You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jikinta shi ya sa bata fiye damuwa da son zuwa
wajan mahaifiyar ta ta ba. Ta share hawaye ta ce
"I knw i made a mistake, but isn't my fault domin Deen ya amshi cikin da bana shi
ba da hannu bibbiyu, burinsa shi ma ya ɗorawa Yaa Sheikh laifin cikin, mun su dayin
auren Aliyu ya kasance dani yadda zan iya cewa bakwaini na haifa, hakan bai kasance
ba nasan na cutar da Yaa Sheikh da maganin dana bashi daga baya kuma na fahimci
tabbas ya je wajan Halisa be tunda matar shi ce, Sai yanzu na gane dalilin da ya
sanya Aliyu baya raɓar inda nake. Ci,sha, ya bani baya takura ni"
Tunda ake wannan abun banda kuka babu abin da Mother take ƙirjinta har ɗagawa yake,
baƙin cikin mugun tabon da Father ya barwa ya ranta shi ke damunta.
Abba Hakimi ya juya kan Father ya ce. "Engineer ka ɓata wayonka, ashe zaka iya yiwa
ɗan daka haifa sharrin da zan gina baƙin ciki a zuciyarsa, ya kuma ɓata kyakkyawan
tulabin halayyar shi da yake ciki?,
Nayi mamaki na kuma kasa fahimtar da gaske abubuwan da kake ji wani waje zai iya
faruwa a inda ka ke" Father ya goge zufa ya ce.
"Na amshi laifina, amma bani ka ɗai bane a family wanda yake son ganin bayan Yaa
Sheikh, sai ki faɗa musu sunan mutumin daya koma Deen" Yaa Sheikh dake tsaye har
yanzu sunan Allah kawai yake ambata a cikin ranshi, idanunsa sukai jajir jijiyoyin
kansa sun fito, sai huci yake fitarwa.
Zahrah tai shiru ta kasa cewa komai Father ya ce.
"Bani ki ka tunawa asiri ba?" Kai tsaye ta ce
"Duk abin da ya samu shamuwa watan bakwai me ya ja mata" Ya ce.
"Ok fine sai ki sanar da su Saif-wazir shi ne Deen stop lying to them" Abba Hakimi
ya dafe kai ya ce.
"Saif-wazir? How can that be possible? Meye nashi na son cin mutumcin Malam? Me ya
yi masa?" Daga bakin ƙofa Saif-wazir daya shigo yanzu ya ce.
"Saboda ka fifita ɗan wani fiye da ɗan daka haifa a cikinka Abba" Abba Hakimi ya
miƙe tsaye bai tsaya jiran komai ya saka hannu ya ɗauke Saif-wazir da mari ya ƙara
ɗauke shi da mari, ya jera masa guda biyar a jere da sauri Mai martaba ya riƙe
hannun Abba Hakimi ya ce
"Idan rai ya ɓaci, nutsuwa ke nemu shi, marin ba mafita bane" Saif-wazir ya kalli
Abba ya ce.
"Like this, irin haka sune suka sanya mini tsanar Yaa Lee, kaƙi bawa yaran daka
haifa space a zuciyarka, har dukiyar dana mallaka sai dana rasata dalilin Yaa Lee,
bani da masaniyya akan Zahrah zata iya auren Yaa Lee wata rana, amma nasan Babanta
Best friend ɗin Father ne, na nemi connection da ita na tsara plan ɗin yadda zata
jawo hankalin shi harta su kasance abu guda na ɓata masa suna, sai ya zamana bana
nasara Yaa Sheikh ko sha'awar dawowa Nigeria ba ya yi, a haka har Allah ya kawo
ranar da aka haɗasu aure kasa barci nayi don farin ciki burina zai cika, Abba ka
mareni kasa an saka ni acinin mari, tun kafin nai wayo har boarding school nai duk
dalilin Yaa Lee, mene laifina dan nayi kishi da shi,bayan nasan ko mutuwa kayi
bashi da gadon ka tunda ba ɗan ka bane"
Ya ƙare maganar yana hawaye. Tunda Abba Hakimi yake ba'a taɓa masa rai irin na yau
ba, ya kama hannun Saif-wazir ya ce
"Aliyu shi ne komai nawa, tunda ya so ƴar dana fi so fiye da komai, ya kareta daga
mugwaye azzalumai, ya kula da ita hai ta haifi Halisa, akan yarinya ƙarama ya zaɓi
aci gaba dayi masa kallon gwauro, tuzuru, wasu na jifan shi da maganganun rashin
ɗa'a akan me ba zan fifita shi fiye daku ba? Me ya Umar-khan bai complain ba? Me ya
sa Ishaq-Hakim bai complain ba sai kai? ba zan aibata ka ba, amma kaje na yafe ka,
ka nemi wani uban!"
