You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki" Idanunta ya cika da hawaye ta ce
"Ba komai Abba, Yaa Sheikh ya yi mini komai yasa na san wace ni ya bani ilimi
sanadin shi na zama mace komar kowa Allah yasa zaɓin shi ne ya zama alheri a gare
ni" Abba Hakimi ya miƙe yana faɗin "Allah ya yi miki Albarka Zahrah, mun yi magana
da Alhaji Farouk mahaifinki ya amince idan ba damuwa ba sai kin koma ba za a kawo
miki Muhammad ɗin"
Tayi godiya Yaa Sheikh miƙe yasan kawo yanzu Halisa hankalinta ya ta shi ta ce "Na
gode sosai"
Yana yin waje abin shi ya ce "Ki ɗauke ni like a brother to you komai ki ke so come
to me, happy marriage life" ya yi waje abin shi ta bisa da kallo zuciyarta nayin
wani zafi. Lokacin daya isa gida Jadda ta jima da yin barci, direct part ɗinsa ya
nufa ya cire Jallabiya ya yi wanka ya sauya kaya zuwa white Pajamas riga da wanda
sai ƙamshin Roja yake yana jin zuciyarsa ta rage nauyi sbd hakƙin Zahrah daya
sauke, daman bata da iddar shi wannan dalilin ya sanya ya ɗaura mata aure da
Saifuddeen wanda shi da kan shi ya amince. Steps ɗin benen yake takawa zuwa
downstairs a haka ya nufi part ɗin Madam Halisa ya murɗa handle bakin shi ɗauke da
sallama, bashi da tabbacin tana parlour sai ta shige bedroom ya sameta tsaye gaban
wardrobe,tana ƙoƙarin sanya night gown cak taji an ɗage ta sama, ta zaro
kumburarrun Idanunta waje ta ce
"Habibi kaya zan saka" yana kwantar da ita tare da rufeta da ƙirjin shi yana goga
mata fuska a wuyanta yana shaƙar ƙamshi murya can ciki ya ce
"No need" ta riƙe shi ta ce "Please mana, kuma.....,"
"Zawja tsarin iyali?" Ya faɗa yana ƙara taɓa gefen hannunta. Ta ce
"Sbd Hala na saka, kuma kasan yanayinka Habibi" ya yi ta kallonta idanunsa sun yi
jajir jijiyoyin kansa duk sun fito sai huci yake ya tsareta da manyan idanunsa a
hankali ya saketa tare da miƙewa zai fita ta diro daga kan bed ɗin tare da shan
gabansa ta ce "Ka fahimce ni Please Habibi bada wata manufa nayi haka ba" ya saka
hannu tare da matsar da ita gefe, ta ƙara yin gaba zata riƙe shi ya buga mata wata
kyakkyawar tsawa cikin faɗa ya ce
"Move!" Taja jikinta wanda yake ta rawa da ɓari bata taɓa jin tsawar daya shigeta
irin wannan ba, sanadin haka ya tayar da Hala ta saka kuka kafin ta ƙarasa yaje ya
ɗauke yarinyar shi tare da bar mata ɗakin.
Kuka ta dinga yi hankalinta ya tashi bata taɓa hango masifar Yaa Sheikh a ƙwayar
idanunsa kamar yanzu ba, ta jima tana kuka wajan ƙarfe 12 ta miƙe ta nufi upstairs
ta samu ƙofar shi a rufe, ta dinga knocking yana jinta ya share. Yaa Sheikh ya daɗe
bai shiga ɓacin rai irin wannan ba, yana so da ƙaunar zuri'a mai yawa da kuma
albarka amma ace tun a haihuwar fari mace tayi tsarin iyali me hakan ke nufi? Ya
dubi Hala Sheikh Aliyu haydar dake ta sukur-sukur a ƙirjinsa ta ƙiyin barci da
alama nono take buƙata, ya shafa kan yarinyar dake cike da suma gwanin sha'awa
kamar ya tsokanota ta saka kuka tana shura ƙafa, ya shiga jijjigata amma fir Hala
taƙi yin shiru zam-zam ya ɗauka ya bata ta sha sosai yarinyar akwai kuka kamar
mahaifiyarta.
