You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutuwa ta"
"Mother ki daina faɗar haka ne ya samu Fattom, me akaiwa Fattom jini ke zuba a
jikinta" Zeefa ta faɗa yarinyar ta gigice da ganin ƴar uwarta cikin wannan halin.
"Maimoon riƙe Nazeeferh ki tabbatar kin kula ku shiga cikin gidan yanzu"
"But Mother" a gigice ta ce "Maimunatu!"
Maimoon ta fashe da kuka ta rungome Zeefa suka bar wajan. Father was speechless
yana ganin idan akwai wanda Mother za tayi Shari'a da shi to babu makkawa shi ne,
domin daman sharri ɗan aike ne, kan me shi yake bi. Faɗin Ubangiji ne, ita zina
bashi ce dole ka biya da hannunka, kama ta diìna tû danò.
Abin da ya shuka yake girba, kashin kajin daya shafuwa kansa ya shafi yarinyar da
bata ji bata gani ba, yarinyar da babu wani kyakkyawan kusanci tsakaninta da shi,
tana ƙyamatar duk abin da zai, tayi masa tsana ainun tun akan Yaa Lee, da ƙyar ya
samu ya lallaɓa ta dawo yadda suke. Ya saki kuka.
"Laifi na ne, it's all my fault kiyi haƙuri Fattoumah" El ya ɗauki Fattoumah ganin
yadda take ta razana ta kuma kafe shi da idanu kamar wacce take jira ya taimaketa,
bai ji nauyin Mother ko Father ba ya shiga mota tare da ita a jininsa cikin sauri
Mother ta nufi gida tana ɗaukan mayafi da key car.
Tasan yadda El yake a fusace da wahala ta same shi, Father ya ce
"Jirani mu tafi tare"
Tayi masa wata muguwar harara tare da yin ƙwafa ta shiga mota tana danna horn ta
mance babu gatekeeper babu alamun shi.
Bai taɓa jin ladamar abinda ya aikatawa Zahrah ba sai yanzu, kunyar haɗa idanu da
duk wani na shi yake uwa uba kuma Mother wacce yake jin babu wacce zai kaita jin
zafin abinda ya faru idan akwai bai shige *Prince El-bashir Ahmad Nuran Sarki* ba.
Ya jima da fahimtar shaƙuwar dake tsakaninsu ba wai iya haɗuwar jini bane, hadda
abin nan da ake kira da _Blind love, first love between heart and heart_.
Bai san ya akai ba, kawai ya ganshi ya yi parking a harabar Aminu Kano teaching
hospital! Ya buɗe mota muryarsa was shaking ya ce
"Nurse, Nurse, Dr"
Cikin sauri wasu Nurse's suka zo suna janye da gadon marasa lafiya ganin shi ɗauke
da kyakkyawar budurwa or under age baby, Fattoumah. She's 14 yrs old going to 15
amma tana da jikin girma so ma sha Allah, kaf cikinsu tafi kowa fuskar kamala tana
da idanu masu sanyi bata son hayaniya, but she's so cute damn cute irin shhhhh ɗin
nan..
Tana da kafiya da zuciya hakan yasa suke zaune da El lafiya komai ta ce Uncle ɗina
ko tana kuka Mother ta ce ke da waye?
Sai ta ce " *UNCLE NE*"
Suka amshi Fattoumah daga wajan El wata ta ce
"Sir You have to change your clothe ya ɓaci da jini" A dame ya ce "Owk" was what
she's sayed to him. Ganin El da police uniform ya sa basu tsaya tambayar police
cikin Raped case ɗin ba.
In few minutes El ya kira Sergeant ya shaida masa, Sergeant ya kira C.F.P
Commissioner of Police. Daga nan ya kira Human rights, wanda suke da haɗin gwiwa da
Ahip tare da Ngo.