"Kada ayi haka Abba, don Allah a saisaita abi komai a sannu" Abba Hakimi ya ce.
"Sarauta ta girmi tsofa, amma ba zan iya yin haka ba, dole Saif-wazir yabar mini
gida" Umma A'isha ta ce
"Ya zama dole, tunda ya zaɓi hakan" Saif-wazir ya kalli Umma A'isha ya juya ya
kalli Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh dake fuskantar ƙofa, sai kawai ya yi murmushi
yabar gidan bakiɗaya.
Mother ta goge idanunta tas ta ce "Allhamdulillah! Hakan ya yi mini daɗi ko ba
komai nasan halin uban yarana, banyi mamakin yadda Mamana Fattoumah bata son ka,
akwai abin data gani tare da kai, Aliyu ina son ka ƙarasa cike mini sakin da kayi
wallahi na gama zama da kai"
Father ya girgiza ya ce
"Abin da ba zan taɓa iyawa ba kenan Maryam, ko sakin da nayi miki ban san nayi ba,
wlh ina son ki ba zan iya rabuwa dake ba _*IDAN BA KE*_ am nothing absolutely
nothing"
Uncle Haroon ya sauke masa wasu tagwayen maruka wanda ya sa Father saurin runtse
idanu yana dafe fuska.
"Shasha ban taɓa jin kunya a rayuwa irin ta yau ba, ka kunya tamu gaban mutanan da
suke da ƙima da martaba a idanunmu, tashi kabar wajan nan" Mother ta ce
"Yaje ina? idan yabar gidan nan ka tabbata ya ƙarasa ciki mini raguwar saki ɗayan"
Cikin tashin hankali ƙarara Father ya ce "Wlh ba zan iya sakin ki ba, duk abin da
za kiyi" yana faɗin hakan ya miƙe jiki ba kuzari, sai da yaje bakin ƙofa Mother ta
ce
"Mu haɗu a Court"
Mai martaba idanunsa akan Dada wani irin sabon son ta na ƙara taso masa ya nisa ya
ce.
"Allah ya kyauta, Ubangiji kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu. Ya cire masa ƙyashi da
hassada" duk suka amsa da abin. Ummul ta duba agogo tare da miƙewa ta ce. "Zan tafi
Allah ya ki ya ye" Sai a lokacin Umma A'isha ta ce.
"Kiyi haƙuri da abin da aka aikatawa Yaron ki Aliyu, ki yafe mana" Ummul tai
murmushi ta ce "Barrister Maryam za ki bawa haƙuri ita ce uwar Malam, kawai zan
nemi Alfarmar ya bini zuwa wajan ka kanin shi" Umma A'isha zatai mgn Abba Hakimi ya
ɗaga mata hannu ya ce
"Allah ya tsare"
Ummul tabi bayan Yaa Sheikh suka fita, ita ke driving shi yana gefen mai zaman
banza, ba tare da sanin su Abba Hakimi sun biyo bayansu ba. A haka suka shiga cikin
asibitin lokaci guda motocinsu sukai parking, har kawo lokacin ba a gane halin da
Yaa Sheikh ke ciki, bada kowa yake haɗa idanu ba kuma yaƙi cewa komai akan
al'amarin. Kai tsaye office ɗin Dr ya nufa yana gaba Ummul na bayan shi, Dr ya miƙe
yana miƙawa Yaa Sheikh cike da martabawa suka zauna Ummul ce ta samu ƙarfin gwiwar
cewa
"Meke faruwa Dr?"
