You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauke numfashi ta ce. "Ya Abban naki? Baya miki komai
dai? Ba wani daya faru?" Kamar ba zatai magana ba sai ta ce. "Lafiya lou Mother,
Ina Maimoon?" Da ace Ummul da Yaa Sheikh na wajan mamakin shirun baki Halisa sai
ya kashe su. "Masha Allah, Allah ya yi miki Albarka muje ko?" Mother ta miƙe itama
ta miƙe tare da bin bayanta. Akan dining room suka samu, Abba Hakimi, Umma A'isha,
Mai martaba, Ishaq-Hakim. Mother taja kujera Halisa ba taja idanunta akan Abba
Hakimi dake vedio call ta zame a hankali ƙirjinta na ɗagawa.
"Sun iso lafiya, saura kai ko?" Cewar Abba Hakimi yana riƙe wayar shi da kyau, ta
cikin wayar suka ji an yi ajjiyar zuciya ba tare da ya ce komai ba.
"Matar ga Abbanki ku gaisa ya miki ya hanya?" Ya juya mata screen ɗin wayar.
Idanunta ya sauka cikin na Yaa Sheikh wanda ya kafeta da idanu shima fuska babu
alamun rahama, sosai yake jin zafinta a ran shi don me zata bi Mai martaba? Akan me
da wanne dalili kuma?
Bakinta na rawa sosai ta ce "Ab... Abbana" ɗib! Ya kashe wayar haske ya mamaye
gurbin kamilalliyyar fuskar Yaa Sheikh dake maƙale jikin screen ɗin wayar.
Hawaye ya sakko mata sosai ta kasa furta komai. Ganin abin da ya faru gaban su Abba
Hakimi ya ƙara tabbatar musu babu Soyayyar Halisa ko kaɗan cikin zuciyar Yaa
Sheikh.
Ya ɗauka zai biyo bayansu a gobe amma amsar daya bawa Abba Hakimi ta bashi mamaki
sosai. Da ƙyar taci abincin zuciyarta babu daɗi ta miƙe tana musu sai da safe.
Har akai sallar Issha Halisa bata fito ba, Mother tayi duk yadda zatai ta bugi
cikin Halisa amma bata samu abin da take son ji ba.
Mother tai mata sai da safe kafin ta fita zuwa nata bedroom ɗin.
Abba Hakimi ya kalli Mai martaba ya ce "Anya ba aljanna ce ta auri Aliyu ba?" Cike
da tarin girmansa shekarun Abba Hakimi Mai martaba ya ce "Meka gani? Don me ya sa
ka ce haka?"
"Na lura da gaske Aliyu babu jimmilar aure a tattare da shi, ina jin tsoro idan
lafiya yake baka lura bai damu da tahowa da Halisa da akai ba?" Murmushi kawai Mai
martaba ya yi, domin abubuwan da Idanun shi suka gane masa a gidan Aliyu yana da
yawan gaske. "A bashi lokaci mana?" Abba Hakimi ya ce "Nayi masa al'ƙawarin zan yi
masa abin da yake so, idan har ya riƙe deal ɗin mu, na fahimci Aliyu ya san girma
da darajar riƙe al'ƙawari, ya yi amfani da yarjejeniyar da mukai, bana son raba
auren Aliyu da yarinyar nan, na rasa mafita"
Mai martaba ya ce "A karo na biyu a kiran Aliyu akan idanun kowa a maimaita
tambayar da akai masa akan Halisa, idan ya furta abin da ya ce abaya, sai muyi masa
abin da yake so, idan kuma ya ce yana son ta sai ka hukunta shi" Abba Hakimi ya ce
"Bana jin zai furta kalmar so akan wata ƴar mace, tunda ya yi rashin abin da yake
so a baya" suka miƙe ganin dare ya yi Mai martaba ya ce "Mu barwa Allah komai,
everything will be fine" Abba Hakimi ya ce "Inn shaa Allah"
Halisa barci ya ƙaura cewa idanunta juyi kawai take akan gado, idan ta tuna tabar
Abbanta da kishiyarta Zahrah a ƙasa ɗaya sai ƙirjinta ya yi mata nauyi zuciyarta
tai zafi da ƙyar take jan numfashi, barci ɓarawo shi ne ya ɗauketa.
Cikin dare ta juya sbd ƙamshin Roja daya cika mata hanci ya hanata sukuni, cikin
magagin barci ta juya sai taji ta a jikin abu mai laushi, slowly slowly ta shiga
buɗe idanun sosai cikin rashin sa a idanunta ya sauka akan kwantaccen sumar ƙirjin
mutum, wanda bata da maraba da sumar namiji...
