You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi
hakan" ya shiga safa da marwa He was completely at a loss, unable to understand
what she was saying to him. "Nayi masa da baibayi ta ko'ina ina da investigator a
cikin ma'aikatan dake aiki a can gidansa na Madina" yana faɗin hakan ya fice rai
ɓace.
"Well-done El-bashir Ahmad Nuran Sarki, kana yin komai bisa tsari kamar yadda aka
shirya" Fulani Atine ta faɗa tana bin bayansa da kallo. Ma martaba Ahmad Sarki ne
ke tafiya shi da Khalil yana yi masa bayanin sauyawar da El-bashir ya yi cikin
kwana biyu. Mai martaba na ƙoƙarin yin magana El-bashir yazo ya shige ta gabansu
tamkar zai ta shi sama, meke damun El? Kamar wanda ya zauce ko wani abu ya taɓa
tunaninsa? "That's what am going to tell you, El ya sauya ko dai akwai abin da yake
faruwa ne?" Mai martaba ya numfasa bai ce komai ba ya shige babban sashinsa, Khalil
kuma ya nufi wajan Oum Juwairah.

Halisa na zaune tana duba Assignment ɗin da aka bata juya littafin kawai take amma
ta rasa ta ina zata fara. Tunda ta dawo gida bata ji motsin Yaa Sheikh ba, ko taji
Ummul ta ce akai masa abinci. Ta miƙe tsaye jikinta sanye da wata riga mai kyau
wacce tazo mata iya gwiwa wandon jikinta 3gauter ne. Zahrah data fito daga ɗakinta
zuwa parlour hannunta riƙe da plate ɗin da aka soya masa ƙwai ta kalli Halisa ta
ce. "Ke ubanwa ya ce kina saka wannan kayan a cikin gidan nan?" Halisa ta kalleta
ta ɗauke kai ita bata ita take ba "Kan uba? Ke dan ƙaniyarki ni sa'ar ta ruga ce
ina magana kina jina?" Halisa ta murguɗa baki cikin tsiwa ta ce "Ban ɗauka magana
ki ke ba" hannu ta ɗaga zata wanka mata mari taji an riƙe hannu, ƙamshin Roja daya
cika parlourn ya gama shaida mata wanda ya riƙe ta. Ta juya da sauri har lokacin
yana riƙe da hannunta ta ce.
"My Excellency yarinyar ta fara raina ni ne, ka barni naci.." wata kyakkyawar tsawa
ya daka mata wacce bata taɓa jin irinta ba, Halisa ta firgita da tsawar ga Yaa
Sheikh ta kwasa da gudu zuwa part ɗin Ummul tana haki.
Zahrah ta ce "Tsawa kai mini akan wannan mara gata da ƴancin ƴar aiki na ce ita ga
Yaa Sheikh?" Ya saki hannunta fuska kame yana gyara yanayinsa ya ce.
"Ba a kanta ba,
Akan zagin da ki ke mana, idan zaki ki bari kije waje" ya faɗa a taƙaice
kwarjininsa yasa Zahrah kasa tanka masa a ranta kuma ta ɗauki niyyar cin uban
Halisa. Cike da kissa da buƙatar mijinta kusa da ita, cikin dake jikinta ya ƙara
sanya mata son kasancewa da namiji ƙwarai da gaske. Ta rungome Yaa Sheikh tana
shassheƙar kuka ta ce "Amma kasan ni ba sa'ar ta bace, kawai zan mayar da ita,
tunda akwai masu aiki a gidan" ya yi mata shiru shi dai bai kuma hanata rungome shi
ba, kallo ɗayan da ya yi mata ya karanci yanayinta. Ganin abin da take ƙoƙarin yin
yasa Yaa Sheikh faɗin. "Asstagafirullah Allah" Zahrah ta tsaya tana kallon shi
kafin ta ce "what do you mean by that? Am your wife exit?" Ya zameta daga jikinsa
tare da juyawa zuwa part ɗinsa sai da ya kusa shigewa ya ce
"Lokacin Sallah, akwai alwala tare dani" tai murmushin jin daɗin ganin ya juya da
alama alwalar da yake riritawa ta lalace dalilin rungumar shi da tayi. "Shikenan,
anjima zan zo" ta juya zuwa nata part ɗin.