Dr ya zare Glasses ɗin idanunsa ya ce.
"Ta farka, ba wani ciwo dake damunta sai babban ciwon daya gama lalata
kwakwalwarta" da sauri Ummul ta ce.
"Meke faruwa? Kayi magana kai tsaye" Ya zaro File ɗin Halisa da wani X-ray ya
miƙawa Yaa Sheikh
"Nasan zaka fahimta"
Zuciyar Yaa Sheikh ta buga file ɗin ya nemi kwace masa, Ummul tayi saurin riƙe
hannun shi tana faɗin "Be careful Arɗo" a fili cikin muryar fargaba ya ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Losing memory?"
Dr ya ce "Haka binciken ya nuna" Ummul wacce ta lura da rikicewar Yaa Sheikh ta
matsa kusa da shi tana bashi side hug ta ce "Memory? Like how" Dr ya danna system
ɗin gabansa tare da juyawa Ummul ya ce
"Memory loss is unusual forgetfulness. You may not be able to remember new events,
recall one or more memories of the past, or both. The memory loss may be for a
short time and then resolve (transient). Or, it may not go away, and, depending on
the cause, it can get worse over time" Ya ƙara danno waje tare da nuna mata wani
waje, kafin ya ce.
"Ta samu Short-term memory loss. Short-term memory loss is when you forget things
that have happened recently, such as an event or something you did, saw, or heard.
It can be caused by a number of factors, including a nutritional deficiency, sleep
deprivation, depression, side effects of some medications, or dementia"
Ummul ta ce
"What causes short time memory loss? Dr" ta faɗa she's still holding onto him,
ganin har yanzu Yaa Sheikh ɗin ya kasa cewa komai, Dr ya ce.
"Possible causes of reversible memory loss include:
Medications. Certain medications or a combination of medications can cause
forgetfulness or confusion.
Minor head trauma or injury.
Emotional disorders.
Alcoholism.
Vitamin B-12 deficiency.
Hypothyroidism.
Brain diseases.
Sleep Apnea. Ita ta samu dalilin Trauma"
Yanayin Ummul duk ya sauya ta ce
"Zamu iya ganinta?" Ya ce "Sure" Yaa Sheikh ya juya tare da zare jikinsa daga na
Ummul ya fita.
Dr ya bi bayan shi, haka Ummul ma.
A ƙofar Room ɗin suka samu Dada da Mai martaba sai Mother duk suna tsaye, Yaa
Sheikh bai ce komai ba ya buɗe ƙofar Room ya shiga.
Tana zaune ta jingina jikin gadon idanunta rufe, da sauri ta buɗe idanunta jin
motsi kamar mai tsoron ganin wanda ya shigo haka ta dinga ɗaga lashes ɗin idanunta
slowly slowly.
Idanunta ya sauka akan Yaa Sheikh ta ƙura masa idanu, shi ma ita ɗin yake kallo ita
kuma kallon sabon mutum take masa a sabuwar duniyar data tsinci kanta.
Ummul ta shigo ita ma
"Sannu Daughter"
Tana sauke maganarta Halisa ta ce
"Sannu Daughter"
Ummul ta kalli Dr ta kalli Yaa Sheikh wanda yake ta kallon Matar Malam.
"Ya jikin naki?" Cewar Ummul da sauri ita ma Halisa ta ce
"Ya jikin naki?" Kan Ummul ya ɗaure sosai ta juya zuwa waje ba jimawa ta dawo ita
da Dada ta ce "Daughter kin gane wannan?" Ta ƙara faɗar the same words ɗin da Ummul
ta ce.
