You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magrib Mother na zaune a parlour ita da Jadda. Jadda ta kaɗa ƙafa ta ce "Amma
dai Allah ya isa, an munafurce ni ko waye kuma yaje shi da Allah, shi yasa yadda
zai yi dashi danni ba zan iya komai ba" "lafiya dai Jadda?" A fusace Jadda ta ce
"Ina batun lafiya Maryam? Ashe haka aka haɗawa Uwar matar can lefe hadda na Allah
ya isa fa? Ni dai babu ruwana na kusa zare hannuna daga al'amarin Aliyu ko na ɗaga
masa nonon kawai tun da nayi niyya" Mother tai murmushi kawai tana jiran zuwan
Maimoon.
Zahrah ta ƙarasu parlourn sanye da ƙaton hijabi irin ta Allah ɗin nan nace, ta
zauna tana faɗin "Sannu da hutawa Mother" a taƙaice ta ce "Yawwa" ta juya kan Jadda
wacce ta haɗe rai sosai ta ce "Barka da gida" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce
"Allah ya isa, Allah ya isa wallahi ban yafe ba" Jadda ta faɗa tana kallon Mother
tare da fashewa da kuka ta ce "To me nayi mata da zata gaishe ni? Sbd Allah ina
ruwanta dani ko nace ina buƙatar gaisuwarta" Zahrah bata ƙara bi takan Jadda ba ta
kalli Mother tana sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Daman zan mayar da Yarinyar nan ne
gida" Mother ta kalli Maimoon dake shigowa tana faɗin "Wacce yarinya?" Zahrah cike
da nuna cewa tafi kowa iya ladabi ta ce "Ƴar fillo, zan tura ta gida" Jadda ta miƙe
ta ce "Wannan farar yarinyar kyakkyawa mai zubin labarawa kamar ita tai kanta? Idan
kin isa Allah ya tsine" Mother tai murmushi ta ce "Me ya sa?" Zahrah tai ƙasa da
kai ta ce "Daman Mimi tace na dawo da ita gida, da ƙyar aka yarda aka bani ita kuma
tana karatu" Mother ta karkaɗa ƙafa ba tare da ta ce komai ba ta danna wayarta babu
jimawa aka ɗaga wayar ta ce "Umar-khan, kayi waya da mutananku na can Madina, a
fara nemawa Halisa gurbin karatu a matakin ajin farko na secondary" gaban Zahrah ya
faɗi, ganin how smart she had. Bayan gama wayar Mother ta ce "kada ki damu Zahrah,
I'll talk to your mom, ki fara shirye-shiryen tafiya" ta miƙe tana faɗin "Na gode
Mother" da sauri ta shige part ɗinta.
Tana zuwa ta rufe ƙofa tare da cire hijabin jikinta inners ne kawai a jikinta cikin
faɗa ta ɗaga wayarta ta ce "haba Deen wai kai wanne irin maye ne?" Deen dake cikin
wayar ya ce "Muna vedio call kika tafi kin barni cikin wani hali Beb" cikin ɗaga
murya ta ce "Jarbabbe duk kai ka koya mini jaraba kwana nake bana barci, nifa batun
tafiya da yarinyar nan ne na fasa,ina hangowa kai na matsala gaba ɗaya ji nake
kamar wani abu zai faru idan na tafi da ita" Deen ya numfasa ta wayar yana faɗin.
"Ya kukai kuma me kike so ayi?" Ta faɗa masa duk yadda sukai da Mother ya ce "Uhm
Sirikarki Educated ce kuma Barrister, ta fiki tunani da hankali idan kina wannan
haukan da wuri za a gano shirinmu, dole ki yafe ɗan cikin ki a gidan Yaa Sheikh,
shi ne zai bamu damar cimma burinmu ya zama dole ki samu kusanci dashi ina nufin ki
samu mu'amalar aure da shi, hakan shi ne hanyar farko, ai ana haihuwa bakwaini ki
san duk yadda kikai kina zuwa Madina ku samu daidaito Zahrah, kece madafin cimma
burina na faɗa miki irin cin amana da zaluntar da akai mini" ta sauke numfashi tare
da ta ce.
