You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali tashe suka kalli juna tare da faɗin "Me ya samu
macijin nan? Ki dai asiri akaiwa Yarinyar nan?".

Halisa a tsorace Macijin a tsorace amma a haka cikin dakiyar zuciya ta ƙara ɗaga
dutsen a karo na biyu ta ƙara bugawa Maciji, Innalillahi a wannan lokaci kururuwar
da Macijin yai sai da kowa na wajan yaji, jini ya sake ɓalle masa a hankali ya
sulale ƙasa baya ko motsi alamar ya mutu... ajjiyar zuciya ta sauke haka kurum taji
kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tai a wajan ta shiga rera kuka tausayin macijin ya
kamata musamman yadda taga jini na zuba a jikinsa, Hamma Yabi ya ƙaraso wajan
Halisa Dajeno Rome tare da ɗagata yana dariya ya ce "Danejon Dada kin kashe
macijin, kin kashe sa bana faɗa miki cewa ba zaki mutu ba? Zamu samu ƙwayar nono da
Nagge masu yawa" ƙanƙame Hamma Yabi tai cikin kuka ta ce "Bana so Hamma Yabi, mu
bar nan wajan kaina juyawa yake, bana son ganin jinin nan kaji" hannunta ya kama
sukai gefe guda. Cike da taƙaici Sarkin ruga yake bin Macijin da kallo bai taɓa
tunanin haka ce zata kasance ba, cike da baƙin ciki ya amshi wani sanda ya shiga
kwarɗawa macijin aka tun macijin na motsi har ya daina jikinsa yai face face da
jini tare da raunuka. "Ka ɗauke sa ku cillar a gefen gaɓar ruwa wani abin yai
kalace dashi" Giɗaɗo da Alƙalin wasan suka ɗauki Macijin tare da nufar cikin jeji
da shi. Suna zuwa suka cillar gefe guda da sauri suka juya cikin Rugar Rome.

Sanyin gaɓar ruwan daya ratsa cikinsa ya sanya ya fara Girgiza yana juyi tare da
murmurɗe jinsa gefe guda, wani kalar ihu yake mai nuni da azabar da yake ciki, ya
daɗe cikin wannan halin kafin yai Girgiza tare da rikiɗewa ya dawo siffarsa yadda
yake fitowa a mutum ba Aljani ba, yana kwance sambal gefen ruwan Farar Alkyabbar
jikinsa duk ta ɓaci da jini. A hankali ya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa inda
yake zubar da jini, runste idanun yai sosai cikin ƙasa da murya ya ce "Ya Allah"
yana nan ƙwance yaji iska ta mamayesa baki ɗaya kafin kace wani abu iskar ta
ɗaukesa zuwa sama.

Duk farin cikin dasu Shatu suke ciki banda Danejo rasa abin da yake mata daɗi tai,
gashi jinin Dada ya matsa ga tunanin dake wanzuwa a cikin zuciyarta. Dada ta kalli
Shatu ta ce "Farin ciki za kiyi Halisa ba damuwa ba, da tuni an rabani dake Allah
bai ba, akwai ƙaddarorin da suke biye dake, amma duk wahala duk tsanani waya rana
zaki zama abar ƙwatance tabbas zaki samu miji wanda zai kula da maraicinki" Danejo
ta ce "Dadana nifa ba marainiyya bace, ina dake ga Hamma Yabi ga kuma Shatu"
jinjina kai Dada tai idanunta akan zoben hannunsa Halisa ta ce "Ina kika samu
wannan Halisa?" Girgiza kai tai cikin damuwa ta ce "Ban sani ba Dada, kawai na
gansa a hannuna"... "Bana son ƙarya fa" da sauri Halisa ta ce "Da gaske nake miki,
kalli kiga" ta faɗa tana nuna mata tambarin zoben, Dada ji tayi kansa ya sara
idanunta akan Zoben da sauri ta riƙe kanta tare da rufe idanunta, kamar mai son
tuna wani abu babu abin da take gani a cikin idanunta sai tambarin masarauta dake
manne cikin zoben. Ganin yadda Dada ta rirriƙeta kanta ya sa Hamma Yabi fita da
gudu ta tatso mata kindirmo mai zafi, da taimakon Halisa Dajeno Rome suka bawa Dada
kindirmon nan da nan zufa ga shiga saukar mata bacci ya ɗauke ta.

