You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Modibbona" Ya kalli direction ɗin Ummul yaga tuni tabar wajan ya jata
tare da mannata a jikinsa ya ce.
"Kankanata" ya zameta yana zama kan kujera ta zauna saman cinyar shi. Ta fara masa
surutu Ummul ta fito hannunta riƙe da tray. Tai kamar ba taga gansu ba, Yaa Sheikh
kuma ya rasa abin yi.
"Ummul" Halisa ta kira sunanta ta ce "Matar Malam, Abar Malam ya yi buɗe baki"
Halisa ta ce "Ummul wlh ina son Abbana, ina son shi sosai na fiki son shi nafi kowa
son shi a duniya" Ummul tai murmushi ta ce "Daman, ni mene haɗina da shi da zan so
shi?" Yaa Sheikh ya marairaice fuska cikin shagwaɓa da sauya murya ya ce.
"Ummul" ta ce "Daɗi naji hau an samu wacce ta fini son Aliyu a duniya" Halisa ta
ce.
"Ummul ni har kiss nake masa ke kina yi masa? Kuka har goya..." Yaa Sheikh ya yi
saurin matse hannunta wanda ya sa tai shiru. Ummul tuni tabar wajan.
Ya kalleta yana dafe kai ya ce "Why? Kin san wace ita?" Ta kasa yi masa magana sai
kissing bakinsa data shiga yi, ya rufe idanu yaga azumi kala-kala amma bai taɓa
ganin irin na yau ba, ya buɗe baki da sumbata ya riƙe fuskarta ya shiga tayata abin
da take sunyi nisa suka ji an fasa ihu akan su tare da jin sautin fashewar abu,
cikin tsoro da firgitar da Halisa tayi tai saurin rungome Abbanta tana mai da
numfashi, a wahale ya shiga buɗe ido kafin ya gama wanin waye akansu yaji anyi
kukan kura an cafki Halisa tare da bugata da jikin table....

Littafina na kuɗi ne
Ba zan ta surutu a media akan ana fitar mini da book ba, amma kuji tsoran Allah da
mai fitarwa, da mai karantawa free. Ku daina raina hakƙi komai ƙanƙantar shi.
₦500
08119237616
Na'ima sulaiman Shu'aibu
Nimcyluv sarauta.
#Sarautar marubuta
#team Yaa Sheikh
#team Halisa
#team Zahrah
#love
#destiny
#jealous
[1/3, 4:48 PM] Abk: Kamar zakin dake neman kalace tsayin shekaru haka Zahrah ta
ƙara damƙar Halisa cikin tashin hankali kiɗima da gigita kamar mahaukaciya sabon
kamu, kafin ta kamata Yaa Sheikh ya yi saurin miƙewa tare da riƙe hannun Zahrah
yana tsareta da idanu ya ce.
"Lafiya? Me tai miki?"
"Kan ubancan! Ni ka ke tambaya ko lafiya Aliyu? Ban sani ba amma idan na nakasata
sai ka gane manufata tayin hakan" ta faɗa tana cire ɗan kwalin kanta gabaɗaya
idanunta ya rufe ta mance batun cikin dake jikinta wanda ya gama bayyana kansa a
zahirance.
Ta ƙara kai wa Halisa damƙa Yaa Sheikh ya ƙara tarewa idanunta ya jirkice masifa da
wutar ɗaukan fansar cin amanar da Halisa tai mata sune kaɗai abin da ake hangowa
cikin Idanun nata.
"Wallahi sai na kasheta, na ga uban wanda ya tsaya mata da har ta nemi cin amanata,
yarinya ƙarama ta zama karuwarka?"
Halisa ta leƙo ta bayan Yaa Sheikh idanunta ya yi jaa sosai sbd bugewar da tayi
amma taƙi kuka sbd tsabar dauriya da ƙarfin zuciya! Cikin rawar murya ta ce.
"Ni ba karuwa ba ce, kuma tambayi Abbana kinji" tana faɗin haka ta koma bayan Yaa
Sheikh da sauri tana riƙe ƙugunsa sbd kukan kurar da Zahrah tayi ta ce.