Ummul ta kalli Halisa dana cewa "Wannan hakin fa? yana da kyau ki nutsu sosai matar
malam" Halisa ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na tsorata sosai Ummul, Allah yasa ba
dokan Anti Zahrah ba" Ummul ta dubeta ta ce "Doka wanne iri, ni wannan Assignment
ɗin naki ba Abin da na gane, kije wajan Abban naki" ta kwanta cinyar Ummul tunanin
Dadarta ya faɗo mata a rai. Tai shiru can kuma ta ce "Ummul Abba mijina ne ko?"
"Me ya sa kike tambaya matar malam?" Cewar Ummul. Halisa ta miƙe zaune zance na
cinta ta ce "Ummul naji baya ce mini matar shi, kuma ni bana son naga Anti
Zahrah..." Wayar Ummul tai ƙara hakan ya hana Halisa ƙarasa maganar. Bayan kammala
wayar Ummul ta ce "kije ya duba littafin naki,ko a buge ki a makaranta" Halisa ta
ɓata fuska ta ce "haka kurum ya dakeni, zaro ido naga ya yi fa?"

"Ko zai daki kowa,
Ai banda matar malam, kawai baya son taurin kai ne, kuma na lura kina da shi tun ba
yau ba" Halisa zata sake magana Ummul ta ce "Tashi kije, sai ki dawo kici dinner
muyi karatu" ta miƙe tana ɗora hula akanta tana tafe tana waƙa da fillatanci. A
hanya taci karo da Bara'at tai mata murmushi.
A hankali ta shiga parlourn dake part ɗinsa, gaba ɗaya baya cikin parlourn sai
kyakkyawan ƙamshin daya bari wanda yake tashi a hankali, tabi ƙofofin dake parlourn
da kallo ta rasa wanne Kofar bedroom ɗinsa, a hankali take tafiya kamar mara gasky
tana raɓewa jikin bango ta shiga leƙa wani ɗaki tsarin bedroom kaɗai ya tabbatar
mata shi ne. Ji tayi an tsaya a bayanta ta juya da sauri taci karo dashi tsaye
towel a hannunsa yana tsane gashin kansa daya kwanto, ganin ruwa na zuba a jikinsa
tasan wanka yayi, maimakon taji kunya a matsayinta cikakkiyar bafullatana sai ta
zubawa wani waje a jikinsa ido. Ya tsare ta da idanu.
"Abba" ta faɗa dimple ɗinta na lomawa ya ɗauke kai ya ce. "Me kike leƙe? Kin yi
ajjiya ne?" Ya tambaya yana bata hanya ta tura baki fuska a narke sai juya bakinta
take ta ce "Ummul ta ce ka koyan karatu, ni ba kai nake nema ba" ya dubi bakin
maganar da kyau, ya ɗauke kai wato fushi take har yanzu.
Ganin yaƙi bata amsa ta saki kuka tana juyawa zata bar wajan, ya damƙi hannunta ya
dawo da ita gabansa. Cikin kula da tausasa harshe ƙamshin shower gel yana fita daga
cikinsa ya saka hannu tare da tallafo haɓarta ɗaya hannun ya dafa kanta dashi, tayi
saurin riƙe ƙugunsa da duk hannunta biyu.
"Abba" ta ƙara faɗa idanun na cika da hawaye wanda suka ƙarawa idanunta sheƙi.
"Rigima dai matar malam, nayi busy banje makaranta ba" ta tsora masa idanu masa
idanu tana ƙara riƙe ƙugunsa ta ce "To darasi zaka duba mini, Abba kuma me ya sa
Anti Zahrah take riƙe ka" ya saki fuskar yana dafe kai ta saki kuka zata juya ta
fita ya saka hannu ya ɗaga ta cak tare da yin bedroom ɗinsa da ita...


