You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tayi tana kallon d'akin wanda babu komai sai wannan carpet d'in dake shimfid'e a k'asa.

Idanunta sun k'ara jujjuyeta ta kalli Mameey tace "wai anan kuke rayuwa Mameey?"

"Eh anan muke tun bayan barinmu Kaduna da wata biyar muka dawo nan"

"A wata biyar d'in nan kuna ina?kafin ku dawo nan?"

"Muna Zaria,bamu da gidan zama tamkar almajirai haka duk inda muka samu muke kwana,Fahad yana zuwa yayi dako ko aikin k'arfi ya samo mana abinci,Janan takardar sallama aka bawa Fahad ko biyar ba'a barmu da ita ba,sai kud'i a hannun Fauziyya dubu biyu dashi muka fara amfani da suka k'are muka zauna a haka,Janan har a bakin juji mun kwana ruwa yayi mana duka,haka Fauziyya ta fara rashin lafiya tamkar bazata rayu ba"

Kuka sosai ta rushe dashi tana fad'in "Allah ka mana sakayya"

Mommy, Adnan da Jalal ba wanda baya hawaye a gurin.

"Kuma baku nemi 'yan uwa ba aka taimaka muka ta side d'inki ko Abba?"

"Fahad yafi sau a k'irga yana zuwa gidan bashar lokacin da Fauziyya ta fara rashin lafiya,sai suka ce muma lokacin da muke dashi bama nemansu dan haka babu abinda zasu iya mana,ko gurin kwana hanamu sukayi dana ga haka sai na hak'ura da zuwa gidan kowa,iyayenmu sun mutu dama sune dolen namu"

Kuka sosai Janan take tana cewa "babu wanda ya kai uncle bashar morar kud'in Abba amma yanzu saboda babu ranshi sun gujemu"

"Wallahi kuwa Janan,a haka naga Fauziyya na neman mace min na kaita asibiti bani da ko sisi,da k'yar aka samu d'ari a hannun Fahad aka siyo file,an bada gado amma babu kud'in biya,haka muka shafa kusan awa goma a opd muna rok'ar likita ya bamu gado ni da kaina zan fita neman kud'i amma suka k'i yarda"


"Ganin numfashinta nayin sama-sama ya saka ni zama a gurin ina kuka,sai a lokacin wani bawon Allah yazo ya biya dukkanin kud'ad'en"

"Watanmu guda muna jinyar Fauziyya ashe cutar ulcer ce ta kamata,wannan bawan Allah mai suna Sagir shi yayi ta d'awainiya damu har ta warke"

"Anan ya nemi ya san labarinmu,ganin irin gudunmawar daya bamu ne yasa ban b'oye masa labarinmu ba,yaji tausayinmu sosai kuma yayi alk'awarin taimaka mana"

"Ya sanar damu shi d'an kano ne,kuma sana'arsa itace wankin mota a wani car wash dake kano, yace da ace yana da kud'in da zai k'wato mana hak'k'i da yayi"

Haka ya biya mana kud'in mota har kano,ya kaimu har gidansu gurin iyayensa da 'yan uwansa sannan ya basu labarinmu suma sun tausaya mana sosai,satinmu d'aya a gidan yace ya kama mana haya saboda mufi sakewa,shine muka dawo nan da zama,ya samawa Fahad aiki a car wash d'in suna zuwa tare kuma tare suke biyan kud'in haya har yanzu"

"Tun kafin ya furta yana son fauziyya nayi mata sha'awar aurensa sai gashi hakan ya tabbata kuma iyayensa suka amince aka yi musu aure shekararsu biyu da yin Aure tana da d'iyarta mace takwararki ce watan yarinyar takwas a duniya"

Shashshek'ar kuka ta cigaba dayi tana kallon gidan.

Ta sake rungume Mameey ta cigaba da kuka.

