Sheikh bata kalla ba, sbd raɗaɗi da baƙin da zuciyarta ke mata, yau ita zatai
sharing mijinta da wata banza? wacce bata da tabbacin ko lafiya lou take bata da
H.I.V ba.
Da hannu ya nuna mata part ɗin dake dama, wanda ƙofar take a rufe, ta juya ta nufi
wajan taji ya kaɗa mata key a hankali ya ce "The key"
Ba yabo ba fallasa ta amshi key ɗin ta buɗe ƙofar part ɗin, tana shiga ta murza
mata key tare da zubewa a baƙin ƙofar tana sakin wani irin kuka mai cin rai.
Zahrah tayi wani irin murmushi tare da takawa cike da gwalli ta ƙarasu wajan Yaa
Sheikh ta ce "Lafiya lou take kowa?" Tayi maganar tana ƙoƙarin rungome shi da
tafiyarsa ta ƙasaita ya matsa yana haurawa saman bene ya ce
"Laá adari" ta bisa da idanu ta ce "Ka duba ta mana, bana son damuwa" ya tsaya cak
yana kallon Zahrah daga upstairs ɗin bai magana ba, sai jinjina mata kai kawai da
ya yi.
Ta dubi haɗaɗɗan parlourn wanda gabaɗaya Yaa Sheikh shine ya zuba komai dake
parlourn, milk and Brown colours ta buɗe part ɗinta ta shiga, parlour ta fara cin
karo da shi, shi ma ya haɗu sosai daga nan kuma sai bedroom , bathroom da kitchen
duk akwai a part ɗin kowa, sharp-sharp tayi wanka ta shirya cikin wata nightgown, a
hankali ta dubi ƙirjinta koda ta haifi Muhammad ƙirjin bai yi cikar da ake tunani
ba, shi yasa batai wasting time na shayar da shi ba, sunan tana shan magani amma
har yanzu bata sauya zani ba, ta ɗauki wata bra mai tudu ta saka ƙirjin ya tashi
kaɗan ta fesa perfume ta saka slippers tare da fitowa ta haura upstairs part ɗin
Yaa Sheikh. Tayi tsaye bakin ƙofar tana riƙe handle ita burinta yau bai shige ta
kwanta da Yaa Sheikh, har mafarkin wannan rana take ranar yau kuma ta kasance
ranarta domin ita ce amarya.
Ta murɗa handle ɗin tare da shiga, wani ƙamshin ya ratsa hancinta ta rufe idanu a
hankali ta ce
"My sweetheart ɗan gayu I love you Beb" baya parlourn dan haka ta shige cikin
bedroom ɗin da taga ƙofar a buɗe, kai tsaye ba tare da sallama ba ta shiga yana
zaune saman doguwar kujerar dake kusa da bed ɗin shi, ya ɗora ƙafarsa saman table
hannunsa riƙe da gorar ruwa yana tsiyayawa cikin glasses, jikinsa na zubar da ruwa
alamar bai jima da fitowa daga shower ba.
Ta dinga binsa da kallo, domin wannan shi ne lokaci na farko data ganshi sanye da
wata milk armless mai buɗaɗɗen ƙirji, sumar ƙirjinsa luf ɗauke da danshi ruwa, haka
gemunsa, ta kalli farar dogwayen ƙafarsa har zuwa cinyarsa, ko'ina na jikinsa
kwance da gargasa, shekaruna suka ɓoye sai samartakar shi data bayyana, nutsuwa da
kamewar shi a fili.
"Ba a shigo mini ba sallama" ta dawo daga kallon maitar da take masa ta ce "Oh My
bad, I screwed up"
Ya yi mata uzurin domin babu mamaki bata saba ba, ko wanne tsuntsu kukan gidansu
yake, wani abun baya blaming nata, a haka a reneta.
Bai ce mata komai ba harta nemi waje kusa da shi ta zauna tana cewa
"Thank you" Ya ɗaga kai ya kalleta alamar ƙarin bayani ta ce "Yau zan kwana tare
dakai, mafarkina zai zama gaskiya, naji daɗi yau Halisa zata bar min kai, we'll
spend the night together zamu raya First night ɗinmu" ita kaɗai take magana bai ce
komai ba, ta zame ta ɗora kanta a ƙirjinsa ta rungome shi ta ce.
