You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki wanke baki, ki
sauya komai na jikin ki, kinji ko?" Ta tura baki sosai ta ce "To wannan duk na mene
Ummul" Ummul ta ce "zaki sani ne" ta fice daga ɗakin.
Yaa na fita kai tsaye Al Masjid an Nabawi ya nufa sbd wani karatu da yake dashi na
musamman, kuma acan yake son yi Sallah ma, da kuma zaman tattaunawa da za su yi da
mahukunta kula da Masallaci harami ana son naɗa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu
matsayin limamin masallacin Haramin wanda zai jagorancin sallar Taraweeh da
Tahajjud, gaba ɗaya azumi saura wata guda ya rage a fara.
Tamkar uwa mahaifiyya haka Yaa Sheikh ya ɗauki Ummul yana ɗaukan minti goma yana
magana da ita, tasan kusan komai nasa kuma tasan da yawa abin da Mother bata sani
ba, tunda yafi rayuwa a Madina fiye da Nigeria. Sai bayan sallar issha Zahrah ta
shigo a gajiye tana tafiya da ƙyar idanunta ya yi jaa, Halisa ta bita da idanu
ganin yadda take tafiya kamar yaron da akaiwa shayi. Duk yadda Halisa tasu taga
dawowar Yaa Sheikh bata gani ba, barci ya ɗauketa a Main parlour. Ƙarfe 12:30 ya
shigo gidan shi kansa a gajiye yake sosai, ganinta a parlourn ya sanya ya tsaya
yana binta da idanu, a hankali ya dubi lokaci sai kuma ya shige part ɗinsa.
Kiran sallar asuba ya farkar da ita, da mmki take bin makeken gadon da take kai da
kallo, an rufe ta da wani haɗaɗɗan duvet mai ƙamshi ga laushi an kuma rage ƙarfin
a.cn ɗakin, ita dai tasan a parlour ta kwanta waya kawota nan? Ko ita ta shigo da
kanta.
Ta miƙe ta nufi toilet yadda Ummul ta koya mata haka tayi, tai wanka da ruwan zafi
ta shafe jikinta da Vaseline Intensive Care Cocoa Glow Body Lotion.

Shiryawa cikin Abaya ta ɗora hijab a nutse take duba littafan da Ummul ta bata,
Ubangiji ya bata fikirar hadda ce, da yawan lokaci ita abu a kanta yake zama, duk
wani abu mai muhimmanci bata wasa da shi. Tana zaune taji saukar muryarsa a
kunnanta yana data kabbarar sallah, shiru tai bata taɓa tunani muryar shi takai
daɗin haka ba sai yanzu. Sallah ta gabatar sannan ta nufi ɓangaren kitchen ta samu
tuni sun Bara'at sun fito. 6:30 Ummul ta ce tayi sauri ta shirya za a kaita
makaranta, wani tsalle tayi ta rungume Ummul daɗi ya kamata jin za a kaita
makaranta abin da take buri a rayuwarta. Ta shirya ta fito tsaf a cikakkiyar ƴar
fillonta Ummul na ganinta tai murmushi tana cewa "Kije ki gaida Abban naki" Halisa
ta ce "Abba kuma Ummul" ta ce "Eh, uban riƙon ka ai uba ne jeki maza" hannunta
ɗauke da yam balls ta nufi ɓangaren shi.
Cikin siririyar murya tai sallama tare da shiga tsaye ta gan shi cikin kyakkyawar
shiga mai ɗan kauri sbd sanyin garin da aka tashi da shi, hannunsa goye a bayansa
ta ƙarasa cikin da sauri tana durƙusawa har wajan ƙafafuwan shi ta ce.

"Jamɓanduna,
Noi sare,Noi kuɗe" ta jera hausuwar ma'ana _“Ina kwana, ya ya gida, ya ayyuka”_ ya
ware gajiyayyun Idanunsa a kanta, yana bin shigar makarantar nata, ta ɗaga kai ta
gan shi tsaye ta miƙe tana kallonsa, ya dubi yam balls ɗin hannunta da raguwar na
gefen bakinta. "Jiya nai barci baka dawo ba, yanzu kuma wai makaranta za a kai ni
inji Ummul" ya jinjina mata alamar _"Eh"_ yana ƙoƙarin juyawa tayi saurin riƙe
ƙugunsa da hannu ɗaya ta ce "Miyetti masin, Allah ya ƙara arziƙi"
Ɗan ƙaramin bakin maganar kawai yake bi da kallo, gumi na tsastsafo masa ta
goshinsa ta saki kyakkyawan murmushi ta ce "Mijina" da sauri ya kalli cikin
idanunta ta ɗauke nata idanun sai murmushi take sbd daɗin zata makaranta.