"Janan a ina kika had'u da Salman shine abinda yafi bani mamaki"

"Mameey sunanshi Adnan fa,kuma dama a wasik'ar Abba ya fad'a min Salman yana raye,a katsina muka had'u kuma shine yayan Jalal dama lokacin nan shiyasa nace Jalal ne Salma ashe 'yan uwa ne"

"Allah sarki mu ai munyi tunanin ya rasu"

Girgiza kai kawai tayi alamar a'a.

"Janan meye labarinki bayan kinzo Kaduna kin tarar Abbanki ya rasu"

Sunkuyar da kai tayi ta sake fashewa da kuka.
Sai da ta shafe kusan minti talatin tana kuka,Mommy taji kamar tazo ta rarrasheta sai taga kuma ai ga Mameey bai dace taje ba.

Sai da taci kuka ta k'oshi sannan ta bada labarin komai,still ta sake b'oye cewar Abba k'arami d'an Aliyu ne,kawai tace zuwanta Katsina k'addara ta fad'a mata har ta haifi yaron kamar yadda ta sanarwa su Mommy,sannan tak'i fad'a mata wasu abubuwan musamman rayuwar gidan Mommy.

"Janan d'an shege fa" Mameey ta fad'a tana hawaye.

Har cikin zuciyarta tana jin zafin yadda ta sheganta yaronta amma babu yadda ta iya tana ganin kamar a gaske ne Abba yayi mata wannan furucin.

"Wannan wace irin k'addara ce" Mameey ta sake fad'a tana kuka.

Fahad dake gefe shima hawayen ne ke fita a idonsa.
"Ni ban lura da idanun Janan ba sai yanzu" ya fad'a yana goge hawaye.

"Haka Allah yaso,ya sunan yaron kuma yana ina?"

Ta goge hawaye tace "sunan Abba nasa,ina ce masa Abba k'arami,yana Yola gurin Momma a gidan dana zauna watanshi 20 yanzu"

"Zanso ganinshi,ina godema Allah daya dawo min dake lafiya"

Ta juya ta kalli Mommy dasu Jalal tayi musu godiya sosai.

"Ba dai k'wace min ita zakiyi ba" sai a lokacin Mommy ta sake yin magana itama tana goge hawayenta.

"Bazan k'wace miki Janan ba ai Janan ta zama taki"

"Dama har an saka bikinsu wata guda ita da Adnan d'in"

"Kuma shi zai aure ta ne bayan tana da yaro?kar dai ayi masa dole"


Wasu zafafan hawaye suka fito daga fuskar Jalal yana kallon Janan d'in kawai yana ganin abin da ta aikata kamar bazata yi ba.

"Babu abinda zance muku sai godiya,nagode sosai da abinda kuka min akan Janan"

"Karki damu ai Janan 'yata ce"

A lokacin suka yi magana yadda za'a tsara bikin da duk wasu shirye-shirye.

20k Mommy ta bawa Mameey da zasu tafi tace gashinan suyi duk wata siyayya ta kayan abinci,anan ta karb'i number Fahad saboda Mameey bata da waya.

Har sun shiga mota taga Janan d'in a tsaye bata da niyyar shiga.

"Janan shigo mana" Mommy ta fad'a.

Kallon Mameey tayi sannan tace "Mommy dan Allah ki barni anan"

"A'a Janan ai bazai yuwu ki zauna ba binsu zakiyi tunda tare kuka zo"

Mommy ce tayi tunanin ya kama ta a barta su zauna su hira da mamanta sosai.

Murmushi tayi tace "shikenan ki zauna amma dai zaki dawo kafin biki ko?"

Cikin jindad'i tace "eh"

"Sati d'aya ma ya isheta"
Mameey ta fad'a.

"To shikenan amma zamuyi kewarki ga babu Abba ma,sunce sai biki zasu zo"

Murmushi kawai tayi.

"To ya za'ai da kayan sawa kuma?"

