You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin da sauri ya maƙala
mata, yana ƙoƙarin janye jikinsa ta ɗora hannunta a tsakiyar tafin hannun shi..
"Uhmmm" ya ce a ransa yana ɗaga idanunsa zuwa gareta ya kalli cikin idanunta ba
tare da ya ce komai ba, Halisa ta sake damƙe hannunsa da kyau cikin rawar murya ta
ce. "Usako miyetti masin" idanu kawai ya lumshe mata tare da matsawa waje guda.
A fusace Zahrah ta kunce blet ɗin jikinta tare da tashi tayi kan Halisa tana kumfar
baki ta ce.
"Ke dan uwarki mijina sa'anki ne da har zaki faɗa kansa da ƙazamin jikinki? Shegiya
mara ƴan ci" Halisa ta kalli Zahrah ta ce "To Anti godiya nayi masa fa, kuma dana
faɗa ƙasa naji ciwi ba ƙwara na faɗa kan shi ba, kuma ai ban masa nauyi ba ko kaji
ciwo?" Ta faɗa tana juyawa tare da kallon Yaa Sheikh, shi gaba ɗaya hankalinsa baya
kansu hannunsa riƙe da darija yana dubawa, tuni ya mayar da hiramin kansa baya
buƙatar kowa yaga wani sashe na jikinsa.
"Kauuu!!" Zahrah ta ɗauke Halisa da mari tare da nuna ta hannu ta ce "zanci uwar
data haifi babarki" ƙarfi da girman zagin yasa Yaa Sheikh kallon Zahrah a zuciyarsa
yana Istigifari bai ɗauka wani zai iya zagin ba, ba a taɓa zagi a gaban shi ba,
hakan ya zama abu sabo a gare shi. Bai ce komai ya ɗauke kai tare daci gaba da duba
jaridar hannunsa, zafin marin yasa Halisa fashewa da kuka sosai tana kifa kanta a
cinyarta, kuka take sosai wanda rabin kukan baƙin cikin zagin da Zahrah tayi mata
ne. Yaa Sheikh kukan yake ji har tsakiyar kansa jin kukan na neman tarwatsa masa
kai yasa ya miƙe tsaye tare da buɗe wata ƙofa ya shiga.
Zahrah ta kasa haɗiye mamakin yadda Yaa Sheikh ya nuna kulawa ga Halisa, haushin
abin da ya yi yasa ta huce akan Halisa ɗin.
Sun yi nisa da tafiya sosai wata maid ta shigo cikin wajan tana tambayar Zahrah me
za a kawo musu, Zahrah ta karɓi abin hannun matar ta duba, kana ta zaɓi abin da
take so. "Nace ko zaki iya sauyawa wannan yarinyar waje?"Flight attendant ta ce.

"Her name please?" Zahrah ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Something Halisa.." ta ɗan
danna wani abu a jikinta tare da yin magana bayan ta gama ta ce. "I think ita ce
Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu right Maah?" Zahrah ta ce "No, bana tunanin ita ce
her name is Halisa Danejo Rome" Flight attendant ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce
"Sorry Maah babu da wani suna a jerin wanda za su yi tafiya yau, Halisa Sheikh
Aliyu haydar Aliyu shi ne" A fili Zahrah ta ce "Kan uba" sai yanzu ta tuna sunan
Yaa Sheikh kenan, da sunansa akai mata visa kenan?.
"Oh maybe she's the one, zaki iya sauya mata wajan zama?" Matar ta ce "Yes Maa,
daman yanzu na duba ta samu sauyin wajan zama tuni" Zahrah tai murmushin jin daɗi
matar ta kalli Halisa wacce ko inda suke bata kalla ba sai Ajjiyar zuciya take
saukewa.
"Can you follow me please?" Zahrah ta ce "ki mata hausa maybe she understand you"
matar tai murmushi ganin yadda Zahrah take kwaɓe fuska ta ce "But she's your
daughter?" Wata uwar harara Zahrah taiwa matar ta ce "Kinga alamar ina da ƴar ne?"
Ita ma tai murmushi ta ce "Ai babu mmki idan nace miki a tunani zaki haifi yara
biyar ma" Zahrah ta kalli jikinta da kyau ta kasa cewa komai, sbd baƙin cikin
Flight attendant.
"Halisa biyo ni kinji" a sanyaye duk da tsoran jirgin da take tabi bayan matar har
zuwa champer 2 na jirgin. Nan ma dai kujeru biyu ce kawai a wajan ba kowa, ta nemi
waje ta zauna cike da tsoro.
