You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai Aliyu"

"Ni kuma ina saka ran zama dake anan gaba,ina sonki Janan"
Yana fad'a yayi saurin wucewa ciki tabi k'ofar da kallo,bayan aurensu bata tab'a jin ya furta mata kalmar so ba sai yau.

Kallon gidan Alh Ibrahim tayi tana hawaye dan bazata koma ba saboda sun hanata tafiya ko ina shiyasa ta yanke hukuncin tafiya ba tare da ta musu sallama ba.

Tana tafiya tana waiwayen unguwar dan ta san bazata tab'a komawa cikinta ba.

**********

Hankici ya d'akko yana goge zufar goshinsa sannan ya juyo ya kalli Momma yace "wallahi momma babu alamun zamu ga yarinyar kinga duk kwatance da nema bazai kaimu ba,yau kwana biyu kenan muna garin nan babu alamun za'a ganta"

"Hakane Muhasin nima na fara fidda rai da ganinta amma zan cigaba da addu'ar Allah ya sadamu da ita da alkhairi dan duk ranar dana ganta tabbas na maka mata"

"Mata kuma Momma?"

"Eh mana"
"Wannan 'Yar k'auyen wallahi na tsaneta ni k'yank'yaninta nake"
.
"K'yank'yani kuma?"

"Wallahi Momma bana k'aunar 'yan k'auye"

"Baka k'aunata kenan?"

"Momma dan Allah ki daina fad'an haka"

"Dole na fad'a saboda kana fad'a min ka tsani wadda tayi silar samun lafiyata"

"Ni bance haka"

"To ka sani in har na ganta koda kayi aure zata kasance matarka itama"

Baice komai ba kawai ya nufi inda motarsu take ya shiga.

"Maganar da na maka ne yasa ka b'ata rai?"

Murmushin dole yayi sannan yace "taya zanyi miki fushi Momma"

"Okay mu shiga cikin Kaduna ina son shiga central market inyi 'yar siyayya"

"Okay" ya fad'a tare da jan motar.

Suna cikin tafiya Momma tana tayi masa fad'an driving d'in da yake gudun yayi yawa,
Murmushi yayi yana fad'in "Momma ai nafi son mu koma yola yau"

"To ai sauri yana daga aikin shaid'an ko kana son muyi accident?"

"Kaiii haba Momma daina fad'a ma Allah y............"
'Kiiii.......ya taka burki tun daga nesan amma bai tsaya ba sai da yaje gabanta yayi sama da ita sannan ya dawo da ita yayi wurgi a tsakiyar titi,hakan ya faru ne da tafiyar da takeyi tun daga layinsu har zuwa bakin titi bata ma san me take ba tsabar tunani(pls mu tausasa zuciyarmu mu rage tunani akan titi musamman mu mata munfi kowa saka abu a rai).

Momma tayi saurin runtse ido tana salati shima salatin yayi tare da saurin bud'e motar ya fito.

Momma ma da sauri ta fita lokacin Muhasin ya kutsa cikin mutanen,bai gane fuskarta saboda yadda jini ya wanke ta yayi mata hawaye.

Momma kuwa tana zuwa ta gane ta,da sauri ta sab'eta tayi mota shima da sauri ya shiga.

"Muhasin mu tafi asibiti kayi sauri"

"Momma ban san asibiti ko d'aya a garin nan ba" ya fad'a a gigice.

"Ka tambayi wani ya kwatanta maka" da sauri yayi gurin mutanen ya tambaya.

********

Suna tsaye a bakin emergency Momma ta kalli Muhasin tace "ina maka fad'an driving da gudu sai ga darasi ka gani,Allah ya tashi kafad'ar yarinyar nan"

"Ameen Momma"

"Munzo nemanta sai gashi Allah ya had'amu da ita a yanayin hatsari"

"Oh Momma wai itace?"

"Eh mana baka gane ta bane?"

"Eh" ya fad'a a sanyaye a dai-dai lokacin da likita ya fito.

"Ku kuka kawo patient d'in nan"

"Eh mune" Momma ta fad'a.

"Ku biyoni office zan muku bayani"

"Okay"

Suna zaune a office duk sun maida hankalinsu ga likitan.