Tayi saurin cewa "Zan karb'o na Yaya Fauzah kawai"

"In dai zai miki ai babu matsala ko kuma bara na baki kud'i sai ki sayi dogayen riguna kafin ki dawo tunda baki taho da kaya ba"

"A'a ki bar shi kawai mungode ai itama Fauziyya girmansu d'aya kayanta zasu shigeta"

"To mun gode Maman Janan sai munyi waya"

"Mune da godiya"

'Daga musu hannu tayi lokacin da motarsu ta tashi.

Da suka koma gida ma sabuwar hira ta sake b'arke musu tana ta sake basu labarib irin wahalar da tasha.

Fahad kuwa ya kira Fauziyya ya sanar mata tace tana nan tafe.

*********

Da gudu fauziyya ta shigo gidan,tana shiga falo ta rungume Janan ta fashe da kuka.

Goyonta ta tsince Janan d'in ta karb'a, sabon kuka ya b'arke tsakaninsu.

"Sister! Aliyu ya cuce mu ya lalata duk wani burinmu"

"Yaya fauzah bana k'aunar ko sunansa a fad'a na tsaneshi wallahi Ashe da gaskiyar Abba daya hanani aurensa amma na kafe"

Labarin suka sake badawa da yadda Aliyu ya rik'a cin mutumcinsu a kotu itama tayi ta basu labarin gwagwarnayar da tasha.

Anan ta basu labarin cewa Abba k'arami d'an Aliyu ne amma ta haramta hakan ga kowa dan Aliyu ya shegantashi tun kafin ta haifeshi yace ba nashi bane sannan a mafarkinta ma Abba ya umarceta da karta sanar da cewa yaron Aliyu ne, hatta a gidansu Jalal babu wanda ya sani sai su Momma kawai.

"Amma kinyi k'ok'ari da har kika iya haihuwa kika yanke cibi,ina mamaki yadda har aljanna ta taimakeki amma kika kasa samun taimako daga gurin mutane,wallahi koni na baki goyon bayan kar wanda ya san d'anshi tunda baya so ko Abba k'arami idan ya girma karki fad'a masa sis" Fauzah tayi maganar

"Wallahi kuwa,suma fa nayi lokacin dana gama yanke cibi,ban tab'a tunanin haka haihuwa take ba sai ranar,gaskiya Allah ya saka miki da alkhairi Mameey"

"Ameen Janan! Amma ya aka yi kika dawo Abuja da kanki kikazo ko kawoki akai gidansu Salman?"

Labarin komai ta basu hatta rayuwarta a gidan da yadda suke bata kulawa da abinda Raihan ta mata da wanda Lubna ma ta mata.

"Dama Raihan Jalal ta aura?" Fauzah tayi tambayar.

"Eh shi ta aura amma yanzu sun rabu ma"

"Meyasa?"

"Mommy ce ta saka Jalal ya saketa saboda irin abubuwan da ta min da kuma wayar da taji,yanzu ma tayi Aure a zaria shine tace zata had'a ni da Jalal da har an saka bikinma da yanzu anyi"

"Allah sarki Lubna ashe haka take da kirki ina ganin kamar Raihan ta fita ashe Raihan muguwa ce"

Mameey ce tace "to ai Lubna tun suna yara suke tare kinga kuwa ai dole tafi Raihan,amma meya hana aurenki da Jalal dan naji Maman nasu tace bikinki da Salman nan da wata d'aya"

Shiru tayi na wasu lokutan sannan tace "saboda na goga wa kaina cutar HIV kuma Adnan d'ina yana da ita"

Duk a tsorace suka kalleta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Janan kin san abinda kike fad'a kuwa?" Mameey tayi tambayar a rikice.