[1/4, 7:47 PM] Abk: Domin ƙara tabbatar da abin da zuciyarta ke faɗa mata ya sanya
ta ɗaga hannu tare da shafa kamilalliyyar fuskar shi,
Hannunta ya sauka a kwantaccen gemun shi mai laushi.
Tsoro ya ƙara kama Halisa tayi saurin tashi zata miƙe ya riƙe ta sosai numfashinsa
na sauka a hankali yanayin fitar numfashin kaɗai zai tabbatar bashi da lafiya,
A ruɗe ta kira sunan shi cikin sanyin murya ta ce
"Abba" ya yi shiru yana sauke numfashi mai zafi
Ganin bai amsa ba kuma bai da niyya ta amsawa ya sanya ta miƙa hannu,
Zata kunna socket ɗin dake gefen gadon.
A hankali cikin murya mara hayaniya ya ce
"Ban son haske"
"To Abba" was yadda ya yi mata magana.
Sukai shiru na wani lokaci ta ce "Yaushe kazo? Ina ne Ummul taje?" Sai a lokacin ya
yunƙura daga kwancan da yake har time ɗin yana riƙe da ita, ya gyara mata zama bisa
tattausan cinyar shi.
ya fesar da numfashi cikin wani irin sabon yanayi na kasala ya manna gemunsa a
wuyanta.
Ta sauke numfashi tana riƙe kafaɗar shi. "Nazo ne ki nemi yafiyata" tayi saurin
cewa "Yafiya kuma?" Ya jinjina mata kai har lokacin fuskarsa ɗaure take.
"Kina cikin fushin Allah, dana Manzon shi haɗi da Mala'iku"Halisa ta zare idanu
domin ita bata san babban laifin data aikata
Har haka ba, wanda yaja mata fushin Ubangiji.
"Me nayi Abba, taya zan jure fushinka bare na Ubangiji?" Ya sauke numfashi a
hankali ya zura hannunsa ta ƙasan rigarta ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta yana
shaƙar wani sahihin ƙamshin,
Wanda yake sanya shi ya yi over acting ba tare da ya yi niyya ba, a nutse ya buɗe
baki tare da manna softness lips ɗin shi ya lashi wuyanta,
Tayi saurin zabura sbd tsigar jikinta data tashi haɗi da zubewa, a karo na biyu ta
ƙara riƙe shi muryarta na rawa ta ce.
"Wayyo Abba"
Ta faɗi hakanne sbd wani sumbata da ya yiwa fatar wuyanta tare da ɗan cizawa, a
hankali yake bin gabaɗaya wuyanta da hot kisses masu zafin gaske da tsayawa a rai,
Ita kanta tayi kewa to ya rayuwarsu zata kasance idan sukai nisa na wani lokaci?
ganin yadda Yaa Sheikh yake komai a gaggauce yasa ta san yau ba sauƙi.
Bai kuma nemi hanyar bi ta sauƙi ba, jikinsa ya ɗauki zafin zazzaɓin masassara dake
damun shi. Ya zame fuska tare da komawa jikin frame ɗin bed ɗin ya jingina yana
sauke numfashi.
"Laifin me na yi Yaa Sheikh? Mena aikata wanda Ubangiji ke fushi dani?" Da ƙyar ya
ware idanunsa ya watsa a kanta yana son gasgata cewa da gaske bata son laifinta ba?
Ko faɗa kawai take.
"Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, kada ku sake ku fita ba tare da
umarnin mazajanku ba, domin sune ku ke ƙarƙashinsu, hadisi ingantacce"
Ya ɗago bakiɗaya tare da manna fuskar shi a nata fuskar ya zagaye ƙugunta da
hannayensa ya goga mata tsinin hancinsa "Why?" Hawaye ya sakko mata ta ce "Mai
martaba ne Abba, nace zan faɗa maka ya ce a'a" Yaa Sheikh ya dinga kallon bakinta
da yadda hawaye ke zuba cikin idanunta kafin ya ce.
"Anya kin nemi hanyar rabauta da aljanna?" Kuka na son fashe mata ta ce "Kayi
haƙuri ban sakewa ka yafe mini" ya sauke numfashi yana komawa jikin frame ɗin ya
kwanta idanunsa lumshe. Ta matsa har ruwan cikin shi tana wasa da sumar ƙirjin shi
ta ce "Abbana kayi haƙuri" ya yi mata banza ita kuma shirun nasa ne bata so, ta
lura yau a sama yake da yawan lokaci tana mamaki yadda amsa sallama ke masa wahala
da kuma yadda yake sake mata suke magana.