Ya sanyata a kafaɗa ta shiga tsotsar fatar wajan murmushi mai laushi ya yi ya ce "I
love you Hala, and i so much love your mother amma halinku ɗaya, mene laifi don ta
sake yin ciki bani nake bata ƙwayayen ba? Ni ban gaji ba sai ita?"
Tayi masa ƙuri da manyan fararen idanunta kamar mai fahimtar mai yake cewa a haka
suka raba dare da ƙyar tayi barci tana tsotsar lips ɗin shi kamar ta samu nono ya
rungumeta yana ƙara jin soyayyar mahaifiyarta a ran shi ya kasa barci kamar yadda
Halisa ta kasa.
Da azuba tana farkawa Idanunta ya sauka akan Hala tayi mmkin yadda aka sauya mata
wajan kwanciya domin a ƙasa barci ya ɗauke ta dab da Subhi yanzu kuma ta ganta akan
gado.
Sallah tayi ta goya Hala ta shiga kitchen ta haɗa breakfast, tana gamawa ta yiwa
Hala wanka ta shiryata ba jimawa barci ya ɗauke ta itama tayaya wanka ta shirya
tsaf cikin wani green lace mai kyau ta murza ɗauri.
Ta samu Jadda a parlour tana shan tea ta haura upstairs, tayi sallama ya amshi
murya can ƙasa yana zaune saman kujera ya ɗora ƙafa idanunsa sanye cikin glasses
hannunsa riƙe da azkar sai laptop a gefe da mug ɗin coffee ta tsokana ta ce
"Mrng Habibi" ya amsa a ciki ta ce "Breakfast is ready" ya yi mata banza. Abu kamar
wasa har tsayin sati Yaa Sheikh ya ɗauke mata huta tsakanin shi da ita gaisuwa idan
ya tabbatar lafiya take sai ya ɗauke hala. Tuni Jadda ta gudu tace ba zata iya da
masifar shiru ba.
A kwana na goma ta same shi kwance ya lumshe idanunsa dawowar shi kenan daga duba
banks da Companies ɗin shi da gidan marayu. Ya ƙarasa gidan Abba Hakimi ya duba
Umma A'isha dake zazzaɓi ya samu Zahrah ta ɗan kwantar da hankalinta.
Yana jinta yaƙi magana ta daddage ta fasa masa ihu aka tare da birgima, bai san
mene ya faru ba sai ganinsa shi ya yi riƙe da ita yana jijjigata ya ɗauka aljanu
take.
"Ke lafiya Zawja?"
"Abba ka mayar dani gida tunda baka so na baka ƙaunata ka juya mini baya, na baka
haƙuri nace na cire in-plan ɗin" yaja jiki ya kalleta da kyau ya ce.
"Zawja ni ne baki so, tunda baki son bani zuri'a daga gareki" tana kuka sosai ta ce
"Kayi haƙuri Habibi ba zan sake ba, surutu ne bana so kada a ganni da wani cikin
nayi maka al'ƙawari haihuwa har sai lokacin da Ubangiji zai tsayar da ita daga
gareni"
Ya kalleta kawai daman tuni ya huce domin sunyi magana da Ummul kawai ya rabu da
ita ne yaga gudun ruwanta. Ta dinga kuka ya ce
"Meye?" "Baka kuya mini baya ba ƴarka kawai ka sani" Ya sakko daga kan kujerar ya
juya mata baya ya ce "Hau" ta maƙale kafaɗa ya ce "Ai baki isa ba, ga bayan nan
dole ki hau" taƙi ya ɗauketa ya sata suka zagaya wajan kana ya sauketa.