Sai da yayi 'yan rubuce-rubuce sannan ya d'ago kai ya kalli Muhasin yace "Ta bugu sosai amma munyi nasarar tsaida jinin sai kuma cikin jikinta Alhamdulillah bai samu mats.................."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" suka ji an fad'a a sanyaye.

Duk Kansu suka kalleta da mamakin yadda akai ta taso tazo.

Momma da sauri ta taso taje bakin k'ofar ta dafa ta tace "meyasa kika taso? baki da lafiya"

"Na shiga uku dan Allah ka fad'a min gaskiya taya za'ace ina da ciki wallahi ban tab'a sanin wani d'a namiji a rayuwata ba"

Shima likitan da sauri ya taso yazo gabanta yace "baki da lafiya taya kika taso?ina nurses d'in?"

Idanunta a jujjuye take kallonshi wasu zafafan hawaye suka sauka a fuskarta,a hankali ta sake fad'in "rayuwata ta gama lalacewa" a haka ta sulale zata fad'i Momma tayi saurin ruk'ota tare da jijjigata cike da fargaba.




_*Fans kuyi hak'uri da wannan,nayi shi d'an kad'an,kuma in brief gashi babu editing sai kunyi hak'uri da ganin errors, hakan ya samo nasaba ga wasunku da suka bini har PC akan inyi typing ko kad'anne amma yau banyi niyyar yi ba saboda ban samu lokaci ba sai dai bana son b'atawa masoyana rai shiyasa nayi d'an kad'an.*_
_#TARENE#_







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




28

"Karki mana haka,dan Allah ki tashi"
Momma ta fara jijjagata tana hawaye.

Nurses ne suka shigo aka d'auketa aka mayar da ita gadon sai a lokacin ta dawo hayyacinta,ta bud'e idanunta wani mugun zugi take ji a k'afarta yayinda wasu hawaye ke k'ara fita a idanunta.

"Kina son k'afarki ya rub'e?" likitan ya fad'a lokacin da yazo dai-dai kanta ya tsaya.

Ba taka kalleshi sai dai hawayen dake idanunta basu daina zuba ba.

"Indai kina so k'afarki ya warke sai kin daina taka ta,ko bakisan kin samu karaya a k'afarki ga kuma ciwo,ki daina takata ki hak'ura har ki samu lafiya"

Idanunta ta lumshe saboda yadda ta fara ganin d'akin yana juya mata.

Momma ta zauna gefen gadon ta rik'e hannun Janan tana kallon fuskarta cike da tausayi.

Mtswww Muhasin yaja tsoki sannan yaja kujera ya zauna yana kallon Janan tamkar ya daketa,yana ta addu'ar karsu had'u amma sai da ta k'ara shigowa rayuwarsu.

_Na gode ma Allah daya kasance cikine da ita da yanzu an lik'an Jaraba auren 'yar k'auye ko wahala_ yayi maganar a zuciyarsa sai kuma ya mayar da kallonsa ga Momma wadda ta k'urama Janan ido tun lokacin data zauna.

"Momma yaushe zamu tafi yolan?"

'Dago idanu tayi ta kalleshi tace "sai munga abinda Allah yayi kaga ai bama tafi mu barta a wannan halin ba"

"Momma to ta fad'i k'auyen da take sai in kira iyayen nata idan yaso sai mu basu kud'in da zai isa su cigaba da jinyarta mu mu tafi"

"Saboda rashin Adalci?"

"A'a amma naga ko muna nan ko bamu nan zata samu lafiya,kinga na bar aiki kwana biyu kenan banje office ba"

"Muhasin!zaka iya tafiya ni ka barni anan,ai nasan hanyar Yola tun kafin na haifeku to zan taho idan ta warware" Momma ta fad'a rai a b'ace.

"Ku tafi kawai" sukaji ta fad'a.
"Nagode da kawoni asibiti da kukayi ku tafi kawai ni na san tawa ta k'are" duk maganar nan da take idanunta a rufe suke.

Shiru su kayi basu ce mata komai ba,Muhasin ko kallonta baya son yi saboda takaici.


_3 days later_

An d'an jingina mata pillow a jikin gadon tana zaune ta jingina bayanta dashi,duk ka idanunta a k'asa tana goge hawayen da basu daina fitowa ba.
Muhasin yana jikin bango ya hard'e hannunsa a k'irji yana kallonta yana mamakin yadda ko gajiya batayi da kuka,shi ya tsani yaga ana rarrashin mutum yana kuma k'ara cigaba da kuka.

