You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo ta sunkuya har ƙasa ta ce
"Ina kwana Abba?" Ya dinga kallonta yana son yaran sosai sai ya kasa shareta ya ce
"Lafiya Hafsat" ta miƙe bayan ta gaida Khalil Yaa Sheikh ya miƙa mata Beeherh ta
amshe ta ce
"Kwana biyu rigima take tai ta kiran Abba, har cewa kada sunan Abbanmu ya ƙare" Ya
lumshe idanunsa da hannu ya nuna mata hanyar tafiya, daga nan suka shiga mota kai
tsaye Yaa Sheikh Na'ibawa ya nufa ba tare da sanin Khalil ba, sai ganinsa ya yi a
haɗaɗɗan grandparents ɗin Yaa Sheikh.
Ummul na zaune ta ji ƙamshin turaren ɗan nata, ta ɗago kai a hankali ta ganshi
tsaye yana tsare ta da idanu
"Me ya sa ka ɗauke komai na Mahaifinka ne Arɗo, babu ko kara ka ɗauki wani abun
nawa?" Ta dube shi da kyau ganin ya faɗa kamar mai jin yunwa ta ce
"Zonan muji, fuskar ka abu biyu ta nuna, akwai damuwa amma farin cikin ya fi yawa"
ya ƙarasu wajanta yana zuwa ya zube a gabanta yana ɗora kan shi a cinyoyinta. Ta
zame hiramin kan shi tasha shafa sumar kan ta ce
"Ya akai Aliyu?" Ya sauke numfashi yana ɗago kan shi ya kalli Ummul ya ce
"She hated me" rauninsa duk ya gama bayyana, wanda kuma iya gaban Ummul ɗin ne
yake haka
Ta riƙe fuskar shi da hannunta ta ce "Abun farin cikin fa?" Ya yi jim nauyin Ummul
ya saukar masa, ita ma ta fahimci haka amma tasan dole ita ce abokiyar shekarar
"She's pregnant, na ƙara jin son ta" farin ciki ya mayaye zuciyar Ummul sosai jin
Halisa nada ciki ta ce "Ma sha Allah, so zan samu granddaughter or son zan ga jinin
Arɗo am so happy" ya lumshe idanu idan ba ita ta ce ya tashi ba, zai ta zama a
durƙoshe ne ta ce
"Haka soyayya ta ke Aliyu, bari na baka labarin soyayyata da Mahaifinka, ban ɗauka
zan so shi ba, wulaƙanci daban na gobe daban, ya yi kuka amma bana damuwa a haka
har na fara tausayin shi,tausayi ya koma soyayya mai zafi, bana iya barci idan ban
ji muryar shi ba, na bijirewa iyeyena ashe duk rabonka ke kira shi kuma ya hadda sa
haka" tai shiru na wani lokaci ta ce
"Idan Halisa ta tsaneka yau, gobe zata so ka, idan taji haushinka yau, gobe zata
tausaya maka, irin haka lamiri mai girma ke tabbatar da shi,tare da rabo bana son
Malam ya gaza tun yanzu, labarin Aliyuna soyayya ce mai zafi,ina fatan shafin gobe
ya sa soyayyar ta zama kaffara a gare shi"
"Ina son ki Ummul"
Ta dungure masa kai tana faɗin "Gashi nan akan mace ka bijire mini sai farkawa nayi
naga ba mota ka gudu can gidan Abba Hakimi" "Ki yafe mini" ta ce "Kada ka sake, ta
shi kayi breakfast idanunka duk ya faɗa da alama ko barci ba kai ba" da hannu irin
yaran kuraman nan ya yi mata nunin azumi yake. Ta kalle shi sai kawai ta girgiza
kai kafin ya tashi Khalil ya yi sallama, sosai ya yi mmkin ganin Yaa Sheikh zube a
gaban Ummul, Yaa Sheikh ya miƙe ya dawo kusa da Ummul.
