You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa magana ya yi tana
sakinsa ya buɗe ƙofar bathroom ya shige ciki... Cikin farin ciki da murna yau itama
tayi abin da Anti Zahrah keyi ta nufi part ɗin Ummul. Ummul ta kalleta ta ce "Kin
dai gane karatun ko?" Ta ɗaga mata kai kawai tana jan plate ɗin da Ummul ke mata,
tana cikin cin abincin ta ce "Ummul kin same?" Ummul ta girgiza kai ta ce "Sai kin
faɗa matar malam" Halisa ta ture abincin dan ba wata yunwa ta keji ba ta ce.
"Me ya sa gumi ke fitowa a goshin Abba? Kuma naga wani abu a jikinsa ba, duk sanda
na gani kaina juyawa yake" Ummul a zuciyarta addu'a take Allah ya sa ba wata
maganar da zata bata Kunya zatai ba, ko wani abu ne ya faru tsakaninta da Yaa
Sheikh ɗin take son faɗa, duk tai mamakin haƙurinsa, daya kawo har yanzu, ta riga
tasan waye Yaa Sheikh da kuma yadda ya ɗauki al'amarin Halisa da girma ko yana jin
tsoran yanayin rigima da ƙuruciyarta ne?.
Halisa ta dawo da Ummul daga tunanin data tafi ta hanyar faɗin "Ummul ni ina son
Abbana" Ummul ta ce "Kina iya bakinki, ba dan abinci kawai Ubangiji ya bamu ciki
ba, hadda ɓoye maganar da bata da ikon a faɗa da riƙe sirri, ki nutsu idan kina
wannan shirman Abban naki ba zai so ki ba" Halisa ta kwanta tana juyawa Ummul baya
ta ce "to naga mijina ne, kuma ina son sa" kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri
domin abu biyu ne ya faɗo mata a wannan lokacin, da maganin da El-bashir ya bata,
wanda take tunanin shi ne ya sanya Abban nata Yaa Sheikh yake fitar da zufar
goshinsa, sai kuma tuna Dada da tayi.
Ummul tabi bayanta da kallo sai kawai ta girgiza kai ta ce "Ubangiji ga Danejo ka
shirya mana ita, Allah ka kawo zama na har abada tsakaninta da Aliyu, ita ce farin
ciki Aliyu, Aliyu shi ne garkuwarta"

Halisa na fita ta nufi part ɗin Zahrah lokacin tana tsaye gaban madubi sai turare
take fesawa ajikinta, ta sanya wasu kaya kamar zata gasar rawa a club Halisa ta ce
"Anti" ta juya ta kalleta ta ce "wai ke wacce daƙiƙiya ce ne? Ko acikin ƴan fulani
ke daban kike, kawai ki faɗo ɗaki kamar wata dabba?" Halisa taji zagin har ƙasan
zuciyarta ta kalli Zahrah ta ce "me ya sa kike haɗani da dabba? Bayan ni mutum ce
kamar ke?" Zahrah ta tsaki ta ce "baki da wani suna da ya shige haka, and you'll
never be like me never" ta goge hawayen idanunta ta ce "Yaushe zan miki aikin ki?
Ina son ki mayar dani rugarmu, ban san haka kike ba kinyi al'ƙawarin kula dani da
kuma Dadata" Zahrah tai wata dry ta ce "Aikin kin kusa gabatar da shi, dan kin gama
zan mayar dake nima zamanki bai mini ba, yanzu bani da lokacin zani wajan mijina"
Halisa ta kalleta da sauri zuciyarta har ɗagawa yake sbd jin zata wajan Yaa Sheikh.