Yana nan tsaye Mother ta ƙarasu a gigice ta ce
"Mubasshir Ina Mamana"
"Clam down, she'll be fine" ta dafe kai tana kuka ta ce "Mubasshir ina cikin tashin
hankali, ace mai gadin gidana the old man ya yi rapping ƴar cikina, mai yasa har
yanzu ba a maganin masu fyaɗe ne? Zan tabbatar daga kan Fattom babu wanda ya ƙara
aikata fyaɗe a jihar Kano" Ta rushe da kuka ta ce "Ya lalata rayuwar Fattom gobenta
nake ji wacce irin jarrabawa ce, mai yasa baƙin halin Ubanta zai sauka kanta?"
Ya kama hannunta har zuwa emergency ɗin ya zaunar da ita, ya kasa cewa komai
zuciyarsa ta tsaya da aiki ya zama kamar wani statue..... Yaa Sheikh ne ke tafiya
cikin kamfanin sarrafa shinkafar shi yana mai lura da komai, cikin nutsuwa yake
jinjina kan shi yana sauraran abin da Umar-khan yake faɗa masa. "An kammala komai
gobe za a fitar da container goma, kafin zuwan azumi dai zamu fitar da containers
kusan 200" he just nodded his head. Silent ringtone ne ke tashi ya zura hannunsa
cikin aljihu ya ɗauki wayarsa Samsung ganin sunan wanda ke yawo saman wayar ya
sanya ya yi jim yana tunani gently kuma ya yi answering call ɗin yana lumshe
gajiyayyun Idanunsa tamkar mai jin barci. Ya kara a kunne.
"Mubasshir Ahmad Nuran Sarki" Yaa Sheikh said. Sbd jin El ya yi shiru sai ajjiyar
zuciya yake saukewa, a hankali kamar zaiwa Yaa Sheikh kuka ya ce "Abba"
"Speak,Son." Cewar Yaa Sheikh yana mai da hankalinsa zuwa ga wayar sbd raunin El
daya bayyana ta ciki.
"Amma zuciyata babu daɗi, anci mutuncin wacce a keso nake burin aura Abba"
Yaa Sheikh ya yi shiru yana jin maganganun ya kasa fahimta. Halin Yaa Sheikh daya
sani ya sa El ya ce "My girlfriend was raped" ya ƙara da faɗin
"I mean Fattoumah"
Ya runtse idanu, yana kiran sunan Allah a zuciyarsa cikin kamala ya ce "Where are
you now?" "At hospital, Aminu Kano teaching hospital" ƙit, ya kashe kiran yana juya
zuwa harabar kamfanin nasa hannunsa ɗaya riƙe da Alkyabbar jikinsa ɗaya kuma yana
shafa gemunsa, Umar-khan ya biyo bayansa da sauri tare da buɗewa Yaa Sheikh bayan
mota, shi kuma ya nufi gaban mota tare da yi mata key suka nufi hospital. Cikin
ƙaramin lokaci Family suka san abin da yake faruwa, hatta Dada ta bata garin kano
al'amarin ya risketa, Abba Hakimi ya dubi Mother ya ce
"Ina ne garin su Mai gadin?" Idanunta ya yi jajir ta ce "A Ɗan-batta yake" Ya dubi
Ishaq-Hakim ya ce "Amshi Address da komai, na yi magana da police kaje ayi
arresting nasa" "To, Abba."
Ya fita waje, Yaa Sheikh da kansa ya ƙara duba Fattoumah tare da yi mata ɗinki
yadda yake girgiza kai da yadda idanunsa sukai jajir zaka san cewa zuciyar Maza
Aliyu ta motsa.