Tuni idanun Dada ya cika da hawaye ta ce
"Danejo baki gane Dadarki ba?" With Emotional kamar yadda Dada tai magana Halisa ta
ce "Danejo baki gane Dadarki ba?" Ummul ta dafe kai ta ce
"What are the symptoms of short-term memory loss?" A take ya ce
"asking the same questions repeatedly.
forgetting where you just put something.
forgetting recent events.
forgetting something you saw or read recently"
Mai martaba ya ce
"Ya Salam, ƙaddara data samu Princess kenan?" Dada ta fashe da kuka tana faɗin.
"Your highness Halisa ta mantani" Ya riƙe ta yana bubbuga bayanta trying to calm
her down.
Yaa Sheikh ya sauke hannayensa gently ya ƙarasa inda take gabaɗaya suka zuba masa
idanu, hatta Halisa kallon shi take a hankali ya miƙa hannu zai riƙe nata tai wani
tsalle tare juyawa ta dire daga kan gadon tana fasa wata gigitacciyar ƙara....
Paid book
Nrml grp 500
Special 1k
08119237616
[1/9, 9:18 PM] Abk: *_IDAN BA KE_*
BOOK2 PAID BOOK
₦500 Via this number 08119237616

‫ِإَّن الّلَه َمَع الَّصاِبِريَن‬

Ilahirin jikinta rawa yake ganin Yaa Sheikh take kamar sabon halitta a cikin
idanunta, ta koma jikin bango ta maƙale tana mai da numfashi ƙirjinta na ɗagawa
numfashinta na sama, ta rufe idanunta ruf bata san ko ganin inda yake. Yaa Sheikh
ya ware jajayen idanunsa wanda suka fara janyewa ya miƙe a hankali tare da nufar ta
tun kafin ya ƙarasa ta buga tsalle ta koma bayan Ummul ta riƙe Ummul sosai tana
ɓoye fuskarta a bayanta. Dr ya ce "Ka rabu da ita" sai a lokacin Abba Hakimi ya ce
"Mijinta ne ai" murmushi Dr ya yi ya ce "Matar da bata san wace ita ba, ta ya zata
fahimci cewa mijinta ne?" Abba Hakimi ya ce "Hakan na nufin ba zata amince da shi
ba?" Dr ya kalli Halisa tare da juyawa ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Ita ai kallon
abin tsoro taka masa, sakamakon shi ne namiji na farko data fara gani bayan
farkawar ta" Ummul ta ce "Akwai matsala idan haka ne, amma mene mafita?" Dr ya ce
"Idan har zai rabe ta anta tashin hankali da ita kenan, ita a yadda take ji ko zai
shekara bai kulata ba she doesn't care, a ko wanne lokaci zata iya recovering"
Ummul ta jinjina kai alamar gamsuwa ba wanda take jin tausayi irin Yaa Sheikh tasan
ba zai jure wannan sabon al'amarin ba.
"Yanzu ya ake ciki"?
Cewar Mother Dr ya ƙara cewa "Sallama zamu bata, a kula da hannunta wanda ya karye,
kada a tsauwala tunaninta wajan tuna wace ita, ku fara koya mata dukkan abin da
kuka san zai zama mai amfani a gare ta" Ya yi ɗan rubuce-rubuce, kana ya miƙawa Yaa
Sheikh, ya sanya hannu ya amsa yana duba abun, some of medicine ne wanda zatai
using da su..
"Thank you Dr"
Yaa Sheikh ya furta cikin murya mafi sanyi rauninsa ya bayyana sosai akan fuskar
shi, da muryar shi, hatta wanda baya fahimtar raunin na Yaa Sheikh yau ya fahimta
kuma ya gane, sun ƙara tabbatarwa Halisa Danejo Rome ita ce duniyar Yaa Sheikh ita
ce kuma raunin shi.
Abba Hakimi ya juya ya fita zuwa Room ɗin El-bashir, Mai martaba ya kama hannun
Dada suka fita, haka mother.
Room ɗin ya rage daga Ummul sai Yaa Sheikh da kuma Halisa dake maƙale a bayan Ummul
ɗin. "Fito daga bayana, tunda yau Abban naki ki ke gudu" ta saka hannu ta zaro ta
daga bayanta tare da dawo da ita gaba.