Juyawa Halisa tai ta kalli Shatu dake barci a nutse ta kalli Hamma Yabi ta ce
"Hamma yaushe Dada zata samu lafiya ne? Kullum a ƙwance take ina tsoran na rasa ta
aradu" Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya ce "Ba zaki rasa Dada ba, gobe zan koma
asiti bamu da kuɗin kai ta asibitin burni" Da sauri Danejon ta ce "A siyar da Nagge
to" zare ido Hamma Yabi yai ya ce "Aradu ƙarya ne, Uban waye zai taɓa Nagge ai mu
dasu mutu karaba" ba tace masa komai ta miƙe tsaye tare da yin waje lokacin rana ta
faɗi, can gefe ta nema ta zauna ita ɗaya sai tunani take a haka har akai magariba
tana zaune, ganin duhu ya fara yasa ta miƙe tare da zagayawa bayan bukka ta kwaɓe
kayan jikinta, halittar jikinta ta tsorawa idanu, musamman ƙirjinta tana mamakin
abun mene amfaninsu a jikinta? Ita a gareta basu da wani abu kullum sai dai su ƙara
girma. Ruwa ta sheƙa babu ko sabulu tana gamawa tai alwala, wasu kayan fulanin ta
ɗauka farare ta saka tare da Ajjiye waɗan can, da sauri tai sallah tana gamawa taci
tsiran da Hamma Yabi ya kawo musu, tana ci ta kwanta barci domin da wuri take son
zuwa kiwo ta dawo ta tafi tallan kindirmo.

Ciki zafin nama Prince ya saka hannu tare da ɗauke Safwan da mari ya ce "Ka fita a
sabgata, kaje ka faɗawa Sarki halin da nake ciki ya ɗaukeni, kuma kasan yana gab da
rabani da matata wanda ba zan iya jure hakan ba sam" Safwan ya kalli Prince cike da
mamaki ya ce "Ban taɓa ganin mai taurin kai a duniyar Aljanu irinka ba Prince,
cutar da yarinyar nan kake fa, babu haɗi tsakanin mutum da Aljani na faɗa maka,
abin kunyane ka rasa wacce zaka so sai Bil adam? Allah zai saka mata fa" banza
Prince yai da Safwan a wannan lokacin rabinsa na mutum rabi kuma na siffar Aljani
da sauri ya juya zai tashi sama Safwan ya ce "Ina zaka? Ba dai wajanta ba?" Prince
ya ce "Ba zan iya yin wasu daƙiƙo ba, ba tare da naga matata ba, da matata nake son
kwana a yau ɗin nan" yana faɗin haka ya ɓace ɓat kai tsaye Rugar Rome ya nufa.
Halisa juya cikin barci taji wani sanyi na ratsa mata jiki, ga wani mafarki da ke
ƙafafuwanta sai motsawa suke amma ta kasa koda motsi bada ji take kamar ana
danneta. Can dai ta farka a firgice Innalillahi a ruɗe ta fara kallon inda take,
tana kwance tsakiyar dokar daji ba gida gaba ba gida baya...
Waye ya kawo Halisa Dajeno Rome cikin dokar daji?...