Ta amsawa Khalil tana sakin murmushi sai yanzu kuma Khalil ya lura da wacece Ummul,
Kyakkyawar mace mai nagarta kuma wayayyiya mai ilimi addini da boka, macan data
ɗauki ɗan ta kamar abokinta friendly to her family. Ta haɗuwa Khalil breakfast,
Suna zaune Granddaughter ɗin Yaa Sheikh ya fita da matar shi Zulaiher suna ce mata
Hajiya.
Halisa zaune tsakiyar parlour Mother ta riƙeta, Abba Hakimi na zaune gabanta
hannunsa riƙe da Alkur'ani da kuma ruwan rubutu. Yaa Sheikh daya shigo ya tsaya
yana kallonsu da son jin abin da ke faruwa, A wahale Halisa ta buɗe ido ta kalli
Yaa Sheikh wata murya ta ce "Modibbo ka ce kada su rabamu ina son ka, ina son ka
zasu rabamu" zuciyar Yaa Sheikh ta buga sai yanzu ya gane kuma ya fahimta daidai,
ya ƙarasu a karo na farko ya zube gaban Abba Hakimi ya ce
"Kada kayi haka Abba, kalli abin da tayi mini da tai losing memory idan ka cire
mutanan jikinta ya zan?" Mother ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Tayi recovering ɗa zo,
tana dawowa daidai kai ta fara tambaya ta ɗaga hankalinta, daman kuma Dr ya ce
short-term memory 10-15 seconds ya ke ɗauka, dalilin ruwan daya kwanta a kanta ya
sa ta jima, ban san me Abba Hakimi ke nufi ba amma ya ce dole ya raba Halisa da
abin da ke kanta" Halisa ta miƙa hannu tana kiran "Abbana ka taimake ni, ka faɗa
masa ban hanaka mu'amala ta matarka ba kada su rabani da jikinta" Abba Hakimi ya
ɗauki ruwan rubutun ya watsa mata a fuska tai ƙara, da sauri Yaa Sheikh ya riƙe
hannun Abba Hakimi idanunsa ya yi jajir jijiyoyin kansa sun fito ya ce "Ka tausaya
mini Abba,kada kai haka" Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Kasan da cewa
Aljanu basa tabbata a jikin mutum? Kasan nasan ba Halisa ke son ka aljanar jikinta
ce, dole na raba su idan har kana son ta ka tsaya ka gina soyayyarka a zuciyarta...


Kamar saka number ta ba shi da amfani, kun hana masu siyan special su siya sbd
fitarwa, na kasa sani hakan Soyayya ce ko ƙiyayya?
[1/12, 6:51 PM] Abk: *_Ƴan Youtube masu tambaya nawa zan siyar musu da IDAN BA KE
su saurara, akwai wanda suke buƙata sai na duba farashi mai yawa tukun😂
TSINTACCIYA,SIRRIN MU, ABU MALEEK Duk Available ne, ZAIN ABEED ma na siyar
08119237616_*

Yaa Sheikh ya ware idanunsa sosai akan Abba Hakimi yana son fahimtar da gaske yake
masa? Koda yake iya zamansu ai Abba Hakimi bai taɓa yi masa wasa da abu mai
muhimmanci ba, dukkan wani ilimin addini mai nagarta da tsafta a wajan Abba Hakimin
ya samu, sai wanda ya ƙaro a makaranta da kuma masana manyan malamai,ya haɗa da
wanda Yake da shi hakan ya sa ya zama babban malamin addinin na gaban kwatance.