Yanzu dai ba Abbanta bane a gabanta, asalin Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu take
gani. Maganganun Abar suke dawo mata, tayi saurin kwanciya saman shi tare da yin
flat a hankali ta kama hannunsa ta manna a ƙirjinta na daba wani irin kukan
shagwaɓa da sangarta ya ƙwace mata "Yaa Sheikh susa mini danna mini ƙirjina baffi
ciwo yake mini" lokacin ƙanƙani ta rikita shi ya yi iya yinsa ya kasa kame kansa da
son nuna bai damu ba, amma Halisa sai faman manna hannunsa take saman ƙirjin tana
kuka tare da ƙanƙame idanunta.
Jikinsa na rawa na wutar data kunna ga zafin zazzaɓi ya mirginata zuwa ƙasa,
idanunsa rufe ya ɓalle bra ɗin tare da yin wurgi da ita gefe guda, tsit! Kukan ya
ɗauke maimakonsa taji tausar hannu sai taji ana yi mata ta baki, ta rufe idanu
sosai sbd zafin da ƙirjinta ya ɗauka,
Bai taɓa yunƙurin kai bakin shi wajan ba sai yanzu, ta fahimci dalilin shi nayin
haka sbd mugun son abun da yake,yana kuma tsole masa idanu ainun.
Ta faɗawa ƴan mutan Rome, da dukkan Fulanin dake cikin Rugar.
A yau ta fahimci da ɓangaren Abba kawai take kallo, amma yau Yaa Sheikh ne gabanta
babu tausayi ba zaka taɓa cewa ya kwana biyu cikin harkar ba, yadda yake yi tamkar
yanzu ne me yasan daɗin auren.
Ta saki kuka sosai lokacin daya mirgina gefenta, a hankali cikin nutsuwa na mutuwar
jiki ya ɗagota bakiɗaya zuwa jikinsa ya rungume abar shi sosai ya shiga bubbuga
bayanta alamar rarrashi amma taƙi yin shiru, ya ciji kunnen tare da kisses skin ɗin
wajan yana hura mata iska ya ce. "Meye na kuka kin cinyewa Mother ɗan ta" ya sauke
numfashi
"Abin da ki ke so ne, sai kiyiwa Malam godiya"
Ta saki kuka ta ce
"Kuma na yau yafi na kullum" a hankali shi ma ya ce "Na haɗa da hukunci ne" ya
gyara yanayin murya ba wasa ya ce "Haliyserh!!!!"
Gabanta ya faɗi jin kiran da ya yi mata. "Na'am Yaa Sheikh" ta furta a sanyaye tana
kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannunsu cikin gashinta yana ya motsawa ya ce
"Fita ko nan da gate sai da umarnin Abbanki, balle barin ƙasar rabauta nake nema
miki" ta jinjina kai ta ce "Ba zan sake ba, ka yafe mini" ya maƙale kafaɗa kamar
yadda tayi yana son kuyi da Annabi akan jan iyali tare da yin wasa dasu bisa sunna.
"Zanyi sai anyi abu ɗaya" ta ce "me zan yi?" Ya nuna mata wuyan shi ya ce "Kiss" ya
ɗora bakin tare da yin kiss kamar yadda ya ce. Ya ƙara nuna mata tsakiyar ƙirjinsa
ya ce "Kiss" nan ma tayi ya kalli cikin idanunta tare da nuna mata marar shi ya ce
"Kiss" ta zare idanu sosai ta kalli wajan ta ce "Aba...." Ya tare ta da faɗin
"riƙe abinki na riƙe yafiyar, Aljanna nake tayaki nema" ta runtse idanunta sosai
kunya ta kamata a hankali ta ɗora baki wajan suka sauke numfashi a tare Yaa Sheikh
ya yi saurin riƙe sumar kanta.
Tai kisses a wajan kafin ta ɗago ya danna kanta yana faɗin "Ubanmu, sarki wanda ya
sanya mana numfashi a gangar jikinmu, ka bamu lafiya da iskar shaka ba tare dako
sisi ba, ina roƙo kayi ma Diƴar Sheikh albarka,ka tsare mutuncin Matar Malam!"
Tayi saurin rufe ido tana rungome shi ta ce.
