You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Danejo ta kalli Saif-wazir kamar zatai magana sai kuma ta murguɗa
masa baki Surry ta kama hannun ta suka shige cikin gidan su Zahrah.
Saif yai dariya son ran shi ya ce "Akwai rigima Yaa Sheikh za ai raino" Khalil
Ahmad Sarki ya daki kafaɗar Saif ya ce.
"I couldn't understand, wai wace yarinyar nan? Na ruɗe fa" Saif ya ce "wato abinne
gaba ɗaya is complicated, muje mu zauna" Ya juya zuwa ga Abba Hakimi wanda ke
sauraran su ya ce "Abba ita ce ƴar fillon da nake baka labari"
Abba Hakimi ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce "Ikon Allah ya kamata mu zauna,
Umar-khan maza kira mini Barrister Maryam a waya" Umar-khan ya ce "To Abba" Abba
Hakimi ya yi gaba Saif-wazir ya bi bayan shi, Umar-khan ya tsaya kiran Mother a
waya.
Khalil Ahmad Sarki ya nufi inda El-bashir yake tsaye ya zuba hannun shi cikin
aljihun wandon shi ɗaya hannun yana shafa sumar kansa.
"Kaga abin da na gani kowa El-bashir?" El-bashir ya juya zuwa ga yayan nashi kamar
ba zai magana ba sai kuma ya ce "A'a duk an cika waje da ihu me zan gani haba kun
zama kamar wasu mata" Khalil ya ce "let's keep a joke a side wata na gani mai mugun
kama da kai" El-bashir ya nuna kansa yana fiddo idanu waje ya ce "Ni kaga me kama
dani?" El-bashir ya tambaya yana gyara tsaiwar shi. Khalil Ahmad Sarki ya ce "Ai
kamannin har sun ɓaci hatta beauty point da gashin girarka daya rabe biyu, hatta
muryarku iri ɗaya ne El-bashir na girgiza" a karo na farko El-bashir ya yi
murmushi kawai yana girgiza kansa ba tare da ya ce komai ba, hakan ya fusata Khalil
ya ce "Ya ina magana akan abu mai muhimmaci kana dariya?" El-bashir ya jingina
jikin mota baka iya gane yanayin shi ya ce "Me zance Abu Juwairah? Kawai kun haɗu
da aljana banda haka ina za a samu wata mai kama dani? ni ba ƙanwa ba ni ba ƴa ba,
Please mu bar wannan maganar" Khalil zai magana wayarsa ta shiga ringing ganin
matarsa ce Oum Juwairah ya sanya yabar wajan yana amsa sallamar ta.
Tunda suka shiga ɗakin Danejo bata kalli inda Zahrah ke zaune ba, kanta a ƙasa ta
haɗe fuska sosai. Zahrah gabanta ya faɗi ganin yadda cikin kwana biyu Halisa Danejo
ta sauya kamar ba ƴar fillo ba, fatar ta na ƙyalli ko'ina na jikin fes yake duguwar
rigar da Surry ta bata ta saka mai purple ta amshi jikinta sosai.
Surry ta ce "kina ta kallon ƴar fillo kamar baki san taba lokaci na shigewa" Zahrah
ta sauke numfashi ta ce "Kada dai ki mata matsayin mai aikatau zaki cikin gudana
ƴar fillo" Danejo ta ɗago kai ta kalli Zahrah cikin sautin siririyar muryar ta ta
ce "Ban manta ba, sunana Halisa Danejo Rome ba ƴar fillo ba" Zahrah taja tsaki ta
ce "Ji banza ina cewa a cikin ruga muka ɗakko ki? Banda warin shanu dana Kindirmo
me kike? Har kece za kice wai ke ba ƴar fillo bace?" Danejo ta shiga kallon Zahrah
zuciyarta na jin zafin maganganun data faɗa mata idanunta har ya cika da ruwan
hawaye saboda ba zata iya mayarwa da Zahrah magana ba bisa umarnin Dadarta.