#Sarautar marubuta
#true life story
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*
https://wa.me/+2348119237616

5..
A zabure ta miƙe tsaye tana ƙarewa cikin dokar dajin kallo, babu abin da ya bata
mamaki irin yadda taga an sauya mata kayan jikinta, daga na Fulani zuwa na wasu
saƙi farare masu kyan gaske. Jikinta na rawa sbd tsoro da tarin fargabar dake ratsa
dukkan wasu lunguna na ƙofofin zuciyarta ta shiga ƙarewa jikinta kallo. Idan
hankalinta yai dubu to ya tashi ta ƙara razana da halin da take ciki a yanzu, domin
ba iya kayan jikinta da aka sauya mata ne kaɗai ya bata mamaki ba, zanan jan lallen
data gani kwance a hannunta shi ne ya ƙara ta hanyar mata da hankali, ga sumar
kanta da akai mata wasu irin kalba manyan gwanin sha'awa ita bata taɓa ganin kanta
yai irin wannan kyan ba sai yau. Waye ya kawota nan Meke shirin faruwa da rayuwarta
ne, ina Dadarta?.

Ƙare wa cikin dajin tai babu ko hanyar da zata bi ta nufi Rugarsu, daɗin daɗawa ita
kanta bata san a inda take ba, wacce kalar rayuwa ce haka? Daga yin barci kuma sai
mutum ya farka ya gansa a tsakiyar daji? Bayan tasan a bukkar Dada tai barci.
Tafiya ta shagayi idan ta kalli gabas da Arewa, guda da yamma sai ta saki kuka tare
da faɗin "Na lalashe jama'a ina nake ina rugar rume tayi, ina Dadata, ina Shatu,
ina Hamma Yabi duk kuna ina wayyooo Hande en boni, Yettore jaumirawo" ta faɗa ɗora
hannunta aka tare da sakin kuka, ta fiya kawai cikin dokar dajin tun tana kuka har
tai shiru sai idanunta da take rarraba wa a ciki dajin.
Kukan da tayi da kuma gudun data jima tana yi sune suka taru suka haifar mata da
wata gajiya wacce ta sanya ko idanunta bata iya buɗewa sosai sbd yadda kanta ke
juyawa da kuma yunwar data keji, lokaci zuwa lokaci tana buɗe idanunta tare da
zubawa zanan lallen hannunta idanu, tana cikin wannan hali ta ƙaraso wani waje
wanda yake da rana sosai hakan yasa Danejo ta wahala fiye da zaton mutum, ga ƙishin
da take ji. Daurewa tai taci gaba da tafiya sai dai duk yadda takai da daurewa ta
kasa bata san lokacin da jiri ya kwashe ta ba, tai baya luuu zata kifa da sauri aka
tareta ana faɗin "Subuhanallahi" mutumin ya faɗa a taushashe yana mai riƙe Danejo
wacce ta faɗo jikinsa babu numfashi alamar ta soma kenan.

Kyakkyawan idanunta mai ɗauke da kuriyar ƙwayar ido su ya ware akan Danejo yana mai
ƙara jin nutsuwa na saukar masa a jikinsa, a hankali a kuma dukkan wata ƙaunarta ta
shiga nunkuwa a zuciyar Prince Bilal. Yanzu ne zai samu cikakken lokacin kasancewa
da ita, irin kasancewar nan ta har abada domin baya jin akwai mutumin daya isa ya
raba shi da Matar Danejo a cikin wannan Dajin, zai zauna da ita zai rayuwa da ita,
tai ta haifa masa yara, ya kuma yi alƙawarin ba zata taɓa sanin shi aljani bane,
zaici gaba da zuwar mata a suffar Balarabe kamar dai suffar wani Sheikh ɗin Malami.
Ɗaukarta ya yi a hannunsa zuwa gaɓar wani ruwa, jallabiyar jikinsa ta sauka har
ƙasa tare da rufe masa ƙofatonsa, a haka ya Ƙarasa tare da kwantar da ita a gefen
ruwan wajan da yake da ɗan danshi danshi musamman daya lura da jigatar da tai duk
da cewa duk wani abu da take akan idanunsa ne. Yana kwantar da ita ya zauna gefenta
idanunsa na juyawa tare da sauya launi zuwa wata kalar, hankalinsa ya karkata gaba
ɗaya zuwa cikinta idan yake hango ɗansa dake maƙale a mararta hakan sai cike da
farin ciki Prince ya saki Murmushi bakin na rawa ya ce. "Ubangiji ya saka mini
sonkiwa zuciyata, tun kina cikin mahaifiyarki, zanci gaba da sonki ba zanyi saken
da za a rabani dake ba, kamar yadda aka rabani da mahaifiyarki tun tana asalin inda
take rayuwa" shafa cikin nata yai idanunsa na tsiyyayar da wani ruwa ya ce "Babu
alaƙa tsakanin mutane da Aljanu, amma naji a wannan karan dama Ubangiji a suffar
mutane ya halittoni, mene yasa bakwa iya ganinmu a suffarmu ta zahiri sai dai mu
muganku? Ina son ki matata Danejo,ina gab da ɗaukeki zuwa duniyarmu" dariya ya saka
gaba ɗaya wajan ya ɗauki rawa da Girgiza can kuma ya ɓace da wajan.

