You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙwaƙwalwa? Babu wani abu da Sheikh ba zai iya ba, In-ina kuma
Ubangiji ya ɗora masa muna fata a koda yaushe ta zama sauƙi a gare shi" "haka ne
Allah ya bashi lafiya, anjima zani gidan Barrister ɗin" Abba Hakimi ya ce "Ki yi
zamanki" ta kalle shi ta ce "Amma me ya sa?" Shiru ya yi mata tasan ba zai bada
amsa ba, kuma tunda ya ce haka yana nufin hakan har ransa.

A can commission Quarter's dake cikin garin Yola/ jimeta a hankali take driving
saman makeken kwaltar da zai sadata har zuwa gida, numfashi ta sauke a karo na ba
adadin tana kallon titi kunnanta kuma ma sauraran abin da Surayyerh ke faɗa tsaki
ta ja ta ce "You bother me with noise wlh Surayyerh koda yaushe problems ɗinki da
mahaifiyarki baya ƙare wa?" Surayyerh ke ta ce "A sbd ba ke bace ko? Gaba ɗaya ta
takura ni wani lokacin gani nake kamar ba ita ta haifan ba" da sauri Zahrah ta juya
ta kalli Surayyerh ta ce "Ashe daƙiƙiyya ce ke? Whatever is your problems ki barni
da tawa matsalar" dry sosai Surayyerh tayi tana tafa hannu ta ce "Oh! Sorry ashe fa
ciki yaƙi zubewa yanzu dole ki amincewa Deen kuyi aure" Zahrah stopped Surayyerh
from what she was saying ta ce "And who told you cikin Deen ne? Ni kai na ban zan
cikin waye ba, ban damu kuma dana sani ba kawai na zubar da shi ba aure a tsarina a
yanzu dai" Surayyerh ta gyara zama sosai ta ce "Kin san Allah a yanzu babu abin da
nake so sama da aure, sai yanzu na fahimci karatun bokon nan is nothing wani abu ne
wanda kana cikin gidan mijinka ma zaka iya yinsa" Zahrah bata ce komai ba tunaninta
yana can yana da tabi cikin jikinta ya zube ba tare da Mimi ta lura da shi ba. A
haka suka ƙarasa gida gatekeeper ya buɗe musu. Sosai tai mamakin ganin motocin Dady
yaushe ya dawo bata da labari? Dawowar gaggawa?. Fitowa tayi hannunta riƙe da L.G
bag daman babu mayafi jikinta kayan sun kama jikinta sosai, jerawa sukai ita da
Surayyerh zuwa cikin gidan. Dady da Mimi ta bi da kallo ganin suna magana a
hankali, Dady yai murmushi ya ce "Finally She's back zo nan Zonan Zahrah" ya miƙa
mata hannunsa ƙara sawa tayi ta zauna kusa dashi tana rungume shi ta ce "Wlcm Dady"
kallonta ya yi da kyau ya ce "Zahrah magana za mu yi mai Muhimmanci" ta gyara zama
ta ce "All ears Dad" ya ce "Kin san aminina Engineer Aliyu?" Ta ɗaga ta ce "I think
I knw him Dad mene ya faru?" Ya ce "Kin san wancan dake jikin photon?" Juyawa tayi
ta tsurawa photon Sheikh Aliyu haydar Aliyu dake maƙale jikin bangon parlournsu
zuciyarta ta ɗan buga ta girgiza kai ta ce "Ban shi ba Dad, amma na san yana da
muhimmanci tunda aka photon sa a gidanmu" ya jinjina kai ya ce "Yana da muhimmanci
a gareni da rayuwata baki ɗaya, Zahrah wannan da kike gani akansa duka wasu
burukana suke, ina son na haɗaku aure da Sheikh Aliyu haydar Aliyu cikin satin nan"
zabura tayi ta miƙe tana zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa sosai ta kasa
magana baki ɗaya. Mimi ta ce "Daman nasan Zahrah ba zata amince ba, domin ko Tafsir
ɗin ta tsana" Dady ya ce "Ya zama dole ta amince sbd karayar arziƙin dake shirin
tunkaro mu ba tare da mun shirya ba, Zahrah ki yarda ki auri Sheikh zaki farin ciki
namiji ko a maza samun irinsa zai wahala kiyi mini wannan alfarmar" Ajjiyar zuciya
ta sauke ta ce "Dady na amince da buƙatar, amma idan har daga ni ba zai sake auren
ko wacce mace ba ina nufin babu kishiya...

