You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jadda da bakinta ke rawa ta ce "Allah ya yi gutsi
gutsi da maƙaryaci" Zahrah taƙi kallon Jadda. Mother ta ce "Ayyah jeki ki huta ba
aiki" Zahrah dai ta kasa riƙe abin da yake ranta ta ce "Yaa Sheikh fa? daman ina
son gaishe shi ne" da hannu Mother ta nuna mata wani part ta ce "zaki iya samun shi
can" ta miƙe da sauri ba kunya ta nufi Part ɗin Yaa Sheikh.
Mother ta ce "Maimoon kira mini Halisa yanzu" Maimoon ta nufi part ɗin Zahrah ta
samu Halisa sai zuba kayan Zahrah take cikin trolley bag tayi saurin riƙe hannunta
ta ce "Kizo Mother na kiranki" Halisa ta ce "Bari na ƙarasa aikin Anty" Maimoon ta
ɗaga ta tsaye ba tare da ta ce komai ba ta jata zuwa waje. Bata samu Mother a
parlour ba sai suka shige bedroom ɗinta tana zaune bakin gado. Mother ta ce "shigo
Halisa, Maimoon jeki ko" Maimoon ta juya Halisa ta shiga kanta a ƙasa haka kunyar
Mother tai mata nauyi taji kunyarta ta ce "Saki jekin ki zo nan" ta kama hannunta
tare da zaunar da ita bakin gado ta ce "Yaya sunanki ma?" A hankali ta ce "Halisa
Danejo Rome" Mother ta jinjina kai ta ce "Ok Zahrah ƴar uwar ki ce?" Ta girgiza kai
ta ce "A'a wai aikatau zan mata" ta faɗi haka a taƙaice. Mother ta jinjina kai
sosai ta ce "Saurare ni da kyau, Zahrah matar Yaa Sheikh ce Wannan babban mutumin
da kika gani fari dashi?" Halisa ta ce "Balarabe?" Mother ta ce "Yawwa shi" haka
kurum idanun Halisa ya cika da ruwa Mother ta ce "Shi ne mijin Zahrah kuma kema
mijinki ne, dan haka ke ba ƴar aiki bace matar shi ce ke, kamar yadda Zahrah take
matar shi haka kema kike matar sa" Halisa tai ta kallon Mother har lokacin idanunta
cike yake da hawaye da gaske Balarabe shi ne mijin Zahrah?. Mother ta katse mata
tunani da faɗin.
"Kece uwar gida, aurenki aka fara ɗaurawa sannan na Zahrah, na kira ki muyi magana
sbd Yaa Sheikh ya ce baya son ki" da sauri Halisa ta miƙe tsaye hawaye na zubu mata
bakinta na rawa ta ce "Amma ni ina son shi ai.....


Ni ina team Yaa Sheikh ku fa?

08119237616
Paid book
₦500[1/3, 4:48 PM] Abk: "Kin san shi ne da kike son shi?" Mother tayi tambayar
idanunta akan Halisa wacce hawaye ya gama cika mata idanu. Ta kasa cewa komai amma
bakinta bai bar rawa ba, ganin yanayin ta ya sanya Mother sassauta murya ta ce
"Kina da ƴan uwa a garin nan?" Ta girgiza ta ce "Aradu babu" "Ok to ki Saurare ni
da kyau, listening to me..." Tsayawa tai da maganar idan ma tayi ta san a banza,
Halisa does not speak English, let alone understand what is being said. Ganin bata
da wani option wanda ya shige tayi magana da harshen da Halisa zata gane ya sanya
Mother tattara nutsuwarta ta ce "Ki ɗauke ni matsayin uwa kafin ki koma gida, zan
riƙe ƙo kamar ƴar dana tsuguna na haifa, da farko ki yarda cewa ke matar Yaa Sheikh
ce Balarabenki kamar yadda kika ce ɗin, Kinga zoben hannunki shi ne sadakinki, abu
na biyu kada ki kuskura koda wasa ki faɗawa Zahra kema matar Yaa Sheikh ce, duk
aikin data saki kiyi zaki samu lada albarkacin igiyar auren dake kanki, duk abin da
Yaa Sheikh zai ce kiyi just do it ina nufin kiyi kai tsaye, ba zai cutar dake ba,
infact ai kin riga da kin san shi ko?"
