You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne?"

"Umma ki bari sai gobe saboda yanzu dare ne kuma kinsan muna da nisa sosai mu cikin k'auye su kuma cikin gari mota ma zatayi wuyar samu"

"To shikenan Allah yasa dai lafiyarsa lau duk da dai na san ba lafiya ba"

Haka ranar suka kwana cikin rashin kwanciyar hankali.

Washe gari tun sassafe Ummi ta dama masu koko suka sayo waina suka ci,sannan ta gyara ko ina a gidan,kusan k'arfe goma ta shirya Umma ta bata kud'in mota dan adaidaita yana da tsada ga wahalar samu daga k'auyen nasu zuwa cikin garin Kaduna.

"Umma ko dai bari zanyi sai zuwa anjima dan naga jikin naki babu dad'i sosai"

"Ciwon kai ne kawai kuma naji d'an dama-dama inason muji halin da Aliyu ke ciki tun jiya bai dawo ba"

"To umma Allah ya sawwak'e bara naje"

Sallamar da aka yi ya dakatar da Ummi daga shirin fitar da take.

Zuhra ce shigo kanta a k'asa tazo ta gaida umma,umma ta amsa cikin jindad'i.

"Umma dama jiya ne Aliyu yazo yace min dai yana cikin Matsala amma in tayashi addu'a zai je cikin gari ya dawo sannan yace idan ya dawo zaizo da dare naji kuma shiru bai zo ba,sai d'azu naji labari a gurin Nura wai har yanzu bai dawo gida ba,shima so yake yaje birnin"

"Wallahi kuwa muma bamu san dalilin rashin dawowar tashi ba tun da bai saba haka ba amma yanzu zan tafi cikin birnin in gani"

"Umma idan babu matsala zan bita" zuhra ta fad'a tana kallon umma.

"Kin tambaya a gida?"
"Nace masu nan na taho dan ganin ko lafiya nasan babu matsala idan na bita"
"Okay Allah ya kiyaye Ku"
"Ameen umma" suka fad'a tare.



Suna cikin mota Zuhra tace ma Ummi "to yanzu ina muka nufa"
"Gidan da yake aiki"
"Kin san gidan"
Farin sani ma"
"Toh ba damuwa"

Sun isa k'ofar gidan lafiya amma shiga cikin gidan ya faskara,Alh.Hashim commissioner of police ne shiga gidansa bazai zama abu mai sauk'i garesu ba,dan ma Ummi tayi dubara tace ma securities d'in wajen Janan suka zo.

Da farko abinda aka fara tambayarsu shine compliment card basu dashi.

Wani daga cikin securities d'in yace "kaji wannan mak'aryatan wai wajen Janan suka zo babu compliment card,babu Waya da zasu kirata suce sunzo wai kuma su k'awayenta ne"

"Hahahah amma dai basu da hankali ka dube su a hakan ne suke k'awayen janan?kai wannan zance ne"

Maigadin ya tausaya masu sosai amma baya da wani iko daya wuce bud'e gate da rufewa.

Sunga wulak'anci da k'ask'anci duk kansu ransu ya b'aci musamman dariya da cin mutuncin talauci da suke masu.

Sun fi awa biyu a zaune a bakin gate tun suna rok'onsu har suka gaji suka daina.

Sai wani security ne daya ga sun kafe sun k'i tafiya kawai ya d'aga Waya ya kirawo Janan yana dariya yana sanar mata ga wasu 'yan k'auye sunzo gurinta wai k'awayenta ne basu da ko waya kuma babu card a hannunsu

Daga d'ayan bangaren Janan tayi dariya tace "basu wayar na tambayesu"

Mik'a masu wayar yayi Ummi tayi saurin karb'a ta kara a kunne.

