You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fito da Halisa wacce take jera
breakfast a dining room, suka kalli juna Halisa ta ɗauke tana faɗin "Ina kwana?"
"Lafiya lou" ta faɗa tana murmushi ta ƙara da cewa "Sannu da aiki, ya jikin naki da
kin kira na tayaki aiki ai" Halisa ta ce "Don my me, zan iya" ƙamshin turaren shi
ya bayyanar musu da sakkowar shi, Suka juya kusan a tare wani irin kallon ya kewa
Halisa da sauri ya ɗauke kai yana gyara zaman alkyabbar shi, Halisa ta daure bata
je gare shi ta rungume shi kamar yadda ta saba ba, duk da cewa girkin ta ne amma
babu daɗin yin haka gaban Zahrah.
Ya ja kujera tare da zama Zahrah ta ce "Ina kwana?" Ya yi mmki domin bata taɓa
gaida shi ba bisa ra'ayin kanta. Ya jinjina mata kai Halisa ta zuba masa breakfast
kana ta zubawa kanta, Zahrah ma babu kunya taja plast ta haɗa tea. Shiru wajan ya
ɗauka Yaa Sheikh yana lura da yadda Halisa ke gumi sbd azabar yaji, ya dubi abinda
ta ke ji ganin bai san mene ba, ya saka hannu ya ƙwace plate ɗin ya tura mata
soyayyan ƙosan daya sha kayan ƙamshi da tea mai kauri wanda bai ƙarasa sha ba. Ta
ce "Nifa shi na keso" Ya ware gajiyayyun Idanunsa akanta ba tare da ya ce komai ba,
ta fahimci shirun nasa ta ce "Ɗan silif ne wallahi daɗi sosai Habibi" ya ajjiye
bottle water yana goge bakinsa da tissue ya miƙe yana faɗin.
"Duk an gama zuba yawo ciki" kamar jira take ta ce "Wata rana sai na ɗore maka
yawon cikin baki" Zahrah duk sai ta zama uncountable kamar wata maid, sosai taji
yadda suke wasa da dariyar kamar wa da ƙanwa sun birgeta, she wishes ace ita Yaa
Sheikh ya kewa haka. Ta goge Hawayen daya zubu mata a ɓoye.
Can ya zauna saman kujera ya ce "Jeki Library ki ɗakko ƙawa'idi guda uku" ta ce
"To" tana barin wajan ya ce "Fatymerh Zahrah" ta amsa da "Na'am" da hannu ya ce ta
zo. Ta miƙe ta dawo wajansa ya kama hannunta ya ce "Kina lafiya?" Ta amsa da
"Allahamdulillah" ya jinjina kai yana riƙe da hannunta har Halisa ta dawo, sosai ta
gani amma bata nuna ba ta koma gefensa ta zauna suka sanya shi tsakiya, ya buɗewa
Zahrah babin da zai musu, yasan Halisa ta sani amma baya son nuna bambanci itama ya
amsa ya buɗe mata. Cikin sanyi da taushin murya ya ce.
*Babin raɓewa wanka*
Ya yi shiru, cikin nutsuwa ya shiga bayanin kamar yadda ya yi wa Halisa lokacin da
suke garin Makkah!. Ya ɗora da faɗin.
"Akwai wakan jinin haila, Janaba na jima'i, wankan jinin biƙi, wankan juma'a,
wankan shiga garin Makkah, wankan mutuwa, shi ne rabe-raben wanka" sukai shiru baki
ɗaya musamman Zahrah ya ɗora da faɗin.
"Janaba: Janaba ɗaya ce daga cikin abubuwan da suke wajabta wanka, wanda yake
hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar haka; *Fitar Mani* Idan maniyyi ya fita
daga mace ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin wankan ya wajaba sai ya zama
maniyyin ya fitane ta hanyar jin daɗi, kamar kallo ko wasa ko tabe-tabe ko
jingina.., amma idan ya fita ba ta hanyar jin daɗi ba ya fitane ta hanyar wahala,
kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma wutar lantarki ta ja shi, to wannan
wanka bai wajaba a kan shi ba sai da kawai ya yi alwala. Shi wannan fitar maniyyi
da ake Magana akan shi ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana barci, idan ya
fita ana farke shine ake maganar an ji dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana
barci ne to ba wata maganar jin dadi wanka ya wajaba"
Yanayin yadda yake bayanin kaɗai ya isa ka fahimci magana bata dame shi ba, shi ya
sa gabaɗaya ko wa'azin shi za'a tura mutum ake jinsa muryarsa mai sanyi ce cikin
haiba ya ce
"Na biyu, saduwa da iyali idan har an tabbatar miji da mata sun zama turmi da
taɓarya babu shakka wanka ya wajabta a gare su, inma namijin ya fitar da maniyyi ko
mai fitar ma haka ma macen, idan mutum sai sadu da Iyali sau goma to wanka ɗaya ne
ba goma ba.Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so ya jinkirta wankan janaba zuwa
an jima to abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala, domin alwalar tana
rage kaifin janaba, sannan kuma tana kara kuzari lokacin da ake so aƙara saduwar.
Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi
kamar yadda bayani ya gabata, to bayan ya yi wankan sai kuma ya ga maniyyi ya zubo,
to anan idan wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan maniyyin wani wankan ya kama
shi, amma idan janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo yanzu to alwala kawai
zai yi" Ya rufe littafin yana amsar ruwan da Zahrah ta miƙa masa ya sha kaɗan ya
ajjiye ya ce. "Mu tsaya nan, sai gobe In shaa Allah, kafin nan ga yadda ake wanka"
Suka kalle shi ya kame fuska ya ce
"Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai siffatul ijza' (ta
wadatar), kuma wacce
ake kira siffatu
kamal' (ta kamala). Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi
ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da
zaka fara yi shi ne: zaka karkato bakin
mazubin ruwanka, ka
wanke hannunka sau
uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka ɗebo ka wanke gaban ka, a dai-
dai lokacin da
zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko
waninsa) wanda yake
wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana
kayi tsarki kenan to
daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a
alwala ta sallah zakayi sai abu ɗaya shi ne wanke
ƙafafuwa to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shi ba, to daga nan sai ka tsoma
hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka ɗebo ruwa ba
sai ka murmurza kanka saboda ko wanne gashi da
ya buɗe a lokacin da
maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya
koma yanda yake, don
gashin dan Adam yakan buɗe musammam
gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka ɗebi ruwa a cikin tafin hannun ka ɗaya sai ka zuba a
kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya
game ko'ina a kanka,
haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka. To idan kayi wannan sai
ka ɗebi ruwa ka game
dukkanin jikin ka da shi
kana mai farawa da
ɓangaren jikin ka na
dama kafin na hagu, sannan na hagu ka
tabbatar ruwa ya taɓa
ko'ina. To idan kayi
wannan ne ka kammala,abu na ƙarshe shi ne sai
ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka tahagu shine cikon alwalarda ka riga ka
faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba. In wankan janaba ne
haka zakayi, in na haila
ne haka za'ayi inma
wanka ne na biƙi haka
mace zata yi, idan
wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi
ma haka zaka yi,
banbanci kawai shi ne
NIYYA" Halisa ta kama hannunsa ta ce
"Allah ya saka da alheri Yaa Sheikh, Allah ya ƙara basira da ilimi mai amfani ya sa
matar malam ta ɗauki halin Malam" Ya girgiza mata kai, Zahrah ta goge hawaye a ɓoye
ta ce "Thank you so much Sweetheart really appreciate" Ya miƙe tsaye yana gyara
zaman alkyabbar da hiramin kan shi ya ce
"Allah ya yi muku albarka" Halisa ta miƙe tana maƙalewa gefensa ta ce "Zan raka ka
mota" Bai ce komai sukai waje Zahrah ta bisu da idanu, addu'a Halisa ta dinga yi
masa kala-kala harda yaji tsoran Allah akan yadda zai taraya dukiyar shi.
Kai tsaye Police station ɗin da ya kai Saif-wazir ya nufa, ya cike komai aka bashi
beli damar kamar ajjiyar shi ya kai, ya nufi gidan Abba Hakimi lokacin Umar-khan ya
shigo tare da iyayen yarinya da hisba suka kama, uwar yarinyar ta dinga kuka kamar
ranta zai fita shi ma kan shi Saif-wazir ya yi laushi ko haɗa idanu ba ya yi da
*Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* kai tsaye kuma Yaa Sheikh ɗin ya nuna auren Saif-
wazir zai haɗa da yarinyar Abba Hakimi ya amince, suka tsayar da maganar nan da
sati mai zuwa ranar juma'a za a ɗaura auren. A nan Abba Hakimi yake shaidawa Yaa
Sheikh an bawa Khalil Ahmad Nuran Sarki auren Maimoon domin ya gaji da sintirin da
yake daga Sokoto zuwa Kano, don haka rana ɗaya za a ɗaura koda Maimoon bata tare
ba.