Halisa ta ɗaga kai da sauri kuma ta ce "Kuma ina son shi ai, ina ganin shi idanuna
idan ina barci" Mouth ta ce "Good, a kullum yana tashi tun ƙarfe 4 na dare baya
komawa barci sai ƙarfe 12 sbd ƙarfe 8 yake zuwa wajan ɗaliban shi, duk inda 12 tayi
ya dawo gida, bai damu da abinci ba sosai ba zai taɓa cewa yana jin yunwa ba,
tsakanin azahar da asr yana barci idan bai ba, ciwon kai yake sosai, sannan baya
rabo da black tea da zuma a ciki, duk ranar Alhamis da Litinin azumi yake, yana son
ƙosai sosai" Halisa ta saki murmushi tare da riƙe hannun Mother ta ce "Innalillahi
ƙoshai aradu daɗi akwai burudi to? Wayyo Allah zanci ƙoshai na mure" dariya Mother
zatai ko takaici bata son duk wannan shirman a wajan Halisa..
"Zaki samu abin da yafi ƙosai ba, amma can idan kina shirme gidan yankan kai suke
kai mutum, ki zama a nutse, bayan haka yana son abincin gargajiya tuwo, dambu da
sauran su dai, ki tabbata kina wanka sau biyu zuwa uku a rana, idan ba haka ba Yaa
Sheikh kurarki zai yi daga gidan shi, kuma kishiyarki ta rabaki da mijinki har
abada" Idanun Halisa ya sauya kala jin abin da Mother ta ce. Bayani Mother taci
gaba dayi mata cike da ƙwarewa ta ɗora da faɗin.
"Kina jin alamun ya dawo, ko babu abin da zai miki kije wajan shi kice kanki ke
ciwo ko ya koya miki karatu, zan zuba miki kayan amfani masu kyau ki tabbatar kina
using dasu amfani kinji?"
"Zan yi ai, amma dai ba zata ƙwace mijina ba ko?" Mother ta haɗiye dryar data zo
mata ta ce "Akan me? Idan kina yin abin da nace bata isa ta ƙwace miji ba, amma
idan bakya yi uhm ko ganin shi kin dai na yi, yawwa sai gaisuwa kullum da safe kije
ki gaishe sa, da yamma haka da kuma daddare, akwai lokacin da yake ciwon kai bai
azabar zafi ganin shi har ɗauke yake ya zama kamar makaho, zan faɗa miki abin da za
ki yi idan ciwon ya tashi, yanzu maza jeki gama aikin ki za kuje a gyara miki
wannan gashin kan" Halisa ta miƙe tsaye kanta a ƙasa ta ce.
"Na gode" "is nothing jeki daughter" sai da taje bakin ƙofa ta juya a hankali ta
kalli Mother idanunta ya yi raurau da hawaye ta ce.
"To yaushe zan faɗawa ina da miji? kuma yaushe zan fara dama masa fura" a ranta
Mother ta ce "na shiga uku, wannan za ayi sirri da ita kam?" A file ta ce "zan faɗa
miki ranar jeki" ta juya ta fita tana ayyana cewa da gaske dai Balarabe mijinta ne.
Kai tsaye ɗakin Zahrah ta koma taci gaba da shirya mata kayan da zata tafi Madina
dasu, zuciyarta cike da tunanin maganganun da Mother ta faɗa mata. Ta sauke ajjiyar
zuciya a fili ta ce "Wallahi kyakkyawa da shi, Allah ya sa na zama kamar shi" ta
faɗa tana taɓa fuskarta sai kuma ta miƙe da sauri tana nufar inda mirror yake, a
hankali ta shiga ƙarewa kanta kallo, bata hango nata kyan zallar kyan da Rabbil
izzati ya yi wa Yaa Sheikh idanunta ke hangowa.
