You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemi motar ya rasa gashi duk wani document yana ciki,dan har a lokacin ma bincike ake.

Ya tambayesu garinda suke suka sanar masa ya k'ara tambayarsu matakin karatu mahaifinmu yace shi bai tab'a karatun boko ba amma yana da ilmi na islama,yayinda Datti yace ya tsaya a matakin secondary,aikuwa yace ya kawo takardun zai sama masa makaranta dan ya cigaba da karatun nasa.

Direba ya sa ya kaisu har kauyensu tare da tarin alkhairi da yayi musu.

Bayan sati biyu da dawowarsu kwatsam sai ga Alhaji yazo ya kawowa mahaifinmu ziyara.

Dad'i sosai sukaji,mahaifinmu ya fita samo masa abinda zaici kasancewar zuwan bazata ne,anan mahaifiyarsa take fada wa Alhajin cewa mahaifinmu ya dad'e baiyi aure ba saboda talauci babu wanda yake k'aunar had'ashi da 'ya'yansa duk da baya da wani hali marar kyau.

Ya tausaya masa sosai amma ko bayan ya dawo basu nuna sunyi wata magana ba,haka aka dama masa fura da nono kindirmo aikuwa yasha sosai.

Bayan tafiyarsa da wata d'aya ya sake dawowa ya ce zasu koma birni nan da sati biyu dan haka su tattara komai nasu.

Da farko har Goggo tak'i yarda saboda zuga da ta samu daga wajen mutane amma daga baya sai taga zaman nata ma babu wani amfani tunda babu wani abu da take a k'auyen dama daga ita sai d'an nata.

Haka kuwa akazo aka d'aukesu a mota suka koma cikin garin Kaduna.

Gidan da ya basu Safe content ne,3 bedrooms 1 parlor sai kitchen da dinning area,each bedroom akwai toilet a ciki.
Sun tsorata ganin cewa anan zasu zauna su sun saba rayuwar ruga,Goggo kuwa fur tace bazata zauna ba da k'yar mahaifinmu ya shawo kanta.

Watansu uku a gidan Alhaji ya d'orashi kan wani kasuwanci nashi,da yaga suna samun riba sosai sai yake bashi contract idan an samu,a wannan yanayin ya cewa mahaifinmu yaje ya nemi 'yar wajensa Nabila idan ta amince sai a d'aura aurensu.

Yayi mamaki sosai da jin maganar Alhaji,bai k'ara shan mamaki ba sai da yaje gurin Nabilar ta amince dashi.

Ansha fad'a gurin danginta dan sunk'i amincewa a cewarsu ta taso cikin arzik'i taya zata auri talaka wanda yake aiki k'ark'ashin mahaifinta,ita kuwa tace tunda Alhaji ne ya zab'a mata ta amince kuma tana son shi.

Basu so dai haka aka yi auren ya basu wani dank'areren gida tare da maigadi da 'yar aiki,Goggo kuwa tuni ta saba da wannan gidan dan haka aka barta da masu aikinta su biyu.

Bara na tak'ace miki labarin,mahaifanmu suna son junansu Yayana aka fara haifa bayan shekara 9 aka haifeni sunsha gata a gurin iyayenmu babu abinda muka rasa har sai da mahaifinmu ya k'ara aure sannan muka fara fuskantar matsala a wurin kishiyar mamanmu,lokacin ina Jss1,tsana tsangwama hatta mahaifiyarmu bata raga mata ba.

Cikin k'ank'anin lokaci mahaifinmu ya juya mana baya,mamanmu bata iya cewa komai saboda abin yafi karfinta.

Bana mantawa ina Ss1 aka d'orawa mahaifiyata sharri wai ta kawo namiji d'akin ta,a gabana mahaifinmu yayi mata duka daga ni har ita kuka kawai muke lokacin Yayana baya nan.

Kwana biyar da faruwar abin ta rasu wanda doctor ya tabbatar mana da cewa zuciyarta ce ta buga.

Abinda zai k'ara baki mamaki shine mahaifinmu bai wani damu da rasuwar tata ba sam.

