You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ba ta juya zuwa ɓangarenta, Umar-khan kuma ya shiga cikin part
ɗin Yaa Sheikh amma ya tsaya iya parlour.
El-bashir ya saki murmushi yana sauke numfashi gabaɗaya conversation ɗin Ummul da
Umar-khan a kunnensa. Idan har rashin Halisa zai iya ajalin Yaa Sheikh me ya sa
yake wahalar da kansa, idan ya raba Halisa da duniyar ba shikenan ba?.
"Yaa Sheikh ka gama yawo" ya furta a fili. Juyawar da zai suka haɗa idanu da Zahrah
wacce ta fito sanye da wasu shegun kaya, suka kalli juna.
Ganin ta nemi waje ta zauna yasa El-bashir ya sauke ɓoyayyiyar Ajjiya, sai da
hantar cikin El-bashir ta kaɗa saboda tsananin tsoro daya shiga. Tunaninsa ya tsaya
na wani lokaci domin zaton shi Zahrah taji abin daya faɗa sai yaga saɓanin haka.
Shima ya zauna idanunsa akan t.v kamar daga sama yaji ta ce.
"Kana da alaƙa da Halisa ne?"
"Me ya sa zan samu alaƙa da ƴar uwarki?" Zahrah tai murmushi ta ce "Ba ƴar uwata
bace, kamanninku sun ɓaci" ya taɓe baki ba tare daya damu da tace ba ƴar-uwarta ba
ce.
Ta miƙe tare da nufar wajan Training ko cikinta zai sace daga kumburin da ya yi
mata, ita kumburin har tsoro ya bata.
Mai martaba ya kalli Yaa Sheikh daya miƙe tsaye sai kuma ya juya ya kalli Abba
Hakimi dake kan screen suna vedio call ya ce "Ina ganin komai ya yi daidai" Abba
Hakimi ya rufe Kur'anin gabansa shi kaɗai yake iya daidaita hargitsin na Yaa Sheikh
kafin ya ce.
"Ina tunanin lokacin da Aliyu zai dawo kusa dani har abada ya yi, banga me yake a
Madina ba, shi ba uwa ba, shi ba Uba ba balle ƴan uwa a can ɗin ba, na rasa me ya
liƙewa a can ɗin" Mai martaba ya ce. "Abi komai a sannu, komai zai shige" Sallama
sukai Mai martaba ganin babu Yaa Sheikh a bedroom ɗin ya nufi hanyar fita.
A hankali take buɗe idanunta wanda ya yi mata nauyi sosai tare da kallon inda take
wani ƙaramin ɗaki ne amma mai kyau da tsari ta yunƙura kaɗan tana jin kanta na
sarawa.
"Kin farka matata?" Tunaninta ya tsaya tunda take Abbanta bai taɓa cewa matata ba,
kenan ya yarda yanzu ita matar shi ce. Ta juya hannunta dafe da kanta sukai idanu
huɗu, yana tsaye a cikin kyakkyawar shigar shi kamar kullum sai dai a wannan karan
Jallabiyar duka ta rufe masa ƙafa ta buɗe baki da ƙyar ta ce.
"Abba, ina ne nan kuma?" Prince Bilal wanda ya yi suffar Yaa Sheikh sak ya ƙara su
inda take yana kama hannunta ya ce.
"Sabon gida mukai Danejo matata, yadda zan samu damar kasancewa dake muyi soyayya
sosai" ta kalle shi ya akai yau Abban nata yake sakin zance ba dadin ita yau ba
darasi sai soyayya ta ce.
"Zanyi wanka Abba, jinin ya tsaya" Bilal ya ce "Jini? Shikenan an gama dani" bata
gane zancan nasa ba, ta nufi bathroom tai wanka duk abin da Ummul ta faɗa tayi ta
fito ɗaure da towel Bilal ya dinga kallonta ya kama hannunta zai rungometa yaji
kamar an buga masa guduma a kai ya saketa da sauri yana faɗin.