Ummul ta tsareta da idanu ta ce.
"Ya sunanki?"
Halisa ta tsare Ummul da idanu ita ma ta ce
"Ya sunanki?"
Ummul ta dafe kai ta ce "yau naga abin da ya fi zare tsayi ni Ummul-khairy" ita dai
Halisa kallon Ummul kawai take, bata san mene so ko shaƙuwa amma taji hankalinta ya
kwanta da Ummul.
Ummul ta juya wajan Yaa Sheikh da yake tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirji tare da
zuba musu ido, ganin idanunsa akan Halisa ya sa Ummul faɗin "Bari na je wajan El-
bashir,sai na dawo mu tafi" bai ce komai ba sai lumshe idanunsa da ya yi
Ta kama hannun Halisa zuwa bakin gadon tare da zaunar da ita ta ce
"Yanzu zan dawo,zauna nan" tai shiru tana marairaice fuska zatai kuka ta ce
"Yanzu zan dawo, idan ki kai kuka to zan barki" tayi shiru Ummul ta ce
"Ki ce to" a sanyaye ta ce
"To!" Ta nufi hanyar fita har ta je bakin ƙofa ta juya ta kalli Yaa Sheikh sai kuma
ta fita tana girgiza kai. Yaa Sheikh ya sauke ajjiyar zuciya wacce ta tafi da
nauyin zuciyarsa, gently ya nufi hanyar fita daga room ɗin, yana zuwa ya ja ƙofar
tare da rufewa ya murɗa mata key.
Ya jingina da jikin ƙofar yana jifanfa da wani irin hargitsatsan kallo, wani irin
sabon shauƙinta na fisgar shi, burinsa ya haɗa gangar jikinsa da nata ko zai samu
daidaito a zuciyarsa,
Kan ta a ƙasa tana kallon fararen yatsun ƙafarta har bata san ya ƙarasu wajan ba,
sai ji tayi a saka hannu tare da ɗaga ta cak zuwa tsaye.
Wani irin zaro ido tayi ƙirjinta ya buga tsoro ƙarara ya bayyana akan fuskar
yarinyar ta,
bata san me zata ce ba domin sai an faɗi magana take maimaitawa ta shiga girgiza
masa kai tana yarfe hannunta, a hankali ya ɗora hannayensa saman shoulders ɗin ta,
ya kalli fuskarta, baki ta buɗe zata saka ihu ya ɗora yatsar shi a bakin ya ce
"Shiiii" ta maƙale kafaɗa ta zare kafaɗarta zata gudu ya yi saurin kamota tare da
haɗata da jikinsa, bayanta ne a jikinsa ita kuma tana kallon direction ɗin gadon,
hannayensa duka biyun zagaye da cikinta ya rungometa so tight fuskar shi a wuyanta
a hankali yake manna mata sajan fuskarsa mai laushi tare da goga mata tsinin
hancinsa a fatar wuyanta.
Tsigar jikinta ta shiga tashi, jikinta ya ɗauki wani abu ya fara yawo a jikinta,
haka nan taji abin da yake mata har tsakiyar ranta kuma tana buƙatar shi, ta rufe
idanunta hawaye tuni ya gama wanke mata fuska har tsoran kallon fuskar shi take sbd
yadda yake mata muni acikin idanunta.
"Why?" Ya ce a hankali muryarsa bata fita sosai komai ya dai na masa daɗi. Halisa
kokawar ƙwace kanta take amma ya yi mata rungumar da ba zata iya hakan ba, ya
juyata suka fuskanci juna idanunsa na yawo a kanta ya kama hannunta tare da ɗorawa
daidai ƙahon zuciyar shi ya ce
"Me ya sa matar malam? Ni ne Abbanki, Modibbonki, Yaa Sheikh na ki, ki daina kafin
zuciyata ta buga" taƙi kallon shi tai kicin-kicin da ranta. Ya ƙara manna hannun a
ƙirjin shi yana tallafo fuskarta ya ce
"Zaki bi ni ko? Nasan kina son Abbanki" kamar wacce aka raɗawa a kunne ta yi saurin
faɗin.