Tsaye tayi a bakin ƙofar da zata kaita parlourn Yaa Sheikh tun a nan kuma ta gane
Yaa Sheikh daban yake a gidan, tsarin shi da yadda yake tafiyar da rayuwar shi,
bata taɓa shakkar tsayawa gaban namiji ba, amma a yanzu tsoro da fargabar tsayawa
gaban Yaa Sheikh da yadda kaifin idanun shi ke tasiri a zuciyarta sun gama cika
Zahrah. "No Zahrah Aliyu mijinki ne, ki koyi zama da shi kafin ki fara juya rayuwar
shi tamkar waina a tanda, dole ragamar rayuwar shi ta dawo tafin hannunki" wata
zuciyar ta shiga gargaɗin haka, jikinta ta kalla tsaf duk da kasancewar ciki ne
jikinta amma ƙirjinta yana kwance ya manne da fata, ita kalar halittar ce ko kuma
garin yawan ta zubar aka gama lalata halittar da Ubangiji ya yi mata wacce kuma
iskancin kawai ta sani sam bata san tsaunin da zata hau tabi ba, zuwa tubalin da
zai gyara mata garkuwar jikinta.
Ta tura ƙofar a hankali ƙamshin air-con da wani air freshener sune suka daki
hancinta, shigar ta parlourn ya yi daidai da sautin karatun Yaa Sheikh dake ratsa
cikin wajan har ya kawowa kunnenta farmaki.
Yana zaune saman kujera ya ɗora farar ƙafarsa akan table idanunsa rufe a haka yake
motsa bakinsa yana karatun cikin baiwar da Ubangiji ya bashi ya sahale masa yin
karatun ba tare da harɗewar harshe ba..
Zahrah ta bi farar Jallabiyar dake jikinsa da kyau da kyau, zuwa kansa dake rufe
hirami hannunsa guda ɗaya riƙe da carbi yana ja.
Ta nemi wajan a kujerar dake kusa da shi ta zauna tana fari da idanu tare da juya
jiki amma ta kasa yi masa magana balle gaisuwa.
A jikinsa yaji ana kallon shi bambancin ƙamshin turaren da bai taɓa ji a gidan yasa
ya fahimci ko waye ba ɗan gidan bane.
Zahrah ta gyara murya ta ce. "My Excellency"
"Shhhh" Yaa Sheikh ya furta a ran shi gaba ɗaya murya ko a maza bai taɓa jin mai
amonta ba.
Ganin ya yi shiru ta ɗauka ko bai ji mai tace bane?.
"Daman nace bari nazo muga juna muyi hirar ku mintuna biyar ne kafin mu tafi
gidanmu" still shiru ya yi mata, ta miƙe tsaye cike da kwarkwasa ta ƙarasa har zuwa
inda yake tare da zama kan armchair ta saka hannu ta shafi fuskar shi kaɗan zuwa
dugun gemun shi ta ce.
"You're just quiet, but I know you hear what I'm saying" a wannan lokacin Yaa
Sheikh ya ɗauka gangar jikinsa zata ƙaryata zuciyarsa, amma sai yaga abin ya zama
diro, ya ƙara tabbatarwa lallai to da gaske bashi da cikakkiyar lafiya irin ta
cikakkun maza, mace ƴar 32 tazo har inda take suyi very close da juna amma ko
tsigar jikin shi bai ji ta motsa ba, balle ya yi zaton zai ji abin da Khalil ke
masa surutu akai.