Ya daidaita nutsuwarsa tare da kame kansa waje guda a taushashe ya ce
"Ka da kayi haka Abba"
Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh yana son karantar yanayin shi sai bai ga komai ba
illa Ilhama da tarin nutsuwar dake shimfiɗe a fuskar ta shi
A karo na babu adadi ya ce "Yaa Sheikh ba son matarka ka ke ba da gaske, kuma baka
nemi hanyar da zata soka da gaskiya da amana ba"
Ya yi jim kaɗan na wani lokaci ya ɗora da
"Ka nemi soyayya ta Gasky wacce take kasancewa har bayan rai, idan kace a haka zaku
tafi to abun ba zai haifar da ɗa mai ido ba"
Halisa ta ƙwace riƙon da Mother tayi mata jikinta na rawa taja gefe zuciyarta na
ɗagawa da sauri Yaa Sheikh ya runtse idanunsa,
Wani abu mai kama da zullumi na ratsa masa zuciya ya daidaita lamarin da yake
addabar zuciyarsa ya numfasa kaɗan idanunsa a narke ya ce "Ba aljana jikinta"
"Na sani" cewar Abba Hakimi. Ya kalli Halisa kafin ya ce "Nayi hakan ne domin nasan
wacce alƙibila zuciyarka take fuskanta, bayan kaci amanata ka yaudareni ka rusa
yarjejeniyar da mukai, bayan kafi kowa sanin muhimmancin al'ƙawari da riƙon amana"
Yaa Sheikh kan shi a ƙasa domin ya manta wanne amana yaci wacce kuma yarjejeniya
Abba Hakimi yake magana akai,
Ya yi murmushi mmkin ƙarfin halin Yaa Sheikh a karo na farko kafin ya ce "Zan
nemeka ne, zaka san kuma da ni ka ke magana, zan nuna maka waye ni, batun aljana
kuma ai kasan akwaita banyi ƙarya ba, kuma kasan dalilin daya sanya ta rabu da
jikin matar taka, Aljanu ke ɗawainiyya daku, ka rabata da Aljanin dake son ta, sai
ka ƙi rabata da aljanar jikinta wacce ke son ka da gaske kamar rai, hakan mugunta
ce ko mene? Aljanin dake son ta shi ne ya nemeka da sharri Aliyu, Aljanar dake son
ka kuma ita ce ta kare ka daga sharrin aljanin, ita kuma ta sanar dakai cikin jikin
Zahrah, kuma ita take hanaka kallon Zahrah da idanun rahama" ya sauke numfashi yana
jin dole ya hora Yaa Sheikh ta yarda zai furta kalmar so da Halisa, ya kuma karɓeta
da hannu bibbiyu, aman da ya yi agaban kowa ya lashe abin shi ya ce "Ka ɗauka ban
san komai ba? Banyi mamaki ba, abu ɗaya ya sanya naji cewa ko wanne namiji zai iya
sauya halayyar shi da ɗabi'a da nagartar ƙwarai da yake da ita akan mace, sufa mata
shaiɗanun maza ne, idan ka iya kallonka kuma sai ka wanke, yanzu kuka fara rayuwa
baka san abin da gobe zata haifar ba, yanzu nayi imani cewa Halisa ita ɗaya ce, ba
wasu aljanu amma kai sai da ka mutu tare da naka" babu wanda ya yi magana. Ya juya
kan Halisa yana faɗin
"Matar kina son Yaa Sheikh? Kina son zama da shi?" Sai a lokacin ta ɗago kanta da
rinannun idanunta numfashinta na fita da ƙyar ta juya ta kalli Yaa Sheikh, bai
kalleta ba amma ƙirjinsa bugawa na tsoran abin da zata furta "Ina son Abbana"
Ya sauke ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya mai ƙarfi na hamdala ga Ubangiji Abba Hakimi ya
sake cewa "Me ya sa ki ke son shi?" Ta marairaice fuska tana juya ƙaramin bakin nan
wanda yake a shirye wajan fidda zayyana ta ce "To ai mijina ne, gashi zan haifa
masa baby ko Yaa Sheikh"
Kunya ta sarƙafe Yaa Sheikh a Wajan bai ɗago ba, bare ya ce mata wani abun data
kalli ƙwayar idanunsa ko ya furta wani abun to zata faɗin abin da ba shi kenan ba,
wanda zai sanya yaji kunyar Idanun mutane ukun nan da suke kan shi
"Amma shi yana son ki ne?" Tayi saurin faɗin
"Ehmn da yawa ma, yana bani darasin littafin Alhayat alzawjia" Abba Hakimi ya
sunkuyar da kan shi ƙasa jin al'amarin ya shahara ya shige tunaninsa. Umma A'isha
ta janye kanta can zuwa wani waje tana mmkin yau ɗaya bakin yarinyar ya buɗe,
Mother ce tayi ƙarfin halin cewa
"Daughter jeki huta ɗakin ki, yanzu dai bakin amince kina son cikin,kuma kina son
Yaa Sheikh ba?" Cikin sanyin muryarta ta ce "Eh, Mother". Mother ta ce
"To tashi ki ke anjima Dadarki zata zo kafin ta shige Sokoto" nan da nan farin
ciki ya mamaye fuskar Halisa zuciyarta yayi fes ta juya tana faɗin "Abba, Abba
Hakimi ya fasa kada zuciyarka ta damu.."