Surry taja gefe guda tana murmushi jin daɗi ba tare da kowa ya lura ba, ita kanta
baza taso tun yanzu Halisa ta fara mayarwa da Zahrah magana ba. Cikin sauri ta ce
"Zahrah dama shiryawa ki kai yanzu 1:30 ance 2:00 daidai jirgi zai tashi" Zahrah ta
miƙe ta ce "Ina son haɗuwa da Deen wlh kwana biyu bana iya barci Surayyerh abin
cikina masifa yasa mini ba zan iya jurewa ba idan ban samu abin da nake ba dole
naje naga Deen" a fili Surry ta ce.
"Wallahi baki da tunani Zahrah ganin Deen a halin yanzu bai dace ba kuma nasan abin
da zaku aikata" a zuciyarta kuma ta ce "Well-done Zahrah ban fatan ki daina bibiyar
maza tun yanzu" Zahrah ta ɗauki hijabi tare da juyawa ta kalli Surry ta ce "Meye
sunan abin da kika bawa yarinyar nan ta saka bani" Surry ta amshi liƙab ɗin hannun
Danejo wacce ta haɗe rai sosai taƙi yarda ta ƙara kallon inda Zahrah take.
Cikin sauri ta gama shiryawa babu mai cewa Zahrah ce ta nufi ƙofar baya akan nan da
20 minutes zata dawo.
Tana fita Surry ta kalli Halisa ta ce "Kina ji ƙanwata, Kinga wannan mutumin da
kika ganu har kika ruɗe kina cewa Balarabe?" Halisa dai kallon Surry take kafin
Surry ta ce "To shi ne mijin Zahrah, ina so ki nutsu ki fahimta Kinga daga can kano
Madina zaku shige, kina wanka sau biyu ko sau uku a rana, haka ma brush da saka
kaya masu kyau...." Ta ci-gaba da faɗa mata komai na yadda zata gyara jikinta da
tsafta ta ɗora da faɗin "Kin fara Al'ada ne?" Danejo ta girgiza kai. Surry ta ce
"stop raising your head, magana zaki" ta ce "Ni ban san wani Al'ada ba" Surry ta
zare ido sai ba tace komai ba, ta shiga lodar kayan shafawa ta sakawa cikin jakar
Halisa tare da faɗin.
"Kada ki kuskura ta gani ko da wasa, idan ta gani ma ki san me za kice kar ki
ambaci sunana"
Abba Hakimi ganin maganar mai muhimmanci ce ya tattara ya barta zuwa lokacin da za
su koma gida ayi a gaban kowa, duk family su san matsayin yarinyar.
Yaa Sheikh yana kwance saman gadon hotel ɗin da suka sauka idanunsa rufe kamar mai
tunani daga shi sai farar Jallabiya ko barcin ya kasa, har lokacin bai bawa auren
muhimmanci ba, balle ya sakawa ran shi nauyi wata ƴar mace ya hau kan shi, iya
auren daya san da gaske an ɗaura kuma matarsa ce bisa tsarin addinin Musulunci, na
ƴar fillo kam yama mance da shi at all baya tunanin shi.
Ya miƙe a hankali zuwa bathroom tare da sakarwa kansa shower ya jima kafin ya fito
ɗaure da bathrobe a jikinsa, cikin sauri ya shirya cikin wani kyakkyawar Voyel mai
manyan zane maroon colour ya ɗora farar Alkyabba ya wani irin sahihin kyau kamar
Prince Hamdan bin Mohammed.