"Amin Abbana" ya shafa kanta kawai ta ƙara cewa "Abba baka taɓa cewa kana so na ba,
me ya sa ko dai baka so na?" Ya yi shiru ta riƙe hannunsa ta ce "Abba ko akwai wani
abu ne?" Ya riƙe hannun ya ɗora daidai saitin zuciyar shi, sosai taji ƙirjin shi na
bugawa kamar zai fito.
"Ba kowa zai gane ba, ki nutsu ƙilan ke ki fahimci Abbanki" ta kasa ajjiye maganar
shi a ko wanne ma'auni, kiran sallar farko na asuba ya fargar da Yaa Sheikh ya zame
ta yana miƙewa tare da saka jallabiya har ya yi waje sai ya dawo da baya ya zuba
mata gajiyayyun Idanunsa ta miƙe tsaye a yanayin da suke ta taka har zuwa inda
yake. Kamar haɗin baki ta nufe shi, shi kuma ya buɗe hannun shi da sauri ya saketa
yana faɗin. "Ki kula, ki fahimta,kuma ki yarda da Abbanki, ki riƙe amana"
Tabi bayan shi da kallo tai murmushi tana shigewa cikin toilet ruwa mai sanyi ta
haɗa tai wanka ta tsarkake jikinta
Ta shirya cikin duguwar riga fitted gown ya atamfa ciganvi.
A can masallaci mamaki ya kama su Abba Hakimi sbd jin muryar Yaa Sheikh yana jan
jam'i cikin daddaɗar muryar shi,bayan an idar da Sallah Yaa Sheikh ya tsaya tafsir.
Abba Hakimi ya kalli Umar-khan ya ce "Lafiya Umaru? Saukar yaushe?" Umar-khan ya ce
"Abba ƙarfe 2:5 muka shigo gidan nan, Father ya matsa da kira" Abba Hakimi ya
jinjina kai ya ce "Ina ita ɗaya matar Aliyun fa?" Ya ce "Umma tasan mun dawo, ita
ta bata bedroom ta kwana" Abba Hakimi ya ce
"Ba laifi, ka cewa Engineer ina son ganin shi by 10" Mai martaba da El-bashir da
Ishaq-Hakim jinsu kawai suke. "Banga Saif-wazir ba?" Ishaq-Hakim ya ce "Saif baya
ƙasa ai, amma ya ce yau zai dawo ko gobe" a haka suka shiga cikin gida, Abba
Hakimi ya zauna parlour Umma A'isha ta kawo masa coffee mai zafi sun jima suna
tattaunawa.
Mother ce ta fito daga bedroom cikin kyakkyawar shiga ta light blue ɗin lace mai
kyau hannunta riƙe da mug ta nufi ɗakin Halisa, kwance ta ganta tana barci na
gajiya sai ta ajjiye cup ɗin tare daja mata ƙofa ta fita.
9:30 ya fito cikin dakakkiyar shadda sai ɗaukan idanu take kalar sararin samaniya
babbar riga da ƴar ciki, ya ɗora hirami akan shi, ya fito a cikakken Malami kuma
Yaa Sheikh ɗin shi.
Mother ta bisa da kallo ta ce "Saukar yaushe Haydar?" Ya nemi waje kusa da Abba
Hakimi ya zauna yana rufe idanu for some minutes ya ce "Jiya da dare" ta ce "Ikon
Allah, bari na kawo maka coffee" ya duba agogo ya ce "Allhamdulillah,zan duba
ɗalibai na" sai a lokacin Abba Hakimi ya ce "Anya? Muna da meeting ka jira, kaje
kazo da Zahrah da Halisa" Mother ta kalli Abba Hakimi ta ce "Halisa na barci" ba
tare daya kalleta ba ya ce "A tashe ta" ta ce "to" ta miƙe ta nufi bedroom ɗin.
"Malam Aliyu ko baka ji ba?" Without saying anything ya miƙe kai tsaye wani
bedroom ya nufa, a tsaye ya samu Zahrah tana ganinsa ta ce "My Excellency" ya
dubeta sosai ganin yadda ta faɗa ya ce.
"Lafiya ki ke?" Ta ƙarasa inda yake ta ce "Bana jin daɗi, maybe ƙarin ke damuna"
cikin kulawa da son sauke nauyin dake kan shi ya ce "kamar lokacin aikin ya yi, sai
aje asibiti, Allah ya sauwaƙa fito" ta ɗauki ƙaton hijabi ta saka hannunta a gaba
tana kare cikinta.