Not too long da zamanta ya shigo tare da zama kan kujera da sauri ta sunkuyar da
kanta domin a tunaninta faɗa zai mata, sai taga mai kulata ba ƙafarsa kawai ya
miƙe. Tana zaune aka turo basket na abinci, zallar fruits ne sai gorar ruwa, aka
ajjiye a gaban Yaa Sheikh ita kuma aka ajjiye mata chips da egg sai haɗin salad da
ruwa. A hankali ya ɗauki orange ya saka bakinsa ya shiga taunawa cikin nutsuwa,
Halisa ta kalle shi bakinta na rawa ta ce.
"Amma wannan abin yabann sha'awa ɗan sammani" ya jita sarai amma yai mata banza sai
da orange ya ɗin ya rage guda uku ya ɗauki guda ɗaya zai ƙara sakawa a bakinsa tayi
saurin riƙe hannun shi, bai zaici haka ba ya kalli hannunta tare da kallon gefen
fuskarta ta langwaɓar da kanta gefe ta ce "Ayya ka sammin bana, ni ma idan kaga
abuna zan maka naga kana ta haka da idanu" yabi idanunta da kallo yadda ta lumshe
su tare da buɗewa tana gwada masa yadda yake, ta kwance na hannunsa tare da kawai
bakinta, ta ɗauka wani daɗi ne a orange ɗin.
Ya sauke numfashi ganin hannunta na neman taɓa dugun gemun shi cikin ƙasa da murya
mai sanyi ya ce. "Ci kani" ta yi saurin saƙona tana komawa wajanta, bai ƙara taɓa
komai ba a kayan sai ruwa daya sha sosai.
Misalin 10 na dare jirginsu ya sauka a Prince Muhammad bin Abdul'aziz International
airport, sai nasarwa ake kowa ya saka blet jirgi zai sauka, ganin bata fahimci me
ake cewa ba ya kalleta da kyau, ya riƙa ya saka blet a jikinsa ba damar cirewa kuma
sun ɗan bada tazara, a hankali jirgi ya fara girgiza yana rawa Halisa ta rikice
daga tai nan sai tayi nan, shuuuuu jirgin ya yo ƙasa tai gaba luuu zata kifa shiru
tayi jin an riƙo kafaɗar ta, ya haɗa da gefen ƙirjinsa tare da riƙeta.
Ƙuri tayi masa da idanu ganin nasa idon a rufe ta kasa motsawa shima kuma bai
saketa ba, tunda har lokacin jirgin bai gama daidaita ba, balle ya samu damar sauka
a titinsa. Ɓangaren Zahrah sosai taji daɗin ganin an ɗauke Halisa yanzu zata samu
damar kasancewa da mijinta hankali kwance, sai dai tun tana jiran dawowar shi amma
shiru gashi bata da ikon tambayar wani, bisa dole tai shiru. Bata tsammaci abin
haka ba, sai ji tayi ana faɗin sun ƙarasu Madina tuni ai. A hankali ta saka blet
tasan dai dole tare zasu tafi gida. Jirgi na yin parking ya saketa da sauri kafin
ta buɗe ido ya fice daga cikin wajan, ta shiga zare idanu yanzu idan guduwa sukai
yaya zatai?. Tana wannan tunanin Umar-khan ya shigo yana murmushi ya ce "Matar
Malam tasu muje" ta miƙe tana kallon Umar-khan ta ce "To kai gida kaje ka dawo ne?"
Yai dare ya ce "Hhhhhh ai kam na koma Nigeria na dawo" tabi bayansa da sauri ta ce
"Kasan me" ya ce "sai kin faɗa" ta lumshe idanun ta buɗe ta ce "A ciki da abin ya
tashi sama kawai na faɗa kan Malam na ɗauka zai dukeni kamar yadda anti da dake ni,
sai naga kawai ya lumshe idanu ni kam nace masa na gode"

"Uhm" kawai Umar-khan ya ce domin bashi data cewa a wanann batun, suna fitowa
Zahrah na fitowa suka kalli juna da Halisa kowa ya ɗauke kai. Bayan sun sauka daga
jirgin Zahrah ta kalli motar dake gabansu ta ce "Ina My Excellency?" Ya ce "Yana da
meeting ne, sai zuwa 12 zai dawo" Zahrah ta ce "meeting da wannan daren?" Umar-khan
ya ce "Manyan mutane daman sai dare suke meeting, muje kada mu ɓata lokaci" Zahrah
ta shiga bayan mota Halisa ba haka, Umar-khan na gaba shi da driver.