A hankali ta buɗe baki a taushashe kuma cikin ƙasa da murya ya ce "Matar m......"
Maganar ta tsaya sbd yam balls data tura masa a cikin baki ta dinga tsalle tana
cewa "Nayi maka wayyo daman ance baka cin abinci" ya lumshe fararen idanunsa tare
da nufar kujera har lokacin tana riƙe da shi. Yana zama ta zauna a ƙasa Yaa Sheikh
sai mai da numfashi yake sam bai niyyar cin komai ba, bisa dole ya shiga tauna yam
balls ɗin bakinsa yana goge zufar dake goshinsa, wanda kuma shi kansa ya san zufar
ta mece ce. Ya ɗauki bottle water tare da tsiyayawa a cup bayan ya sha ruwan ya mai
da numfashi. Halisa ta ce "nace Ummul tayi maka wani na cinye gaba ɗaya tas" gently
ya buɗe idanun a kanta ganin yadda yake bin fuskarta da kallo sosai yasa tai masa
kyakkyawar murmushi tana lumshe idanu tare da buɗewa kamar yadda yai, a hankali ya
ɗan ranƙwafa daidai kanta ya sanya fararen tafukan hannayensa tare da kama fuskarta
da kyau babban hannunsa yasa yaja kumatunta numfashinsa na sauka a fuskarta ya ce.
"Zaki fasa mini kai da surutu Matar Malam, shiru kan na ɗinke bakin......

Not edited
Paid book
₦500
08119237616
Sarautar marubuta.

_Ubangiji ya haɗamu da alkairan da suke cikin jumma'h. Mu haɗu Monday❤‍🔥
_
[1/3, 4:48 PM] Abk: _I unite you with the greatness of God a daina fitar mini da
littafin IDAN BA KE. What you want will not be difficult for you to buy. This is
not appropriate at all.🫰🏿har zuwa ake a nuna mini wai an samu book ɗin Idan ba ke as
free irin ga masifaffiyar nan bari nai ta ihu a media😂 I love my book lovers
wherever they are. Amma don Allah a daina fitar da book ɗin... It's 500 via
6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616_


Kasa ƙarasa maganar ya yi sbd gemunsa data kama tana cewa "Yasunan wannan abun?
Kuma da gaske ni matar malam ce, naje na faɗawa Ummul nace kace mini matar malam?"
Ya lumshe idanunsa na wani lokaci kafin ya buɗe su a kanta tare da ɗora hannunsa
akan nata data riƙe gemunsa ya zare yana girgiza mata kai.
Zata sake yin magana ya miƙe tsaye yana nufar hanyar bedroom ɗinsa dole sai ya
sauya kaya gaba ɗaya ta goge masa maiƙon hannunta a jiki, da sauri ta biyo bayansa
ta ce "To baka faɗa mini sunan wannan dugun abin ba, kuma waye zai kaini makarantar
ina son zama babbar mace" ya juya tare da kallonta a nutse yana mai mamakin surutun
ta, yana da masaniyya akan yadda take amma bai ɗaukan surutun ya yi girma da tsayin
haka ba. Bai ce mata komai ba ya juya yana mai sakin murmushi shirmanta a karo na
farko da suka kasance tare domin sauran duk baɗini yake ganinsu. Ummul na kitchen
Halisa ta dawo ta kalleta cikin kyakkyawan lafazi ta ce "Ba dai haka kika je da
hannunki ba?" Ta kalli hannun kuma ta kalli Ummul ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na
goge masa" Ummul tai shiru daman tasan za a rina, kuma sam ba tayi mamakin hakan
ba. Maid Suhaima ta ce "Wa kika gogewa?" Da sauri Halisa ta ce "Malam, nikam ya
sunan wannan dugun abin na fuskar shi? naji yana da laushi aradu" Ummul ta dafe kai
da sauri kuma ta miƙe tsaye tana kama hannun Halisa suka nufi can part ɗin Ummul
ɗin.
Bayan sun shiga Ummul ta kalli Halisa sai kawai tai murmushi kafin ta ce "jeki
wanke hannun ko?" A sanyaye ta ce "To" ta nufi bathroom ta wanke tas tare da wanke
bakin ta fito har lokacin Ummul na zaune tai shiru tana kallon hanyar toilet ɗin,
ganin yadda Ummul tai shiru yasa Halisa faɗin "Ummul" ta buɗe idanu ta ce "Kin
gama? Lokaci na tafiya zaki buƙaci abinci a can, lunch box naki yana cikin mota"
suka fita Main parlour daidai nan Zahrah ta fito da kayan barci da alama ko sallah
ba tayi ba, balle ashirin zancan wanka tabi Ummul da kallo ta ce.
"Wace ke? daga ina bana hana ana shigowa kai tsaye ba, ba tare da permission ba, ke
kuma jeki gyara mini bed ki haɗa mini ruwan wanka" Halisa ta ce "makaranta za a kai
ni, idan na dawo zan haɗa miki sai Kiyi wankan" Ummul ta danne dryar data zo mata.
Da mamaki sosai Zahrah ta ce "School? Da izinin waye kuma? babu wata makaranta da
zaki, baki zo gidan nan dan kije makaranta ba" ta faɗa tana fisgo hannun Halisa
daga kusa da Ummul.
"Ke kuma da kika tsaya kina ƙwalala mini idanu da alama kina da masaniyya, tell me
waye zai kai ta makarantar"