"I love You to the rest of my life.....,"
"Tea" ya katse da faɗin haka, ta ce "Tea kuma?" Ya jinjina kai ya ce "Ban son suger
sosai, ki saka honey" gabanta ya faɗi ita kam ai batai zaton haka ba, she don't
know how to make tea, ita kunna gas na bata wani iya sosai ba ta ce
"Sweetheart tea yanzu? Why not safiya" ya duba time yaga kusan 11 na dare ya zareta
daga jikinsa yana miƙewa tsaye ya ce "Good night"
Da mamaki ta ce "Night? But I want to sleep on your arms Beb" ya kama hannunta har
zuwa baƙin ƙofa murya can ƙasa ya ce "We'll talk tomorrow In sha Allah" hawaye ya
cika a Idanunta gashi ta shanye maganin da aka haɗa mata tass ta shirya amsar
mijinta da hannu bibbiyu, a sanyaye ta ce
"Ban taɓa ganin aure haka ba, at least mu kwana tare koda babu komai tsakani, daman
nasan alfarma kayi mini ba so na kake ba, ka tasauyawa halin da nake ciki da bana
son ka ba zan nace ka aureni ba" ta saki kukan makircin tana riƙe ƙirjinta ta soma
tari tayi kamar ciwonta zai ta shi. "Stop Zahrah"
Ta tsaya tana kallonsa ya harɗe hannayensa a ƙirji yana binta da kallo da kayan
data saka, bashi da wani feelings ko kaɗan a kanta, amma ya san hakƙinta ne kuma
dole Allah zai tambaye shi. Kamar an tilasta masa ya yi magana ya ƙasa da murya ya
ce
"Me ki ke so?" Da sauri ta ce "You" Ya rufe ido ya buɗe in a romantic style ya ce
"Gani" kambala'i yana nufin bai fahimta ba? Ko yaya ne? Wasu hawayen ya taro cikin
Idanunta tayi murmushi ta ce "Good night"
Zata juya ya kama hannunta sbd shi har ranshi tausayinta yake ji, musamman idan ya
tuna watanni biyar suka rage mata a duniya sbd ciwon Cancer babba abune da yake
kisa cikin lokaci ƙanƙani, ya ɗan rungometa ta gefe murya ƙasa ya ce "Am not in the
mood" kamar jira take ta rungome shi sosai tana sakin kuka wanda duk rabi na kissa
ne, ta fahimci hankalinsa baya tare da ita, kamar yadda ta sani haka ne domin
gabaɗaya tunaninsa yana ga Matar Malam da kuma halin da take ciki, yana son zuwa ya
kwantar da rikicin ta tun kafin safiya tayi ta rikice masa ya kasa fahimta..
"Don Allah sweetheart yau ɗaya, yau kawai ka barni na kwanta tare da kai don..."
Sai ta fara tari tana riƙe ƙirjinta tare da ɗauke numfashinta.
Yaa Sheikh ya riƙeta tare da janta gefen gado ya kwantar ya ce
"Clam down, it's okay" ta jinjina kai tana kallonsa ya ja mata duvet yana miƙewa ta
ce "Ina zaka?" Ya nuna mata ƙofa alamar rufewa zai, ƙofar yaje ya rufe, abu biyu
sukai haɗe masa, idan bai sha tea ba sam baya jin daɗin, ga tunaninsa yana ga
matarsa da cikinsa dake Jikinta.
Zahrah kallon sumar kansa kawai take yadda ta kwanta har wuya, gashi ta rabo gida
biyu, six packs ɗinsa a murɗe full options. A jikinsa yaji kallonsa take kuma shi
ɗin take jira, ya kashe hasken bedroom ɗin ya dawo ya zauna bakin gado yana jingina
da frame, yana kwanciya ta dawo kusa da shi tare da ɗora kanta a ƙirjinsa ta ce
"Ina son ƙare rayuwata dakai, amma na kusa barin duniyar nan ko yanzu na mutu don
Allah kada ka bawa kowa Muhammad ka riƙe shi na bar maka har abada, burina yanzu
bai huce na samu farin ciki tare dakai na tsayin lokacin da suka rage mini a
duniya" ya saka hannu ya rufe bakin tare da faɗin "Shhhha"
Yana zaune har barci ya ɗauketa tana shafa lips ɗinsa da take jin kamar tayi
kissing amma ya kame fuska babu dama, gently ya zame jikinsa daga nata tare da
miƙewa ya buɗe wani bedroom, haɗaɗɗene sosai a ciki kuma harda bene wanda zai mayar
dakai downstairs.