"Da akwai wani abu a jikin ki, maza cire" Halisa ta dinga duba jikinta amma ba taga
komai ba ta ce "Abba ba komai, wai Abbana meya sameka?" Ta faɗa tana shigewa
jikinsa Bilal ta birkice ko ya ya Halisa ta taɓa shi masifa ya keji.
Ya cireta yana cewa "Lafiya nake shirya kiga" tai murmushi tana cewa "Ko wanka ne
baka son kayi ne?" Ya yi mata shiru tare da ɗauke kai domin ya fara riƙiɗewa kamar
Aljani.
Ta shirya cikin kayan daya bata tai sallah duk a ɗakin. Dare nayi ya bata abinci
taci kaɗan kamar wacce tasan meke faruwa sai bata ƙara zuwa inda yake ba, Bilal
kuma ya wanzu yana bin jikinta da kallo ko zai gano abin da yake masa shamaki da
ita.
Cikin dare Yaa Sheikh ya kasa barci duk inda yake tunanin zai ga matar Malam babu
ita. Wajan uku na dare ya fito direct ɓangaren Ummul ya nufa kamar tasan zai zo
ƙofar a buɗe take, tana zaune saman ladduma taji ƙamshin Roja ta kallesa taga ya
kalleta shima ta ɗauka zai je saman kujera sai taga kai tsaye ya dawo kusa da ita
ya zauna, bai ce komai ba ya ɗora kansa a cinyarta ya dinga sauke ajjiyar zuciya.
Abu kamar wasa har ana igobe ɗaukan azumi babu Halisa, babu wanda yasan halin da
ake ciki na rigimar Yaa Sheikh sai Ummul, Zahrah ko a jikinta. Da sassafe Yaa
Sheikh ya fita Zahrah kuma ta shiga ɗakin Ummul tana zuwa ta ce "Ki faɗa mini abin
da yake faruwa da mijina da baya son raɓar inda nake" Ummul tai shiru Zahrah ta ce
"Wallahi munafuka ce ke kin san komai ki faɗa mini abin da zan yi mijina ya raɓeni"
Ummul tai murmushi ta ce "Tausayi ki ke bani, naga har yanzu kin kasa fahimtar waye
Aliyu kin kasa gane cewa shi ba cikakken namiji bane, shiyasa aka auren haɗi
tsakanin ke da Aliyu" gaban Zahrah ya faɗi ta ce "Kina nufin Yaa Sheikh bashi da
lafiya?" Ummul ta ce "Ba a faɗa miki bane daman? Aliyu ai ba zai taɓa iya tarayya
da mace ba, likitoci sun tabbatar da haka, zaman ibada zaki da kulawa da shi"
Zahrah ta ƙunduma wani zagi tare da yin waje wayarta ta ɗauka ta shiga kiran number
Father ringing ɗin farko aka ɗauka Father ya ce.
"My daughter ya ki ke?" Cikin rashin ladabi Zahrah ta ce "Ban san ya nake ba, ashe
kasan cewa ɗanka Aliyu nakashasshe ne bashi da lafiyar tarayya da mace shine kasa
mukai aure?....

Paid book
500
08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: Ta cikin wayar Father ya ce "Kika ce me? Na kasa fahimtar zubin
maganar taki" Zahrah ta ce "An shaida mini Yaa Sheikh bashi da cikakkiyar lafiyar
zama da mace,shi ya sa tunda akai auren bamu taɓa haɗa shimfiɗa ba" Father ya yi
sai yaushe Yaa Sheikh ya samu larura? Ko hakan yasa bai damu da yin aure ba tsayin
shekaru?. Zahrah ta katse tunaninsa da faɗin.
"Kasan ɗanka lusari ka aura mini shi? To idan bashi da lafiya ni ina da ita, kuma
ba zan jure zama haka ba, inma ya samu mafita ko ya sakeni" mmkin Zahrah ya cika
zuciyar Father shin daman haka take babu manner of speech? Ko yanzu ta sauya hali?
Kafin ya yi magana Zahrah ta kashe wayar ta shiga safa da marwa tunaninta ya tsaya
baki ɗaya. Cikin sauri ta kira Deen tai ta ringing kafin ya ɗauka rai ɓace ta ce.