Acan Rugar Rome kowa gari na wayewa suka saba Danejo na tashi zuwa garken Nagge
ƙara tatsar nono, hakan yasa Dada bata damu ba sbd ganin Danejon bata cikin bukkar
sai Shatu dake kwance a gefe tana barci, Hamma Yabi ya fita tun sassafe zuwa
asibitin dake gefen Rugar Rome domin samawa Dada layi. Yana tsaye a a ɗan wajan da
mutane suke tsayawa gaba ɗaya mutanan ba sufi mutum goma ba, suna zuwa kamar mutum
biyar zai koma ya ɗakko Dada. Wani Likita ne hannunsu riƙe da waya yana dubawa ya
raɓa ta gefen Hamma Yabi ya shiga office, Fuskarsa ɗauke da fara'a ya kalli mutumin
dake cikin office ɗin ya ce "Dr Hamza na ganka a zaune ina patients ɗin?" Dr Hamza
ya dubi Dr Iliya yana ƙara ware idanunsa ya ce "Patients suna can waje, bani da
time na duba su serious,idan zaka shekara kana duban jama'ar Rugar nan ba zaka taɓa
samunsu da cikakkiyar lafiya ba, ƙazanta ita take ƙara lalata musu lafiyar jikinsu
na gaji wallahi, sai Shegen son shanunsu amma basu san yadda zasu kula da lafiyar
jikinsu ba" Dr Iliya yaja kujera tare da zama sosai yana faɗin "Ai Dr Hamza sai
haƙuri, kasan cikin karkara musamman ruga haka ba komai suka sani ba, kai dai barsu
da arziƙinsu wato Nagge su kawai suka sani" Dr Hamza ya ce "Let's leave this
matter, it is not in front of me" ya faɗa yana duba wani file, "I got the message
you want to see me up, lafiya dai kake mini kiran gaggawa haka?" Dr Iliya ya
tambayi Dr Hamza cike da jin don abin dake faruwa. Gyara zama Dr Hamza ya yi kafin
ya ce "The government has given free medicine to the people of Ruga, maganin da
gwamnati ta bayar suna da yawa, akwai maganin Suger, Hawan jini, Maleriya, da
sauran maganin cuccutikan, yawwa sai maganin sikila irin folic acid, Paludrine,
Peniciillin V,Hydroxyurea. Anfi kawo maganin Sickler sbd yawaitar samunta da ake
cikin karkara, shiyasa nace a kiraka" cikin jin Daɗi Dr Iliya ya ce "Masha Allah
yanzu yaya za'ai kenan?" Wani kallo Dr ya Hamza yaiwa Dr Iliya kafin ya ce "Ya kowa
za'ai? Kasan Rugar nan ko an basu magani a banza, basu san important ɗinsa ba, so
that zamu kwashi 88% a cikin 100 mu siyar mu raba kuɗin, kai ba kana da chamist ba?
Sai ka zuba kawai acikin chamist ɗin naka" cike da gamsuwa Dr Iliya ya ce "that's
good, amma gwamnati ƙoƙari sosai fa, banda haka wannan maganin sunfi ƙarfin miliyan
3 da wani abu fa,ana kula yanzu da ɓangaren lafiya sosai da masu juna biyu,
anywhere zuwa dare zan zo da mota na ɗauki rabona" Sallama sukai tare da fitowa a
tare ganin hakan yasa Hamma Yabi saurin kallon Dr Hamza ya ce "Aradun Allah na
shafe awanni a nan gashi muna ta jira" a faɗace Dr Hamza ya ce "Wai kai fillon nan
wani irin banza ne bagidaje ne kai? You doesn't know anything akan asibiti ka
addabi mutane da wautarku ta Fulani, mu bamu da wasu kayan aiki cikin Asibitin nan
kana kallo da idanunka ai, dan haka kada ka sake zuwa idan an kawo kayan aiki zamu
sanar get out" jiki babu ƙwari Hamma Yabi ya koma cikin Rugar Rome, yana zuwa ya
sake tarar da wani tashin hankalin babu Danejo gaba ɗaya acikin Rugar, sanadin
hakan yasa jikin Dada ƙara rikicewa abu kamar wasa duk inda suke tunanin ganin
Danejo babu ita sam har kusan kwana biyu.