If you read for free it's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity
bank shaidar biya 08119237616.
[1/3, 4:48 PM] Abk: Kokawar ƙwace kanta take amma ta kasa ya sauke ta saman kujerar
dake kusa da bed ɗin ɗakin nasa, bai kula ta ba ya nufi deep freezer ya ɗauki Apple
guda ɗaya wacce tai sanyi. Cikin nutsuwarsa da son kame kansa daga yanayin da yake
ciki ya nemi waje saman gado ya zauna, kyakkyawan numfashi ya sauke yana ƙara
daidaita kansa a karo na babu adadi. Ya ɗago kai yana duban direction ɗin da take,
dole sai ta sanya ma gantu ya miƙa hannu cikin taushin murya ya ce..
"Zonan naji, rigimar me ce?" kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake domin bata iya
bijirewa umarninsa. Ya dubeta da kyau amma taƙi yarda ta kallesa cikin son jin meke
faruwa ya kamo hannunta zuwa inda yake zaune muryarsa har kullum a taushashe ya ce.
"Ya akai matar malam? waye?" Hawaye na sakko mata ta ce "Abba kai ne, Mother ta ce
kai miji na ne, me ya sa kake bari Anti Zahrah take taɓa ka" ya dafe kansa cike da
mmkin kaifin bakin Halisa ya ce "Ba zaki bar mganar mijin nan ba? You're too young
to understand that"
"Abba ina son ka ai" Ya girgiza kai ya lura rigima take ji kuma ta shirya bashi
kunya a Idanun kowa. Yana mamakin yadda maganar miji ta zauna a bakinta raɗau kamar
wacce akewa bita akan hakan. Ya dubeta yana dawo da ita gefensa tare da riƙe
hannunta ya ce "Matar Malam ki bar mganar mijin nan, ba zaki gane ba, ki dai bar
Anti ta faɗa ok?" Ta maƙale ka faɗa alamar bata amince da zancan ba kaifin ta ce
"Abba...." Sai kuma tai shiru ya ɗago kanta tare da tallafo haɓarta yana duba cikin
idanunta da hawaye ya kwanta. "Matar malam" ta marairaice fuska tare da faɗin
"Abba yaushe zan zama matar malam ɗin? Kuma yaushe zan zama kamar Anti Zahrah nima
na dinga rungomeka?" Ya kau da fuska tare da lumshe idanunsa a hankali ya ce "Baki
son Antin naki tana haka? Ni kuma fa" ya ƙare maganar yana ƙara riƙe fuskarta a
hannunsa da kyau, gaba ɗaya ta marairaice fuska ita a dole bata son abin da Zahrah
ke masa, haka kurum ranta ke ɓaci taji kuka yazo mata ta ce "Abba zanna yi maka, da
safe da rana, da daddare" ya shafa kanta cikin nutsuwa ya ce.
"Kada mu fara haka, ki tsaya a ƴar rainonki" ta langwaɓe kai ta ce "Abba ni ban son
rainon Ummul ta ce kayi mini karatu" bai biyewa surutun nata ba, ya amshi littafin
nata duk dan a rabu lafiya, burinsa kuma bai shige ta tafi part ɗinsa ba, ko zata
barshi ya samu salama daga surutun nata mara dalili da toshe.
Cikin sauƙin harshen yake mata bayani akan Social studies ɗin, da kuma
muhimmancinsa. Ya kama hannunta ya ɗora saman littafin a hankali ya ɗora nasa
hannun akan nata ya fara nuna mata yadda zatai rubutu, yana lura da ƙwazonta ko dan
akwai son karatun a ranta duk abin da ya nuna mata ɗauke shi take.