Ya fito cikin parlourn ɗakin ƙamshin Roja ya cika ko'ina a wajan wanda ya jawo
hankalin Khalil dake waya da Oum Juwairah ya ɗago kai bai san lokacin da ya ce
"Masha Allah" duk rashin tsaurin idon mutum ba zai iya tsayawa gaban Yaa Sheikh ya
yi ba, Ilhamar da Ubangiji ya bashi ta musamman ce, a kallo ɗaya yake dagula
lissafin mutum. Yaa Sheikh da jikinsa ya bashi kallon shi ake ya ɗago kai suka haɗa
idanu da Khalil ya kafe shi da ido alamar lafiya? Wannan kallon fa? Khalil ya shafa
kai sbd Kunya ya ce "Muje ko?" Yaa Sheikh yana gaba Khalil na bayan shi, cikin
nutsuwa yake tafiya har suka ƙarasu wani room a ƙofar room ɗin suka ci karo da wani
saurayi rungome da mace wacce take rusa masa kuka kamar ranta zai fita. Yaa Sheikh
ya ɗauke ido da sauri a ransa ya ce "Asstagafirullah Yaa Allah" Khalil kuma ya taɓe
baki a haka suka fitar zuwa reception na hotel ɗin daidai nan kuma Mai martaba da
abokin nasa El-bashir suka fito suma, haka Abba Hakimi da nasa abokan Umar-khan,
Ishaq-Hakim, Saif-wazir. Father daman yana can ba Alhj Farouk mahaifin amarya.
Jirginsu Yaa Sheikh daban na Amarya da ƴan uwanta da suka yanki tickets daban.
A airport suka haɗu baki ɗaya har lokacin Zahrah bata taho ba, Danejo tunda
idanunta ya sauka akan jirgi ta gigice tsoro ya kamata.
Yaa Sheikh da Abba Hakimi da kuma Mai martaba Ahmad Sarki tare da Father duk suna
Vip. Sauran kuma suna nrml waje. Jirginsu ne ya fara tashi babu jimawa Zahrah ta
ƙarasu wajan ta sha kwalliya cikin wata lafaya mai kyau da tsada. Tofa kallon ya
dawo kan Danejo ta rantse da abin da zai kashe ta ba zata shiga jirgin ba kuka
sosai. Wasu nayi mata dry. Da ƙyar Surry ta lallaɓata gudun abin da zai je ya dawo
ta zauna kusa da ita.
Danejo ta ƙanƙame jikinta wanda yake rawa hawaye na zubuwa daga cikin idanunta ta
ce "Na lalashe Dadata na kaɗe, na bushe shikenan zai a shige sama dani" Surry ta ce
"ki nutsu Halisa babu abin da zai sameki kinji ko?" Ita dai kuka take when the
plane will take off numfashinta ya tsaya cak Surry ta shiga girgizata tana amsar
ruwa tare da yayyafa mata da ƙyar ta dawo daidai ta fara yunƙurin amai yaƙi zuba,
lokaci guda ta fita hayyacinta jirgin yana wullawa sama ta fara wata uwar ƙara tana
faɗin "Na mutu, Wallahi na mutu.."

Misalin 4:45 manyan motocin da suka ɗakko dangin amarya daga airport suka shiga
parking a harabar gidan Mother. Wasu ƴan uwan Zahrah da yayar mahaifiyarta da
ƙanwar mahaifiyarta sune suka kamo Zahrah da aka rufe mata fuska zuwa cikin gidan
sauran friends suka bi bayansu. A parlour akai musu masauƙi su gaisa da dangin miji
kafin a basu masauki. Jadda dake zaune ta ce "Wai ina matar Gadangar ne sai wasu
yamutsastsun fuskoki nake gani?" Ladidi ta ce "Gata nan Zahrah buɗe fuskarki ai
miki bayanin dangin miji" Mother dai na zaune hankalinta na can waje guda sai kaɗa
ƙafa take.
Dr A'isha ma na zaune taci uban kwalliya kana ganinta kasan ba talauci inda take,
Yaya Halima ma haka, sai Momi tare da ƴan uwan father, da matar Uncle Haroon.
