You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanaku yin
kwalliya a bikin yayan naku ko Maimoon?" Maimoon ta ce "Haba Mother bakya farin
ciki da auren akan me mu kuma za mu yi har muje muyi wani henna da saloon?" Zeefa
ta ce "Wallahi Moon, ni fa tun kafin naga amaryar naji na tsaneta kamar Father ya
fifita ta akanmu" Auta Fattoumah fuska a haɗe hannunta riƙe da handle ɗin game ta
ce "I hate her too, because of her the happiness in our house is gone"
Mother ta saki baki da hanci tana bin yaran nata da kallo kafin ta ce "Akwai wanda
ya halicci Zahrah a cikin ku? Balle kuyi ƙorafin sauyin halittar ta? Kul na kuma
jin magana irin wannan, musamman ke Maimoon, Mamana ke kuma waye ce miki sbd ita
farin cikinmu ya tafi?" Fattoumah ta yarda handle ta ce "Mother nasan komai fa,
gashi har father yana cewa ana nemawa Yaa Lee mahaifi" Mother ta runtse idanu sosai
wato kaf yaranta idan aka ɗauke Sheikh babu mai kaifin tunani da basira irin
Fattoumah,ga riƙo tana lura da komai. A sanyaye ta ce "Maza ga mai henna can tana
yiwa Dr A'isha kuje ayi muku" tana faɗin hakan tai waje.
A main parlour ta samu Dr A'isha da Yaya Halima sai friends ɗinta irin su Barrister
Zainab. Mother ta zauna a kujera idanunta akan t.v ba tare data cewa kowa komai
ba. "Sheikh ya yi lunch kowa?" Cewar Dr A'isha. Mother ta ɗan kalleta kaɗan ta ce
"Anya? Kamar dai azumi yake" Yaya Halima ta ce "ba kama bane, yau Alhamis ai"
"Oh haka ne fa, na manta azumin Alhamis da Litinin Allah ya bamu lada" Barrister
Zainab tai murmushi ta ce "Wato ke Dr A'isha ba zaki iya ba? Shi yasa ɗan naki ya
rainaki" tai dry sosai ta ce "Azumi kam sai manyan malamai irin su Sheikh Aliyu
haydar Aliyu".
Sheikh na zaune shigowar shi kenan daga masjid yin sallar asr, a hankali ya sauke
numfashi. A nutse ya ajjiye azkar ɗin hannun shi tare da miƙewa yabar cikin Library
ɗin na shi kai tsaye ya nufi haɗaɗɗan bedroom ɗin sa wanda yaji kayan more rayuwa
ko'ina na bedroom ɗin ƙamshi yake, ya zame jallabiyar jikinsa wanda ƙa'ida idan zai
shiga wanka sai ya cire komai ya rage daga shi sai boxer yake shiga. Tsarin
halittar jikinsa ta bayyana yana ɗan kare jikinsa da hannu a haka ya shige bathroom
tare da sakarwa kansa shower ta warm water. Fitowa ya yi sanye da towel jikinsa ka
fitar da ƙamshin MUD BEGIN Natural shower Gel. Idanunsa na lumshewa kamar mai jin
barci a haka ya shafa versiline mai kanshi tare da fesa body spray. Wata duguwar
Jallabiya mai nauyi da tsada ya ɗauka ya sanya, jallabiyar daban take domin har
wani zane ne jikinta kamar alkyabba. Yana gama sawa ya naɗa rawani kamar kullum
tare da ɗora hirami saman ƙafaɗar shi. tsaf ya kammala shigar shi irinta manyan
malamai wanda suka san me suke ko a maluntar. Jikinsa na fidda ƙamshin Roja wanda
ya bayyanar da zuwan shi cikin Main parlour ɗin gidan. Kansa a ƙasa ba tare daya
kalli kowa ba, kamar yadda zuciyar shi ta raya masa hakan ce ta kasance Dr A'isha
na ganinsa ta fara buɗa tare da faɗin.
"Ayyiri yiri the lastest ango of the year" ya ƙara kame fuskar shi babu walwala
hannun shi akan gemunsa yana ɗan ja haka yai waje ba tare da kalle ta ba, balle
yace mata wani abun duk da yaso ya tsaya yayi mata bayanin aya da hadisai Manzon
Allah akan muhimmancin muryar mace. Da kuma rashin amfanin wannan ihun da take.