"Ni ce ajalinki ko uwarki tayi kaɗan ta shiga sabgar mijina balle ke, daman talaka
bai iya neman zama ba, taimako ya zame mini masifa yanzu Aliyu ka rasa dawa zakai
iskanci sai da ƴar aikina? Ni zaka wulaƙanta a idanunta? Daman da yawan malamai duk
ƴan iska ne" Halisa ta ƙara leƙowa ta ce.
"Abbana ba ɗan iska bane, ke ce dai" Da ƙarfi Yaa Sheikh ya bugawa Halisa tsawa ya
ce.
"Haliyserh!"
Cikin sauri ta shiga nutsuwarta ta koma bayansa ta ce "Kayi haƙuri Modibbo" Zahrah
ta lailayo wani ashar ta ƙunduma gabaɗaya kanta ya ɗaure ta kasa fahimtar abin da
yake faruwa ko yake shirin faruwa, tunaninta ya tsaya zuciyarta na ɗagawa Allah ya
gani tana son mijinta akan Yaa Sheikh zata iya komai.
"Kai cuceni daka bawa wannan tsinanniyar yarinyar abin da nake fata da burin
samunsa daga gare ka, sai na zama ajalinta kuma sai na faɗawa duniya irin zaman da
ka ke da ƴar aikin ka, ka mayar da ita karuwar ka, ka fake da addini kana aikata
zini aban ƙasa" kamar da ga sama suka ji Ummul ta ce.
"Matar ƙwarai bata taɓa faɗar sirrin mijinta" kafin kowa ya yi magana Halisa ta
ƙara leƙowa ta bayan Yaa Sheikh ta ce.
"Shi ya sa ban faɗin darasin auren da mukai da Abba ba, har ya ce sunana kankana"
Yaa Sheikh ya dafe kansa abin da yake ta gudu kenan gashi ta kasa sarrafa bakin
nata.
"Kankana?" Zahrah ta faɗa a bayyane cikin ɗaure kai!
"Eh kankana Anti Abbana ya ce ina da zaƙi" a wannan karan Yaa Sheikh ya kasa jurewa
sbd tsananin kunyar Ummul dake binsu da idanu tayi mutuwar tsaye, yawun bakinta ya
ƙafe.
"Zan naka saki kuma zama a gidan mijina ya ƙare ki koma can wajan muguwar uwarki
wacce bata iya haihuwa ba, daman ko sisi ban taɓa aika mata mata ba"
Jikin Halisa ya yi sanyi idanunta ya cika da hawaye ta ce.
"Kada ki sake zagin Dadata" a hargitse Idanun Zahrah har rufewa yake sbd masifar
dake cinta ta ce.
"Naci uwar data haifeta bama ita ba, dan kaza-kazanta" Halisa ta fito daga bayan
Yaa Sheikh ta ce.
"Idan ki sake ni ma zan rama, ke ki ka ɗakkoni har Rugar Rome, bada son raina ba,
mene laifina da zaki dinga jifana akan abin da bani da laifi? Idan kishi ne ya saki
hakan, wannan ba kishi bane hauka ne, kuma duk kishinki baki kama ƙafata ba, ina
son mijina fiye da yadda ki ke son sa, ina son Abbana, ina son Modibbona kada ki
sake zagin wanda ya zame mini garkuwa akan idanuna"
Ummul ta girgiza da jin maganganun Halisa masu cike da hikima kuma a nutse Yaa
Sheikh tsaye ya yi ya kasa cewa komai, ban yi tunanin ranar zata zo nan kusa ba,
duk da ya kwana da sanin cewa dole Zahran zata san gasky soona or later.
Zahrah ta rasa a wanne tubali zata saka zancan na Halisa wanda da tunaninta ya kasa
fahimtar da ita komai. Cikin rashin fahimta ta ce. "Waye mijin naki? A gidan uban
ki kai auren? Ko maza ki ka fara bi shi ne ki ka biyo ta kan mijina? Ko dai takari
ki ka zama?"