"Salamu alaikum"
"Wa alaikumussalam,yace min ke kawata ce amma ya akai bani da contact dake"

"Ni k'anwar Aliyu ce,ban san kowa ba a gidannan sai ke da yake yawan magana,dan Allah ki bamu dama mu ganki dan musan halin da d'an uwanmu ke ciki"

"Okay bama wanda ya baki wayar"
"Toh" ta fad'a tare da mik'a masa

"Hello hajiya"

"Ka shigo dasu cikin Babban falo"
"Okay"

Dariya yayi yace "to k'annen Ali direba Ku shigo"
"Oh dama k'annen Ali ne?hahah no wonder na gansu a haka" wani ya fad'a yana shek'a dariya.

Maigadi kuwa sai barka yake masu cike da tausaya wa dan ya san Ali mutumin kirki ne.


Janan kuwa da sauri ta sakko zuwa babban falo ta tarar da Mameey zaune tare da bak'inta

"Ina zuwa naga kin sakko da sauri"

Saida ta fara gaida bak'in sannan tace "wallahi mameey bak'i nayi yanzu Mudan zai shigo dasu"
"Okay"

Tana tsaye har suka shigo,Ummi sai kallon gidan take tana ganin yadda masu kud'i ke cikin aljannar duniya.

"Sannunku da zuwa" Janan ta fad'a tana murmushi.
Suka amsa sannan suka sunkuya suka gaida su Mameey.

"Ya sunan 'ya'yan nawa?" Mameey ta tambaya cikin bark'wanci,suma suka d'an saki rai suka fad'a mata.

Kallon Janan tayi tace ki kaisu falon bak'i ko naku ko kuma k'aramin falo"

"A'a bedroom d'ina zamu"
"Okay ba damuwa"

"Ku muje"
Tashi sukayi suka bita.

Bayan sun shiga duk kansu zasu zauna a k'asa tayi saurin cewa a'a dan Allah karku zauna a k'asa ga sofa ga gado" ,Zuhra ce tayi murmushi suka zauna kan sofa.

Itama zama tayi kusa dasu tace "sannunku da zuwa" "yawwa" suka amsa

"Amma ni Ummi naji yana yawan fad'a min a matsayin k'anwarsa"

Murmushi tayi tace "eh wannan Zuhra itace wadda zai aura"

Gabanta sai da yayi mummunar fad'uwa ji tayi kamar an caka mata mashi a lokacin da Ummi ke fad'a mata"

Ummi ta lura da hakan dama ta fad'a ne dan ta k'ular da ita.

"Bai tab'a baki labarina bane?" Zuhra ta tambaya.

Murmushin k'arfin hali tayi tace "yana fad'a min amma manta sunan nake" ta fad'a ne kawai dan kar Zuhra taji haushi.

"Ai na san dole yayi maganarta yadda yake k'aunarta"

"Uhmm bara na kowa maku ruwa na san kunsha hanya"

"A'a ki barshi mu dai kawai munzo muji ko lafiya Yaya Aliyu bai koma gida ba tun jiya"

"Karki damu bara dai na kawo maku ruwan"

Da Sauri ta tashi ta fita.

Ummi ta kalli Zuhra tace "ga yadda aka k'awata gida da kud'inmu"

"Kud'inku kuma?" Zuhra ta tambaya

"Eh mana kud'inmu mu talakawa mana ai har ke"

"Uhmm dama,amma Kin San me?"

"A'a sai kin fad'a"

"A yadda ake cewa masu kud'i na da wulak'anci sai naga sauk'in kanta sosai tana da mutunci da sakin fuska"

"Na munafurci ba" maganar zuciya tayi Wanda bata san ya fito fili ba sai ji tayi zuhra tace "kamar ya"

Sauri tayi ta canza maganar da fad'in "gashi sun saka yayana a matsala bamu san dalili ba"

"Insha Allah komai lafiya"

"Ni wallahi haushi nake ga d'akin nan wai duk girmansa na bacci ne kawai"

Murmushi Zuhra tayi tace "amma kamar ya tab'a cemin ya tsani wata janan"

"Wannan shegiyar Janan d'in 'yar Zaria ce taso raina masa hankali" ta maze

"Oh nayi tunanin wannan"

"A'a wannan ai tana da kirki ba karmar waccan ba"

Dariya zuhra tayi ba tare da ta fuskanci komai ba.