A nutse yake taka strais ɗin har ya sauka, ya nufi wata ƙofa tare da saka key ya
buɗe, shiru bedroom ɗin sai ƙarar karatun Alkur'ani dake tashi da kuma sanyin a.cn
dake ratsa ko'ina, ya duba saman bed ya ga bata kai, harya juya zuwa bathroom ya
hangota kwance saman prayer mat ta cure waje guda, ya durƙosa ya saka hannu tare da
ɗaukanta bakiɗaya ya cire hijabin har lokacin kayan da tazo dasu ne a Jikinta ko
wanka ba tayi, Jikinta zafi zau alamar zazzaɓi ne ke damunta, ya zauna da ita a
jininsa ya shiga ƙarasa zame raguwar kayan ya rage daga bra sai under wear a
Jikinta, sai kuma cikinta daya fara girma tare da nuna kansa a fili, ya saka hannu
ya shafa cikin yana ƙara shigar da ita jikinsa da kyau, idanunsa rufe da suka fara
rikicewa ƙamshin turaren Jikinta na rikita shi ga wani laushi da tsantsi da fatar
jikin nata ta ƙara, Ɗumin da Halisa daji na shigar ta ya sanya ta ƙara shigewa
jikinsa ta luff tana narke fuska cikin magagin barci ta ce
"Zan mutu Abbana, ka gujeni ka zaɓi wata, You left me"
Ya ɗora fuskarsa a tata yana goga mata tsinin hancinsa a hankali ya yi kissing lips
ɗinta with all his heart ya ce "Bbyn Abba, Zawja rigima"
Kamar tana jinsa ta tura baki tana ƙara shige masa da kyau, hakan ya ƙara rikita
Yaa Sheikh ya kame bakinta ya shiga kissing cikin zafin nawa da kewa, tayi saurin
buɗe ido sbd juyawar da abin cikinta ya yi ya daki mararta nan da nan fitsari ya
taso mata, kallonsa kawai tayi tare da zare Jikinta ta nufi bathroom, tunda ta
shiga bata fito ba har barci ya fara ɗaukan shi.
Da Subhi Zahrah ta farka ta shafa taji babu Yaa Sheikh, ƙirjinta ya harba ta miƙe
da sauri tana tashi taga ya buɗe ƙofa ya shigo jikinsa kayan jiya ne, amma kamar
wanka ya yi gabaɗaya sumar kansa ta kwanta tana zubar da ruwa, bai bari ta kalli
cikin idanunsa ba ya shige bathroom ɗin shi, Alwala ya ɗaura tunda ya riga da ya yi
wankan da bai niyya ba, ya fito ya ganta tsaye bai ce komai ba, ya shirya cikin ash
ɗin Jallabiya mai kyau ya nufi masjid, Zahrah ta koma tare da kwanciya ta ci-gaba
da barci.
Da ƙyar Halisa tayi sallah sbd ciwon da Jikinta yake, da gajiyar da Abbanta ya tara
mata, sai jiya ta ƙara tabbatarwa Yaa Sheikh namiji ne bai nuni tausayi ko ɗaya a
gareta ba, sai daya fanshe gabaɗaya kewar daya ɗauka, duka abinda ya tara a jikinsa
sai daya juye mata shi, da ƙyar ta samu kanta, ta miƙe da ga kan prayer mat ta nufi
kitchen ta kunna gas ta shiga haɗa tea ta yanka albasa da Attahiru, bayan ta
kammala dafa tea ɗin da yaji kayan ƙamshi domin komai an zuba mata a kitchen
musamman kayan ƙamshi, ta soya lafiyayyan ƙwai da yaji albasa. Ta juye tea ɗin a
mug mai ɗan girma ta zuba soyayyan egg ɗin a plate mai faɗi.