Wayam! Ko inuwar Yaa Sheikh babu tun a sakin layinta na biyu ya sulale yabar
parlourn gudun abin da zata iya faɗa anjima, su kansu ba ita ba sunyi mmkin yadda
ya bar wajan ba tare da kowa ya lura ba.
Ta miƙe tsaye tare da nufar bedroom ɗinta, Mother ta bita da idanu ganin yadda
jikinta ya sauya, ƙirjinta ya ciko sosai fatar jikinta ta ƙara haska sosai fiye da
baya har wani yellow take, gabaɗaya sauyin shigar sabon ciki ya bayyana a jikinta.
"Yanzu ya za ai da wannan lamarin na Zahrah?" Abba Hakimi ya ce "Dole iyayenta za
tabi da zarar sun zo, tunda Engineer yaƙi yiwa yaron huɗuba zan saka Yaa Sheikh ya
yi masa" Mother da take jin maganar na dokan ƙaho zuciyarta sosai ta ce
"Mene haɗin Yaa Sheikh da wannan yaron kuma? Ni wallahi banga amfanin zamanta a
gidan nan ba"
"Kada ki zama mai son ki Maryama, ke macace ya kamata ki fahimci zafin da yarinyar
ke ji a ranta, laifinta ƙanƙani ne cikin wannan lamarin" Idanun Mother ya sauya ta
ce
"Abba kasan babu macan da za aiwa haka ranta ya yi ɗaya, idan naga yarinyar da abin
data haifa zafi na keji, zuciyata babu daɗi" Abba Hakimi ya miƙe tsaye yana kallon
hanya ya ce
"Yaro baya da laifi, nasan daman za kiji zafi amma laifin mijinki ne" ran mother ya
ƙara ɓaci sosai ta ce "Ni ba mijina bane, nakai ƙara court ma dole ya ƙarasa saki
na" Abba Hakimi bai ƙara cewa komai ba ya nufi ɓangaren shi, domin Mai martaba da
Dada suna asibiti wajan El-bashir.
Yaa Sheikh na zaune daga shi sai Jallabiya hannunsa riƙe da azkar yana dubawa, a
hankali ya dubi lokaci ya ga rana ta kusa faɗuwa an kusa kiran magriba
Kamar ance ya ɗago kan shi ya hangota a bakin ƙofa tana leƙen shi suna haɗa idanu
ta koma ta ɓoya tana dafe ƙirji,gani take kamar Abban nata an sauya mata shi, idan
ba kuskure tayi ba gani tayi furfura gemun shi ta sake yawa ainun.
Ta ƙara leƙowa taga kan shi a ƙasa yana duba littafin hannunsa ta bishi da idanu
tana jin son shi da ƙaunar shi na ƙara ninkuwa a zuciyarta, SO mai tsanani ya ƙara
mamaye ko wacce ƙofa dake zuciyarta.
Kamar daga sama taji saukar kamilalliyyar muryarsa mai kamala ya ce "Zonan
Haliyserh"
Ya faɗa a taushashe har lokacin bai ɗago kan shi ba. Ta ƙarasu bakinta ɗauke da
sallama sanye da hijabi har ƙasa kamar ma daga wanka ta fito ko shiryawa ba tai ba,
ta nufo wajan na shi.