"Ai ko giwa ta faɗi,ta fi ƙarfin Allah sarki, ko yanzu goma ta zube tafi biyar
albarka" Halisa ta juya kan Yaa Sheikh tare da riƙe ƙugunsa cikin ƙasa da murya
wacce shi kansa bai santa da ita ba ta ce.
"Abbana ka shaida mata ni matarka ce, ta daina cin zarafin biyayyar da Dada ta
bani, ka faɗa mata ba zaman haramci muke ba, ta daina lalata maka sunanka, _I love
You so much Sweetheart Abbana_"
Yaa Sheikh yaja numfashi ya kasa riƙe mmkin da take shayar da shi ya yi saurin riƙe
hannunta. Kafin ya yi magana Ummul ta fasa ƙara ta ce.
"Aliyu, Halisa!"
Ta faɗa cikin fargabar yadda taga Zahrah ta zari plate ɗin glasses wanda yake shaƙe
da fruits ta yo kan Halisa.
Yaa Sheikh ya yi saurin juyar da Halisa ta koma cikinsa ya rungometa sosai.
Tass! Sautin saukar Glasses ɗin akan Yaa Sheikh ya runtse idanunsa sbd sosai ya
shigesa jini ya fara zuba.
"Ka faɗa mini wace ita, ka faɗa mini matsayinta kada ka sake bakinka ya ambace ta
matsayin matar ka" Yaa Sheikh bai iya hayaniya ba, bai san ya ake ba, amma dole ya
nuna mata shi namiji ne tsayayye a gidansa..
Kansa na zubar da jini ya juya zuwa gare ta ya ce.
"Matata ce, halaliyata, abu mai daraja na bayar na sameta ki sassauta maganganun
naki akan ta" jiri ya kwashi Zahrah tayi baya luuu! Ummul tai saurin tare ta, domin
ta lura abin da abin da yake jikinta. A zafafe ta kai hannu ta ɗauke Ummul da
marin.
Kafin ta sauke hannunta taji saukar maruka a jere har sau uku, marin daya sanya
tayi zaman ƴan bori a ƙasa, ɗan cikinta ya motsa sbd faɗuwar da tayi. Idanunta ya
cika da hawaye ta nuna Ummul da hannu ta ce.
"Akan wannan ƴar aikin taka ka mareni Aliyu? Wannan matar wacce bata isa na haɗa
inuwa da ita ba?" Yaa Sheikh yanayinsa ya sauya ya ce.
"Mene? Ƴar aiki fa ki ka ce, to ita ɗin" Ummul tayi saurin rufe bakin Yaa Sheikh ta
ce "Aliyu! Wannan duk bai dace ba, kada kaga laifinta ko wacce mace zata iya aikata
haka idan har tana son mijinta, balle batun kishiya lokaci guda"
Zahrah ta fashe da kukan baƙin ciki ta ce.
"Don Allah kada kayi mini haka Aliyu, kada ka haɗani kishi da wacce nafi tsana a
rayuwa sama da komai, idan ka ƙi yarda wlh zan kasheta mahaukaciya ce ni akan
soyayyarka"
Halisa ita ma ta fashe da kuka ta riƙe Yaa Sheikh ta ce "Ina son ka ni ma Abbana,
idan na tuna Anti Zahrah matarka ce ina jin kamar na ɗauki wuƙa na cakawa kai na"
Kafin su yi magana Zahrah ta miƙe a sukwane ta nufi inda taga wuƙa kamar
zautacciyya ta nufi wajan Halisa ta ce.
"Na kashe ta, na kashe ka Aliyu, na kashe kai na gabaɗaya ma haɗu lahira ai mana
hisabi, nasan ni ce da riba" Halisa ta firgita ta fasa ihu ganin yadda Zahrah tai
kanta da wuƙa, kafin ta caka mata Yaa Sheikh ya saka hannu ya tare wuƙar ta sauka a
hannunsa jini ya fara zuba.