Kuka ta fara tana basu labarin rayuwar Adnan d'in da irin wahalar daya sha ta k'ara da cewa "ina son shi Mameey ganin da gaske baza'a bani shi ba yasa nayi amfani da razor na gogawa kaina cutarsa"

Kuka Mameey ta fara tana fad'in "Ashe har yanzu baki da hankali Janan"

"Mameey kowa kallon haka yake min amma ni ina kallon girman so ne"

"Meyasa zakiyi haka sister?ni a ganina da Jalal da Salman duk d'aya ne tunda so iri d'aya suke miki"

"Yaya Fauzah ni kuma bana son Jalal na rasa ya zanyi in cusa son shi a raina indai har ina ganin Adnan babu wanda zansu kamarsa"

"Na yarda so guba ne"

"Tabbas so guba ne amma Jalal ya kasa gane hakan yanzu haka fushi yake dani"

Mameey ta kalleta ta girgiza kai tace "ko nima ji nake kamar na tashi na bar gurin ko kunya baki ji ba kika sakawa kanki ciwo kawai saboda kina son Salman,dole Jalal yayi tunanin kin tsaneshi ne kawai"


"amma sis ai saiki hak'ura tunda yana sonki,wallahi tun satin bikinki ya gane bawan Allahn nan sonki yake"

"Nima ina son shi amma ba irin son da kuke tunani ba,Kenan abinda nayi kuskure ne?"

"Da butulci ba,bazaki gane illar abinda kikayi ba sai nan gaba,Janan meyasa kike da taurin kai meyasa bakida tunani cutar k'anjamau fa,mai karya garkuwar d'an Adam,dole wata rana kiyi dana sani musamman lokacin da cutar zata bayyana a jikinki kina ji kina gani ta kasheta" Mameey ta fad'a tana hawaye.

Rungume ta Janan tayi tana kuka tace "ance ana shan magani bata fitowa Mameey karki min baki wallahi kin tsorata ni"

"Ba baki nake miki ba amma tabbas kinyi kuskure uwa uba kin zalunci Jalal"

"Zalunci kuma?"

"K'warai kuwa saboda kin nuna k'iyayya ga mutumin daya nuna soyayya a gareki" sai a lokacin Fahad yayi magana tare da tashi ya fita.

"Kenan abinda nayi ba daidai bane,na shiga uku"

"Baki shiga ba wannan jarabawarki ce ki cigaba da addu'ar neman rahamar ubangiji kawai"

Haka sukayi ta tattaunawa har aka kira magriba.

Janan ce ta goya little Janan suka yi sallah.

Lokacin mijin Fauziyya yazo suka sha hira sosai,yaga Janan d'in da yake ta jin labarinta.

Sai k'arfe goma sannan ya d'auki fauziyya a lifan d'insa suka tafi.
Tace gobe da safe zaizo ya d'auki Janan d'in ya kaita ta taya ta hira.

Ranar Janan bata runtsa ba tunanin maganganun da suka yi kawai take,dan ma sunyi waya da Adnan shine kawai sassaucin da ta samu.

_Washe gari._

'Karfe 11 mijin Fauziyya yazo ya d'auki Janan ya kaita,tacewa Mameey zata dawo da anyi la'asar.

A Dorayi Fauzah take gidanta baya da wani girma,ciki da falo ne sai toilet da kitchen a tsakar gida sai wani extra room shima a gefe.

Labari take ta bata yadda rayuwarta ke gudana a gidan.

Duk da mijinta baya da wani k'arfi amma yana k'ok'arin kyautata mata,gashi 'yan uwansa duk suna sonta.

Janan taji dad'in haka sosai tayi musu addu'ar bud'i nagari.

"Kin san meye jindad'i na sis?"

"Sai kin fad'a"

"Wallahi jiya har mafarki nayi an tono ramin dukiyar su Aliyu su karb'i nasu su bamu namu,wallahi ba dan ba dan ba da babu wanda zaici gado sai mu saboda 'yan uwan Abba basu k'aunarmu"

"Ke dai bari kawai ina ma Abba na nan a raye"

Hawaye Fauzah ta goge sannan tace "wallahi duk ranar da dukiyarmu ta dawo zan ci mutumcin Aliyu sai dai kawai Abba k'arami ya yafe amma baiyi sa'ar mahaifi ba"

"Ki daina had'asu Abba k'arami maraya ne babansa ya rasu tun yana ciki,koya girma haka zance masa"

Tare ta taya ta suka yi aikin komai.