Janan kuwa tsaya wa tayi jikin step tayi kukan bak'in cikin wai Aliyu yana da wadda zai aura,sannan ta goge hawayenta,taje babban kitchen ta bada umarnin a kaiwa bak'inta abinci da fruit,sannan ta d'auki plate ta koma d'akin.







_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




_Wannan Shafin naku ne 'yan group d'ina *TASKAR SANAZ* bazan iya musalta farin cikina a gareku yadda kuke bani k'arfin gwiwa akan novels d'ina,nagode sosai ina alfahari daku Allahu ya barmu tare ya kuma bar zumunci_
*#ILYMTYE😍😘*



09

Fridge ta bud'e ta d'akko lemo da ruwa ta d'ora kan plate d'in sannan ta d'auki cups guda biyu ta nufo inda suke ta ajje
"Bismilla"

Ruwa suka zuba suka sha sannan Ummi ta sake tambayarta Aliyu a karo na biyu.

"Nafiso sai kun ci abinci kun huta yanzu za'a kawo maku"

"Dan Allah ki fad'a mana gaskiya ko dai ya mutu ne kike son b'oye mana?" Zuhra ta tambaya.

Ajiyar zuciya tayi ta kalleta tace "ki kwantar da hankalinki Aliyu yana raye nd am vry sure lafiyarsa k'alau"

"To idan hakane yana ina?" Ummi ta tambaya.

"Kinsan ai. .........." Knocking da ake na k'ofa yasa tayi shiru tare cewa "shigo"

'Yan aikinsu suka shigo hannunsu d'auke da tray na abinci da plates sai plate d'in fruit .

"Bismillah Ku ajje" tayi masu umarni,bayan sun ajje sun fita sannan ta juyo ta kallesu.

"Ai ya fad'a maku abinda ya faru jiya ko?"

"Eh amma wallahi yaya bashi da laifi bazai tab'a iya aikata zina ba"

"Hakane nima zan shaideshi akan hakan,amma matsala d'aya da suka zauna d'aki d'aya a hotel kuma da Abba yazo sai ya gudu,shiyasa kowa ya shiga zulumi akan shiya jata ko ita taja shi"

"Amma kinsan idan mahaifinku ya zo a lokacin yaya baya da wani uzuri zai iya fuskantar ko wace matsala"

"Toh,yanzu dai Abba yasa an tafi dashi cell tun jiya itama yaya fauziyya ya saka an kulleta a d'aki sannan yace babu belin"

"Na shiga uku ni Ummi me zan cewa umma meyasa rayuwarmu ke tafiya a haka"

Zuhra ta ruk'o Ummi tana kuka, hakan ne yasa Janan taji hawaye ya sauka a fuskarta.

"Yanzu ko ganinsa bazamu iya yi ba?" Zuhra ta tambaya.

"Za muje daku Ku ganshi"

Da sauri Ummi ta tashi ta kalli Janan "dan Allah mu tafi yanzu ki taimaka mana"

Tausayi ta bata sosai dan haka ta tashi ta d'auki mayafi sannan ta d'auki jakarta ta kallesu "zamuje mufara yiwa Mameey sallama amma dan Allah Ku goge hawayenku Ku saki ranku karta gane wane abu bare ta hanamu zuwa"

Haka suka tashi jiki a sanyaye suka fita,Mameey still tana falo,Janan ta zauna kusa da ita tace "Mameey ina son kaisu gida gashi babu direba"

"Ina Mato?"
"Kin san mato ba yawan zama yake ba,Baita kuma ya fita da Abba"

"To ya za'ayi?"
"Mameey inyi driving d'in?"
"Ina tsoron fad'an mahaifinku Janan"
"Zan dawo kafin ya dawo insha Allah"
"Okay ki kiyaye janan karki ja mana fad'a"
"Insha Allahu"
"Kije d'akina ki d'akko masu laces guda biyu da turaruka,ki basu 10k"
"To Mameey"

"Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Zuhra ta fad'a.

