You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki hanani auren adalal mace"

Batace masa komai ba ta kwanta tana ta karkarwa idonta a rufe tana hawaye ga jikinta yayi zafi zum.

Batayi bacci ba har sai da aka kira assalatu a kunnenta,da k'yar ta iyayin alwallah tayi sallah saboda sanyin da take ji.

************

Ji tayi ana dukanta da k'arfi,a hankali ta bud'e ido tare da yaye mayafin.

"Ki tashi ki dama koko gashi can an siyo gasara,Ummi ta tafi siyo k'osai"

A hankali ta mik'e zaune,akwai zazzab'i a jikinta amma ba kamar da dare ba.

Wani azababben ciwon kai take dan haka bata ma iya bud'esu sosai.

"Magana fa nake miki"

A hankali ta furta "ni ban iya ba na san koko amma ni bansan miye gasara ba"

"Kan uba! Ke ni kike fad'awa haka?"

Da Sauri ta Saka hannayenta a fuska dan karya mareta.

"Ki tashi ki fito yanzu-yanzu ki had'a wuta ki dama"

"Aliyu bana son in maku abinda zaizo bai ciwu ba ni ban Iya irin abincinku ba"

"Wallahi sai kin dama minti d'aya na baki yanzu-yanzu ki fito"

Ya fice ya barta.

Jakarta ta bud'e ta d'akko brush da maclean ta fita.

Ruwa ta zuba a budar ta zauna tana shirin farawa kawai taji an warce.

A tsorace ta d'ago kai ta kalleta.
"Umma lafiya?"

"Ni kike tambaya dan uwarki?"

Jin maganar tayi ta dira a k'irjinta,ga bata son hayaniya saboda bata da lafiya,shiru tayi ta sadda kai,Umma ta cigaba da fad'in "sannu d'iyar shugaban k'asa kowa yana wanke baki da gawayi ke kinayi da maclean ko"

_gawayi kuma?cab Allah ya sawwak'e min_ ta fad'a a zuciyarta.

"Oh ga 'yar iska tana magana kin shareta ko"

"Umma ina mamaki ne"

"Na uban me?"

"Ina ganinku ne tamkar aljanu dan bana ganin isowarku sai dai in ganku a gabana"

Wani wawan duka da takai mata a baya yasa ta bank'arewa tare da maida kanta ta had'e da gwiwa.

Fad'a umma tayi tayi tamkar ana tunzurata.

Aliyu na shigowa ta zayyana masa maganganun cin mutumci wai Janan ce ta fad'a mata,sai kuma ta hau kukan k'arya.

Ganin Janan d'in ta kifa kai bata d'ago ba yasa shi cewa "Janan me na fad'a miki?"

Ta d'ago kanta fuskarnan sharkaf da hawaye hancinta yayi jajir fatar idonta ma tayi jajir ta kumbura.

"Ina son nayi brush kafin na d'ora kuma ta k'wace min,haka wayata ma tun jiya bata dawo min da ita ba"

"Da wayar da wannan d'in duk kin rasasu ki d'auki gawayi ki daka ki wanke bakin kamar yadda kowa keyi" Umma ta fad'a.

Aliyu shima cewa yayi "kiyi yadda tace,idan kuma baza kiyi ba kanki,ni dai kije ki dama mana koko dan yunwa nakeji kuma inason shiga Kaduna yin magana da ubanki dan shima ya dace ya fara fuskantar k'alubale daga yanzu"

A rud'e ta kalleshi,shi kuma ko a jikinsa ya wuce d'aki kawai.

Umma tayi dariya ta fita tana fad'in "Allah yayi maka albarka d'ana"

Jikin Janan a sanyaye ta tashi ta nufi can tsakar gidan taje gefen murhunsu ta d'ebo gawayi ta koma ta d'auki dutse ta wankeshi sosai sannan ta daka,a tsantsance tayi brush da gawayi da yatsanta.