*_3 weeks ago_*
Har kawo lokacin babu abinda ya haɗa Zahrah da *Yaa Sheikh* haƙurinta ya ƙara
bayyana, bata sake masa maganar komai Halisa cikinta ya girma sosai domin kusan
wata na takwas yake ta kusa shiga na tara ta zama babbar mace. Abu ɗaya ke damun
Zahrah yadda take yawan mafarkai da jarirai guda uku suna binta suna kuka duk inda
tayi suna maƙale da ita ɗaya hannunsa riƙe da almakashi, ɗaya safa, ɗaya kuma da
magani duk ta firgita kuma ta kasa faɗawa Yaa Sheikh. Wani lokacin suna zaune zata
sabura tana "Don Allah kuyi haƙuri ban sanku ba, ba yara na bane" al'amarin kamar
wacce zata zauce. Satin daya kama Yaa Sheikh yaso kai Halisa Sokoto can masarauta
amma girman cikinta ya hana shi, ya ɗauketa ya kaita wajan Umma A'isha, Zahrah kuma
ya ce ta shirya su je Yola ta nuna bata so ko kamar iyayenta bata ƙaunar ya yi, sai
da ya yi mata jan idanu ta amince. Yaa Sheikh da Ummul da kuma Zahrah suka nufi
Yola, gaisuwa kawai ke haɗa Ummul da Zahrah suna zuwa suka sauketa a Jimeta. Suka
shige Rugar Bello, har inda Layar take Ummul taje ana haƙowa ta buɗe tas taci karo
da rubutu kamar haka.
*_Kariya ne daga dukkan jinin mai wannan layar, babu shi babu aikata zina, duk inda
zina take mu aljanun Arɗon Rugar Bello mun haramtawa jinin Arɗo raɓar inda take, ko
ya haɗu da makira wacce ta aikata hakan to mazantakar shi ba zatai aiki ba, matarsa
wacce take tsarkakkiya a gare shi ita ce zata same shi, babu mai iya lalata wannan
aikin domin wanann layar bata gaskiya ba ce, ta gaskiyar na wajanmu Wannan shaida
ce domin ku sani, idan wanda ya mutu zai dawo to lallai mazantakar shi wata rana
zatai aiki, idan wanda ya mutu ba zai dawo ba babu shakka shi da wanda ya ke zina
ko ya taɓa har abada......


*Note*
_Masu magana akan auren Yaa Sheikh da zata ba zai taɓa faruwa a zahiri ba,to
wallahi wallahi za kuyi ladama kuma za kuyi kaffara ku saisaita rantsuwarku ni ke
da labari na fiku sanin mene zai faru, babu hujjar da zata saka littafi ya ƙare na
dinga jansa bisa jin daɗina rubutun nan da wahala ba, komai ma rubuta daman a tsare
a yake sai abinda aka cire..... Nayi magana akan wanka na tsagaita bayanin nawa sbd
nauyin wata maganar amma ku bincika littafan Fiqhu, ko Umdatul ahhakam_
[2/11, 12:32 PM] Abk: *_Arewabooks@Na'ima Sulaiman Sarauta76_*
"So that's the reason?" Ummul ta faɗa a ranta tana ƙara kallon rubutun, Yaa Sheikh
ya kalleta kawai, sai kuma ya miƙa mata hannu ta bashi shi ma ya karanta kamar
yadda tayi. Sai taga sam bai damu ba, ko dan ba a gane damuwar shi ne ya sanya
haka? shi ɗin kaifi ɗaya ne kuma mai wahalar fahimta, wannan magana ce mai matuƙar
nauyi Yaa Sheikh kuma ya kasance namiji ba mace ba, bare ta tsaya su tattauna
makomar Zahrah take tunani, bata jin yarinyar a ranta amma tana girmama auren dake
tsakaninta da Yaa Sheikh ɗin, infact Ummul bata ɗauki Zahrah matsayin,Daughter-in-
law ɗin ta ba. Ummul tabi bayan Yaa Sheikh zuwa cikin Rugar Bello domin daga baya
ne inda aka ɓoye layar take tana zuwa ta samu Yaa Sheikh shi da Labo suna magana
wanda ya wancin maganar Labo ke yinta Yaa Sheikh jinjina kai kawai yake sbd
tsananin gajiya, akwai tarin abubuwa a gabansa baya jin zai zauna a Rugar Bello
zuwa wani lokaci. Wata Bukka Labo ya nunawa Yaa Sheikh ya durƙosa tare da shiga
ciki bakinsa ɗauke da Tasbihi. Ya zauna saman wata tabarmar kaba yana tankwashe
ƙafarsa, Ummul ta shigo ta zauna ba jimawa aka kawo musu Kindirmo fal cikin ƙwaya
da zafinsa, tsananin daɗin Kindirmon ya sanya Yaa Sheikh rufe idanu ya sha son ran
shi a lokacin kewar mahaifinsa da matarsa ne suka lulluɓe zuciyarsa.