"Na tsaneka!"
Kalmar ta daki zuciyar shi, har sai daya runtse idanunsa ya fesar da Iska, a
hankali ya buɗe idanu suka haɗa ido, ba tsoro ko ladama bare fargaba cikin ƙwayar
idanunta, kafin ya yi motsi ta ƙara cewa
"Na tsaneka, na tsaneka na...," Caraf ya kame bakin domin ba zai iya ɗaukan kalmar
tsana daga gare ta, ko a wasa balle har ƙasan zuciyarta maganar ke fitowa.
Ta zaro idanu waje ta kuma kasa koda motsi ya yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjin shi
dake fitar da ƙamshin Roja
Hannunsa ɗaya riƙe da kanta ɗaya kuma ya riƙe ƙugunta ya haɗa da jikin shi. Wani
irin hot kisses yake mata wanda shi kan shi ya san ya yi abin da zuciyarsa ke
umartar shi kenan, ya yi abin da yafi ƙarfin ta da tunaninta bakiɗaya, gabaɗaya ya
sauke zafin goma da ashirin ɗin da aka tara masa a bakinta, labɓanta sukai jajir
maimakon tayi ƙorafi sai yaga tana lumshe idanunta alamar abin nayi mata daɗi sai
numfashi da ajjiyar zuciya yake saukewa, hannunsa guda ɗaya a bayanta yana
bubbugawa kaɗan kamar ƙaramar yarinya.
Knocking ɗin ƙofa ya dawo da Yaa Sheikh daga duniyar da ya tafi ya zare bakin shi
daga nata a hankali, ita kuma tayi saurin ƙasa da kanta he still holding onto her.
Ya sauke numfashi ya daidaita nutsuwa da kamewar shi, ya yi over acting da yawa
hannunta daya karye ya kama yana kallo, a nan ya fahimci ɗorin bai daidai ba duba
da yadda fatar hannun tai laushi har ta fara kure, ya ɗora tafin hannunsa a
tsakiyar nata tare da saka babbar yatsar shi ya danna, ta saki ihu saboda zafin da
hannun ya ɗauka, ya yi saurin saki yana shafa sumar kanta yana faɗin
"Sorry, Sorry!"
Har lokacin knocking ƙofar ake Yaa Sheikh kuma yaƙi sakinta shi su yake ko
gwarancin tayi yaji muryarta amma tayi shiru sai kuka take tana kaiwa hannun shi
cizo, ya haɗata da jikinsa tare da ɗora kanta a ƙirjinsa a hankali ya sauke
numfashi ya ce.
"‫السي أخرا فقط أنت‬،‫ أريدك أنت‬.‫و أحرص على قلبي لأنك فيه‬. ‫"تعالي إلي أو خذيني‬.
Ya faɗa a taushashe, yasan gabaɗaya ba fahimta take ba, da ace tana cikin
hankalinta to zata gane larabcin na shi,amma yanzu jin maganar ta shi take kamar ta
kurame,
A zahiri kuma idan ka cire larabcin yana nufin
_“Come back to me, or take me with you. Take care of my heart, because you're in
it. I want you, nothing ey, just you_”
Ya manna mata sumbata a goshinta irin ta sunna da kuma cikakkun Malamai tare da
sakinta ya nufi ƙofar, yana sakinta tayi saurin kwanciya kan bed ɗin asibitin ta
jawo bargo ta rufe gabaɗaya jikinta har fuskarta, abu goma da ashirin ya shiga juya
mata tunani, Kiss ɗin Yaa Sheikh ya tsaya a zuciyarta daram! Kamar yadda ƙiyayyar
shi ta samu gurbi mai girma a zuciyarta, kuma tana shi she needs more na kisses
ɗin, tana jin kuma ba zata sake zuwa inda yake bata ta saka hannu ta ƙanƙame
jikinta ta hannunta ɗaya da yake mata masifar zafi da zugi.