Tana gamawa ta shiga d'akin ta same shi a kwance.

"Aliyu nayi brush da gawayin" ta fad'a tana kallon shi.

"Wannan kuma ruwanki,ni dai kije kiyi abinda aka saki dan na fad'a miki fita zanyi"

Durk'usawa tayi a k'asa tace "Aliyu wallahi ban aureka da wata manufa ba,na aureka da zuciya d'aya kuma saboda son da nake maka meyasa bazaka soni kamar yadda nake sonka ba?"

Wata mahaukaciyar dariya ya shek'e da ita sannan ya kalleta yace "so kuma? Ban tab'a jin ina sonki ba,fansa kawai zan d'auka in kad'aki"

"To amma ni meye laifina da zaka rik'a azabtar dani haka?"

"Laifinki ke d'iyar maha'inci ce azzalumi,sannan kin girma an kuma ciyar dake da haram"

"To naji amma dan Allah zan so in san laifin da Abba yayi muku?"

"Ba damuwarki bane"

"To amma ai mahaifina ne"

Kallonta yake ba tare da yace komai ba.

Ta cigaba da fad'in "na yarda zan muku bauta duk abinda kuke so ko ban Iya ba zan iya in muku,duk abinda zakayi wa mahaifina ka dawo dashi kaina dan Allah karka cutar da mahaifina na yarda zan jure komai"

"Har mutuwa?"

"Eh zan iya bada rayuwata saboda soyayya"

"Son da nake maka kai da Abba"

"Hmmm gaskiyane"

"Hakane ai soyayya ba k'arya bace Aliyu,sannan ko wane mahaifi yana da daraja"

"Yayi kyau idan kin gama surutun sai ki tashi ki fita dan ni wallahi na tsaneki"

Tashi yayi ya fice ya barta anan.

Jikinta a sanyaye ta tashi ta fita.

Kallon Ummi tayi wadda tayi cirko-cirko a tsaye tace "ina garin kokon"

Kallonta tayi a yatsine tace "sai yanzu kikaga damar fitowa"

'Daki ta shiga ta d'akko ta mik'o mata tare da fad'in "ga karare da yayi can ki had'a wutar"

Kallon gasarar tayi ita a tunaninta ma kokon ne dan ta ganta fara tas.
_to ya akeyi ne?_ ta tambayi zuciyarta sannan ta wuce dan ta san bata da amsa.

Hayak'i sai tashi yake tana k'ara hura wutar da baki.

Idanunta sun yi jajir sai hawaye take.

Da k'yar ta samu ruwan ya tafasa,wata murar dole ce ta kamata saboda hayak'i.

'Daukan gasarar tayi ta zuba kan ruwan da yake tafasa.

Cigaba tayi da hura wutar tana jiran ya dahu.

Bayan ta gama ta juye a cikin kwanon da suka kawo mata sannan ta d'auka ta nufi d'akin Umma kanta nata zafi saboda ciwo.

Da sallama ta bud'e labilen sannan ta ajje a gaban Umma tace "gashinan na gama"

"Dama koko kusan awa guda,gaskiya yarinya da sauranki"

"Ummi d'akko Kofi in zubawa Aliyu idan yaga dama ya rage mata"

Mik'owa Umma tayi tana fad'in "Umma yau rogo zata dafa mana da rana"

"In kin gama karyawa sai kije ki siyo bushsh........" Bata gama fad'a ba ta tsaya cak yadda taga kokon wani guda-guda gashi ya canza kala ma,a tak'aice ba wanda zai iya sha.

"Meye wannan?" Umma ta fad'a da k'arfi.

Duburburcewa Janan tayi ta rasa me zata ce ma.

"Tabb lallai ke d'in nan kin cika 'yar rainin wayo" Ummi ta fad'a.