Ummul ta ce "To ɗan na gada, sai yanzu ka ƙara fitowa matsayin Fulanin Yola Usul
kuma cikakke, Fulanin ma ɓangaren makiyaya masu dukiya"
Ya dubi Ummul ɗin tasa yana janye ƙwayar ya ce
"Fulani da Barebari ba a zama lafiya fa naji"
"Wani ya ce maka ni barebari ce?" Ummul ta faɗa tana watsa masa harara ya yi
murmushi kawai yana lumshe idanunsa, a wannan daren Yaa Sheikh ya zauna da ƴan
uwansa Fulani ya shaida musu baya buƙatar maye gurbin mahaifinsa kawai su kasance
masu adalci wa juna, banda ƙyashi da hassada, Yola ita ce mahaifar shi duk da ba a
nan aka binne cibiyar shi ba. Washegari suka ƙarasa Rugar Rome, yaso da ƴar
fillonsa ya zo idan akwai abin da ba zata manta ba, shi ne rayuwar da tayi a cikin
wannan Rugar, da dukkan wanda yake cikinta ba zata manta da su ba. Shatu ta ƙara
girma da wayo, Ummul ta tambayi umarnin tafiya da ita aka bata, zo kaga murna wajan
Shatu.
Zahrah ta share hawayen idanunta ta kalli Mimi ta ce "Baki taɓa zaunar dani kince
abin da nake ba daidai ba ne, kina cewa na maida hankali a karatu amma me ya sa ki
banbanta mini karatun boko dana addini, baki nuna mini yadda zan samu lahira ba sai
ki ka nuna mini yadda zan san duniya, ita ma ta sanni"
Ta fashe da kuka sosai numfashinta na riƙewa Idanunta ya yi jajir cikin zaucewa ta
ce
"Nayi rayuwa irinta dabbobi, na zama jahila na kuma zauna cikin jahilanci, kun
cutar da rayuwata tun ina ƙarama da wando da riga na buɗe idanu da sunan sune kaya
na, ina 4yrs kuka sani play grp, na san kun sani islamiyya ban san yaushe na daina
ba, ban kuma san dalilin daya sanya na daina ba, ina shigar da bata dace ba, ina
fita inda nake so kina ganin sauyi a jikina amma baki taɓa cewa fitar da nake bai
dace ba....," Yaa Sheikh dake bakin ƙofa shi da mahaifin Zahrah Alhaji Farouk ya ce
"Kee!!"