Tana zuwa ta nemi zama kan cinyar shi, ya yi saurin riƙe hannunta tare da ɗago
kanshi idanunsa ya sauka akan fuskarta idanunsa ya sauka tsakiyar nata tayi saurin
janye nata, saboda kaifin na shi idanun. A hankali ya ajjiye littafin yana jawota
tare da zaunar da ita saman ƙafafuwan shi tayi saurin juyawa suka fuskanci juna!
Ya dubi bakinta ganin kamar tana cin abu tare da saka hannu ɗaya ya tallafo haɓarta
tare da saka hannu ya buɗe bakin nata, ya buɗe idanunsa akan ta, tare da mayar da
idanunsa cikin bakin tayi saurin riƙe hannun ta ce
"Abba ina so, kada ka cire" ya kame fuska tare tsare ta da idanu a hankali ya zare
raguwar ƙanƙarar dake bakinta "leƙe ko? baki san mijin naki ba ne" tayi murmushi ta
ce "Abba naga ka ƙara babba, kayi kyau shi ne fa" ta ƙare maganar tana son ƙwace
ƙanƙarar daga hannu shi.
Shiru ya yi hakan ya sa ta ce "Ka bani to, yawuna duk ya tsinke" ya ƙara haɗe fuska
ta ce "Don Allah, wallahi zan maka amai idan baka ban ba"
Ya sauke numfashi yana juya idanu a hankali ya ce "Me ya sa? sanyi zai miki illa
fa?"
Ta saƙalo wuyan shi hannunta ɗaya tana shafa sajan shi zuwa dugun gemun shi ta ce
"Kawai naji ita nake so, bana son komai sai ita"
ganin da gaske ice ɗin take so, gashi nan tana ƙoƙarin kakarin amai ya yi saurin
zura mata a baki, taka duguwar ajjiyar zuciya idanunta na lumshe duk ta narke a
hannun shi.
A hankali ta ji saukar hannunsa a flat ɗin cikinta ya shafa kaɗan, tayi saurin
kallon shi, Yaa Sheikh soyayyar abin da ke cikin matar malam ɗin ya mamaye zuciyar
shi, yana ƙara yiwa Ubangiji godiya daya azurta matar da zuciyarsa ke so fiye da
komai, da samun cikinsa jininsa ke kwance a ƙasan mararta.
"Allhamdulillah!"
Ya faɗa a taƙaice. Halisa ta ce "Abbana mene?" A daidai kunnanta ya ce "My
kankanaty, baki san azumi nake ba? Ohya ɗaga ni" ta ce
"Azumin me Yaa Sheikh?" Halisa Said while playing with his beard.
Ya ɗaga ta daga jikinsa yana nufar bathroom ya ce "lokaci, sallah" yana ƙoƙarin
shiga cikin toilet ɗin yaji ta rungome shi ta baya hannunta bakiɗaya ta saka ta
riƙe ƙugun shi, ƙirjinta dake gogar bayan shi ya sanya tsigar jikinsa ta shi, ya
rufe idanu a fili ya ce
"Yasubuhanallah! Ya Rasulullah! Zaki ɗauki hakki" ta saki dariya sosai ta ce "hakin
me zan ɗauka Abba?" Yana ƙoƙarin magana yaji saukar hannunta inda bai yi tunani ba,
ya zare hannunta daga marar shi kamar zai kuka, duk ya ɗan birkice ya kame fuska
tare da juyawa ya ce "Burinki ki karya azumi? Allah ya takaita mini wahala an kira
sallah na yarda mata shaiɗanu ne wannan ɗaukan hakƙi ne Zawja"
Ya yi saurin turata baya tare da tura ƙofar tana dariya ta ce
_“I love you Yaa Sheikh Ya shehin malamina”_ Ya girgiza kai kawai kamar yadda Ummul
ke yi idan abu ya bata mamaki, ya daɗe tsaye yana mai da numfashi, ya tabbatar da
kafin a kira sallah tai masa haka to ya yi wahalar banza babu inda azumin za shi.