"A meye haka? Alsulhu khair buɗe fuskar uban kowa ya gani"
"Ai Hajiya kin san amare da kunya" Jadda ta ce "kaji masifa ko? Waye sa dake wace
ke? daga gidan wa zuwa ina?" Ladidi tai shiru amma Jadda ta fara ƙular da ita.
"Muhammadur Rasulullah s.a.w wannan ai uwa aka aura Aliyu ba mata ba? Gidan ubawa
Aliyu zai kai ɗirkekiyyar matar nan ni kai na ta kusa haifata yau na shiga uku da
gaske wannan ce matar Malam ɗin?" Jadda ta faɗa bayan ta saka hannu ta buɗe fuskar
Zahrah. Surry na gefe tana danne dariyar dake ranta.
"Maryam zo kiga abin al'ajabi yoo Allah na tuba ko ke ai kinfi matar malam kyan
gani? Allah sarki Gadanga an haɗaka da uwar mata" sai kuma ta fashe da kuka sosai
ta ce "Innalillahi ashe har gashin doki take saka zunubi babba" ta saka hannu ta
kama hannun Zahrah ta ce "Wanne tsinannen abu ne wannan kuma?" Ta faɗa tana duba
farcen hannun Zahrah.
"Haba Hajiya wannan abun duk na mene? Ya daga kawo yarinyar sai cin mutunci?" Jadda
ta miƙe ta nufi kan me maganar ta dungure mata kai ta ce "Algunguma ai duk duniya
an gama cutar Malam an haɗa shi da arniyya" "Arniyya wacce ira kuma Hajiya?" Ladidi
ta faɗa rai ɓace. Jadda ta kunce ɗan kwalin kanta tare dacin ɗamara ta ce "Arniyya
ƙatuwa ma, mene bambancin su? ga tafkeken zunubi ba tausayi ba komai aka cirewa
doki gashin shi aka saka mata, gata narkekiyya mai idanu a tsakar kai, gashi ta
wani ɗashe kamar mace mai shigar sabon ciki Innalillahi masifa ta saukarwa Malam"
gaban Zahrah ya faɗi tai saurin rufe fuskarta.
Dr A'isha ta fashe da dry wacce tun ɗazo take danne ta. Yaya Halima girgiza kai
kawai take kafin ta ce "Kuyi haƙuri don Allah muke ga masauƙi can" Mother
hankalinta na kan Danejo wacce take ɗan ɗaga liƙab ɗin fuskarta tana leƙewa da sun
haɗa idanu da mother sai ta mayar ta rufe.
Babu wanda Jadda bata ciwa mutumcin ba kafin su bar wajan. Mamaki ya kama Ladidi
ganin uwar mijin ta Zahrah ci kanku ba ta ce ba. Kwanan su biyu suka koma Yola aka
bar Zahrah tare da Halisa.
Yaa Sheikh ne durƙushe a gaban Abba Hakimi da Uncle Haroon sai Uncle Bashir ga
Mother da Yaya Halima da kuma Momi matar Abba Hakimi. "Ina magana kayi shiru
Aliyu?" Abba Hakimi ya faɗa cikin sassauta murya. Yaa Sheikh ya ɗago kan idanunsa
ya sauka akan yarinyar da ake nuna masa, ya ƙara duban Halisa da kyau sai yanzu yai
mata cikakken kalo ya mai da idanunsa kan Abba Hakimi ya ce.
"Wace? kamar ban waye ta ba?" Uncle Haroon yai murmushi yana jinjina halin Yaa
Sheikh. Abba Hakimi ya ce "Amma kasan Rugar Bello? Ka kuma san Arɗon rugar ka gane
abin ya faru,ka kuma shaida zoben hannunta?" Yaa Sheikh ya ɗan kallin kyakkyawan
hannun Danejo wanda yake maƙale da zoben da yake so har ransa nan take ransa ya
ɓaci, a lokacin ya tuna everything ya shanye mmkin kamannin da yake gani a fuskar
yarinyar, shi kam a rayuwa ko zai so mace ai banda ƴar cikinsa wannan gwaliliyyar
yarinyar bata shige raino ba, ita za a kalla ace wai matarsa? Shi kam ya zai yi da
mata biyu ba?. Yai shiru yaƙi bada damar da za a karanci halin da zuciyarsa ke
ciki. Uncle Bashir ya ce "Da alama ya fahimta" Abba Hakimi ya ce "Halisa maza je
aikyan yayar taki kada taga kin daɗe" ta miƙe da sauri domin daman a takure take
Yaa Sheikh duk ya firgitar da ita. Abba Hakimi ya ce.