"It's ok Deen, na maka al'ƙawarin ƙwato maka hakƙin ka, ina son ka, burina ka tsaya
dani banda wata macen" ya yi murmushi ta wayar ya ce.
"Zahrah kenan, kina so na kullum kike cewa, amma son da kikewa Yaa Sheikh yafi son
da ki ke mini, duk da hakan me ya sa kika amince zaki cutar da shi bayan kina son
shi?".
Zahrah ta ce "kada ka damu wannan sirri na ne, sunna or later zaka sani, Yaa Sheikh
manufa ne, kai kuma makami ko wanne nada amfani, amma dole muyi wani abu akan
Halisa" ya ja tsaki a ran shi sam bai ga abin damuwa akan wata Halisa ba.
"A kashe ta? Ko kuma a haukata ta?". Zahrah ta ce "Hauka kuma, zan yi tunani akan
haka, muje vedio call na nuna maka wani abu mai yaji" dry ya yi ya ce "Zahrah bana
son ganin wannan shafaffen ƙirjin naki, wanda yake kwance har ciki serious tun
kafin Yaa Sheikh yasan wace ke ya kamata ki nemi magani" maganar Deen ta daki
zuciyar Zahrah ta kashe wayar rai ɓace.
Khalil ya ce "Mother daman zuwa nayi nai miki sallama, yanzu zamu tafi airport" ta
ce "To sai yaushe kuma" ya shafa kai ya ce "Ina tunanin sai bikin Maimoon ko idan
matar Yaa Sheikh ta haihu".

"Ikon Allah daga aure sai haihuwa, Maimoon kam ai da sauran ta" ya ƙara shafa kai
idanunsa akan Maimoon dake tura masa baki.
"To Allah ya tsare, a gaida Oum Juwairah" ya miƙe yana faɗin "za taji ai tana gidan
Abba Hakimi" kafin Mother tai magana idanun Khalil ya sauka akan yatsun Halisa da
mmkin yake kallon Zoben dake maƙale a yatsar zai magana El ya ce "Zan tafi ni dai"
ya ce "kafi jirgin sama tashi" Halisa ta kalli El suka haɗa idanu sun jima suna
kallon juna kafin tai ƙasa da kanta, tun jiya da suka je visa ta daina walwala taƙi
kula kowa surutun ya rago sosai.
El-bashir ya fita Khalil ya ce "Ƴar tsuhuwa Maimunatu zo ki kaiwa Matar Yaa Sheikh
gift ɗinta" ta miƙe kafin ta ƙarasa yayi waje, tana zuwa corridor taji an jawota
zuwa jikin mutum, a tsorace ta buɗe baki zatai ihu Khalil ya yi saurin rufe bakin
ya ce "Haba Amaryata yaushe za mu yi auren ne?" Ta ce "Allah ya sauwaƙe na auri me
mata ni ban so" ya ce "Ni kuma na miki al'ƙawarin wallahi sai kin aureni na haɗa
mata biyu a cikin masarauta" tai masa shiru, tun Maimoon na ƙarama yake mutuwar son
yarinyar. Ya ɗan ƙara matseta a jikinsa daidai kunnanta ya ce "I love you" yana
faɗin hakan ya saketa yana damƙa wani box ya ce "For our In-law, and this na ki ne"
ya ƙara damƙa mata wani box ɗin ya juya da sauri tare da ficewa.