Tunda ya kwantar da ita a gaɓar ruwan har gari ya waye ta kwana a wajan, wani daren
ya yi ta sake kwana, kwana biyu kenan amma bata motsa ba. Bata kuma da ranar tashi
sai lokacin da Ubangiji ya nufa ko kuma ya tsara. A can cikin barci ta fara mafarki
gata da namiji suna kasancewa waje guda, wani abu mai kama dana auratayya na
gilmawa a tsakaninsu. Numfashi ta sauke tana motsa ƙafafuwanta zuwa cinyoyinta da
suke mata zafi, tana jin kamar an daddaneta a firgice ta farka tana kurma ihu tare
da kiran sunan Dada, ba addu'a babu komai. Cikin tsoro ta fara bin jikinta da kallo
babu komai lafiyarta ƙalau domin ba wani sauyi da taji. Ajjiyar zuciya ta sauke a
bayyane tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka, kenan haka
rayuwarta zata ƙare cikin dokar dajin ko yaya ne? ya akai ta tsinci kanta a dajin
gaba ɗaya ta rasa amsar tambayoyin zuciyarta. A hankali ta fara jin dariya na
karaɗe wajan, tare da surutu ƙasa ƙasa. Miƙewa ta yi da sauri ta shiga duba inda
take jiyo sautin dryar a haka ta ƙaraso jikin wata ƙatuwar bishiya, cike da tsoro
da kuma tarin zullumi ta ɗaga kansa zuwa saman bishiyar idanunta ya sauka akan wani
ganyen bishiya dake lilo shi ɗaya, sai ka ɗauka iska ke kaɗa shi amma abin mamaki
shi kaɗai ne yake lilo daga cikin sauran ganyen bishiyar. Prince Bill wanda a yanzu
ya rikiɗe zuwa suffarsa ta asalin aljani yana kwance saman ganyen yana karkaɗa
ƙafarsa wacce ita ce take sanya ganyen bishiyar motsawa, Danejo dai kallon ganyen
take cike da mamaki tana tsaye taci mangoro ya faɗo kanta abinka da mai jin yunwa
da sauri ta ɗauki mangoron babu Bisimillah ta shiga sha idanunta na lumshewa sbd
daɗi. Daga bayanta taci ance. "Kisha a hankali da wasu da yawa idan kina buƙata"
juyawa tai da sauri baki buɗe take kallon mai maganar, iya tsoro da razani ta shiga
domin bata taɓa ganin halitta irin wannan ba, mangoron ta saka tare fasa wani Ihu
ta ɗaga ƙafa zata gudu yai saurin riƙe hannunta.

