You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar musulmai ba a magana..
A hankali yake sakkowa cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan idanu yake,
ya ɗora Alkyabba jikinsa wani irin sahihin kyau ya yi na musamman, bakinsa ɗauke da
tasbihi na tafiya masallaci.
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, la'ilaha illallah! Allahu Akbar khabira,
Walahamdulillah kasira, Wasubuhanallahi bukuratan wa'asila" a fili yake faɗa har ya
sakko ƙasa. Ya samu Umar-khan cikin sabbin tufafi, sai Mai martaba Ahmad Sarki da
El-bashir tare da Ummul.
Kafin kowa ya yi magana idanunsa ya sauka akanta ta fito cikin duguwar riga fara
sol da ita ta yi rolling kanta da veil ba wani make up tai ba, amma tai wani kyau
mai ɗaukan hankali bakinta sai kyallin lips lamp yake, ta ƙara girma da kyau da
haske ko'ina na jikinta ya buɗe.
Idanunta rufe ba tare data lura da su Mai martaba ba ta nufi wajan Yaa Sheikh.
A hankali ya furta..
"No kankana bar Abba" shi kaɗai ya yi maganar shi kaɗai kuma yaji tana zuwa ta faɗa
jikinsa ta rungome shi tana riƙe hannun ta ce.
"Kafi mazan duniya kyau Abbana, ina son ka da yawa" Suka ji saukar maganar Mai
martaba ya ce. "Abbanki dai ki ka sani, amma ko ni ai nafi shi kyau" Yaa Sheikh dai
ya kasa cewa komai ita daman Ummul tasan za a rina. "Da gaske Abbana mai kyau ne
Mai martaba, banda abinka ai kai ka tsofa"
Umar-khan ya ce.
"Kuma ke ki ke kiɗanki ki ke rawar ki, Yaa Lee bai ce kinyi kyau ba" Yaa Sheikh ya
fahimci kowa shi dai bai isa an saka ya faɗi abin da bai niyya ba..
"Kafin nace ya yi kyau shi ya fara faɗa ai"
"Mu bamu ji ba, yaushe akai haka?" Ta ce "Idanunsa sune suka faɗan, Modibbo ka faɗa
yanzu kowa yaji kaga suna tsokanata Please kace nai kyau" gabaɗaya suka gyara zama,
sun san da Kamar wuya gurguwa da auren ne sa.
"Abba ka ce, ka faɗa musu na yi kyau zan yi fushi idan ka ƙi" nan da nan zufa ta
fara yanko masa harshensa ya harɗe ya shiga ƙoƙarin yin magana ya kasa, cikin
ƙarfin hali ya ɗan buga ƙafarsa a ƙasa ya riƙe kafaɗunta da kyau kamar zai kuka
cikin In-ina ya ce...

*Allah ya nuna mana Monday lafiya, mai son posting har* *weekend zai ƙara adding
500 a saka shi a Special grp*
*08119237616*
[1/3, 4:48 PM] Abk: Kasa faɗar abin da ya yi niyya ya yi, cikin sauri ya juya ta,
shi kuma ya juyawa su Mai martaba baya ya zama ba a ganin Halisa sai bayan Yaa
Sheikh.
A hankali ya kalli cikin idanunta wanda suka ciki da hawayen rigimar dasu Umar-khan
suka kunnanta, ya lumshe idanu tare da buɗewa ya juya mata su, kai tsaye ta gane
karatun na shi.
A hankali ta taka cikin tarin nutsuwar da kwana biyu ta tsinci kanta ciki, ta shige
jikinsa gabaɗaya suka sauke ajjiyar zuciya cikin ƙasa da murya ta ce.
"Abba zuciyarka bugawa take da ƙarfi" A zuciyarsa ya ce "Ba dole ba, kankana tai
jajir tai kyau!" A fili kuma ido kawai ya rufe yana ɗan matseta jikinsa da sauri
kuma ya saketa tare da juyawa.