Chevrolet silverado car wacce ta kasance blue black ya nufa, harabar gidan shiru
hakan yasa ya rufe idanu yanayin na masa daɗi na shaƙar fresh air ga ƙamshin
na'ana'a dake ɗan nesa da shi, Bismillah ya yi tare da shiga motar sai da ya yi
addu'a kafin a hankali ya yi wa motar key gatekeeper ya buɗe masa, cikin nutsuwa da
haiba yake driving motar har ya harbata kan titi.

A harabar gidan Abba Hakimi ya yi parking motar, ganin motoci da yawa ya sanya shi
taɓe fuska baya son hayaniya sam. Ya fito a kame yana jan gemunsa kaɗan ta baya
yabi a ƙoƙarin shi na son shiga part ɗin nasa ba tare da kowa ya gansa ba. Yaje
corner kenan yaji ance.
"Yaa Sheikh" Khalil Ahmad Sarki ya faɗa yana murmushi hannun shi riƙe da gorar
ruwa. "Yanzu nake shirin zuwa can gida muji yadda al'amarin bikin zai kama, nasan
dai bikin Yaa Sheikh dole ba events ba D.j" Sheikh ya ware idanu da kyau yana bin
Khalil da kallo. Khalil ya ce "na ƙosa naga matar Yaa Sheikh, nasan dole ta zama
Malama kamar haka, Wow! Ga Yaa Sheikh ga Malama what a beautiful couples wlh dole
love yaci ƙaniyar shi"
Yaa Sheikh ya ɗauke Idanunshi tare da kama hannun Khalil Ahmad sarki suka nufi
hanyar ƙofa Khalil ya ce "Ya dai kamata ka fito tun ɗazo Mai martaba ya shigo" har
lokacin Yaa Sheikh bai ce komai ba, yana zuwa bakin ƙofa ya tura Khalil waje tare
da rufo ƙofar ya murɗa key. Khalil ya dinga dry daman ya lura zan can damun Yaa
Sheikh yake yana mmkin yadda baya ƙaunar ai masa maganar mace?. Ya juya inda yabar
su Abba Hakimi yana zuwa ya ce "Abba Hakimi ai ga ɗan naka can ya gudu part ɗin
shi" Abba Hakimi ya ce "Za mu yi faɗa dakai yanzu Ibrahimul-khalil" Khalil ya yi
murmushi ya ce "Nikam ina ruwar gida Momi ne?" Abba Hakimi ya ce "Tana can tana
kayan buɗe baki na Aliyu, ƙosai da kunun gyaɗa"... "Ah! Lallai aikin lada take
kenan" Mai martaba Ahmad Sarki ya kalli Ishaq-Hakim cikin kamala ya ce "kira
Sheikh" da mutumtaka ya ce "To ranka ya daɗe Allah yaja kwana" kafin Ishaq-Hakim ya
miƙe El-bashir wanda tun ɗazo yake hakimce saman kujera ya miƙe cikin nutsuwa hannu
cikin aljihun suit ya nufi hanyar fita Abba Hakimi ya bisa da kallo yana nazartar
yanayin yaron wanda baya son haɗa inuwa da Yaa Sheikh gaba ɗaya. "El-bashir kada
kai nisa" cewar Mai martaba. He just nods his head and quickly leave the parlour.
Bayan sallar magrib Yaa Sheikh na zaune a ƙawataccen parlournsa gabansa ɗauke da
kayan buɗe baki, inibi yaci sai ƙosan da yake mai zafi ya yi laushi sosai sbd ƙwai
da aka zuba cikin haɗin, hakan yasa ya ɗan saki jiki ci ƙosan da kunun gyaɗar.
Yana jin gine da jikin kujera yana kallon Aljazzera yaji Sallamar Abba Hakimi shi
ne kawai ke shigowa kai tsaye cikin part ɗin na shi, ya gyara zama sosai yana mai
amsa sallamar ta Abba Hakimi. Bayan Abban ya zauna ya dubi Yaa Sheikh ya ce. "Aliyu
haydar" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa gaba ɗaya tare da kallon Abba Hakimi da yake faɗin
"Jibi ɗaurin auren ka, ya ya zakai da uwar gidan naka kafin amaryar tazo?"