A ruɗe Ummul ta ce "Modibbona, Aliyu, Arɗona" ita kanta bata san ta faɗa ba, ta
kama hannun Aliyu wanda yake zubar da jini ta cire wuƙar da ƙyar ta ce.
"Kana kallo zata kashe mini kai, ba zan iya ba Aliyu wacce matar ƙaddara ce da bata
iya ɗaukan ƙaddara?" Sai a lokacin jikin Zahrah ya yi sanyi ganin yadda wuƙar tai
rami a hannun Yaa Sheikh. Halisa ta riƙe Yaa Sheikh cikin kuka ta ce.
"Abbana me ya sa zaka tare mini, akai na take faɗan nan, idan zata kashe ka akai
na, gwara ka rabu..." Ya saka hannu ya damƙi hannun Halisa idanunsa akan Ummul ya
ce.
"Ummul shirya ki fito, ke kuma taku ɗaya ki ka ƙara bare ki fita akan igiyoyinki"
Ummul ta juya ta shirya tare ɗakko jakarta. Har ya fita ya tsaya ya ce "kin ce ƙari
ya fito miki, amma baki duba yanayinki ba?" Ya fi ce a hanya ya ci karo da Umar-
khan, ganin yanayin ya sa Umar-khan kiran Dr a waya. Gabaɗaya suka shiga mota,kuka
sosai Halisa take kamar ranta zai fita, Ummul ta riƙe hannun Yaa Sheikh ta naɗa
masa wani gyalle amma har lokacin jini zuba yake..
A haukace Zahrah ta dinga jifa da komai na parlourn ta shiga fasa Glasses ɗin
ko'ina dake parlourn ta jiwa kanta rauni gabaɗaya ta zama abar tausayi.
"Ina son ka Aliyu, wallahi ina son ka" sai surutai ta ke. Ta ɗauki waya ta kira
Deen ta faɗa masa komai da sauri ya ce.
"Gani nan zuwa" cikin kuka ta ce "A'a kada kazo, ka bani hasken yadda za mu yi da
yarinyar" Deen ya ce "A kasheta kawai" ta ce "Kasheta kawai, kayi duk yadda kayi
tabar duniya" ta kashe wayar tana ƙara sautin kukanta.....
Cikin sauri Father yake tako steps ɗin benen zuwa downstairs "Maryam, Maryam" ya
shiga kiran sunan Mother wacce ta gama cire henna ɗin da akai mata, ta miƙe tana
kallon Maimoon ta ce "Maimoon je ki duba kayan aikin da aka kawo, ina son kammala
komai cikin daren nan kafin gobe idi" Maimoon ta ce "Tom" Maimoon ta nufi kitchen
wajan da ake aikin abincin sallah, mother ta nufi inda take jin Muryar Father.
Gabanta ya faɗi sosai ta ce "Engineer lafiya ka ke wannan kiran?" Ya nunata da
hannu ya ce.
"Munafuka, magulmaciyya, makira shaiɗaniyya" shi ne kalaman da Father yake jifan
mother dasu, a sanyaye ta ce.
"Me nayi maka ka ke jifana da wannan maganganun Engineer? Lokaci na samun lada ka
mayar matsayin na data husuma?" Ya tare ta da faɗin "Dole ki ƙasƙantar da kan ki,
saboda abin da ki ka aikata" ta ce "me na aikata har haka, a wannan watan na samun
lada da rahamar Ubangiji me nayi maka Engineer?" Ya jinjina kai yana ƙwafa ya ce.
"Da haɗin bakin ki Aliyu ya yi aure? Auren ma ƴar cikinsa mai aikin Zahrah?" Mother
tai murmushi ta ce "Oh! Akan haka ka ke ɗaga murya? to! Bani naiwa Sheikh Aure ba,
duk da ina niyya faɗuwa ce ta zo daidai da zama" ya ce
"Ƙarya ki ke, daman kinyi iƙirarin mata biyu zai aura, kin yi abin da ki kai niyya
kuma ki ke so, ni ma zan yi abin da naga dama" Mother ta ranta ya fara ɓaci bata
son ta ɗaga murya sbd su Maimoon ta ce.