Yana buɗe ƙofar yaga Mother da Ummul tsaye suna magana, ganin shi tsaye fuska kame
ya sa suka ratsa ta gefen shi suka shige, bai koma room ɗin ba, ya nufi room ɗin da
El-bashir yake ciki, a nan ya samu Mai martaba yana yi wa El-bashir faɗa kamar
ƙaramin yaro, Abba Hakimi kuma na tsaye Dada na zaune saman kujera, ƙamshin Roja
data ji ya sa ta ɗago kanta ta kalli inda Yaa Sheikh ya ke, ta saki murmushi tana
faɗin.
"Yanzu nake shirin zuwa wajanka Besty" ya ɗan kalleta sai bai ce komai ya lura bata
yi masa kallon siriki shi kuma yana mata haka da idanun tsarkakkiyar zuciyar shi.
Mai martaba ya ce
"Ka bani mamaki Mubasshir, ban ɗauka zaka iya jin ƙiyayyar wani musulmi ba, balle
mutum kamar Yaa Sheikh, idan ka shiga aikin police da wannan niyyar ne, ya zama
dole ka shirya barin aikin dan ba zan lamunta ba" ya yi shiru domin ya manta rabon
da ya yi magana mai tsayin haka, ya sauke numfashi kafin ya kalli El-bashir ya ce
"Garin son zuciyarka ka sanya Zuciyar wani cikin zullumi da damuwa, ka ɗauke masa
farin cikin shi" ya ƙara yin shiru kafin ya ce.
"Say sorry to him, ka nemi ya fiyar shi yanzu nan Mubasshir" El-bashir ya ɗago
kansa tare da kallon Yaa Sheikh a hankali ya ce
"Am sorry Abba, ka yafe mini" bai san cewa har kawo yanzu Yaa Sheikh bai ji zafin
shi ba, yasan duk abin da El-bashir yake akwai wanda ya ɗora shi akan hanya, ya
taka a hankali zuwa bakin gadon tare da neman waje ya zauna
El-bashir ya sake kallon Yaa Sheikh ya ce
"Kayi haƙuri Abba" Yaa Sheikh ya jinjina kai tare da kama hannun da yake mai lafiya
ya riƙe a na shi, nan take soyayyar Yaa Sheikh ta samu gurbi a zuciyar El-bashir ya
yi ta kallon Yaa Sheikh.
Ya sauke numfashi kafin ya ce "Ya jikin?"
"Da sauƙi Abba, forgive me please, na ɗauka kai na ka kashe mini Ammi ka yafe mini"
Yaa Sheikh ya ce "Shhhh! Sannu, Allah ya sauwaƙa" El ya ɗago kai ya ce
"Ya jikin Sister ɗina? Nasan bata so na" Yaa Sheikh ya girgiza kai kamar ba zai
magana ba sai ya ce.
"Zaka iya gina soyayyarka a zuciyarta yanzu, idan akwai wanda bata so yanzu to ni
ne" ya saki hannun El-bashir tare da miƙewa ya yi waje, Abba Hakimi yabi Yaa Sheikh
da idanu cike da tausayawa, da sauri Dada ta miƙe suka jere da Yaa Sheikh magana
take masa yana jinjina kan shi, a hankali yaja ya tsaya tare da juyawa ya kalleta
ta ce.
"Mene kuma Besty?"