Ta juya idanunta fal hawaye tare da barin ɗakin. Zahrah ta nufi part ɗin Yaa Sheikh
ko'ina na part ɗin gwanin sha'awa ne, ko wacce kusurwa an kafe kalmar sunan Allah,
a hankali sautin ƙira'ar Alkur'ani ke tashi, amma ta nemi ƙofar bathroom ɗin nasa
ta rasa. Ta juya da sauri zuwa sashin Ummul ta sameta tare da Bara'at daga tsaye ta
ce "Naje part ɗin Yaa Sheikh na rasa ina ne bedroom ɗinsa, ina buƙatar sani sbd ina
son kasancewa da mijina"
"Amma shi mijin na son kasancewa dake?" Cewar Ummul. Zahrah ta ce "Ni matarsa ce,
dole ya buƙace ni" Ummul tai murmushi ta ce "Zahrah ki zauna muyi magana mai
muhimmanci, maybe ki gane sosai" Zahrah ta ce "ki riƙe maganarki mijina nake
tambaya" Ummul ta ce "Malam yana kan rabuta Alkur'ani yanzu, kafin azumi yake son
kammala rubutun, ba zai iya ganin kowa ba" Zahrah ta juya rai ɓace gashi masifa ke
cinta kamar taci babu.
Ummul bata da zaɓi wanda ya shige faɗin hakan, tasan ba lallai Zahrah ta samu abin
da take so ba. Washegari tun da Halisa ta tashi bata da wani karsha shi ta wakana
da tunanin ko Zahrah ta je wajan Abbanta? Tai sallah Asuba tare da Azkar ɗin da
Ummul ta bata, 6:30 ta nufi kitchen tasan a nan zata samu Ummul ɗin, Tana zuwa
Bara'at ta ce "Sannu da zuwa Halisa" Suhaima ta ce "Baki zo da wuri ba" tai
murmushi kawai ta ce "Ina kwana Ummul?" Cike da farin ciki Ummul ta ce "Allhmd.
Sanyi bai ka maki ba?" Ta ɗaga kai tana taya Bara'at aiki tare da ita suka kammala
breakfast. Ummul ta bata shayin Yaa Sheikh ta kai masa bayan ta shirya zuwa kayan
makaranta. Ta amshi shayin ta mufi part ɗinsa kai tsaye.
Fitowar sa kenan sbd barcin da bai samu ba jiya, kana kallon yanayinsa da sauyin
idanunsa kasan akwai matsala. Yana zama kan kujera ta shigo bakinta ɗauke da
sallama ta ajjiya tray ɗin tana zubewa wajan ƙafafuwansa ta ce. "Abba ina kwana?"
Ya jinjina tare da zuba black tea ɗin ya shiga sha a hankali ta gyara zama ta ce
"Abba" ya ware ido a kanta ba tare daya tanka ta ba. Ta ce "Anti Zahrah ta zo
jiya?" Hawaye ya cika idanunta ganin ya kasa cewa komai, zai gumi dake tsastsafo
masa ta goshinsa jijiyoyin kansa sun ta shi. Ya ajjiye mug ɗin hannunta bayan ya
gama shan tea ɗin tare da miƙewa tsaye, ta miƙe da sauri ta ce "Abba baka da
lafiya?" Sai a lokacin sauke numfashi yana jin kansa kamar zai rabe yana ɗan yin
gaba ya ce.
"Ki kula,ba wasa" ranta bai mata daɗi ba, shi kansa ya kasa riƙe sauyin nasa gudun
kada wani ya ankare baya son kuma Ummul ta san halin da ake ciki... Ta fita tana
jin kamar kada taje makarantar.
Har ta yini a makaranta cir bata da wata walwala haka kurum ta tsinci kanta cikin
sukuni, Abir tai ƙoƙari sosai wajan fahimtar da ita duk subjects ɗin da sukai
attending. Har suka taɓa hira sai lokacin ma Halisa ta saki jikinta jin Abir itama
asalinta ƴar Nigeria ce.
Yau ma Umar-khan ya dawo da ita ya lura da sauyin nata bai kulata ba, tunda ba
huruminsa bane yin magana da matar malam ɗin. Tana shigowa gidan bata nufi part ɗin
Ummul ɗin ba, ta nufi Main parlour zata shige part ɗin ta Zahrah ta ce.

