You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da wannan maganganu to lallai zamu raba hanya,bazan lamunta ba"

"Umma ni fa ba da wani abu na fad'a ba,na fad'a ne kawai dan muje mu karya asirin da waccan matsiyaciyar tayi wa Yaya,kuma idan komai ya daidai ta sai mu nemi yafiyar Allah ai shi gafurur rahim ne"(kuskuren da yawancin mutane keyi yanzu,wai kace zaka aikata aikin sab'o saboda kasan idan ka tuba Allah zai yafe maka saboda shi Allah mai gafara ne, 'yan uwa shin idan muka mutu muna aikata zunubin fa?wannan fa Babban ganganci ne da kuma hud'ubar shad'an,mu kiyaye)

"Eh hakane amma fa ina tsoro"

"Karki wani tsorata ai hadisi na hud'u cikin arba'una hadis yayi magana akan komai Umma"(wa iyazubillah Allah ka karemu daga fad'awa halaka)


" Shikenan ki bari sai na samo k'wararren malami wanda zai mana aiki kamar yankan wuk'a"

"Yawwa Umma".

**********

Suna zaune ita da Nura a falo suna ta b'ab'b'aka dariya.

" amma Zuhra baki da dama,kamar bazaki iya aikatawa ba"

"Hmmm Nura kenan ai komai kamawa take"

"Kasan Allah ni ina yi mata ne saboda taji rad'ad'in irin muzgunawar da tayi wa Janan,saboda tun kafin na auri Aliyu nayi alk'awarin k'watowa Janan hak'k'inta in na Aure shi"

"Amma ai zaki barsu ko"

"Eh duk lokacin da naji ta furta alamun ta saduda abinda tayi wa Janan to zan k'yaleta in kuma fara mata biyayya,su fa a tunaninsu wai asiri na musu,cab Allah ya kiyasheni da yin asiri,babana Babban malamine na izala,Ahlul sunnah aikuwa kowa ya san babu kalar asiri a gidanmu sai tsantsan sanin qur'ani, hadisai,sira,tauhid,da sauran littattafai da yawa"

"Hakane kuwa babu wanda bai san Malam cikakken mai rik'o da sunnar manzo Allah (S.A.W) bane idonsu ne kawai ya rufe"

"Da kuma tsabagen son kud'i,barin ma wannan mai kama da figaggiyar kaza yanda kasan d'iyar gomna haka take ji da kanta duk zan saitasu ai"

"Kedai ki cigaba da addu'a dan wallahi gani nake Janan ma ba haka nan suka k'yaleshi ba shi kansa Aliyu"

"Hakane ne ai bana wasa da addu'a da nafilfili da kuma azumin litinin da Alhamis"

Shigowar Aliyu falon ne yasa sukayi shiru.

"Ya hak'uri Nura na barka a zaune wallahi wai ina can ina yiwa Ummi fafutukar neman admission"

"Ai kuwa da ka dawo kaga bani nan dan har na gaji da zama"

"Ah haba dai"

Zuhra tayi masa sannu ta zuwa kawai ta wuce d'akinta.


*******

"Ah har yanzu baka tafi gurin aikin ba?"

Yayi d'an tsaki na gajiya sannan ya kalli agogon hannunsa.
"Wallahi Momma ban tafi ba amma ina shirin tafiyar"

Hmmm tayi ajiyar zuciya sannan taja stool ta zauna gabanshi.

"Janan ko?"
Yayi sauri ya d'ago kai ya kalleta.