"Uhm ba kullum ina faɗa ba ana mini kallon ƴar hau, ƴar guguwa? Kawai ka ɗauki
ƙaton banza a gidanka kace wai mai gadi bayan kana da zataran ƴan mata balagaggu a
gidan" ba wanda ya kula Jadda ta ƙara cewa "Ga irinta nan, kayi mugun gado ita
daman zina rance ce ka fara biya duk akan Zara'u Allah yaga son da na kewa yarinyar
nan wallahi da Munari ce ba zan damu ba" Ta fashe da kuka sosai tana matse ƙwalla
ta ce
"Masifa yanzu Haruna idan babu damuwa kawai ka tattara yaran nan ka riƙe wajanka
ina tsoran a ɗirkawa wata ciki a gidan nan, shi ya sa ake son mutum ya aikata abu
mai kyau ba komai yake zama ƙaddarar bawa ba, hadda son zuciya, kayiwa ƴar wasu
anyiwa taka"
"Jadda ki daina wannan maganar" ta miƙe tana kallon Uncle Bashir ta ce
"Algungumi gaskiya ce baka son na faɗa ko? ai dama ƙawata Didi na nan tabbas da mun
haɗu munci mutunci ko wanne ɗan banza, ai duk tare mukai ƙuruciya tasan halin uban
baku club club ba wanda bai sani ba a faɗin jihar Kanon dabon lijeriya"
"To Allah ya kyau"
"Ya kyauta abin da ya fi haka ai, kawai ya cuci yarinya ni wanda zai aureta nake
tunani, mazan yanzu daba kunya gare su ba"
"Ko yanzu aka ɗaura mini aure da Faɗimerh na shirya" Jadda ta kalli El ta ce
"Allahu Akbar, kun wanda bai damu da duniya ba ko? To ubanwa zai hanaka auren
Zara'u"
Fitowar Yaa Sheikh daga cikin wani emergency room ya sanya Jadda yin shiru tana
kallon Yaa Sheikh wanda ya ƙara cika idanu fiye da baya, bai kula kowa ba ya nufi
wani office kai tsaye yana dafe kansa yadda yaga jikin Fattom ya yi ya sanya shi
shiga cikin tashin hankali, baya son depression and stress su kama shi, Ya rufe
idanu da kyau da sauri ya buɗe ganin yadda yake hasko cin mutuncin da tsohon ya
yiwa Fattoumah. Zuciyoyin kowa babu daɗi babu kamar Barrister Maryam da IGP kuma
Prince El-bashir Ahmad Nuran Sarki. Tana ganin an gama lalata rayuwa da goben
ƴarta, abu ne wanda kan iya zama tabo a zuciyar Fattoumah za kuma taji zafin
mahaifinta Father da gaske idan ta san cewa shi ne sila, El yana ganin kamar shi
aka ruguzawa rayuwa anci mutunci his fiance, an lalata kima da darajar uwar yaran
shi... Halisa na zaune gabaɗaya yau bata jin daɗi ko sallah a zaune take cikinta ya
sakko ƙasa sosai tun safen kuma ruwa ke fita a jikinta gudun kada ta tayar da
hankalin Yaa Sheikh ya sanya bata gaya masa ba, shima ya lura sai ya kawo rikici ne
kawai irin nata domin tun jiya faɗa take ji da shi abu kaɗan zata ce ita ba haka
kai ni ka fita ma daga ɗakin kawai, ya kan lallaɓata a samu zama lafiya. A lokutan
ya dawo dayin azumi cikin kullum yana lazumtar ko wacce rana gudun faɗawa halaka,
baya iya kusantar Halisa sbd condition ɗin ta, Ga Zahrah zero take gare shi baya
iya komai. Zahrah dake kallo ta dubi Halisa data ɗan ja tsaki ta ce "Lafiya kike
dai ko?" "Uhm lafiya" was abinda ta ce. Wayarta ta ɗauka ta kira Mother tana ta
ringing ba a amsa ba, can ta kira ta Maimoon babu jimawa ta ɗaga jin muryarta babu
daɗi ya sa cikin dauriya Halisa ta ce
"Moon lafiya?" Maimoon ta fashe da kuka ta ce
"Mai gadin Gidanmu ne ya yiwa Fattom fyaɗe" Halisa ta miƙe tsaye sai kuma ta ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!"
Wani irin murɗewa mararta tayi, lokacin guda bayanta ya riƙe ta kasa motsawa cikin
tashin hankali ta yarda wayar sbd tasowar wani irin masifaffan ciwo mai kama dana
mutuwa a firgice ta ce.