"Zaka iya, amma ka sani bani naiwa Aliyu aure ba, auren shi da Halisa tsarin
Ubangiji ne" Father ya haura sama ba tare da ya ce komai ba.
Jikinta a sanyaye sbd musayar yawun da tayi da mijinta cikin azumi. Ta dawo Main
parlour da sauri Auta Fattoumah ta ce. "Mother ke da waye?" Mother ta ce "Ban son
surutu Fattoumah, kije ki kwanta zaki sallar idi gobe" kafin Fattoumah tai magana
Father ya sakko tare da cillowa Mother paper ta ce.
"A cikin daren nan, ki tattara kayan ki, ki bar mini gida, na sake ki saki ɗaya ni
da ke sai a hanya kada ki tafi da yara ko ɗaya" saki cikin watan Ramadana,
Innalillaha wa'inna ilahir raji'un!
Ta miƙe idanunta cike da hawaye ta ce "Me kace Engineer kamar saki naji?" Ya juya
hannunsa riƙe da key ya ce "Na sake ki Maryam, na sake ki Maryam ki Bama ɗaya ba na
sake ki saki biyu!...

*Am sorry ina ta samu matsala ban kula ba, sai yanzu dana dawo baya ina karantawa,
nace aikin Hajji maimakon Oummara! Please bear with me ba aikin hajji bane, muna
watan Ramadan ne omara ce. Ita kuma Omara ko wanne lokaci, ko wanne wata ana iya
yinta.*
[1/3, 4:48 PM] Abk: Kafin Father ya ƙarasa faɗin sauran mugwayen maganganun na shi
akan Mother, cikin Jadda ta yi tsalle ta dire ta ce.
"Kana ƙarasa sakin sai dai ka nemi wata uwar bani Jadda ba, ka tabbatar mini kai ba
ɗan arziƙi bane wanda ya san addini, ashe baka da imani da taƙawa Ali?
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Duk duniya suna maka kallo mai hankali ashe
mahaukaci na haifa bani da lafiya, sai da da jama'a suka dinga samu na, suna cewa
nayi hankali da kai, sam banji ba shi ne yanzu zaka nuna mini kai mahaukaci riƙaƙƙe
ne kuma?" Father ya kalli Mother ya ce.
"Jadda baki san me tayi mini ba, ta nuna ban isa da ita ba ta kunya tani a idanun
abokina, tai wa Aliyu aure ba tare da sani ko yarda ta ba a matsayina na uban shi,
ta kuma san danginsu Zahrah ba ai musu kishiya"
Cikin ihun murna Jadda ta ce "Ka ce Malam ya yi aure? To Ubangiji ya yi miki
Albarka Maryam, ita kuma zuza take ko zura ba zan iya masifa ba, Allah ya yi gutsi
gutsi da ita da dangin nata,
Daman ai cutar Malam sukai na rantse sai da suka buga tabbatiyada kafin su yi
maganar aurenta da Malam, mace babu fasali balle tsari har naci ƴan matanci na auri
ubanka ban taɓa ganin mai zubin halitta irin nata ba, nono shimfiɗe kamar kamar
dindimari ta hau kwalta, ɗuwawun nan tamkar wainar fulawa ta kasko, huhuhu! Azaba
Allah dai ya isan Gadanga an haɗi shi da irin bokan irin masifa wannan ba lallai ta
san hakƙin aure ba, dole ne na kira Daurawa ko isa Fantami su yi wa ƴar banza
wa'azi,
Kai kuma ba zan kulaka ba, ba san masifa da kai ba, jama'a su yi ta kwashe mini
Albarka sai na fara bincikar ƙwaƙwalwarka, fita kuma babu inda Maryam zata daga nan
har Malam ya sauka a Larjeriyya minti nawa ne zuwan"
Father ya ce "Jadda yarinyar nan Zahrah kaf Familynsu babu mai iliminta, tayi
primary, secondary, N.c.e, degree, H.n.d, master duk wani kwali da ɗan boko yake
mafarkin samu ta samu, ba gata akaiwa Aliyu da aka haɗa shi aure da wacce zata kula
da dukiyar shi ba? Shi za a wulaƙanta ta, a aura mini ƴar aikinta, to wlh bada
yawuna ba, ni nake da ikon zaɓarwa Aliyu macen da tayi mini,
Kuma ita uwar ta shi data ɗaure masa gindi ina ita ɗaya ce a gidan aurenta ko nayi
mata kishiya ne?"