"Na san tunaninta ya hanaka zuwa office karka damu kayi mata addu'a kawai amma idan kace tunanin Janan zaka saka a ranka koda yaushe zaka zauna a b'acin rai gashi ka kusa Aure kaga inni na lamunta matarka bazata lamunta ba Muhasin na fika damuwa da rashin Janan amma kai kafini rashin hak'uri"

"Momma ba haka bane,Janan ta canza rayuwar gidannan gaba d'aya, fitar da ita a rai tabbas zaiyi wuya,wallahi har cikin zuciyata inason Janan Momma"

"Karka damu Muhasin Allah ya bayyana mana ita,kuma yasa tana cikin kwanciyar hankali a duk inda take"

"Ameen Momma,kusan wata tara kenan"

"Allah ya bayyanata"

"Ameen"











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Safnah luv & Mrs Xerks```


_kuyi hak'uri fans_


36

A hankali ta bud'e idanunta tana k'arewa d'akin kallo.

Abubuwan da suka faru ne suka fara dawo mata tayi saurin tashi tana kiran "d'ana ina yarona?" kuka sosai take tana furta ina d'anta.

A rud'e nurses biyu suka shigo.
"Lafiya ya kike jin jikin naki?"

"Ina d'ana?" ta sake tambaya tana kuka.

'Daya daga cikin nurses d'in ta dafata tace "baiwar Allah ki kwantar da hankalinki d'anki yana cikin kulawa kinji"

"A'a Ku fad'amin inda yake inje in ganshi dan Allah"

Ganin ta rud'e ne yasa suka rakata har d'akin da Abba k'arami yake.

A rud'e ta k'arasa jikin gadon tana k'ok'arin d'aukarta suka hanata.

"Baki ganin baya da lafiya?ki bari ya tashi sai ki d'aukeshi"

Kuka ta fara ganin fuskarshi da bandeshi,tana fad'in "karka mutu Abba k'arami dan Allah karka mutu ka barni kaine gatana ka tausaya min kaji"

Su kansu nurses d'in sai da suka tausaya mata.

Kujera taja ta zauna ta kifa kanta akan gadon ta cigaba da kukan da ta san bazata tab'a dainawa ba.

********

Yana jingine da filo hannunsa rik'e da kansa yana cije leb'e cikin jin zafin ciwon yace "doctor yanzu ko da sanda bazan iya taka k'afata ba?"

Murmushi doctor yayi yace "kana cije leb'e amma kana tunanin tafiya a yanzu?"

"Indai zan iya takawa to zan tafi"

"Zuwa ina?ai in fad'a maka su Mommy suna kan hanya dan na fad'a mata komai" Abbas yayi maganar.

"Me?ka fad'awa Mommy dagaske?haba Abbas meyasa zaka min haka?"

"Saboda ina sonka kuma kasan bazan bari rayuwarka ta lalace akan wata banza ba,dubi yadda ka koma kayi wuju-wuju kusan kullum ana abu d'aya"

"Wa'izubillah,Abbas kana daukar alhakin Janan me tayi maka?shin ka santa a baya ne ta maka laifine?akan me zaka rik'a muzantata?"

"Saboda kana da mata,na tabbatar idan Raihan taji bata tab'a jindad'i ba"

"To bari Raihan d'in tazo sai na tabbatar mata naga Janan kaji me zata ce"

Shiru yayi baice komai ba shima Jalal ya kwanta ya juya masa baya.

Da yamma su Mommy suka k'araso aikuwa ta rufe Jalal d'in da fad'a akan me yasa zai samu ciwo amma ya kasa fad'a mata.
Raihan kuwa har da kukan ta.

Adnan lallab'a shi ya rik'a yi yana masa sannu.

Sunso su mayar dashi can asibitin a Abuja amma yak'i yarda dole ta sa suka juya Raihan kuma ta zauna dan ta cigaba da kula dashi.

Bayan sallar Magrib Najwa tazo,ganin Raihan ne yasa tayi turus tana neman watso tambaya dan yadda taga Raihan na wani shishishigewa Jalal.
Abbas yayi saurin tarar numfashinta da fad'in "wannan matar Jalal ce sunan ta Raihan"

"Oh sannu" ta fad'a ranta a d'an b'ace

"Yawwa,wacece wannan Jalal?"
Tayi tambayar tare da kafeshi da idanu.