Na kusa gama free pages. IDAN BA KE it's 500 gaba ɗaya book 1,2 har ƙarshe. Via
6850917335 Na'ima Shuraihu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616 ƴan
niger suyi mini magana na faɗa musu yadda zasu biya.

DESTINY
TRUE LOVE
ROMANCE
TRUST
SARAUTAR MARUBUTA
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Nimcyluv sarauta_*

13.....
Mimi ta ce "baki son kishiya kuma? Ina ruwanki da wata kishiya?" Dady ya ɗaga hannu
yana murmushi ya ce "Ni ma bana fatan Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya yi wa Zahrah
kishiya,domin za a rage mini abin da nake tunani" cikin rashin fahimta Mimi ta ce
"kamarya Alhaji?" "Ba sai kinji ba, ki shirya aurar da yarinyar ki cikin satin nan"
ya faɗa yana miƙewa tsaye cikin jin daɗin amincewar da Zahrah ta yi.
Jikinta na rawa ta haura upstairs tana zuwa ɗakinta ta samu Surayyerh ciki daman
bata tsaya a parlour ba sama ya shige ɗakin Zahran. "Wayyo daɗi kashe ni, na samu
mijin da nake fata da burin samu cikin sauƙi" ta faɗa gado tana sakin ƙarar farin
ciki. Surayyerh ta ce "Pardon? Ban fahimta?" Miƙewa Zahrah ta yi ta ce "C'mon yanzu
Dady yake sanar mini za a haɗa aurena da Sheikh Aliyu" mamaki ya hana Surayyerh
rufe baki sai da Zahrah ta saka hannu ta rufe mata baki, Surayyerh ta samu damar
faɗin "Are you serious Zahrah? Gaskiya am happy for you daman kina son Sheikh?"
Tayi fari da idanu irin na gogaggun matan nan ta ce "Fiye da yadda bakya zato,
soyayyar Sheikh ta hanani aure, abin mamaki ban taɓa ganin shi a zahiri ba sai dai
photo a wajan Dady ko idan yana tafsir, nasan shi ma bai sanni ba"