"Uuuu...uu... Uwar gggg gida? Am am amarya?" Ya faɗa yana kallon Abba alamar rashin
fahimta. Abba Hakimi ya lura da gaske Yaa Sheikh bai gane ba ya ce "Yarinyar da aka
ɗaura maka aure da ita a can Yola? Ka tuna?" Tab yakan manta abubuwa amma wannan
abun ya zama abu na farko da ya yi saurin mantawa da shi. "Ina jinka,ina so muje
can rugar tasu ne" magana zarar bunu cikin rashin sani Yaa Sheikh ya ce "Uhm bani
da labarin hakan Abba, idan akwai auren ma zan kunce shi yanzu...


*Don Allah kada a fitar😒 littafin IDAN BA KE na kuɗi it's 500 via this account
6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Via evidence 08119237616.


SARAUTAR MARUBUTA
[1/3, 4:48 PM] Abk: Murmushin manya Abba Hakimi ya yi yana mamakin yadda kai tsaye
Yaa Sheikh yake nuna zallar ƙiyaya ga ƴa mace balle kuma ai masa batun aure, ya san
dai rayuwa ba zata taɓa yin yiwuwa ga babban mutum irin Sheikh Aliyu haydar Aliyu
ba aure ba. Yana sakin murmushi ya ce.
"Baka sonta? Ko auren ne baka so?" Yaa Sheikh ya yi shiru kansa a ƙasa ba tare da
ya ce komai ba, hakan bai damu Abba Hakimi ba domin ya riga yasan waye Yaa Sheikh
sai dai ya bawa wani labari sanin da ya yi masa baya tunanin ko Mahaifin shi
Engineer ya sani. "Shi kenan, Allah ya kyauta, ka jira sakin muga ko?" Abba Hakimi
ya furta hakan yana miƙewa tsaye hannun shi riƙe da sanda. Yaa Sheikh ya a miƙe
tsaye shima suka jera shi da Abban na shi duk da bai so fita wajan ba.
A parlour suka samu Mai martaba Ahmad Sarki shi da Khalil suna tattaunawa a hankali
lokacin guda kuma fuskar Mai martaba ɗin ta sauya launi sosai. Bayan sun zauna
Khalil da bakinshi baya shiru ya ce "Abba ka fito da ango kenan, ban taɓa ganin
ango kamar shi ba He doesn't want to talk about his marriage at all" Abba Hakimi
ya kalli Mai martaba ya ce "Your highness mai ya sa ka taho da wannan ne? Ina ya
bar matar ta shi" murmushi girma kawai Mai martaba ya yi ba tare da ya ce komai ba
idanun shi akan Yaa Sheikh yana taso ya faɗa masa wata magana amma ya kasa.
"Yaushe El-bashir ya zama haka ne? Kamar wanda wani abu ke damun shi?"
Khalil cikin rashin jin daɗi ya ce "Na lura da hakan, matsalar El-bashir taurin
kai, komai ya yi zafi a rayuwa maganin shi Allah yabi komai a sannu har Ubangiji ya
bayyana abin da yake rufe ko?" Abba Hakimi ya ce "haka Innalillaha ma'al sabirin" a
hankali Mai martaba ya duba lokaci yana mai miƙewa tsaye kafin ya kalli Yaa Sheikh
ya ce "Yaa Sheikh aci gaba dayi mana addu'a, ina nan ina ta sadaƙa, kamar yadda
kace" Yaa Sheikh ya buɗe ido wanda tunda suke magana idanun suke rufe, tare zubawa
Mai martaba idanun cikin nutsuwa ya ɗaga kai tare da ɗan faɗaɗa fuskar shi da
murmushi. Abba Hakimi ya ce "ba zaka zauna a nan ɗin ba?" Mai martaba yana gyara
sandar hannun shi ya ce "Anya? Gwara naje can hotel ɗin zaifi" sai da safe ya yi
musu Yaa Sheikh da Abba Hakimi suka zauna zaman karatu kamar yadda suka saba
kullum.