"La'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah S.a.w wayo bayana wayyo Abbana zan mutu"
zufa ta shiga yanko mata cikinta ya shiga rawa da ɓari na tsananin ciwo.
"Subuhanallah ba dai naƙuda ba Halisa" "Kira mini Abbana mutuwa" Zahrah ta gigice
tausayin Halisa ya kamata domin bata mance wahalar data sha lokacin haihuwar
Muhammad ba, Halisa na kuka Zahrah na kuka suka rasa yadda za suyi, cikin sa a
Zahrah tunani ya faɗo mata har zata kira shi da number sai tayi tunanin idan da
number Halisa ta kira zai fi ɗagawa, tana ɗauka ta shiga ɓangaren calls babu wasu
kira sai number ɗaya wacce a rana sai ayi waya goma da number babu suna sai Double
kisses a jikin number tayi kiran number ba jimawa ya ɗauka, cikin nutsuwa daman
kiran nata yake jira jin shiru ya sanya Yaa Sheikh sauke numfashi yana rufe
idanunsu tare da lafewa jikin kujera ya ce "Kankanaty"
"Ba ita ba ce" Ya zaro idanu sai kuma ya basar ya riƙe kansa da kyau ya ce "Sorry
Wife"
"It's okay, Halisa wanted to speak with you"
"Oh!" Ya ce yana rufe idanu jikinsa ya saki. Ihun! Halisa ya sanya Yaa Sheikh buɗe
ido yana furta "Yaa Rasulullah!" Cikin kuka da ciwon dake cinta ta ce
"Abbana zan mutu, cikina, marata, bayana babyn zai fito ta baki wayyo Allah na
mutuwa zan yi" Ya runtse idanunsa ya miƙe cikin nutsuwa duk da a rikice zuciyarsa
take ya ce.
"Yi addu'a, Zahrah karɓi waya" Halisa ta ƙara wani kukan da gaske ji take ba zata
rayuwa ba.
"Wife" Zahrah ta ce
"Na'am" ya ce
"Can you drive?" "Sure"
Ta ce tana riƙe Halisa wacce jikinta ke rawa ta durƙoshe tana yarfe hannunta, kukan
Halisa duk ya dagula masa lissafi ya ce "Fito da Zawja ina tunanin motar ta akwai
mai maza zuwa Aminu Kano, kiyi driving a nutse"
"In sha Allah sweetheart ka kwantar da hankali" ta miƙe zuwa part ɗin Halisa ta
ɗakko mata ƙaramin hijab wanda ba zai takura ta ba, itama ta saka hijab da ƙyar ta
iya miƙar da Halisa zuwa shiga mota ta sakata a baya, cikin nutsuwa take driving
lokaci zuwa lokaci take cewa "Sannu ki dai na kuka"
Yaa Sheikh ya nufi labor room ba tare da sanin kowa ba, ya cire kayan jikinsa
idanunsa kwance a mararsa wacce ta kumbura yana kallon yadda kayan aikinsa suke
numfashi ya ɗauke idanu ya zura wata green riga da hula tare da mars a fuska
hannunsa ya saka safa, baya aiki a hospital amma yana da right na shiga duk
hospital ɗin da ya yi niyya.
Yana fitowa ya samu Police sun dawo ɗauke da tsohon El ya shaƙi wuyan shi yana duka
ya ce "Wannan dandatsa ya dace ayi masa" Jadda ta ce "Alkur'an a gutsire
tsinanniyar abar uban kowa ya huta"
"Kada ku ɗauki doka a hannu fa"
"Har abada ba zan huce ba, idan ba nakasta shi nayi ba" Jadda ta zuro kanta ta
tsakanin ƴan sandan ta ce "Ka rugurguza mazakutan shi kawai, ɗan hau daga gani
daman ya daɗe yana sharholiyya"
"Ba haka za ai ba"
Cewar Abba Hakimi, ya juya zuwa ga El ya ce
"Abokina Mubasshir sake shi" El yana huci ya kalli Abba Hakimi ya ce
"But grandfather"
"Mubasshir!" Yaa Sheikh ya kira sunan a tsawa ce, cikin sauri El ya saki tsohon har
ya juya ya dawo da baya tare da dunƙule hannu ya daki bakin tsohon, abinka da dokan
police nan take haƙora biyu suka zube, ya ƙara dunƙule hannu ya daki gaban tsohon
ya ƙara dokan gaban wajan kayan aiki wani ihu! Tsohon ya kurma jin kamar an saka
almakashi an gutsire abar sbd tsananin azaba cikin azaba ya fice daga world ɗin.