Ta ɗago kai ta kallesa taga hankalinsa baya kanta gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa
zuwa ga abin da yake nuna mata.
"Abba" Halisa ta faɗa tana ƙarewa fuskar shi kallon yaƙi kulata ta leƙa fuskar shi
ta ƙara cewa "Abba kana da kyau sosai, kaga gobe idan naje makaranta zance mijina
ne ya yi mini aikin ko?" Nan ma bai kulata ba amma tsat yake ɗauke zancan nata a
zuciyarsa tasbihi kawai yake. Taja gemunsa cikin sauri ya miƙe tsaye yana damƙa
mata littafin tare da janta zuwa bakin ƙofa kamar an masa dole ya ce. "Ki kula,
akwai sanyi" ta ɗaga kai tana faɗin "To Abba" har ta juya zata fita ta dawo da
sauri zuwa bedroom ɗin Yaa Sheikh kuma a lokacin ya juya hannunsa ɗauke da azkar na
dare yana dubawa..
Kyakkyawar rungumar data bashi da baya ya sanya Azkar ɗin suɓuce masa cikin In-inar
data zo masa a lokacin zufa na yanko daga goshinsa ya ce.
"Yaaa....yaaaa... Allahu ya ya... Ya Rahman, Yasubuhanallah" ta saki dry tana
riƙesa ta ce "Abba kaga nayi maka ta dare sai da safe" kasa magana ya yi tana
sakinsa ya buɗe ƙofar bathroom ya shige ciki... Cikin farin ciki da murna yau itama
tayi abin da Anti Zahrah keyi ta nufi part ɗin Ummul. Ummul ta kalleta ta ce "Kin
dai gane karatun ko?" Ta ɗaga mata kai kawai tana jan plate ɗin da Ummul ke mata,
tana cikin cin abincin ta ce "Ummul kin same?" Ummul ta girgiza kai ta ce "Sai kin
faɗa matar malam" Halisa ta ture abincin dan ba wata yunwa ta keji ba ta ce.
"Me ya sa gumi ke fitowa a goshin Abba? Kuma naga wani abu a jikinsa ba, duk sanda
na gani kaina juyawa yake" Ummul a zuciyarta addu'a take Allah ya sa ba wata
maganar da zata bata Kunya zatai ba, ko wani abu ne ya faru tsakaninta da Yaa
Sheikh ɗin take son faɗa, duk tai mamakin haƙurinsa, daya kawo har yanzu, ta riga
tasan waye Yaa Sheikh da kuma yadda ya ɗauki al'amarin Halisa da girma ko yana jin
tsoran yanayin rigima da ƙuruciyarta ne?.
Halisa ta dawo da Ummul daga tunanin data tafi ta hanyar faɗin "Ummul ni ina son
Abbana" Ummul ta ce "Kina iya bakinki, ba dan abinci kawai Ubangiji ya bamu ciki
ba, hadda ɓoye maganar da bata da ikon a faɗa da riƙe sirri, ki nutsu idan kina
wannan shirman Abban naki ba zai so ki ba" Halisa ta kwanta tana juyawa Ummul baya
ta ce "to naga mijina ne, kuma ina son sa" kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri
domin abu biyu ne ya faɗo mata a wannan lokacin, da maganin da El-bashir ya bata,
wanda take tunanin shi ne ya sanya Abban nata Yaa Sheikh yake fitar da zufar
goshinsa, sai kuma tuna Dada da tayi.