"Itace wadda ta kad'eni" ya fad'a kai tsaye
"Oh kece kika so rabani da farin cikin raina ko?" Ta fad'a tana murmushi

Ganin hakane yasa itama Najwa tayi murmushin tace "a'a tsautsayi dai ko"

Zama tayi a kan kujera sai kuma hira ta b'arke tsakaninsu(mata ba wuyar sabo).

Jalal kuwa baya cewa komai shi tunanin sa d'aya taya zai bayyanawa Raihan Janan?
A zuciyarsa ya kud'urta cewar bazai bayyanata ga kowa ba har sai ya warke dan kar a samu matsala.

Haka Raihan ta cigaba da jinyar Jalal su Mommy kullum suna hanyar katsina.

Janan ma ta cigaba da jinyar d'anta ba tare da ta san wa yake d'aukar d'awainiyarsu ba,ta san komai ma'aikatan ke kawo mata hatta abinci,koda ta nemi ta sani ance mata wani bawon Allah amma sam bata tab'a kawowa a ranta Jalal ne.

Shi kam Jalal kullum tunanin sa da burinsa shine yaje yaga lafiyarsu amma babu dama k'afarsa tak'i sai dai yakan tura Abbas ya gano amma baya zuwa sai dai yayi shawagi ya dawo yace tace tana dubashi kuma jikin yaron da sauk'i.
Abu d'aya ne Abbas yayi daya k'i fad'awa Raihan Janan na nan kamar yadda Jalal ya haneshi.


*_2 weeks later_*

Tana tsaye doctor yana rubutu a takardar magani,kallon takardar kawai take yadda taga ya cika yana k'ok'arin juya baya tayi saurin cewa "doctor amma naga kamar ya samu lafiya sosai ma gashi har yana wasansa nayi tunanin za'a sallamemu"

"Za'a sallameku amma sai ya gama warwarewa,kije ki karb'o wannan magungunan ai kin san wurin ko?"

"Eh na sani" ta fad'a tare da fita da sauri dan batason ta barshi shi kad'ai.

Tana tsaye tana jiran layi kawai ta hango Raihan d'in tsaye ita da wata mata suna magana.

Cikin farin ciki ta tafi da sauri gurin.

Tunda Raihan d'in ta hangota ta tsaya tana kallonta cike da mamaki.

"Raihan dama ashe zan sake ganinki?"

"Lallai Janan ashe katsina kuka dawo" ta furta kamar batayi murna da ganin Janan d'in ba.

Sam Janan bataji dad'in yadda ta mata magana ba amma ta dake tace "eh! Meya kawoki asibitin nan?"

"Mijina ne babu lafiya,Janan share-share kike anan?"

Yadda tayi maganar yayi mutuk'ar b'atawa Janan rai ta kalleta rai babu dad'i tace "haba Raihan shara fa?"

"Ahh to ai gaskiya ne dan na san ko kwalin diploma baki rik'e ba,kuma na ganki kaca-kaca,kinga a gurguje Jalal ne mijina kuma jinyarsa nake anan sannan dan Allah bana so ki yarda ku had'u dan nemanki yake kuma da zarar ya ganki zaki iya dagula aurena"

Kasa motsawa Janan tayi dan abinda Raihan take fad'a tana jinshi tamkar saukar aradu a kanta.

"Kinga na bar Jalal shi kad'ai sai anjima"

Har ta juya ta fara tafiya Janan tayi saurin cewa "saboda Jalal d'in kike fad'a min maganganu son ranki Raihan?"

Juyowa tayi ta dawo daf da ita tace "eh saboda shine,kuma dalilinsa zan iya miki abinda yafi wannan"

Ta juya ta tafi,a jikin bangon Janan ta mak'ale tana kuka.
Sai da tayi mai isarta sannan ta share hawayenta taje ta karb'i magungunan ta tafi.