"Yawwa ke nake jira dama, ki shirya zamu asibiti" Halisa ta kalleta tana mmkin waye
babu lfy kuma? Sai kuma gabanta ya faɗi ko dai Abbanta ne bashi da lfy, ta rikice
rikicewar da Zahrah taso ta ɗaure mata kai ta ce.
"Bana son shirme mene haka kuma? Kije kafin mu tafi ki gyara mini ɗaki kizo ki ɗan
danna mini ƙafata" Halisa ta tsurawa cikin Zahrah idanu har bata ji abin da Zahran
ta faɗa ba, tayi saurin jan riga ta rufe cikin da ya ƙara girma fiye da ko yaushe.
Ta juya tare da shigewa part ɗin nata, duk ta gigice tana shiga kuma ta fara duba
maganin da El-bashir ya bata, ƙila shi ne maganin da Abban nata yake sha bata sani
ba. "Kayi haƙuri Abba, laifi na ne" ta faɗa a sanyaye idanunta na cika da hawaye.
Zahrah ta miƙe tare da shigewa ɓangarenta, kai tsaye wayarta ta ɗauka tare da kiran
number Deen, kamar wanda yake jiran kiran nata yai picking call ɗin ta ce "Akwai
matsala Deen" ta cikin wayar ya ce.
"Yanzu muka fara samun matsala idan har ba zaki abin da ya dace ba, yanzu mene?" Ta
ce "Cikin nan girma yake, yau ƴar fillon nan ta gani amma kamar bata gane ba, kasan
kamar shirme ya yi mata yawa, shi ya sa na zaɓi nayi aikin nan da ita" Deen dake
zaune idanunsa sauke akan wata Balarabiyya dake ɗakinsa ya ce.
"Kada ki damu da wannan ƴar fillon na yanke shawarar abin da za mu yi mata, kawai
ki tabbatar Yaa Sheikh ya samu kusanci da Halisa, ki daure ko a tea ne ki zuba
maganin feeling ɗin, yana da ƙarfi sosai" Zahrah ta sauke numfashi ta ce "Amma kada
a raunata ƴar mutane, nice daidai da Yaa Sheikh mai zai hana ni naje gareja bana
tunanin zai gane bani da budurci" Deen yaja tsaki sosai ya ce "Kina da matsala
Zahrah,ki fito kice bana gamsar dake mijinki kike buƙata tunda naga alamar ba sanya
a wannan ɓangaren ba, listing to me Zahrah nasan waye Yaa Sheikh, nasan shi sanin
da zaki mamaki, duk yadda kike tunanin basirarsa ya shige nan, duk abin da zai same
shi yana ji a jikinsa, ki tura yarinyar kawai babu damu da duk irin abin da zai
mata ba" ɓoyayyan numfashi ta sauke tare da shafa cikinta wanda ya fara motsawa
alamar yana cikin ƙosashiyar lafiya ta ce "Deen what's your plan?" Ya ce "ban gane
ba? Ina tare dake muke tsara plan ɗin? Are you doubting me?" Ta kasa cewa komai sai
kashe wayar da tayi. Ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗin duk ranar da Yaa Sheikh ya
kusanci Halisa maybe ita kuma zuciyarta ta buga, a ƴan kwanakin nan wata sabuwar
Soyayyar Yaa Sheikh ta wanzu a zuciyarta, duk da bai bata wata dama ta Kasancewa
dashi ba, amma kullum da soyayyar shi take kwana a rai.