Ummi kuwa ba yabo ba fallasa.

Da sauri Janan ta shiga d'akin mameey ta d'akko komai kamar yadda ta fad'a.

Suka yiwa Mameey sallama suka tafi.

*******

A k'ofar police station tayi parking suka shiga.

Lokacin da aka fito da Aliyu saida Janan tayi mugun firgita dan kana ganinshi kasan yasha duka.

Ummi kuwa kuka ta fara yayinda Zuhra ta dafe kai tana karanto addu'o'i.

"An zalinceka yaya Allah ya saka maka"

"Idris amma akan me za'a dake shi haka?"

"Umarnine daga wurin Commissioner"

"A wane dalili akan me?"
Shiru kawai sukai dan basu san me zasu ce mata ba.

"Cab wallahi zan wa abba magana amma akan me bayan bashine da laifi ba"

"Ummi" ya kira sunanta cikin dakiya.
Kallonshi tayi ba tare da ta amsa ba

"Ina fatan keda umma duk kuna lafiya"
"Eh yaya meyasa bazasu bamu belin ka ba?"

"Karki damu ko shekara nawa zanyi anan dole zan fita"

Basu wani dad'e suna magana ba suka tashi suka fita.

Har k'auyen su Janan ta kaisu, sai da suka fara sauke Zuhra a k'ofar gidansu sannan suka wuce.


Janan kamar bazata shiga gidansu Aliyu ba sai da Ummi ta rok'eta sannan suka shiga.

Umma na ganinsu ta mik'e tsaye
"Ummi ya ake ciki ina Aliyu yake?"

"Ki kwantar da hankalinki umma yanzu ma daga gurin shi muke, an kulleshi ne akan dai matsalar data faru jiya"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wane irin zalinci ne"

Janan ta k'araso kusa da ita tace "umma kiyi hakuri insha Allahu komai zai zama normal"

"Ummi wace wannan?"
"Ita ce Janan"
"Meyasa kika taho min da ita me zata min?"

Fad'uwar gaban Janan ta yawaita,idan har Mahaifiyar Aliyu bata k'aunarta taya rayuwarsu zata cigaba da tafiya da Aliyun.

"Fitar mana daga gida" ta sinkayi muryar umma na fad'ar haka.

Har k'asa ta durk'usa tana kuka tace "dan Allah kiyi hak'uri karkiyi sanadin rabani da Aliyu"

"Rabuwarki da Aliyu tazo tunda har bazaki iya kub'utar dashi daga wannan k'azafin ba"

"Zanyi iya bakin k'ok'arina nayi maki alk'awarin Aliyu zai dawo gida gobe insha Allahu"

"Idan kuma bai dawo ba fa"

Tayi rau rau da ido tace "zai dawo da iznin Allah"

"To ki sani idan har Aliyu bai dawo gida gobe ba, babu ke bashi, ban tsaneki ba ina miki haka ne dan ki gane irin yadda Aliyu ya d'aukeki a zuciyarshi"

"To umma nagode" jikinta a sanyaye tayi masu sallama ta tafi.

Ummi tayi tsaki ta kalli ledar hannunta "umma har da bamu lace da kud'i"

"Akan me?"

"Wai kyauta ce, umma kinga kuwa yadda aka k'awata gidan wani tangameme kamar aljannar duniya"

"Ki rabu dasu sakayya zata zo nan bada dad'ewa ba, ba tana son Aliyu ba in har naga ta saka an saki Aliyu a gobe tabbas zanyi amfani da wannan damar a d'aura masu aure nan da wata gudu"

"Wallahi ni duk haushinsu nake, ita kuwa Zuhra sai yabonta take"

"Itama dan bata san wace ita ba shiyasa take yabonta, yanzu wannan kayan ajjesu zamuyi har sai ranar data shigo hannunmu zamu bata tsiyarsu".