Wata haɗaɗɗiyar area suka nufa gaba ɗaya mazauna wajan larabawa ne, gidan dake kusa
da na Yaa Sheikh sune hausawa, faɗar kyau da tsarin gidan Yaa Sheikh ɓata baki ne,
flat gida na zamani, motoci birjik a harabar gidan ga tarin flowers da ɓangaren
swimming pool, ga
Wajan tsuntsayen shi kusan duk rubutun gidan da rabci ne, yana da ɓangare na
Musamman da yake bawa manyan mutane darasi.
Zahrah ta dubi haɗaɗɗan parlourn mai ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru, sai ƙamshi
yake, ga wasu fitito masu kyau iya haɗuwa ya haɗu. Umar-khan ya kammala shigo da
kayansu ya ce. "Ɓangare uku ne a gidan, wancan ɓangaren Yaa Sheikh na tsakiyar
kenan, na gefen dama babu na kowa na hango ma babu kowa, ya ce ki zaɓi wanda kike
so, ɗayar ki bawa mai aikin naki" Zahrah ta kalli part ɗin hannun hango taga bayan
na Yaa Sheikh yafi kyau dan haka ta ce "Na ɗauki na ɓangaren hango ka shigo mini da
kayana ciki" tana faɗin haka ya miƙa mata key ɗin ɓangaren ta amsa hana shigewa
ciki. Ya kalli Halisa ya ce.
"Daman girman kine shiga ɓangaren damar" murmushi kawai tayi, Umar-khan ya riga
yasan da ɓangaren Yaa Sheikh da wanda Halisa zata zauna a manne suke, domin akwai
ƙofa kai tsaye daga ɗakin Yaa Sheikh wacce zata kawo shi ɓangaren Halisa ɗin. Ya ja
mata kayan zuwa jiki, ya yi mata bayanin komai da kitchen da banɗaki komai dai,
kana ya nuna mata yadda ake amfani da kayan kallon ɓangaren ta.. "Sai da safe Matar
Malam" ta jinjina masa kai. Zahrah ma ya kai mata kayan kana ya nufi nasa gidan.
Misalin 1:30 motar Yaa Sheikh tai parking driver ya buɗe masa ƙofa, a hankali ya
fito ya ɗan tsaya yana duba ko wanne ɓangare yana yin addu'a sbd ya saba, ganin
hadari a garin kuma yasa duk ya rufe Windows na gidan. Ya nufi ɓangaren shi, wanka
ya yi ya ɗora jallabiya mai kyau a jikinsa, black tea yake son sha amma bai san
yarda zai ba, gashi kuma yasa a sallami masu aikin shi. Haka dole ya zame
jallabiyar ya saka kayan barci yana buƙatar hutawa sosai, sbd ya samu peace of mind
kwana biyu yana stressed kansa da yawa. Kiran sallar farko a kunan Yaa Sheikh da
Halisa domin zamanta wajan mother ta saba da tashin asuba, a hankali ya nufi
bathroom tare da sakarwa kansa ruwa mai zafi kana ya yi alwala tare da yin brush,
cikin zafin nama ya shirya cikin kyakkyawar shigar shi wacce ya saba, farar
jallabiya ya ɗora hirami a kan shi, bakinsa ɗauke da aswaƙ ya nufi Masjid Malik
wanda shi ke gabatar da jam'i a can, bayan idar da Sallah ya yi karatu wa jama'a
kamar yadda ya saba.
7:00 ya shigo gidan da mmki yake jin parlour ƙamshi mai daɗi, yana ƙoƙarin shigewa
part ɗin shi ta ce "Jamɓanduna?" Jin fillatanci yasa ya fahimci ba Zahrah bace
amanar shi ce kuma ƴar riƙonsa, ya juya tare da kallon ta, tana cikin wata duguwar
riga mai kyau plush pink sai baby hijab a kanta, kai ya ɗauke ta ce.
"Anti Zahrah ba ta shi ba, ni tun ɗazo na tashi ina ta kallo" shi dai bai ce komai
ba ya shige part ɗinsa tabi bayan shi da kallo kafin ta juya zuwa kollon girke-
girken da ta keyi.