"Dan Allah ki bar kukan nan ki tsaya ki fad'a min meke faruwa naga tun da na tambayi iyayenki kike kuka,abinda yasa na tambayeki saboda yau muke son tafiya kuma ai bazamu barki ke d'aya ba shiyasa na tambaya saboda na san suna can hankalinsu a tashe tsawon kwana uku bakya nan,idan kuma cikin jikinki kike tsoron su sani ni zan musu bayani saboda babu wanda yake kaucewa rubutacciyar k'addararshi"

"Momma akwai sakaci fa,ni fa naga k'ok'arinki da kuka zauna asibiti jinya a tsohon kwana uku babu wata dangantaka"

"Muhasin idan ka sake magana sai na tsab'a maka"

'Daga kai Janan tayi ta sake kallonsa sannan tayi saurin kawar da kanta saboda gaba d'aya tsoronshi take,har yanzu idan ta tuno marin da yayi mata tana jin zafinsa.

Kallon Momma tayi tana goge hawaye tana d'an murmushi tace "karki damu nagode sosai da taimakon lafiyata da kuka yi,karki damu zan cigaba da jinyar kaina"

"Kamarya kenan?"

Shiru tayi bata ce komai ba.
Momma ta rik'o hannunta tace "dan Allah ki fad'an labarinki 'yata kina nufin baki da kowa?"

Wasu hawayen suka zubo a fuskarta ta girgiza kai alamar a'a.

"Suna ina?"

Ai tana jin haka a b'arke da sabon kuka tana shashshek'a, muryarta na rawa tace "Mahaifina ya rasu,Mahaifiyata da yayye na kuma ban san ina suke ba tun bayan rasuwar mahaifina suka bar garin nan"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Momma ta cigaba da nanatawa.

Rungume Janan d'in tayi tana ta rarrashi sai da ta d'auki fin minti talatin tana kuka sannan ta daina sai hawaye kawai daya cigaba da fita.

"Mene sunanki?

" Janan" ta fad'a murya a dashi.

"Jannat kenan?"
Ta d'aga kai alamar eh.

_wai Janan ashe 'yan k'auye ma sun yi wayewar da zasu saka sunan wayayyu._ ya sake furtawa a ransa ba tare daya damu da halin da take ciki ba.

"Ki fad'a min labarinki mana,dan abin yana d'aure min kai"

Idanunta a k'asa muryarta na cigaba da rawa tace "labarina yana da tsayi zaiyi wahala in iya baki shi a yanzu"

"To karki damu ki fad'amin gidan 'yan uwanki da kike zaune sai mu kirasu ko"

Girgiza kai tayi tace "bani da kowa saboda dangina na san babu wanda zai karb'eni saboda ko lokacin da babanmu yana da rai ba wani zumunci ake ba"

"To yanzu ya za'ai?"

"Shiyasa nace ku tafi ku barni kawai"

"Anan wai?"

"Eh" ta fad'a tana d'aga kai.

Muhasin yayi saurin cewa "Momma tun da tac......."
"Yi min shiru Muhasin" ta dakatar dashi.

"Dan k'aunarki da annabi Muhammad (S.A.W) ki fad'a min labarinki saboda sai naji labarinki sannan in san wane taimako zan miki"

Kallonta tayi sannan ta sake sadda kai "labarina yana da tsayi amma zan fad'a miki shi a gurguje"

"Ni haifaffiyar garinnan ce dan anan na tashi na ganni,tun lokacin dana taso nayi wayo nasan babana d'an sanda ne ya rik'e post-post da yawa kafin ya zama _commissioner of the office_.
Mu uku ya haifa yayuna biyu mace da namiji sai ni auta".