Wayam! Ba kowa a parlourn kamar an kure su Yaa Sheikh ya juya ya kalli Halisa yana
ɓata fuska irin "Kinga abin da ki ka jaa?" Ita kam murmushi tai mai kyau ta riƙe
tsakiyar hannunsa.
Bai kulata ba ya ci-gaba da tafiya zuwa harabar gidan, motarsa kawai ta rage tare
da motocin securities ɗin da zasu take masa baya.
Ya shiga gidan baya, ita ma ta shiga driver ya jasu zuwa masallacin da zasu gabatar
da sallar idi, tunda suka tafi babu wanda ya ƙara magana, ganin ya kame kansa
idanunsa rufe ita ma tai masa shiru.
An gabatar da sallar idi lafiya kowa na farin ciki ana ta kaisa tare da yiwa juna
fatan ganin shekara mai zuwa, El-bashir ya rungome Mai martaba ya ce. "Barka da
Sallah One and in millions father's"
"Barka dai Auta" Umar-khan ya gaida Mai martaba yana cewa.
"Yanzu Mai martaba wannan ƙaton ne Auta?" Mai martaba ya yi murmushi yana riƙe
hannun El-bashir ya ce.
"Eh to kusan haka, amma bani da wani Auta sama da Mubasshir shi ne ƙarami kaf
masarauta" sukai dry.
Kusan tare motarsu Yaa Sheikh dasu Ummul da Mai martaba sukai parking a harabar
gidan, cike da nutsuwa da kamewar nan ta shi ya fito daga cikin bayan motar, Halisa
ma ta fito.
Ya kalli Mai martaba wanda shi ma ya fito Yaa Sheikh ya nufe shi tare da yi masa
gaisuwar larabawa ya rungome Mai martaba ya ce.
"Taƙabbalallahu minna waa minka, idil mubarak alaina wa'alaika" Mai martaba ya ce.
"Barka da shan ruwa babban Malaminmu, fatan munyi ibada karɓaɓɓiyya" ya ce.
"Amin" Umar-khan ya durƙosa har ƙasa ya ce.
"Barka da Sallah Yaa Lee??" Ya jinjina kai yana dafa kan Umar-khan ya ce. "Mun yi
sallah lafiya Omer?" Umar-khan ya ce.
"Allhamdulillah"
Gabaɗaya suka nufi cikin gidan daman tuni Halisa ta shige sbd ganin El-bashir dake
ta binta da idanu. Babu kowa a Main parlourn sai kayan abinci da aka kere saman
dining room.
Kai tsaye Yaa Sheikh bedroom ɗin Ummul ya nufa ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, a
tsaye ya sameta hannunta riƙe da gorar zam-zam tana sha, Halisa kuma na kwance ta
rufe ido kamar mai barci, kallo ɗaya ya yi mata ya san idanunta biyu.
Ya daɗe yana tunanin abin da zai ce a taushashe ya ce "Ta shi ki gaida Mai martaba"
tasan da ita yake, kuma baya magana biyu.
Ta miƙe tana karkaɗe jiki ta fita kanta a ƙasa.
Tana fita da sassarfa Yaa Sheikh ya nufi wajan Ummul, ta ajjiye gorar zam-zam ɗin
da sauri tana sakin murmushi,
Yana zuwa ya shige jikinsa ya rungome Ummul sosai yana sakin tagwayen ajjiyar
zuciya, ta rungume shi tana faɗin.
"Baka girma ne Arɗo? ƴar rainonka tun tana zanin goyo ka ke abu ɗaya, kalli yadda
ya girma i want my Arɗo to became a big man"
Ya yi murmushi wanda ta saba ganin shi a kan kamilalliyyar fuskar ta shi idan suna
tare.
"Ummul" ya faɗa a taushashe.
"Kaga ci kani, kafin baki abin magana ta zo, yanzu musha tambayoyi" ya sumbaci
goshinta tare da sakinta ya nemi waje ya zauna.
"Water, da dabino" ya ce bayan ya zauna, ta ɗauki ruwan mai sauƙin sanyi tare da
dabinon ajwa ta bashi. Ya rufe ido lokacin da zaƙin haɗi da garɗin dabinon ya ratsa
cikin kunnensa. Ya ci sosai yana ɗan kaɗa ƙafa.