Yana shiga part ɗin sa ya zauna saman kujera, tare da kiran number Umar-khan babu
jimawa ya ɗauka a nutse ya ce "Ka yi komai, kada ya shige kwana biyu a nemi gurbin
karatun" yana faɗin hakan ya kashe wayar, tare da kiran wata number mgn ɗaya ya yi
ya kashe..
Halisa na zaune taji telephone line na ƙara ta miƙe sauri daman Umar-khan ya faɗa
mata yadda ake amfani da ita, tana ɗagawa taji ance "Mrng maaa, the breakfast is
ready Yaa Sheikh na jira" Halisa ta ce "Kika ce me?" Ta ce "Abincin Yaa Sheikh ya
kammala kina magana da ɓangaren kitchen, yanzu maid zata kawo" Halisa ta taɓe baki
tare da komawa ta zauna, babu jimawa wata mata mai fararen kaya ta shigo ɗauke da
tray da butar shayi ta ce "Mrng Maa ga shi Yaa Sheikh na jira"
Halisa ta amsa tana miƙewa tsaye Zahrah ta fito cikin kayan barci da alama ko
sallar ba tai ba, ta kalli matar ta ce "lafiya?" Tai mata bayani ta ya mutsa fuska
ta ce "Ok daman ita ce mai aiki bata ta kai, ki sama mini breakfast mai kyau yanzu"
matar ta juya Halisa ta riƙe tray Zahrah ta ce "Sai ki fara aikin ki tun yanzu,
kije ki kai masa breakfast ɗin ki dawo ki shirya mini kayana a wardrobe" Halisa ba
ta ce komai ta juyawa zuwa inda taga Yaa Sheikh ya nufa, bakinta ɗauke da sallama
bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune kan kujera ta ƙarasu har inda
yake ta tsuguna ta ce "Ga shi wai" ya gyara zama yana tsiyaya tea ɗin tare da
kaiwa bakinsa. "To kai iya wannan kake sha ne? Ko nayi maka abinci?" Da idanu
kawai yake bin gefen fuskarta da kallo ta gyara zama ta ce "Mother ta ce kai mijina
ne" ya ware idanu da sauri yana binta da idanu, ta buɗe baki zata sake magana caraf
ya saka hannu tare da kame bakin.....

08119237616
Paid book
Not edited
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Shiru" ya ce yana sakin bakin tare da mai da Idanunsa kan
glass cup ɗin da ya tsiyaya tea aciki. Ta tura baki gaba ba tace komai ba duk da
irin ƙaiƙayin da bakin yake mata, haka nan taji kamar ana mintsininta akan Halisa
yi magana cikin sauri ta ce.
"Nima ina jin yunwa na sha shayin naka?" Cak ya ajjiye tea ɗin daga hannunsa yana
ɗaukan tissue tare da goge bakinsa, ta ɗauki shayin daya rage zata kai bakinta ta
ji ance "A'a" ta ajjiye cup tana miƙewa tare da bin bayansa, sahun tafiya da yaji a
bayansa yasa ya tsaya, tayi saurin dawowa gabansa suna haɗa ido ya ware mata manyan
idanunsa masu kaifi ta tura baki ta ce "Na sake magana banga ka riƙe bakin ba ai"
Yaa Sheikh ya girgiza kai kawai tare da shigewa bedroom ɗinsa yana ɓoye yanayin
fuskar shi. Ta kalli inda ya shiga sai kuma ta juya tana kwashe tray ɗin. A main
parlour ta samu Zahrah zaune tana breakfast ga wata maid nayi mata tausa a ƙafa.
"Ke zonan" cewar Zahrah Halisa ta dawo ta zauna tana ɗauke kai gefe guda, saboda
har yanzu bata mance mari da zagin da Zahran tai mata ba, Zahrah ta ajjiye spoon
ɗin hannunta wanda take shan tea da shi ta ce.