"Me ka ke so?" Ya girgiza mata kai ta ce "Kana nufin babu? Abba kwana goma bama
tare fa?" Ya buɗe baki zai magana tayi saurin haɗe bakinsu ta shiga bashi wani
kyakkyawan kisses a wannan lokaci sai da Halisa ta goge gabaɗaya fushin Yaa Sheikh
ta ƙara bashi mmki domin ta gama gane lagwan shi.
*2 months later*
Mai gadin su Fattoumah aka yanke masa hukuncin jifa kamar yadda addini ya faɗa, ɗan
shi kuma aka yanke masa hukumcin zaman kaso akan amfani da kayan soja da tuhumar
shi kan siyar da miyagun kwayoyi. Ɓangaren Fulani Atine hauka sai abinda ya ƙaro
babu sauƙi cikin lamarin.
Dada na fama cikin wata huɗu, Maimoon da Hafsat duk cike gare su haka matar
Saifuddeen.. a lokacin Zeefa ta samu miji itama aka sanya aurenta. Rayuwa taiwa
kowa daɗi banda Surayyerh dake faman neman miji idanu rufe amma bata samu ba,
gabaɗaya samarin sun gudu taƙi amfani da damar da Ubangiji ya bata tun tana da
lokaci taƙi amfani da shawarar mahaifiyarta.
Ummul ta riƙe Shatu wajanta tana kula da komai nata taƙi yin aure duk har zuciyar
Yaa Sheikh yana son yaga mahaifiyar ta shi da aure amma ya kasa furta mata. El
tunda ya ɗauke Fattoumah Angela ba'a ƙara jin motsin shi ba.
Ta dubi cikin gerden ɗin da ya ya yi mata kyau sosai a hankali ta ɗaga kanta zuwa
gefe wajan wani ruwa taga an saka.
*_Happy 1 year Anniversary_*
Ta ƙara juyawa zuwa wani wajan da aka saka _*To My wife Zawja*_ ta dubi ƙaton zanan
heart ɗin gently ta taka zuwa ƴar rumfa mai kujeru guda biyu an saka cake a tsakiya
da ƙaton frame na picture nasu su biyu an rubuta.
_*"OUMU-HALA*_ Marrying you was the smartest thing I ever did, happy 1 year
Anniversary Zawja"
[2/23, 4:59 PM] Abk: _*IDAN BA KE 83 End*_
O Allah, I have greatly wronged myself and no one forgives sins but You. So, grant
me forgiveness and have mercy on me. Surely, you are Forgiving, Merciful. My
biggest Fans i no words to thank you, ban sani ba amma kullum masoya ƙaruwa suke,
Ba zan saka *IDAN BA KE* cikin tops popular book's ba, but i can say zai iya zama
The best book among the other's, godiya ga *Paid grp 1* godiya ga *Paid grp 2*
special thanks to *My special grp* girmamawa ta musamman ga *Arewabooks* Nimcyluv
sarauta loves you always forever ever.

_Special thanks to these people who are important to me_ NASIR NID, FAUZIYYA D
SULAIMAN BRIGHT PENS, Sauran marubutan da suka bibiyeni a wannan littafin kuna da
yawa i can't list them thank you all.

Thank you my parents thanks for support and care rabbi ya saka muku da alheri. 🤣 Ƴan
wasa na ina godiya Uncle Sheikh Aliyu ina tsoran haɗuwa da kai serious, Brother
Bashir Mubasshir, Ummul and the rest Sorry Khalil . _Oh! I almost frgt to thank my
people those who read my book as free nasan soyayya ce ba zance ban yafe ba amma
littafin kuɗi ne ga duk wanda ya yi niyyar biya contact me 08119237616. Ƙofa a buɗe
take ga abinda aka yi kuskure, yabawa, jinjinawa, sharhi yadda kuka ji daɗin
labarin da gyaran ban ɗaukewa kowa ba am ready to accept my mistakes👏🏻_
Complete Book 1 2 ga mai so dubu ɗaya 1k.