"Ni ne" ya faɗa a taushashe yana mai fitowa daga inda yake tsaye, yana sanye da
sabbin shiga saɓanin ta ɗazo, farar dakakkiyar shadda ya sanya mai jamper da babbar
riga, ya ɗora hirami ɗaya a kansa ɗaya kuma a kafaɗa..
Ta saki Halisa ta nufi inda yake ta ce "My Excellency amma daga zuwa sai batun
makaranta, kuma ya kamata a faɗa mini, ni bani da ra'ayin yarinyar nan tai
makaranta" Halisa ta tura baki tana mai jin haushin yadda Zahrah ta wani matsa kusa
da Yaa Sheikh haka kawai taji zuciyarta ta cunkushe, amma hakan bai hanata cewa.
"Amma ai Dada tana da niyya ko Anti, da izinin zani makaranta ta baki...." Cikin
rawar murya Zahrah ta ce "Oh ok it's ok you can go, but waye zai kai ta?" Sai a
lokacin Ummul ta ce.
"Umar-khan, kafin driver ya fara kai ta, Aliyu yana da lecture da ɗaliban shi, zai
iya magana" Ummul ta faɗi haka ne domin Zahrah ta bawa Yaa Sheikh hanya. Haka kurum
Zahrah taji sha'awar kasancewa da mijinta ya bijiro mata, musamman da ƙamshin Roja
ke ƙara narkar da zuciyarta, Yaa Sheikh na musamman ne, idan zaka kalli cikin
idanun shi yayin magana to ba zaka taɓa yi masa ƙarya ba, ɗaya daga cikin baiwar
shi kenan. Babu kunya ta rungome shi a gaban Ummul tana faɗin "Am going to miss you
My Excellency back soon please" gani sukai Halisa ta juya da sauri zuwa part ɗin
ta, Ummul ba tai magana ba. A hankali ya zame jikinsa daga na Zahrah ta ce "Bari
naje nai wanka da Sallah bye" Ummul ta kalli lokacin 7 harta gota ba dai sallar
asuba ba, sai dai walaha.
Bayan shigewar Zahrah Yaa Sheikh numfasa yana mai gyara murya a kasalance ya ce.