"Maza ki kirawo min Aliyu a waje" Umma ta fad'a hannunta rik'e da murfin kwanon har lokacin bata rufe ba

Ummi ta tashi da sauri ta fita,ita kuwa Janan tun kafin ya shigo ta fara kuka dan ta san duka ne zata sha tamkar Jaka.








_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*🎢🎢Wannan taken na masoya neπŸ‘―πŸ»β€β™‚wannan shafin na masoya neπŸ’ƒ.🎢🎢*_
_Ban san yadda zan iya musalta jindad'i na gareku masoyana,wannan comments d'in naku yana matuk'ar ratsa zuciya ta,ta hakane nake samun more ideas,kuma kuna k'arfafan gwiwa ina yinku sosai masoyana makarantana wannan shafin naku ne kyauta🎁❀_.



20

Kafin yazo ta tashi tayi saurin shigewa d'aki.

Rufowa tayi ta saka sakata ta ciki.

'Kirjinta sai bugawa yake musamman lokacin da taji yana fad'in "Janan ki bud'e ko in b'alla k'ofar"

Zuciyarta nata wasi-wasin akan ta bud'e ko karta bud'e.

Daga k'arshe dai kawai ta bud'e tare da komawa gefe.

Yana shigowa ya shak'ota,da k'arfi ta k'waci kanta ta fito tsakar gidan,ya biyo ta yana ta duka.

Ganin yana neman kasheta ne ya saka tayi hanyar waje,zata fita yayi dai-dai da shigowar Zuhra gidan.

Da sauri ta tare ta tare da fad'in "Subhanallah"

Baima damu da ganin Zuhrar ba ya taho gadan-gadan,da sauri Zuhra ta shiga gabanta tare da tare wa da hannunta.

"Meye hakan?" Ya fad'a

"Kai zan tambaya meye hakan"

Iccen hannunsa ya yadda tare da hard'e hannunshi yana kallonta "shin wama yace kizo gidannan da sassafe haka?"

"Allah" ta fad'a tana masa kallon mamaki sannan ta cigaba da cewa "Allah ne ya saka na zo gidan nan yanzu dan ya nuna min irin yadda kake azabtar da matarka dan ya yanke min wahala"

"Kamar ya kenan?"

"Kamar yadda na fad'a dan bazan tab'a auren miji mai dukan matarsa ba,bari in tak'aita maka daga ranar da mijina ya kai hannunsa jikina to tabbas ya tsinka igiyar aurensa"

Ta juya ta kalli Janan taga yadda duk sauro yayi mata tamkar kuraje sunyi jajir,ga fuskarta da jikinta duk sahun duka.

"Wannan ai abin kunya ne,kuma ka jawa kanka zagi a k'auyennan,da a haka zata fita kai kuma kana binta da duka ko d'ankwali babu a kanta Aliyu ina ilminka?"
Wasu hawaye ne suka sauka a fuskarta ta saka hannu ta goge.

"Zo muje" taja hannun Janan zasu fita yayi saurin cewa.

"Idan kika fita wallahi sai kin fuskanci tsatstsauran hukunci"

Cak ta tsaya tana k'ok'arin janye hannunta daga na Zuhra.
Zuhra tayi-tayi Janan ta bita amma tace a'a kawai,ita tsoronta d'aya karya saketa dan son da take masa ta gwammace ta zauna a hakan.

Cikin b'acin rai Zuhra ta tafi,Janan ta juyo tare da ajje gwiwoyinta a k'asa
"Umma dan Allah kuyi hak'uri"

"Dalla yi mana shiru munafuka kawai"

"Yaya yanzu shikenan ta rabaku da Zuhra" a fusace ya juyo ya kalli Ummi Wanda kallon ya saka ta yin shiru dan yadda taga idonsa ya kad'a yayi jajir.

Bai sake yin magana ba kawai ya fice ya bar gidan.

**********

A babban falon gidansu Janan yake zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana jiran fitowar Abba.