Duk abin da yake tana kallon shi.
Bayan ya gama ta ce.
"Mene mafita? Ka yi wa Zahrah laifi, kuma ka barta ita ɗaya?" Bai ce komai ba,
tasan ba zai ce ɗin ba. "Kuma naji kamar kace bata jin daɗi" sai a lokacin ya ware
idanu akan Ummul yana miƙewa tsaye ya ce.
"Oh! Ƙari ya fito mata ko a ciki? za ai mata aiki"
Ummul ta ce "Wayyo Allah sarki, haka wata friend ɗina ta taɓa tsintar kanta ciki,
abin tausayi kai ka ɗauka tsohun ciki ne yau haihu ko gobe, cikin ikon Allah kuma
akai mata aiki, ban sani ba kam da nayi mata sannu ya kamata kaje gare ta"
Bai tanka ba kuma bata san yanayin fuskar shi ba da zata iya fahimtar kurman baƙin
na shi.
Lokacin da Halisa ta fita idanun El-bashir ya sauka kanta zuciyarsa tai kyakkyawan
bugawa, bai taɓa gani muguwar kamar da suke ba sai yanzu, kamar har ta ɓaci.
Ta watsa masa harara ya ɗauke kai yana jin zafinta tare da jin burinsa ya kusa
cika.
Cikin sakin fuska ta durƙosa wajan ƙafafuwan Mai martaba ta ce. "Barka da Sallah
Mai martaba" ya yi murmushi yana jinta har ran shi ya ce.
"Yawwa Matar Malam data Abba Hakimi" ta kumbura fuska ta ce.
"Ni Abbana kawai nake so, kuma shi kaɗai ne mijina Allah bana son kowa bayan shi"
Mai martaba ya ce.
"Ah lallai, bari Yaa Sheikh ya zo naji abin da yake miki har ya saye zuciyar ki"
ita ma ta tari numfashin Mai martaba ta ce. "Rai da numfashi ne kawai bai ban ba,
bayan Wannan ya bani komai"
"Iyee! Allah ya kawo ranar da Yaa Sheikh zai ce haka akan ki, mudai ajjiya muka ba
shi" ta ce "Ajjiyar me kuma mai rawani?" Ya ce.
"Abu mai mahimmanci mara rawani" da gangan Mai martaba yake janta da hira hakan
daɗi yake masa, ta zage suna ta hira wani abu idan ta faɗa sai ya yi saurin
kallonta wani abun kuma ya yi murmushi kawai.
Yaa Sheikh ne ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa Ummul abayan shi suka
ƙarasu parlourn, ta ce "Ga abinci can saman dining" suka miƙe bakiɗaya, Mai martaba
yana ta son ya tambayi Yaa Sheikh game da Ummul ɗin amma ya kasa El-bashir daman ba
wani shiga sabgar mutane yake ba, suka nufi dining ɗin Yaa Sheikh kuma ya nufi
upstairs yana faɗin.
"I need coffee"
Ummul ta ce "Halisa zo ki miƙa masa" bata san mene ya faru ba amma fushi take da
Abban nata haka kurum ta miƙe tana kumbure kumbure Ummul na lura da ita tai mata
banza.
Coffee mai zafi ta haɗa masa a mug tare da ƙaramin cup, El-bashir ya bita da idanu
lokacin data zo hawa upstairs wani abu na faɗo masa a rai. A hankali ta tura ƙofar
cikin siririyar muryarta ba kowa a parlourn saman na shi tayi saurin ajjiye tray
ɗin zata juya taji an riƙe hannunta ko ba a faɗa ba tasan shi ne, dan ta nuna bata
gane ta buɗe baki zata saki ihu ya yi saurin ɗora tafin hannunsa a kan bakin,
Ya dawo da ita baya tare da juyo da ita suka fuskanci juna.
Ta haɗe fuska tare da yin kicin-kicin da rai Yaa Sheikh ya riƙe ƙugu da hannu ɗaya.