Tana ta sauri dan ta san tafi minti talatin da fitowa ga Abba k'arami shi kad'ai a d'akin.

Tana tura k'ofar taga Jalal rik'e da Abba k'arami.

Ganin Jalal ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba amma wanda ta gani zaune kan kujera shine ya sa har numfashinta ya fara k'ok'arin d'aukewa.

Shima ya tsorata da ganinta sosai amma ya daure kawai ya kafe ta da ido.

Idanunta duk sun firfito kasancewar tana harara garke ne yasa Jalal d'in yayi tunanin ganinsa ne yasa ta kid'ima.

Hannunta rik'e da k'irjinta bakinta yana k'ok'arin furta kalmar SALMAN amma ta kasa.

Jiri ne ya fara d'aukarta tana k'ok'arin fad'uwa kawai ta dafe bango ta zauna a k'asa dirshan.

Sai lokacin hawaye ya fara zuba a fuskarta tamkar an bud'e fanfo.

Jalal ya taso ya durk'usa gabanta yace "Janan dan Allah kiyi hak'uri da abinda nace wallahi b'acin rai ne,kin san irin neman da na miki bazan tab'a k'ink'i a rayuwata ba"

Runtse idanunta kawai tayi har lokacin hawaye na fita.

Adnan kuwa ya kasa motsa ko d'an yatsan shi daga inda yake zaune.

Jalal ya juyo ya kalleshi yace "Bro itace fa,wallahi dama na san hakan sai ta faru dan Allah ka bata hak'uri kasa baki kaima"

Cikin dauriya da jarumta ya taso yazo inda suke ya tsaya "kiyi hak'uri pls" abinda ya iya fad'a kenan ya kalli Jalal yace "bara naje mun bar Raihan ita kad'ai ka rarrasheta zan dawo.

Tana jin ya fita ta bud'e ido tace " Ku fita daga rayuwata dan Allah ku k'yaleni haka karku haukata ni"

"Bazan tab'a k'yaleki ba zan yarda ki sake rayuwar wahala ba ina tare dake har abada"

"Zan mutu Jalal k'irjina zafi yake" ta rik'e k'irjinta tana kakari kamar zata amayo zuciyarta.

Da sauri Jalal ya tashi yana d'angesa k'afa ya fita,a bakin k'ofa yaci karo da Adnan jingine da bango fuskarshi sharkaf da hawaye.

Cike da mamaki ya tsaya yana fad'in "kuka Adnan?"

A tsoroce Adnan ya d'ago ido ya kalleshi.





_*kuyi Manage pls,nayi alk'awarin insha Allahu gobe zan muku typing mai yawa*_











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁





_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





37

Murmushi yayi tare da matse leb'b'ansa sannan yace "Yarima ina mamaki da tausayin yarinyar nan wai wannan matsitsiyar yarinyar itace ta haifi yaron nan kuma take rayuwa a wahalce haka"

Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace "wallahi bro ka ganta dai bata fi shekara 17-18 ba amma da kanta ta haihu babu d'an taimako"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Adnan ya fad'a yana dafe goshinsa.

"Bara naje na kira doctor ka shiga bro kafin in dawo"

Girgiza kai yayi yace "a'a baka da lafiya ka koma bara naje na kira doctor"

Bai jira amsarsa ba kawai ya wuce.

A inda ya barsu nan ya dawo ya gansu ta kifa kanta tana ta kuka tamkar k'aramar yarinya 'yar shekara 3.

Fizge-fizge ta fara lokacin da doctor na k'ok'arin dubata amma ta k'i yarda ta tsaya.

Da k'arfi nurses suka rik'e ta,allurar bacci yayi mata dan itace mafi sauk'i saboda yadda take abubuwa a lokacin tamkar mahaukaciya.