"Algungumi tsohon najado, da ƙyar kaga Annabi ai mai kayan ɗan sandan can ɗan gidan
sarkin Sokoto ya kyauta, so nayi a cire munafukar abar a zura a leda a dinga shela
da ita ana nunawa sbd masu halin ƴan taure irinsa"
Mother har lokacin kuka take, Dr A'isha da bata jima da zuwa ba ta dinga bata baki,
Yaya Halima kuma bata ƙasar.
Ganin Yaa Sheikh cikin kayan aiki na likitoci wanda sukai masa kyau da gaske ya
sanya suka dube shi kafin suyi magana ya ɗaga wayar shi da sauri ganin Zahrah na
kira, jinjina kai kawai ya yi ya nufi waje.
Da hannu ya yiwa Nurse's nuni da gado suka biyo bayan shi janye da gadon yana zuwa
Zahrah na fitowa lokacin Halisa ta gama fita daga hayyacinta sunan Allah kawai take
ambata, ya ɗauketa da kansa zuwa gadon suna zuwa Mother ta miƙe ta ce "Ya Salam
Daughter haihuwar ce" Halisa ta saki kuka ta ce "Mother haka Dadata taji da zata
haifan, wallahi ba zan ƙara ciki ba, na gama haihuwa ni na tsani Abbana bana son
shi wayyo mutuwa zan" Jadda ta buga tafi ta ce "Ƴar jakar uba lokacin da kike sake
jikinki ya luguda ubanwa ya sani, ai shi namiji ba ruwan shi wai azaba ranar
haihuwa ake ji daman" Dr A'isha ta miƙe ta ce "Lemme help you" Yadda Halisa keyi
dole ta baka tausayi ƙarfinta duk ya ƙare jikinta ya saki abinda ba a son mai
haihuwa tayi... Dr A'isha ta dubi Yaa Sheikh dake riƙe da hannun Matar Malam ta ce
"Bana jin zata iya haihuwa da kanta....

08119237616
[2/15, 1:01 PM] Abk: Hannu Yaa Sheikh ya saka yana shafa kan ƴar fillon shi yana
mai sauke numfashi da hamdala a ran shi. Idanun Dr A'isha bai hana shi sunkuyawa ya
sumbaci goshi da ƙuncin Halisa ba. Bai san mai zai ce da Ubangiji ba sai godiya.
Cikin lokacin ƙanƙani ya azurta shi da tarin abubuwan masu yawan gaske!
Ita ɗin alheri ce, kyauta ce daga Ubangiji. Ya lumshe idanunsa yana jin abu na
kwanciya cikinsu, sautin kukan babyn na ratsa cikin kunnensa.
"Allhamdulillah!" Cewar Dr A'isha tana zare babyn daga ƙasan Halisa wacce ta
galabaita tare da ficewa daga cikin hayyacinta.
Ta riƙe hannu Modibbo da ƙyar naman jikinta duk rawa yake. Yaa Sheikh kasa taɓoka
komai ya yi, Dr A'isha ta yanke cibiya tare da goge babyn da zaiton kana ta naɗe
cikin showel.
"It's a baby girl"
Ya jinjina kai, fita tayi daga room ɗin, bayan ta kwantar da babyn a baby bed.