Kasancewar ya gaji kuma yunwa yake ji sosai yasa 6 daidai ya dawo gidan, mmki ya
ƙara kama shi ganin Zahrah kwance ya nufeta yana bubbuga pillow ta buɗe ido ta ce
"Sweetheart" a taƙaice ya ce "Kinyi sallah?" Ta ce "What's the time? 10 ya yi" ya
buɗe baki ya ce "10? To tashi ki koma part naki idan yyi kiyi sallah" kafin tayi
magana yaji ƙamshin Matar Malam ya kawo masa ziyara, yana daga tsaye ya juya suka
haɗa idanu sai yaga ta sakar masa murmushi fararan haƙoranta a bayyane, Zahrah dake
kan bed ta kalli Halisa batai tunani zata kula Yaa Sheikh a yanzu ba, Halisa ta
ajjiye tray ɗin hannunta ta zuba ƙamshin turare daga ita sai wata riga ƙarama sai
wando three gaiter cinyoyinta duk a waje ta ɗaure kanta da ribbon, tana zuwa ta
rungome Yaa Sheikh tare da yin tsayin ƙafa shi kuma ya riƙe ƙugunta, ta sumbaci
cheeks ɗinsa both sides, Idanunta cikin nasa ta ɗora bakinta a nasa tayi kissing ta
ce "Sabahul khair ‫"حبيبة قلبي‬
Halisa ta juya ta kalli Zahrah da tayi tsaye ciki da mmkin makircin yarinyar ta ce
"Ke bakisan yau rana ta bace?" Halisa marairaccen fuska ta ce "Sorry Anty Zahrah,
Abbana yunwa yake ji ba zan iya barinsa haka" Ta saka hannu taja gemun Yaa Sheikh
daya kasa cewa komai har lokacin hannunsa yana riƙe da ƙugunta ta ɗan bugi ƙirjinsa
ta ce "Abbana shi ne da muna wanka ɗazo a bathroom na ka gudu ko? Bayan ko rama
cizon da kayi mini a breast ɗina ban yi ba.....[2/1, 10:38 AM] Abk: Gabaɗaya Idanun
Zahrah ya rufe sbd tashin hankali, ta ƙara buɗe idanunta akan Yaa Sheikh da yaƙi
yarda ya kalleta cikin damuwa taja tsaki tare da juyawa tabar ɗakin ko gabanta bata
gani ta riƙe ƙirjinta dake mata zafi. Tana fita daga bedroom ɗin Halisa ta zame
jikinta daga na Yaa Sheikh tana haɗe fuska tare da yin kicin-kicin da ranta kamar
ba ita ta gama kissa da kisisina ba.
Ganin zata juya ya riƙo hannunta yana dawo da ita cikin murya mai sanyi ya ce "Baki
isa ba"
"Kana jin yunwa, kuma aikina ne banda haka babu abinda zan zo nayi" ta faɗa tana
ɗauke fuskarta dake tafin hannunsa, ya zame tare da zama saman kujera idanunsa
lumshe sbd gabaɗaya ta gama kashe masa jiki garin kurar wata daga bedroom ɗin.
Ganin da gaske barin ɗakin za tayi ya sanya Yaa Sheikh haɗe yatsun hannunsa suka
bada sauti fuska kame ya ce
"Don't leave Haliyserh Sheikh Aliyu haydar Aliyu" muryarsa babu wasa cikinta, ya
kuma kame alamun umarni yake bata ba shawara yake nema ba.
Ta dawo tare da zubewa a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta saki wani irin raunataccen kuka,
bai ce mata komai ba domin tana buƙatar kukan har zuciyarta tayi sanyi cikin kuka
ta ce
"Modibbo ya kake so nayi? Kasan yadda naji dana zo naga Anty Zahrah kwance a
gadonka, sabon gadon da ko zama banyi akai ba amma har matarka ta kwanta kenan a
jikinka ta kwanta tayi barci"
Ya harɗe hannu a ƙirji tare da buɗe ido yana kallon yadda take rigima da rikici
wanda zallar kishi ne ya haifar da su.
Ta miƙe tsaye, tare da cire rigar Jikinta, ya rage sai bra a Jikinta, tana kuka
sosai ta ƙara cire three gaiter ɗin Jikinta nan ma ya rage daga ita sai white lace
pat.
Tuni idanun Yaa Sheikh ya jirkice ya juye tare da yin ja, wani abu na fisgar shi
bai taɓa ganinta zahiri a cikin haske ba sai yau. Duk inda yaso yake cilla idanunsa
ya kalla a jikin nata, a ransa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake.
Halisa ta juya ta ƙara juyawa ta ce
"Ka faɗa mini wacce halitta ce a jigina bata cika ba har kaje ka auri raguwar wasu?