"Ban san meke damun Janan ba wallahi bro idan ka ganta a baya bazaka ce ita bace,amma rayuwar Janan gaba d'aya ta canza,nayi alk'awarin zan zamo farin cikin rayuwarta zan dawo mata da duk wani farin ciki data rasa,wlh Adnan ina son Janan ina jin zabin yanayin nan nata"

Shiru Adnan yayi dan shi kansa ya san dauriya yake,ji yake kamar ana watsa masa garwashin wuta a jikinsa.
Da sauri ya mik'e ya fita kawai.

Motarshi ya shiga yaja da k'arfi ya bar cikin asibitin.

Sai daya fara fita daga gari sannan yayi parking a gefen titi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya rik'a furtawa lokacin guda fuskarshi ta canza hawaye gaba d'aya ya b'ata masa fuska.

"Janan d'ina yau na gani kamar a mafarki,shekara kusan bakwai ban ganta ba sai yanzu,kuma a wannan hali,dama ashe Janan ce wadda Jalal ke bani labari,Janan d'ina ce Jalal yayi soyayya da ita,taya zan sanar dasu itace Janan d'ita bayan ban tab'a fad'a musu sunanta ba?"

Hawayen idonsa ya fara gogewa ya cigaba da fad'in "zanyi k'ok'arin nunawa Janan bani bane Salman d'inta nagode wa Allah daya saka Abba ya hanani auren Janan da yanzu na cuceta na saka mata cuta bata ji ba bata gani ba,na san wannan ma baiwace tunda har Allah yasa Jalal zai rik'e min ita,dole in bar abin nan a zuciya bazan bari kowa ya san itace Janan d'ina ba"

Zuciyarsa cike take da tambayoyi da yake son yi mata amma kuma babu dama saboda baya so ta yarda shi d'in ne,amma yana mamakin yadda Janan ta zama haka,gata kuma da d'a.

Sai da Jalal ya dameshi da kira sannan ya koma,yadda ya ga Raihan ta d'aga hankalinta tana fad'in maganganu abin bai masa dad'i ba.

Kiransu yayi gefe yana tambayar meyasa zatayi haka.

Kuka ta fara tana fad'in "ita in har Janan ta dawo gidansu ta san Jalal gudunta zaiyi saboda ya fifita Janan fiye da komai"

"Karki manta ke fa matarshi ce,idan baki rufa masa asiri ba wazai rufa masa?sannan kin san bashi da lafiya amma kina neman d'aga masa hankali meyasa zaki haka Raihan?"

"Ni ban d'aga masa hankali ba amma tun d'azu ya tafi wajenta ya barni ni kad'ai sai da yaronta ya fara kuka zai kawo min"

"Ka rabu da ita Adnan wallahi saina d'aga mata hankali yadda ta d'aga min nawa" Jalal ya fad'a

"Kaji abinda yake fad'a fa Yaya" Raihan ta fad'a tana kuka.

"Jalal dan Allah karku d'aga hankulanku ni bana son Mommy taji komai har sai Janan ta warke kaga kaima an kusa sallamarka"

"Bro Janan fa k'awarta ce amma wai har ta kasa d'aukar d'anta saboda kishi"

"Eh a kanka zan iya yin komai"

Hannu Adnan ya mik'a ya karb'i Abba k'arami yana fad'in muje ka zauna ka huta.

Da k'yar ya sasanta tsakaninsu suka nufi d'akin da Janan take har lokacin bacci take,wucewa d'akin Jalal d'in sukayi Adnan na rumgume da Abba k'arami yana jin yaron har cikin ransa.

Da dare kuwa,yaron yana ta kuka Jalal da Adnan kowa karb'a yake yana jijjiga amma yak'i daina kuka,Adnan har fita yayi ya sayo madarar NAN amma da suka dama masa k'in karb'a yayi.
Raihan kuwa duk ta wani cune bata ko karb'eshi ba,har sai da wata nurse tace ita mace ce ta karb'eshi mana ai k'ila in yaji jikin mace ya daina kuka.