Aikuwa ta hanata tafiya ranar a gidan ta kwana.

Tun azzahar take ta cewa "nifa anayin sallah la'asar zan tafi son ganin Mameey nake"

"Ke sis dan Allah ki bari sai gobe"

"A'a gobe ma cewa zakiyi sai gobe"

"Bazan ce ba"

"A'a muna gama aikinnan zan tafi"

'Karfe uku na rana Fahad ya shigo gidan.

Duk suka gaidashi yana daga tsaye yace "Janan ga Jalal yazo fa tun d'azu ya kawo miki kayanki saida ya huta Mameey tace na rakoshi nan ku gaisa"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa.

Fauziyya tayi saurin cewa "Yaya ya shigo mana bara na bud'e d'akin can dama a gyare yake"

"Okay ni wuce wa zanyi gurin aiki daga nan"

Suna zaune a falon bayan ta gaidashi ta kasa fad'in komai.

Fauziyya ce ta shigo suka gaisa ta kawo masa abinci da ruwa.

"A k'oshe ma nake naci abincin Mameey"

"A'a dan Allah kaci wannan ma"

"To nagode"

Tashi tayi ta fita ta barsu.

Kallonta ya sake yi kanta na k'asa k'irjinta sai bugawa yake.

"Janan" ya kira sunanta a hankali.

Bakinta na karkarwa tana son cewa na'am amma ta kasa.

Shima bai damu ta amsa ba ya cigaba da cewa "jiya banyi bacci ba har sai da na tabbatar na samu transfer aikina zuwa Singapore, sannan da safe naje na karb'i takardar sheda sannan na taho kano,yanzu haka na fara neman visa dan bana son na k'ara koda sati d'aya a garinnan"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi,ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sadda kai.

"Zanyi nesa da ku saboda ganinki zai rik'a tuna min abubuwa da dama,bana son ruguza rayuwarki keda Adnan,kin sakawa kanki cuta saboda kina son shi ni kuma ina son duk abinda kuke so kuma na san shima yana sonki,zanyi k'ok'arin cireki a raina saboda kin zama matar yayana,alfarma d'aya nake nema a gurin ki shine idan kun haifi d'a namiji ku saka sunana zan rik'a ziyartar gida duk bayan shekara uku,idan Allah yasa na samu mata nima zanyi Aure a can ki gafarceni idan har na b'ata miki rai a iya zamanmu"

Hawaye gaba d'aya ya wanke mata fuska kalamansa sun k'ara raunana mata zuciya.

Hannu ya zira a aljihu ya fito mata da wrist watch d'in ta.

"Ga wannan" ya mik'a mata.

'Dago kai tayi ta k'urawa agogon ido.

"Tun ranar da kika samu ciwon nan nake ajiye dashi kullum ina ganin shi a matsayin soyayyarki amma yanzu dole in rabu dashi hakan zai tabbatar da cewa na rabu da soyayyarki"
Ajje mata yayi a gabanta.

Kukanta na neman fitowa fili tayi saurin toshe bakinta.

"A cikin trolleynki akwai wata Leda ki bud'e ki duba abinda ke ciki shine gift d'in biki dana baki,sai kuma k'aramar trolley siyayyar da nayiwa prince saboda na san zai dawo bana nan,nayi magana da wanda zai kawo furniture a sakawa Mameey na bashi number ki should incase"

Sai kuma ya mik'o mata ATM d'insa yace "gashi ATM d'ina ne bana amfani dashi sosai code d'in 2345 current ne karki manta zan rubuta miki, akwai 500k a ciki kuma zan rik'a turo kud'i each month kuma amfanin yau da kullum da kud'in,idan anyi biki ki bawa Mameey ko Fahad saboda kar zargi ya shiga tsakaninki da Adnan"

"Jalal...."