A hankali Halisa ke tafiya cikin wasu kayan shan iska sbd sanyin garin ya lafa, ta
sauke numfashi ganin Zahrah bata parlour kai tsaye ta nufi part ɗin Yaa Sheikh, ta
shiga bakinta ɗauke da sallama Umar-khan dake yiwa Yaa Sheikh bayani ya ɗago kansa
tare da kallon Halisa, da sauri ya ɗauke kai ganin kayan dake jikinta, Yaa Sheikh
dake jingine jikin kujera sanye da Jallabiya sabuwa kamar ko yaushe ya miƙe tsaye
tare da amsar ducoment ɗin da Umar ke basa, Umar ya ce "Ban gama yi maka bayani ba"
Yaa Sheikh shiru da Umar ganin haka yasa Umar miƙewa yana ɗauke idanunsa daga kan
Halisa, Ta ce "Umar-khan teacher ya ce gobe ka same shi a officer" ganin kamar bai
jita ba yasa ta sake cewa "Umar-khan, Umar-khan" ta faɗa tana ƙoƙarin bin bayansa
cak taji anyi sama da ita tare da nufar bedroom da ita.....
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Ya subuhanallah, wa...wa wa'auzubillah" sune kalmomin da suka
samu fita daga cikin bakin Yaa Sheikh wanda suka kasance iya zuwa. Ya riƙe kanta da
kyau yana ƙara ware idanunsa akan ta, mmkin ya cika shi yaushe matar malam ƴar
amanar shi tasan duk wannan? ya ɗauke numfashi yana ƙoƙarin sauya yanayin yaji ta
ƙara riƙe bakinsa da kyau idanunta rufe, al'amarin da bai taɓa ji ba shi yake neman
bijiro masa.
Ilahirin jiyoyin kansa sun fito tare da yin kwance a saman goshinsa. Ya zare
bakinsa da ƙyar ba dan ta daina abin da take ba, Halisa ta marairaice fuska
idanunta na cikowa da hawaye ta ce "Abbana" ya goga fuskarsa a wuyanta yana tura
dukkan hannunsa cikin sumar kanta ta sauke numfashi tana bin fuskar shi da kallo
tare da kama gemunsa tana ja..
Cikin wata kalar raunatacciyyar murya wacce shi kaɗai yasan ma'anar ta ya ce _"Ta
fuɗɗu ko a wawata famtugo nder majuum"_ karo na farko da taji fillatanci a bakinsa
wanda ya zauna raɗau kai kace harshen shi ne na Iyaye. Ta ce "Abba zan iya gane
darasin da gaske" "Uhm" ya ce kawai dan bakinsa ya yi nauyi sosai, yarinyar ta
shayar da shi mmki.
"Sallah zaki" ta ce "Abba ba zan iya tashi ba, kuma zanyi fitsari" ya miƙe da ita
tsaye tare da nufar bathroom. Suna zuwa ya sauketa tare da ƙoƙarin juyawa tayi
saurin maƙale kafaɗa ta ce.
"Ka tsayani, tsoro ina" ya kalleta sai kawai ya tsaya tare da juyawa mata baya.
Bayan ta kammala ya yi mata alwala da kansa a taushashe ya ce.
"Walk" bata gane zaran zancan nasa ba da hannu ya nuna mata ƙofa ta shagwaɓe fuska
sosai kamar yadda take masa a shekarun baya amma duk ta mance. "Ni ka ɗaukeni ba
zan iya tafiya ba" ya girgiza kai tare da sunkuya ya ɗauketa ta saƙalo wuyansa. A
jingine a jikinsa a haka ta gabatar da Sallar duk yana kallon ta, saura kaɗan gabar
ya kassara mata jiki gabaɗaya bata da kuzari duk babu kazar kazar ɗin. ganin tana
lumshe idanu ya ce "Gajiya? Jikin? Yunwa?" Ya faɗa a taƙaice ta girgiza kai ta ce.
"Abba Dadata yaushe zan ganta? Ni goyani take idan bani da lafiya" ya ware manyan
idanunsa yana hango zallar rigima dake kwance a nata idanun. "Abba ka goyani" ya
dubeta a dole sai ta saka ya magantu ya ce.
"Ki rufa mini asiri, goyo tun shekarun baya baki mance ba?" ta saki kuka da gaske
domin ita har zuciyarta take son a goyatan ƴar rigima ce, idan abin ya motsa bata
ji bata gani.