**********

Tana shiga umma ta sanar mata dasu Raihan sun zo suna k'aramin falo.

Da sauri ta nufi d'akin cike da zumud'i.

"Ah harda wannan 'yar rainin hankalin akazo"

Lubna tayi dariya tace "darajar besty kika ci da bazan zo ba"

"Oh zuwanshi ne kenan ba naki ba?"

"Eh mana aini na rasa tsakaninku da besty ko dai snatching kike son yimin"

"Ah to waya san abu a duhu"
"Aikuwa baki isa ba"

"Kedai kawai ki kama k'afa dani koba haka ba Raihan"

"Hakane k'awas dan besty yana mugun yinki"

"To kinji fa"

"Ai baki isa ba"

"Naji, bara na kawo maku ruwa"

Dariya Raihan tayi tare da fad'in "kodai a rud'e kike?bakiga ruwa a gabanmu ba"

Dafe goshi tayi tace "wallahi kuwa ina cikin matsala Raihan"

Labarin komai ta basu da yadda sukayi da mahaifiyar Aliyu sai dai bata fad'a masu ga dalilin rufeshi ba ta dai ce yayiwa Abba laifi ne.

"Wallahi mugun mamaki kike bani Janan"

"Mamakin me?ai kece kika dasa min son Aliyu dan haka duk abinda ya faru ko Alkhairi ko sharri to kece Sanadi"

"Ni kuma kiji zata min sharri Raihan"

"Gaskiya ce, gani nake kamar anyi min asari, na rasa wane irin so nakewa Aliyu wallahi har ya zarta son da nayiwa Salman"

"Baki iya soyayya ba Janan sannan kina soyayya da wanda bai dace dake ba"

"Babu rashin dace a soyayya, kuma soyayya bata shawara kiga irin cin mutumcin da nakewa Aliyu amma a yanzu shi nakeso ya kasance abokin rayuwata"

"Cab to babu yadda Allah bayayi mu dai fatanmu Allah ya zab'a miki mafi alkhairi"

"Ameen my Raihan na san Aliyu alkhairi ne a cikin rayuwata"

Kallonta kawai Raihan take ita kam kawai hakanan taji bata son tarayyarsu da Aliyu.

Lubna kuwa tsokanarta take akan taga kyakkyawa ta d'afe masa.

Sun shafe kusan awa biyu kafin su mata sallama su tafi.







_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





10

Bayan sunyi sallar isha'i sun ci abinci Abba ya buk'aci ganinsu a babban falon gidan.

Janan ta k'udiri niyyar zata fad'a masa cewar ya saki Aliyu dan bashi da laifi koda zai kasheta zata tsaya da k'afafunta dan k'watar masa hak'k'insa.

Su hud'u ne a falo, Abba, Mameey, Fahad, Janan duk kansu sunyi shiru, Abba ne ya fara magana da fad'in "zan saka a saki yaron nan sannan na sallameshi bazai sake aiki a gidana ba, ita kuma Fauziyya zan mata horo mai tsanani dan sai tayi wata bata fita ko ina ba, idan ta fara samun carryover zata nutsu tasan mahaifinta cikakken d'an sanda ne kuma baya da wasa"

Janan ji tayi kamar an sakata a aljanna, cikin sauk'i za'a saki Aliyu,hamdala tayi a zuciyarta ko babu komai ta san umma bazata hanata Aliyu ba.

Fahad kuwa yaji dad'in hukuncin Abba dan bai tab'a tunanin Fauziyya zata iya abinda tayi ba.

Mameey kuwa jikinta duk yayi la'asar, a haka tattaunawarsu ta k'are.