"Ba wasa muka zauna yi ba, jibi zaka shige Madina kafin nan kana son yarinyar nan
ko baka son ta?" Yaa Sheikh yai shiru ya kasa fahimtar abin da suke nufi dashi, shi
kam duk ranar da ya ce yana son mace ai sai ya yi azumin kaffara shi ya sa har
abada ba zai taɓa cewa yana son wata ba.
Ya girgiza kai a hankali "Baka son ta?" Cewar Uncle Haroon. Bai kalli Uncle Haroon
ba ya kalli Abba Hakimi. Abba Hakimi ya gyara zama yana sakin murmushi ya ce "Ka
shirya sakinta? baka san me gobe zata haifar ba?" Yaa Sheikh ya riƙe hannunsa da
kyau yana girgiza kansa harshen shi na harɗewa ya ɗan motsa ƙafarsa ɗaya cikin In-
ina ya ce "Ha...hhh...har... Har abada ba ba ba zan zan so ta ba"

_IDAN BA KE it's paid book ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity
bank shaidar biya 08119237616..... Isn't free if you read for free _
[1/3, 4:48 PM] Abk: Yaa Sheikh ya faɗi hakan kai tsaye. Abba Hakimi ya ce "To kafin
nan muyi wata game mana, idan kaci ni kuma nayi al'ƙawarin raba aurenku har abada,
ka zauna kai ɗaya da ita Zahrah tunda ba a son Ƴar fillo" Mother ta juya ta kalli
Yaa Sheikh kafin ta ce.
"Yanzu meye laifin yarinyar? ba tafi wacce aka haɗaka da ita ba? to a karo na farko
zan faɗa maka zama da wannan babu fashi a wajanka Aliyu" Uncle Haroon ya ce "A'a
Barrister labarin aure baza kici haka ba, ana yin aure dan farin ciki da kwanciyar
hankali,idan ba yajin yarinyar a ran shi bai kamata a takura masa wajan zama da ita
ba, zai iya amincewa bisa takurar kuma ya cutar da ita, a dai bi komai a hankali"
Mother ta girgiza kai ta ce "Uncle Haroon ka rabu da Aliyu, tunda ya amince dana
Zahrah zai amince da wannan ɗin ma sai ya tattara su tafi can Madina su ƙarata"
Yaya Halima ta kalle su baki ɗaya kafin ta ce "duk ba Wannan ba, na tambayi Zahrah
a sigar wasa cewa wannan ƙanwarta ce? Sai ta ce mini wai ƴar aiki aka samu mata,
That's the position of a maid in Aliyu's house" Dr A'isha tai murmushi ta ce "Matar
gida ko ƴar aiki? dama a ɗauke ni aikin gidan Aliyu naga yadda zaman zai kasance"
Yaa Sheikh ya ɗaga kansa a hankali kamar zai kalli Dr A'isha sai kuma ya fasa ya
mai da kan ƙasa.
Sai a lokacin Uncle Bashir ya ce "Ya kamata kada ita Zahrah tasan cewa itama
yarinyar matar Yaa Sheikh, a barta ta tafi da ita a matsayin ƴar aikin kamar yadda
tazo da ita da manufar hakan"
"I also agree with this decision, she took it as her worker" cewar Dr A'isha. Abba
Hakimi ya sauke numfashi yana duba lokaci,bayan nazartar maganganun sauran ya ce.