Tare da Mameey suka sakko wanda yana ganin ran Aliyu ya b'ace ya kawo a ransa cewa lallai k'ila Janan ta masa laifi Wanda shi yace babu ruwanshi game da aurensu.

Zaunawa sukayi yana binsu da ido,ganin yak'i ko gaishesu ne yasa Mameey fad'in "na aika akai muku breakfast akace gidan a kulle"

"Ke kike tare da yunwa amma bani ba" yadda ya fad'i maganar ne ya saka ta saurin tashi daga kishingid'e ta kalleshi "Aliyu kasan kuwa dawa kake magana?"

" 'Kwarai kuwa Fatsima ce uwar Janan"

Abba ne ya tashi zai kifa masa mari ya rik'e hannunsa yace "dakata Hashim idan wannan hannun ya saba Marin Janan to ni nafi k'arfin ka mareni"

"Securities" Abba ya fad'a da k'arfi.

Aikuwa su wajen 5 suka shigo har lokacin Aliyu bai saki hannunsa ba.

"Ku kamashi Ku rufe min har sai na nemeshi"

Suna rik'eshi ya fara magana da k'arfi "Shekaru 8 nayi a prison dalilinka,ka kashe min mahaifina da k'anwata kuma matata sannan a wannan karon ma kana neman aikata haka,to wallahi ka tabbatar idan aka rufeni tamkar an rufe Janan a kabari ne,saboda na bada sallahun idan ban dawo ba a kasheta"

Jin hakane yasa Abba yace su sake shi sannan ya basu umarnin su fita.

Kallon Aliyu ya sake yi yace "waye kai?"

"Haidar abokin shahararren mai shigo da miyagun k'wayoyi Usman Attahir wanda a shekaru goma da suka wuce ka kamani ka saka a prison har tsawon shekara takwas dan haka yau nazo d'aukar fansa"

Shiru Abba yayi dan har yanzu ya kasa tuno ko wane ne.

"Lokacin da aka kawoni gurinku kuna meeting kasa aka fita dani kace a kulleni har sai ka nemeni tsahon shekaru takwas baka duba case d'in ba kuma kasan bani da laifi,sai wani bawan Allah ne yayi min hanya aka sake ni,ka cuci rayuwata ni da mahaifiyata da k'anwata da kuma Mahaifina da matata daka kashe,lokacin da na fito nan gidan shine gidanmu amma ina zuwa naga komai ya canza hatta mak'otanmu babu su duk an had'e har gidansu a gina maka tamfatsetsen gida, sanin da nayiwa unguwarnan a da bamu da yawa dan wajen garice sosai amma sai gashi ta dawo unguwa ta masu kud'i kuma cikin gari ,dukiyarmu da gadonmu gonakinmu da filayenmu duk suna gidan nan"

"Haka nayi ta garari tsawon wata biyar ina neman dangina,a sanadin wata yarinya zuhriyya na samu iyayena a can wani k'auye kusa da nan Kaduna,tun daga lokacin na shirya d'aukar fansa har na samu aiki a gidan nan kuma naga babu yadda za'ayi na d'au fansa ba tare da na auri zuri'arka ba,haka nayi ta addu'ar cimma nasara har Allah ya kawoni lokacin"

"Janan ta fara shan uk'uba domin kai bazan iya yi maka komai kai tsaye ba amma ka shirya amsar gayyata daga kotu dan daga nan can na nufa"

Ya juya zai fita Mameey ta fara kuka tana fad'in "Janan baiwar Allah ce karka cutar da ita"

"Nima bawan Allah ne amma an cutar dani"

"Kayi hak'uri Haidar" Abba ya fad'a a sanyaye.

"Ka rik'e hak'urinka zai maka amfani a kotu bana buk'atar jin wani abu"

Da sauri ya fice,Abba ya zube akan kujera yana fad'in "Allah ka sani banyi da niyya ba bani da shirin cutar kowa" hawaye ne ya sauka a fuskarsa Mameey tayi saurin cewa.