Zahrah ta kai hannu zata ƙara jan gemun shi ya buɗe narkakkun idanunsa na mai kama
da mai jin barci. He didn't give her a full look, because looking at people is not
his style. Bai sake kallonta ba ya miƙe tsaye yana goya hannunsa a baya, ya nufi
bedroom ɗinsa, Zahrah ta ce "Amma dai ni matarka ce ka sani?" Ya tsaya cak ba tare
daya juya zuwa gare ta ba, kamar zai magana sai kuma ya fasa ya shige cikin bedroom
ɗin, Zahrah tabi bayan shi da kallo me hakan yake nufi? Ta ɗauka zuwanta gare shi
zai nuna wata buƙuwa ta miji ga matar shi sai kuma taga saɓanin haka.
Ta juya ta sauri Dr A'isha dake Main parlour tabi Zahrah da kallo wato halitta
kala-kala ce, ita bayan shekaru da zubin halittar jikinta har wani tumbi take dashi
kamar namiji?. A fili Dr A'isha ta ce "Allah ya kyauta" tana faɗin hakan ta miƙe
zuwa bedroom ɗin Mother itama a yau take son shigewa gidan mijinta.
Zahrah na shiga bedroom ɗinta ta saka ƙafa ta murje yatsun Halisa cikin faɗa ta ce
"ke kam wacce jakar yarinya ce? kina ganin mutum ba zaki matsa daga hanya ba?"
Halisa da idanunta yayi jaa sbd zafin da yatsun suke mata, ta kalli Zahrah ta ce
"Kiyi haƙuri" ta saka hannu ta ɗauke Halisa da mari ta ce "haƙurin uwarki? Ni dai
na shiga ban ɗauka fulani mahaukatan gaske bane sai yanzu" gigicewar da Halisa tayi
yasa ko gabanta bata iya gani, ba a taɓa yi mata mari da tafkeken hannu kamar na
maza irin wannan ba. Ruɗewar da tayi yasa ta nufi wata ƙofa a tunaninta part ɗin su
Maimoon ne, tana fita taci karo da mutum a hanyar zuwa swimming pool. El-bashir
yaja baya da sauri yana kallon farar kyakkyawar yarinyar data fito hannunta a fuska
tana shassheƙar kuka, ya taɓe baki yana ƙoƙarin shigewa Halisa tayi saurin kama
hannunsa cikin matsanancin kuka ta ce. "Hamma fuskata zata cire wayyo Dadata
fuskata ka taimaka mini" sai murza fuskar take da hannunta guda ɗaya, ɗaya kuma ta
riƙe hannun El-bashir da shi. Hannunsa ya sanya zuwa hannunta dake fuskarta cikin
ƙasa da murya ya ce "Sorry" ya faɗi hakan yana ɗauke hannunta.
Cikin daƙiƙo ya nemi ji da ganinsa ya rasa, tunaninsa ya tsaya cak, ya zama kamar
wani stateu yana ganin tarin kamanni amma bai taɓa cin karo da zallar kama irin ta
yau ba. Hannunsa na rawa ya kama fuskar Halisa da kyau yana ƙare wa hukuncin Rabbil
izzati ido, ita dai kuka take sosai ba ƙaramin gigita marin ya yi ba. El-bashir ya
sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da haɗiye mamakinsa, ko ita ce
yarinyar da Khalil ke bashi labari?.
Ya shiga goge mata hawayen fuska tare da faɗin "ke dawa? Wace ke? Mene sunanki?" Ya
jera mata tambayoyin.
Halisa ta marairaice fuska tare da shagwaɓewa ta zama wata narkakkiyya hannunta
cikin baki alamar shagwaɓarta a zahirance take bata ɓoyewa. "Uhm magana nake" tai
saurin ɗaga kanta zuwa fuskar shi, baki da hanci ta saka ta kasa cewa komai El-
bashir ya ƙifta mata idanu tare da ware su ya ce "Keee.
"Wallahi kama muke, kai ma kasanni ya naga fuskarmu iya ɗaya?" Ta ƙare maganar tana
ƙoƙarin taɓa fuskar shi domin tabbatarwa. El-bashir ya haɗe fuska ya ce "Bani amsa?