Jadda ta fashe da kuka sosai tana kama bakin zani ta ce "Yanzu daga magana akan
la'ananniyar yarinya wacce shaiɗan ya yi wa fitsari aka shi ne ka ke zagina Ali? Ni
kake tsinewa ka ke cewa na fitar maka daga gidana ai ba kai kaɗai na haifa ba? Ni
ce uwar banza ko ba shakka, sbd Allah ina ruwana da shiga masifar yara daga cewa
Malam bai kyauta ba shi ne ka zageni ka zagin uwa da uban da suka kawo ni duniya"
ta face majina tayi mitsi mitsi da idanu ta ce. "Maimunatu masa kira mimi Haruna,
shi da ɗan uwan shi Ubangiji ya ƙaddara na haifi wasu ba shi kaɗai bane"
Father ya ƙarasu wajan Jadda ya ce "Don Allah Jadda kiyi haƙuri wlh ba zagi nayi
ba, fushina na sauke akan muna.....,"
"Idan ka sake cewa Maryam munafuka zaka tabbatar ƴar iska ce ni, fita ka bani wake
kada na sake ganin fuskarka a gabana" Mother dai na zaune a kujera kanta a ƙasa ta
harɗe hannu a ƙirji sai girgiza ƙafa take, ko ba a faɗa ba kasan cewa ranta ya yi
mugun ɓaci.
Maimoon ta bawa Jadda waya jin Uncle Haroon ya ɗaga ta cikin wayar ya ce "Maimunatu
ƴar Engineer da Barrister ya akai ne ƙawar?" Jadda ta ce "Masifa da bala'i,to kakar
Maimunatu ce" ya yi saurin cewa "Barka ansha ruwa lafiya Jadda?" Ta fashe da kuka
sosai hankalin Uncle Haroon ya ta shi ta ce "Kana can gidan matanka yaƙi ya ɓarke a
gidan Ali, kafin ya kashe ni maza maza na ganka a gidan kai da Bashir, amma dai Ali
yaci mini mutunci ya zageni tas zagin da ba a taɓa yi mini ba" ta kashe wayar murya
can ƙasa ƙasa ta ce. "Alsulhu khair! Gashi nayi magana a nutse ba faɗa ba ihu, ke
kuma Maryam ki barni da shi zai gane ni ba tsohuwar banza ba ce"
Father ya kasa cewa komai, gabaɗaya kansa ya kulle kunyar Alhaji Farouk ta kama
cinye shi. Maimoon da Zeefa sai kuka suke, Auta Fattoumah tai shiru tare da kafe
Father da idanu tana jin zafin shi a ranta fiye da ko wanne lokaci.
A kusan tare manyan motoci guda uku sukai parking a harabar gidan, Uncle Haroon
daga Zaria road, Uncle Bashir da ga unguwa uku, sai Abba Hakimi daga Dawaki road.
Uncle Bashir ya fara fitowa cikin wata dakakkiyar shadda sky blue, sai Uncle Haroon
ya fito cikin farar shadda shi ma, gabaɗaya suka tsaya domin gaisawa da Abba
Hakimi, Saif-wazir ya buɗewa Abba Hakimi mota, ya fito cikin kyakkyawar tufar shi
shadda ruwan madara ɗinkin jamper da babbar riga, ya ɗora hirami akan shi kamar
yadda Yaa Sheikh.
Suka rusuna bakiɗaya tare da haɗa baki wajan faɗin. "Barka da dare Abba Hakimi, Ya
ibada?" Ya saki murmushi irin nasu na manya ya ce.