Share🥰🥰🥰
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈IDAN BA KE 🌈*

6....
*_Arewabooks@Nimcyluv_*

"Na shiga uku Aljani Balarabe" Danejo ta faɗa a ruɗe tana ƙoƙarin kwace Hannunta
daya riƙe cikin nasa. A nutse Prince ya ware idanunsa sosai a kanta yana Mmkin
Yadda duk ta ruɗe kamar taga mugun abu. "Me ya baki tsoro" murguɗa masa baki tai
tana suɗe hannunta dake ɗauke da ruwan mangoron ba tare data ce komai ba. Prince ya
saki tattausan murmushi mai kyau da tsari yana binta da kallo musamman idan ya tuna
abubuwa da suke faruwa a tsakaninsu, sai yaji nutsuwa ta kamasa. Hannunsu ta make
ta ce "Sakeni haka kurum kai mini ciki, bayan Dada ta ce ba kyau namiji ya taɓa
mace" ta ƙare Maganar tana binsa da kallo, sai a lokacin da a shiga ƙarewa tsarin
hallitar jikinsa da kallo, fari ne tas kamar ka taɓa shi jine ya fito, yana da
faɗin ƙirji fuskarsa mai cike da ilhama, ga wani gudun saje wanda ya kewaye
fuskarsa zuwa ƙasa wajan gemunsa, fuskarsa mai faɗi ce babu wani abu da zai bamban
tasa da jinsin larabawa. Prince ya saketa yana mai faɗin "Ciki na nawa kuma?"
Zuciyarta na bugawa sosai ta ce "Me kace?" Ya girgiza mata kai yana ware hannun shi
ya ce "Babu komai Danejo" zare ido tai tana dafe ƙirji sosai a tsorace ta ce "Kasan
sunana? don Allah kasan rugarmu wallahi ɓata nayi ka taimaka kaji ɗan Balarabe"
idanunsa ya ɗaga sama tare da daidaita juyawar launin idanunsa ganin yana neman
rikiɗe masa, jikinta duk rawa yake tai saurin cakumarsa tare da rirriƙesa wanda yai
sanadiyar fitowar wata jela a bayansa, sbd ko yaya ya samu kusanci da ita, baya iya
zama a zallar mutum, dole sai wani sashi na jikinsa ya juye zuwa na aljani. "Ukkkkk
heee" ya faɗa cikin kumburarriyar wacce ta amsa kuuwa cikin kunan Danejo. Gaba ɗaya
rikicewa tai ganin yadda take neman maƙalesa baki ɗaya saboda tsoro da fargaba har
take shirin bayyanar da kofatonsa yasa yai saurin riƙo Fuskarta tare da hura mata
iska a fuska. Ƙuri tai masa da idanu a rarrabe ta shiga faɗin "Ka kaini wajan
Dadata kaji, bana son zama a nan tsoro na keji Da...da...ta.." ta kasa ƙarasa
maganar sbd idanunta da suka ruf wani barci mai nauyi ya ɗauketa.