This page dedicated to my husband much much love ❤️❤️❤️❤️❤️



Ta juya da sauri domin ba ƙaramin surprising nata ya yi, idanunta cike da ƙwalla da
kuma soyayyar mijinta ta riƙe Yaa Sheikh ta ce
"Yaa Allah, i so much love you Habiba you're the best husband ever Allah ya ƙara
maka arziƙi da wadata ya taimake ka" ya holding nata back yana sakin murmushi mai
kyau idanunsa lumshe ya ɗauki wayarsa tare jawota jikinsa sosai ya yi musu selpie.
Hala nada shekara ɗaya ciff a duniya Halisa ta kuma samun wani cikin a wannan
lokacin farin cikin Yaa Sheikh har yafi na baya, Ummul ta kalli Yaa Sheikh daya
fito daga ɗakin grandpa ɗin shi ta ce "Ku barni mini Hala mana, sbd yayeta dole za
tayi" Ya kasa cewa komai domin ba ƙaramin nauyi ya ke ji ba, ganin yanayinsa ya sa
ta ce "Ina Halisar fa?"
"Tana wajan Mubasshir waje" Ummul ta buɗe ido ta ce "Yau kuma, yaushe yazo da
Fattoumah?" Yana yin waje tare da covering jikinsa da Alkyabbar jikinsa ya ce
"Uhm maybe yau ko?"
"Ok kirata muji" ya nufi waje tun daga nesa ya hango hasken fatar jikinta domin
shigar sabon cikin ya sanya tayi wani irin fari kamar wacce jini ya ƙarewa.. da
idanu ya kalleta ta miƙe tsaye tana kallon Fattoumah ta ce "Mijina na kira, ke kam
Hamma El ya lalata miki tarbiyya" El dake jingine jikin mota Hala na riƙe gemunsa
yaji maganar Halisa sama-sama ya ce
"Angela me princess take cewa?" Fattoumah tayi murmushi ta ce
"Cewa tayi yaushe zaka sama mini kamar Hala?" Ta faɗa tana kashe masa idanu ɗaya.
Ya girgiza mata kai ya ce
"Bayan ajjiyar da nayi tun watan daya shige wani kuma ki ke so? Don't worry I'll
give you more"
"Kasan kuna kama da Hala? Dama kawai abar mana" El ya ce
"Rufa mini asiri Angela daga Abba Sheikh har Princess babu mai iya bayar da Hala
wannan yarinyar kamar gold, kuma maganar kama ai ba abin mmki bane ni da babarta
kamar twins haka muke wajan kama da juna, Hala kuma kamar su ɗaya da babarta that's
means mu uku muna kama da juna"
Fattoumah dariya tayi tana shigewa cikin gida wajan Ummul El Yabi bayanta yana zuwa
Halisa ta ce "Prince ɗan muga Hala zan saka mata ring" bai kawo komai a ran shi ba
ya miƙa mata ita ya shige ciki, yana shiga Yaa Sheikh ya kama hannu matar shi zuwa
mota ya jasu har zuwa airport a hanya ya kira Umar-khan suka haɗu ya bashi key ɗin
motar Umar-khan na tsaye shi da Hafsat da Jaririyarta mai suna Ajimal har jirgin su
Yaa Sheikh ya lula sama zuwa gari mai albarka Madinatul-munauwara.
A vip suke _very important people_ suna shiga ya zame Alkyabbar jikinsa ya ajjiye
gefe yana lumshe idanunsa tare da jan numfashi sai yanzu abin ya bashi dariya da
kunya sun gudu da ƴar su sbd kasa su barta wajan Ummul. "Habibi ƙalbi naji kunyar
Ummul"
"Uhm" ya ce yana kallonta kafin a hankali ya miƙa mata hannu ya ce "Zo kiji" ta
kwantar da Hala a kan wata kujera ta ƙarasa wajansa suka kalli cikin idanun juna,
ba zata iya cewa ga abinda Idanunta ya hango mata ba, tana karantar kallon shi, ko
shirun shi amma yau abubuwan da suke gilmawa a cikin idanunsa daban suke.
"Shekarar ki nawa ne?"