"Meye samun Ƴar fillo"
Tai masa shiru tana ɗauke kai, ya shammaceta tare da sunkutar ta yana manneta da
jikinsa ya ce.
"Babyn Abba rigima dai"
Ta kalle shi da kyau jin ya furta _Baby_ amma sai tai shiru har ya shiga haɗaɗɗan
bedroom ɗinsa ƙin ajjiye ta ya yi, da ƙafa ya tura ƙofar yana murza key.
Ya direta ta ce "Ummul na jira na fa" ya ware manyan gajiyayyun Idanunsa irin.
_What elxty wrong with her?_ ɗin nan. Ya yi shiru kawai, tare da cire Alkyabba ya
cire rawanin kansa, duk tana tsaye taƙi kallonsa sbd gabanta dake faɗuwa.
Ya rage daga shi sai trousers a karo na farko kenan gaban ɗiya mace domin ko single
babu jikinsa, suma ce ko ta ina lub saman fatar shi.
Ya miƙa mata hannu tare cewa "Zo kiji" ta maƙale kafaɗa ta ce.
"Coffee ɗin ka" ya kame fuska yana kallonta ya ce. "Ban so" jikinta ya yi sanyi ta
ce "Please You have to drink or eat something" da ɗumbin mmki ya dubeta da kyau da
bakin turancin.
Sai kawai ya miƙe tayi saurin rufe idanunta jikinta rawa,
Bata taɓa ganinsa so sexcy haka ba, jikinsa duk a murɗe yake gashi trousers ɗin iya
laps. Her heart was pounding because of his breath on her neck,She was completely
confused and wanted to run away.
Ya gane nufinta dan hana ya saka hannu ya jawota yana faɗin..
"Al'amarin mace sai addu'a,kamata idan banci darajar igiyoyi ba, naci ta furfura"
tana ji ya juyota gabansa hannunsa ƙirjinta yana balle bottles na abaya lokacin
daya gama tayi saurin riƙi hannunsa a rarrabe ta ce.
"Ah...Abba" ya girgiza kai kawai kamar ba zai magana ba sai ya ce.
"Ni dai ba mijin novels ba ne, dan haka nutsu" ta buɗe ido ta ce.
"Amma ai kana da kyau" bai kalleta ba ya sutale rigar tare da yin cilli da ita,
bata saka wasu inners ba.
Sai wani palazzo pants, Iya haɗuwa ya haɗu _You can never go wrong with a pair of
palazzo pants as they are very fashionable_ daga palazzo sai white Padded bra. Mai
butterfly a tsakiyar ta.
Shap ɗinta ya bayyana Yaa Sheikh idanunsa ya jirkice ya sake ta yana juyawa tare da
danna wani waje, hasken bedroom ɗin yafi na ɗazo. Ya tsaya jikin bango yana harɗe
hannayensa a ƙirji ya shiga ƙare mata kallo From head to toe.
She looks so sexcya and damn cute.
Zata ɗauki abayar ya ce.
"Noo!! Ajjiye abar nan"
Ta marairaice ta ce "Abba na zauna ba suttura?" Ya share maganar ta, ya ƙarasu idan
take har lokacin yana ƙare mata kallo ƴar raino dai da gaske ta girma.
"Akwai iyayi dai cikin sutturar mace.... Ita wannan ba a cire ta?" Ya nuna bra ɗin
jikinta kunya ta kamata ta ce.
"Kai Abba, ni kunya nake ji" ya kasa magana sai jawota da ya yi jikinsa naked
jikinsu ya mannu waje guda wanda ya haifar wa da Halisa wani irin shock.
"Say Allahamdulillah!" Ta furta "Allhmd"
Ya jata har gefen gado ya zauna tare da zaunar da ita saman cinyoyinsa, ya zagaye
hannuwansa a ƙasan ƙirjinta ya ɗora kansa a shoulder ɗin ta.
Sukai shiru suna jin ɗumin juna
Sun jima yana murza tsakiyar ƙirjinta kafin ya zame fuskarsa zuwa bayanta ya shiga
goga mata hanci ya ce.