Fuskarta yabi da ido yana hango lokacin da yake tare da mahaifiyarta, duk yadda ya
nunawa Dada so da ƙauna amma haka wani mugun babban Malami ya raba shi da ita, ba
shi da niyyar cutar da Dada kawai ƙauna ce tasa yake tare da ita, yai ihun tare da
magiya amma haka Malamin ya fatatakesa daga cikin Dada bayan ya ƙona shi. Wannan
dalilin ya sa yai jinya sosai har bai san inda Dada tai ba sai kwatsam ya ganta
lokacin tana ɗauke da cikin Danejo, tun daga wannan lokacin ya ɗauki son duniya ya
ɗora akan Danejo, ya manta da batun Dada ɗan tayin dake cikinta kawai yake muradin
yaga ya zo duniya.
Sauke numfashi yai yana binta da idanunsa daya gama rikiɗewa har wani hayaƙi yake
fiddawa, hannunta ya riƙo ya kama yatsan dake ɗauke da zoben daya saka mata ya jima
yana kallonta kafin ya saketa zuwa ƙasa ya kwantar. Tsakiyar dajin ya koma yana
Girgiza da surutai cikin ƙaramin lokacin ya koma asalin suffarsa ta aljani yana
wani ihu da gurnani kafin kace wani abu ya gama haukata dajin can kuma ya ɓace ɓat.
Yamma Yabi ne da Shatu tare da Sarkin ruga da kuma Giɗaɗo kwance a gaban Dada wacce
take cikin halin rayuwa ko mutuwa, bata san inda kanta yake ba, sunan Halisa Dajeno
Rome ne kawai a bakinta. Giɗaɗo ya ce "A jiƙa wannan maganin a bata" da sauri Hamma
Yabi ya amsa tare da jiƙawa da taimakon Shatu ya ɗaga Dada suka ɗora mata maganin,
wani shaƙuwa tai jikinta ya shiga jijjiga can kuma ta kwanta shakaf barci ya
ɗauketa. "Na shiga uku na lalashe Hamma Dada ta mutu wayyo yanzu yaya za mu yi Dada
ki tashi" idanun Hamma Yabi na taruwa da ruwan hawaye ya kama Shatu tare da riƙeta
ya ce "Assha Assha Shatu Dada nada rai, daina kuka yaro barci Dada tai" kuka kawai
Shatu take, duk da ƙarancin shekarunta amma ta fahimci cewa Dada ita ce cikon farin
cikin su, tare da jin daɗinsu. Sarkin ruga ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Allah shi
bata lafiya, Aradu tana gab da mutuwa" jin kalmar Sarkin ruga yasa Shatu ƙara sakin
kuka tana jijjiga Dada tare da faɗin ta tashi kada ta mutu ta barsu cikin ƙuncin
rayuwa. Cike da takaicin kalamar Sarkin ruga Hamma Yabi ya bisa da kallo yana
addu'ar Ubangiji shi ya ɗauki rayuwarsa yabar Dada a duniya ko dan farin cikin
Shatu da Halisa. "Ba a samu labarin Danejo ba har yanzu?" Girgiza kai Hamma Yabi
yai yace "Aradu ta ɓace babu ita kaf cikin ruga da kuma daji" cikin tausayawa
Giɗaɗo ya ce "Wayyo Allah shi baiyyanata" "Kawai iskanci ta tafi, amma ina ne
Danejo bata sani ba cikin ruga da dajin ba har kiwo take zuwa ba?" Da sauri Hamma
Yabi ya ce "Danejo ba zatai iskanci ba, domin bata san shi ba" fita duk sukai daga
cikin bukkar. Hamma Yabi ya dubi Shatu da barci ya ɗauketa a jikinsa a hankali ya
kwantar da ita, tare da fita daga cikin bukkar. Yana fita ya shiga irga Nagge wanda
ya zama al'adarsa kullum tunaninsa za a iya sace musu Nagge shi ya sa a rana sai ya
irgasu sau biyar. Kai tsaye asibiti ya nufa lokacin ana zubawa Dr Iliya magani a
cikin mota.

Saukar ruwan ruwan sama ne ya haddasa farkawar ta daga barci, da sauri ta miƙe
tsaye jirkinta na rawar ɗari sbd gaba ruwan ya gama yi mata doka, ganin bata da
wata mafita ya sa ta fara ƙoƙarin ɗaga ƙafarta Innalillahi sai a lokacin ta lura
ashe a kan wani ƙaton dutse mai tsayin gaske take, ita kanta bata iya hango ƙasan
dutsen, a hankali ta koma tare da zama saman dutsen "Innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un wacce kalar rayuwa ce take ciki haka? kenan akan dutsen ta kwana? ina ne
nan kuma kwananta nawa? ta haukace ne ko mene? Anya ita ce ba wata Danejon bace
daman?" Wani raunataccen kuka ta saka kuka take da dukkan ƙarfinta kenan ita da
Rugarsu har abada ina za taga Dadarta? Kuka take sosai na rashin mafita ga
rayuwarta ga ruwan sama na dukanta, yunwa take ji sosai, hannunta ta tara ruwa ya
shiga sauka a hannun cikin sauri ta shiga shan ruwa sai daya isheta sosai sannan ta
koma ta kwanta barci ya ƙara ɗauketa saman dutsen.