Ya faɗa cikin ɗaga sauti, hakan ya sanya ta tsaya da maganarta fuskarta tayi caɓa-
caɓa da hawaye ga majina ta ce
"Sweetheart ranar wanka ba a ɓoye cibi, duk halin dana shiga she's the reason
behind"
"Ki fahimta Zahrah, bayin kai na ba ne soyayyar da muke miki ya sanya idanunmu ya
rufe bama son damuwarki, bama son duk wani abu da zai baki matsala a rayuwa,
tunanina kullum zamu rasaki" Zahrah ta fashe da dariya while kuma hawaye na zuba
daga idanunta ta ce "Gaskiyar bahaushe, daman ance ka ƙi naka duniya ta so shi,
kaso naka duniya ta ƙi shi, tun banje ko'ina ba ina ganin ishara kala-kala a
duniya, Ubangiji ya fara hukuntani da soyayyar wanda bana ran shi, kullum ji nake
zuciyata kamar zata fashe naji kamar na bar gidan Yaa Sheikh" Ta girgiza kai ta ce
"Soyayyar da nake masa ta rinjayi duk abinda zuciyata ke raya mini, motsin Yaa
Sheikh kawai idan naji yana sauƙaƙa mini ƙuncin da kuka jefani da halaka na tsayin
shekaru, balle nayi tuzali da fuskarsa sai naji iya hakan kawai ya wadatar dani"
Ta miƙe tsaye tare da dawowa wajan Yaa Sheikh ta ce "Ba miji na ɗauke shi ba, ina
masa kallon Yayana ne, wanda zai iya tsare mutuncina, ya fito dani daga ranar da
kuka sanya ni zuwa inuwa, na gane bambanci mai ilimi da jahili na gode Allah da bai
barni na dauwama haka ba, balle na zo duniya a banza na koma a iska"
Tas ta goge hawayen idanunta ta ɗauki mayafi ta yafa ta ce "Muje Sweetheart"
"Fatymerh Zahrah!"
Yaa Sheikh ya furta iya gareta, ta kalle shi sai tayi murmushi ta ce
"Wallahi ba zan ƙara kwana a gidan nan ba, kuma daga yau su ɗauka basu taɓa haihuwa
ba balle su tuna suna da yarinya kamata, wannan shi ne girban abin da suka shuka"
Mimi ta fashe da kuka ta kasa magana ta zube a wajanta ta ce
"Ni ɗin wacce irin uwa ce mara lura da tarbiyya me zan faɗawa Ubangiji"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Alhaji Farouk ya furta, yana cikin masifa
goma da ashirin.
Ta kama hannun Yaa Sheikh dake tsaye bai tanka musu ba, ya juya ya bita zuwa
compound Ummul na zaune cikin mota domin daga nan Airport za su shige, ta dinga
kallon Yaa Sheikh da mmki ya shaida mata a nan gida zai bar Zahrah amma ya akai
suka fito tare. Zahrah ta saki Yaa Sheikh ya dubeta cikin nutsuwa da tarin kulawa
yana ɓoye yanayin da yake ciki ya ce
"Iyaye fa?" "Na yafe musu, nima yafiyar Ubangiji nake nema ko zaka dubeni da idanun
Rahama ka tuna nima matarka ce ka bani kulawar da nake so"
"Ina son barinki nan" ta kalle shi da mmki sai ta ce "Zaka iya barina, amma kana
fita zan fita zanje duk inda Allah ya nufa na san ba zan wulaƙanta ba, amma yanzu
kai Allah zai tambaya tunda ina ƙarƙashin ka"
Ya rasa bakin yi mata bayani ta fashe da kuka sosai ta tsuguna daidai ƙafarsa ta ce
"Ni ɗin daman ai ƙaddarar ka ce, amma don Allah kaji tausayina ko zauna dani
kulawarka kawai na keso ba wani abu ba" ta ƙara sakin wani raunataccen kuka mai
ciwo da cin zuciya ta ce "Tun ina jin haushin Matarka har na dai na, ganin son da
ka ke mata na fara son ta ko za kaji tausayina" ya numfasa yana riƙe kansa dake
sara masa.
"Stand up" ya faɗa a taƙaice. Ta ƙasa miƙewa sbd kukan da yaci ƙarfinta ya saka
hannu ya miƙar da ita, tana tashi ta faɗa jikinsa ta ce
"Rayuwata bata da amfani Yaa Sheikh nayi ladama, soyayyarka zaka kashe ni" jin
numfashinta na fita da ƙyar yana ɗan bata side hug yana bubbuga bayanta alamar
rarrashi. Ta shiga sauke ajjiyar zuciya a hankali ya zareta suka nufi mota ya nuna
mata gaban mota, shi kuma ya shiga baya kusa da Ummul suka nufi airport.