" mun taso cikin so da k'auna ga iyayenmu amma babanmu yana da tsatstsauran ra'ayi,dan shi a rayuwarshi baya da wani buri kamar yaga mun samu ingantacce ilmi shiyasa baya mana ko maganar mu tsaya kula samari"

"Ina Ss3 Allah ya had'ani da wani muka fara soyayya sanadin had'uwata dashi mun taso daga skul naji yana maganar mamanshi babu lafiya gashi baya da kud'i yana ta rok'an wani mai shago wanda kana gani kasan akwai alak'a tsakaninsu amma mutumin wulak'anta shi yake yana fad'in baya da sana'a taya zai biyashi idan ya bashi"

"Ganin haka yasa nayi saurin k'arasawa gurin nace masa bawon Allah nawa kake nema? Ya juyo a rud'e yace ban sani ba tana gida bani da ko kud'in kaita asibiti"

"Nayi saurin ce masa muje gidan,shi yayi gaba ina binsa a baya,inajin mai shagon yana cewa kaje ga masu kud'in banza"

"Ban ko juya na kalleshi ba,haka muka sha tafiya Wanda a lokacin naga nisan gidan saboda ban saba doguwar tafiya a k'afa ba,lokacin da mukaje k'ofar gidan har hawaye na zubda ganin wai dama akwai masu irin wannan rayuwa gidansu tamkar kango dan ya tsufa ya rub'e sosai amma cikin gidan a tsaftace a share yake tas,ganin mahaifiyar shi da wata tsohuwa ba k'aramin d'agamin hankali yayi ba yadda naga jini a bakinta ashe wai amman jini take saboda ciwon zuciya"

"Haka muka tafi asibiti da ita aka kwantar,ni na biya kud'in komai da yake bana barin Atm d'ina a gida kullum yana cikin jakana"

"Bayan an gama test har an sayo jini za'a k'ara sannan nace masa zan tafi gida kar a nemeni,sai a lokacin ya lura da uniform ne a jikina"

"Ke d'aliba ce a ina kika samu kud'i haka?"

"Kallon mamanshi nayi da take kwance kamar gawa nace,duk wata mahaifinmu na tura mana dubu talatin wataran hamsin"

"Baice komai ba yayi godiya ya rakani na hau napep na tafi,nasha fad'a sosai gurin Mamana saboda anje d'aukana ba'a ganni ba duk hankalinsu ya tashi gashi babana baya son hawa napep wai kar a sace mu"

"Dana shiga d'aki na bawa mamana labari itama ta tausaya musu sosai da yamma tare mukaje dubiya,a haka muka cigaba da jinyar Maman shi abinci ma daga gidanmu ake kawo musu,har Allah ya had'a jininmu sosai muka fara soyayya dashi ba tare dana hango k'alubalen da zan fuskanta daga mahaifina ba"

"Bani mantawa a ranar da mamanshi zata rasu da safe da yake asabar ne nina kai musu abinci break nida 'yan aikinmu,mun gaisa na d'an zauna da yake muna extra lesson sai na tashi zan tafi kawai ta rik'o hannuna tace min dan Allah ga amanar Salman na damk'a miki, shi maraya ne kuma shi kad'ai na mallaka,kimin alk'awarin zaki aure shi ko bayan raina karki gujeshi,cikin rauni na fara hawaye ina mata alk'awarin bani da wani miji da ya wuce shi,dana tafi ina dawowa da rana aka ce sun tafi saboda Allah ya mata rasuwa,a gigice na koma driver ya kaini har gidan wanda tun a waje na jaddada mutuwarta dana ga mutane a zazzaune kan tabarma wasu a tsaye lokacin ko kaita ba'ayi ba,aikuwa ina shiga na tsugunna gaban gawarta ina kuka ina mata addu'a,a ranar banma samu ganin Salman ba sai washe gari muka zo da 'yan gidanmu duka har babana"

"Haka aka shafe har arba'in sannan ya fara min maganar Aure saboda ya gaji da zama shi kad'ai shiru,gashi baya da sana'a sai dai in ya samu yayi a biyasa kud'i,nace masa ya jira sai mun gama jaraba lokacin mun fara neco"

"Ina gama exams banyi k'asa a gwiwa ba na fad'awa babanmu dan banyi tunanin abin zai zo min ba sauk'i ba,babanmu yasa na kirashi a nayi tunanin zai masa magana ne ya fara shirye-shirye sai gashi a gabana a gaban 'yan gidanmu yaci masa mutumci yace kuma bazai aurawa 'yarshi talaka ba kuma mara asali saboda dama daga shi sai mamanshi suke rayuwa a gidansu"