"Haba gwarzon namiji bai kamata ana ganin hawaye a fuskarka ba,duk kanmu musan baka cuceshi ba,hasalima bazaka ce ga kamanninshi ba in ba yanzu daya bayyana kanshi, shima idan zaiyi tunani ya san da ka cuceshi to zaka gane shi kuma ka hanashi aiki a gidanka bare auren 'yarka"

"Ni yanzu kawai Janan nake ji na san tana cikin wani hali gashi sun bar wancan gidan dana basu a tunanina"


"Karki dameni da maganar Janan babu ruwana da ita komai ya faru damu ita ce sila"

" Janan yarinya ce she's just 16 dole in damu da ita dan bata da wani wayo"

"Amma a hakan ai ta san tace tana son wani ko?"

"Ka daina wannan zancen soyayya ai daban ce"

"Nima ki daina min zancen Janan ki k'yaleni inji da lamarin yaron nan"

"Wai to da yake ik'irarin gidan nan nasu ne shin ba siya kayi ba?kuma ai kana da takardun filin"

"Babu nashi a ciki dan lokacin dana siyi filin mak'otansu shi gidansu babu kowa naga babu yadda zanyi in raba ginina kawai na saka aka had'a min dashi da niyyar idan masu gidan sun zo zan basu kud'in gidan ko nawa suke buk'ata,banma san gidansu Haidar bane, wallahi aiki ya shige min na manta shaf da case d'insa sai da aka yi shekara takwas sannan aka zo min da labarin har yanzu yana nan to a lokacin ne na rubuta aka sake shi dan ni ko kamannin shi ban sani ba a lokacin amma nace a bashi hak'uri kawai"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,yallab'ai meyasa ka had'e da gidan da baka san ko na wane ba,yanzu dai kawai ka bashi hak'k'insa"

"Tabbas a lokacin ance min 'yan gidan sun tashi ba'asan ina suka shiga ba tun lokacin da 'yan sanda suka kawo musu farmaki suka kashe mutum d'aya suka tafi da mutum d'aya,ban tab'a kawowa a raina Haidar ne dan na manta da case d'inshi tun da dama kawo min akayi ina jin ko wani abu sukawa 'yan sanda ko rashin kunya shiyasa sukayi kisa,zan nemishi ya fad'i ko nawa yake buk'ata a matsayin kud'in gidan zan bashi,amma ni ban san labarin dukiyarshi da gonaki da filayen shi da yace suna hannuna ba"

"Allah ya rabamu da sharrin mugu yasa abin ya tsaya iya haka"

"Ameen" Abba ya fad'a.

Haka suka yini cikin damuwa,Mameey sai kiran Janan take amma wayarta a kashe.

Koda Fahad da Fauziyya suka dawo Mameey ta basu labari, Fahad yace k'arya yake kurin banzane babu abinda zai iya,Fauziyya kuwa tace zataje gobe ta gano lafiyar Janan tunda ta san k'auyen su Aliyun.


*********

Tana zaune gaban Malam tana kuka, Aliyu na d'ayan gefen Malam ji yake zuciyarsa na k'ara zafi idan yana kukan.

Malam ya cigaba da fad'in "karka damu Aliyu duk kishi ne ke damun matan yanzu su a dole bazasu auri mai mata ba amma ai mune muke da iko dasu dan haka ka fara shirye-shirye wata na kamawa za'ayi aurenku da iznin Allah"

"Allah ya yarda Malam" Aliyu ya amsa cikin jindad'i.

"Tashi ki bamu guri" Malam ya fad'a

Jikinta a sanyaye ta fita dan bata da ikon musawa iyayenta kuma tana son Aliyu amma ta tsorata da lamarinsa.
***
Yana shiga gida ya tarar dasu Umma zaune a tsakar gida suna cin abinci.

Ya k'arasa ya zauna "Umma zan kai maganar kotu"

"Kotu kuma?"