"Ai ta kira kamar baka kusa?" Ya gyara zama a ina yake zaune ya ce.
"Nasan ta tsuniyar gizo bata shige ta ƙoƙi, Yaa Sheikh.. Yaa Sheikh.. Halisa ƴar
fillo haka dai, something new?" Ta ce
"Babbar matsala, Yaa Sheikh bashi da lafiyar tarayya da mace shi ya sa yaƙi bani da
ta haɗa shimfiɗa da shi" Deen ya yi shiru for some minutes kafin ya ce.
"Just go to the point, ban fahimta ba"
Ta ce "I mean by words, target naka shi ne maƙalawa Yaa Sheikh cikin jikina, ciki
kuma ya zube, mu ɗauka zai saurareni daya sha maganin sai muka ga saɓanin haka,mene
next what's your plan?" Kamar ya shiga tunaninta taji ya ce. "Ki bari zuwa bayan
Ramadan, I'll think about it" badan ta so ba ta ce "Ok" daga ta kira Surry suka
tattauna sai kuma ta kira Babarta.
Halisa ta saki murmushi idanunta akan Bilal wanda zaton ta Yaa Sheikh ne ta ce.
"Abba yau ba darasi ne?" Bilal ya ƙara ɓoye kofaton ƙafarsa yana sakin murmushi ya
ce.
"Akwai mana, so nake kiyi barci sai abin ya fi" ta kama gemunsa sosai tana murɗewa
kamar yadda ta saba ta ce.
"Shikenan, amma ni ai ina so ko?" Gabaɗaya dauriya yake ya yi tunani da bincike
amma ya kasa fahimtar wanne kalar ƙulli Yaa Sheikh ya yi wa Halisa da har akai masa
hijabi da jikinta.
Ta riƙe shi ta ce "Yau nayi mafarki, wai kana ta kuka Abbana,bana son ganin kukan
ka kaji?" Bilal ya faki Idanun Halisa ya wangale asalin tafkeken bakinsa kafin ya
dawo daidai ya ce.
"Idan baki son nai kuka kiyi mini al'ƙawari" ta juya idanunta a cikin nasa tana
sauraran abin da zai ce.
"Kiyi al'ƙawarin bayan ni ba zaki kula kowa ba, kiyi mini al'ƙawarin ba zaki taɓa
bawa wani namiji damar shiga fadar daba tashi ba" tayi saurin cewa
"Fada kuma, ina ne fada?" Bilal ya kalleta wato dai har kullum ba zata sauya ba? Ya
ce "Ina nufin kada ki bari wani namijin ya kusance ki, ni nake da wannan ikon ni
zaki haifawa yara dan ma anyi mini asarar cikina amma zan baki wani cikin"
Ta hangame baki sosai ta ce "Tab, shi cikin to ta ina zan same shi?" Ya kalli
gabaɗaya ɗakin da suke ciki ya ce "Zan faɗa miki, amma kafin nan akwai wanda yake
son rabani dake, yake son yaga ya wahalar da zuciyoyinmu, kada ki manta nine na
kawo rugarku lokacin da kika ɓata, kuma nine na taimaki lokacin da aka haɗaki gasa
da maciji, wani zai zo mai kama dani zai so ya rabamu kada ki bashi damar haka, ni
kalli hannuna akwai zane, koda wani yazo idan baki yarda ba ki fara duba hannunsa
idan babu wannan zanan to bani bane"
Tai shiru tana sauraran Bilal ganin ta kasa cewa komai ya riƙe hannunta ya ce "Kada
ki barni, kada ki bari a rabamu" idanunta ya cika da hawaye ta kasa magana sai
girgiza kai take tana shassheƙa kamar zatai kuka. Bilal ya riƙo fuskarta ya ce "Ko
baki son Abbanki Danejo kizo muje duniyata, na miki al'ƙawarin zamanki sarauniyar
duniyar" ta girgiza kai ta ce "Ina son ka Abba, ka daina cewa za a rabamu tsoro
nake ji, ina son ka kada ka barni?" Ta faɗa jikin Bilal tana ƙanƙame shi..