_Washe gari_

Kamar yadda Abba ya fad'a haka ya cika alk'awarinsa dama shi kam da wuya ya fad'i magana ya k'i aikatawa, sai dai baima yarda Aliyu yazo gidan ba daga can station yace ya tafi sannan baya son ya k'ara ganinsa a gidanshi, haka ya dawo masu da labarin ya sallami Aliyu kuma babban hukuncin da yayi masa shine rashin biyansa albashinsa na wannan watan.

Janan bata ji dad'i ba amma babu yadda ta iya da mahaifinta, ita dai dad'inta d'aya an sake shi.



A b'angaren Aliyu kuwa napep ya tara ya kaishi har k'ofar gidansu.

Yana yin sallama kuwa duk kansu suka tashi suka nufo shi, dama duk suna tsakar gida suna wanki.

"Aliyu haka ka canza?meyasa mutanen nan basu da imani?"

"Umma ai wannan ba bak'on abu bane a gurinmu kin san halinsu ai"

"Allah ya saka mana, Ummi maza d'ora masa ruwa yayi wanka"

"To umma".


Bayan yayi wanka yasha maganin ciwon jiki ya huta sannan umma ta bashi labarin zuwan Janan, haka ummi ma ta bashi labarin irin cin mutuncin da aka musu kafin su samu damar shiga gidan.

"Janan zan fara azabtarwa Umma, sai na gasa mata aya a hannunta, nafi tsanarta ita da mahaifinta domin ita ta fara nuna min tsana, kuma ta zagi mahaifina"

"Bana so ka tausayawa duk wani zuri'ar Alhaji Hashim, ina son duk runtsi ka samu damar da za'a d'aura aurenku da yarinyar nan a wata d'aya"

"Duk yadda kika ce haka za'ayi umma wannan damar ce zata bani damar auren zuhra ba tare dana sha wahala ba, Janan kuwa bayan na gama k'ask'antar da ita sannan inyi mata sakin wulak'anci"

"Tabbas bazamu raga musu ba yaya domin sunyi mana babbar illa".

********

_Bayan kwana 4_

Janan ce ta tura k'ofar cikin sallama ta shiga.

Hankalinsa na kan takardun da yake dubawa ko bayan amsa sallamarta da yayi kawai ya cigaba da duba abinda yake.

Kan sofa ta nufa ta zauna tare da fad'in " magana nazo muyi yaya"

"Indai akan wannan mara mutuncin ce karma ki soma"

"Yaya hannunka baya tab'a rub'ewa kace zaka yanke"

Kallonta yayi tare da fad'in "idan har hannun bai isheka da azaba ba, amma idan yana azabtar dakai ai tuni zaka yanke ka wantsar dashi"

"Wannan bai azabtar ba yaya hukuncin da Abba yayiwa yaya fauziyya yayi tsauri da yawa, friends d'inta sai kirana suke ana tayi masu lectures har da test yaya ka duba fa koni Abba ya hana na ganta dan Allah ka bashi hak'uri"

"Janan Abba ya yarda da fauziyya fiye da tsammaninki shiyasa ya bata har mota ke yana ganin kina da taurin kai da rawar kai shiyasa ya hanaki amma a k'arshe ki duba kiga abinda tayi, ai Abba ya san tabbas Aliyu bashi da laifi ya saka a hukuntashi ne kawai saboda ya kasa kiranshi a waya tun lokacin da sukaje hotel kinsan Abba da zafin rai"

"Hakane amma na san Abba da ka bashi hak'uri zai sakko"

"To zan k'ok'arta nagani"

"Yawwa yaya nagode, bara na barka ka cigaba da aikinka"

"Okay"

Cike da murna da jindad'i ta koma d'akinta ta kira number Aliyu.

Tayi ringing har ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kira, shima har ta kusa katsewa sannan ya d'aga.