Da k'yar na gama secondary school shima a government school na k'arasa,yayana yana ta fafutukar neman aiki a lokacin bai samu ba kuma mahaifinmu yak'i dafa mana da k'yar ya samu ya fara sayar da layin waya duk da babu riba sosai amma yana d'an samu,ni kuma zaman hakannan nake,dangin mahaifiyarmu sam basa sonmu saboda babanmu dan haka ko munje gurinsu ba dad'in zaman muke ji ba,sannan mahaifinmu baya barinmu muje rigarsu,rabonmu da can tun suna zaman lafiya da mamanmu,Alhaji da Goggo kuwa duk sun rasu dama sune masu k'aunar tamu,a k'alla yanzu nayi shekara 32 a duniya ni kaina.

Mahaifinmu da kishiyar mamanmu sun hanamu aure na rasa dalili amma har na barwa Allah zab'i,Yayana kuwa ya kasa hak'ura duk wata macen daya kawo sai an masa k'azafin da zata rabu dashi hakan tasa ya fara shaye-shaye duk lokacin da ransa ya b'aci sai yasha ya bugu, daddy ya sa a kulleshi a cell ni kuma a rufeni a d'aki ayi ta jibga da wayar wuta,dagani har yayana kusan duk jikinmu akwai tabon duka.

Kusan shekara d'aya data wuce ya samu aiki a wani asibitin kudi wato private hospital na dad'e banga yayi dariya ba sai ta dalilinki na dad'e banga yayi shaye-shaye ba sai ta dalilin k'in amincewarki,dan Allah kiso Yayana ku fitar dashi daga k'angi.

Kallonta Janan tayi ta sake b'ata rai tace "lallai ma kin raina min hankali,kizo har gabana kina cewa inso mashayi"

"Janan kiji tausayinsa dan Allah ki fitar damu daga wannan matsalar na san da kin amince masa zai daina sha"

"To meye damuwa na a ciki ki fita nace ki tashi ki fita tun kafin ranki da nawa su b'aci kinga ke babba ce dan kin girmeni nesa ba kusa ba dan yanzun banfi shekara 22 a duniya ba zanso ki tafi dan kar wani mummunan abu ya faru"

Mik'ewa tayi tsaye itama Janan ta mik'e.

Kallonta Salima ta sakeyi sannan ta fita idanunta cike da hawaye.

Da sauri Janan ta kulle k'ofar da key sannan ta dawo ta zauna tare da dafe goshinta.

_na shiga uku ni Janan taurin kaina ya jawo min matsaloli da dama,yau ko Mameey zata kasheni dole in kwana a gidanmu._ abinda ta fada kenan sannan ta tashi ta shiga toilet dan ta watsa ruwa.

**********

Tana tura k'ofar falo taga Daddy tsaye yana ta fad'a,duk da bata san akan mene ba amma tasha jinin jikinta musamman da taga ya juyo ya kalleta a fusace yace "zo nan".
Duk ilahirin jikinta tsuma yake,a hankali ta tako zuwa inda yake,wani mari daya kai mata saida ta durk'ushe a k'asa.

" ni zaki cuta ki ha'inta Salima? Wannan itace tarbiyyar dana baki kenan?"
'Dago idanunta tayi a tsorace ta kalli kwaroron robar dake hannun Daddy,tashin hankalinta ya k'ara k'aruwa,bakinta na karkarwa tace "kayi hak'uri dan Allah, dama" bata kai ga k'arasawa ba ya doke bakin tare da d'akko sark'a irin wadda ake d'aure doki ya zubata a gadon bayanta.

Wani k'ara ta saki a gigice take k'ok'arin rik'e chain d'in saboda tsananin zafin da taji.

K'ara zuba ta yayi a kanta wanda har ya sauka kan kafad'arta,cikin tsananin gigita ta ruga da gudu ta fita.

Da sauri yake dad'in "karka bari ta fita maigadi" ya fad'a yana yowa wajen,ganin halin da take ciki yasa maigadi yayi tamkar ta bugeshi ta fita ne dan har fad'uwa k'asa yayi.

Janan kuwa da sauri ta fito daga hotel d'in,hannunta rik'e da wayarta tana tunanin ta kunna ko kuma ta barta a kashen dan tun ranar da ta zo Jalal ya kira ta kashe bata sake kunnawa ba,d'ago kai da zatayi kawai ta saukesu ana Abbas.

Gabanta ya fad'i shi kuma kai tsaye ya k'araso kusa da ita.

"Mayaudariya" ya fad'a yana kallonta.