Ya runtse idanunsa azaba yake ji kamar ana huda masa jiki. Ya dinga busa mata isa a
fuska wanda yasa cikin ƙaramin lokaci barci ya ɗauke ta barcin da aka sanyata yi na
dole.
Cikin barci taji kamar tana mafarki ta shiga motsa ƙafafuwanta wanda ake ƙara wara
mata su cikin hukumcin Ubangiji a mafarki ta dinga ambaton sunan Allah. Amma
al'amarin yafi ko wanne mafarkinta tsamari, sai nishi nake jikinta na jijjiga.
A hankali yake tafiya cikin farar jallabiya mai kyau ya ɗora Alkyabba akai
rawaninsa ya fito sosai ya bayyana a salin Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu babban
malamin da ƙasoshi da dama suke alfahari da shi. Ya ɗan saurara da tafiya yana
sauraran abin da Sheikh Hafix yake cewa.
"Naga Dutsen Jabal an-Nour" Yaa Sheikh ya jinjina kai domin hankalinsa baya wajan,
bai ma ɗauka da ya zo Makkah ɗin ba zai daɗe haka ba. Yana ƙoƙarin komawa Madina
Sarkin Makka ɗin ya ɓukaci a tattaki domin tabbatar da komai Lafiya yake kafin a
ɗauki azumi a daren yau.
_Jabal an-Nour dutse ne da ke kusa da Makka a yankin Hejaz na kasar Saudiyya.
Dutsen ya kunshi kogon Hira'a, wanda ke da mahimmaci ga musulmi a duk fadin duniya,
kamar yadda aka ce annabin Musulunci_

"Ina tunanin ai ba sai ka koma Madina ba, waye zai fara jan jam'i, an kammala
shirya maka gidan daka buƙata" Sarkin Makka ya kalli Yaa Sheikh dan ya lura baya
tare da su ya ce.
"Ina fatan za a sakani cikin addu'a wacce ta kasance mai muhimmanci, Masallacin
harami ya ɗauki niyya da dubban mutanan da suka ziyarci aikin hajji daga ƙasashe
daban-daban, da kuma na garin Makka da Madinah" Yaa Sheikh ya sauke numfashi ya ce.
"Allah ya kaimu, ya haɗamu da ladan dake cikin wannan wata" duk manyan malaman da
Sarkin Makka suka amsa da _“Amin”_ kafin Sheikh Hafix ya duba lokaci ya ce.
"Wa'adin duba wata a sama ya yi, daman ma'aikata sun ƙara sa filin duba wajan da
abin hange"
_Masallacin Harami da ke Birnin Makka na kasar Saudiyya shi ne masallaci mafi girma
da tsarki a ban-ƙasa,Shi ne masallacin da ake nunka ladan sallah sau dubu dari fiye
da sallah a sauran masallatai.A cikinsa ne Dakin Ka'aba yake, wanda shi ne ginin
farko a duniya kamar yadda musulunci ya nuna, kuma shi ne Al-Kiblar da Musulmai ke
kallo a duk lokacin da za su yi sallah daga ko ina a duniya.
Girman Masallacin Harami na Makka ya kai murabba'in mita 356,800, kuma yana iya
daukar kusan mutum 800,000 masu ibada a lokacin aikin hajji,
A wannan tsarkakakken masallaci akwai Ka'abatul Musharrafa, wato Dakin Allah Mai
Tsarki, inda nan ce alkiblar da duk musulman duniya ke fuskanta idan suna salla.
Tsawon Ka'aba ya kai mita 12, fadinta kuma mita 10 sannan tudunta ya kai mita 15.
An lullube ta da Bakin Yadi da ake kira Kiswah, wanda yake dauke da rubutun Kur'ani
mai girma da ruwan gwal. Duk shekara ake sauya Kiswah.
Kofar shiga Dakin Ka'aba tana daga bangon arewa maso gabashin dakin.
A jikin Ka'aba akwai Bakin Dutse, wato Hajrul Aswad inda daga nan ne ake fara
dawafi, kuma ana so mai dawafi ya sumbanci dutsen, in ya samu dama.