Ka faɗa mini dame ta fini har ka aureta ba tare da sani na ba sbd bani da
muhimmanci a wajanka, why Abba why me ya sa kasan zafi da raɗaɗin da nake ji a
raina kasan yadda kishinki ke barazanar ɗauke rayuwata?" Bata duba cikin Jikinta ba
ta durƙoshe a wajanta tana kuka sosai ta ƙara cewa
"Ka mayar dani wajan Ummul ni ba zan zauna dakai ba, ba zan iya sharing mijina da
wata ba" Ya wani irin kyakkyawan murmushi Yaa Sheikh ya yi wanda ya fidda fararan
haƙoransa gently ya miƙe tsaye tare da ƙara sawa inda take ya ce.
"Stand up" tayi shiru tana shassheƙar kuka, ya saka hannu ya ɗagota tsaye yana
janta zuwa bakin gadon shi ya zauna, tare da zaunar da ita saman cinyarsa ta saka
hannu zata ɗauki riga ta saka ya kame hannunsa bakinsa a kunnanta ya ce.
"Kinyi kaɗan" ta ƙara ɓata fuska ta ce "Ka sakeni, ai baka marmarin jikina kana da
wanda ya fishi, bani rigata" shi dai bai ce komai ba ya rungumeta ta baya yana
shafa cikinta ta ce
"Abba me ya sa" a taushashe ya ce "Ƙaddara Zawja, ban son rigima" ta juya ta kalle
shi ta ce "Au rigima? Wannan abin ka ɗauka matsayin rigima Yaa Sheikh?" Ya dubi
cikin idanunta ya numfasa ya ce "Ko wanne bawa yana da zanan ƙaddarar shi a bangon
littafin shi wanda aka bashi na tsayin rayuwa...," Ya yi jim yana ɗora kanta a
ƙirjinsa ya riƙe hannuwanta ya ce
"Yarda da ƙaddara shi ne cikar imani, kinsan zan aureki?" Ta girgiza masa kai ta ce
"Amma ina ganinka ai, a barci na" Ya yi murmushi mai kyau ya ce "To auren Zahrah a
farko ƙaddara ce, haka yanzu ma, Ubangiji ya umarci mu da auren mata sama da ɗaya
idan muna da hali da iko, ya ce idan ba zamuyi adalci ba mu auri ɗaya ita ce mafita
a garemu, ki duba suratul Nisâ'i 3 ayat zuwa 4 Hafizata"
Ta ce "Meyasa ka ɓoye mini? Meyasa kuma ka gudu ka barni? Meyasa kace ka divorce
paper nawa through bashi bane?" Ganin yana ta kallonta ya kasa cewa komai ta ce "I
understand,amma kasan ina sonka ko Yaa Sheikh?" Nan ma ya yi mata shiru, bisa dole
tayi shiru tasan idan ya yi haka akwai dalili, inma yanayin da yake ji yafi
ƙarfinsa,ko kuma abinda yake zuciyarsa yake son faɗa amma ya yi masa nauyi a
harshe.
Kamar daga sama taji ya ce "Ki bari na gwada miki banbanci a aikace, kin kurar mini
mata kinzo kina rikici sunan Breakfast aka kawo, Ya Allah ka dubi bawanka Aliyu" ta
tura baki gaba ta ce "to ina ruwana da matarka tazo ta zauna mana, ba wani kurarta
da nayi gulma ce kawai"
Ya haɗe fuska cikin nutsuwa da kulawa ya ce
"Zawja ki tayani yin adalci, yanzu ku biyu ne kowa ni yake buƙata kina da
muhimmanci a gareni ki yarda ƙaddara ce auren Zahrah, kin san idan kina haka
tsakani da Allah ni zaki jefa a wuta ya zaki dinga tsirara kina ƙulla mini sharri"
Ta kalle shi ganin da gaske kuma bai taɓa magana mai tsayin haka ba ta ce "Tom
Malam"
Yai mata shiru ta ce
"Tea ɗin fa?" Ya miƙa mata hannu ta ɗauki cup ta tsiyaya masa ta saka 2spoon na
honey kana ta bashi. Cikin nutsuwa yake sha har lokacin tana zaune akan ƙafafuwansa
ta ce "Malam ina da tambaya" ya jinjina mata kai ta ce "Wannan zumar meye
amfaninta?"