Ta saka kuka sosai ya ɗauketa gabaɗaya tare da jijjigata ya ce "Kina son rikitani
Amanata, ki tauyasawa Abbanki" ta maƙale kafaɗa daidai kunnanta ya shiga yin wasu
baitotoci na waƙar larabci na addini. Tai shiru tana tunani kamar tasan waƙar, Yaa
Sheikh yasan dole ta haka zai shawo kan rigimar ta ce "Abba kai ma ka iya?" Ya
zauna bakin gado yana ɗorata akan cinyarsa ya ɗan kalli time yaga goma ta kusa.
"Kin taɓa ji ne?" Ta ɗaga masa kai ta ce "Kamar dai" tai shiru alamar tunani da
sauri ta ce "Abba na tuna, wani na manta sunan mai rufe fuska shi ne yake yi mini a
Rugar Rome" ya ɗauke kai yana mai sassauta fuska kamar wanda murmushi zai ƙwacewa.
Ya gyara mata zama tare da zagaye bayanta ya ɗora kansa a wuyanta tattausan gemunsa
na gogar fatar wuyanta ya ce.
"Duba can?" Ya nuna mata direction da hannu idanunta ya sauka akan wani photo a
prame photon baby girl ne zata iya yin 10 mnts da haihuwa, idanunta rufe sumar
kanta har gaban goshi. Anyi wani rubutu kala biyu ɗaya da hausa ɗaya da turanci.
_“Angel my world”_ shi ne abin da aka rubuta da turanci da larabci kuma aka saka
_“Ƴar Aljanna Mrs Aliyu haydar Aliyu”_ yanayin yadda aka tsara photon zaka san cewa
ana matuƙar ji da shi, ta juya ta ce "Abba wace?" Ya shafa kanta da hannunsa har
lokacin fuskarsa na kifa a wuyanta yana murza mata sajansa mai laushi ya ce.
"Zaɓin Allah, matar ƙwarai, hasken zuciya" nan da nan yanayinta ya sauya ta ce
"Abba nifa? Da gaske baka so na?" Ya ware bakinsa kamar zai magana sai kuma ya fasa
Halisa tau saurin sauke numfashi jin tongue ɗinsa a skin na wuyanta yana yawo.
"Baka so na Abba?" Ya buɗe ido tare da ɗagowa baki ɗaya. "Kina so a soki ne?" Ta
ɗaga masa kai ya numfasa tare da kwantar da ita yana sauke mata numfashi ya ce.
"Ban son ina kwana, every morning come and Peck my cheeks, left and right, shi ne
gaisuwar" ta ɗaga masa kai. Duk sukai shiru can ya miƙe ya bisa da idanu.
Kai tsaye sashin Ummul ya nufa Ummul na ganinsa ta miƙe tsaye ita kanta kwarjinin
Yaa Sheikh rikita ta yake haibarsa da kamala har sun yi yawa.
"Ya jikin nata? da sauƙi dai? ta faɗa maka wanda ya bata gubar" Ya juya yana yin
wace ya ce.
"Allhmd. Ba buƙata" daga nan ya nufi Library ɗinsa, yaci gaba da rubutun
Alkur'anin da yake da ka, wanda yake son ya zama cikakken kafin zuwan Ramadan da
shi zai amfani wajan yin tafsir. 1:00 ya tashi bayan ya tabbatar komai lafiya yake,
ya watsa ruwa tare da yin alwala. Sallah ya gabatar sosai ya zauna zaman azkar sai
2:30 ya shirya cikin fararen kayan barci ya fesa turare ya nufi duguwar kujera tare
da duvet ya kwanta, daga ina yanke ya hangota sai barci take numfashi na sauka a
hankali gabaɗaya ta kwaɓe fuska.