Ya yatsine ta karb'eshi tamkar zata karb'i kashi sannan ta k'ara da cewa "nifa na tsani kukan yaro wallahi"
Ran Jalal ya b'aci yayinda Adnan yaji haushinta da tsanarta dan ya san koda ya rasa Janan bazai yarda a wulak'anta ta ba.

"Kawoshi na fita kawai dashi" tayi saurin mik'a masa ya sab'a shi a kafad'a ya juya kenan ta murd'a k'ofar ta shigo.

Sau d'aya ta kalleshi ta d'auke idonta kawai ta saka hannu ta karb'i yaron ta fita.

"Bro taya akai ta tashi?"

"Jini mana,watak'ila taji kukan yaron"

"Allah yasa bata ji maganar Raihan ba dan bazataji dad'i ba"

"Ina tunanin taji bara na bita"

Da sauri ya fita.

Yana tura k'ofar tayi saurin Jan hijabi ta rude jikinta dan ya shigo tana shayar da d'anta babu ko sallama.

"Amma baiwar Allah bai kamata kiyi haka ba,kin d'auki d'anki kawai kin fita"

Cike da mamaki ta kalleshi idonta taf da k'walla.

_wai Salman ne ya ke nuna baima santa ba_ ta fad'a a ranta lokacin hawaye suka sauka a kuncinta.

"Amma ko dan yadda Jalal ya damu dake bai dac............."

"Dakata Malam" ta tari numfashinsa,Muryarta na sark'ewa ta fara fad'in "d'ana ne ai ko?to ban nemi taimakonku ba karku kuskura ku sake min katsaladam"

Furucinta ya matuk'ar bashi mamaki
Ji yayi tamkar ya bayyana kansa a gareta amma sai ya dake yace "sai kace ba musulma ba har ayi miki abin alkhairi ki kasa karb'a?"

"Bana so a barni yadda aka ganni"

"Bazan iya ba Janan,na yarda duk hukuncin daya dace ki d'auka a kaina amma banda rabuwa dani"

Adnan ya juya ya kalli Jalal daya shigo,itama idon nata akan Jalal d'in yake.

Kujera yaja ya zauna ya cigaba da cewa "Janan ki tausayi min dan Allah wallahi ina sonki sosai ba zan iya rabuwa dake ba tunda har na samu damar ganinki bayan wahalar nemanki dana sha"

Kuka ya sake kufce mata sai da tayi mai isarta ta gama Adnan d'in yana tsaye ya kasa komai zuciyarsa tamkar zata fashe Jalal kuwa rarrashi kawai yake.

Raihan ce ta turo k'ofar ta shigo daga jikin bango ta lafe lokacin Janan tasa hannu tana goge hawayen idanunta.

"Jalal" ta kira sunanshi a sanyaye.

Bai bata amsa ba dan shima idonsa cike yake da hawaye.

"Nagode da taimakon da kayiwa rayuwata dan na san abinda kamin ba kowa ne zai iya yi min ba,amma na san ba zan iya zama daku ba,ku masu kud'i ni talaka almajira sannan ga yaron nan kai kanka ba sonshi kake ba"

"Ke ba talaka bace da gatanki Janan ba zan yarda kije ko ina ba k'afarki k'afata har Abuja,zan nuna wa Mommy ke domin ta dad'e tana son ganinki"

"A'a bazanje ba,babu inda zan bika Jalal"

"Janan karki min haka"

"Bazai yuwu ba inje gidanku in zauna"

"Kinfi so ki rik'a kwana a titi?"

"Eh saboda anan na rayu har na haifi yaron nan na san Allah yana tare dani"

"Bara na kira Mommy a waya" ya fito da wayar tayi saurin cewa
"Karka min rashin adalci karka sa inyi kaffara Jalal na riga na rantse bazan tab'a k'ara zama a inuwar da ba tawa ba"

"To shikenan zamu siya miki gida"

"Wallahi bazan zauna ba dan Allah ka k'yaleni Jalal" ta fad'a tana zubda hawaye.