Juyi yake saman lafiyayyan royal bed ɗin na shi ya kasa barci baki ɗaya mafarkin da
yake ya hana shi runtsawa, gashi duk karatun shi bashi da masaniyya akan fassarar
mafarki, ya miƙe zaune yana mai motsa bakinshi alamar addu'a cikin nutsuwa ya kunna
blue light haske ya ƙara bayyana a bedroom ɗin, daga shi sai white night wears masu
taushi da kyau, ya saka Hermes slippers tare da shigewa bathroom ya wanke bakin shi
tas kai tsaye ƙaramin parlournsa ya koma, hannunshi riƙe da kwalin Dabino yana zama
kan kujerar ya zari dabino ɗaya ɗaya tare da kaiwa bakinshi, zaƙi da garɗin dabinon
suka ratsa saman harshensa tare da kaiwa jijiyoyin dake sarrafa kwakwalwar dake
basa umarnin ziyara, kai tsaye dukkan wani daɗin dabinon ya gama ratsa ko'ina na
bakinshi. Iska mai daɗi ta fara kaɗa shi kafin can kuma ya fara jiyo kukan mage
ƙasa-ƙasa bashi da wata alaƙa da mage infact baya son mage a rayuwarshi da alama
kuma so ake a firgita shi da ita. Babu tsoro a fuskarshi ya miƙe hannu goye a
bayansa bakinsa ɗauke da addu'a a haka ya fara bin hanyar da kukan yake tasuwa ba
tare da tunanin komai ba. A can corridor ya ga wata baƙar mage jibgegiyya wacce
bai taɓa ganin irinta ba, a kallo ɗaya kuma ya fahimci ba mage bace irin jama'arsa
ce masu takura masa. Girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi
hanyar bedroom ɗin kamar daga sama yaji magen ta ce.
"Zahrah da zaka aura tana da ciki, tana ciki, tana da ciki" ya tsaya daga tafiyar
da yake tare da juyowa baki ɗaya yana harɗe hannu a ƙirji, duk kusan wani abu da
zai faru da shi a rayuwa yana mafarki da shi, inma mai kyau ko mara kyau, ya yarda
cewa kuma mafarki ba gaskiya bane bai taɓa yarda da abubuwan da yake gani ɗin ba.
Wani lokaci jama'arsa da suke bibiye da shi sune suke faɗa masa wani abun.
Ya sauke numfashi cikin laushin murya ya ce.
"Ta nan aka ɓullo, raba aure zaku koma?" Ya faɗa a taushashe yana zubawa magen
idanun ta ce "musan abin da baka sani ba, tana da ciki, tana da ciki" Yaa Sheikh ya
jawo aya mai zafi cikin kamilalliyyar muryarsa gumi na tsastsafo masa ya ce
"Ubangiji shi ya san komai" ya sauke numfashi yana mai ƙara cewa "matsa nan, kafin
raina ya ɓaci" kasancewa ko a malamai suna shakkar Yaa Sheikh cikin ƙaramin lokaci
ta ɓacewa ganinsa, da ya san sune ma babu abin da zai tsanya ya fito Maganar Zahrah
da cikin ya tattara ya sanya su a mala.

Washegari ya kama juma'a Yaa Sheikh ya fito cikin wata dakakkiyar shadda gezner
fara tas sai ɗaukan idanu take, bai saka Alkyabba ba kasancewar jamper da babbar
riga ya sanya sai rawani kawai da ya yi ya ɗora hirami saman ƙafaɗarsa. 1:30 daidai
motarsa tai parking a babban masallacin juma'a dake nan Kano. Cikin sauri gudu
harɗewar harshensa ya fara huɗu ba akan muhimmancin sadaƙa da kariyar da take
bayarwa dan gane da asara. 2:00 ya data iƙima na sallah ana idarwa kamar yadda ya
saba ya nufi gidan marayu da naƙasassu yana basu taimako. 3:30 ya dawo gida kiran
Father ne ya ƙara sanyawa ya yo gidan kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, yana
gaba Khalil na gefen shi a haka suka shigo cikin parlourn mai ɗauke da some of
relatives nasa, idanunsa akan Fattoumah wacce akai wa henna a hannu da ƙafa tana
ganin shi ta miƙe da sauri tana faɗin "Yaa Lee, Yaa Lee" da sauri yaja baya domin
baya son abar hannunta infact he doesn't know menene ba, ya zauna saman kujera yana
harɗe hannu a ƙirji ba tare daya kula Auta Fattoumah ba. Dr A'isha ta ce "Ango
kasha ƙamshi, wata tsiyar ma sai jibi amarya ta zo can wait to see this day" Yaya
Halima ta ce "ke dai Dr bakya kalan girma Wallahi ta ya ya ɗan naki zai girmama
ki?" Kafin kowa ya yi magana Jadda ta fito zani na faɗuwa ta ce "Ga Malam ga Malam,
huhu azabar duniya ya naga duk an sa shi gaba kamar wata tattabara sabuwar ƙinƙisa?