"Nasha kuka kamar raina zai fita,haka bayan kwana biyu yazo yace min zai bar garin nan saboda bazai iya zama yaga an bada ni ga waninsa"

"Tun daya tafi na fara rashin lafiya tamkar bazan rayu ba wani lokacin ma bana hayyacina,a haka akayi ta jinya ta har waje,bayan na fara samun lafiya babana yazo min da labarin Salman ya rasu a Lagos,nayi kuka sosai daga baya nayi tawakkali"

"Kuma tun daga lokacin in dai an zauna hira babanmu zaice nifa bazan aurar da 'ya'yana ba sai sunyi karatu sun kai har matsayin masters wani lokacin mamana takance ai shi Aure lokaci ne idan yazo babu tantama sai anyi"

"Na samu gurbin karatu a polytechnic lokacin yayata na jami'a L2,muna second semester baban mu ya kawo mana sabon driver wanda da da kanmu muke zuwa skul"

"A haka dai muke zuwa daga k'arshe ma ya zama driver na yayata aka siya mata mota shi kuma lokacin yayana already yana aikinsa"

"Kasancewar na tsani a wulak'anta talakka wannan shine mafarin fara soyayya da *Direban gidanmu* wanda shima banda mamana ta jajirce da bazan aureshi ba,dan har akayi bikinmu babana yana fushi dani akan na auri talaka *direban gidanmu*"

"Mamana ce tayi komai wanda uba da uwa keyi,sannan ta bashi jari mai yawa wanda zai rik'emu dashi sannan ta bashi kyautar gidan da zamu zauna"

"Ranar da za'a kaini babana ya bud'i baki yace babu ni babu shi sannan kar in sake in zo masa gida duk abinda zai faru,tsabar so ya rufe min ido ban iya cewa komai ba"

"Washe garin ranar da aka kaini kuwa yace in had'a kayana zamuyi tafiya haka na had'a akwati uku muna tafiya na ganni kawai a wannan k'auyen cikin gidansu yace anan zan cigaba da rayuwa,nace gaskiya bazan iyaba aikuwa ya fara fad'a yana fad'in shi dama auren manufa yayi dani ya aureni saboda ya karb'o musu gadonsu a gurin babana sannan ya rama abinda yayi masa haka suka had'u da mamanshi da k'anwarsa su kayi ta zagin iyayena ina ji ina gani"

"Nasha kuka sosai na rik'a rok'ansa ya fad'a min abinda mahaifina yayi masa yak'i fad'an"

"Kullum sai sun jibgeni babu rana da bazai min duka ko mamansa ta min ba,haka zasu saka inje in d'ebo ruwa sannan suce in yi girki ni kuma ban iya irin girkinsu ba idan nayi baya ciyiwa haka zasu dakeni suce nayi musu asarar kud'i saboda ban san ciwon kudi ba,ni kudin haram babana yake ciyar dani,akwatinan dana zo dasu ya kwashe ya kawo min wani tare da kaya kala biyar yace wancan lefe zai dasu kuma gidan da nake tak'ama da cewa mamana ta bashi ina gani wata zata zauna,ranar daya sakeni zai wulak'antani da zarar ya karb'o gadonsa a gurin babana zaimin sakin wulak'anci,haka nake jure komai saboda son da nake masa"

"Ranar dana fara tsanarsa shine ranar da naje skul k'awata take bani labarin ya shigar da babana kotu ana shari'a ga wulakanci da zagin mamana da yake,a ranar naje gida babana daya ganni tamkar zai shid'e yace in fita kuma idan ya mutu nice sila"

"Ina kuka na fita na koma gidan su k'awar tawa to a lokacin ta bani labarin wai babana ya tab'a kulleshi shekara takwas saboda an kamashi da miyagun k'wayoyi wanda ba laifinsa bane abokinsa ne ya kawo masa shi kuma babana ya manta da case d'in har tsawon shekara takwas sannan aka zo aka fad'a masa yayi bincike sosai ya gane baya da laifi yasa a bashi hak'uri a sake shi dan yana jin kunyar had'uwa dashi,nayi niyyar zama a gidansu babanta ya koreni yace ya rabamu saboda bazai zauna da azzalumai ba,haka na fita ina kuka wanda bani da inda zan koma in ba wannan k'auyen ba,ina zuwa yayi min duka wai yace kar inje ko ina shine na biya gidanmu,mamanshi tazo tace in d'ebo ruwa in dafa abinci,koda na fita kawai nayi rafi da niyyar in kashe kaina kawai in huta,kwatsam sai Allah ya kawo ku wanda na d'auki wannan a matsayin Allah ya turo min ku ne saboda ya kub'utar dani saboda idan na kashe kaina tabbas na mutu kafura"