"Ki mana alfarma kije gidanmu ki zauna koda a matsayin 'yar aiki ne ko dan rayuwar d'anki karya tashi a titi,na rok'i alfarmarki a karo na farko ki min wannan alfarmar Janan" Sai a lokacin Adnan yayi magana.

Kallonshi tayi lokaci guda taji zuciyarta na harbawa da k'arfi,abinda yake sake k'ona mata zuciya shine yadda Salman ya nuna halin ko in kula a kanta,yana nuna tamkar bai santa ba"

_Haushin Abba yasa Salman zai min haka?meyasa zai min haka bayan bani da laifi?dole in dauki shawararsa ko dan in inganta rayuwar Abba k'arami._

'Dago jajayen idonta tayi tana kallon Adnan sannan ta sauke su tana fad'in "na yarda inje gidanku a matsayin 'yar aiki amma da sharad'in bazaku tausaya min ba a matsayin Janan sai matsayin 'yar aiki ku rik'a kallona tamkar 'yar aikin sannan kada ku nuna kun sanni koda wasa bare har wani ya gane zanje ne a matsayin 'yar aiki saboda yarona sannan kada ku k'ara albashina yafi wanda ya dace a bawa mai aiki idan har kun yarda nima na yarda idan har kuka sab'a zaka nemeni ka rasa Jalal"

"Gaskiya ban yarda ba bazan iya jurewa ba" Jalal ya fad'a a raunane.

Adnan ya dako har inda yake ya dafa shi yana fad'in "karka damu Yarima in har zata zauna cikin mutane da sauk'i"

Haka Adnan yayi ta bashi baki har ya hak'ura suka fita neman takardar sallama a lokacin Raihan ta matso inda take cikin b'acin rai ta fara magana.....