Wace ke?" Ta tura baki gaba ta ce "Sunana Halisa Danejo Rome, kuma ni matar
Balarabe ce" El-bashir ya ware idanu ya ce "What are you married? Waye Balarabe?"
Ta ce "Ace kada na faɗawa kowa sai lokaci ya yi amma dai ni zan dinga yiwa Matar
Yaa Sheikh aiki, kuma ance jibi zamu tafi ko'ina ne, haka.....,"
"Heyyy will you shut up your mouth caaaaa haba" ta tura baki gaba fuska duk a
shagwaɓe taƙi cewa komai. Ya gyara tsaiwa ya ce "Oh Halisa, dake Yaa Sheikh zai
tafi ko?" Tayi saurin kallon shi ta ce "Eh" ya ce "Ok good, daman shi ya aike ni
yanzu, kuma ke ya ce na bawa aikin domin ya yarda da hankalinki" tamkar wacce bata
yarda da maganar El-bashir ba haka take kallon shi, wanne aike? daman yana sane da
ita kenan yana son ta shi ma?..
"Riƙe wannan, ya ce ki ɓoye wajanki har sai kunje Madina, maganin shi ne, zaki zuba
masa a cikin shayi ko abinci, kada ki bar kowa yasan da abin a wajanki, idan ba
haka ba zai kureki daga gidan shi kinji?" Ta ɗaga kai ta ce "Amma bari na bawa
Mother ajjiya ko?" Ta faɗa zata juya ya yi saurin riƙe hannunta ya ce..
"Ai har Mother ba a so tasan da maganin a wajanki, ki zama mace mai sirri ki
tabbatar kin zuba masa, idan ba haka mutuwa zai gaba ɗaya" ta shiga girgiza kai
tsoro da fargabar abin da El-bashir ɗin ke faɗa suka firgitar da Halisa ta ce
"Wallahi ba zai mutu ba, ba zan barshi ya mutu ba, ni da kai na zan zuba masa
maganin" wani irin kyakkyawan murmushi mara sauti El-bashir ya yi kafin ya ce "Good
girl" ganin ya yi gaba ta ce.
"Kai ya sunanka to?" "Ki ce El" ya faɗa a taƙaice tayi saurin faɗi "Ban iya faɗa
ba, tunda muna kama ɗaya zan dinga cewa Hamma ka yarda?" Ya tsaya tare da juyawa
wani abu nayi masa yawo akan abubuwa da yawa, kalmar kamannin data faɗa suka ƙara
dagula masa lissafi. Ya jinjina mata kai tare sakar mata murmushi.
Halisa bata da riƙo lokaci guda ta mance marin da Zahrah tayi mata.
Cikin sauri ta ɓoye maganin da El-bashir ya bata tare da juyawa tabar wajan.
Barinta wajan ya sanya Yaa Sheikh sauke numfashi tare da zame idanun shi daga
saitin wajan da Halisa da El-bashir suka tsaya, yana mai ɗan girgiza kai tare da ya
motsa fuska.
Father ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Kaje ka duba visa ɗin Zahrah da Yarinyar da zatai
mata aikin" Yaa Sheikh ya jinjina kai alamar "to" tare da miƙewa sai da ya je bakin
ƙofa Father ya ce "Ka shiga part ɗin nata, da kanka ba aike ba kace ta shirya kuje
tare, matarka ce saɓa mata tamkar zaɓa mini ne, kai ne mai auren amma ni ne mai
zartar da hukunci ko da wasa ka sake Zahrah ta kawo ƙararka za kaga yarda za mu yi
dakai Aliyu, kaji tsoran Allah kai Malami ne kasan hakƙin aure da sauke nauyin miji
ga mata, kada ka yarda saboda baka son ta kace zaka tauye hakƙinta wallahi wallahi
Allah Aliyu akan aurenka da Zahrah sai nayi maka baki" Yaa Sheikh ya juya da sauri
ya kalli Father kalmar shi ta ƙarshe ta daki zuciyar Yaa Sheikh, kansa a ƙasa ya
nufi wajan Father yana zuwa ya zube a wajan ƙafafuwan Father, cikin ƙasa da murya
mai tarin nutsuwa da Ilham yana mai ɓoye abin da yake ransa a kame ya ce.