Ummul tabi bayanta da kallo sai kawai ta girgiza kai ta ce "Ubangiji ga Danejo ka
shirya mana ita, Allah ka kawo zama na har abada tsakaninta da Aliyu, ita ce farin
ciki Aliyu, Aliyu shi ne garkuwarta"

Halisa na fita ta nufi part ɗin Zahrah lokacin tana tsaye gaban madubi sai turare
take fesawa ajikinta, ta sanya wasu kaya kamar zata gasar rawa a club Halisa ta ce
"Anti" ta juya ta kalleta ta ce "wai ke wacce daƙiƙiya ce ne? Ko acikin ƴan fulani
ke daban kike, kawai ki faɗo ɗaki kamar wata dabba?" Halisa taji zagin har ƙasan
zuciyarta ta kalli Zahrah ta ce "me ya sa kike haɗani da dabba? Bayan ni mutum ce
kamar ke?" Zahrah ta tsaki ta ce "baki da wani suna da ya shige haka, and you'll
never be like me never" ta goge hawayen idanunta ta ce "Yaushe zan miki aikin ki?
Ina son ki mayar dani rugarmu, ban san haka kike ba kinyi al'ƙawarin kula dani da
kuma Dadata" Zahrah tai wata dry ta ce "Aikin kin kusa gabatar da shi, dan kin gama
zan mayar dake nima zamanki bai mini ba, yanzu bani da lokacin zani wajan mijina"
Halisa ta kalleta da sauri zuciyarta har ɗagawa yake sbd jin zata wajan Yaa Sheikh.
Ta juya idanunta fal hawaye tare da barin ɗakin. Zahrah ta nufi part ɗin Yaa Sheikh
ko'ina na part ɗin gwanin sha'awa ne, ko wacce kusurwa an kafe kalmar sunan Allah,
a hankali sautin ƙira'ar Alkur'ani ke tashi, amma ta nemi ƙofar bathroom ɗin nasa
ta rasa. Ta juya da sauri zuwa sashin Ummul ta sameta tare da Bara'at daga tsaye ta
ce "Naje part ɗin Yaa Sheikh na rasa ina ne bedroom ɗinsa, ina buƙatar sani sbd ina
son kasancewa da mijina"
"Amma shi mijin na son kasancewa dake?" Cewar Ummul. Zahrah ta ce "Ni matarsa ce,
dole ya buƙace ni" Ummul tai murmushi ta ce "Zahrah ki zauna muyi magana mai
muhimmanci, maybe ki gane sosai" Zahrah ta ce "ki riƙe maganarki mijina nake
tambaya" Ummul ta ce "Malam yana kan rabuta Alkur'ani yanzu, kafin azumi yake son
kammala rubutun, ba zai iya ganin kowa ba" Zahrah ta juya rai ɓace gashi masifa ke
cinta kamar taci babu.
Ummul bata da zaɓi wanda ya shige faɗin hakan, tasan ba lallai Zahrah ta samu abin
da take so ba. Washegari tun da Halisa ta tashi bata da wani karsha shi ta wakana
da tunanin ko Zahrah ta je wajan Abbanta? Tai sallah Asuba tare da Azkar ɗin da
Ummul ta bata, 6:30 ta nufi kitchen tasan a nan zata samu Ummul ɗin, Tana zuwa
Bara'at ta ce "Sannu da zuwa Halisa" Suhaima ta ce "Baki zo da wuri ba" tai
murmushi kawai ta ce "Ina kwana Ummul?" Cike da farin ciki Ummul ta ce "Allhmd.
Sanyi bai ka maki ba?" Ta ɗaga kai tana taya Bara'at aiki tare da ita suka kammala
breakfast. Ummul ta bata shayin Yaa Sheikh ta kai masa bayan ta shirya zuwa kayan
makaranta. Ta amshi shayin ta mufi part ɗinsa kai tsaye.
Fitowar sa kenan sbd barcin da bai samu ba jiya, kana kallon yanayinsa da sauyin
idanunsa kasan akwai matsala. Yana zama kan kujera ta shigo bakinta ɗauke da
sallama ta ajjiya tray ɗin tana zubewa wajan ƙafafuwansa ta ce. "Abba ina kwana?"