"Yanzu duk ba Wannan ba, ya ya zaki da cikin jikin ki tunda likita ya tabbatar ba
zai zube ba? Gashi kuma aure ya zo babu shiri?" Zahrah ta ce "Kada ki damu da cikin
zanyi auren, ko da haihuwa nayi sai nace bakwaini ne ai anayi" Surayyerh ta jinjina
makircin Zahrah amma ta share ta ce "Idan kin ɓoye cikin ya zaki idan ya san ke ba
budurwa ce ba?" "Oh! My God what exactly wrong with you Surayyerh ki ke neman yi
mini baki? Ai ba zai sani bama ɗinki zanje ayi mini" Surayyerh ta ce "Uhm shi fa
babban Malami ne You never lie to him Malamai sun san komai infact sun fi kowa iya
soyayya kiyi tunani ki nemi mafita" share zan can Surayyerh Zahrah tayi a yanzu
yadda za taga Sheikh Aliyu haydar Aliyu a zahiri shi ne burinta. Da magrib
Surayyerh ta tafi gida akan gobe zata dawo domin fara shirye-shiryen haɗa events.
Tun a bakin parlour Surayyerh ta san akwai matsala tana shiga Umma ta kalleta sosai
ta ce "Daga ina kike?" Turo baki tayi tana musmus da bakinta kamar mai zagi ta ce
"Wai ke Umma zargina kike ne? Haba don Allah na fara gajiya ciki kike tsoro ko
mene?" Umma mamaki ya kasheta a tsaye ta ce "Surayyerh ni mahaifiyar ki kike faɗawa
haka sbd ina kare kiwon da Ubangiji ya bani?" "Wani irin kiwo kamar wata dabba
Umma? Kawai takurawar taki ce ta yi yawa, ki barni da abin da yake damuna gashi duk
iskanci Zahrah rana tsaka ta samu miji na kece raini wanda ba zan taɓa samun irinsa
ba" jirin dake neman yadda Umma yasa ta nemi saman kujera ta zauna. Ubangiji ya
gani kuma shi ne shaida tayi iya yinta ta fara gajiya tana ganin gaba gaba
Surayyerh dokanta zatai ita kam wannan karatun bokon bai mata rana ba. Hawayen daya
cika idanunta ta mayar sbd babu dacewar yiwa Surayyerh kuka sai ta sake lalacewa.
Surayyerh ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗinta tunani ya yi mata yawa abin da bata
tsammata ba a yanzu ya kawo mata farmaki.
A firgice Halisa Danejo Rome ya farka daga nauyayyen barcin daya ɗauke ta mai cike
da mafarkai wanda bata taɓa yin kamarsa ba, me ya sa Balaraban nan ke zuwar mata
cikin barci ne? Amma gaba ɗaya yadda ta gansa a daji ya bambanta a farki, na cikin
mafarkinta yafi kyau da kamala nutsuwarsa da kamewar shi tafi bayyana, kwarjinin
dana mafarkinta yake dashi na zahiri baya da shi, duk mutum ɗaya ne? Ta tambayi
kanta a cikin zuciyarta shiru tayi cike da damuwa domin ta fara gajiya da
mafarkinsa. Motsin da taji kusa da ita ya sanya ta juya idanuna ya sauka akan Dada
wacce take sanƙame numfashi na fita da ƙurar ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa. "Na lalashe
na shiga uku Dada jikin ne? Sannu Dadata zaki samu lafiya" ta faɗa hawaye na wanke
mata fuska gaba ɗaya ta ƙara zama wata kala damuwar ciwon Dada ya sata gaba, gashi
yanzu Hamma Yabi baya yini gida sbd neman kuɗin zuwa asibitin burni. Jigum tayi
tana kallon yadda kumfa ke fita ta bakin Dadar amma bata san me zatai mata ba, bata
da wanda zata kira a cikin bukkar. Shatu dake rakuɓe ta kalli Danejo ta ce "Dada
mutuwa zatai ko?" Girgiza kai Danejo tayi ta ce "Waya faɗa miki? Babu inda Dada
zata yafi ta barmu aradu muna tare da ita" wata ƙara da Dada tayi tana sanƙamewa ya
sanya Shatu fashewa da kuka, da gudu kuma Halisa Danejo Rome tayi waje. Karo sukai
da Hamma Yabi wando ya shigo hannunsa riƙe da ƙwayar magani daya amsu, ya riƙe
Danejo da kyau wacce take ƙoƙarin fita daga hayyacinta. "Hande en boni, Danejo
lalashewa ya sameka me ya samu Dada?" Gaba ɗaya ta rikice sai ƙanƙame hannun Hamma
Yabi take ganin bata hayyacinta ya jata ciki yana zuwa ya kwantar da ita yana rufe
mata fuska shiru tayi har lokacin cikinta bai bar rawa ba, domin gani take kamar
Dada tabarta kenan ta mutu ta tafi. Ya girgiza yana komawa wajan Dada tare da
ɗagata ya bata maganinsu ya shafa mata zuwa fuska da wuya Ajjiyar zuciya ta sauke
tana buɗe idanunta, hannun Hamma Yabi ta kama da kyau tana son tambayar shi mene ya
samu Halisarta amma ta kasa, a haka barci ya ɗauke ta cikin mayuyacin hali.
Washegari kamar kullum Danejo ta tatsi nono a ƙwayar, tun kafin gari ya yi haske ta
fita kiwo da shanunsu, sai da ta ɗauki awa uku ta dawo cikin sauri tana tafe tana
kaɗa naggen bayan ta ɗaure su ko abinci bata ci ba ta nufi cikin burni kawai tsaye
zuwa Abti America. Yadda taje haka ta dawo babu wanda ya sanya kuɗi ya sai nonon
balle su samu na abinci, a wahale ta shiga Rugar idanunta na rufewa ta kafa baki a
nonon wata nagge ta shiga sha sai da cikinta ya ɗago taja Ajjiyar zuciya tare da
nufar bukkarsu.