In kuma bai samu damar sunbata ba, sai ya taba da hannu, ko kuma ma ya nuna shi da
hannu in bai samu damar tabawar ba.Multazam ma wani bangare ne na Ka'aba da masu
ibadah kan tsaya don yin addu'a. Yana tsakanin dutsen Hajarun Aswada da kofar
Ka'aba.
Ana so idan mutum ya samu dama ya kara kirjinsa da cikinsa da hannayensa a wajen.
Yana daga wuraren amsa addu'a. Fadinsa ya kai mita biyu.
Akwai kuma Makamu Ibrahim inda a bayansa ne ake so a yi sallah raka'a biyu bayan
kammala dawafi. A nan ne aka ajiye dutsen da ke dauke da alamar sawun Annabi
Ibrahim AS wanda ya taka lokacin da ya ke ginin Ka'aba.
Hijri Isma'il wanda ake kuma kira Hateem wani bango ne a jikin Ka'aba. An zagaye
bangaren kadan, kuma yana daga bangaren arewa maso yammacin Ka'aba. Wajen shi ma
yana cikin Ka'abah.
Kuraishawa ne suka fitar da shi daga Ka'aba lokacin da suka sake ginin ɗakin,Dutsen
Safa da Marwa kamar yadda Allah ya fada a Alkur'ani mai girma "Lallai ne Safa da
Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi aikin Hajji a dakin ko kuwa
ya yi Umra, to, babu laifi a kansa ya yi dawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya kara yin
wani aikin alheri to, lallai ne wadannan su ne shiryayyu." Surah Bakara aya ta 158.
Dutsen Safa inda daga nan ake fara Sa'ayi yana da nisan kilomita 0.80 daga Dakin
Ka'aba. Yayin da Dutsen Marwah yake da nisan mita 100 daga Dakin Ka'abah.
Nisan da ke tsakanin duwatsun biyu kuwa mita 450 ne.Rijiyar Zam-zam
Rijiyar Zam-zam na daga ɓangaren gabas da Ka'aba da nisan mita 20.
Wannan rijiya na samar da isasshhn ruwan da bai taba ƙafewa ba tun lokacin da
Ubangiji Subhanahu Wa Ta'ala ya samar da ita a zamanin Annabi Ibrahim AS, kamar
yadda malaman tarihi suka ruwaito.
Kofofin masallacin
Akwai kofoi biyar waɗanda su ne manya-manya a Masallacin Harami da suke hada da:
Kofar Sarki Abdulaziz - Bab Abdulaziz
Kofar Fateh - Bab Fateh
Kofar Safa - Bab Safa
Kofar Umra - Bab Umra
Kofar Sarki Fahad - Bab Fahad".

Sheikh Hafix ya saki kyakkyawan murmushi ganin yadda aka ƙara ƙawata komai a Makka
ya ce "A wanann shekarar naga dubban mutane sun ƙaro akan adadin mutanan da muke
samun ziyarar tasu" Sarkin Makka ya ce "Nima nai mamaki ƙwarai, Ubangiji ya ƙara
ɗaukaka musulunci da Musulmai"
A taushashe Yaa Sheikh ya ce "Amin Ya Allah" tsayawa ya yi daga tafiyar ba suyi
masa magana ba sanin cewa yana da tsari, a hankali yake hawa saman Dutsen Jabal an-
Nour tunda yaji kamar ana jansa wajan yasan akwai matsala, yana zuwa idanunsa ya
sauka akanta tana kwance a saman dutsen wasu ƙananun kaya ne a jikinta farar
cinyarta sai sheƙi take gashinta ya bazu wato nan aka cillota? Walking slowly ya
nufeta kafin ya ƙarasa inda take yaga an ɗagata sama ba tare daya ga mutum ba.
Wani lallausan murmushi ya saɓucewa Yaa Sheikh ya ce.
"Ba hayaniya zaman, domin a waje mai tsarki nake" Bilal dake tsaye ba tare daya
bayyana kansa ba ya ce "Ba kai ba matata, ka fita hanyar matata" Yaa Sheikh ya
kalli gabas, yamma, kudu, arewa yaga akwai ɗaiɗaikun mutane wanda suka zo neman
tabarraki a Jabal an-Nour ɗin.