"Allahamdulillah, baƙo na shirin tafiya ya barmu da kewa" duk sukai murmushi Uncle
Haroon ya ce "To Allah ya bamu lada ya wanke dattin Laifuka" ya ce.
"Amin" Abba Hakimi ya kalli Saif-wazir ya ce.
"Ka jira nan"
Suka nufi cikin gidan, a main parlour suka samu Jadda zaune, Mother ma na zaune har
yanzu bata motsa ko gyara zamanta ba, sai da taji muryar Abba Hakimi ta ɗago kai
cikin rauni suna haɗa ido ya girgiza mata kai.
Suka zauna bayan sun gaida Jadda ta amsa ba yabo ba fallasa.
Mother ta gaida Abba Hakimi dasu Uncle Bashir.
"Fatan lafiya ne, wannan kiran gaggawa dare har ya fara" Jadda ta fara matse ƙwalla
ta ce.
"Lafiyar kenan, ku kira ɗan uwanka kuji dalilin sakin Maryam har saki biyu" Suka
saki salati Abba Hakimi ya yi murmushi kawai he's speechless.
"Wanne irin saki ana zaune lafiya,saki kuma cikin azumi?" Jadda ta ce "Idan mutum
ya fara shan wiwi da tiramol sai abin da aka gani" Uncle Bashir ya miƙe zuwa
upstairs ya samu Father na waya daka gani mai muhimmaci ce, yadda yake ta begen.
"Ka fito muna jiranka" ya miƙe tsaye tare dabin bayan Yayan na shi.
"Wani irin shirme ne haka Aliyu? mai Barrister ta aikata a gareka har haka?" Ka
tsaye Father ya ce.
"Ta yi wa Sheikh aure ba tare dana sani ba, kuma ta aura masa yarinya mafi ƙasƙanci
a idanun Zahrah, daɗin da ɗawa ba aiwa Familynsu Zahrah kishiya na shaida mata
hakan, shi ya sa na yanke hukuncin laifukan da tayi mini, kafin Aliyun ya sauka
ƙasar"
Uncle Haroon ya ce.
"Mu kuma sai ka ɗaure mu, tunda mune muka bada shawarar kada ka sani ɗin, mun san
da auren tun kafin Aliyu yabar ƙasa zuwa wajan aikin shi, auren Halisa aka fara
ɗaurawa kafin na ƴar gaban goshin taka".
"Ni dai bada yawuna ba, Aliyuna ɗa na ne" Uncle Bashir ya ce "Sannu mai ɗa, ka faɗa
mana wanda bai da zuri'a a nan balle kayi mana gori, ko ɗan kana ne to yanzu ƙarfin
ikonmu ya ƙwace Malam daga wajanka"
Jadda ta ce "Gwara ya zage ku kamar yadda ya yi mini, abin duka ya ɗauka zai dake
ni fa? Uhm uhm Allah kada ka nuna mini masifar dana gani ɗazo"
Uncle Haroon ya ce "kaga let by gone be by gone, mu duka ba sa'aninka sa'insarka
bane, ba zamu ce komai daga nan har Sheikh ya sauka ƙasar nan, kuma Barrister tana
gidan nan ina tabbatar maka za kai ladamar sakin da kayi mata" sai a lokacin Abba
Hakimi ya ce.
"A'a Inn shaa Allah da Maryamu zan tafi, ya riƙe yaran shi na tafi da ƴar ɗan-
uwana" ya juya kan Mother ya ce.
"Ta shi ki shirya" Uncle Haroon ya ce "Baza ai haka ba Abba Hakimi, ko sbd su
Fattoumah" Abba Hakimi ya miƙe ya jima da sanin Father ba ɗan ƙwarai bane son rai
dana zuciyar shi kawai yake bi.
Mother ta kwantar da Auta Fattoumah saman kujera, ta nufi bedroom ta ɗauki mayafi
waya da hand bag sai kayanta dake torelly bag.
Maimoon ta dinga kuka tana rungome Mother.
Mother ta kasa cewa komai idanunta ya yi jaa ta nufi Main parlour.