Alhaji Farouk yana tsaye ya zama kamar statue yaji ƙarar notifications yana dubawa
yaga an zare kuɗi daga acct ɗinsa kuɗi masu yawan gaske. Kafin ya motsa bank sun
kira shi sun bashi tabbacin ya samu hackers sun kwashe masa kuɗi, gumi ya dinga
yanko masa yana zubewa wajan. Kafin ya ƙara wani tunani manger kamfanin shi ya masa
waya yanzu haka kamfanin ya kama da wuta. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un wayo
Allah Allah na tuba Allah ka tausaya mini Allah ka dubi idanuna ka yafe mini" ya
dinga faɗa yana fashewa da kuka. Karayar arziƙi ta dimfaro shi..... A hankali yake
ware idanunsa akan harabar Orphanage ɗin na shi cikin nutsuwa da tarin kamala ya
murza yatsun hannunsa yana duba lokacin tare da tunanin inda Umar-khan ya tsaya,
slowly ya ɗago kan shi cikin sa a ya sauke idanunsa akan Umar-khan shi da Hafsat
suna hira kamar sun jima da kamuwa da junansu, Ya girgiza kai kawai tare da komawa
ya jingina da jigin motar shi. Beeherh ta taho da gudu ta ce
"Abbana shi ne tun daga ranar nan baka dawo ba, kuma Mumy bata zo ba?"
Ya durƙosa ya ɗauketa yana kallon Kyakkyawar fuskarta ta yarinyarta ga baby hijab a
jikinta ta saka hannu ta fara wasa da gemun shi ta ce
"Ni yau wajan Mumy zan kwana" Yaa Sheikh ya fesar da numfashi ya ce
"Rigima Beeherh,yau za kiga Mumy" daidai lokacin Umar-khan ya ƙarasu Hafsat ta
durƙusa ta ce "Ina yini Abba" ya jinjina mata kai yana buɗe bayan mota tare da saka
Beeherh ciki, Umar-khan ya shafa kan shi ganin kallon da Yaa Sheikh yake masa.
Cikin rawar murya ya ce "Uhm dama....dama...dam"
"Mene haɗinku?" Yaa Sheikh ya katse kunyar Umar-khan cikin inda inda ya ce "Yaa Lee
ina son Hafsat ne, ina son aurenta idan ka bani dama" Yaa Sheikh ya kalli Hafsat ya
ce "Kina son shi?" Ta kasa magana sbd kunya ita duk duniya ta yarda ta kuma amince
Yaa Sheikh shi ne babanta domin a wajan shi ta tasu "Uhm"
Sanin halinsa tayi saurin cewa "Eh Abba" tana faɗa ta kwasa da gudu tayi ciki. Ya
girgiza kai, Umar-khan ya buɗewa Yaa Sheikh mota ya shiga, daman yau gabaɗaya
kamfanin shi dake kano ya zaga wanda suke wata jahar ne bai je ba....kafin su zo
gida Beeherh tayi barci Halisa dake zaune a parlour da ƙaton ciki haihuwa Yau ko
gobe ta miƙe da ƙyar tana riƙe kujera cikin saurinsa ya ƙarasu tare da kwantar da
Beeherh ya kama Halisa ya zaunar da ita a ƙasan carpet ya ɗauki pillow ya saka mata
ta ɗora ƙafarta tayi murmushi tana jan hancinsa ta ce
"Na gode Yallaɓai" Ya zauna yana danna mata ƙafar cikin tsananin so da kulawa wacce
kullum take ƙara yawa a zuciyarsa ya lumshe idanunsa jin tayi masa wlcm da zazzafan
kisses ɗita tun daga bakinsa har zuwa wuya suka kalli juna ta ce "Sannu da zuwa" Ya
jinjina kai sbd ya gaji da gaske, gashi bashi da burin fita wata ƙasar. Ta kalle
shi ta ce
"Yarinya muka samu?"