"Sauketa" ya faɗa babu alamar wasa a fuskarsa Bilal jikinsa ya fara rawa ya ce
"Kada kayi mini haka, na fika sonta" Yaa Sheikh ya gyara tsaiwa ya ce.
"Banda son zuciya da mugunta irin na Aljani mene haɗinka da Bil'adama? Ina tunanin
munyi yarjejeniya dakai tun ba yanzu ba"
"Ba zan iya jurewa ba, ina son matata, kuma na shirya tafiya da ita duniyarmu"
Bilal ya faɗa murya na rawa kallon Yaa Sheikh ɗin kawai ya firgita shi. "Me nace
maka?" Bilal ya ce "Kace idan na sake bayyana zaka ƙona ni" Yaa Sheikh wani baƙin
ciki da takaicin yadda ya ɗaga masa Ƴar Aljannar shi a sama ya cika masa zuciya ya
ce.
"Bani da laifi idan nayi haka yanzu, kabar uwa ka dawo kan ƴar ka yi wa kan ka
adalci kowa?" Bilal ya ce "Abin da kayi nayi, yadda kabar uwa ka dawo kan ƴar haka
nima nayi, kuma ba zan barta ba ina tare da ita har abada" Yaa Sheikh ya nemi waje
mai kyau a saman dutsen ya zauna yana harɗe ƙafafuwansa waje guda cikin
kamilalliyyar muryarsa ya ce.
"Bisimillah!" Fatih ya fara karantawa ya ɗora da Yaásin. Bilal ya fara motsi cikin
sauri ya sauke Halisa ƙasa nan take ta farka daga barcin da take, Bilal ya
rungometa a jikinsa lokaci guda kuma ya dawo suffar Yaa Sheikh shima, sai ya zama
dashi da Yaa Sheikh kamar twins ne.
Zafin karatun dake rasa jikinsa yasa Bilal fara ihu tare da sakin kuka cikin sautin
murya mara daɗin Amo!
"Kada ka yi haka, kada ya rabani da ita kayiwa Allah kada rabani da matata wallahi
ina son ta" Yaa Sheikh ya dakata da karatun ya kalli yadda ya rungome masa mata ya
ce.
"To ai nima matar tawa ce" Bilal ya ce "Na fika iko da ita, har cikina ta samu aka
cire" Yaa Sheikh ya jinjina kai yana goge zufa ya ce.
"Nima zan tabbatar da hakan, zan cike nawa igiyoyin" Bilal ya kwarara ihu wanda ya
sanya Halisa firgita ta saki kuka ta kasa gane abin da yake faruwa, muryoyin
Abbanta ya kaso biyu, ɗaya cikin kuka kuma mara sauti ɗaya kuma a nutse cike da
Ilhama.
"Baka isa ba, zan kashe kowa naka idan ka kusanci matata ni kaɗai nake da wannan
ƙarfin ikon"
"Dan gidanku sai ka hana, nawa ma ba irin naka bane, ba ciki ba, ni cikkona zan
zuba mata da ƙwayayen da Ubangiji ya azurtani dasu" Yaa Sheikh ya ci-gaba da
karatunsa Bilal kuma ya dinga ihu da kururuwa Halisa ta ƙwace jikinta a ruɗe take
kallon Abbanta sai kuma ta juya ta kalli Bilal dake tsaye wanda ya yi kama da Yaa
Sheikh sak!
Tunaninta ya raɓauta firgice na son kassara ƙaramar ƙwaƙwalwarta. Yaa Sheikh ya
kalleta tare da miƙa mata hannu alamar ta zo. Bilal ya yi saurin cewa "Kinyi mini
al'ƙawarin babu mai rabamu,daman nace wani zai rabamu ki biyuni muje" Zaratan
mazan suka dagula mata lissafi wa zata bi? Waye kuma Abbanta.
Kamar ana janta tayi saurin riƙe Bilal ta ce "Tsoro nake ji kai ni gida Abba" Yaa
Sheikh ya ce.