"Wace Dada?"
Ta kalle shi da sauri tana juyawa bakiɗaya suka fuskanci juna ta ce.
"Babata ce, ita ta haife ni kuma ta haifi Shatu da Hamma Yabi" ya jinjina kai ya ce
"Allah ya jiƙan shi" ta ce.
"Kasan shi ne?" Ya tura baki ɗaya fuskarsa ƙirjinta yana sauke numfashi a hankali
ya shiga unhooking na bra ɗin jikinta yana gamawa ya yi cilli da ita ta ƙanƙame shi
ya sauka numfashi tare da jan duvet ya rufe su bakiɗaya. "Please Abba kada ka ƙara
baffi" ya shafa kanta yana kwantar da ita saman jikinsa ya ce..
"Barci za mu yi, ba zan ba" ta jinjina masa kai.
Sai wajan sallar Asr Yaa Sheikh ya farka yana rungome abu ya ji pillow ashe ta
gudu. Ya girgiza kai kawai, yana shigewa bathroom.
Ƙamshin turaren Roja ya cika platforn wanda ya tabbatar musu da Yaa Sheikh ɗin ya
fito, cikin rashin fahimta yake bin su Mai martaba da kallo ganinsu shirye ga
Halisa dake jikin Ummul tana ta kuka kamar ranta zai fita,
Sai torelly bag ɗin da kayan ta ke ciki.
Ya gyara zaman jallabiyar jikinsa Mai martaba ya ce
"Aliyu daman kai nake jira, jirgi yana ta jirana kuma ban son ta shinka, sbd
muhimmancin barcin naka" yana ɓalle diamond rolex ɗin shi ya ce. "Fatan dai
lafiya?"
Ya tambaya idanunsa akan Halisa.
Mai martaba ya ce "Al'ƙawarin Abbanka Hakimi zan cika na tafiya da ita" nan fa ɗaya
Yaa Sheikh ya yi ta kallon Mai martaba ya ce.
"Zamu zo tare ko?"
"Na riga nai al'ƙawari bana jin zan saɓa, dole naje da ita, kai ma sauƙi ne gare
ka?" Yaa Sheikh ya kalli Ummul ta jinjina masa kai.
Ko ba a faɗa ba a wannan karan Yaa Sheikh ya shiga damuwa ya yi gaba yana cewa.
"Allah ya ki ya ye" ko Halisar bai kalli inda take ba, gani yake kawai tana sane
data amince zata bisu, yafi jin zafinta fiye da Mai martaba ɗin..
Ummul ta dinga rarrashin Halisa ta ce tare zasu tafi itama za taga gidansu.
Aka bar gida daga Umar-khan sai Yaa Sheikh da ya tafi masallaci. Tun safe daya kira
number Zahrah ya ji a kashe bai sake nema ba. Jirginsu Mai martaba ya ɗaga da El-
bashir, Ummul sai Halisa wacce gabaɗaya zuciyarta na Saudiyya gangar jikinta kawai
ke cikin jirgin.
Har suka isa airport ɗin dake nan garin Kano Halisa bata bar kuka ba, Mai martaba
ya shiga motar Abba Hakimi daya zo ɗaukar shi.
Ummul da Halisa na baya El-bashir na driving motar wanda ya karɓa a airport ɗin.
Sun yi nisa ya ɗauke hanya ya shiga nausawa cikin daji sosai Ummul da Halisa dai da
idanu suke binsa tunda basu san hanya ba, ya yi parking gaban wani gida fuska ba
walwala ya ce "Ke fito" tsoro ya kama Halisa ta ce "Naje ina? Ai ba gidan mother
bane nan" Ummul dai na zaune tana murmushi ba tare da ta ce komai ba. Ya saka hannu
ya fisgo Halisa da ƙarfin gaske ta fasa ihu.