Tambayar ta bata baki sosai kafin ta ɗaga Idanunta sama alamar tunani ta daki
ƙirjin shi ta ce "I think 18 going to 19 what happing?"
Ya girgiza kai ya ce
"No! kin zama big Mama Zawja" tayi dry sosai tana kama gemunsa tare da kitsawa ta
ce
"Ba dole ba, ina samun kwanciyar hankali, soyayyar miji kulawa ka romantic style
naka kala-kala" ya zura hannunsa a ƙirjinta yana sauke wani zazzafan numfashi
idanunsa ya jirkice ya tura kan shi a wuyanta tare da manna lips ɗinsa ya shiga bin
fatar wajan da tongue ɗin shi. "Modibbo"
Ta zame fuskar shi da ƙyar ya watsa mata idanu ta ce "I love you Modibbona" ya
runtse idanu ya buɗe yasan bata san tasirin da I love you ɗinta ke da shi a
zuciyarsa shi ne a sanya kullum take narkar masa da zuciya da hakan.
"Tsoho ki ke so?"
"Bana kallon tsofan kyakkyawan saurayi nake kallo" ya jinjina mata kai tare da kafe
ta da kallo.
"Wannan kallon fa?"
Ya riƙe kafaɗunta cikin nutsuwa ta sarƙewar murya ya ce
"Shekaruna 37 cif, shekarunki 19 lokacin cika she 40yrs kina 22 ba za kiga tsofana
da furfurana ki juya mini bay...," Bakinta da yaji cikin nasa tayi masa wata
kyakkyawar sumbata yasa ya ƙarasa haɗiye sauran maganar a zuciyarsa. Sai da tayi
kisses nasa da kyau kafin ta ce "Har abada, gaban abada idan zan rayu to dakai ne"
Ya lumshe ya girgiza "I feel empty without you IDAN BA KE Just..."
Sai kawai ya rungumeta a ƙirjinsa yana shafa cikinta ɗumin cikin na ratsa hannunsa
farin ciki sosai yake ciki za'a ƙara haifa masa Baby.
Sai dare jirginsu ya sauka haɗaɗɗun motoci suka zo ɗaukan shi, har gidan shi aka
kai shi daren ranar basu runtsa ba gefe guda aka ajjiye Hala suka kwashi soyayya
mai cike da tsafta. YAA SHEIKH bakinsa baya iya furta abubuwan da yake ji game da
Halisa Danejo Rome, gangar jikinsa ita ke fansar bakinsa hakan yasa yake ƙara
shigewa zuciyar Halisa a ko wanne lokaci,ko wacce daƙiƙa ko wanne harbawar seconds.
Faɗan su baya ɗorewa domin Halisa ta gama gane waye mijinta duk son da yake mata ta
nayin ba daidai ba zai rufe idanu ya yi mata faɗa tas, idan kuma ta ce kawai ya
mayar da ita gida a lokacin zan sakko daga dokin zuciyar tare da accepting
apologies ɗin ta, ta hanyar sauke mata mazantakar shi.
Ɗaliban shi na ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA. Sukai farin ciki sosai domin suna
ƙaunar lecture ɗin shi, yana nan da kame kan shi fuska kame Kullum ya ƙara daddako
cikikar kamala kwarjini ba a magana.
Rayuwa ta dinga juyawa ci-gaba ya dinga zuwa ta ko'ina, a haka har Halisa ta ƙara
haihuwar kyakkyawar yarinya sak mai kama da ita, idan Yaa Sheikh ya kalli Halisa ya
kalli Hala ya kalli Rohna mamaki yake gabaɗaya kamannin Zawja suka ɗauka lallai ya
amince Ƴar fillo ta fishi fitina da ƙwazo. Da shi da wata bahaushiya suka dinga
kulawa da Halisa har ta samu cikakken wata biyu. A wannan lokacin ne kuma aka fara
azumi. Ana gobe sallah tarihi ya maimaita kan shi domin kiran gaggawa suka samu
daga ƙasa Nigeria an kuma ƙi faɗa musu abinda yake faruwa. Babban tashin hankalin
Yaa Sheikh bai shige yadda yake kiran Ummul wayar a kashe a haka har suka dira a
Nigeria.