Jikin Jadda na rawa ta ce "Ya..ya..ya ya ake ciki" Murmushi Dr A'isha tayi ta ce
"Ma sha Allah, she give birth to baby girl" Jadda ta rangaɗa buɗa ta ce
"Allahu Akbar, Allahu Akbar kaji yarinya da halin manya Ubangiji ka sanya war haka
mu ƙara dawo amsar haihuwa"
"Amin Ya Allah, mene tukuci?" Mother wacce farin cikin saukar Halisa lafiya ya rage
mata kaso 50 na daga cikin damuwarta ta ce
"Tukucin faɗar haihuwar matar malam ai na musamman ne, ki kira mijinta ya zo"
Dr A'isha ta wara hannu ta ce "that's good, kawai zan tura account details"
"Go ahead" suka saki murmushi. Farin ciki ya mamaye zuciyar gabaɗaya Familyn,
haihuwar Halisa ya ƙara zama abu mafi muhimmanci a cikin zuri'ar. Zahrah ita kanta
tayi farin ciki domin ta shiga damuwa.
Shi da kansa ya tura gadon da take kai zuwa resting room, domin sama mata cikakken
hutu. Ya sanarwar da wani Dr ya kawo masa drip da Injection ya sanya mata. Har
lokacin bai bawa kowa damar shigowar inda take ba.
Yana riƙe da hannunta gam! Yana kallon yadda take barci a wahale numfashi na fita
da ƙyar, ya damƙe hannun cikin laushin murya mai cike da tsananin gajiya da nuna
farin cikinsa a fili ya ce "Barakallahu fiik Zawja, meu amor!
So lucky to have you in my life!"
"Ya kamata kaje ka huta, domin kasha ciwo da ya ƙushi, she's so lazy"
Ya kalli Dr A'isha sai ya miƙe yana zame hannunsa daga cikin na Halisa, kai ka
ɗauka shi ne mai haihuwar, duk yadda yaso riƙe kan shi ya gangara.
Yana fitowa Jadda tayi masa ka tana rangaɗa buɗa, ya marairaice domin har tsakiyar
kan shi yake ji, baya son takura ko hayaniya zautar da shi suke.
"Congratulations Yaa Lee" Ya jinjina kai ba tare daya kalli Umar-khan ba.
Dr A'isha ta fito hannunta ɗauke da baby dake barci, Abba Hakimi ya fara amsar ta
tare da yi mata addu'a, kana Father sai kuma Umma A'isha.
Mother tabi kyakkyawar fuskar yarinyar da kallo, babu inda ta bar Halisa, hatta
ƙaramin bakin iri ɗaya ne. Yanayin gashin kanta ne yake kama dana Yaa Sheikh da
yatsun hannunta, wani irin sahihin kyau yarinya ke da shi, gata ƙatuwa tubarkallah
kamar ba ƴar fari ba. "Daughter ta haifi mai kama da ita" Umma A'isha ta ce "Anya?
Kamar ta Malam nake gani shimfiɗe a fuskarta, bakin ne dai na surutu irin na
uwarta"
"Ni fa Ƴar gidan Modibbo babyn ke mini kama"
Dr A'isha ta ce "Sure, They look alike"
Mother ta ce "God made her behave like her father" Sai a lokacin Zahrah ta ce "Kuma
Halisa nada kyan hali, open heart gare ta"
Gabaɗaya sun manta tana wajan, sai kunya ta kama su. Mother ta miƙa mata babyn ta
ce
"Ga Daughter ɗin taku Zahrah" caraf, Jadda ta ƙwace babyn tana zare idanu ta ce
"Allah ya isa, tsakani na dake sai Allah ni ban zan kulaki ba, kowa yasan jinya
nazo, to ba zan zuba idani a bawa kishiya ƴar kishiya ba, salon a shafa mata
taitanos mu shiga uku, a cuci yarinya ko gama zafin haihuwar bata gama ba" Zahrah
ta sunkuyar da kanta ƙasa, haihuwa na taruwa a cikin Idanunta.