"Rigimammiyata" ya furta a fili yana rufe idanu. Cikin dare sanyin zazzaɓi ya
takura mata da wani irin ciwon kai sosai kuma duk yana cikin matsalar da gubar ya
haddasa mata, ta yayar bargon da take ciki kai tsaye idanunta ya sauka akan Abban
nata ta nufi kujerar tare da hayewa saman shi ta zagaye hannuwanta ta riƙesa sosai
kanta a ƙirji nan take barci ya sake ɗauketa. Ba barci yake ba yana jinta kuma dama
ya san dole zata ta shi yaja bargon ya rufesu tas sai a lokacin barci ya ɗauke shi.
Duk yadda ya makara a kwanciya hakan bai hana shi tashi tun kiran sallar farko ba.
Ya buɗe bakinsa ɗauke da addu'a a hankali ya yunƙura zai tashi yaji an ƙanƙamesa,
ya kai idanunsa zuwa jikinsa ya sauke numfashi tare da komawa ya kwanta gaba ɗaya
ya manta a jikinsa ta kwana, gently ya miƙe da ita yana ji tana riƙesa tsoran kada
ta faɗi a haka ya kwantar da ita saman bed tare da rufeta da duvet yana matsawa ta
mirgina tare da cire duvet ɗin a haka taci gaba da barcin.
Cikakken wanka ya yi tare da ɗaura alwala ya shirya cikin embrodiery Islamic
jallabiya jikinsa sai fidda ƙamshin Nivea Men Active Clean Shower Gel, ƙafarsa
sanye cikin Scuff faux-shearling slippers ya nufi fita daga gidan zuwa Masjid sai
baza ƙamshi Roja yake. Sai da ya gabatar da raka'atul fjr kana yaja jam'i cikin
daddaɗar muryarsa cikin makarijul huruf da fidda hakƙin tajwid yake karatun. Ana
idarwa ya fara gabatar da karatu wanda ya kasance da mutane da yawa, ya ɗago kai
tare da kallon mutanan kana ya bayar zuwa ga littafin dake gabansa a taushashe ya
ce.
_“ Babin da yake bayani akan tilasta mace zuwa ga shimfiɗa bada yarda ta ba, a
turance kuma Sexual violence”_ ya gyara zama sosai gaba ɗaya larabawan wajan sukai
shiru suna sauraran abin da zai ce. A hankali ya ce.

7:00 ya shigo gidan bayan ya biya ta wajan tsuntsayensa, daman yasan ba zai samu
kowa a main parlour ba. Kai tsaye part ɗinsa ya nufa da mmki yake dubanta tana
kwance saman prayer kar sai gyangyaɗi take. Ya nufeta bai ce komai ba taji an
ɗagata sama tayi saurin buɗe idanu suka kalli juna sai kawai tai murmushi mai kyau
tana kwantar da kanta. Bayan ya sauketa saman bed ya ce.
"Sanyi sai kama ki, a daina kwanciya ƙasa" ta ɗaga masa kai tare da faɗin "To Abba
makaranta fa?" Ya tsare ta da idanu kafin yai magana wayar shi ta gida ta fara
ringing ya miƙe tsaye a hankali ya manna wayar a kunnansa. Umar-khan dake kan layi
ya ce.
"Barka da safiya Yaa Lee, ya mai jiki? Ummul na neman iso na shigowa sashin naka"
"Uhm" ya ce yana ajjiye wayar. Babu jimawa Ummul ta shigo hannunta ɗauke da babban
tray.
"Barka da safiya, ya jikin nata?" Yana zama kan kujera tare da naɗe ƙafarsa ya ce.
"Mun tashi lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah, Ya jikin ƴar Abba" Halisa tana daga
kwancan ta ce "Naji sauƙi Ummul, tambayi Abba kiji shi ne ya ɗaukeni yanzu kuma a
jikinsa na kwana" kamar ƙasa ta tsage ta shiga haka Ummul taji kunyar Yaa Sheikh ta
kamata Halisa ta ƙara cewa.
"Ummul Abbana ɗan gayo ne ba kiji bakinsa ba..."