Washegari gari da safe Yaa Sheikh ne yake fitowa a hankali daga part ɗin sa, yana
sanye da jallabiya fara tas ƙafarsa sanye cikin slippers, hannunsa goye a bayansa
ya ɗan tsaya a parlourn sbd shiru da yaji juyawa ya yi idanunsa ya sauka akanta
tana ƙawance akan duguwar kujera ta kifa kanta a hannunta kamar mai barci, jar
rigar dake jikinta ta ƙara fidda tsarin jikinta, madaidaitan hips ɗinta sun bayyana
a fili ya ɗauke idanu yana ya mutsa fuska, remote ya ɗauka tare da kunna karatun
Alkur'ani ya danna ƙara ya cika gidan. A firgice Halisa ta miƙe tsaye jikinta duk
rawa yake, jajayen idanun da kusan kwana biyu suka ƙi dawowa dade ta buɗe su akan
Yaa Sheikh dake zaune akan kujera yana ɗan jan gemunsa. Ba tare da ta ce komai ba
sbd kanta dake juyawa da sauri ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga cikin
parlourn wacce kai tsaye kuma zata kaita har waje bakin hanya, Allah Allah take ta
fita sbd karatun dake gigita mata lissafi kamar zai fasa kanta.
Tana zuwa daidai inda yake zata gilma ta shige ya sanya farin hannunsa mai laushi
ya damƙota tare da dawo da ita baya...

Paid book
It's 500
Via 08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: Dawo da ita baya ya yi tare da zaunar da ita a ƙasa wajan
ƙafafuwansa, yana mai sakin hannunta da sauri. Tamkar wacce take gane abin da
shirun nasa yake nufi haka ta zauna waje guda taƙi yarda ta ɗago kanta kamar yadda
yasu sbd ya fahimci abin da yake tunani.
Yasan har abada indai tana cikin wannan yanayin to ba zata taɓa kallon cikin ƙwayar
idanun shi ba, sai dai idan marasa kunya ne suke tattare da ita.. hannunsa daya
riƙe nata ya dunƙule waje guda a haka Mother ta fito sanye da duguwar riga ganin
Yaa Sheikh a main parlour da sassafe ya bata mamaki, idanunta akan shi kana ta zame
zuwa kan Halisa dake zaune kusa da ƙafar shi ta dama. Da mmki tana zama ta ce
"lafiya dai Haydar? fitowa da safiya, Halisa fa?" Ta tambaya tana kallon Halisa
elxty yadda Yaa Sheikh yake abu lokacin yana yaro haka yanzu Halisa tayi. Ya buɗe
idanun shi yana ajjiye carbin hannunsa cikin kamilalliyyar muryarsa ya ce. "Mun
tashi lafiya Mother?" Ta saki murmushi tana faɗin "Allahamdulillah Haydar, Halisa
fa?" Ya ƙara ware idanu yana kwaɓe fuska alamar tambayar batai masa ba, kamar zai
share ya numfasa kaɗan ya ce.
"Wafa?" Mother ta ce "Meya fito da Halisa da wannan safiyar kuma gata kusa dakai
kamar bata da lafiya?" Ya jima yana tunanin amsar da zai bawa Mother baya ƙarya
baya kuma faɗin abin da bashi da tabbacin sai ya yi shiru Mother ta miƙe tsaye tana
faɗin.
"Black tea ko? Bari na kawo maka,ka jira ina son magana dakai" ya jinjina kai.
Mother na tafiya ya juya kansa zuwa inda Halisa take zaune a hankali ya miƙa
tattausan farin hannunsa mai taushi ya ɗora saman goshinta.
Zabura tayi zata gudu ya riƙe kan da kyau, sosai yaji kanta ya ɗauki zafi yana
harbawa. Ya jima riƙe da kan yana ɗan murza babban yatsar shi a tsakiyar goshinta
kafin yaji taja duguwar ajjiyar zuciya tare buɗe idanu.
Ya zame hannun shi daga kan, itama ta kasa kallon shi ta kuma kasa motsawa.
Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe jiri na ɗaukanta ta nufi part ɗin su Maimoon
domin anan ne take kwana yanzu. Barin ta parlourn ya yi daidai da dawowar Mother
daga kitchen, bayan ta zauna tare da tsiyayawa Yaa Sheikh black tea ɗin tare da 2
spoon na honey yana tiriri ta miƙa masa.
A nutse yake sha ganin ya kusa shanyewa ta kalle shi ta ce "You need more? with
chips or kunnu?" Ya jinjina kai alamar "Eh" kitchen ta shiga not too long ta dawo
ɗauke da tray, Spoon ɗin ya ɗauka ya fara cakar chips yana taunawa a hankali, haka
kawai jikin shi ya bashi ana kallon shi gently ya ɗago kai da sauri ta koma ciki
tana dafe ƙirji, ya girgiza kai domin idanunsa sun riga da sun ganta tuni.
Mamakin cin abincin na Yaa Sheikh yau ya kama Mother tana zaune tasan ko tayi
magana ba zai fahimta ba, sai da ya goge baki da tissue kana ya zaro Aswaq daga
cikin aljihu ya fara yi.
"Ina son yin magana da kai ta fahimta Aliyu" ya maida hankali sosai akan Mother ta
gyara zama ta ce.
"Halisa bata da kowa, bata da wanda kareta ya kuma ja ragamar rayuwar ta, ko da
baka san yaya akai tazo gidan nan ba, amma ka tuna cewa matar kace, ban damu da kai
mata kallon mata ba, wannan deal kai da Abbanka, amma ka zama garkuwa a gare ta don
Allah don Annabi ba danni ba Aliyu" ta haɗe hannaye biyu alamar roƙo a gare shi, a
taushashe ya kama hannun Mother duk biyun, ya jima kafin ya ce.
"Fiye da yadda kike zato, al'ƙawari ne" tai murmushi ta ce "Allah ya yi maka
Albarka Malam, tare da matanka, kayi ƙoƙarin sauke hakƙin ko wacce mace a cikinsu,
kada ka tauye na wani ko fifitawa" ya jinjina mata kai yana miƙewa tsaye.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa tare da ɗaukan system ya shige Library ɗinsa, wasu
muhimman ayyuka ne dashi gashi yana son tattara komai wajan Saif-wazir tunda da
Umar-khan zasu koma, ɗalibai na can suna jiran shi da gidan marayunsa.
Misalin 10 kowa yana zaune akan dinning ana dinner Father ya ajjiye Spoon ɗin
hannunsa ya kalli Zahrah ya ce "Aliyu ya faɗa miki 12 jirginku zai tashi ko?" Ganin
Idanun Mother yasa Zahrah faɗin "Eh Father, nama gama shirya kayana" Jadda ta fashe
da kuka tana share majina da gefen zani ta ce "Ubangiji ya bawa Malam haƙuri, an
haɗa shi da wacce tafi ƙarfin shi, na rantse uwata ta haifan ban taɓa ganin ƙatuwa
budurwa irinta ba, an bashi sa'ar babar shi da kaɗan fa na girme mata, gaskiya dole
Malam ya ƙara aure zan nemi Hakimi da kai na ai shela a sama masa mata ko cikin
masarauta ne" gaban Zahrah ya faɗi sosai kishiya za ayi mata? To ai Yaa Sheikh shi
da wata mace har abada,da ita zai ta rayuwa da daɗi ba daɗi,idan har tana raye babu
wacce ta isa ta shigo cikin gidanta, ba zata taɓa haɗa Mijinta da wata ƴa mace ba.
Father ya ce "Bayan auren da yake dashi?" Jadda ta ce "A'a zan maka Allah ya isa
Aliyu, tun nazo gidanka kaji na kulaka? Nifa ba zan yarda Malam ya zauna da
ɗirkekiyyar mace kamar durunar ruwa ba, ko ni bata ban sha'awa ba balle namiji,
kana kallon ƙirjin kamar an zuba kwalta a titin gwammaja, dole ya auri ƴar ƙarama
wacce zai mure ƙuruciyarta ai Alsulhu khair" bakin Halisa na rawa ta ce "To ai
nima matar shi ce kuma ƴar ƙarama ce ni....," Kafin ta ƙarasa maganar Mother tayi
saurin rufe mata baki, faɗan da Jadda kewa Father yasa babu wanda yaji maganar sai
Maimoon.