"Me nayi maka? daman nasan kai babu Allah cikin ranka tunda ka nemi kashe Abbana"
El-bashir ya ce "Abban naki macuci, Azzalumi, ma yaudari wanda kassara rayuwata, ya
lalata mini farin cikina, ya mayar dani abin tausayi cikin ƴan uwana har shi ki ke
jin tausayi?" Cikin kuka ta ce "Ƙarya ka ke, Modibbo ba mugu bane, kai ne Azzalumi
wanda ka nemi kashe shi" El-bashir ya zaro bindiga ya ce "Yanzu kuma ke zan kashe
tunda ke ce rayuwar shi, ba zai iya rayuwa babu ke ba, idan na kashe ki nasan zai
mutu ya yinda ya kasa jure rashin ki" Halisa ta kalli Ummul wacce take tsaye jikin
mota ko a jikinsa sai waya ma da take dannawa tana ɗan waƙarta. "Ummul kina jin me
yake cewa zai kashe ni akan idanunki?" El-bashir ya saki dariya ya ce "Wai wannan
ki ke tunanin zata kuɓutar dake? Waye ya bada shawarar a bawa Yaa Sheikh poison?
Waye ya shaida mini ke ce raunin Yaa Sheikh? Waye ke mini aiki gidan Yaa Sheikh?
You have no idea about it, ki yi numfashi na ƙarshe" El-bashir na shirin sakarwa
Halisa bindiga ya ji an ɗora masa bindiga akan shi. Ya juya da sauri ya yi idanu
biyu da Ummul dake tsaye hannunta riƙe da bindiga ta zare a bayar jikinta kayan ƴan
sanda ya bayyana a jikinta. Ya kalleta ya ce.
"ASP Ummul-khairy ni uban gidanki ki ke ɗagawa bindiga.....
[1/4, 7:47 PM] Abk: "Mamakin yadda na ɗora maka bindiga aka, ka ke yi ko IGP?"
El-bashir ya kasa magana sai kallon ASP Ummul-khairy yake mamakin yadda ta juya
reshe zuwa mujiya yake.
"Me hakan yake nufi Asp? Ni shugabanki ki ke sakawa bindiga akai? For what reason?"
El-bashir ya faɗa yana gyara tsaiwar shi. Ummul ta ce. "Oh! You're so fool El-
bashir Ahmad Nuran Sarki, You lost completely lost" El-bashir ya ja numfashi
fargaba da mamaki sauyawar al'amarin lokaci guda,
Ya shige shi.
"Ba haka mukai dake ba, kinje gidan Yaa Sheikh domin kawo mini information na abin
da yake faruwa a can"
Ya girgiza kai launinsa na sauyawa ya ce.
"Why Asp Ummul-khairy? Ke na faɗawa Abin da Yaa Sheikh ya aikata mini, na yarda
dake ka amince maki don me za kici amanata?
akan me zaki hana ni kashe Halisa bayan dake muka haɗa plan ɗin zan kasheta?"
Ummul ta ƙara gyara tsaiwa still tana riƙe da bindiga ta ce.
"You're right El-bashir Ahmad Nuran Sarki, kayi kuskuren saurin yarda dani, without
knowing me, kana tunanin zan zuba idanu ka kassara ni ka kassara zuciyata?"
"Mene haɗin kashe Halisa da zuciyarki?"
Cewar El-bashir.
Ummul ta kalli Halisa ta ce. "Enter into the car"
Jikin Halisa na rawa ta buɗe ƙofa ta shiga hawaye kawai take zubarwa,
Ga rashin sallama da ba suyi ba da Abbanta, ga firgicin bindigar da El-bashir ya
nuna mata,
Uwa uba sabon al'amarin daya kunnu kai,
Ganin Ummul cikin police uniform ta ƙara tayar da hankalin Halisa.
Ummul ta ɗauke shirun da cewa.
"Dan me na shiga aikin ƴan sanda baka sani ba, kuma ni na nemeka da aiki ba kai ba
kai ka nemeni da aiki ba, El-bashir kayi kuskure daka hari Asp Ummul-khairy ta san
sirrinka ta kuma san manufarka, kana tunani zan zuba maka idanu ka kashe mini
sirika? Ko kana tunanin zan saka maka idanu ka kassara zuciyar wanda ta cika da son
ka?