Ya kalli Beeherh dake barci a nutse ya ce
*"Beeherh Sheikh Aliyu haydar Aliyu"* ta ce
"Yaa Sheikh mai yara da yawa" Yana shafa cikinta idanunsa tuni ya juye ya ce "Ina
son yara, sosai ina son nawa na kai na sama da ashirin" ta zare idanu ta ce
"Ashirin tab"
Zahrah dake fitowa hannunta riƙe da Azkar ta ce "Haba Uwar gida kada ki zama raguwa
mana" Halisa ta ce
"Ba wani nan, kiyi masa hanya kawai ya ƙara aure" Yaa Sheikh dai idanunsa a rufe
yake ya ce "Kwana biyu na lura Fatymerh Zahrah tafi jin tausayina" Ya miƙe tsaye
Halisa ta miƙe suka haura sama suna shiga ta cire masa rigar jikinsa ya jawota ya
baya tare da mannata a ƙirjinsa idanunsa rufe yake sauke mata wasu lafiyayyun
kisses masu wahalar fassaruwa ya saka hannu ya farke bra ɗin jikinta ya ƙara farke
under wear ɗin cak ya ɗauke zuwa toilet ta ce "Mene haka kuma" ya ciji kunnenta ya
ce
"Wanka zaki mini".... Mother na zaune a parlour hankalinta gabaɗaya baya jikinta ta
ce "Maimoon bi bayan Fattoumah" Maimoon ta ce "Mother kin san halin Auta da sanyin
jiki daga kai abinci sai ta zauna" Father ya ce "Haba Maimunatu jeki mana" ta miƙe
tsaye tana fita Compound El na fitowa daga mota sanye da kayan police ya yi wani
irin kyau ta ce "Uncle El da yamma" ya taɓe baki kamar zai shiru ya ce "Ban waje
wajan Fattoumah na zo" Maimoon ta ce "Komai Fattoumah idan tayi wari za muji" El ya
buɗe mata idanu ya ce "Ke kuma munafuka halinki ɗaya da mijin naki ai" ta rufe baki
ta ce "Au kana Nufin Prince Khalil munafiki ne?" Ya mata banza tayi dry kawai ta
nufi bakin ƙofar ɗakin gatekeeper ta ce "Baba Fattoumah data kawo maka abinci fita
waje tayi ne?" Shiru ba amsa ta ƙara magana shiru, sai kawai ta tura ƙofar wata
irin gigitacciyar ƙara wacce ta cika compound ɗin ta fasa hakan ya sanya El fitowa
da bindiga a sukwane, da gudu Mother da Father suka fito El-bashir ya ce "Ke
lafiya?" Banda rawa da ɓari babu abinda jikinta ke yi ta kasa magana, El ya shiga
cikin ɗakin kai tsaye idanunsa ya sauka akan Fattoumah dake kwance an ɗaureta da
igiya an rufe bakinta da wani abu, jini na zuba ta ƙasanta alamar fyaɗe akai
mata......


*Masu tambayar complete book's ɗina👇🏾*
Tsintacciya 500
Uncle ne 400
Sirrin mu 500
Abu maleek 500
Sai na aureta 300
Izzar so 300
The new emir 300
👇🏾
Zain Abeed 1,23 ₦1000
Dare da duhu 1000
Idan ba ke 1000
08119237616👈🏾 kuyi magana WhatsApp.
[2/13, 9:24 PM] Abk: *_Arewabooks@Nimcyluv77_*
*Women Adviser*
*Elegant online Writer's leader*
*Hausa Novelist*
*Social media presenter, Ngo, human rights*
Follow the link👇🏾
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL

El-bashir was shocked ya kasa motsawa duk da kasancewar shi Namiji, kan shi ya yi
wani irin sarawa zuciyarsa na harbawa, idanunsa sukai jajir wani irin ruwa ya
kwanta a cikinsu, ya ɗauke kai da sauri daga kan Fattoumah wacce take numfashin
wahala. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya furta a fili.
Cikin sauri kuma ya shiga ciki yana durƙosawa yadda Fattoumah take kallon El-bashir
babu ƙifatawa ya ƙara sanyawa El wani irin tashin hankali a fuskar shi aka ajiye
masa tabon da har abada ba zai taɓa gogewa ba, his whole body was shaking zufa na
yanko masa all over his body.
"Fattoumah!" Mother ta kira sunanta a gigice tana ɗora hannu a ƙirji lokacin da El
yake kunce igiyar jikinsa tare da zare abin da aka sanya mata a baki. Mother ta
saki kuka tana cewa
"Allah ya isa, Allah ya isa, Allah ya isa Ubangiji ya saka miki Mamana ko Uban waye
shi wallahi sai nayi Shari'a da shi"
Ta ƙara sakin wani kukan tana riƙe Maimoon da Zeefa gani take kamar suma haka zai
faru da su yanzu. Ta ƙanƙame su a jikinta ta ce
"Ya Allah wacce irin rana nake gani yau ni Maryamu, wacce jarrabawa ce me ya sa na
aikeki wajan mugu azzalumi Fattoumah, me ki kai masa ya zaɓi ya lalata gobenki da
rayuwarki bakiɗaya Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya Allah da ganin Wannan
ranar gwara

Please Login or Register in order to submit comment