Nifa masifar Sa'idu ce bana son uban kowa kuma ya san babu kyau ai" Khalil ya saki
baki yana kallon Jadda. "To dan mun gaisa da shi ai bai zama laifi ba ko?" A fusace
Jadda ta ce "Alkur'an ya zama? Ki faɗi inda kuka haɗa jini da Malam? Ba dangin iya
balle na baba, sai ihun cewa ke ƙanwar uwar shi ce, gaba kuma kice ke uwar shi
bayan ko ƙaton kashi baki taɓa ba, balle haihuwa tirrr da iri na irin naki, ke dai
baki yo gadon haihuwa ba, Insha Allah duk inda wata tara tayi matar Malam ta sauke
cikin fari ke dai kiyi ta zama" nan da nan idanun Dr A'isha ya cika da hawaye babu
abin data tsana irin ai mata gorin haihuwa. Yaya Halima itama da ranta ya ɓaci ta
ce "Jadda amma dai kin san haihuwa lokaci ce ko? Duk wanda ya haihu Allah ne ya
bashi ai" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce "Ai baki cika ƴar halak ba Halima
indai baki zo kin dake ni ba, na faɗa ta haihu ne? Naga shekara guda akai bikin ita
A'isha take kowa da kuma siyan Akuyar da nayi, gashi nan sai haihuwa take kamar
almara ko yanzu ciki gareta ina ta rabawa jama'a domin su sami irin albarka" Dr
A'isha ta fashe da kuka sosai tana ciwo sosai a ranta. Yaa Sheikh dai yana zaune
tare da sauraran komai ba, jin ihun Jadda ya yi yawa ya sanya ya miƙe tsaye tare da
saurin barin wajan, yana zuwa dab da Dr A'isha ya kama gefen rigarta ya jata can
part ɗin mother. Bai ce mata komai ba, amma ya lura da irin zafin da take ji a
zuciyar ta. Sai data gama kukan ta fara shassheƙa ya lumfasa kaɗan ya ce.
"ka yi bushara ga masu hakuri (155) su ne waɗan da idan wata musiba ta same su,
sai su ce: mu daga gare shi muke kuma gare shi za mu koma, Baqara (!56)" ya yi
shiru saboda In-inar data zo masa, shirun daya sanya Dr A'isha ɗago jajayen
idanunta tare zuba masa su, sai taga ba ita yake kallo ba, gaba ɗaya ya tattara
gaban babbar rigarsa ya riƙe ƙam hannunsa na rawa, alamar da gaske magana yake son
yi, jikinsa ya bashi kallon shi take da sauri ya juya zai bar wajan kamar fitar
gashi daga cikin nono haka maganarsa ta fito ya ce.
"Wannan ayar ta kur’ani ana kiranta da ayar maidowa kuma tana karantar da mu
darasin cewa kada mu yi baƙin ciki da faduwar falala, domin duk wannan baiwar Allah
ce. Wata rana ya yafe, washegari kuma ya ga dama ya dawo mana da ita, su biyun su
ne maslahar mu. Ki yi haƙuri"
Yana faɗin hakan yabar wajan kamar walƙiyya Dr A'isha ta saki Ajjiyar zuciya tana
jin sanyi a ranta, yau Yaa Sheikh da kansa ya jata har ya yi mata wa'azi lallai ta
zama ta musamman ko a cikin ƴan uwa.

Jadda kuma ta inda ta shiga bata nan take fita ba. "Ko wanne ɗan hau idan ba zai
iya zama bai yai gaba, idan mutum yaja baki yai gum sai ace ya yi wulaƙanci, ya yi
magana kuma ace shi ɗan iska bai iya magana ba, huuuu wannan azabar Alkur'an ba
dani ba Alsulhu khair" tana ganin Yaa Sheikh yaja baki tai shiru akan idanunta ya
haura upstairs part ɗin father, kamar yadda yai tunani yana parlourn shi zaune sai
haɗa gift yake wanda zai bawa bride's family. Yaa Sheikh zai sallama Father ya ɗaga
hannu ya ce "shigo kawai, riƙe sallamar ka" hakan bai damu Yaa Sheikh ba, ya nemi
waje ƙasan carpet ya zauna.
"Akwai events da Zahrah zatai, kuma tana buƙatar kaje iya friends ɗinta ne, kai ma
kaje da friends naka, 12 na dare zasu fara event ɗin gobe, You can check by
yourself" Yaa Sheikh bai ce komai ba, kuma bai amsa ba, domin ya san ba za shi ba.