"Ke! Ke! Baiwar Allah" aka shiga kiran sunanta wanda yasa ta buɗe idanunta da sauri
tare da fatan Allah ya sanya a cikin Rugar Rome take, wasu fatake ta gani su wajan
biyar tsaye a kanta ko wanne hannunsa riƙe da abu. Sai a lokacin ta lura ashe a
kwance take saman wani ya shi saɓanin ɗazo da take kan dutse. Idanunta take
rattabawa tare da binsu da ido ganin ba wanda ta sani yasa ta mayar da kanta ƙasa
"Baiwar Allah wace ke daga ina kike? Kin san ina ne nan a Maiduguri kike fa?" Da
sauri ta kalli mai maganar sai bata ce komai ba. Wani daga ciki ya ce "Ko bata
magana ne? Kamar bafulatana" "Akwai abin da ke damunta Allah kaɗai ya sani" cewar
wani, yin duniya sukai tai magana ko ta faɗi garin da take amma tai shiru kamar an
kulle mata baki dole suka barta bayan sun yi mata fatan alkairi.
"Danejo" aka kira sunan a taushashe sautin Muryarsa da taji yasa tai saurin Miƙewa
yana tsaye kamar kullum sanye da fararen kaya ga tarin nutsuwa da ilhama a tattare
da shi. da sauri ta nufesa kamar zata riƙesa sai kuma ya tsaya dab dashi tana sakin
kuka tare da faɗin "Ɗan Balarabe ka kaiki gida kaji, tsoro na keji ina son nasan
halin da Dadata ke ciki" Prince ya sake mata murmushi yana faɗin "Waya kawoki nan?"
Hannu ta watsa alamar bata sani ba da sauri ta ce "Amma ka sanni ko? naji ka iya
kiran sunana do Allah ka kaini wajan Dadata" yana kama hannunta ya ce "Ban san inda
kike ba, Danejo kuma sunan matata ne ina iya kiran sunan kowa da ita" da fararen
idanunta ta kallesa ba tace komai ba, sai hawayen dake suntiri a cikin idanun nata.
Hannunta ya riƙe yana janta da Shira tun tana kuka harta daina, tana zaune taga ya
kawo mata naman kaji da yawa da kuma kayan marmari ƙin cin komai tai sai da ya fara
mata wasa yana bata labarin abin dry sannan ta saki jiki taci kayan marmarin. "Zan
kaiki gida" da sauri ta ce "Da gaske kake Balarabe?" Kai ya ɗaga mata yana faɗin
"E, Matata" turo baki tai ta ce "Ni ba matarka ce ba" ya ce "Daman ba dake nake ba"
kamar ba zatai Magana ba sai ta ce "Yaushe zaka kaini wajan Dada" yana riƙo
hannunta ya ce "Ko yaushe, amma kiyi mini Al'ƙawarin na dinga zuwa ina koya miki
karatu, kuma kiyi al'ƙawarin zamu zama ƙawaye a duk sanda na buƙace ki, kizo gareni
ba zan cutar dake ba na rantse da Ubangiji al'arshi, ba zan bari kuma kowa ya cutar
dake ba" tunda ya fara magana take kallonsa cikin rashin sani ya ce "Kuma Dadata
zata samu lafiya?" Shiru yai mata an

Please Login or Register in order to submit comment