Lokacin biyu ga sallah Halisa ta samu tayi Oummara a karo na biyu hajji ne Allah
bai bata iko ba. Yaa Sheikh ya dubi idanun El-bashir da yazo ɗaukan su a airport,
sosai ya firgita da yanayin El. Ya kasa jurewa ya ce "Mene ya faru Mubasshir?" Da
sauri El-bashir ya rungume Yaa Sheikh yana sakin ajjiyar zuciya.
Maimoon wacce ita tayi namijin ƙoƙarin bayanta goye da Ajimal ta amshi Rohna Shatu
ta amshi Hala wacce ta fara dabo Yarinyar gwanin sha'awa tayi ƙiba sosai sai tayi
kamar haifaffiyar Makka ɗin. Halisa ta kasa fahimta tunaninta ya tsaya duk yadda
taso ta fahimci abinda yake faruwa ta kasa ganewa. Da ƙyar El ya yi driving har
zuwa gida tun a ƙofar gida ƙirjin Yaa Sheikh ya buga sbd cikar mutane.
Ganin Yaa Sheikh ya dawo musu da mutuwar sabuwa fil! A zuƙatan su Umar-khan, Ishaq-
Hakim, Saif-wazir suka rungume Yaa bakiɗaya suna kuka sosai domin yanzu shi suke
kallo matsayin Uba.
Mother, Dr A'isha da Yaya Halima duk suka zagaye shi tare da zuba masa idanu ya
rasa mene ke faruwa da shi, ko a ba'a faɗa ba kai tsaye ya fahimci cewa Abba Hakimi
gone, he's no more, he pasted away!
That's means Halisa's grandpa babu shi baya nan a raye a wannan duniya.
Ya zame jiki da ƙyar kai tsaye part ɗinsa na gidan Ya nufa jiri na kwasar shi luuu
ya yi Ummul dake zaune daman ta san za ayi haka tayi saurin riƙe shi, gabaɗaya
jikinsa rawa yake ya rungume Ummul sosai ya hanata motsi lokaci ɗaya zazzafan
zazzaɓi ya rufe shi, Shi ɗaya tal a duniya ya kewa kallon Uba majin gina tun yana
yaro a ƙasa matsayin rarrafe Abba Hakimi ya fifita shi fiye da yaran daya haifa.
Tsayin kwana uku babu mai zuwa wajan Yaa Sheikh ya yi tawakkali amma shirun bayin
kan shi bane, jama'ar dake kan shi suka rufe masa baki baya ko tari sai kallo da
idanu. Lokacin daya dawo daidai abinda ya fara tambaya shi ne mene ya faru? Aka
shaida masa ciwon ciki ne farat ɗaya bayan ya ɗauki sahur da asuba kafin Assalatu
rai ya yi halin shi. Yaa Sheikh ya tattara gabaɗaya dukiyar Abba Hakimi akaiwa
yaran shi rabon gado. Tun daga ranar suka ɗauki Yaa Sheikh matsayin Uba yadda su
kewa Abba Hakimi kallon Uba haka suke masa.
Ya tsaya tsayin daka akansu har tsayin shekaru huɗu lokacin yana da shekara 40
ciff, yaransu biyar Hala, Rohna, Huda, sai namiji Aka sanya masa sunan Abba Hakimi
suna ce masa Hakimi sai ƙaramin su Taujid. Huda da Hakimi tagwaye aka haife su,
kwanakina take zubawa sosai duk shekara sai ciki abin ya dameta amma fur Yaa ya
rufe idanu ya ce Allah ya hore masa idan ma duk wata zata haihu dole ta dage da
gyara.