"Ya isa haka, yau naga takai ne ni Ummul" Halisa ta juya za taiwa Yaa Sheikh magana
amma ko inuwarsa babu a bedroom da alama ya daɗe ta ficewa tun da yaji abin kunyar
da take neman haɗa shi da ita. Ummul sam batai wani mmki ba, ita juriya da haƙurin
Yaa Sheikh kawai take gani.
"Ƴar Abba ba komai ake faɗa ba, shi aure sirri ne, duk abin ya faru ki barshi a
ranki, kinji?" Ta ɗaga mata ta ce "maza sha tea kinji?" Ta maƙale kafaɗa ta ce
"Modibbona zai ban kije kawai Ummul, kuma me ya sa ki ka daina cewa matar malam?"
Ummul ta ce.
"Because he's no longer your husband" tana faɗin haka ta fita. Ita kuma Halisa sam
bata gane ba. Tana fita Yaa Sheikh ya fito daga bathroom suna haɗa ido da Halisa ya
watsa mata harara ita dry ya bata ma.
Zahrah na tsaye ta kafe Ummul da idanu tana tirketa da manyan tambayoyi. "Ina ƴar
aikina take, ya zama last question da zan miki" Ummul ta ce. "Bata jin daɗi, a part
ɗina ta kwana" Zahrah tai shiru sai kuma ta ce "Muje akwai aikin da za tayi mini
yanzu?" Ummul ta ce "Bata lafiya fa?" A fusace Zahrah ta ce "And so what? Ke rashin
lafiyarta ya dama" Ummul ta ɗauke ta ce.
"To Umar-khan ya tafi kai ta asibiti" yaja tsaki tare da juyawa ta ce "Bari naje
wajan Yaa Sheikh ɗin naji wanda ya bada lasisin yiwa ƴar fillo abu ba tare da
izinina ba" Ummul tai bedroom ɗinta da sauri ta kira Umar-khan ta ce.
"Ka kira Yaa Sheikh yanzu ga matarsa Zahrah nan zuwa, kasan Halisa na wajansa" tana
faɗin hakan ta kashe kiran.
Kiran telephone line ya tsayar da Zahrah daga tafiya part ɗin Yaa Sheikh, ta ɗaga
kiran tare da cewa "Hello" Jadda dake bisa layi ta ce "Waye ne za a fasa mini kunne
kamar yaƙi?" Zahrah taja tsaki a ranta ta ce "Matar Aliyu mana?" Jadda ta zabga
Salati ta ce "Yaushe Gadanga ya yi aure kuma?" Zahrah ranta ya ɓaci ta ce "matarsa
Zahrah" Jadda ta ce "Uban meye kuma Zahra? A to Allah ya isa ban yafe ba maganar da
nayi dake, maza maza mutum nake nema bake ba don Allah, kije kiji da Iyaye abu a
kwance kamar tawul ɗin wankan mai jego" wani kyakkyawan tsaki Zahrah ta ja. Tamkar
Jadda ta fasa wayar haka tayi ta ce "Uwarki ki kaiwa tsaki, ai sai yanzu na
tabbatar Gadanga bai aure mace ba, mai siffa irin ta fir'auna da ƙaruna, baki kamar
maliya tayi ambaliya" kashe wayar Zahrah tayi baki ɗaya tsanar mata ya ƙara zama
daram a zuciyarta.
Ko sallama ba tayi ba a haka ta shiga part ɗin Yaa Sheikh, a tsaye ta gansa ya baza
Alkyabba sai ƙamshi yake zabgawa wani irin kyau ya yi mata wanda bata taɓa ganinsa
ba, ya ƙara girma da faɗi.
Ta sauya tafiya tana kaɗa jiki cike da kissa ta nufesa tana zuwa ta ce.