Baƙin ciki ya cika Zahrah jin daɗinta ɗaya babu Yaa Sheikh a wajan. Cikin makirci
Zahrah ta fashe da kuka tana zubewa gaban Jadda ta ce "Don Allah kiyi haƙuri Jadda,
kada ki rabani da mijina yana so na, ina son shi" Jadda tai mitsi mitsi da idanu
tana riƙe haɓa ta ce "Mai ƙarya aƙona shi a wuta, nifa na rarrashi Malam na bashi
baki akan ya aureki da ƙyar sai dana zubar da hawaye, nace zanbi duniya kawai idan
bai yarda da aurenki ba, shi ne zaki ce yana son ki?" Da sauri Zahrah ta nufi part
ɗin ta, sbd gab take da yiwa Jadda rashin mutuncin wallahi.
Jadda ta ce "To ai kaga nayi mata bayani cikin sauƙi,ta fahimta da faɗa nai mata
sai ta ƙulla ce ni, ai Alsulhu khair"
"Ai kam dai munga Sulhu, bamu sani ba ko zai zama alheri" cewar Auta Fattoumah.
Jadda ta ce "A'a kowa ya yi ta kansa, bana shiga abin da bai shafan ba, amma fa na
girgiza a bawa mutum auren sa'ar uwar shi?"
Halisa ta ajjiye Spoon ɗin hannunta idanunta ya yi jajir kalmar..
_“Yana so na, ina son shi”_ ya shiga yi mata yawo a cikin kunne. Ta miƙe a hankali
tare da nufar ɗakin su Maimoon. Tana zuwa Mother ta biyu bayanta..
Ta kasa kallon Mother bakinta kuma ya ƙiyin shiru ta ce. "To yaushe zan faɗawa kowa
ina da aure kuma Malam ne mijina?"
Mother ta girgiza kai ta ce "Ba yanzu ba, inda kika faɗawa wani to mun ɓata kuma
zance Yaa Sheikh kada ya saki makaranta"
Da sauri tana zare ido ta ce "A'a ba zan faɗa ba, amma zan dinga ce masa mijina ko?
ko Baffa?" Mother ta rasa me zata ce, surutun yarinyar baya sarrafuwa idan har ya
fito to dole ta furta.. "duk yadda kika gani, amma idan kika ce miji ai Zahrah zata
gane, kice Abba Sheikh" bayani ta ƙara yi mata cike da hikima na zaman rayuwa, da
kuma wasu muhimman abubuwa akan Yaa Sheikh ɗin.
"Maza ta shi kije Maimoon ta ƙara yi miki saloon" ta miƙe tana cewa "To" sai da
taje bakin ƙofa zata fita ta tsaya tare da kallon Mother ta ce.
"Amma idan naje can Madina zan iya faɗawa kowa ayi mini aure ina da miji?" Mother
ta tafe kai tare da faɗin "Na shiga uku"..