Ya jinjina tare da zuba black tea ɗin ya shiga sha a hankali ta gyara zama ta ce
"Abba" ya ware ido a kanta ba tare daya tanka ta ba. Ta ce "Anti Zahrah ta zo
jiya?" Hawaye ya cika idanunta ganin ya kasa cewa komai, zai gumi dake tsastsafo
masa ta goshinsa jijiyoyin kansa sun ta shi. Ya ajjiye mug ɗin hannunta bayan ya
gama shan tea ɗin tare da miƙewa tsaye, ta miƙe da sauri ta ce "Abba baka da
lafiya?" Sai a lokacin sauke numfashi yana jin kansa kamar zai rabe yana ɗan yin
gaba ya ce.
"Ki kula,ba wasa" ranta bai mata daɗi ba, shi kansa ya kasa riƙe sauyin nasa gudun
kada wani ya ankare baya son kuma Ummul ta san halin da ake ciki... Ta fita tana
jin kamar kada taje makarantar.
Har ta yini a makaranta cir bata da wata walwala haka kurum ta tsinci kanta cikin
sukuni, Abir tai ƙoƙari sosai wajan fahimtar da ita duk subjects ɗin da sukai
attending. Har suka taɓa hira sai lokacin ma Halisa ta saki jikinta jin Abir itama
asalinta ƴar Nigeria ce.
Yau ma Umar-khan ya dawo da ita ya lura da sauyin nata bai kulata ba, tunda ba
huruminsa bane yin magana da matar malam ɗin. Tana shigowa gidan bata nufi part ɗin
Ummul ɗin ba, ta nufi Main parlour zata shige part ɗin ta Zahrah ta ce.

"Yawwa ke nake jira dama, ki shirya zamu asibiti" Halisa ta kalleta tana mmkin waye
babu lfy kuma? Sai kuma gabanta ya faɗi ko dai Abbanta ne bashi da lfy, ta rikice
rikicewar da Zahrah taso ta ɗaure mata kai ta ce.
"Bana son shirme mene haka kuma? Kije kafin mu tafi ki gyara mini ɗaki kizo ki ɗan
danna mini ƙafata" Halisa ta tsurawa cikin Zahrah idanu har bata ji abin da Zahran
ta faɗa ba, tayi saurin jan riga ta rufe cikin da ya ƙara girma fiye da ko yaushe.
Ta juya tare da shigewa part ɗin nata, duk ta gigice tana shiga kuma ta fara duba
maganin da El-bashir ya bata, ƙila shi ne maganin da Abban nata yake sha bata sani
ba. "Kayi haƙuri Abba, laifi na ne" ta faɗa a sanyaye idanunta na cika da hawaye.
Zahrah ta miƙe tare da shigewa ɓangarenta, kai tsaye wayarta ta ɗauka tare da kiran
number Deen, kamar wanda yake jiran kiran nata yai picking call ɗin ta ce "Akwai
matsala Deen" ta cikin wayar ya ce.
"Yanzu muka fara samun matsala idan har ba zaki abin da ya dace ba, yanzu mene?" Ta
ce "Cikin nan girma yake, yau ƴar fillon nan ta gani amma kamar bata gane ba, kasan
kamar shirme ya yi mata yawa, shi ya sa na zaɓi nayi aikin nan da ita" Deen dake
zaune idanunsa sauke akan wata Balarabiyya dake ɗakinsa ya ce.