"Mun kwana lafiya,
Ummul?" Ummul ta ce "lafiya lou, kaga ƴar rigima ko? kamar kuka naga ta nayi?" Ya
saki fuska daga kamewar da ya yi shima yana duba lokaci a diamond rolex watch
ɗinsa.
"Aje a duba, kin san hali tun ba yau ba" tai murmushi ta ce "Wallahi fa" ta nufi
part ɗin Halisa shi kuma ya goya hannunsa a baya tare da tsaiwa a tsakiyar
parlourn. Kwance Ummul ta samu Halisa ta cire baby hijab ɗin jikinta sai kuka take
kamar ranta zai fita. Ummul ta zauna cikin sakin fuska ta ce "Matar Malam lafiya?
Wani abun ne? ko wani gurin ke miki ciwo?" Kuka kawai take taƙi magana tamkar zata
shiɗe haka take kukan. "Faɗa mini mene? ke dawa" ta miƙe zaune cikin shassheƙar
kuka ta ce "Ummul Dada zani, ni na fasa zaman wajan Dadata zani ki saka a bayar
dani" Ummul ta ware idanu da kaɗuwa sosai ta ce.
"Yanzu Matar Malam ina ke ina zuwa gida, keda kika zo bautar Ubangiji? Maza tashi
akai ki makarantar ga shi can yana zuwa kin san kuma akwai inda zashi" idanunta ya
yi jajir hawaye na zuba daga cikinsu ta ce "banso, na fasa makarantar ni rugarmu
zan koma" yin duniya taƙi yarda Ummul ta ce "To dai na kukan bari na faɗa masa" ta
juya tana mmkin sauyin da yarinyar ta samu lokacin gudu, me akai mata me kuma ya
sauya mata tunaninta daga sha'awar zuwa makarantar.
A tsaye Ummul ta same shi, bai kalleta ba amma tunaninsa da hankalinsa na kanta ta
ce. "Kuka take sosai, wai bata son makarantar kuma a bayar da ita can ruga"
maimakon ya fita sai ya juya zuwa part ɗin shi ba tare daya amsa maganar ta Ummul
ba. Ta gane yaran kuraman nashi dan haka ta ƙarasa juyawa zuwa sashin na Halisa.
kanta kife idanunta data rufe su take hango rungumar da Zahrah taiwa Yaa Sheikh,
kuma bata manta maganar da Maimoon ta faɗa mata ba, idan kana son mutum da zarar
wata macen ta raɓesa zaka ji kishinsa, ita a yanzu ta kasa fahimtar me ya sa taji
komai ya dameta zuciyarta babu daɗi ne? Da wannan tunanin Ummul ta dawo ɗakin tare
da ce mata "Ki saka hijab ɗin, kije Abban naki yana kira zai mayar dake" ta kalli
Ummul sosai amma bata ce komai ba, hijabin a hannu ta nufi part ɗinsa. Ummul ta
girgiza kai tana sakin murmushi kawo yanzu ta gama gane abin da ke damun Halisarta
ta fahimci zallar rigima da shagwaɓa ce ke damunta akan dalili mara toshe.
Yana zaune hannunsa riƙe da azkar yana dubawa yaji saukar siririyar muryarta tayi
sallama, amsata ya yi a rai, yana mai ɗago kansa tsaye ya ganta taƙi ƙarasuwa sai
cukurkuɗe hijab ɗin hannunta take. Shi bai fiya son yin surutu ba kwana biyu kuma
tana neman sashi, gashi kamar ciwon kanshi na neman ta shi. Ajjiye azkar ɗin
hannunsa ya yi, tare da miƙa mata hannunsa alamar tazo, kanta a ƙasa ta matsa inda
yake zata zame a ƙasan ƙafafuwansa ta zauna a ƙasa ya kamo hannuna tare da zaunar
da ita a gefen shi yana kafeta da idanunsa. Kafin ya ce komai ta fashe da kuka
sosai tana jan numfashi, ya tallafo haɓarta da hannunsa mai taushi idanunsa na yawo
a fuskarta.
"Ya akai?
Ke dawa?" Ya faɗa yana mai sauke numfashi tare da jan jikinsa zuwa jikin kujerar.
Muryata na rawa ta ce "Abba gida zani, ni Dadata zan koma" ya lumshe ido kana ya
buɗe a sauƙaƙe cikin son dakatar da kukan dake neman fasa masa kai ya ce. "Karatun
fa? Ban son rigima" ta girgiza suna haɗa ido ta tura masa baki ta ce "Shi ma banso,
kuma..." Sai kuma tai shiru tana ɗauke kai.
Kallon yadda fuskarta tai jajir ya yi sosai duk ta birgita kanta sbd rigima, he's
still holding her face ya fesar da iska ya ce.
"Gida kike so? Ta ɗaga masa sai kuma ta ce "Eh wajan Dada zaka kaini kaji Abba"