Da idanu ya kalleta bai mata amsa ba, ta saka hannu ta fara cin soyayyan egg ɗin,
harta manta da batun Zahrah domin ta samu Soyayyar mijinta, abu ɗaya ne ba zata iya
jure ganinsu waje guda ba, ta ciro wani zata kai bakin ya kama hannun tare da
turawa bakinsa yana ɗan yatsuna fuska, daga cin abinci Yaa Sheikh ya fara juye mata
duk da yana iya ƙoƙarin shi wajan ganin bai shiga hakƙin Zahrah ba amma sai ya yi
da gaske.
Ta miƙe tare da ɗaukan kayan rigarta cikin sauri tabar bedroom ɗin tana masa gwalo
ya bita da gajiyayyun Idanunsa. Ya jima a wajan kafin ya miƙe ya wanke bakinsa tas
ya nufi bed ɗin shi ya kwanta yana lumshe idanunsa, kwana biyu yana stressed kansa
da yawa jiya kuma da zai huta ya ƙarar da Lokacin shi wajan yin ibada da raya sunna
ta Manzon Allah. Zahrah tana shiga ɗakinta ta shiga safa da marwa kanta ya ɗaure ta
kira number Surry tana ɗagawa ta ce "Surry kina ina?" Ta ce "Gidan surukanki mana"
ta ce "Ina son ganinki yanzu pls" Surry ta ce "Rite away Maa" hanging up na kirar
sukai, bata tashi a wajan ba sai wajan 9 sbd ciwon da kanta yake mata sosai, tayi
wanka tare da Alwala sai a lokacin tayi sallar Subhi kana ta shirya cikin fitted
gown na atamfa Holand blue and white tayi mata kyau, duk abinda take bata jin daɗin
ranta, gudun kada zuciyarta ya buga da abin da bata shirya gani ba ta nemi waje ta
zauna tana chat a wayarta. 12:45 daidai ya shiga sakkowa daga upstairs ɗin sanye da
Ash ɗin shadda shampoo sai ɗaukan idanu take ya ɗora hula jaddara hannunsa a baya
nutsuwarsa ta bayyana shekarunsa a fili ya dinga bin main parlour ɗin da kallo jin
shiru ba motsin kowa sai ƙamshin dake fitowa ba tare da yasan daga ina bane.
Fita ya yi zuwa Masjid ɗin dake unguwar a lokacin kuma wata black ɗin mota ta shigo
gidan, bai bi takan motar ba ya shige abinsa, Dr A'isha da Surry suka dinga kallon
Yaa Sheikh har sai da Surry ta ce "Wannan kallon fa Dr" Dr A'isha ta ce "Na rasa
wanne kyau Yaa Lee ke da shi, Ummul nada kyau haka grandparents nasa, but shi ɗin
kamar ruwa biyu ne" Surry ta ce
"Kin san Fulani nada kyau amma ko? Kuma ita kanta Ummul banji asali bahaushiya ce,
ni nutsuwa da kwarjinin shi ke hanani nutsuwa idan yana waje" Dr A'isha ta rufe
idanu tana sauke nauyin ta ce "let's go in"
Fitowa suka yi tare da shiga ciki, gabaɗaya suka zauna a main parlour Surry ta
ɗauki wayarta ta shiga kiran number Zahrah tana ɗagawa ta ce "Ina parlour" ta
ajjiye wayar tana bin parlourn da kallo ko'ina birgeta yake, an narka dukiya wacce
baki ba zai taɓa iya faɗa ba.
Babu jimawa ta fito tana rangaji ganin Dr A'isha kuma yasa tayi turus sai kuma ta
zauna tana faɗin "Wlcm" Surry ta ce "Sannu Amaryar Yaa Sheikh, na ɗauka yau ai ba
zamu samu ganinki ba sbd soyayya"
Zahrah ta ce "Uhm wacce soyayya nayi kwanan baƙin ciki" Surry ta ce "Subuhanallah,
bar faɗa" ta ce "Bari kawai, can you imagine a gabana yarinyar nan ke rungome Yaa
Sheikh tana faɗin wai ya cije ta ji nayi zuciyata ta buga ƙirjina ya fara zafi"
Surry ta dinga dry tana riƙe ciki ta ce "What funny, bar raina Allura, ƙarfe ce
wallahi"
Kafin suyi magana Halisa ta fito hannunta riƙe da waya, ta kallesu sau ɗaya ta
marairaice fuska ta ce "Habibi ƙalbi sai kace baƙi akai shiyasa ka tafi lambu,
bari nazo musha lambun soyayya" ta cire wayar ta ɗora a

Please Login or Register in order to submit comment