"Eh dan nan ne kad'ai za'a k'watar mana hak'k'inmu,kuma mun gama magana da Malam yace wata mai kamawa za'ayi bikinmu da Zuhra dan ta kwashe abinda ya faru da safe ta fad'a masa tace kuma ta fasa aurena to bai yarda ba kuma yace dole ne aurena da ita da iznin Allah"

'Daga hannu Umma tayi tana godiya ga Allah tare da k'arfafa masa gwiwa akan ya kai kotu.

"Yaya waccan sakaran fa tana d'aki tun safe da ka fita ko abincin rana sai mu mukayi kuma bamu kai mata ba dan mu ba bayinta bane,tun d'azu take mana aman munafurci wai zazzab'i take"

"Ki rabu da ita duk zata ajje rawar kannan"

Karaf a kunnen mak'ociyarsu Asabe,ta tausayawa Janan sosai,tana jin Aliyu na fad'in ya fita ita kuwa tayi saurin d'ibar guntun taliyar data ajje in anjima yaranta suci,mayafi ta zura kawai tayi gidan dan ta bawa Janan.









_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


21

Da sallama ta shigo gidan ta gaida Umma sannan tace "Ni kuwa amarya na nan?"

Ummi ta kalleta tace "wace Amarya kuma"

"Amaryar gidan nan mana"

"Ai bamu da Amarya mu"

"To Janan nake nufi"

"Tana d'akinta" Ummin ta fad'a tana tab'e baki.

Asabe ta wuce zuwa d'akin Janan.

"Umma kiga wani tsegumi wurin Asabe?"

"To ke ina ruwanki"

"Uhmmm"

Asabe na shiga taga Janan d'in ta tattare guri d'aya sai nishi take,k'arasawa tayi kan tabarmar ta zauna tare da d'ago Janan.

Bata abincin tayi idonta a rufe ta girgiza kai tare da fad'in "na k'oshi"

"A'a ki daure"

Da k'yar ta samu Janan d'in ta fara cin abincin,cokali uku tayi sai amai,Asabe ce ta bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ta wanke gurin.

"Ki k'arasa cin abinci Janan"

"A'a na k'oshi kaina ciwo yake"

"Rashin cin abincin da kikayi tun safe shine ya jawo miki hakan,ki daure ki k'arasa ci,sai inje in d'akko miki magani na san in kika sha cikin k'ank'anin lokaci zaki samu sauk'i insha Allahu"

Haka Janan ta daure taci abincin ba dan yana mata dad'i ba sai dan yunwar da takeji kawai.

Asabe ta koma gidanta ta jik'owa Janan magani ta kawo mata,runtse ido kawai tayi tasha.

Aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi ya d'auketa,Asabe ta gyara mata komai sannan ta fita.

Tana farkawa taji wata muguwar kasala,ga uban zuffa duk ta had'e mata jiki,kallon agogon hannunta tayi taga biyar da rabi ma ta wuce.

Tashi tayi ta zuba ruwa a bokiti ta nufi band'aki tayi wanka,duk dai a tsantsance take rayuwar gidan da k'auyen ba irin tata ba.

Sai da ta dawo d'akin ta lura babu akwatunanta sai wani guda d'aya wanda bata san meya kawo shi ba kuma bata san na waye ba.

A hankali ta taka har gurin,ta janyo ta bud'e,atamfofi ta gani ta fara d'agasu duk kansu robber ne(lagona) d'inkakku guda 5 sai Vaseline da kwalli da farar powder a gefe,sai kuma hijabai milk and black da wani takalmi irin na narkakkiyar robber wanda ake sayar dasu 500-800 shima black ne.

Abin ya matuk'ar bata mamaki dan tana d'aga kayan ta gansu tamkar an gwada ta.

"Nawa ne?hmm to ina lefen da Mameey tayi min?"

Murmushi kawai tayi lokacin data tabbatar Aliyu ne ya d'auke akwatunan ko shakka babu ta san shine.