"Kada ka aibata ni Abbi, zan riƙeta, ka saka albarka a kai na a karo na farko na
rayuwata Father" Father ya kalli Yaa Sheikh kafin ya ce "Kaje Allah ya yi maka
Albarka" Yaa Sheikh ya kifa kansa a ƙafar Father farin ciki ko baƙin ciki zai ji?
Yau Father ya saka masa albarka dalilin Zahrah?.
"Ka tashi kaje nace, kuɗi ne kama fini shi me zan maka? Ko akwai abin da ka ke
buƙata?" Yaa Sheikh ya yi shiru can kuma ya miƙe tsaye tare da yin waje. A hankali
ya haɗu da Maimoon da Halisa shi sam ba zai ce yaga Halisa ba domin direct idanunsa
ya sauka akan Maimoon ɗin.
Part ɗin Zahrah ya nufa lokaci wata farar riga ce a jikinta iya gwiwa waya riƙe a
hannunta ta ce "No Deen ka bari muyi 1week a Madina sai ka zo ɗin? I will arrange a
day when we can meet, I don't want to be recognized....," Ƙamshin Roja da hancinta
ya shaƙa yasa tayi saurin ajjiye wayar tana duban door way, idanunta ya sauka akan
Yaa Sheikh dake tsaye bakin ƙofar yaƙi shigowa ciki. Zahrah duk ga ruɗe bata
tsammaci ganin shi a yanzu ba, ta sakko tana yin murmushi tare da girgiza jiki ta
ƙarasu tana faɗin "My Excellency" Yaa Sheikh ya duba ta da kyau, har zai larabci ya
tuna ba lallai tana ji ba, shi kuma he's not interested akan english.
"Ki saman waje, mota" ya faɗa a taƙaice cikin rarrabe murya.
Bai aune ba yaji Zahrah ta shige jikinsa tare da rungome shi. Bakinsa na rawa cikin
rashin ya ce "Asstagafirullah, Allah na tuba" ya faɗa yana zame jikinsa tare da
barin part ɗin da sauri.
Yana zaune a bayan mota idanun shi rufe yana ta Asstagafirullah akan rungumar da
zara tai masa, ba wani sauyi a jikinsa amma that is forbidden.
Umar-khan ya ɓoyewa Zahrah bayan mota har zata shiga sai kuma ta tsaya ganin kamar
maca ce a gaban motar, ta tsaya tana faɗin "Umar-khan wace wannan a gaban motar
mijina?" Umar-khan ya kalli Halisa wacce take sanye da wata Marron ɗin turkish
Abaya wacce Mother ta bata, Maimoon kuma tai mata rolling vail ɗin abaya a
fuskarta, ƙaramar round face ta fito sosai farinta ya ƙara bayyana, gashin idanun
nan lub zara-zara dasu idan ba magana tai ba, ba zaka taɓa cewa ƴat fillon Rugar
Rome bace, ta kame kanta sosai bisa gargaɗin Mother. Umar-khan ya danne dariyar
dake cin sa ya ce "Motar mijinku dai" "me kace?" Cewar Zahrah ya ce "cewa nayi baki
gane wace ba?" Ta girgiza ta ce "Idan na gane wace mene amfanin tambayar?" Yaa
Sheikh dai duk abin da suke cewa yana jinsu bai magana ba. Umar-khan ya ce "Ikon
Allah, Ƴar fillo ce fa? Mai aikinki ina nufin Halisa ce a gaban motar garkuwarta"
wani irin bugawa ƙirjin Zahrah tayi ta ƙara leƙa motar Halisa ta sakar mata wani
cute smile ta ce "Laa Anti ni ce fa, mai aikin ki Halisa Danejo Rome" wani jiri ya
ɗebi Zahrah tayi saurin riƙe motar a cikin ranta ta ce "Da sake wallahi ba zai yiwu
ba....