Fuska kame ya ce "Koma" ta ce "To ai mun daɗe bamu haɗu ba, akwai abin da nake son
faɗa maka" ya yi mata shiru zata sake magana ya buɗe mata idanu cikin gajiyawa ya
ce
"Ya Allah, surutunki Ƴar fillo ta ɗauka ashe,jeki" ya nuna mata hanya" ta juya ba
tare da ta ce komai ba. A hankali Yaa Sheikh yaci karo da Ummul ta ce "Muje ko?" Ya
kalleta ya kalli bayanta ta gane me yake nufi sai tayi kamar bata gane ba tace
"Ya akai kuma?" Ya marairaccen mata fuska kamar ba shi ya ce "Ummul kin gane" ta ce
"Ni ban gane ba, tunda sanin gaibu sai Allah" a hankali ya ce "Matata"
Fuska haɗe ta ce
"Yaushe Arɗona ya zama haka ne? Koda yake mace na sauya halayya da ɗabi'ar namiji
daman, ba shakka Halisa tayi tasiri wajan sau yaka" bai cewa mahaifiyar ta shi
komai ba ta ƙara cewa
"Ba zaka samu yadda ka ke a wajanta ba yanzu, dole ka nemi haƙuri ka sakawa
zuciyarka Aliyu" sai a lokacin ya kama hannun Ummul ya ce
"Yaushe haƙurin nawa zai ƙare? Nayi na kuma Ummul, I want her in my life" sai ya
bata tausayi tasan duk Abin da Yaa Sheikh ya ce to har zuciyar shi ne, idan abu
yafi ƙarfin shi yana faɗa mata kai tsaye ne.
"Muje mota" ya kasa motsawa ta ce "Arɗo ka gane ka fahimta, Halisa zata koma
masarauta kafin komai ya daidaita sun tafi gida da Barrister Maryam, kai ma kuma
zaka bi ni ne" Ya dinga kallon Ummul da rikitattun idanunsa, shi kam a yanzu a
shige level ɗin da za ana gindaya masa wasu sharuɗa, ganin ran Ummul ya fara ɓaci
yabi bayanta zaune ya sameta gaban mota wajan driver ya zagaya mazaunin mai zaman
banza ya zauna, bakinsa ɗauke da addu'a ko zai samu sassauci daga zuciyar shi.
Sun yi nisa akan titi ta ce
"Lokaci ya yi da zaka koma Yola, ka ɗauki ragamar Rugar Bello a hannunka, ka maye
gurbin mahaifinka, suna buƙatar ka a can" ya yi shiru ta juya ta kalle shi, taga ya
kifa fuskarsa a tafukan hannayensa ta ce "Zamu matsala da kai idan zaka bayyanar da
damuwarka a fili" ya ɗago kai idanunshi sun yi ja sun ri ne ya ce.
"'ana 'uhabuha"
Ta ce "Ni na nasan haka, amma ita fa? Iyayenta Abba Hakimi fa? Sun sani,ko ka taɓa
furtawa kana son ta? Ka aureta without her permission dana iyayenta baka taɓa cewa
kana son ta" ya yi shiru can ya nisa ya ce
"Kamar ba sai na faɗa ba, amma ki faɗa musu" ta kalle shi kawai ta girgiza kai ta
ci-gaba da driving har zuwa Na'ibawa, gatekeeper ya buɗe mata gate ta shi ga da
motar a hankali tai parking a harabar gidan tare da fitowa, Yaa Sheikh ya fito kan
shi na sarawa sbd ciwon da yake masa zuciyar shi tayi nauyi.
Idanunsa ya sauka akan wani dattijo dake zaune a saman kujera, kamanin shi da Yaa
Sheikh sun ɓaci komai nasu iri ɗaya, Ummul tai murmushi ta ce "Your grandfather"
Yaa Sheikh ya ƙarasa Dattijon ya miƙe riƙe da sanda ya ce "Yau gani ga babban
malami lale" gabaɗaya suka shige cikin gidan.
A can gida Mother ta nunawa Halisa komai, hankalinta ya kwanta ganin babu Yaa
Sheikh a gidan, Zahrah tana ɗakin tana aikin kuka tuni akaiwa iyayenta waya ana
buƙatar ganinsu.
Misalin ƙarfe 10:30 na dare Mother ta tura ƙofar bedroom da Halisa ke ciki, a zaune
ta sameta riƙe da hannun alamar zafi yake mata, ta nemi waje ta zauna cikin kulawa
ta ce.
"Kina son sanin sunanki

Please Login or Register in order to submit comment