"Ki matsa daga jikinsa shi ne wanda ke son jawo rayuwarki daga inuwa zuwa rana,
matsa nan nace" cikin ƙarfin murya da ɗaga sauti Bilal ya ce.
"Ƙarya yake, ƙarya ne kada ki yarda da shi" aka shiga fafatawa tsakanin Yaa Sheikh
da Aljani Prince Bilal. Ganin a wannan karan da gaske Bilal ba zai bar masa mata ta
daɗi ba, yasa Yaa Sheikh miƙewa a hankali ya shiga takowa yana ƙara sautin ƙira'ar
da yake wanda yake ƙara zautar da Bilal yana zuwa yasa hannu ya finciko Halisa ya
mannata da jikinsa tare da rungometa tsam, ta sauke wani ɓoyayyen numfashi lokacin
da jikinta ya haɗu dana Abbanta. Bai fasa karatun da yake ba Bilal bai fasa ihu ba
da ƙoƙarin kamo Halisa.
A hankali Yaa Sheikh ya zame Alkyabbar jikinsa tare da riƙo ƙugun Halisa ya manna
da nashi ya ɗora mata Alkyabbar tare da rufe ruf a jikinsa.
Ya saurara da karatun da yake gently ya tallafo haɓarta tare da manna fuskarsa akan
nata yana fesa mata zazzafan numfashi ya kalli bakinta wanda ya bushe sosai sbd
wahala cikin nutsuwa ya ɗora bakinsa akan nata wani irin damƙa ya yi wa lips ɗinta
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Kada ka kusantar mini mata, zan illataka na illata Ahhalinka
Malam" Yaa Sheikh bai saurari maganar da Bilal yake ba, idanunsa akan fuskar Halisa
wacce jikinta ke rawa tsoro ya kamata kallo ɗaya zakai mata kasan cewa ta gama
firgita da abin da yake faruwa. Ƙirjinta na ɗagawa sosai numfashinta nayin sama
hakan yasa Yaa Sheikh ƙara shigar da ita jikinsa da kyau yana mai zame bakinsa daga
nata sbd ganin Bilal ya gama haukacewa ihu yake da kururuwa wanda Yaa Sheikh da
Halisa ne kawai ke jin haka.
"Ban son cutar da wata halitta ta ubangiji,, meyasa ka zaɓi cutar dani?" Bilal ya
buɗe tangamemen bakinsa ya ce "Kai ne ka fara cutar dani, me ya sa zaka rabani da
wacce na saba da ita? na wanzu ina rayuwa a jikinta, rana tsaka kayi mini kutse ka
rabani ruhi da gangar jikina dana sahibar zuciyata" Ya faɗa yana ƙara sautin
kukansa yana cewa.
"Matata, matata yake matata kizo gareni, na wanzu ina son uwa yanzu na dawo kan ƴa
shi ne za a rabamu, zan rasa jin daɗi kwanciyar hankali idan bake Danejo, kada ki
bari ya yi ajalina"
Ta ɗago kanta tana son fitowa daga cikin Alkyabbar Yaa Sheikh ya yi saurin mayar da
kan ya haɗa da ƙirjinsa wanda gaban Jallabiyar ya ɗan buɗe kaɗan sai kwantacciyyar
sumar wajan da tayi luf.
"Abba me ya sa muryarka ke rabuwa gida biyu? Me ya sa kake kuka?"
Ya matseta a jikinsa sosai hannunsa guda ɗaya yana shafa kanta.
Cikin nutsuwa ba tare daya kalli Bilal ba ya ce.
"Dani kai wanda ya fasa, yanzu zan nuna maka ƙarfin ikon Allah, zan ƙonaka da
manyan ayoyin Alkur'ani mai girma" yana faɗin hakan ya fara karatu cikin nutsuwa
ayoyi masu zafin gaske yake karantawa, Bilal ya birkice cikin ƙaramin lokaci guduwa
ta mamaye wajan tare da ƙara da kururuwa.