Zahrah duk daga kan Muhammad bata sake samun haihuwa ba data samu cikin zai zube
baya zama, haka ya riƙe Muhammad ya yi wayo sosai. Umar-khan da Hafsat a tsayin
shekara shida ɗin nan yaransu biyu, haka Maimoon da Khalil, El-bashir Ahmad Nuran
Sarki da Fattoumah Aliyu ɗan su ɗaya mai sunan mai martaba a yanzu kuma shi ne
Sarkin Sokoto.
Arziƙin Yaa Sheikh ya ninka haka bisa jajircewa da taimako.
*20 year's later*
Gidan cike yake Hala da Rohna sai kuka suke kamar ransu zai fita Hala ta ƙanƙame
mahaifinta tana cewa "Abbi ban so, ban son auren kada a rabani daku na fasa auren"
kuka take sosai Yaa Sheikh yana ƙaunar yarinyar shi ƙwarai komai nata na Halisa ne
shi yasa yake jinta daban a zuciyarsa. Ya rungumeta yana bubbuga bayanta shekarun
shi 60 cif ya zama babba mutum wanda ake kwatance da shi a hankali ya ce "Sorry
Mamana, sorry" ta girgiza kai tana riƙe shi Rohna kuma Halisa ta riƙe tana cewa
"Mami ki ce Abbi kada ya basu mu" school mate ɗinsu sai vedio suke musu haka
photographers abin ya zama wani extraordinary. Mother da Dr A'isha suna kallon ikon
Allah basu taɓa sanin haka Yaa Sheikh yake ƙaunar yaransa ba sai yanzu. Daga gefe
guda aka saki tsaki mai kyau Hakimi ya juya zuwa ga ɗan yaron da ba zai shige 16yrs
ba, baƙi ne shi sosai har sheƙi yake gabaɗaya shi ne ya banbanta a cikinsu ba zaka
taɓa cewa daga cikin Halisa ya fito ba, shi ne last born nata.
Labɓansa jajaye ne tas haka idanunsa farare ne gabaɗaya jikinsa zanan tattoo ne
ra'ayin shi ya bambanta da duka sauran yaran. Ya ƙara jan tsaki yana saka hannu
tare da har gitsa sumar kan shi wacce ta zama irinta Yaa Sheikh kala biyu. Hakimi
ya ce
"Abraham what exactly wrong with you?" Ya ɗaga manyan idanunsa yana miƙewa tsaye
tare da bada faɗi idanunsa na lumshewa kamar mai jin barci a hankali speaking
calmly ya ce
"I don't know what exactly wrong with me, wannan ihun yana gab da fasa mini kai
Please Hakimi do something i need to rest duk an cika mana gida da ihu kamar gidan
mutuwa"
Hakimi ya ce "Yaron nan baka da hankali, Big sister's naka suna kukan rabuwa da
Mami da Abbi damu kanmu amma kana zancan iska"
Abraham ya watsa hannu tare da buɗe ido sai ka ɗauka shi ne babba ya ce
"And so what? Na faɗawa Abbi yaran nan ba zasu iya zaman aure ba, dani ya yi wa ta
gidan ubanwa zan zauna ina kuka" Hakimi yabi ƙaramin ƙanin nasu da idanu yana mmkin
faɗin ran yaron har tsoro yake bashi. Abraham rai ɓace ya saka hannu ya fisge Hala
daga jikin Yaa Sheikh daidai lokacin angwayen suka shigo jin abinda ke faruwa.
Idanun Abraham har wani ruwa ruwa ne yake kwanciya cikinsu ya kalli Junaid-Ali ya
ce "Brother take your wife ta dame mu" Junaid-Ali ya yi murmushi ya ɗauke Hala cak
tana zunduma ihu ya yi waje da abar shi.
Haka ya ƙara fisgo Rohna ya damƙawa Abuturab ya ce "And you too take your wife" shi
ma ya riƙe Rohna yaran sunyi mugun shaƙuwa da iyayensu sosai. Huda kuka take sosai
na rabuwa da ƴan uwanta haka Hakimi idanunsa ya yi jajir banda uban tafiya Abraham
ko a jikinsa sai ma riƙe kan shi da ya yi da hannu bibbiyu sbd juyawa yake baya
ƙaunar hayaniya. Halisa ta juya zuwa bedroom ta dinga kukan rabuwa da yaranta
tausayinsu ya kamata.