Wanka ya yi sosai kana ya ɗaura alwala, ya fito jikinsa na zubar da ruwa ƙamshin
Lifeline skin care pro plus shower Gel na fita daga Jikinsa ya shirya cikin wata
white Embrodiery design jallabiya, ya ɗora hirami tare da rufe kan shi sai fuskar
shi da gemunsa dake bayyane, direct fita ya yi ƙamshin Roja ya sanya Abba Hakimi da
Mai martaba kallon direction ɗin duk da sun riga san waye, bai magana ya nufi
Masjid. Bayan yaja sallah ya dawo gida kai tsaye part ɗin shi ya nufa, Mother na
zaune ita ma idar da sallarta kenan ta kammala shirya wa Yaa Sheikh kayan buɗe
baki. Ta kalli Halisa data fito sanye da blue ɗin hijab ta ce "Daughter ga Abincin
Yaa Sheikh maza zo ki kai masa" kafin Halisa tai magana Abba Hakimi ya ce "Ba dai
ita ba, ki kai masa da kan ki, idan kin kai kice ina buƙatar ganin shi da zarar ya
gama" Halisa bata ji daɗi ba, amma ta kasa cewa komai ganin Abba Hakimi ya haɗe
fuska sosai. Mother ta kai masa ta kuma sanar masa umarnin Abba.
Suna zaune duka a parlour Dada ta fito wani ihu Halisa tayi tare da rungome Dada
idanunta cike da hawaye ta ce
"Dadata nai ta jiran ganin ki" Dada tai murmushi sosai wani daɗi ya kamata ta ce
"Ke kam baki girma" Umma A'isha ta ce "Ba batun girma, ni dai abin da ke tare da
ita nake ji, garin tsalle tsallen nan zai a zubar da shi" Mother ta ce
"Ah Allah ya ki yaye Umma, na lura wasan jika da kaka ki kewa Daughter" ita Halisa
hankalinta na wajan Dada ta ce "Ina ki kai shiga, Dadata nayi missing naki da yawa"
Data ta zauna tana cewa "Munje wajan El-bashir duba jikin shi" Annurin fuskar
Halisa ya sauya jin ance El, bata mance abin da ya yi wa Abbanta ba, kuma ita ma ba
zata taɓa son shi ba. Ta zauna tana cewa
"Ina Shatu?" "Tana Rugar Rome, za a kawota gobe idan Allah ya kai mu" Halisa ta
miƙe ta ce
"Bari na faɗawa Yaa Sheikh kin zo ko?" Ba walwala a fuskar Abba Hakimi ya ce
"Kada naga ƙafar ki a part ɗin shi" tayi saurin cewa "To me ya sa, bayan lada zan
samu" Mother ta ɗauke jin za a fara halin, Umma A'isha murmushi kawai take, Dada
kuma tai shiru dan ba huruminta ba ne.
"Haka na ce, muddin ki ka je ki tabbata zaki bi iyayenki Masarauta" ta haɗe fuska
idanunta na kawo ruwa cikin rawar murya ta ce
"To a gasky Jon wuro ban gane ba, gwara kawai mu koma makka zaman can yafi daɗi
tunda babu saka idanu" Abba Hakimi maganar ta dage shi, yasan kuma da iyakar
gaskiyar ta take faɗa. "Tashi kibar wajan nan Dajeno" cewar Dada ta miƙe tare da
yin bedroom ɗinta ta ce "Mutum da mijinta"
Gabaɗaya sukai kamar basu ji me ta ce ba, Abba Hakimi ya tura a kira Zahrah ba
jimawa ta fito ɗauke da jaririn. Zamanta kenan ƙamshin Roja ya daki hancinta, tayi
saurin lumshe idanunta nutsuwa na saukar mata, ta tsare Yaa Sheikh da idanu shi kam
bai kalli inda take ya nemi waje ya zauna saman kujera yana rufe.