"Karki ce komai Janan kinfi k'arfin komai a gurina" ya ajje ATM d'in kusa da agogon.

"Na shiga uku" ta fad'a tana kuka.

"Yawwa nayi magana da Sule dan ta gidanshi na biya yace zai nemi Adnan da zarar ogansu yazo ki zama cikin shiri,Mommy da Asabe da Adnan duk sunce suna gaidaki"

Tashi yayi tare da fad'in "sai Allah ya k'addara saduwa"

Kukanta ya fito fili sosai ta fara rerawa,yana fita fauziyya ta shigo.

Da sauri Janan ta rik'ota.
"Naji komai sis amma pls muje kiyi masa sallama"

Da k'yar ta tashi suka fita lokacin yana k'ok'arin shiga mota Fauziyya tayi saurin cewa "to mungode sosai ka gaida gida"

"Nine da godiya" ya bawa Fauziyya amsa amma tamkar Janan yake bawa dan idonshi a kanta.

Itama ta kafe nata a kanshi tamkar tana harararshi dan dai kawai ya san a haka suke.

Fauziyya nata zungurarta kan tayi magana amma ta kasa cewa komai.

Yana jan motar ta runtse ido ta saki kuka.

"Haba sis kar mutane su tsaya kanki"

Bud'e idon tayi da niyyar tayi mata magana kawai taga matar tsaye inda Jalal ya bari.

"Kinyi sake" abinda ta fad'a kenan tana dariya.

Janan ta k'ura mata ido kamar baza tayi magana ba sai kuma tace "kina nufin ya tafi kenan?"

"K'wari kuwa ai kin cuci kanki da har kika bari cutar k'anjamau ta shige ki"

"Da gaske na kamu da ciwon?"

Fauziyya ce ta rik'ota dan tana tunanin kamar rikicewa ce ta saka ta surutai.

Fuzge hannunta tayi sannan ta matsa kusa da matar cikin kuka ta sake fad'in "ki fad'a min na kamu da ciwon?"

"Keda kika samarwa ciwon gurbi a jikinki har ni kike tambaya k'arin bayani"

"Ki taimaka ki hana Jalal tafiya ko ina dan Allah"

"Kada ki sake rok'ona,da kin san Allah amma kika iya yin butulci,zan k'ara ingiza Jalal ya tafi ya barki kici soyayya,kin cuci kanki kin yiwa kanki babbar illa,butulu kawai keda ganin Jalal sai dai a lahira" b'at ta b'ace.

Janan d'in ta k'walla k'ara tare da zubewa k'asa.

_*1hour later*_

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ta fara furtawa da ta bud'e ido.

Fauziyya dake gefenta tayi saurin d'agota tare da fad'in "sannu Janan,kin d'aga min hankali wallahi"

"Ya akai kika shigo dani" ta fad'a tana hawaye.

"Janan ai baki da wani nauyin da zan kasa d'agaki,ki sassauta ranki pls"

"Na cuci rayuwata na cuci Jalal"

"Ki fidda komai a ranki mana"

"Tayaya?na san Allah bazai yafe min irin abubuwan dana masa ,ki bani waya ta in kirashi in nemi gafararshi,tunda har aljan yace nayi butulci to nayi"

"Kina nufin aljanar nan tazo?"

"Eh tace ni butulu ce"

"Karki gaskata maganarsu sis"

"Ban gaskata ba dan dama ba k'unata take ba amma dan Allah ni dai ki bani waya na kira Jalal"

Mik'o mata wayar tayi cike da tausayinta.









_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




46

Ta kirashi kusan sau goma amma yak'i d'agawa.

Ta kasa nutsuwa dan haka ta ari wayar Fauzah ta kira still bai d'auka ba.

Kuka tayi-tayi dan shi kad'ai ne jindad'inta.