Sheikh Aliyu haydar na kwance saman makaken gadonsa idanunsa akan screen ɗin laptop
ɗinsa yana sauraran abin da ake faɗa ta cikin laptop ɗin. Can dai ya ja tsaki ya
girgiza kai, speaking calmly ya ce "Ni ni niii da dddddd dama zaka zaka zaka sauya
labarin nan naka Khalil, in anyway banga amm am am amfaninsa ba..." Dry sosai wanda
aka kira da Khalil ya yi ganin yadda Sheikh ke runtse idanunsa yana buga kai duk
dan ya kare kansa "To ai ni yana da amfani a wajena tun da abin da ya shafi Sheikh
Aliyu haydar Aliyu ai shafi Khalil Ahmad Sarki, look Sheikh don Allah cire son
zuciya ka faɗa mini mai mata sukai maka? Let me know" Sheikh ya shafa lallausan
gashin kansa wanda yake kwance gwanin sha'awa, cikin son cire damuwar father a
ransa ya dage yake hira da Khalil duk da yana shan wahalar magana ya jima bai
magana mai tsayin haka ba, idanunsa lumshe ya ce "kakaka....ka kasan me?" Sheikh ya
faɗa yana buga kansa jikin pillow yana riƙe ɗaya hannunsa sbd In-ina. Kallonsa
kawai Khalil yake yana jiran jin abin da Sheikh ɗin zai faɗa, a wahale cikin In-ina
wacce yake son ya saba magana da ita ya mirgina kaɗan yana riƙe kansa da hannu
bibbiyu ya ce "man ta ta manta kawai, ya ya yaushe za za kazo?" Murmushi Khalil ya
yi cike da ƙaunar Sheikh Aliyu haydar ya ce "Zamu zo da mai martaba wajan Hakimi, I
think I will spend my two weeks vacation with you in Kano" jinjina kai kawai Sheikh
ya yi ba tare da ya ce komai ba. "You are just afraid of women because you see
yourself as a Sheikh, women are the happiness of a man, try and see" Girgiza kai
kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kashe vedio call ɗin.
Umar-khan ne ke driving a hankali idanunsa akan titi amma hankalinsu na kan Sheikh
dake manyan mota cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora golden ɗin Alkyabba
sai rawanin daya ƙarawa fuskarsa kyau da haiba ya yi wani irin kyau kamar Balarabe
ƙamshin Roja ya cika motar sosai. Yana ki shingiɗe a bayan motar tunani yadda zai
sauya ya koma kamar yadda father yake buƙata, a haka suka ƙarasa Wani Restaurant
mai kyau da tsari mara hayaniya, Umar-khan ya yi parking kasancewar fitar sirri ce
yasa babu wasu masu take masa baya, cikin sauri ya buɗe Sheikh mota a nutse ya fito
yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da goya hannunsa a baya cikin kamala ya yi
gaba Umar-khan na biye da shi zuwa cikin Restaurant ɗin. Zama Sheikh ya yi tare da
kallon mutanan da zasu tattauna dasu, bayan sun gaida Sheikh ya ɗaga musu kai suka
shiga nuna masa zanan bank ɗin daya buƙata na reshe uku, kaduna, Abuja, da Lagos.
Baya cewa komai sai da Umar-khan suke tattaunawa gani ya yi zanan bai masa ba,
domin babban bank yake so wanda ba a taɓa yin mai girman sa ba. Hakan ya sa ya
amshi carbon paper da pen a nutse ya zana yadda yake so, zanan ya bawa ma'aikatan
mamaki abin da basu sani ba, kaɗan kenan daga cikin baiwar Sheikh duk abin da ya
sanya ransa yana gwadawa yake yi daidai. Sallama sukai bayan anyi musu transfer
miliyoyin kuɗi domin fara aiki gadan-gadan. Ɓangaren Kamfanin sarrafa shinkafa ma
tuni aiki ya yi nisa, ya yi ordern injina masu kyau daga Chaina. A gajiye ya dawo
gida idanunsa na rufewa kansa ya sakarwa shower lokacin 1:30 ya saba barci tsakanin
azahar zuwa sallar asr, fresh milk ya tsiyaya a cup tare da zuba honey ya sha
kaɗan ya wanke baki, yana kwanciya barci ya ɗauke shi daman ya riga daya saba.
Washegari ya kama weekend Sheikh bai san meke faruwa ba, sai daya farka yaji
labarin tun 7 su Uncle Haroon da Abba Hakimi tare da Baffansa suka nufi garin Yola
nema masa aure. Ko ajikinsa bai ɗauki auren matsayin wani abu, shi dai ya san ko
farcen mace bai taɓa sha'awa ba balle ya birgensa. Da yamma su Abba Hakimi suka
dawo cikin jin daɗin an basu auren Zahrah nan da sati mai kamawa za a ɗaura aure.
Kasancewar yau Friday ne ya sanya Sheikh ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda
fara tas da ita mai ɗinki jamper da babbar riga, bai sanya hula ba sai hirami daya
saka a saman sumar kansa ya ɗauki zagayayyen abun nan na larabawa Black colour ya
ɗora saman hiramin, shekarunsa suka bayyana a jikinsa, domin kowa ya kalli Sheikh
Aliyu haydar ya san ba yaro bane, girma ya fara hawa jikinsa babu mamaki ya yi aure
a same shi da yara biyar haka, shekaru 34 ba wasa bane ba. Kai tsaye babban
masallacin juma'a ya nufa sai da ya yi huɗu ba sosai mai ratsa jiki akan tsaida
sallah a lokacin ta, tunda duk In-inar Sheikh inda karatu zai yi yana farawa ake
nemanta a rasa. Bayan idar da Sallah ya nufi zaga gidan marayu kamar yadda ya saɓa
idan yana ƙasa, a hankali yake tafiya hannunsa goye a bayansa kansa a ƙasa fitowar
su kenan daga gidan marayu zasu shiga mota yaje gida wajan Mother, kamar daga sama
wata budurwa kyakkyawa ajin farko ta tsaya a gabansu da sauri Umar-khan da Saif-
wazir suka sha gabanta tun kafin securities su ƙarasu bakinta na rawa ta ce "Don
Allah ku barni nayi magana da shi, na jima ina son haɗuwa da shi" Umar-khan ya daka
mata tsawa ya ce "Baya buƙatar ganin kowa, kuma a mu'amalar shi baya yi da mata ki
nemi wani wajan" A nutse Sheikh ya dakata tare da juyawa idanunsa zuwa inda
budurwar take, waro fararen idanunsa waje ya yi yana mamakin abin da ya haɗa shi da
bayin Allan nan da suke bibiyar shi. Murmushi mai laushi ya yi ba tare daya bari
kowa ya gansa ba, yana mai ƙarewar budurwar kallo musamman ƙafarta. "Ka taimaka
mini daga yanzu ba zan sake zuwa inda yake ba" Umar-khan ya yi mata wani ban zan
kallo ya ce "Ke ko mayya ce ke baki isa kije inda Sheikh yake ba, kunne masu
ƙullawa mutane sharri ko?" Sosai taji zafin maganar Umar-khan sai kawai ta juya
kamar zata kifa sbd sauri. Tana barin wajan Umar-khan ya dafe kansa Saif-wazir ya
ce "Are you okay?" Ya ce "Kai na ke ciwo, zazzaɓi nake ji" Umar-khan ya faɗa
bakinsa na rawa kafin kace wani abu wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Umar-khan.
Girgiza kai kawai Sheikh ya yi domin ya san za a rina waya aiki Khan musayar yawo
da aljani?.