Yaa Sheikh ya haura upstairs. Sauran ƴan bikin suka shiga mota zuwa rakiyar amare.
Yana daga kwance ya miƙe zumbur yana jan lafiyayyan tsaki ya ce
"Ni meye nawa laifin da ba za a yi mini aure ba?" "Kai yanzu idan akai maka auren
kayi me?" Ya girgiza kai kawai yana jin tambayar rainin hankalin da Hakimi yake
masa.
Ya haura upstairs zuwa part ɗinsa har ya juya ya ce "And don't forget wallahi
babbar mace nake so In sha Allah irin 40 to above ɗin nan ko 50" yana faɗin haka ya
shige part ɗinsa yana taune lips.
Surry har yanzu babu mijin aure, Jadda nan tsofa ya gama cin ƙarfinta Ummul daman
bata zo bikin ba sbd bata ƙasar bakiɗaya.
Shigowa ya yi ƙamshin Roja ya shiga hancinta ta ɗago suka kalli juna idanunta a
kumbure ya yi murmushi yana zare Glasses ɗin idanunsa ya ce "Mene ya samu Mami ne?"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Are questing me? Bayan an rabani da yarana" ya jawota jikinsa
ya ce "Oh! Sangartar Abraham ya yi yawa zo muje na baki wasu ƙwayayen haihuwar
yanzu ki ƙinƙishi"
Ya bugi ƙirjinsa ta ce "Ina tausayin Rohna" "Ni Hala" ta kalle shi ta ce
"Hala gaba take da Rohna fa?" Ya rungumeta yana zame hannunta daga riƙe fuskar shi
ya ɗauketa yana cewa
"Mamana halinki ta ɗauka, mijinta zai sha barbaɗa da surutun ba a tambayeta ba amma
bata da juriya kamar ki that's why" ta lumshe idanu ta ce "Thank you Abba, ka gama
yi mini komai I love you"
Ya yi mata rumfa sosai ya ce "Ni ne da godiya, kin bani Mamana, Kin bani Khadijah,
kin bani Mother Maryama (Huda) da Abba Hakimi, ga auta Ibrahimul-khalil Abraham,
kin zame mini komai kin mamaye mini gida da zuri'a masu Albarka, *IDAN BA KE*
that's means babu YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU" ya rufe idanu ta ce
"Allahamdulillah, Allah na gode daka bani miji kamar Yaa Sheikh i love You Habibi
ƙalbi"
Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir bakinsa ya shiga rawa ya faɗa buga kan shi, Halisa ta
tsaya kallon ikon Allah cikin sarƙewar harshe da wata In-ina ya ce
"I.... I... I...." Wasu irin hawaye Masu zafi suka sakko daga cikin idanunsa yana
matseta kamar zai rabata gida biyu cikin In-ina ya ce
"I.... I.... Lov...love... I love You" dam! Zuciyarta ta bada sauti sbd tasirin
kalmar tunda suke sai yau ya ce mata I love you, ya yi murmushi itama tayi murmushi
ta gama fahimtar a yanzu ba Yaa Sheikh ɗinta bane kawai ya juye zuwa MUTUM DA ALJAN
tana ganin yadda jikinsa ke murɗewa kamar wani maciji ya ƙara ɗaga murya ya ce "I
love you Zawja" yana faɗa yana rungumeta sosai ta ce "Allahamdulillah" tana faɗa ya
ce "I love you Haliyserh Sheikh Aliyu haydar Aliyu I love ƴar fillo,I love you
Danejo I so much love you princess Queen of my heart IDAN BA KE ba Sheikh Aliyu
haydar Aliyu Allahamdulillah"
"Abraham laɓe ka kewa su Abbi" ya kame fuska hannunsa riƙe da iphone system zai
kaiwa Yaa Sheikh

Please Login or Register in order to submit comment