Fitowar su ya yi daidai da shigowar Father, suka kalli juna da Yaa Sheikh father ya
kalli Zahrah bai ce komai ba ya shige zuwa parlourn.
Lokacin Halisa ta shigo ta saka hijabi tana zaune ƙasan carpet, Yaa Sheikh ya
zauna, Mai martaba haka, suna zaune Uncle Haroon ya shigo da Uncle Bashir. A wannan
lokacin ko breakfast basuyi ba, Abba Hakimi ya buɗe taro da addu'a kafin ya numfasa
ya ce.
"Engineer Aliyu ka takura Akan auren da Malam ya yi, har ka saki babar shi saki
biyu, akwai laifi ne?" Father ya ce.
"Yasan da cewa ba a yi wa familyn su Zahrah kishiya, kuma babu umarni na da
sahalewa ta cikin auren da ya yi, infact am not interested for the married"
gabaɗaya suka kalli Father. "Amma ba hujja ba ce kace ba yiwa Familynsu kishiya,
faɗar Ubangiji cewa.
‫ُحو۟ا َما َطاَب َلُكم ِّمَن لِّنَسٓاِء َمْثَن‬ ‫َأ‬
‫َعۖ َفِإ ْن ِخْفُتْم‬
ۖ ‫َثٰـ‬
‫ٰـَوُرَب‬ ‫ٰـ َوُثَل‬
‫ٰىٰـ‬ ‫ٰى‬ ‫َفنِك‬ ‫۟اى‬
‫َتٰـَم ٱ ٰى‬ ‫ُط ٰىٱ‬
‫و۟ا ِف ْلَي‬ ‫َوِإْن ِخْفُتْم اَّل ُتْقِس ۟اٱ ٰـ‬
‫َأ‬ ‫َأ‬ ‫َأ‬ ‫َأ‬
‫اَّل َتْعِدُل۟ا َٰو ٰـوۚ َف۟اَٰوِحَدًة ْو َما َمَلَك‬‫َأ‬
‫ٰٓى اَّل َتُعوُل ۟ا‬
‫و۟ا‬ ‫ۚ َٰذِلَك ْدَنٰٓى‬
‫َٰذ‬‫ْتٰـُنُكْم‬
‫ْيَم‬
Kuma kai awa duk wannan ayoyin kace ba za ai kishiya ba? Bayan Ubangiji ya halarta
yinta,kuma Malam nada wadatar riƙe su? Anya Engineer ka ɗauki hanya mai ɓullewa
kada ka shiga lamarin Ubangiji" Father ya ce "Haka ne duk abin da kace Abba Hakimi,
amma ba haka mukai da iyayenta ba, idan harni na haifi Aliyun dole ne ya rubuta
takardar saki yanzu agaban kowa ya bawa yarinya ita kuma ta nemi mijin aure" Uncle
Haroon ya ce "Ikon Allah, kai ka ke da iko ko kuma Yaa Sheikh? Idan kuma akwai idda
ko ciki fa?" Father ya ce "Bare ma babu, na tabbatar da haka"
"Mene hujja?" Cewar Uncle Bashir, Father ya ce "Sbd Zahran ta shaida mini Aliyu
bashi da lafiyar zama da iyali" Yaa Sheikh ya ɗago da sauri ya kalli Zahrah itama
ta kalle shi. Halisa ta miƙe tare da yin waje da gudu ba zata iya zama akan
idanunta a rubuta mata takardar saki ba.
"Kuma Wallahi idan Aliyu ba saki Halisa ba sai na tsine masa" Zahrah tayi saurin
cewa "Ina son Yaa Father kada ya barni" ya ce "kwantar da hankalin ki" Abba Hakimi
ya ce "Ni kuma idan har Aliyu ya buɗe baki a yanzu ya ce yana son Halisa zai zauna
da ita wlh Engineer kayi tsararo kasa ya saketa, ruwanka bai kai tsaiko ba" Ya juya
kan Yaa Sheikh dake zaune ya kasa cewa komai ya ce "Nasan akwai yarjejeniya
tsakaninmu, amma nasan ka riƙe amana tunda ance baka da lafiya, idan har ka faɗa
mini yanzu a gaban kowa kana son Halisa a yanzu zan baka ita ka koma Madina ko ka
nufi gidanka da ita, kana son Halisa kana son zama da ita matsayin mata da miji?"