*_Ku min afuwa fans_*👏


_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



*_by SaNaz deeyah_*👄





```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```


_Wannan shafin na sadaukar dashi ga beebah luv_✍

38

"Janan naga alama kina neman ruguza aurena to wallahi baki isa ba,zan miki warning ne, a 'yar aiki zaki zo to a ita nake son kizo bani son ko da wasa ki nuna wa Mommy kece Janan bare har ta ji tausayinki,dan babu yadda zanyi ne da wallahi baza kije gidana ba to amma da kije gidan da yace zai siya miki gwara kije gidana don kar ayi min sakiyar da ba ruwa"

Kallonta tayi tana murmushin takaici tana girgiza kai tace "bana mamaki maganganunki a kaina saboda na san ba ko wane d'an adam ya san halacci ba,bana tantama idan lubna ce bazata min haka ba" ta k'arashe maganar tana hawaye

"Karki fad'a min magana Janan dan wallahi yanzu zan wulak'anta ki,lubnar da tuni ta mance da tarihin rayuwarki k'ila ma bazata ganeki ba idan ta ganki kucaka haka"

Za tayi magana aka turo k'ofar duk suka mai da hankalinsu gurin.

Adnan ne ya shigo ya zauna yana fad'in "mun amso takardar sallama ki shirya nan da 5minutes zamu tafi"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa amma babu yadda zatayi haka ta d'auki tsumman Abba k'arami ta goyashi ta zauna gefen gadon ta rafka uban tagumi lokacin duk sun fita.

Sai bayan mintuna 20 sannan ya dawo yace ta fito su tafi.

Hawaye zafafa suka sauka a kuncinta a fili ta furta "Abba ka yafe min na kasa cika burinka akan lokaci amma nayi alk'awari zan tara kudi in shiga k'asar nijar ko rayuwa ta zata k'are a can sai nayi abin da ya kaini"

Kallonta ya tsaya yi tana ta goge hawaye wani na sake zuba.

Yana so ya rarrasheta amma bazai iya ba baya so ta gane shine,bai san tuni ta gane ba.


A mota ta tarar da Jalal da Raihan,ran Jalal d'in a had'e yake idanunsa a lumshe,sai da ta shiga motar sannan ya juyo ya kalleta sai kuma ya d'auke kai.

Adnan ne yayi driving amma fa zuciyarshi a cunsheta take tunanin janan ya rufe ko wane b'angare na zuciyarshi,kusan sau uku yana neman karawa mota Allah ne ya kaisu lafiya amma da sai sun koma asibiti jinya koma wani ya rasa nashi ran.

Duk tsawon tafiyar nan da sukayi babu wanda yawa wani magana sai karatu kawai da Adnan yasa a motar.

A Kaduna ma da suka tsaya cin abinci Janan k'in fitowa tayi daga motar haka da Jalal yayo mata takeaway tak'i ci.

Karb'ar Abba k'arami yayi ya rik'a bashi fresh milk har yasha ya k'oshi sannan ya mik'a mata.
Hakan ba k'aramin zafi yayi wa Raihan ba,ta kuma k'udurta sai tayi abinda zai sa Janan ta gudu daga gidan da k'afarta.

Sai gaf da magriba suka isa gida.

Mommy ji tayi tamkar ta had'iye 'ya'yan nata saboda farin ciki,tana son ganin 'ya'yan nata a tare da ita.

Sai bayan sunyi sallar isha'i sannan suka had'u a babban falo.

"Adnan wacece wannan kuma?"

Ya d'an gyara murya sannan yace "Mommy 'yar aiki muka sama miki"

" 'yar aiki kuma?a wane dalili?" Mommy ta tambaya tana kallon Janan.

"Mommy tana cikin wahala ne shiyasa muka ga ya dace mu taimaka mata gashi kema kina neman taimako kuma aiki yama Asabe yawa"

"Saboda aiki yama Asabe yawa shiyasa ka d'akko min 'yar aiki mai d'anyan goyo?akan wane dalili?to bana so saboda nida Asabe muna yin komai"

Gaban Jalal ba k'aramin fad'uwa yayi ba,ya kalli Mommy zaiyi magana tayi saurin cewa "karka ce komai Jalal ku mayar da ita inda kuka d'akkota"

Janan kuwa tuni idonta ya fara zubda hawaye ganin abinda tafi k'arfi yau gashi yafi k'arfinta.

"Mommy kota tafi bata da kowa wallahi dan Allah ki taimaka"

Cikin fad'a tace "to wai aikin me?ga Asabe gani ga Raihan sai kun d'akko wata da ban kuma ba tare da iznina ba,bazata zauna ba bana son rigima Adnan"


"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Jalal ya fad'a sannan ya tashi ya shige ciki dan hawaye ke nemen fitowa daga idanuwansa.

Jikin ta a sanyaye ta tashi ta goya Abba k'arami tana shashshek'a.

Sosai Mommy taji tausayinta tace "zo nan baiwar Allah"

Jikin ta a sanyaye ta k'arasa gabanta ta durk'usa k'asa.

"Ina mijinki?meya rabaki da mijinki ko iyayenki a k'arancin shekarunki kike yawo a titi?"

Gabanta ba k'aramin fad'uwa yayi ba,kukanta na neman fitowa fili amma ta damk'e.

Ganin bazata fad'a bane yasa Mommy ta sake cewa "zaki iya aikin gidannan?kingan shi dai babbane sosai"

"Zan iya komai ma dan Allah ki taimaka min bani da inda zanje wallahi in har kika koreni to bansan madafa ba"

Adnan ya sunkuyar da kai yana goge hawaye,Raihan kuwa sai tab'e tab'en baki take.

"Raihan kirawo min

Please Login or Register in order to submit comment