Mai ta shafa sannan ta d'akko d'aya daga cikin atamfofin ta saka,riga da zani ne kina ganin d'inkin kin san a k'auyen aka yi shi.

Sai ta koma kamar irin wayayyiyar k'auyen nan.

Ita kanta data kalli kanta sai da tayi dariya tace "oh dubeni tamkar 'yar k'auye,lallai soyayya kenan Allah ka karkato da hankalin mijina gareni kasa ya soni fiye da yadda nake sonshi ya kuma yafewa Abba laifin da yace yayi masa.

Haka Janan ta cigaba da fuskantar matsaloli da ban da ban daga gurin su Aliyu amma tana jure komai duka da zagi har sun zame mata jiki,akwatunanta kuwa cewa yayi ya sayar da wasu sauran kuwa Zuhra zai kaiwa lefe.

Kullum babu ranar da bazai doketa ba saboda girki ita babu abinda ta iya a irin girkinsu in ba shinkafa da taliya ba su kam tsuro mata da abu suke Wanda Sam bata sansu ba,haka zatayi yak'i ciyuwa shi kuma ya jibgeta.

Yau ta kasance Monday satinta d'aya a gidan Aliyu bata ma san wainar da ake toyawa ba a gidansu.

Tashi tayi kawai da son taje skul yau,dan haka ta shirya da wuri ta tambayeshi yace
"ban hanaki ba amma ko gwandala ta bazan baki ba kuma bance ki biya gidan kowa ba,daga makaranta ki dawo gida idan naji kin biya wani gurin ranki sai yayi mummunan b'aci"

"An gama" ta fad'a tana murmushi dan abubuwan sun zame mata jiki.

Har zata fita taji Umma tace "ina zaki je?"

Juyowa tayi ta kalleta tace "Zanje makaranta"

"Wa kike son ya miki girki?waye bawanki?"

"Zan dawo da wuri Umma"

"Babu inda zaki je"

"Umma k'yaleta taja munafurci ne ke damunta" suka juya duka suka kalli Aliyu.

"Oh kaine ka mara mata baya akan ta tafi"

"Umma ki barta kawai ai ta sani nace kartaje ko ina daga can ta dawo nan"

"Kaima ai bakayi karatu ba dan haka itama baza tayi ba"

Da k'yar Umma ta yarda Janan ta tafi,ita Janan ma har mamaki take da Aliyu ya barta.

**********

Tun daga nesa lubna ta tsaya tana k'are mata kallo"

Tab'o Raihan tayi tace "kinga wata can tana tafiya kamar zata fad'i kuma wallahi kamar Janan"

Raihan ta tashi da sauri tace "wallahi itace" duk kansu suka k'arasa gurinta da sauri.

"Ke meye hakan?" Raihan ta tambayeta.

"Kamarya?"

"Naje gidanki sau biyu baki nan wayarki kuma bata shiga"

Murmushi tayi tace "ai mun canza gida mun koma can _kangire_"

"ina ne kuma haka?"

"Garin su Aliyu mana"

"Wannan d'an iskan?" Lubna ta fad'a tana tab'e baki.

"Mijina ne d'an iskan?"

"Haba lubna bai kamata kice haka ba" Raihan tayi maganar,tare da jan hannun Janan
"zo muje plantation akwai maganar da zamuyi"

Su ukun suka tafi,lubna da Janan suka zauna Raihan ta tsaya a tsaye ta hard'e hannu ta kalli Janan tace "duk wanda ya sanki a baya ya ganki yanzu yasan kina cikin wahala"

Zama tayi gefenta ta cigaba da fad'in "Janan kin ganki kuwa ?hijabin dake jikinki ma bai b'oye ramarki ba,kayan jikinki tamkar na masu furar bakin asibiti wanda wanki d'aya zaka musu su koma tsumma,takalmin k'afarki tamkar bathroom silifas d'inki haba Janan auren talaka hauka ne?at least ai ya kamata ki banbanta dasu ina uban kayan da Mameey ta had'a miki"