Waje ya yi shiru Yaa Sheikh ya kasa furta komai sai zufa dake yanko masa. Da gudu
Umar-khan ya shigo ya ce. "Yaa Lee Halisa..." Mother ta Mike tana faɗin "Mai ya
sameta?" Ina Yaa Sheikh tuni ya yi waje bai tsaya jiran jin komai ba, Umar-khan ya
ce "El-bashir ya ya ɗauketa, yaja mota sunyi waje akwai matsala" suka ɗauki salati.
Gabaɗaya sukai waje, suna fita harabar gidan motar Yaa Sheikh na fita daga gate.
Cikin sa a ya hango motar El-bashir ya ƙara gudun tashi, ta cikin madubi El-bashir
ya hango motar Yaa Sheikh ya yi murmushi yana sakin dariya, burinsa ko zai mutu ya
kashe Halisa ya ɗauki fansar abin da Yaa Sheikh ya aikata masa shekarun baya. Ihu
sosai Halisa take tana kiran sunan Dada da kuma Yaa Sheikh, da ganga El-bashir ya
saki kan motar gabaɗaya ta nufi wajan wata ƙaruwar tirela sukai aran gama, motarsu
Halisa ta kifa ta ƙara kifawa a hankali ta gangara ta tsakiyar titi ta daki wani
ƙaton dutse....
[1/4, 7:59 PM] Abk: "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abin da ɗauka kin
jama'ar wajan suka shiga faɗa, lokacin da motar su Halisa ta ƙara kifawa dalilin
dutsen da suka daka. Daidai lokacin motar Yaa Sheikh ta ƙarasu, bai san mene ya
faru ba amma ya samu kan shi cikin faɗuwar gaba ganin yadda go-slow ya yi yawa a
saman titin.
Ya yi parking a can nesa kaɗan bakinsa ɗauke da addu'a ya fito daga motar yana
gyara zaman babbar rigar jikinsa, wani daga gefe ya ji yana faɗin. "Allahu Akbar,
Ubangiji yasa ransu yaje a sa a" ɗaya daga gefe ya ce "Amin Amin, yadda motar nan
tayi da wahala a samu mai rai a ciki, Allah kasa mu cika da imani" "Ai daka gani
tukin ganganci ne, nafa hango shi gabaɗaya ya shige ƙa'ida, mutane na ganganci da
rayukansu" wanda ya yi magana daga farko ya sake cewa
"Kawai Allah ya ƙaddara ta haka ransu zai koma gare shi, jama'a nawa suke driving
ba daidai ba, wani ba shaye-shaye yake wani yana waya, wani na danna waya, duk ba
daidai ba ne"
Wannan tarin maganganu suka ƙara saka Yaa Sheikh cikin zullumi ya samu kansa cikin
tsoran abin da idanunsa suka gane masa, ƙafarsa ta gagara motsawa balle ya yi
yunƙurin duba wanda hatsarin ya faru a kansu, ya jima yana addu'a kafin ya ɗaga
ƙafa da ƙyar sbd kukan Ambulance da ya ji. Sai a lokacin wani ya lura da Yaa Sheikh
ya ƙarasa yana faɗin
"Yaa Sheikh da kan shi, abu ne ya faru babu kyan gani" Yaa Sheikh ya kalli mutumin
a rarrabe ya ce.. "Ya Allah!"
Sai kuma ya ratsa ta gefen mutumin, jiri ya nemi ɗaukar shi, numfashinsa ya tsaya
cak! Na wani lokaci ya zama tamkar statue ganin motar da El-bashir ya ɗauka ta
gidan Abba Hakimi kwance duk ta farfashe, glasses ɗin ya yi rugu-rugu.
Bai san mene ya faru da shi ba, amma gabaɗaya ya rasa ganewa da gaske motar El-
bashir ce a haka? hakan na nufin Halisa na ciki!
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya furta a fili ta yarda duk wanda yake kusa
da shi zai iya ji.
Ya nufi motar da sauri lokacin da wani yake cewa "Ayi sauri a cire su, ko za a samu
wani card da za ai amfani da shi wajan kiran Ahhalinsu" wani ya ce "Gaskiya, motar
kamar hayaƙi take kada wuta ta tashi fa?"
Yaa Sheikh ya yi namijn ƙoƙari ya ƙarfafa zuciyar shi, tunda yaji kuma zuciyar
tashi na bugawa ya tabbata she's still alive! Ya ƙarasa wajan wani police ya ce
"You know

Please Login or Register in order to submit comment