Ana kiran sallar magriba suka sauka a napep ita da Fauzah, Fauzah ta biya mai napep kud'in sannan suka shiga gida.

Mameey taga damuwa a fuskarsu amma ta kauda kai kawai tace "Ku d'auki buta kuyi alwallah"

Bayan sun idar Janan ta rab'e jikin Mameey tana kuka tana basu labarin abinda ya faru tsakaninsu da Jalal.

"Gaskiya ban tab'a ganin mutum mai mutumci kamar Jalal ba yanzu da zamu rabu ya bani 50k yace inja jari kafin wani lokacin da k'yar ma na karb'a" Fahad yayi maganar

Mameey tace "ga kuma uban kayan abinci daya kawo kuma sannan yanzu yace furniture"

"Haka yace" shine abinda Janan ta fad'a tana goge hawayen da basu daina zubowa ba"

"Na yarda banyi adalci ba Mameey na zama butulu" ta k'ara fashewa da kuka Mameey na ta rarrashinta.

"Janan kin riga kin yi kuskure sai dai ki gyara nan gaba, Allah yasa ki cinye jarabawarki"

"Ameen duk suka amsa.

Bata bud'e trolley ba sai da safe bayan tayi wanka.

Wani d'an box ne baifi tafin hannu ba,tana bud'ewa taga 'yar k'aramar ring,ta d'akko ta kalla sosai taga irin English ring d'innan ce.

Wasu zafafan hawaye suka sauka a fuskarta a take ta d'auka ta zura a hannunta.

Ta janyo trolley da yace na Abba k'arami ne ta bud'a taga kayan sawa ne sababbi da kayan wasa da kuma chocolate kala-kala.

" Allah sarki Jalal wallahi ban tab'a dana sanin abinda na aikata ba sai yanzu,ina neman yafiya a gareka Jalal".



Haka ta hak'ura ta cigaba da addu'a.

Kwana biyar da zuwan Jalal Adnan ma yazo,a ranar yake sanar da ita Jalal ya tafi kwananshi d'aya har lokacin ma bai isa Singapore d'in ba.

Zuciyarsa sosai ta rik'a bugawa tayi k'ok'ari sosai wajen b'oye damuwarta da fad'in "amma meyasa Jalal ya tafi?"

"Ya cewa Mommy transfer aka yi masa amma tace dole ya rik'a ziyartarta akai-akai"

"Allah sarki to Allah ya taimaka"

"Ameen"

Sosai suka yi hira harta manta da wani babin Jalal.

Adnan ya sanar mata ranar asabar mutumin nan zaizo kano tayi murna sosai dan gani take burinta ya kusa cika.

Sai kuma da dare da tazo kwanciya bacci ta kasa tunanin Jalal ya hanata sakat.

Tashi tayi ta d'oro alwallah ta fara jera nafiloli na neman tsari daga shaid'an dake ta mata wasi-wasi.

Mameey ma tashi tayi ta d'oro alwallah itama ta fara yi kamar yadda ta saba,sai da suka yi sallar asuba sannan suka koma bacci.


*******

Sai da ta d'aga trolleyn sosai sannan ta dara ta da k'asa a farfajiyar gidan.

"Oyaa abar min gidan miji"

"Mu kike wa haka Zuhra?"

"Nayi muku d'in,ai umarnine daga mijina"

Juyawa tayi tace bara na kira Jalal d'in.

"Umma wai mu Yaya zaisa a yiwa korar rashin mutumci?muma fa muna da gado "

Kuka baisa Umma tayi magana ba har Aliyu ya fito.

"Umma dan Allah ku tafi ku koma k'auye zan nemeku"

"Ni kake fad'awa haka Aliyu?"

"Umma ai kinji me nace dan Allah ku fice"

Muryarta har sark'ewa take saboda kuka.
"Zamu fita Aliyu amma ka sani ban yafe maka ba,na nema maka hanyar k'watar 'yancinmu amma kana neman tura ni a rana"

"Dan Allah kuje naji" ya sake fad'a.