Ya miƙe tsaye yana gyara zaman hiramin jikinsa. Sai da ya ɗan jima a tsaye ya ce
"Allah ya taimaka" yana faɗin hakan ya juya cikin sauri tare da barin gidan baki
ɗaya shi da Khalil.

Surayyerh ta zame jikinta daga cikin friends ɗin Zahrah tana duba agogo dake nuna
10:15 na safiyar ranar asabar. Cikin sauri ta nufi compound na gidan tare da shiga
mota, tana yi tana dubawa gudun kada wani ya kanta, driving motar dake da gudu har
tabar Commissioners Quarter's kai tsaye ta nufi wani babban mall parking tayi,
kasancewar mall ɗin na manyan mutanai ne ya sanya aka fara yi mata Wlcm tun daga
bakin gate. Tana shiga ciki wata mata ta ce "Wlcm Maaah" ta ɗaga mata kai, kai
tsaye ta nufi ɓangaren kayan mata ta saka wata maid ta zo. Tana zaune saman kujera
lemo a hannunta maid ɗin ta ce "Yes Maaah, how can I help you?" Surry ta ya motsa
fuska tana kallon maid ɗin ta ce "Ina buƙatar, Abaya's, perpumes, body spray, body
lotion, shower gel, everything na mace masu kyau na ƴar 17yrs ki haɗu ki kawo mini
yanzu" Maid ɗin ta rusuna ta ce "Insha Allah Maaah, enjoy your time" ta juya da
nufin tafiya Surry ta ce "hiii nace ba" Maid ta ce "Yes" Surry ta miƙe tsaye tana
ƙare wa wajan kallo ta ce "Ki tabbatar body lotion ɗin sai sauya fata cikin kwana
biyu" Maid ɗin tai murmushi cikin hausar ta ta ce "kada ki damu kinji" kaya masu
mahaukacin kyau aka haɗawa Surry ga tsada ka cika aiki, komai na babban company aka
zaɓo, ta biya kuɗi aka loda mata kayan aleda daga mall ɗin Specialist Yola ta nufa,
tana zuwa ta samu Danejo zaune a gaban room ɗin da aka kwantar da Dada, ta miƙe
tsaye fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Sannu da hanya Adda" Surry ta haɗe rai ta ce
"Ba nace bana son Addar nan ba, kice Anty" tai ƙasa da kanta tana wasa da hannu "Ya
na ganku a nan?" Danejo taƙi cewa komai sai Shatu da ta ce "Ana duba Dada ne" ta
jinjina kai tare da neman wajan zama, sai duba lokaci take tasan anytime Zahrah
zata iya nemanta sbd shirye-shiryen zuwa event anjima. Likitocin suka fito Danejo
na ganin haka ta shiga room da sauri Shatu ta mara mata baya, Surry tabi bayansu A
zaune ta samu Dada cikin ranta ta ce "Wow, ashe Halisa gado tayi" Kyakkyawa ce
sosai Dada ajin ƙarshe, ta faɗaɗa fuska idanunta akan Surry wacce ke mata sannu
cikin sanyin muryar ta ce "Allahamdulillah, ke ɗaya yau?" Surry ta ce "Wallahi,
hanya ta biyo dani bama sai an faɗa mata nazo ba, anjima likita zai sallame ki"
Dada ta ƙara sakin murmushi ta ce "To ba damuwa, Allah ya saka muku da alkairi,
Halisa ta faɗa mini aiki sai dai ban gane ba" Surry tai murmushi ta ce "Oh! Daman
ƙawata zatai aure shi ne za a ɗauke ta aiki sbd mun yaba da hankalinta, kuma duk
shekara ko wata za a dinga biyan ta kuɗin aikin, kuma sa a sakata a makaranta akan
wannan sharaɗin da tace zata cika muka kawo ki asibitin" da sauri Danejo ta kalli
Surry domin tasan ba haka akai ba, bakinta na rawa kasancewar bata barin magana a
ciki ta buɗe baki ta ce "Lalashewa ta sameki Anty Aradu ƙarya ne ba haka akai ba,
shewa sukai zan..." cikin sauri Surry ta tare Danejo da faɗin "wannan daban ne
kinji ƙanwata Halisa, zo kiga kayan da na siyo miki" tai shiru tana ware idanunta
itafa haka kurum ba za a dinga rainata mata hankali ba. Surry ta buɗe ƙatuwar
shopping bag ɗin ta shiga zaro dugwayen riguna kala-kala, masu kyau da tsari.