Bayan ni abu biyu Yaa Sheikh yake so kuma yake ƙauna, da kai da kuma Halisa Danejo
Rome, bani da lokacin yi maka bayani amma ka sani na shige tunaninka, ko da nace ka
bawa Halisa poison tazo da shi sbd nasan har abada Halisa ba zata bawa Yaa Sheikh
poison ba, ban faɗa mata komai akan haka ba, amma aljanun dake kanta tun yarinyarta
ko nace tun tana ciki ba zasu bari Yaa Sheikh ya sha poison ba,
Next target naka shi ne zuba hudar iblis cikin kayan Companyn Sarrafa shinkafa na
Yaa Sheikh,
Ka saurara ka tsaya da wasan iya nan, Aliyu ba sakarai bane baka san waye shi ba,
zakai ladama mai ciwo ta har abada idan kasan abin da ya akai ta"
Ta sauke bindigar tana mayar da ita gefen wandonta, ta ɗauki abaya ta riƙe ta ce.
"Ka sakani abin da ban niyya ba Mubasshir, i don't know how to explain idan mai
surutun nan ta tambaya, ka jamu zuwa gidansu Yaa Sheikh kada kai tunanin yin komai
domin ina da record naka"
Ta buɗe mota ta shiga Halisa na ganinta tayi saurin saka kuka ta ce.
"Meke faruwa ne Ummul,me ya sa zai kashe ni? Naji bana son shi" Ummul ta riƙe ta.
Tana faɗin "Ba komai Daughter nutsu"
"Ummul Abbana" Ummul ta riƙeta da kyau ganin gabaɗaya duk ta tsorata ta ce.
"Arɗona, ko Modibbonki jirkin shi na hanya, bari muje kuyi waya ko"
"Ummul bana son wannan mugu ne, azzalumi ne tsoro ya kamani ki kai mu gida da kai
ki" Ummul ta girgiza kai kawai.
"Ban san area naku ba, shi ne da kan shi zai kaimu" Ta jinjina kai tana yin shiru.
Ummul tai murmushi tana danna wata number a wayarta.
El-bashir sai hargitsa sumar kan shi yake,
Ta shammace shi, bai zaton haka ba, yana ta shuka a idon makwarwa,
Ya ɗauka da gaske ya samu amintacciyar investigator ashe ita aiki take da shi,
Tsakanin shi da ita wake farautar wani ne?.
No Answer!
Shi ne kawai, ya rasa yarda zai yana ji yana gani ba zai bari Ummul ta tuna masa
asiri acikin jama'a da Idanun Mai martaba ba,
Kuma ba zai taɓa barin Yaa Sheikh ba, dole ne ya yi masa rauni a zuciya kamar yadda
shi ma ya yi masa. Rai ɓace ya buɗe gaban motar ya shiga tare da yi mata key.
Babu wanda ya sake magana har sukai nisa lokacin tuni barci ya ɗauke Halisa jikin
Ummul, suna zuwa wani waje Ummul ta ce.
"Drop me here"
Ya yi kamar bai ji ba ta sake cewa "Ka sauke ni a nan" ya yi parking gefen titi
Ummul ta zare Halisa a hankali tare da kwantar da ita. Ta fita tana daidaita kanta
ta ce.
"A gaida jama'ar gidan, kada ka manta I Asp Ummul-khairy Abdullahi Abdul-majeed"
Ya figi motar da ƙarfi tare da yin gaba, murmushi kawai Ummul tayi tana kiran
number ana ɗagawa ta ce.
"Na iso"
Tana nan tsaye wata haɗaɗɗiyar mota ta tsaya a gabanta ta buɗe ta shiga motar ta
harba kan titi. Abba Hakimi ne tsaye yana duba agogo kafin ya juya ya kalli Mai
martaba ya ce.
"Kace El-bashir ya ɗakko su?" Mai martaba ya ɗaga kai with so much respect ya ce
"Shi ne, i wonder why ya jima haka"
"To Allah ya kawo su lafiya, amma sun jima ga mutuniyar sai a hankali"
Mai martaba ya ce "Allah dai ya sa ba rigima take ba" Abba Hakimi ya yi murmushin
manya ya ce.