Da sauri Hamma Yabi ya shigo bukkarsu hannunsu ɗauke da kuɗi ya kalli Danejo wacce
take sumar kanta ya ce "shai Alhmd kuɗi shun samu gobe zan kai Dada asibitin burni"
murmushi Danejo tayi wanda ya ƙara fidda kyanta na fili ta ce "Kai Allah abin gdy
Dadata zata samu lafiya yau ba zan barci ba sbd farin ciki aradu" Hamma Yabi ya
kalli Dada dake kwance kamar haka cikin farin ciki ya ce "Insha Allah, da sassafe
sai burni" fita ya yi farin ciki ya cika zuciyar Danejo Dada zata tashi su koma
yadda suke rayuwa a baya. Hamma yabi bai dawo ba sai dare riƙe da ƙullin buduri da
ƙosai mai zafi wanda ake a can wajan gari. Sai dai ko zama bai ba suka fara jiyo
harbi ta ko wanne waje alamar ƴan fashi ne suka shigo cikin Rugar Rome. "Bone Hamma
harbi harbi....," Bata ƙarasa faɗa ba suka ji an shigo bukkarsu wani mutum mai riƙe
da bindiga ya kalli Hamma Yabi yana faɗin "Kuɗi,kawo kuɗi bamu da lokaci" jikin
Hamma Yabi na rawa ya ce "Ba kuɗi bamu da shi" mutumin ya yi wata dry sosai ya ce
"Babu? idan na bincika na samu duk hukuncin dana ɗauka akan kai ka sani" yana faɗin
hakan ya fara bincike bukkar daga can waje harbi ake ta ko wanne sashe, cikin
rashin sa a mutumin yaga kuɗin da Hamma Yabi zai kai Dada asibiti "Aradun Allah
kuɗin asibiti ne, kayi mini ka taimaka Dada zamu bawa lafiya.....," Harbin da
akaiwa Hamma Yabi a ciki ya sanya ya fasa ƙara tare da faɗuwa ƙasa ihu Danejo ta
fasa ganin yadda jini ke zuba a jikin Hamma Yabi tana ƙoƙarin zuwa inda yake
mutumin ya ƙara sakarwa Hamma harbi a tsakiyar kansa......