"Kuna tafiya kawai naji ana min tafi,ina juyawa na ganshi yace min dama abinda nake aikatawa kenan,kafin nayi masa bayani ya mareni tare da tureni na fad'i ban k'ara tsintar kaina ba sai a wani gida"

"Ashe wani skul friend d'ina ne yazo wucewa ya ganni cikin jini ya d'aukeni ya kaini gidansa"

"Ina farfad'owa na ganni da drip aikuwa likitanshi na ciremin nace gida zani saboda kar zargi ya shiga,bai hanani fita ba amma ina fita na dawo saboda 'yan iska da suka so b'ata min rayuwa Ashe dare ne sosai,ranar wallahi ban runtsa ba har safiya sannan ya kaini gida,tun a waje mijina ya fara dukana yana zagi wai abin har ya kai inyi iskanci saurayin ya kawo ni gida,hak'uri na rik'a bawa friend d'in nawa saboda na san na jaza masa wulak'anci cikin b'acin rai ya tafi"

"Ina shiga gidan mamansa ta d'akko Razer ta yanka min k'afa tun daga babban yatsa har gwiwa sannan ta watsa gishiri a gurin na kwalla ihu saboda ba k'aramar azaba naji ba"

Momma ta runtse ido sannan ta bud'e tana hawaye lokacin da Jannan ta bud'e k'afar tana nuna musu gurin har ya kusa k'arasa warkewa ga karaya kuma a k'afar still.

Ta cigaba da fad'in "a ranar sai da mak'ociyar mu ta rakani har gida babana ya sake korana"

"Abinda yafi d'aga min hankali shine ana gama shari'ar da kwana biyu babana ya rasu saboda bak'in cikin abinda aka masa amma har yayi kwana uku su mamana da 'yan uwana sun bar garin sannan na sani shima lokacin munzo garin da niyyar mun dawo nan da zama,akwai wasu abubuwa da yawa wanda shi mijin nawa baiyi bincike ba sannan abin ya had'a da shari'a mara gaskiya bak'in cikin wannan abin ne yasa babana ya rasu,nayi alk'awarin bazan sake furta dalilan ba har sai na d'aukarwa mahaifina fansa,naje na karb'i takardar saki a hannunsa wanda bana fatan mu sake wani zama dashi amma kuma ace min wai ina da ciki,taya ya? Bamu yi zaman arzik'i dashi ba hasalima ko yatsana bai tab'a tab'awa ba in ba da niyyar duka ba ko mari,bamu tab'a had'a gurin kwana dashi ba ina na samu ciki? Wallahi tun da uwata ta haifeni ban tab'a aikata zina ba"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Momma ta rik'a nanatawa tana kuka"

Muhasin shi yazo yana ta rarrashinta akan tayi hak'uri kar ciwonta ya tashi.

Kallon shi tayi lokaci guda idanunta sunyi jajir
"Muhasin ban tab'a ganin mutum kamar Janan ba,'ya'yan talakawan ma fa gudun 'yan uwansu suke sunfi son auren mai kud'i saboda su huta da yake yanzu ba soyayyar gaskiya ake sosai ba,labarinta tamkar shirin film ko littafi,wannan wane irin azzalumi ne"

Itama Janan d'in kuka take sosai,shi kansa Muhasin mamaki take bashi ta sadaukar da far in cikinta akan soyayya ashe dama 'yar hutu ce amma ta mayar da kanta tamkar wadda bata tab'a shiga class ba.

Sai tausayinta ya rufe shi a lokacin yayi nadamar marin da wulak'anci da yayi mata.

Ji yayi Momma ta sake fad'in "Muhasin duk cikin 'ya'yana kai ne kad'ai ke jin magana ta dan Allah kayi koyi da halin Janan,kirki,hak'uri,nutsuwa,tawakkali, da tausayi"

Baiyi magana ba sai kanshi kawai daya sauke k'asa.