"Aliyu na kira ka domin kayiwa Yaron Zahrah huɗu ba" Ya kalli Abba Hakimi na wani
lokaci kana ya jinjina kai, da sauri Zahrah ta miƙawa Yaa Sheikh babyn da yake ta
barci gwanin sha'awa ya ƙara girma, a hankali ya ɗora bakinsa a kunnen bbyn tare da
yin Bisimillah kana ya yi masa huɗuba da suna.
MUHAMMAD.
"Ma sha Allah, Rabbi ya raya Muhammad" cewar Umma A'isha Dada ta amshi yaron,
hawaye ne ya dinga sauka daga idanun Zahrah ji take kamar taje ta rungome Yaa
Sheikh ta ɗora kanta a shoulder ɗin shi tayi kuka mai yawa ko zai tauyasa mata, ta
goge hawayen ta ce "Na gode Yaa Sheikh, don Allah kayi haƙuri ka yafe mini"
Kamar daga sama su kaga Father ya faɗo parlourn hannunsa riƙe da Zeefa ya fita
hayyacinsa ya zube gaban Mother ya ce
"Maryam ashe zaki iya kai uban yaranki ƙara court?" Tai masa Shiru idanunta akan
Auta Fattoumah ta miƙa mata hannu da sauri ta nufi mother tana zuwa ta rungometa,
Maimoon na tsaye taci kuka ta ƙoshi komai ya daina yi mata daɗi. "Ki tausaya mini
ki janye wannan ƙarar" tai wani irin dariya tana kaɗa ƙafa ta ce
"Wallahi Allah kaji na rantse maka Engineer Aliyu sai ka sakeni wannan cikon ɗayar
da Jadda ta hanaka ita nake buƙata yanzu" kamar zai kurma ihu ya ce
"Wallahi ba zan taɓa rabuwa dake ba Barrister sai dai mu zauna daga ni harke ba
aure" Mother ta ce "Ka zauna dai? Amma ni aure babu fashi wata ɗaya ya yi yawa
banda darajar idda, kuma banda abinka baga uwar shegen ɗanka nan ba sai ka aureta
kuci gaba daga inda kuka tsaya"
Da sauri Auta Fattoumah ta ce "Mother bana son babyn na tsane shi ba ɗan uwanmu
bane" Mother ta ce "He never been your brother Mamana, tafi bedroom ki kwanta"
Father ya yi saurin janye Auta Fattoumah ya ce "Ta tafi ina? Ƙafata ƙafar yarana
idan kin damu da su ki dawo gare su, na shirya shi ga Court duk abin da zaki kiyi
amma ba zan taɓa sakin ba" ya ɗauki Auta Fattoumah tana rusa ihu ya saka hannu ya
kama na Zeefa da Maimoon sukai waje.
Da sauri ta miƙe zata bi bayan shi Abba Hakimi ya ce "Kada ki fara" takaici ya sa
tayi bedroom tana sakin kuka. Abba Hakimi ya kafa ya tsare daga Halisa ta fito yake
fatattakarta bedroom, Ogan da kan shi ya fito yana fitowa suka haɗa idanu da Abba
Hakimi, bai ce masa komai har Yaa Sheikh ya gama zaman shi ya koma part ɗinsa, ya
kasa barci ɗumin jikin matar dana gudan jinin shi kawai yake so yaji, gashi gobe
Alhamis zai ta shi da azumi still, ya miƙe da ƙyar ya nufi bathroom ya saukarwa
kansa ruwa mai sanyi ko zaiji sauƙi, ɓangaren Halisa kusan haka ne, cikin dake
Jikinta ya ƙara mata muguwar sha'awa ta buƙatuwa fiye da kima, gashi ita babu
damara ta dinga malelekuwa a kan gado, da ƙarshe ta miƙe zaune tare da fashewa da
kuka, su duka sai bayan sallar asuba barci ya ɗauke su.