Zahrah ce ke waya da Surry ta ce "Wallahi Surry ko da wasa aka bawa Yaa Sheikh
auren wata sai na kasheta, ina da tsananin kishi akan abin da nake so, balle mutum
kamar Yaa Sheikh wanda banyi tunanin zan same shi matsayin miji ba" Surry ta ce
"Tab, sai ki san yadda ki kai kika tare da mijinki idan kuka tara zuri'a babu mai
rabaki da shi ai" Zahrah ta ce "You're right jirginmu zai tashi, yama sunan maganin
dake saka mutum feelings in 5 minutes?" Surry ta faɗa mata sunan maganin ta ɗora da
faɗin "Amma dole Yaa Sheikh ya gane bake bace" murmushin mugunta Zahrah tayi tana
girgiza kai ta ce "Idan kuma yana cikin maye fa?" Surry ta zare ido ta cikin wayar
ta ce "Bugar dashi zaki? Kada ki cutar da ƴar mutane yafi ƙarfin ta ba"

"Surayyerh kenan, na shige duk tunaninki, kada ki manta Zahrah Farouk nake, ita
kuwa Zahrah ba mahaukaciya bace ta san me take, Ƴar fillo data gama aikinta zan
aiwatar da burina a kanta gudun matsala" Zahrah tai wa Surry ba zata, gashi bata da
hanyar da zata taiwa Halisa magana. "Do you want to just leave me alone now? these
past few days have been a bother" "Okay bey" cewar Zahrah. Tana gama wayar Halisa
ta shigo tai tsaye fuska a haɗe.
"Oh su ƴar fillo an samu duniya, bari muje wannan farin na jikin ki sai na ɓatar da
shi" ta tura baki gaba cikin surutu ta ce.
"Ai farin daga Allah ne" Zahrah ta ce "magana ki kai?" Tai shiru ta kalleta da kyau
ta ce..
"Ki gane baki da haɗi da dangin mijina, ke ƴar aikina ce, ki daina cusa kanki inda
baki da mazauni ba zaki taɓa samun karɓuwa ba, saura ki faɗawa wani ke ba ƴar uwata
bace kamar yadda nace"
"Sai dai kishiya ba ƴar uwa ba" da sauri Zahrah ta ce "kika ce me?" Ta girgiza kai
ta ce "Salati nayi"
Ta ja tsaki tare da cewa "Get out jakar kawai"
11:00 Yaa Sheikh ya fito cikin wata haɗaɗɗiyar Alkyabba mai kyau da tsari, ya naɗa
rawani wanda ya ƙara fidda haibarsa da cikar kamalar da yake da ita, fuska kame.
Hannu goye abaya tare da carbi yana ja. Banda ƙamshin Roja babu abin da ke tashi a
main parlour.
"Allahu Akbar Allah ya baka haƙurin zama da uwar mata Malam, ni tsoro na ɗaya kada
a dinga nunaka da baki ana ka mijin sa'ar babar shi" Zahrah data ƙarasu parlourn
tai tsaye a gefen Yaa Sheikh ba tare data kula Jadda ba ta ce.
"You look good My Excellency".
A can bedroom Kuka sosai Halisa take sai rigima take ita kawai wajan Dada zata, da
ƙyar Mother ta rarrasheta, ta zuba mata komai na buƙata cikin torelly bag ba tare
da sanin Zahrah ba.
Maimoon ta ce "Matar Yaa Lee ga gift inji Yarima Khalil" Mother ta ce "Gift?"
"Eh, shi ya bani wai na bawa matar Yaa Sheikh, ni kuma kawai zan bawa Halisa"
Mother ta amshi box ɗin ta buɗe, wani gold ring ne mai kyau sai ƙyalli yake, ta ce
"Zan ajjiye waje na, hannunta akwai ring har biyu ya isa, Allah ya tsare ya ki yaye
sai na kira waya Daughter" Halisa ta kalli Maimoon tana mata gwalo ta ce.
"Yarinya na tafi gidan mijina, duk abin da ya faru zan ajjiye miki labari ko na
dinga faɗawa Mother tana gaya miki" Mother ta ce "A'a na shiga uku bani a nan" Yaa
Sheikh tuni ya shiga mota, shi kaɗai ne a baya Saif-wazir na driving..
Zahrah a motar Ishaq-Hakim ita da Halisa da Maimoon. Mother ta ce ba zai taje
rakiya ba.