"Baki son Malam?" Ya tambaya kai tsaye domin shawo kan rigimar tata, ta riƙe
hannunsa ta ce "Ina so bana, to ba naga Anti Zahrah ta rungomeka ba, shi ne naji
kawai kuka yazo mini kaga gwanda na tafi gida" ya miƙe da sauri tare da shigewa
bedroom ɗinsa not too long ya dawo fuska a kame, a tsaye ya sameta kallon da yake
masa yasa ta saka hijab ɗin. Kana tabi bayansa babu kowa a main parlour dan haka ya
nufi compound direct.
Yana zuwa Umar-khan na fitowa daga mota tare da faɗin. "Good Mrng Yaa Lee" kai ya
ɗaga masa ya shiga bayan mota, itama Halisa ta shiga bayan motar gatekeeper ya buɗe
musu fita.
Sun jima da tafiya amma abin mamaki Halisa bata ce komai ba, ko Umar-khan bata
gaisar ba, a haka suka ƙarasa Al Aqeeq International School. Umar-khan ya yi
parking a harabar makarantar tare da fita yabar musu motar, ƙoƙarin buɗe motar take
ta fita taji ya kamo hannunta taƙi yarda ta kallesa alamar dai She's still angry
with him. Wani sirrin baƙin zare ya ɗaura mata a hannunta, ya riƙo hannun da kyau
ta yadda dole ne ta matso kusa dashi idan taji an jawota, sukai kusa da juna.
"Ƴar fillo" ya ce a hankali da sauri ta kallesa sai taga ba ita yake kallo ba, ta
ce "gidan zaka bayar dani?" Sai a lokacin ya juya gaba ɗaya zuwa gareta a hankali
numfashinsa ke sauka cikin murya ta yanayin gajiya da kasala ya ce.
"Anti ba zata sake ba,
Amma idan Anti bata rungome Malam ba waye zai rungome shi?" Bakinta na rawa ta ce
"Ni matar malam zanyi" ya buɗe ido sosai da sosai yana mmkin ƙarfin halinta. "Da
gaske ni kullum sai na rungome ka nace maka mijina" bashi da wani option wanda ya
shige bin bakin mganar da kallo ya daɗe yana kallonta kafin ya ce.
"Uhm" da sauri bakinta na rawa ta ce "Ai na iya bari ka gani" kafin ya yi magana ko
wani yunƙuri yaji gaba ɗaya ta zagaye hannuwanta tare da rungome shi, ta ɗora kanta
a ƙirjinsa, ya buɗe idanu da sauri cikin In-inar data zo masa ya ce. "Su...su...
Subuhanallah Ya Allah....
[1/3, 4:48 PM] Abk: Ta saki dry sosai ta ce "Abba Allah na iya kaji ai?" He was
completely lost for words and just shook his head. Bayan wasu giftawar seconds ya
nuna mata ƙofa da hannu ta buɗe ƙofa tare da fita, a hankali shima ya buɗe ƙofa ya
fita tare da fitowa yana ƙara covering jikinsa da kyakkyawar shigar dake jikinsa.
Umar-khan na ganin fitowar Yaa Sheikh ya ƙarasu wajan yana mai sakin murmushi,kai
tsaye office ɗin headmaster school ɗin Yaa Sheikh ya nufa, gaba ɗaya teachers na
school mmkin ganin Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu a cikin makarantarsu ya kama su,
kowa sai durƙusawa yake yana miƙa gaisuwa a nutse cike da kamala nutsuwa yake ɗaga
musu hannu yana ƙara kame kansa wanda yake fidda kwarjinin shi.
Cikin mutunci Headmaster ɗin mai suna Ayyan ya miƙe yana gaida Yaa Sheikh. Umar-
khan ya ce "you did the interview for her, then you look at the one class that is
suitable for her" Headmaster ɗin ya kalli Halisa cike da birgewa ya ce. "What's
your name?" Tai ƙasa da kanta sam bata ji me yace ba, balle ta fahimci me yake
cewa. Ya ɗauka bata gane english sai ya juya zuwa cewa.
"ma asmuk?
kam eumarka?" Nan ma tai shiru Ayyan ya kalli Yaa Sheikh cike da martabawa ya ce