"Ya sai dasu saboda bashi da kud'i kuma nima ban hana ba kuma nina bashi da kaina"

"K'arya kike Janan ko ince k'ayar yake?akwai dalili dai dubi yadda kika zama fuskarki duk k'uraje da cizon sauro wanda da ba haka kike ba,ada fatarki smooth ce,sannan ga kuncinki nan sahun yatsu biyar bai b'ace ba,ko zaki b'oyewa kowa damuwarki bai kamata ki b'oye min ba saboda tare muka taso dake tun muna yara Janan"

Sai a lokacin yanayinta ya canza idonta duk ya cicciko ta kalli lubna tace "karku min tambayar titsiye dan Allah ni dai kawai ku tayani da addu'a Allah ya kawo min sassauci amma tabbas ina shan wahala kullum sai naci duka a gidan Aliyu"

"Mafita d'aya shine kice ya baki takardarki tun da babu dole"

"Haba lubna ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru" Raihan ta fad'a.

"Ai gaskiya ce"

"Ina sonshi shiyasa nake jure duk wata wahala" ta fad'a lokacin da hawaye ya sauka a idonta.

"Kina da cikinsa ne?" Lubna ta sake tambaya.

"Babu abinda ya tab'a shiga tsakaninmu"

"To ni zanje in ci masa mutumci in kuma karb'ar miki takardar saki"

Mik'ewa tayi tsaye tace "karki soma lubna"

"Amma zaki iya cewa kinfi son Aliyu akan Abba?"

"Karki had'a iyaye da miji dan babu had'i"

"To in kuwa hakane kin iya banzar soyayya dan babu yadda za'ai ki cigaba da zama da Aliyu"

"Lubna kiyi shiru haka mana" Raihan ta fad'a a tsawace

"Dole in fad'a mata gaskiya"

"Shikenan"

Kallon Janan tayi tace "to Aliyu ya kai Abba kotu suna shari'a dan ranar laraba ma za'a cigaba da shari'ar"

"Me akan me?" Janan tana maganar tana kuka.

"Akan wata banzar hujjarsa,labarin yana da tsawo Janan sai mun zauna dan ko yaushe ina zuwa ina kuma jin shari'ar gaskiya Aliyu baya da mutumci"

Da sauri Janan ta juya,Raihan tayi saurin rik'ota.

"Ina zaki?"

"Gida" ta bata amsa sannan ta fuzge hannunta ta cigaba da tafiya da sauri.

Suka biyo ta a baya.

Ta inda Yarima yake zaune shi da friends d'insa ta wuce,da sauri ya tashi yasha gabanta.

"Amarya lafiya?yaushe kika shigo?me akayi miki?"
Hawayen fuskarta ta goge tana kallonsa tace "bakomai"

A lokacin su Raihan suka k'araso,ya tambayesu suka ce suma basu sani ba.

Yayi k'ok'arin binta Raihan tayi saurin wayencewa ta tsaya dashi ita kuwa Lubna ta bita.

Napep suka tara har k'ofar gidan.

Babu alamar security ko d'aya a gidan hakan ne ya tabbatar mata akwai matsala.

Tayi knocking maigadi ya fito,kallonta yayi sannan yace ''a'a Janan ce a gidan?"

"Eh ina su baita"

"Suna daga ciki" ya fad'a,taji dad'in hakan tana shiga kuwa ta gansu a farfajiyar gidan.

Da sauri kuwa baita ya taso yazo gurinta "Hajiya Janan sannu"
"Yawwa baita"
"Ciki zaki shiga?"
Tambayar ta bata mamaki ta kalleshi tace "da matsala ne?"

"Eh yace in dai kika zo karmu bari ki shigo"

"Cab wallahi

Please Login or Register in order to submit comment