Jadda ta ce "A'a fa bawai magana na faɗa ba, balle a ƙullace ni duniyar ga da babu
gasky haka kurum ba za a suɗe mini kurwa ba" "Kiyi haƙuri nifa ba mayya bace"
Zahrah ta furta a raunace.
"Kaji mafisa ko? Babu dama kayi magana sai a ƙullaceka, to aniyyar ko wanne ɗan
ƙaniyya ta bisa duk yadda kaso da kame baki sai an saka ka faɗar zunubi"
Daidai lokacin Yaa Sheikh ya fito cikin wata Jallabiya Ash colour mai laushi da
santsi, ta kwanta sosai saman farar fatar shi, ya naɗe kan shi da hirami.
Yadda fuskarsa ke motsawa tana faɗaɗa zaka fahimci yana cikin farin ciki mara
misaltuwa. Ya dubi Zahrah da ta bar wajan tana goge hawaye.
"Hufii, to don Allah haka ba yafi ba? Da cewa nayi ta tashi tabar wajan Alkur'an
sai ta tsaneni yanzu dana kame baki nayi magana a nutse ba gashi ta fahimta ba,
Alsulhu khair!"
"Eh gwarai ga sulhu nan"
Dr A'isha Said
"Lafiya?" Yaa Sheikh ya furta a taushashe ƙamshin turaren shi na Roja ya cika
wajan, wanda ya sanya Dr A'isha sauke numfashi a ɓoye tana riƙe kanta.
"Matarka ta kura, ta hanata ɗaukan baby"
Jadda ta zare idanu tana dafe ƙirji sai kuma tayi shiru ganin yadda Yaa Sheikh ya
kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi da sanya mutum shiga cikin nutsuwar shi
"Allah ya raya Baby Ubangiji ya sanya albarka" Umma A'isha ta ce "Allah ya sanya
kuma matar malam tayi hankali" Sai a lokacin cikin sakin fuska yana jan jikinsa
ganin Ummul na zuwa ya furta.
"Matana da hankali"
Mother ta ce "Ba shakka"
Duk abin nan da ake hankalinta na kan Fattoumah ita da Father daya bar wajan yanzu.
Idanun da sukai yawa a wajan ya hana Yaa Sheikh rungume Ummul kamar yadda ya saba,
a hankali yake binta da idanu wanda take ganin tsananin farin cikin dake cikin su.
Suka amsa mata sallamar. Tayi murmushi ta ce "Barrister ya jikin Faɗima? Abu bai yi
daɗi ba Ubangiji ya ki yaye ya kuma taƙaita ya bata lafiya" Mother ta ce
"Amin Ya Allah" Dr A'isha ta dinga kallon Ummul ganin yadda take komai a waye cikin
nutsuwa da kamala, da shigar nan nata wanda ba a rabata da ita Abaya's masu kyau da
tsada.
"Can Mubasshir ya sameni, ina ga ya manta da na tura resigning letter " Mother ta
ce
"Ikon Allah, amma ba lokacin barin aikin ne ya yi ba?"
"Not at all,There is a reason why I joined the police force, and now I let El-
Bashir finish the job". "To Allah ya taimaka" Ummul tayi kyakkyawan murmushi ta ce
"Anyi baby kuma, Allah ya raya ya bawa mahaifiyar lafiyar shayarwa" suka amsa da
Amin. Ta juya ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Arɗo You left your wife alone, and i think
she's crying".
Bai ce komai ba, bai kuma motsa ba idanunsa akan Jaririyar hannun Ummul, yana jin
son yarinyar da komai na wanzuwa a zuciyar shi.
Ya juya zuwa Room ɗin da Halisa ke ciki, har lokacin barcin wahala take yana daga
bakin ƙofa ya shiga ƙare mata kallo sai kawai ya girgiza kai fararen haƙoransa a
bayyane alamar dariyar ya yi mai kyau a fili ya ce
"Ƴar kwailar matata"
Ya fita zuwa reception Zahrah na ganinsa ta goge hawayen idanunta tana miƙewa tsaye
cikin inda inda ta ce
"A.... You" ya bita da kallo tayi murmushi ta ce
"Congratulations sweetheart, ina maka murna da samun babyn" bai ce mata komai ya
kama hannunta zuwa ciki ta ce "Zan koma gida"
A hankali ya ce
"Zuwa anjima" ta ce "To zan jira nan" ya dubeta da kyau ta ce "I wanted to be alone
kawai fresh air nake so" Cikin ɗaga murya ba wasa ya ce
"Fatymerh Zahrah!"