"Idan tayi ba laifi, amma nasan Aliyu ba zai taɓa biyo sahunta ba, tunda dole mukai
masa na tafiya da ita"
Mai martaba ya ce "Anya? Ka shirya rabasu kenan?" Kafin Abba Hakimi ya yi magana
motar El-bashir ta shigo da gudu ashe ya jima yana horn kafin gatekeeper ya buɗe
masa gate ɗin gidan.
Gabaɗaya suka bi motar da kallo El-bashir ya fito ganin babu wanda ya a fito yasa
Abba Hakimi kallon El-bashir ya ce.
"Mubasshir ina sauran, Halisa da baƙuwar da aka ce?" Yana shiga cikin gidan ya ce.
"Tana mota, ɗayar kuma ta sauka" ya ƙare maganar yana shigewa cikin gidan. Kafin
Abba Hakimi ya ce komai Mother ta fito fuskarta ɗauke da farin ciki ta nufi motar,
ganin Halisa kwance na barci ta ce.
"Ikon Allah!"
Ta buɗe motar a hankali ta shiga bubbuga kumatunta ta ce.
"Daughter, Daughter"
Halisa ta buɗe idanu da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "Ummul" Mother tai murmushi
ta ce..
"Da alamar Ummul na neman ƙwace mini ɗiya, zan so naga Ummul ɗin nan" da idanu
kawai Halisa ke bin Mother kafin ta juya cikin motar ta ce "tare muke da ita fa,
shi ne ta barni ba Abba ba ita?" Mother ta ce.
"Oh! Ita ce? El-bashir ya ce ta sauka a hanya ai muje ciki daughter"
Gabaɗaya suka nufi cikin gidan Mother sai jan Halisa take jiki ganin yadda ta sauya
bakiɗaya ta ƙara kyau haske ƙiba, skin ɗinta sai glowing take. Umma A'isha ta saki
murmushi ta ce.
"Maraba da baƙin Saudiyya, barka lale" ganin yadda suke ta nan nan da ita yasa
Halisa sakin jikinta ta ce.
"Ina yini Umma?" Umma A'isha ta ce "Lafiya lou Halisa ya Abban naki?" Tai murmushi
kawai tana kallon Mother, Mother ta ce "Kije kiyi wanka akwai kaya dana ɗakko miki,
ki shirya kizo kici abinci ko?" A sanyaye ta ce.
"To Mother" ta shiga bedroom ɗin da aka nuna mata, tana shiga ta fara kallon ɗakin
komai tsaf ya haɗu sosai.
Ta lumshe fararen idanunta hawaye ya shiga sakko mata babu wanda take son sakawa a
cikin idanunta kamar Yaa Sheikh, ta lura da zafinta a cikin idanunsa ko kallonta
bai ba lokacin da zasu bar ƙasar Saudiyya. wanka tayi ta shirya cikin simple ɗin
Abaya baby peach ta zauna jikinta sosai ta ƙara haska fatar ta, ta shimfiɗa ladduma
tai sallar magriba wacce aka kira yanzu..
Bayan ta idar tai shiru a hankali kuma ta sauke numfashi tana riƙe jikinta moment
ɗinsu da Abbanta Yaa Sheikh take tunawa komai nasa nada banne, salon shi da yadda
yake gabatar da komai. "Kayi haƙuri ka yafe mini Abba"
"Me ki kace?" Cewar Mother tana shigowa cikin bedroom ɗin. Tai murmushi kawai ba
tare da ta ce komai ba, Mother ta nemi waje ta zauna tana lura da sabuwar nutsuwar
Halisa ta yaba da ƙoƙarin Yaa Sheikh wajan bata tarbiyya da karatu mai kyau ya riƙe
amanar da aka bashi da hannu biyu, duk ƙoƙarin Mother na hango wani abu tattare da
Halisa bata fahimta ba, ta

Please Login or Register in order to submit comment