"Kai breakfast ɗin sai yanzu? Ko bai ta shi bane" Halisa ta kalle ta sai kuma ta
ɗauke kai tana faɗin. "Shi ya ce na tsaya" Zahrah ta ce "Shi Yaa Sheikh ɗin?" Tai
shiru ba tare da ta ce komai, tasan indai zatai magana to zata saki layi ne, Maid
ɗin ta kalli Halisa da sauri, ai ko ita da tayi shekara da shekaru tana aiki a
gidan Yaa Sheikh magana bata taɓa haɗa su ba, infact ko parlourn shi bata san ya
yake ba, Ummul ce kawai take kai masa breakfast ita ma iya dining room, sai ya gama
yabar wajan take zuwa ta kwashe, idan kuma yini gida zai yi a ranar basa taɓa zuwa
part ɗin, Umar-khan ne ke kai masa dinner, bai fiya cin lunch ba sai dinner,
anytime yana tare da butar shayi kamar buzu. Mamaki ya cika Maid ɗin jin abin da
Halisa ta faɗa wai shi ya ce ta jira? Who is she to him?.... "Whatever, Ke yama
kika ce sunanki?" Maid ɗin ta ce "Bara'at" Zahrah ta ce "Ok, duk wani aiki na part
ɗin nan, zuwa part ɗin Yaa Sheikh ya dawo hannun wannan yarinyar, idan kun kammala
abinci na Yaa Sheikh ita zata dinga kai masa, bana son na dinga ganin wani abu na
ba daidai ba, bana son surutu da hayaniya yana saka mini ciwon kai, ko a gidan
ubana ban taɓa sanin hanyar kitchen ba, to a nan ba zan fara saninsa ba, kuna gama
girki ki bata ta kawo mini nawa" daga Halisa har Bara'at kallon Zahrah suke, suna
mamakin ƙarfin ikon nata, duk da cewa Bara'at bata san matsayin Zahrah ba, amma
tasan dole da akwai abin da ta taka a gidan... Zahrah ta kaɗa ƙafa tana faɗin "Ku
ɗauke idanunku daga kan mijina, daga nesa kuka ganshi ku sauya hanya, duk abin da
kuke nema ni zaku faɗawa, koda abin cin gidan ne ya ƙare" Bara'at ta ce "Ok, amma
kula da abincin gidan yana wajan Ummul" It's your problem, I just finished planning
what I want" ta juya kan Halisa tana faɗin.. "Jeki breakfast ki saman a bedroom"
tana faɗin hakan ta shige part ɗinta, Halisa ta bita da kallo a zuciyarta tana
mmkin halin Zahrah. Miƙewa Bara'at tayi Halisa ma haka, tabi bayanta har zuwa
sashen kitchen, ma'aikata ta gani mata da yawa ko wanne da abin da suke a kitchen
ɗin. Da sauri Bara'at ta nufi wajan Ummul tana ce wa "Yau naga abin mamaki Ummul"
kyakkyawar matashiyar matar wacce zata iya shekaru 50 zuwa sama ta kalli Bara'at ta
ce. "Da akai me Ukkuti Bara'at?" Bara'at ta sauke numfashi ta ce "Wata mata na
gani, mai iko da isa, wallahi na tsorata da yanayinta" Ummul tai murmushi tana
ajjiye abin hannunta ta ce "Faɗimatul-zahrah bin Umar Farouk, matar Yaa Sheikh" a
tare duk suka ce "Matar Yaa Sheikh?" Ummul ta kallesu ta ce "Na manta ban shaida
muku bane, sai a haƙuri da juna ko?" Idanunta ya sauka akan Halisa wacce take dube
dube duk abin da suke faɗa tana ji amma hirar bata gabanta, Ummul ta girgiza kai
kawai, tana mai jin wani abu a ranta, yarinyar tana nan dai babu sauyi a tare da
ita kamar yadda yake nuna mata ita a waya. Hawaye ya sakkowa Ummul ko yanzu ta mutu
ta yi farin ciki, Aliyu ya samu gefen rayuwar shi kamar yadda yake faɗa mata a koda
yaushe.
Bara'at ta ce "Ummul wace ita kuma wannan?" Ummul ta ce "Masu gidan ce" "Masu gidan
kuma?" Cewar Suhaima Ummul ta ce "Ina nufin mai aikin Zahrah ce" ta kalli Halisa da
kyau tana mai sakin murmushi ta ce "Sunanta Halisa, ƴar uwar Zahrah ce an bawa Yaa
Sheikh riƙon ta amana ne, zatai amfani da sunan Halisa bin Sheikh Aliyu haydar
Aliyu" Halisa ta ƙarasu wajan Ummul da sauri fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi
ta kama hannun Ummul ta ce "Laa kema kin sanni ashe, kuma kin san anyi...." Ummul
tayi saurin rufe bakin nata tana cewa "Ba'a yin surutu a ɗakin girki, Bara'at akwai
tray tana shirya breakfast ki bawa halisa" Bara'at ta ɗakko tray ta bawa Halisa ita
kuma ta ce a kitchen ɗin zata zauna ta ci.