"Na amince baka son ƴar fillo, suma sun yarda da hakan, zaka tafi da ita can
gidanka dake Madina matsayin matar ka kuma ƴar aikin matar ka, zaka iya zuba idanu
matar ka ta zama baiwa a cikin gidan aurenta, ra'ayinka ne,
Ni bance kaji tausayin ta ba, kawai ina son ka riƙe mini ita a wajanka na tsayin
shekara ɗaya ciff, ka sata makaranta, ni bance ko sau ɗaya kayiwa Halisa Danejo
kallon matar ka ba, ita ɗin kamar ajjiya ce na baka, ka dawo mini da ita shekara
guda, kada naga wani sauyi a tare da ita, ka tabbatar yadda take budurwa a haka ka
dawo mini da ita, nayi maka al'ƙawarin shekara nayi zan raba auren naku rabawa ta
har abada" gaba ɗaya mutanan parlourn suka zubawa Abba Hakimi idanu, su basu ga
dabarar haka ba, sun san ko shekarar biyar aka bawa Yaa Sheikh there is nothing he
will do, there will never be any change from him, balle ya furta da bakin shi ya ce
yana son ta,That will never happen.
Abba Hakimi ya gyara zama sosai idanunsa akan Yaa Sheikh ya ce "Amma Wallahi
Wallahi Allah kenan Aliyu ban taɓa rantsuwa akan ka kamar haka ba, shekara guda
tayi ka dawo mini da yarinyar nan saɓanin yadda nai tunani zaka sha mamakina, kai
ba yaro bane ka fahimci mai nake son faɗa maka, babu dalilin da zai sanya ka lalata
budurcin yarinya kuma ba son ta kake ba, This is a deal" Uncle Bashir ya ce "Amma
Abba Hakimi wannan deal ɗin bai tsauri ga Malam ba?" Abba Hakimi ya ce "Ba kaji kai
ma kace Malam ba? Yaa Sheikh zai iya ɗaukan wannan game ɗin" Murmushi Uncle Haroon
ya yi kai tsaye ya yarda da abin da Abba Hakimi ya zartar cikin fara'a ya ce "To
idan haka ne ina tsagin uwar gidan Halisa, za muje matsayin masu aikin gida kawai"
Uncle Bashir ma ya ce "Ni ma dai ina team ɗin uwar gida" yaya Halima tai murmushi
ta ce "Ikon Allah, to ina team ɗin Aliyu koma mai zai faru ya faru she is his wife
matar shi ce babu laifi" Dr A'isha ta ce "Ni dai ba zan zaɓi team tun yanzu ba, sai
naje Madina naga yadda zaman zai kasance" Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir shi kam a
rayuwa mai Abba Hakimi ya mai da shi? Ina ruwan shi da wata ƴar fillo balle har
yaje gareta matsayin miji mai buƙatar hakƙin shi wajan matarsa? Zai bawa kowa
mamaki. Miƙewa ya yi a hankali zai bar wajan Abba Hakimi ya ce "No tayaya ka taɓa
ganin anyi deal ba saka hannu, maza saka hannu a wannan dairy ɗin" Yaa Sheikh ya
kalli Abba Hakimi da kyau, shi kam Abba Hakimi ya ɗauke kan shi alamar bai gane
meke nufi ba. Cikin sauri ya saka hannu tare da saka suna da date da kuma time.
Yana gamawa ya juya jiri na ɗaukan shi sbd ciwon kai ya nufi Part ɗin shi.