Kai tsaye gidan Abba Hakimi suka nufa. Yaa Sheikh ne kawai ya shiga sbd babu
lokaci, ya shige jikin Abba Hakimi yana sauke numfashi, rauninsa ya bayyana
kasancewar yana jikin Abban nasa, a karo na farko ya riƙe Abban da kyau murya bata
fita ya ce.
"Ba zan iya ba Abba" Abba Hakimi bai fahimta dan haka ya ce "Kai mutum ne mai
tsoran Allah da gudun hakƙin wani, balle matarka kada ka damu, ita Halisa ƴar riƙo
ce shekara nayi zan amshi abata" ya zare jikinsa yana sauke numfashi tare da yin
sallama.
Daga nan suka ɗauki Umar-khan kai tsaye suka shige Airport inda jirgi ke jira.
Tunda daga jirgin hankalinta ya tashi amma bata nuna ba, ta riƙe hannunta da kyau,
Umar-khan na gaba sai Zahrah Halisa na biye da ita a haka suka shiga cikin jirgin,
suna shiga Halisa ta riƙe kanta sbd tsoro, Umar-khan ya kalli Zahrah ya ce "Wajenku
na cikin vip" Zahrah ta kalle shi ta ce "Yana ciki ne?" Umar na zama a mazauninsa
ya ce "Gaskiya ban sani ba, ku shiga ku gani" ba tare da Zahrah ta ce komai ba ta
nufi vip ɗin, jin takun tafiya a bayanta yasa ta tsaya tare da kallon Halisa ta ce
"Ke kuma lafiya kike boye ni? Na manta ba a saba ba, Umar nuna mata wajan zama"bai
ɗago kai ba ya ce "Wajan zamanku ɗaya ne ai duk vip" Zahrah ta riƙe ƙugu ta ce "kan
uba, tayaya haka ya kasance kana nufin tare zan zauna da ita ga mijina kuma?" Sai a
lokacin ya ɗaga kansa tare da kallonta ya ce "To ai suna ɗaya kuka amsa, matsayi
ɗaya"

"Kamar yaya suna ɗaya? Umar ya kamata kasan me zaka ce dani, ka gane" ya haɗe
hannaye waje guda ya ce.
"A'a ranki ya daɗe, mai da wuƙar mijin naki shi ne ya bada umarnin haka" ta haɗiye
yawun takaici tare da shigewa vip, daman ita Halisa ta jima da shigewa, dan haka
Zahrah na shiga ta samu Halisa zaune ta sunkuyar da kanta ƙasa, wajan ya haɗu sosai
akwai duguwar kujera wacce Halisa take zaune akai, sai kujera mai guda biyu,
tunanin Zahrah ya bata mai guda biyun ita ce wacce zasu zauna ita da Yaa Sheikh, ta
nemi waje ta zauna idanunta akan Halisa ta ce.
"Ina mijina?" Tai shiru taƙi cewa komai. "Ba magana nake miki ba, na lura kin fara
ganin wajan barcina?" Ta ɗago lulu eye's ɗinta wanda suke sheƙi kamar an tara musu
ruwa sbd yadda hawaye ya kwanta cikinsu. A tsiwa ta ce.
"Ina mijina?" Zahrah ta zare ido tare sakin baki da jin abin da Halisa ta ce. Ƴar
fillo tai murmushi kawai tare da girgiza kai ta ce "nifa kamar haka naji kince Anti
shi ne nake ƙara tambaya, to a haka naga wajan kam" Zahrah ta ɗaga hannu zata ɗauke
Halisa da mari suka ji gyaran murya.
Gaba ɗaya suka ɗaga kai a tare daga Uwar gidan har amarya Zahrah, basu yake kallo
ba wayarsa yake sakawa a airplane mode. Yaa Sheikh ya riƙe ya saba akan duguwar
kujera yake zama, sbd yana ɗan samun hutu yayi barci kafin ya isa inda zashi, kai
tsaye ba tare daya lura da Halisa ba ya nufi duguwar kujera tare da zama dab da
ita. Numfashin Halisa ya kusa ɗaukewa sbd wani mugun shaƙar ƙamshin Roja da tayi,
gashi Yaa Sheikh ya zama ƙato babba sosai har kafaɗar shi na rufe kanta.