Bayan ta gama cin abincin Ummul ta miƙa mata farar madara mai ɗauke da zuma a ciki,
batai musu ba ta amsa "Nima ina son na iya girki sosai, ina son yi wa Yaa Sheikh
girki mai daɗi" Ummul tayi kamar bata ji zancen na Halisa ba, taci gaba dayin aikin
gabanta tana son a akai gidan ciyarwa Yaa Sheikh abincin akan lokaci.
Zahrah na tsaye a gaban mirrow anci uwar kwalliya sai ƙarinin mai take, wayarta
dake ringing ta ɗauka ganin sunan Deen ta ce "Uhm maye daman nasan babu mai kirana
sai kai" daga cikin wayar ya ce "Ba wannan zaki tambaya ba, fara duba number" da
sauri Zahrah ta duba number da mmkin take kallon number ta Saudiya ce,what does
that means? Ya katse mata tunani da faɗin "Ki daina mamaki na riga ki sauka a
Madina, ke kawai nake jira, don't make any mistakes nazo da maganin da ki ke
buƙata, ina son ganinki" The surprise of his behavior prevented Zahrah from
speaking. "Wallahi ki san yadda akai ki ka zo, ko ki ganni a gidanki" yana faɗin
haka ya kashe wayar babu jimawa ya tura mata address ɗin inda yake, Zahrah ta dafa
kai da sauri kuma ta juyawa zuwa ɗaya bedroom ɗin nata a nan ta samu Halisa tana
shirya mata kaya a wardrobe, zama tayi ta ce "Ke kin fara menstrual?" Halisa ta
ɗauka gyaran kayan take nufi kai tsaye ta ɗaga mata kai alamar eh. Juyawa tayi ta
nufi part ɗin Yaa Sheikh.
Fitowar shi kenan daga Library room ɗinsa, ya zauna sanye da wata tattausar
Jallabiya a jikinsa hannunsa cikin sumar kansa, cikin nutsuwa ya gyara zama akan
duguwar kujerar da yake kai hannunsa riƙe da Cup yana shan green tea wanda Ummul ta
kawo masa da kanta, speaking calmly ya ce da Khalil.
"Uhm surutu dai" Ta cikin waya Khalil ya saki dariya ya ce "Ya muke da matarka?
Allah ya nuna mini ranar da zata barbabaɗa tana ɗauke da cikin Yaa Sheikh, koda
yake kace baka son ta ai, auren dole akai maka" Yaa Sheikh yaja idanu ya rufe yana
jinsa fresh sbd barcin da ya yi, cikin son dakatar da Khalil ya ce.
"Wallahi ba auren dole bane, ni na zaɓi matata It was completely my plan..." Katse
wayar ya yi jin yana faɗin abin da mai shirya ba, tare da rufe kansa. Tsaye ya
ganta a kansa babu sallama ya ɗauke kai kawai yana ci-gaba da danna waya tare da
duba abubuwan da Umar-khan ya tura masa.
Ta zauna kusa da shi tana cewa "My Excellency baka fito ba har yanzu hope lafiya?"
Kai kawai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, ta haɗe jikinta da nashi tana
cewa "Daman nace ina neman permission zamu shopping da ƴar fillo" har lokacin
idanunsa yana kan waya bai ce komai ba. Ta shafi fuskar shi tare da cewa "Ba
jimawa za mu yi ba kaji My Excellency" Jotter ya ɗauka da pen ya yi rubutu kana ya
ajjiye mata a gefenta haka kurum yaji harshensa ya harɗe baya jin yin maganar.
Ganin ƙoƙarin rungome shi take son yi ya ɗan miƙe tsaye, yasan cewa hakƙinta take
nema, kuma yasan girma da ƙarfin hakƙi amma ya zai? He's not interested at all,
baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin.
Tabi bayan shi da kallo, tana ji a ranta dole ne ma tayi gaggawar aiwatar da burin
dake ranta, Yaa Sheikh ya dawo hannunta sai yadda tai da shi tayi imani da Allah
idan ya zo hannunta shi da wata ƴar mace kuma har abada, ba zai iya kallon kowa a
matsayin mace ba dole sai ita, What is the solution? where will she start and what
will she do now.