"My Excellency, you look good kayi kyau sosai" ta rungumesa ta ce "I love you
husband" ya buɗe ido yasan daman babu gaisuwa a tsarinta. "Yaushe zaka bani damar
zuwa sashinka na tayaka barci? Na fara gajiya kawaici na ya ƙare ina buƙatar
mijina" sai a lokacin ya kalleta sosai a hankali ya ce "Sanda ki ka shirya" zata
sumbaci bakinsa taji kamar wani abu yana yi mata yawo a jiki ta ɗan motsa ta ce
"Uhm daman nace a daina fita da ƴar aikina ba tare dana sani ba, kuma idan da hali
ta kwashe kayan zuwa sashen masu aikin gidan nan" ta zabura sbd abin da yake ƙara
bin jikinta gudun kada ta bata kanta a gaban Yaa Sheikh tayi saurin cewa "I'll be
back" ya lumshe idanun tare da buɗewa tai saurin ficewa.
Wani irin fisgar numfashi ya yi jin yadda ta riƙesa sosai ta baya, gaba ɗaya ta
jiƙa masa bayan riga ta bakinta. Ya saka tattausan hannunsa tare da fito da ita
waje daga cikin Alkyabbar jikinsa.
Ya dubeta ya kalli hannunta brush ne wanda ta wanke baki ta tura baki ta ce.
"Ji nayi tana cewa zata kwana dakai fa Abba shi ya sa" wato ita ta kuri Zahrah?.
Ya juya zuwa bedroom har lokacin jikinta baƙwari sosai suna zuwa taga ya jawo
Injection yana zuƙar ruwa gabanta ya faɗi sosai. "Allah sarki Abbana waye babu
lafiya kuma?" Da ace dry halinsa ne babu abin da zai hana shi yi ya juya ya ce.
"Ƴar fillo" ta haɗiye yawo ta ce "A'a wallahi lafiya nake,don girman Allah Abba
kada kayi mini don soyayyarka da Annabi wlh banso" ganin ta gaske yi mata zai ta
kwasa zata gudu ya damƙota tare da zama da ita akan cinyarsa ya ce.
"Shhhhh, ina gaisuwata?" Ya faɗa yana ajjiye allurar gefe ɗaya. Ta sauke numfashi
ta ce "Naji tsoro ashe bani za aiwa ba" ya dai bita da idanu a hankali ta saƙalo
wuyansa tare da ɗora bakinsa a kumatunsa, ta sakar masa kiss ya saka hannunsa a
bayanta tare da yin ƙasa da trousers ɗin jikinta, idanunsa cikin nata a haka ya
ɗauki Injection. Halisa tai murmushi tana ƙara yi masa kiss a kumatu shi kuma ya
saita Injection ɗin a jikinta. A hankali ta dawo bakinsa sai kuma ta fasa ta ɗaga
idanu tare da kallon Yaa Sheikh ta ce "Abbana ina son ka" a karo na farko ya sakar
mata murmushi wanda yasa ta zuba masa idanu kamar bata taɓa ganinsa ba, ya sumbaci
goshinta ya ce.
"I na... Ina.." tai dry ta ce "Yawwa Modibbona ni ma kace kana so na" ya ɗora
tsinin allurar sosai a jikinta ya ce "Ina.. ina son" bai ƙarasa ba ta ce "Ina son
k....," wani ihu ta fasa daidai lokacin daya tsira mata tana ƙoƙarin sakin kuka ya
kame bakin kukan da nasa bakin ya rungometa sosai a jikinsa...

Paid book
500
08119237616
Allah ya nuna mana Monday ai weekend lfy🥱
[1/3, 4:48 PM] Abk: _I unite you with the greatness of God a daina fitar mini da
littafin IDAN BA KE. What you want will not be difficult for you to buy. This is
not appropriate at all.🫰🏿har zuwa ake a nuna mini wai an samu book ɗin Idan ba ke as
free irin ga masifaffiyar nan bari nai ta ihu a media😂 I love my book lovers
wherever they are. Amma don Allah a daina fitar da book ɗin... It's 500 via
6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616_


Kasa ƙarasa maganar ya yi sbd gemunsa data

Please Login or Register in order to submit comment