"‫"سنضعها في الصف الأول حتى تتمكن من أخذ الدروس‬
_“Zamu sakata a matakin farko domin ta fara darasin”_ cewar Ayyan Yaa Sheikh ya
numfasa ba dai ce komai ba. Ayyan ɗin ya ce. "Zata samu gogewa cikin ƙaramin lokaci
Insha Allah, kuma a nemata mai darasi a gida,that will help her study more" Umar-
khan ya yi murmushi ya ce "How long do you think she can take the time before she
can learn everything, and get experience" Ayyan ya ɗan kalli Halisa yana karantar
how smart she's kafin ya ce "I can't say how long it will take,But she will get
good academic training" Umar-khan ya ce "that's good, amma matar...." Gyaran Muryar
da Yaa Sheikh ya yi ya hana Umar-khan faɗin abin da ya ke shirin faɗa ɗin. Yaa
Sheikh ne ya fara miƙewa yana kallon lokaci a nutse ya ce.
"A kula, banda wasa" ta miƙe tsaye tana shirin yin magana ya yi waje abinsa domin
yasan zata iya faɗin abin da ba shikenan ba, bai shirya ɗaukan abin kunyarta cikin
mutane Yanzu ba. Idanunta ya cika da hawaye sosai tana neman yin kuka a haka
Headmaster ɗin ya kaita Jss 1. Akan idanunta kuma motar Abban nata da Umar-khan ta
fita waje. Ita ɗaya ce a table nata, gaba ɗaya class ɗin basu da yawa dukkansu
farare dasu gwanin sha'awa, itama ta saje dasu sbd farin da take dashi mai tsari.
Shiru tayi tana kallon kowa da idanu kowa na ajin harkar gabansa yake a haka
Headmaster ya gabatar da ita ya fita. Babu jimawa wani kyakkyawan balarabe ya shigo
cikin jallabiya ash ya ɗora half ɗin hula a kansa, bai tsaya jiran gaisuwarsu ba.
Ya nufi blackboard inda suke duba kamar computer haka ya shiga latsa abubuwa sai ga
sunan subject ya fito

_Social studies_
A ƙasa kuma aka rubuta _MEANING, SCOPE AND NATURE OF SOCIAL STUDIES_
Matashin ya kalli students ɗin dake gabansa, har lokacin idanunsa bai kai inda
Halisa take ba, cikin kamala ya ce.
"Alhmd, yau zamu fara da meaning na social studies, please who can tell me the full
meaning of Social studies?" Duk sukai shiru ya ce.
"It's okay" ya ɗan duba abu kaɗan kana ya mai da attention nasa ga ɗaliban ya ce.
_“Social studies can be defined as the study of man and his environment. Social
studies can also be defined as the totality of man’s physical and social
environment”_ daga nan ya yi musu explanation yadda zasu fahimta ya saka english ya
saka Larabci maybe they can understand very well. Yana ƙoƙarin yin magana yaji
ance.

"To aradu nidai tunda ka fara magana ban san me kace ba, idan zaka faɗa da hausa
kawai ka faɗa ko kayi shiru" ya juya gaba ɗaya zuwa direction ɗin da daddaɗar
muryar dake tashi, yana juya a ƙaramin bakinta idanunsa ya sauka, magana take sosai
ko haɗiyar yawo ba tayi. AZAAN ya ware fararen idanunsa akanta da kyau, da alama
ita ɗin new student ce, yasan magana take amma baya gane me take cewa sosai, ya dai
san hausa take.
Ya ɗauke bai tankata ba ya ce.
_“SCOPE OF SOCIAL STUDIES”_
_The word “man” in the definition given above connotes human beings while man’s
environment has a huge influence on mankind in all spheres of life. Man’s
environment affect their language, dressing, food and every other thing one can
think of in the society,_ _Man also interacts with two environments which are:_
Physical environment (Natural)
Social environment (Artificial)".