"Babu inda zamu Umma saboda akwai gadonmu muma a gidan nan" Ummi ta fad'a rai a b'ace.

"To ki dawo ki gani idan ban kakkaryaki ba wawuya kawai"

"K'yalesu Ummi muje,indai malamai ne munsan inda zamu nemo su muma"

"Ni da Allah na dogara"

"Malamin soro ba,ki jira nan da la'asar kiga abinda zai sameki"

"Alkhairi zan gani da yardar Allah"

Basu d'auki trolleyn ba kawai suka fita.

"Umma to ina zamu?"

"Gidan Malam daga nan kuma shi da kanshi Aliyu zai dawo yana rok'ona mu komo"

"Ni wallahi bana son zuwa gidan boka gaskiya,wannan shirkace fa "

"Uban wa ya ce miki gidan boka zamu,gidan Malam muma zamu zata ga tagayyara.

Suna tsaye bakin titi suna neman napep d'in da zai kaisu tasha,wata mota Ash k'irar Accord tazo ta wuce sai kuma tayo baya.

Mamallakin motar wanda a k'alla zaiyi shekara 45 a duniya ya zuge glass d'in motar.

" sannu hajiya,'yan mata ina zuwa haka?"

Had'e rai tayi sosai ganin haka ne yasa Umma tayi saurin cewa "zamu je k'auyen kangire ne"

"Ku shigo mana in ba damuwa sai na kaiku"

"A'a ka barshi mun gode" Ummi tayi saurin fad'a.

Umma ta dalla mata harara sannan ta kalle shi tace "Malam mun gode".

Da sauri taja hannun Ummi ," Umma kawai bamu san mutum ba sai mu shiga motarsa"
"Ki min shiru Ummi" b'ata rai tayi suka shiga bayan motar Ummi sai cizewa take ranta baya so suka shiga.

Suna shiga ya d'auki wata kwalbar turare ya fesa a bayan motar basu k'ara tsintar kansu ba sai a wani d'aki duk Kansu an d'auresu.


"Umma wayyo Allah na shiga uku ina ne nan?,Umma sai da nace karmu shiga kika yi mana dole"

Kuka kawai Umma take ta rasa abin cewa ma.

Kusan awarsu guda a gurin suna kuka babu k'ak'k'autawa.

'Katti uku ne suka shigo d'akin.

'Daya daga ciki ya daka musu tsawa tare da fad'in "dalla ku mana shiru idan zaku kwana dubu kuna kururuwa babu wanda zai jiku"

"Dan Allah ku rufa mana asiri ku mayar damu inda kuka d'akko mu" Ummi ta fad'a cikin matsanancin kuka.

"Ban d'akko ku ba dan na barku ku tafi salin alin" wanda ya d'akko sun ne ya shigo dagashi sai singlet da boxer.

Duk idanunsa ya firfito waje.

"Ke kika haife ta?" Ya tambayi Umma.

"Eh 'yata ce"


"Amma mama kin iya haihuwa" ya fad'a yana lasar harshe tamkar wani maye.

"Karka cutar min da ita wallahi duk abinda kayiwa 'yar wani sai an wa 'ya'yanka"

Juyowa yayi ya kifawa Umma mari tare da fad'in "duk abinda zaki kada ki ambata alkaba'ir akan 'ya'yana"

Ya kalli k'attin yace "ku tube min ita inyi lalata da ita a gaban uwarta ta ga yanda ake isa da iko"

Ummi na kuka Umma nayi haka aka rabata da kayan jikinta Umma ta runtse ido sosai tun tana jin k'arar Ummi har ta daina.

Sai daya gama abinda zaiyi da ita sannan yace
"Zan tafi ina son kafin in dawo ko wanne yayi abinda yake so da ita"

A tak'aice sai da aka shafe kusan awa biyar cikin su hud'u babu wanda baiyi amfani

Please Login or Register in order to submit comment