Abba Hakimi yabi bayan shi da kallo a zuciyarsa ya ce "let's see ko Aliyuna waliyyi
ne"
Wajan ya yi shiru kowa da abin da yake tunani a ran shi, Mother na tunaninsu yadda
zata cusa Halisa a zuciyar Yaa Sheikh, kallo ɗaya ta yi wa yarinyar hankalinta ya
kwanta da ita, kawai dai ta fahimci bakin yarinyar babu control kamar ba a gasa
mata shi ba. Yaya Halima kam gani take kamar Yaa Sheikh ba zai iya tsallake wannan
gasar ba, lura da yanayin Halisa da komai sai tafi Zahrah jan hankalin ɗa namiji
kowa zaman zai kaya ohhu! "Kada a bari Jadda da Engineer su san maganar auren
wannan yarinyar Halisa da Yaa Sheikh, mu bari muga abin da hali zai aga yanayin
zaman maybe a samu sauyin ra'ayi game da Yaa Sheikh akan yarinyar" cewar Uncle
Haroon. Abba Hakimi ya miƙe tsaye haka Uncle Haroon da Uncle Bashir sukai wa Mother
sallama.
Bayan tafiyar su yaya Halima ta kalli Mother ta ce "Yanzu me zaki Barrister?"
Mother ta girgiza kanta idanunta akan wayarta tana neman contact ɗin wata mata ta
ce "me zan yi kowa yaya? ga Abban Sheikh nan ya gama magana" ta faɗi hakan tana
danna call.
"Tun ɗazo da nace ki kawo mini bottle water ina kika tsaya?" Zahrah ta tambayi
Halisa tana zare mata idanu. Ta turo baki gaba ita tsakani ga Allah take son faɗawa
Zahrah abin da ta fahimta wajansu Abba Hakimi. Zahrah ta ce "ba dake nake ba dan
ubanki?" Da sauri Halisa ta kalli Zahrah bakinta na rawa ta ce "Baffana kika zaga?
Ya mutu fa?" Wani tsaki Zahrah taja ta ce "Idan ya mutu ni na mutu? Waye shi da ba
za a zage shi ba" Halisa ta jima tana kallon Zahrah idanunta ya yi jajir ga abin
masifa babu halin yi sbd ka shaidin Dada a gareta.
"Matsa ki bani waje ai dama har uwar suka haɗu suka mutu Kinga baki da sauran wani
gata kiyi mini aiki hankali kwance" Halisa ta juya da gudu tare da fashewa da kuka
hannunta a fuskarta tana karewa. karo suka ci da Maimoon data ɗakko warmers ɗin
lunch wanda akace ta kaiwa Zahrah, Maimoon ta ja baya da sauri tana faɗin
"Subuhanallah ya akai kike kuka haka ke dawa?" Halisa ta kasa kuka sai shassheƙa da
zata iya ita gida kawai zata gudu wallahi. Maimoon ta ce "Ok ya isa daina kukan
jirani a nan wajan kinji?" Ta ɗaga kai a nutse alamar "to". Zahrah na kwance waya a
hannunta suna vedio call da Deen wanda gaba ɗaya ba vedion Allah da Annabi bane,
ita dai Maimoon taji wani sauti kamar gurnani da sauri Zahrah taja duguwar rigarta
zuwa ƙasa tana rufe wajan data buɗe. She pretended not to notice what she had done.
Tana ajjiye warmers zata juya Zahrah ta ce "Hey you" Maimoon tai banza kamar ba
taji ba. "Ina magana" Maimoon ta juya kaɗan suka haɗa idanu ta ce "dani kike?" Ta
ce "to waye a ɗaki?" Maimoon ta ce "Huh na ɗauka kina magana da wayar hannun ki ce"
Zahrah ta sakko daga kan gadon ta ce "what the do you mean by that?" Maimoon tai
shiru can Zahrah ta ce "What's your name?" "Maimoon" ta bata amsa Zahrah ta ce "Ok
At least you have to respect me ni matar yayanki ce, kin shigo bedroom without my
permission da muna tare Yaa Sheikh fa?" Maimoon ta ware idanu sosai ta ce "Yaa Lee
a bedrooms ɗinki? Shhhh" tana faɗin hakan tai waje da sauri.
"Kan uba wannan yarinyar sai na saita mata zama kalli Yadda take mayar mini da
matar tani?" Waya ta ɗauka ta shiga kiran Surry.