"Tab ni dai dama ba wannan makarantar aka sani ba, malamin ba babu abin da ya iya"
Azaan ya dubi Halisa ya ce "What's your name" ta tura ƙaramin bakinta ta ce "Me
kace?" Wata wacce ba zata shige age mate ɗin Halisa ba mai suna ABIR ta ce "Ya ce
ya ya sunanki?" Halisa ta ƙaramin murmushi kawai cikin siririyar murya ta ce
"Halisa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Azaan ya buɗe idanu da kyau cike da mamakin
jin sunan data alaƙanta kanta dashi, Yaa Sheikh take nufi ko wanne? Dama yana da
yarinya yaushe ma ya yi aure har ya samu yarinya kamarta?. Azaan ya ce.
"Abir make her understand, explain to her" Abir ta ce "Okey Sir" mai Hali baya
fasawa domin Azaan na shirin fita ta ce "Kuma na manta na faɗa maka ina da aure"
Azaan ya kalleta sai kawai ya fice dan ya lura bama tasan shi kansa auren ba har
take cewa haka. Ya tafi cike da sha'awar surutunta wanda ya birgesa lokaci guda.
Abir taiwa Halisa bayanin komai na topic ɗin cikin harshen hausa, ta ce amma ta
rage surutu da yawa a haka ta ƙare zaman makarantar wani karatun ta gane wani a'a,
Umar-khan da kansa yazo ɗaukanta sbd Yaa Sheikh yana can wajan lecture ba zai samu
dama ba.

Sarki Ahmad Nuran Kingdom.
Da sauri yake tafiya hannunsa zube cikin aljihu cikin yanayin kaɗuwa da kuma tashi
hankali, saukarsa kenan ƙasar kullum cikin tafiye-tafiye yake, kana kallon fuskarsa
kasan baya cikin nutsuwa da walwala. Ko'ina ya gilma acikin gidan sarautar bayi da
kuyangi ke zubewa suna gaida shi, amma kallon arziƙi basa samu daga gare shi. Kai
tsaye sashin Fulani Atine ya nufa, wata kuyanga ta sanar da Fulani Atine zuwan
yarima cikin jin daɗi ta bashi izinin shigowa bayan ta sallami hadiman nata. Tsaye
ya yi yana kallonta kafin ta ce. "Meke faruwa da kai El-bashir? Yaushe ka tafi da
har zaka dawo?" Yaƙi magana sai huce yake tamkar zakin dake neman abinci bai samu
ba. "Wannan ɓacin ran na mene What is the reason for bringing you back to this
country now?" Ya ɗauke idanunsa cikin ɗaga murya ya ce "Idan ina raye sai naga
bayan Yaa Sheikh hankalina zai kwanta, sai na tabbatar ya wahala a rayuwa kamar
yadda ya wahalar dani, zan tirkesa na musguna masa kamar yadda ya sanya ni cikin
damuwa da ƙonar zuciya na tsayin shekaru, sanyi amfani da uniform ɗin dake jikina
na police na jasa zuciya hanyar da zata ɓata suna da martabar da yake iko da su, ba
zan taɓa farin ciki ba muddin ina ganin gilmar Yaa Sheikh a duniya" Fulani Atine
tayi murmushi tana mmkin zafin zuciyar da El-bashir yake da ita, a hankali ta ce
"El-bashir duk bai kai wannan extent ɗin ba, pls i want u to calm down" cikin zafin
zuciya El-bashir ya ce "Ya kai har ya shige extent ɗin da da kike faɗa, a wannan
karan dole nayi gaba da gaba da Yaa Sheikh dole nai amfani da mutum mafi kusanci da
shi wajan ruguza rayuwarsa data ahhalinsa" Fulani Atine ta ce "Kana da hujja kenan?
kana da shaidar da zaka iya kurfanar da Yaa Sheikh a court? Kada ka manta lokacin
da al'amarin nan ya faru Yaa Sheikh baya ƙasar bare ka zurfafa cewa shi ya aikata,
kada ka tirke kanka maimakon Aliyu, nice shaidarka akan idanuna komai ya faru" El-
bashir ya riƙe hannun Fulani Atine ya ce "Ki taimaka mini na ɗauki revenge akan Yaa
Sheikh, ba zan iya ba, na kasa haƙura na kasa jurewa Fulani, ya rabani da jin
daɗina" Fulani Atine ta ce "Kafin ɗaukan fansa, dole ka nemi kusanci da Yaa
Sheikh, dole ka nemi gurbi a zuciyar ƴar fillon da ake magana, kasan yadda kayi ta
fifitaka akan shi" El-bashir yai shiru for some minutes kafin ya ce "Mene amfanin
saka ƴar fillo cikin al'amarin nan?" Fulani tai murmushi yaro yaro ne, daman ance
daka na gaba ake gane zurfin ruwa, ta ce "Idan ka taɓa ƴar fillo kamar ka taɓa
zuciyar dake sarrafa tunani Yaa Sheikh ne, nasan abin da kai baka sani ba,

Please Login or Register in order to submit comment