Maganar da yayi ce ta bata mamaki yadda yana d'auka kai tsaye yace "ina wani uzurin ne zan kiraki idan na gama"

"Kada ka katse min Waya Aliyu na san baka da wani Uzuri da kake"

"Kenan nayi miki k'arya?"

"A'a ba haka nake nufi ba amma ya kamata ka zamo mai yafiya Aliyu,banyi maka laifi amma kana son ka dawo da komai kaina,kullum na kiraka sai kace min kana da Uzuri bayan ba haka bane"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "bai kamata mu cigaba da yaudarar kanmu ba muna wahalar da zuciyoyin mu domin nasan Abba bazai tab'a aura miki ni ba"

"Baka da tabbas akan hakan"

"Ni nake da tabbas saboda an fad'a min Abba bazai muku aure ba sai kun gama masters sannan shi zai zab'a muku mijin dayaga ya dace daku,ni kuma umma tace in fito da mata nan da wata d'aya ayi bikina dan ta gaji da ganina haka babu aure, Janan na san babu yadda za'ayi Abba ya aura miki ni,bayan abinda ya faru gashi kuma ni direba ne,muna son junanmu amma dole mu hak'ura da juna"

Wani guntun hawayene ya zubo a fuskarta,tafi seconds goma kafin tace "bazamu tab'a rabuwa ba da yardar Allah please a ina zamu had'u muyi maganar?"

"A skul d'inku" ya bata amsa kai tsaye.

"Okay idan na shiga skul gobe zan kiraka"

"Allah ya kaimu"

"Ameen" ta fad'a a sanyaye.

Shi kuwa cikin murna ya ajje wayar dan ya san hak'onsa ya kusa cimma ruwa.


'Dakin Fahad ta koma ta rok'eshi daya barta taga Fauziyya,da k'yar ya yarda ya bata key d'in d'akin sannan yace ta tabbatar ta dawo dashi.

Jikinta a sanyaye ta bud'e d'akin cikin sallama ta shiga.

Fauziyyar na kan sallaya bayanta jingine da gado.

Jiyowa tayi ta kalleta tayi murmushi "sai yau zakizo ganina ko?"

Yadda Janan taji muryar Fauziyya ta canza sai tayi matuk'ar bata tausayi.

Zama tayi kusa da ita tace "kinsan Abba yace kada a bari kowa yazo wurinki"

Kamo hannunta tayi ta rik'e wasu zafafan hawaye suka zubo a fuskarta "Janan na san Abba yana fushi dani,watak'ilma yanzu ya tsaneni ko kuma yana dana Sanin haihuwata"

Da sauri ta rufe mata baki tare da fad'in "haba dai ki daina fad'in haka kina nan a zuciyar Abba kamar yadda kike da" ta k'arasa maganar tana hawaye

"Hmmm Janan kenan na san halin Abba kuma na san tabbas yana fushi dani amma ki rok'ar min gafara gurin Mameey da Aliyu,ina ganin kamar gawata ce zata fita a d'akin nan"

"Ya salam!dan Allah ki daina furucin nan Yaya Fauzah komai fa zai wuce"

"Na sani Janan amma ina jin ciwon abinda na aikata duk da Allah ya kub'utar dani Aliyu yana da hali mai kyau amma da wani ne na san da tuni mutuncina ya zube kuma duk laifin Abba ne da Sharrin k'awa,Janan k'awa tana da mugun had'ari"

"Wacece ta baki shawarar nan?"

"Zubaida ce,amma kin san da laifin Abba"

"Abba d'an boko ne addu'a kawai zamu cigaba dayi,ita kuma Zubaida wallahi sai ta gane kurenta wato shiyasa ta dameni da kira tana tambayar ina kike"

"Ni dai fata na kowa ya yafe min zan yi k'ok'arin gyara laifina"

"Allah ya yafe mana baki d'aya"

"Ameen,yanzu ina Aliyun?"