A karo na farko zuciyar Zahrah ta shiga bugawa gabanta ya faɗi,ta juya ta kalli
Halisa wacce ta kafe Yaa Sheikh da idanu, a hankali kuma ta kalli Yaa Sheikh wanda
ya nuna kamar bai san da mutane a wajan ba. Ta kasa magana ta rasa a wanne ma'auni
zata saka haka, anya bata hau tsaunin da zai kaita zuwa ga hallaka ba?. A zahiri
Yaa Sheikh ya mance ya taho da matayen nasa har biyu, da uwar mata da kuma ƴar
rainon shi. A hankali aka fara sanarwar a ɗaura blet, Zahrah ta ɗaura Halisa kuma
ta rasa me ake cewa sbd cikin harshen turanci ake maganar, sai faɗa computer take
tana ƙara sanarwa.
A nutse ya ware rawani kansa domin duk a zaton shi, shi kaɗai ne a cikin vip ɗin,
kyakkyawar sumar shi ta bayyana abin mamaki ilahirin sumar kan shi daga gaba jajir
take tamkar wanda ya fara furfura, daga baya kuma baƙaƙirin tai luff har wuyan shi.
Ya sauke hannunsa akan Alkyabbar jikinsa ya ɗan buɗe gaban kaɗan sbd nauyi da tayi
masa, yana kammalawa yaja blet, daidai lokacin aka fara sanarwar a shirya jirgi zai
tashi, Halisa ta razana ta ƙanƙame jikinta, kanta ya shiga juyawa sai tayi nan luu
tayi nan luu, lokacin da jirgi ya ɗaga zuwa sama Yaa Sheikh ya lumshe idanunsa ba
zato ba tsammani yaji an fasa wata gigitacciyar ƙara kafin ya buɗe idanu ta faɗo
kan cinyarsa babu numfashi....

Paid
It's 500
08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: Da fararen idanunsa masu tsari yake bin ta da idanu da mamaki,
ganin da gaske bata mutsi tsoran da ya yi mata yawa ya sanya numfashinta ya ɗauke,
hannunsa basu taushi ya sanya akan fuskarta kamar mai jin tsoran gently ya shiga
bubbuga kumatunta amma ko motsi ba tayi ba, ya ɓata fuska ganin tun ba a je ko'ina
ba, yarinyar zata fara bashi wahala.
Yatsun hannunta biyu ya kama yaja da ƙarfi yana buga tsakiyar kanta ajjiyar zuciya
ta sauke da ƙarfi tana jan numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana riƙe wanda taji
kusa da ita sosai cikin fillatanci take faɗin.
"Don Allah ku sakko dani ƙasa zan mutu wayyo Dada wajanki zan dawo" saukar
numfashin da yaji yana sauka a fuskarta da ƙamshin da ba zata manta da shi ba ya
sanya ta buɗe idanunta wanda ta rufe su saboda tsoro, wanda ta gani take jikinsa ya
bata mamaki numfashinta ya kusan ɗaukewa, sbd yadda ya yi mata kwarjini a idanu ga
Alkyabbar jikinsa duk ta rufe mata jiki, a jikinsa yaji shi take kallo bai kalleta
ba, ya sanya hannu tare da riƙo kafaɗunta da kyau yana zaunar da ita akan kujerar
sosai.
Yana daga inda yake ya ranƙwafa sosai tare da miƙa hannu zuwa inda blet ɗin take,
kwantaccen sajansa ya shafi fuskarta ta sauke numfashi mai zafi wanda ya sanya Yaa
Sheikh daka tawa da kama blet ya jima kafin ya zaro blet

Please Login or Register in order to submit comment