Sai kawai ta fashe da kuka ta ce "Am sorry, ba zan iya jure abin da Jadda zata faɗa
ba, daman Halisa na kawo Thank God ta sauka lafiya zan koma" ya riƙe hannun da kyau
ya nufi ciki da ita, sai da suka je corridor ya rungomota jikinsa ya ce "Sorry"
"Na kasa jurewa, na jawa kai na mugun tabo, wanda ya sanya na kasa samun soyayyar
ƴan uwanka, na kasa samun taka soyayyar balle nayi zaton samun baby tare da kai,
lalai na cancanci haka" Ya yi mata shiru yana dai rungume ta ita.
"Yaa Sheikh" ta ɗago kanta ya kalleta yana lumshe idanunsa ta ce
"Don Allah kada ka barni, nayi al'ƙawarin zama dakai ko ba zan samu farin ciki ba"
Ya share mata hawayen ya ce
"Ki riƙe Allah" ya faɗa yana zare ta a jikinsa tayi murmushi ta ce "In sha Allah"
Haƙurinta yana ƙara bashi yaƙinin tabbas Ubangiji ba zai barta haka ba. "I love You
sweetheart"
"Wife" ya ce kawai... Har Issha El-bashir bai shigo ba. Walking slowly yake tafiya
a world ɗin, hannunsa zube jikin aljihun wandon Camouflage-print cargo trousers sai
Sleeveless jersey tank top a jikinsa, idanunsa maƙale da Sunglass black. Yanayin
yadda yake tafiya sai sanya kasan jinin Mai martaba Ahmad Nuran ne yake gudana a
jikinsa.
Fuska a haɗe babu walwala sbd zafin zuciyar da yake ciki.
Ya murɗa handle ya shiga suka haɗa idanu da Fattoumah ya ɗauke ido ganin Mother ya
yi tsaye zube da aljihu.
"Sai haƙuri, Allah ya bi mata kadinta" Ya shafa kai ya ce "Oops it's okay"
Ya fito da waya yana dannawa fita Mother tayi a sanyaye Fattoumah ta ce "Uncle"
"Angela" El ya furta yana zama tare da kama hannunta ta ce "Kada ka barshi Uncle
muguwa ne"
Ya runtse idanu yana ayyana azabar da Baba mai gadi ya ganawa Angela ɗin shi.
"Ya zan na bar wanda ya san gonata kafin na sani? He most pay"
Ganin tana ta kallonsa ya ce "Mene Angela?"
"Fitsari zan yi" ya saka hannu ya ɗagota ya ce "Zaki iya takawa?" Ta girgiza kai
domin har ɗinki akai mata. Cak ya sunkuceta zuwa toilet, ihu! Ta fasa sbd azabar
zafi lokacin da fitsarin zai fita tana kuka sosai jikinta na rawa da ƙyar tayi, sam
El bai damu da ganin jikinta ba ya fahimci ita ɗin kawai yake ba wani abu nata ba,
ya taimaka mata da wanke wajan tana miƙewa ta shige jikinsa tana sakin wani kuka.
Yadda take kukan zaka san wahala take sha, ya riƙe da kyau a jikinsa a hankali yake
cewa
"Sorry, am sorry Angela" ya ɗauketa zuwa bed ɗin tana kwance a cinyar shi yana waya
a hankali ya ce "Oh, ina buƙatar a shige da shi state C.I.D, kafin shiga Court"
A tsawa ce ya ce
"Zanci Ubanki ɗan iska, kai baka san waye ni ba You hve no idea akan abin

Please Login or Register in order to submit comment