"Kada ki damu da wannan ƴar fillon na yanke shawarar abin da za mu yi mata, kawai
ki tabbatar Yaa Sheikh ya samu kusanci da Halisa, ki daure ko a tea ne ki zuba
maganin feeling ɗin, yana da ƙarfi sosai" Zahrah ta sauke numfashi ta ce "Amma kada
a raunata ƴar mutane, nice daidai da Yaa Sheikh mai zai hana ni naje gareja bana
tunanin zai gane bani da budurci" Deen yaja tsaki sosai ya ce "Kina da matsala
Zahrah,ki fito kice bana gamsar dake mijinki kike buƙata tunda naga alamar ba sanya
a wannan ɓangaren ba, listing to me Zahrah nasan waye Yaa Sheikh, nasan shi sanin
da zaki mamaki, duk yadda kike tunanin basirarsa ya shige nan, duk abin da zai same
shi yana ji a jikinsa, ki tura yarinyar kawai babu damu da duk irin abin da zai
mata ba" ɓoyayyan numfashi ta sauke tare da shafa cikinta wanda ya fara motsawa
alamar yana cikin ƙosashiyar lafiya ta ce "Deen what's your plan?" Ya ce "ban gane
ba? Ina tare dake muke tsara plan ɗin? Are you doubting me?" Ta kasa cewa komai sai
kashe wayar da tayi. Ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗin duk ranar da Yaa Sheikh ya
kusanci Halisa maybe ita kuma zuciyarta ta buga, a ƴan kwanakin nan wata sabuwar
Soyayyar Yaa Sheikh ta wanzu a zuciyarta, duk da bai bata wata dama ta Kasancewa
dashi ba, amma kullum da soyayyar shi take kwana a rai.
A hankali Halisa ke tafiya cikin wasu kayan shan iska sbd sanyin garin ya lafa, ta
sauke numfashi ganin Zahrah bata parlour kai tsaye ta nufi part ɗin Yaa Sheikh, ta
shiga bakinta ɗauke da sallama Umar-khan dake yiwa Yaa Sheikh bayani ya ɗago kansa
tare da kallon Halisa, da sauri ya ɗauke kai ganin kayan dake jikinta, Yaa Sheikh
dake jingine jikin kujera sanye da Jallabiya sabuwa kamar ko yaushe ya miƙe tsaye
tare da amsar ducoment ɗin da Umar ke basa, Umar ya ce "Ban gama yi maka bayani ba"
Yaa Sheikh shiru da Umar ganin haka yasa Umar miƙewa yana ɗauke idanunsa daga kan
Halisa, Ta ce "Umar-khan teacher ya ce gobe ka same shi a officer" ganin kamar bai
jita ba yasa ta sake cewa "Umar-khan, Umar-khan" ta faɗa tana ƙoƙarin bin bayansa
cak taji anyi sama da ita tare da nufar bedroom da ita.....
[1/3, 4:48 PM] Abk: Ya direta gabansa yana binta da gajiyayyun Idanunsa masu kaifi,
ya shiga ƙarewa kayan jikinta kallo can dai ya juya zuwa wani ƙaramin bedroom dake
jikin wanda suke ciki, ya dawo hannunsa riƙe da hawaya bai ce mata komai ba, sai
hannunta daya kama zuwa bakin gado ya nemi waje ya zauna tare da zaunar da ita a
gefensa. "Kina son Allah ya kama ki ne matar malam?" Ta marairaice tana narke fuska
ta ce "Abba me na yi? Kuma wai baka da lfy naji Anti ta ce wai na shirya zamu
asibiti" ya dubeta da kyau tare da kawar da batun Antin ya ce. "Baki san me ki kai
ba? Ki nutsu ƴar fillo" ta tura baki zata ta shi ya tsare ta da idanu sosai kafin
ya yi magana wayarsa ta fara ringing ganin sunan Abba Hakimi yasa Yaa Sheikh ya
danna wayar a handsfree.
"Malam, ina ajjiyata ne?" Halisa tai murmushi jin muryar Abba Hakimi, kafin Yaa
Sheikh ya ce wani abu ta ce "Jon wuro" Abba Hakimi ya saki murmushi ta waya ya ce
"To matar ni dai ban iya yaran nan ba, dama dai Abban naki ne" ta juya tare da
kallon Yaa Sheikh taga idanunsa a rufe amma kamar mai jin zafi duk zufa ta gama
rufe masa fuska sai gemunsa yake shafawa.