"You can go,
Ina buƙatar gyaran part,
With food" shi ne abin da ya rubuta mata a jikin Jotter ɗin, ta duba kenan dole
mutum ɗaya ya tsaya, ita gasky ba wani gyaran ɗaki da zata iya, bayanta ciwo yake
idan ta yi,kuma bata saba ba. Fita tayi ta samu Halisa a main parlour a kwance
barci ya ɗauke ta tunda ta farka da asuba bata koma ba, gashi tai aiki ta gaji
sosai bata san barcin ya ɗauketa bama sbd kallo take. Tana zuwa ta fisgo ƙafar
Halisa zuwa ƙasa ta faɗo daga kan kujerar, a tsorace ta ce "Hande en boni me na yi
Anti?" Zahrah ta ce "Ai hutu kika samu kenan? Ai babu ranar da zaki huta, zaki ta
wahala har abada, kije ki gyara part ɗin Yaa Sheikh, ki kai masa lunch zan fita
unguwa" kanta a ƙasa ta kasa cewa komai, tana zaune a parlourn Zahrah ta fito cikin
wata duguwar riga ta yana mayafi hannunta riƙe da hand bag, kamar yadda Zahrah bata
kulata ba itama bata kula ta ba. A compound ta ci karo da Umar-khan yana fitowa
daga mota hannunsa riƙe da takarda. Ya ce "Evening" ta share sa, ta nufi wajan wani
da alama shi ne drivern gidan.
Kai tsaye Umar-khan gidan ya shige ya samu Halisa zaune kanta a ƙasa tana gyangyaɗi
ya ce "Matar Malam" tai saurin jan mayafin abayar ta ɗora a kanta tana yi masa
murmushi ta ce "Ina yini?"
"Lafiya, barci a nan kuma? Yaa Sheikh ɗin yana ciki?" Ta ce "Ban sani ba" ya
jinjina kai ya ce "Ok bari na duba, kije ki kwanta mana" ita dai ba tace komai ba
ya nufi Part ɗin Yaa Sheikh barci yaci ƙarfinta, ta kwanta nan ƙasan carpet.
Umar-khan ya zauna bayan ya gaida Yaa Sheikh ya ce "Na cike komai na makarantar,
gobe aka bada izinin ta fara zuwa, Mother ta ce komai cikin gaggawa take buƙata" ya
miƙawa Yaa Sheikh file ɗin takardun Halisa bai amsa ba, sai tsare Umar ɗin da idanu
da ya yi, Umar yana fahimtar shirun na Yaa Sheikh hakan ya sa ya ce.
"Al Aqeeq International School for Girls, Safiya Opens 7:30 ita ce makarantar" Yaa
Sheikh ya jinjina kansa tare da miƙewa ya shigewa ɗaki. Wajan mintuna goma suka
fito tare da Umar-khan wata Milk ɗin jallabiya ce a jikinsa, sai golden ɗin
Alkyabba daya ɗora a kan jallabiyar, ya fito a babban malaminsa sai ƙamshin Roja
yake bazawa, yana fitowa idanunsa ya sauka akan Halisa wacce ta cure waje guda tana
barci, ya tsaya cak tare da kallon Umar-khan, Umar ya nufi ɓangaren Ummul babu
jimawa suka dawo tare, Ummul ta kallesa ta ce "Malam za a fita ne?
Ba kaci abincin kirki ba?" Ya ɗan ɗauke kai zuwa hanyar fita yana faɗin. "Sanyi zai
illata ta, a sauya mata waje" sai a lokacin Ummul ta lura da Halisa.
"Tom babu damuwa, Allah ya tsare" ta nufi wajan Halisa ta shiga tashinta tare da
faɗin "Matar Malam, matar Malam" ta buɗe ido tana kallon Ummul ta ce "Maza ta shi
ki koma ɗaki, a kwai sanyi zai kama jikin ki" ta buɗe ido sosai ta ce "Anti Zahrah
ta dawo ne?" Ummul ta ce.
"Fita tayi ne? ta shi lokacin sallah ma ya yi ai muje ko" har part ɗin Halisa Ummul
ta shiga, akan idanunta Halisa tai alwala kana tai Sallah. Ummul ta ce "ƙarfe biyar
kizo ɗakina, zan nuna miki yadda ake cikakkiyar sallah, na fara karanta miki
Alkur'ani, yanzu ki kwanta wajan ƙarfe 4:30 ki tashi ki wanka

Please Login or Register in order to submit comment