Washegari parlourn Abba Hakimi ya cika da mutane har wanda Yaa Sheikh bai zata ba,
Uncle Haroon, Uncle Bashir, Mahaifin Zahrah da Mimi, tare da Surry, Mother, Umma
A'isha, Dada, Yaya Halima, Dr A'isha. Sai Ummul dake zaune gefe guda cikin wani
white lace mai kyau da tsari, ƙamshin Roja da taji yasa ta ɗago kanta zuwa inda
jarumin ɗan nata yake tsaye, Yaa Sheikh mamakin yadda duk mutanan suka zo lokaci
guda yake, ya nemi waje kusa da Ummul babu ko kunya ya zauna. Aka buɗe taro da
addu'a Kafin Abba Hakimi ya kalli Uncle Haroon ya ce "Haroon ɗan fito mini da dairy
ɗin nan" Uncle Haroon ya miƙawa Abba Hakimi, shi kuma ya buɗe wajan deal ɗin su da
Yaa Sheikh da saka hannu da komai. A hankali ya miƙewa Yaa Sheikh ya daɗe kafin ya
saka hannu ya amsa. Abba Hakimi ya ce "Ka duba deal ɗin nan, ka yanke hukunci
tsakanin ni da kai ga shaidu a gabanmu, ka riƙe amana? Ko dai kaci Amana? Kai inama
zaka ci wata mana bayan baka son ta, ba zaka taɓa son ta ba har abada....
[1/14, 10:34 AM] Abk: _*Ga masu buƙatar yi musu tallah su yi magana 08119237616,
har kullum Idan ba ke na kuɗi ne akan ₦500 🫰🏽1k for Special*_


Uncle Bashir ya ce "Abba Hakimi da anyi masa afuwa, hakan ma kaɗai ya isa yaji
nauyinka" Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh yana jinjina ƙarfin hali da zurfin cikin
shi ya ce "Anya Bashir? Ai Aliyu bai ɗauki hanyar da zamu shirya ba, basshi ya faɗa
mini saka hannun waye wannan a cikin dairy ɗin?" Yaa Sheikh ya rufe ido ya buɗe,
yana mai ta'ajujin abin a ran shi, gabaɗaya ya manta da batun wani deal a tsakanin
shi da Abba, shi bai ga abin ɗaga zancan ba idan ba so Abban yake ya kunyata shi
gaban sirikan shi ba. "Sa hannuna ne"
Ya faɗa a taushashe yana mai daidaita zaman shi babu tsoro akan idanunsa, cikin
nutsuwa ba kwanakwana ya shaidawa Abba Hakimin haka. "Hakan na nufin kaci amana
kenan Yaa Sheikh?" Yaa Sheikh ya yi shiru he refuse to answer the question. Ya
ƙara cewa "kamar ba babban malamin da ya yi magana akan al'ƙawari da muhimmancin
shi ba?" Yaa Sheikh ya zare nauyin Abba Hakimi da yake ji cikin ladabi ya ce
"Abba na fa ce maka ba zan iya ba? Ka manta ne?" Dr A'isha tayi saurin cewa "Ba
zaka iya riƙe amanar ba?" Ko inda take bai kalla ba, amma yadda ya kame fuska waje
guda zaka san mganar ta, sam ba tayi masa ba, kuma bai fiya son shisshigi ba a
rayuwar shi.
Abba Hakimi ya yi murmushin manya ya ce "To ka amsa mata mana?" Yaa Sheikh ya harɗe
hannunsa a ƙirjin tare da yin baya idanunsa rufe, Ummul kanta a ƙasa ba ta ce komai
ba, amma ita kanta zurfin cikin Yaa Sheikh yana damunta kuma a shirye take da huran
da Abba zai masa
"Kada na sake tambaya kayi mini shiru Aliyu" Yaa Sheikh ya ce.
"Abba nifa na nemi aurenta, taya zan riƙe wannan deal ɗin?....," Dr A'isha ta ƙara
cewa "hakan nuni da cewa kana

Please Login or Register in order to submit comment