Abba Hakimi ya kama hannun Mother suka fice daga gidan zuciyoyin ko wannensu babu
daɗi.
Da ƙyar aka samu jinin dake zuba a hannun Yaa Sheikh ya tsaya, akai masa Allura
baya son magani shi kuma sai dole, Zuciyar Halisa ta ɗauki zafi haka kurum taji har
Abban nata zafin shi take ji, don mai zai bari wata banza tana faɗa masa magana
kuma ta gaji ta ɓoye batun auren su.
Ta shige ɗaki ta kwanta sai kuka take, cikin dare ta kasa barci ta dinga juyi ta
saba da jikin Yaa Sheikh. Ta dubi lokaci taga ƙarfe 2:30 na dare, ta miƙe a hankali
jikinta sanye da farar night gown kanta ba kitso, ta saka slippers har ta fita sai
ta dawo ta ɗauki perpumes ta fesa, ta shiga fitowa a hankali.
Ta samu Ummul zaune saman kujera a main parlour hannunta riƙe da casbawa. Suka
kalli juna ta ce "Lafiya ki ka fito a daren nan?" Ta ce.
"Wajan Abbana zani" maganar ta girmi Ummul ta ce "Ina jin ya yi barci fa?" Halisa
ta kalli Ummul ta ce "Bana jin Abbana ya yi barci tun da ni ma na kasa" kunya ta
kama Ummul ita kam oganniyyar ko a jikinta.
"Koma to, tunda baki san yadda zaki riƙe Abban naki ba" Halisa bata gane ba, bada
son ranta ba ta juya Ummul ta bita da idanu, dole ta gyara mata zama shi namiji a
rayuwa bashi da tabbas idan kullum zaka sakar masa jikinka haka yake buƙata, amma
dole ta koyi yadda zata dinga juya Yaa Sheikh duk da bata da haufi a kan shi.
Babu jimawa da tafiyar Halisa Yaa Sheikh ya fito cikin ash ɗin Jallabiya mai
ƙaramin hannu a wannan karan bai ɗora hirami ba, sumar kansa mai kala biyu ta
bayyana.
Mamaki ya kama Ummul ta ɗauka tuni ya yi barci ya dawo kusa da ita ya zauna.
"Bakai barci ba Arɗo?"
Ya jinjina kai ya ce "Bana ji Ummul" ta ƙara gasgata zancan Halisa ashe da gaske
duk ba za su iya barci ba juna ba?
Yaushe sukai wannan mugun sabon har haka? Ta share shi tana kallo yana duba
ɓangaren Halisa amma baya da ikon zuwa sbd zaman Ummul ɗin,ai kam kamar daga sama
su kaga ta sake fitowa.
Da sauri ta ƙarasu ta ce.
"Ummul daman nace ba zai iya barci ba" ta faɗi hakan tana nufar Yaa Sheikh ya yi
saurin rufe idanunsa sbd nauyin Ummul yake ji. Halisa ta zauna saman cinyar shi
tare da kwanciya jikinsa ta rungome shi ta ce.
"I miss You Modibbo"
Ummul ta miƙe domin tuni salatin ya ƙwace mata ta ce.
"Allah ya kyauta" tana barin wajan Yaa Sheikh ya sunkuceta yana mannata da ƙirjinsa
duk da ciwon hannunsa ya ciji fatar kunnenta kaɗan ya ce.
"Kankanata, yau ban sha ruwa ba" ta lumshe idanunsa tana jin soyayyar shi na ƙara
haɓawa tare da tunɓasa a zuciyarta tana yaɗo ta ko wacce ƙofa dake zuciyarta..
Washegari tun Subhi ya farka ita kam kasa motsi tayi har yanzu ta kasa sabawa da
yanayin Abban nata kullum da salon da yake zuwar mata. Yau take sallah, an sallame
azumi mutane Al'ummar Annabi kowa yana haramar tafiya masallaci, ranar da ko yake
jiran zuwanta farin ciki a

Please Login or Register in order to submit comment