"Wannan kayan duk na mene?" Cewar Dada domin ganin kayan ya sanya kanta sarawa ta
rufe idanu da sauri. Surayyerh ta ce "Kaya ne, na kawowa ƙanwata Halisa ta fara
amfani da su kafin mu tafi da ita" Dada ta kasa cewa komai domin tana ganin tafiya
da Halisa wani wajan ba ƙaramin babban ƙibi bane a rayuwarta, kuma ba zata jure
kalar rayuwar da suke ba, Halisa tana da saurin baki bata da haƙuri wani lokacin
kana yi mata take maka zafin rai gareta. Surry ta ce "Anjima Dr zai zo, zuwa anjima
ko da safe zamu zo mu tafi da Halisa ɗin, akwai wani Sani mai p.o.s a wajan shi
zaki dinga karɓar kuɗin aikin Halisa na duk shekara, zan baki number waya koda kina
buƙatar jin muryar yarinyar ki sai ki bawa mai p.o.s ɗin ya kira, gaba ɗaya aikin
shekara biyu zatai...." Da sauri jikin Danejo na rawa ta ce "Wallahi ba inda zani,
ba zan biko ba taimakon da ku kaiwa Dadata Allah ya saka ni dai ba zani ba daman
wayo nayi muku dan ku kai Dadata asibitin burni...


Pay before you read.... IDAN BA KE it's paid book 500. Via 6850917335 Na'ima
Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.... Don Allah kada a
fitar😒😂.


SARAUTAR MARUBUTA
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Subuhanallah yi haƙuri bata kula ba" Surry ta faɗa da sauri
tana kama hannun Halisa ba tare data bari ta buɗe liƙab ɗin ba. Ita dai Halisa
kallon Yaa Sheikh take kamar idanunta zai faɗo ta cikin liƙab ɗin.
Yaa Sheikh ya ratsa ta gefen Halisa zai shige tayi saurin shan gabansa tana kwace
hannunta, duk da ta tsorata da yanayin shi amma bai hanata ƙara binsa da idanu ba
da ƙarfi ta ce.
"Laa Wallahi shi ne, Balarabe ashe zan sake ganinka?" Dam! Zuciyar Surry ta buga,
Umar-khan zai magana Abba Hakimi ya girgiza masa kawai alamar yai shiru.
A wannan karan ba Yaa Sheikh bai kalli yarinyar dake gabansa ba, sai ƙara ɗauke
idanu yake gefe guda, ganin yadda ya yi mata ya sanya Halisa ta saka hannu ta cire
liƙab ɗin tare da matsawa gaban Yaa Sheikh ta ce "Baka gane ni ba? Nasan ka gane ni
ni ce fa Halisa Danejo Rome ka manta ni?
Ina kaje bana ganinka?" Tarin makami da ya yiwa Saif-wazir yawa ya sanya ya
hangame baki, anya yarinyar nan ba aljana bace ko kuma wacce Aljanu suka shafa?.
Khalil Ahmad Sarki ya juya da sauri ya kalli El-bashir dake can gefe ɗaya yana
waya, ya ƙara juyawa ya kalli Halisa wacce ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa tana yiwa
Yaa Sheikh rantsuwar Wallahi ya gane ta yana sani yaƙi kulata. Ahmad Sarki da har
yanzu yake kallon Danejo sai ya juya ya kalli El-bashir makami kamannin su na
rikita masa lissafi musamman da yaji muryar Danejo wacce take iri ɗaya data El-
bashir sak! Sai dai ita ɗin macace saɓanin El-bashir da yake namiji. "The wonder
never ends" Khalil ya furta a fili na dafe kansa.
Danejo ta ce "Yanzu baka gane ni ba, nice fa? har ka taɓa bani mangoro?" Yaa Sheikh
ya ware fararen idanunsa sosai tare da sauke ganinsa akan zagayayyiyar fuskar ta,
kai tsaye ƙwayar idanunsa ta shiga cikin nata. Danejo ta haɗiye sauran maganar sbd
idanun Yaa Sheikh da sukai mata kaifi, a kallo ɗaya da ya yi mata ya saka mata
shakkar shi, tsoro da kuma ganin girman shi. A hankali ya zame hannun yana mai
barin wajan Danejo ta bisa da idanu..
"Kin san shi ne?"

Please Login or Register in order to submit comment