"Kinsan Abba ya koreshi ko albashin watan nan bai ba shi ba"

"Kanga matsalar ko Janan,amma ya kamata ace ya bashi hak'k'insa"

"Abba yana da zafi sai dai muce Allah ya sassauta masa zamuyi iya bakin k'ok'arin mu dan ganin mun fitar dake daga wannan k'angin"

"Janan kenan,ni wallahi bana son fita saboda kunyar had'a ido da Mameey"

"Mameey ta san baki da laifi duk aikin shaid'an ne wannan"

"Hmmm"

"Zan tafi kada a gane ina nan,idan na samu chance zan sake zuwa"

"Shikenan Janan nagode"

"To saida safe"
"Allah ya kaimu"
"Ameen"

Jan k'ofar tayi ta rufe,ta maidawa Fahad key d'in sannan ta tafi d'akinta da Zumud'in gobe tayi su had'u da Aliyu.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



11

Batayi bacci da wuri ba hakan ne yasa ta makara sosai,dan sai kusan k'arfe 6:30am ta farka,ko sallar asuba batayi ba,da sauri ta fad'a bathroom ta d'ora alwallah ta fito ta gabatar da farilla.

Komawa ciki tayi tayi wanka ta fito ta fara shirin fita.

'Karfe tara ta fito k'aramin falo dan gabatar da break fast,sanye take cikin wani Swiss material yellow da touch d'in red a jiki,ta yana d'an k'aramin veil(million stones), fuskarta d'auke makeup yauma ta saka fashion glass d'inta brown color,tayi kyau ainun.

Bata tarar da kowa a dinning area ba dan haka ita kad'ai ta zauna tayi breakfast sannan ta tashi ta nufi d'akin Mameey.

Da sallama ta shiga ta gaidata sannan tayi mata sallama,harta juya zata tafi Mameey tace "waye zai kaiki?"

"Baita! na fad'a masa tun jiya"
"Okay ki kula"
"Insha Allahu"

*******

Suna zaune a plantation suna hira bayan sun fito daga lecture,Raihan ta kalleta tace "naga kina yawan duba time lafiya"

"Eh lafiya lau ina dubawa ne saboda Aliyu yace k'arfe sha biyu zaizo"

"Amma Janan me zai miki?"

Dariya tayi tana sake duba agogon hannunta tace "yanzu har an tambayi dalilin zuwan saurayi gurin budurwarsa"

"A'a amma ai inajin kinsan zamu shiga lecture na cost Accounting ko?kuma 12 d'inne sannan kinsan halin Mr Eze"

"Ki min attendance bazan samu damar shiga ba"

"Lallai yarinyar nan kin shirya rungumar carryover kenan"

Kallonta tayi ta yatsina fuska tace "kawai dan banyi attending lecture guda 1 ba sai in samu carryover?"

"To naga kina neman yin wasa da karatunki Janan"

"Kinga Raihan ki rik'e wannan jawabin idan na dawo kin d'ora daga inda kika tsaya Aliyu ya kirani" da sauri ta tashi ta bar gurin.

"Ohni Raihan ya Allah ka magancewa Janan wannan mahaukaciyar soyayyar".

Janan kuwa tana barin gurin ta d'aga kiran " hello kana ina?"
"Inda kika ce mu had'u"
"Okay gani nan"

Cike da zumud'i ta nufi side d'in can wajen Faculty of engineering dan nan ne babu mutane sosai.

Tunda ta hangoshi take murmushi shi kuma gaba d'aya idanuwansa a kanta yana ta shiryo irin muguntar da zai shirya mata.

"Barka da zuwa"

"Yawwa sarauniya" ya fad'a yana murmushi.

Zama tayi kan kujerar dake facing d'insa ta kalleshi tace "kamar kana cikin damuwa"

"Eh damuwa mara misaltuwa kuwa"

"Subhanallah meya faru?"

"Gani nake kamar zan rasa ki Janan,kuma rasa ki tamkar rasa rayuwata ne" ya k'arasa maganar kamar

Please Login or Register in order to submit comment