Maimoon ta kalli Halisa wacce ke zaune a ƙasan carpet ta ce "Sister tasu muje part
ɗin mu" Halisa ta girgiza kai Maimoon ta ce "Anty Zahrah ta ce mu tafi tare zuwa
dare sai ki dawo" ta miƙe tana faɗin "Ita ta ce haka?" Maimoon ta ce "ita ce mana"
hannunta ta kama suna zuwa Main parlour El-bashir na tashi tare da ɗaga waya ya
nufi ƙofa, Halisa ta bi bayan shi da kallo ta ɗauka Balarabe ne. Maimoon taja
hannunta har zuwa part ɗin su, Zeefa da auta Fattoumah suna zaune ganin Halisa yasa
Auta Fattoumah faɗin "Wow yaya Moon wannan kyakkyawa ce She's very beautiful she
looks like bro El" Maimoon ta ce "to sarkin surutu" ta zaunar da Halisa ta shiga
ɗakko mata su ice cream da chocolate amma sam Halisa taƙi ce sbd bata saba dasu ba,
ta ɗago kai a hankali ta ce "bana cin irin wannan" Nazeefa ta ce "To sai me?" A
hankali kanta a ƙasa ta ce "Kindirmo nake shu" a tare suka zare idanu tare da faɗin
"what?" Tai shiru tana kallon su can Maimoon ta ce "Zeefa haɗa mata ruwan wanka a
bathroom bari na kawo mata kindirmon" tana faɗin hakan tai waje har lokacin
Maimoon ta kasa mance abin da idanunta ya gani a bedroom ɗin Zahrah. Cikin sauri
Zeefa ta haɗa mata ruwan wanka tare da nuna mata komai a toilet ɗin da yadda ake
amfani da su. Suna bakin toilet ɗin suka ji ana knocking "Halisa duba kiga waye?"
Kamar ba zata ba sai ta nufi ƙofar jiki a sanyaye zagin da Zahrah tayi mata har
yanzu damun zuciyarta yake.
Halisa ta tsaya bakin ƙofa ta rasa me za ta ce can dai ta ce "waye?" Ta faɗa cikin
ƙasa da murya. El-bashir ya gyara tsaiwa hannunsa riƙe da waya da kuma chocolate ya
ce "Buɗe ki gani mana?" Halisa ta murguɗa baki tana ƙoƙarin buɗe ƙofar Zeefa ta ce
"jeki kiyi wankan bari na buɗe ƙila Maimoon ce" Halisa ta juya zuwa bathroom ba
tare da ta ce komai ba, Zeefa na buɗe ƙofar taga El-bashir tsaye fuska ɗaure ta ce
"Yaya El" ya wurga mata harara ya ce "wace take tambayar waye?" Zeefa ta juya ta
kalli ƙofar bathroom ta ce "Laa Halisa ce bata sanka bane" ya ce "I'll break her
legs" chocolate ya bawa Zeefa ya juya yana faɗin "Kira mini Fattoumah" ya nufi Main
parlour Mother dake zaune ta ce "Yau zaka shige ne?" Ya ce "I don't think so.. sai
abin da Mai martaba ya ce" ta ce "Ohh abokin Mai martaba".

Washegari Zahrah na zaune ta caɓa ado cikin wata atamfa mai kyau ruwan ƙwai ta yafa
mayafi babba kamar ta Allah. A hankali ta fito zuwa Main ta samu Mother zaune ita
da Jadda suna hira sai Maimoon Zeefa da Auta Fattoumah suna makaranta. Zahrah ta
durƙusa ta ce "Ina yini Mother?" Mother ta ce "kina lafiya ya kwanan baƙunta?"
Zahrah ta ƙara sunkuyar da kai alamar kunya ta ce "Allahamdulillah, daman cewa nayi
bari nazo idan da aiki nayi"

Please Login or Register in order to submit comment