_IDAN BA KE it's paid book... ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity
bank shaidar biya 08119237616. If you read for free😂 _
[1/3, 4:48 PM] Abk: Umar-khan ya katse mata tunani da faɗin "Ki shiga muje" Zahrah
ta ɗan basar tare da faɗin "Dake ban kula da kyau bane, amma ita me za ta je yi?"
Ta tambaya idanunta akan Halisa wacce wayar Umar-khan ke hannunta sai latsa ko'ina
take ba tare data san ta kanta ba. Umar-khan ya ce "Ayya ko kin manta Glasses ɗin
naki ne, ita za ai mata visa ne" baƙin cikin maganar da umar-khan ya yarfa mata ya
sanya ta kasa cewa komai ta shiga cikin motar tana sauke numfashi sbd ƙamshin Roja
data shaƙa ga daddaɗan freshener dake tashi a motar.
Tana shiga Umar-khan shi ma ya shiga a hankali ya yi wa motar key sbd Yaa Sheikh
baya son gudu da yawa, gatekeeper ya buɗe gate suka nufi wajan da za ai photo a
haɗa musu visa. Bayan sun yi nisa akan titi Umar-khan ya juya ya kalli Halisa ya ce
"Madam idan kika latata mini waya mijinki zai biya" Zahrah ta ɗago kai tare da
duban saitin Umar-khan, bata fahimcin zancen ba domin ita ta ɗauka waya yake.
Halisa ta buɗe fararen daidaiton haƙoranta masu kyau ta ce "To ai baya da kuɗi"
"Injiwa?" Umar-khan ya tambaya idanunsa akan titi, ta ɗan turo baki tare da watsa
hannu alamar bata sani ba, ya girgiza kai ya ce "Shi ke da kuɗi, hakan ne ma ya sa
ban ƙwace wayata ba, albarkacin ki sai a siya mini iphone 13max pro Matar Malam na
makka da madina" taja lulu eye's ɗinta lumshe wanda hakan ya zama jiki a gareta,
magana zarar bunu cikin rashin sani da kuma sabo da surutu yasa Halisa faɗin.
"Kai ma kasan ayi mini aure ne? Ko na faɗa maka yanzu" Umar-khan ya tuntsire da
dariya sosai yana faɗin "Ina zan sani ƴar fillo? Kuma......,"

Yaa Sheikh da tun ɗazo idanunsa yake a rufe ya buɗe su a hankali kai tsaye ganinsa
ya sauka akan ƙaramin bakinta wanda yake motsawa a hankali ta cikin madubin motar.
Yaa Sheikh ya ɗauke idanunsa da sauri yana mai ɗan dafe kai cikin nutsuwa da kamewa
wacce ta zauna a jikinsa ya buɗe baki da ƙyar ya ce.
"Ka kula, Umar-khan"
"Ok Yaa Lee" cewar Umar-khan with so much respect. Zahrah ta matsa kaɗan kusa da
Yaa Sheikh tare da ɗora hannunta a saman na shi. "Asstagafirullah, Allah na tuba"
ya furta cikin ranshi a zahiri bai motsa ba, sai ma rufe idanunsa da ya yi kamar
mai barci. Zahrah taja gemunsa wanda yake matuƙar ɗaukan hankalinta ta ce "I love
you My Excellency" baki ta miƙa zata sumbaci gefen fuskar shi, tari ya turnuƙe
Halisa a kiɗime Umar-khan ya ƙara slow da driving ɗin ya ce.