Ƙam! Yaa Sheikh ya rungome matarsa itama ta zagaye hannuwanta ta riƙe ƙugunsa ta
ɓoye fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa yana jin yadda take sauke masa numfashi mai zafi.
"Shikenan naji zan fita, zan tafi zan barta amma kai ma ya zama dole ka rasata
kamar yadda na rasata" Yaa Sheikh bai saurara da karatun ba cikin kuka Bilal ya ce.
"Ashe zaki iya bari a rabamu? Ni ne mijinki abin son ki nace zaki bani ƴa ƴa da
yawa ki tausaya mini"
Wani ihu da ƙara Halisa ta fasa jikinta ya saki baki ɗaya tana neman zubewa ƙasa
Yaa Sheikh ya yi saurin taro ta tare da saka hannu ya ɗauke ta cak ya mannata da
jikinsa.
A nan kuma ya nemi Prince Bilal ya rasa sai wani hayaƙi dake fita daga bakin
Halisa, ta dinga jijjiga tana kaiwa Yaa Sheikh doka ta ko'ina tana neman ƙwacewa
amma ya riƙeta sosai tare da ɗora bakinsa a kunnanta yaci gaba da karatu.
"Wallahi zan tafi ka barni haka da raina, yanzu haka ka ƙona mini rabin jikina, zan
bar maka mata amma kada ka kusanceta kada ka sadu da matata Danejo"
Yaa Sheikh yaja numfashi sbd yadda take son fin ƙarfinsa ya ce.
"Ikon Allah ne kawai zai hanani mallakar matata cikin watan Ramadana" tun Halisa
ƙara ta dawo kuka sosai a hankali kukan ya fara raguwa can kuma tai hamma tare da
yin atishawa ta kwanta jikin Yaa Sheikh barci ya ɗauketa..
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya shima Yaa Sheikh ya sauke daga ita harshi zufa ke yanko
musu ta ko'ina duk da kasancewarsu a saman dutsen Jabal an-Nour ɗin.
A hankali ya fara tafiya yana sakkowa ƙasa har ya gama sakkowa da idanu yake bin
Umar-khan ba tare da ya ce komai ba.
"Mai martaba ya gama zirayar da zai a madina yana son ɗaukan azumi a Makka, yanzu
haka yana masaukin da aka bashi, shi da El-bashir, Ummul ta shaida mini zatai aikin
hajjin tama biye kuɗin an gama komai" Yaa Sheikh ya jinjina kai tare da shiga bayan
motar ya zauna har lokacin yana rungome da ita.
Umar-khan ya shiga motar kai tsaye ya nufi wani babban masaukin da aka bawa Yaa
Sheikh wanda bashi da nisa da masallacin ka'abah.
Sai da sukai nisa Umar-khan ya ce.
"Father ya kira, da alama magana ce mai muhimmanci kuma ta shafi Zahrah ya ce dai
ka kira shi immediately idan ka dawo"
Yaa Sheikh yaja idanunsa ya rufe shi kansa a gajiye yake kuma ya wahala, amma
zuciyarsa yanzu ta samu nutsuwa dan dan ba a tantance farin cikin Yaa Sheikh da
baƙin cikin Yaa Sheikh shi ya sa ba a iya gane sauyin yanayinsa.
Zubin halittar da Ubangiji ya yi masa daban ne dana sauran dukkan Ahhalin gidan
nasu. Ya buɗe idanu yana faɗaɗa fuskarsa kamar anyi masa bushara da gidan Aljanna
ya kalli fuskar Halisa a hankali ya riƙe tafin hannunta ya haɗa tana shi ya riƙe
sosai cikin ƙasa da murya ya ce. "Matar malam mai gayyar aljanu shikenan an gane
mini matasan ƙirjin da nake kiwo"
"Magana kake?" Cewar Umar-khan Yaa Sheikh ya yi masa banza.
A haka suka kawo gidan tun daga nesa yake ɗauke da jami'an tsaro ta ko wacce
kusurwa. Umar-khan ya tsaya sbd wani Security daya tsayar da shi cikin harshen
larabci ya ce.
"I.d card" kafin Umar-khan ya yi magana Yaa

Please Login or Register in order to submit comment