Wannan littafin na kuɗi zaka samu book 1, 2 akan ₦500 daga farkon labarin har
ƙarshe ka tura ta wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity
bank shaidar biya 08119237616.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

14......
Cikin ƙaramin lokaci ƴan Rugar Rome suka shiga cikin tashin hankali musamman wajan
su Danejo. Ko kuka ta kasa ta kafe gawar Hamma Yabi da kallo sai Ajjiyar zuciya
take, shatu na gefe ta ƙanƙame jikin Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba
sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi
an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta
shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan
gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo
bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci
a wajen ta bace. "Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam"
Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce "Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu"
da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce "Da gaske Hamma
Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?" Ta faɗa cikin rauwanin
muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna.
"Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba" ƙurr ta kafe Giɗaɗo da
idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu
numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa
kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. "Sannu kin farka Danejo?"
Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta
juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce "Ina Hamma Yabi? Ya tafi
da Dada asibitin burni?" Shatu tayi saurin faɗin "Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an
rufe shi a ƙasa" zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro
da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina
zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan
da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka
bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin
idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce "Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba
ga Dada ba muna tare da ita?" Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce "Ba kuka nake
ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo" miƙewa tayi jikinta
sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da
kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe
a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar
Sarkin ruga ta ce "A'a Danejo ne bismillah shigo" kamar ba zata shiga ba sai kuma
ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce.
"Jamɓanduna. _Ina kwana_" Ya ce "Jamni.. _lafiya_" zata sake yi masa wata gaisuwar
ya dakatar da ita da faɗin "mene ya kawo ki?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta
ce. "daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?" Kallon
tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
"Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?"
Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle
shi tana faɗin "Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne,
kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka" Ya ce "E, to buɗe kunne kiji kaf
cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan
ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun
naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma" kasa cewa
komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne
Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa
cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule
ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake
mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.

Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka
ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin
kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. "Ina fatan komai ya
yi yadda kake so?" Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa
yana mai jinjina shi a nutse alamar "Ya yi" Umar-khan yai murmushi kaɗan yana
jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita.
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a
hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin
ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya
rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi
na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a
parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin
ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi
mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole
ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi
Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A
zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da
kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na
motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. "Ba sai kace ba,
Allhamdulillah" Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke
fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
"Naga baka shirin auren naka, kamar dai you're not ready if i not mistaken?" Sheikh
ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya

Please Login or Register in order to submit comment