"Sannu mene ya sameki, are you sick? Baki da lafiya ne?" Ganin tarin ya kasa
tsayawa yasa Umar-khan faɗin "Yaa Sheikh ko zaka taimaka mata da ruwan wajanka,
babu raguwar a motar" bai ɗago ba, ba kuma zakai tunanin da shi ake maganar ba..
"Sannu, sannu" ya ƙara jerawa Halisa cike da tausayi. Yana driving ya kalli Yaa
Sheikh ta madubi da kuma Zahrah wacce takaicin Halisa ya cika ta duk ta hana su
sakat tasu a lokaci na farko ta bawa Yaa Sheikh ɗin kyakkyawar sumbata wacce zata
ruguza shi tun yanzu, tasan ba lallai ya iya riƙe kansa ba, dole ya zo gareta.
Umar ya ɗauke idanunsa yana faɗin "Yaa Sheikh Please ta wahala da yawa" ya ajjiye
carbin hannunsa tare da ɗago kansa kamar mai nazari ya shiga kallon Umar-khan, not
looking at her place ya kame kansa murya kamar anyi forcing nasa na magana ya ce..
"Stop the car" Yasan idan har Yaa Sheikh ya buɗe baki ya yi magana to yana nufin
abin da ya faɗa ne har cikin ran shi a hankali ya yi parking motar zuwa gefen titi.
Zahrah ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Daman bai kamata mu shiga mota ɗaya dasu ba, ga
wannan shegiyar yarinyar ƴar fillo, kawai su nemi abin hawa i can drive us kaji My
Excellency" ya ɗan kalleta kaɗan ta wani kashe masa idanu tana shirin kama hannun
shi ya fita daga cikin motar, yana fitowa ya shiga takawa a gefen titin hannunsa
goye a bayansa, ganin yadda ya tsaya waje guda kansa a ƙasa yada Umar-khan fita
yana tunanin ko lafiya? Ya nufi wajan shi tare da faɗin "Yaa Lee lafiya?" Ya ɗago
kai ya kalli Umar-khan, mamaki ya kama Umar ganin yadda goshin Yaa Sheikh yake
fitar da zufa ya jiƙe sosai da gumi.
Bai magana ba ya miƙa hannunsa tare da amsar key car ɗin hannun Umar-khan, da hannu
ya nunawa Umar-khan bayan motar alamar ya shiga ciki ya zauna, mamaki ya kashe Umar
a tsaye yau Yaa Sheikh zai yi driving ɗin mutane a mota bana shi ɗaya ba? Me hakan
yake nufi.
Zahrah dake bayan mota tana jiran ace Halisa ta fita ita kuma ta dawo gaba ita da
mijinta su tafi iya su biyu sai gani tayi Umar-khan ya buɗe bayan motar ya shigo,
mamakin sauyin al'amarin cikin ƙaramin lokaci ya hanata magana.
Yaa Sheikh ya sanya tattausan farin hannunsa mai ɗauke da suma lub ya buɗe murfin
gaban motar, ƙafarsa ta hannun dama ya fara shigarwa kana ya shiga ya zauna baki
ɗaya.
"Ban gane wani ƙaton namijin ya zauna dani ba, bayan ina matarka?" Babu wanda ya
bata amsa sai ji tayi ya yi wa motar key. Murmushi kawai Umar ya yi yana ayyana
wani abu a ran shi..
Yaa Sheikh ya yi tunanin zata cika shi da surutu kamar yadda ta cika Umar-khan da
hayaniya mara tushe, amma sai yaga saɓanin haka bawai kallonta ya yi ba, ya fahimci
hakanne ta madubin motar.
Kanta a ƙasa idanunta ya yi masifar jaaa jikinta na ɗan rawa a hankali, saukar
sautin ƙira'ar daya cika motar har ya kawo zuwa kunnenta yasa ta sauke numfashi mai
ƙarfi jikinta ya saki kafin su ƙarasa barci ya ɗauke ta sai ajjiyar zuciya take
saukewa.
Bayan

Please Login or Register in order to submit comment