"Jon wuro Abba ya iya fillatanci ne?" Abba Hakimi ya ce "Eh sosai, fiye da ke ɗin,
baki taɓa ji ya yi bane?" Ta ce "Jon wuro ai baya nunawa yaji me nace ko da fulde
nai magana, to Bafullatani ne Abban nawa?" Abba Hakimi ya ce "Matar baga ki kusa
dashi ba? Ki tambaye shi, ni dai nasan duk wani motsi na Fulani a idanunsa yake"
tai murmushi kawai har lokacin kallon Yaa Sheikh take shi kuma yaƙi yarda ya buɗe
idanu, amma yana jin idanunta na yawo a jikinsa.
Abba Hakimi da yaji shiru ya ce "Abban naki yana kula dake? kuma yana kusa yanzu"
da sauri ta ce "Ai shi ya ɗauke....." Tattausan hannunsa da taji a bakinta yasa
tayi saurin zaro ido suna haɗa idanu ya ware mata ido yana ya mutsa fuska gaba ɗaya
yanayinsa ya sauya jin tunan asirin da take shirin yi masa. Ya miƙe baki ɗaya yana
daidaita zamansa ya zagaya hannunsa ɗaya ɓangaren nata.

"Shhhh" ya ce yana tare da yi mata alamar tai shiru. Abba Hakimi ya saki murmushi
daga wayar kafin ya ce "Da alama kinyi nisan kiwo, ki bawa Abban naki" ta sauke
numfashi bayan Yaa Sheikh ya zare hannunsa daga bakinta cikin ƙasa da murya ta ce.
"Jon wuro Abba ya ce nai shiru kada nace ya ɗauke ni" tamkar Yaa Sheikh ya ce ya
shiga uku haka yaji shi kam tayaya zai fara nuna mata illar surutun nan? Abba
Hakimi ya yi kamar bai ji ba ya ce.
"Me kika ce, ntwrk na rawa" Yaa Sheikh ya zare wayar tare da kashe handsfree ɗin a
hankali ya manna wayar a kunnansa ya ce.
"Abba" ya faɗa tamkar baya son maganar. "Aliyu" Abba Hakimi ya kira sunan cike da
girmama kamar yadda yawancin lokaci yake ambatar sunan kai tsaye. Yaa Sheikh ya ce
"Uhm".
"Ina fatan baka mance deal namu ba, ka watsa mini ƙasa a idanu, kai tsaye na nuna
buƙatar ka zauna da yarinyar nan, amma ka ce baka sonta? acikin shekara munci sati
ko sama da haka, kamar yau Ubangiji zai nuna mini cikar shekarar. Wallahi Aliyu
naga saɓanin yadda muka ajjiye yarjejeniyar zaka san bani da kirki zaka san waye
Ostman-zannur" Yaa Sheikh ya juya tare da kallon ƴar rainon da ake kafa masa
sharuɗa akanta cikin lafazi mai kyau ya ce. "Abba zan dawo da ita"
"Alfarmar riƙon nata ne ba zaka iya ba?" Yaa Sheikh ya ɗan ya mutsa fuska kaɗan ya
ce "Ramadan zai zo Abba, ba lokaci ba zan iya ba" sautin murmushin Abba Hakimi ya
ratsa kunnan Yaa Sheikh ya ce "Kai kaɗai ne a gidan? da wasa ka bari Matarka taci
zalin Halisa wallahi sai nayi maganinku duk" kafin Yaa Sheikh ya sake cewa komai
Halisa ta miƙe tare da zama kan ƙafafuwansa tare da zagaya hannunta ta riƙesa da
kyau ta ce.
"Ina son ka Abbana, kuma...." Ƙitt Yaa Sheikh ya kashe wayar baki ɗaya yana rufe
idanu tare da dafe kansa da hannu.
Tuni Abba Hakimi yaji abin da Halisa ta faɗa kafin Yaa Sheikh ya kashe wayar.
Halisa ita bata ɗauka wani abu tai ba ta ce "Abbana, ni ma kace kana so na" ya
sanya hannu ya share zufar dake binsa kafin ya buɗe ido ya kalleta a

Please Login or Register in order to submit comment