Da rana Muhasin ya tafi yi musu takeaway Momma ta kalleta tace "Janan zan miki wasu tambayoyi"

Shiru bata ce komai ba sai da Momma tace "daga aurenki zuwa ranar da kika rabu da mijinki baki tab'a ji kin tashi kinga jikinki wani iri ba,ba sai na fad'a ba kin gane dai"

Shiru tayi na 'yan wasu lokutan sannan tace "Daren aurena na wayi gari a wani yanayi dan har wankan tsarki nayi amma ban kawo komai ba wallahi saboda Aliyu bai kwana a d'akin ba kuma ni ba maganin bacci nasha ba"

Murmushi Momma tayi tace "wannan cikin nashi ne"

Zabura Janan tayi Momma tayi saurin ruk'ota.
"Ki kwantar da hankalinki"

"Na shiga uku" ta sake rushewa da kuka.

Momma tayi ta rarrashinta da k'yar tayi shiru.

Tana kwance tayi lamo Momma tace "Za muje gurin 'yan uwanki wanda suke shak'ik'ai a gurin mahaifinki idan sun karb'eki to idan basu karb'eki ba kuma ni zan rik'e ki,sannan zamuje gurin mijin naki a sanar dashi halin da kike ciki ba dan ya bada komai ba sai dan ya san akwai jininsa a tare dake ko dan wataran"

Hawaye kawai ke zuba a fuskarta bata fad'an komai.









_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*Fatima Muhammad Ali,sak'onki ya iso gareni da farko dai ina amsa gaisuwarki kuma nagode sosai nima ina sonki da yawa nagode da fatan alkhairi da kika min,kuma nima ina miki fatan alkhairi a duk inda kike😍*_

_'yan group na TASKAR SANAZ dana MRS OMAR da sauran groups dake bibiyar novel d'ina nagode sosai😘_



29

Muhasin haka ya koma yola ya d'ebowa Momma kayan sakawa,sannan ya siyowa Janan kaya ita ma.

Ya koma yola shi, sai dai duk k'arshen sati yana zuwa kaduna duba su yana mutuk'ar tausayin Janan d'in.

******

Hawayen daya kasa mak'alewa ne ya samu damar sauka a kuncinsa.

Kallon Raihan yayi ya girgiza kai sannan ya tashi yana neman tafiya tayi saurin cewa "dan Allah Jalal ka tsaya kaji"

"Me zan ji bayan abinda na gama ji yanzu"

"Amma ya kama ta ka saurare ni"

"Lokaci na k'ure min Raihan nafi so naje na kai cigiyar su a kafafan yad'a labarai tun kafin suyi nisa"

"Dan Allah kada ka Ka kai tunda ba b'ata sukayi ba"

"Ni a gurina sun b'ata ne"

"Bazasu ji dad'i ba ina ganin kamar tozarci ne"

Zama yayi yace "to ya kike so nayi?"

"Hak'uri da kuma addu'a"

"Amma meyasa kika min haka Raihan?meyasa tun abin yana d'anye baku fad'amin ba sai da bakin alk'alami ya bushe"

Shiru tayi kawai itama zuciyarta na k'una.

"Ina son Janan kuma na fara sonta had'uwata ta farko da ita,har Janan tayi Aure ban tab'a jin sonta ya ragu a zuciyata ba,na danne kawai saboda na san tayi min nisa,amma meyasa zaku k'i sanar dani halin da take ciki bayan kunsan ita d'in jinin jikina ce"

"So kuma?" Ta fad'a lokacin da ta kasa b'oye damuwarta.

"Eh so da kika sani"

Wani irin kishin Janan taji duk da bata kusa da ita.

_Allah ya k'ara nisantar da Janan yasa karta ji sha'awar dawowa Kaduna_ ta fad'a a zuciyarta yayinda ta rik'a jin haushin kanta da tayi mata differing.

"Ki min alk'awari Raihan" ta tsinkayi maganarsa kamar daga sama.

"Ina jin ka"

"Dan Allah ina son ki tayani addu'a Allah ya dawo min da Janan a cikin kwanakin nan"

"Insha Allah"

"Nagode! Yanzu zanje gidan su Lubna"

"Zan raka ka"

"A'a kiyi zamanki ba kince lecture zaku

Please Login or Register in order to submit comment