Bata ce masa komai ba,ya nuna ta da yatsa yace "kin had'a wuta a Abuja shine kika dawo nan kina zaman kanki ko?to ki sani Jalal na gab da zuwa Kaduna kinsan zai sab'a miki tunda kin zama azzaluma"

"Zaluncin me nayi?"
"Ki rufa min baki kafin na b'ata miki rai"
Juyawa yayi ya shige motarsa yaja da gudu,bin motar tayi da ido cike da mamakin abinda ya mata tare da tunanin me yasa yazo Kaduna ya akai ya san anan take bayan rabonta dashi tun a Katsina,Adnan ne ya fad'o mata arai rasa hannu ta goge hawayen idonta.

Tana tsaye tana jiran napep taga wani Napep d'in ya tunkaro yana k'ok'arin bugeta,da sauri ta d'an matsa gefe,a hankali Salima ke k'ok'arin fitowa idonta a lumshe daga gani kasan tana jin zafin ciwon dake jikinta.

Ganin jini dake jikinta ba k'aramin d'agawa Janan hankali yayi ba.

"Subhanallah me nake gani ne? Meya sameta" ta fad'a lokacin da ta rik'ota tare da maidata ciki itama ta zauna.

"Ki taimakeni Janan" shine abinda Salima ta fad'a tare da k'ank'ame Janan tana wani irin kuka.

"Ka kaimu asibiti dan Allah kaimu private "

"Wallahi hajiya nima dana ga yanayin nata saida nace na kaita asibiti tace a'a nan take son zuwa"

Jikin Janan itama duk ya b'aci da jini tamkar ita aka jima ciwon.

Karb'ar gaggawa aka musu tare da shigar da ita cikin Emergency dan lokacin had ta suma, Janan ta tsaya tana kallon gurin tare da tunanin ko 'yan fashine suka tare ta a hanya tunda ko mayafi da takalmi babu a jikinta,da sauri ta nufi inda ake yankar kati ta gama komai sannan ta dawo,mutane sai kallonta ake yadda jini ya b'ata gaban rigarta da mayafinta.





_Sadeey_✍🏻
[3/5, 11:43 PM] ‪+234 803 254 3874‬: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah👄*_



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


61

Tana nan tsaye doctor ya fito,da sauri ta k'arasa gabansa tace "doctor ya jikin nata"

"Ki biyo ni office" ya fad'a sannan ya wuce,da sauri ta bishi office yana shiga ta shiga.

Kujera ta samu ta zauna sannan ta mayar da hankalinta ga doctor "doctor lafiya kuwa?meya sameta?"

Hannunsa ya zube akan table sannan yace "wannan wane irin duka ne?su waye suka mata wannan mummunan dukan?"

Shiru ta d'anyi na wani lokacin sannan tace "bani da masaniya akan hakan"

"Kamarya kenan?kinsan ya dace ku fara zuwa police station sannan kuzo nan saboda 'yan sands su samu masaniya,bamu fiya karb'ar case kai tsaye irin wannan ba"

Rasa me zata ce tayi ta d'an duburburce sannan tace "Eh sisterna ce amma ba gidanmu d'aya ba"

Ganin haka ya share maganar ya sake fad'in "an aske kusan rabin gashin kanta anyi mata d'inki a inda ta samu ciwo sannan muna buk'atar jini leda d'aya idan da wanda zaku kawo to in kuma a lab zaki siyo duk d'aya ne"

Ya mik'a mata katunan yace "wannan shine na jini,wannan kuma na magani da allurai da zaki sayo"

Tashi tayi da sauri ta fita,lab ta fara zuwa ta kai saboda layi sannan ta dawo pharmacy shima still da layin haka tayi ta zirga-zirga.

Sai da har aka sawa Salima jini sannan ta tafi dan har lokacin Salima bata farfad'o ba.

Kai tsaye gidansu ta nufa dan ta gaji da rayuwar hotel bayan iyayenta na raye.

A falon gidan taci karo da Mameey tana k'ok'arin shiga kitchen Jalal na zaune kan kujera.

Idonta cike da kwalla ta kalli Mameey, itama Mameey a tsorace ta k'araso gurin tana jijjigata tana fad'in "meya sameki haka Janan?"

Jalal wanda ya k'araso gurin da sauri ya kalleta yana fad'in "meya faru dake Janan?"

'Kasa ta durk'usa gwiwoyinta jikinta a sanyaye tace "dan Allah kuyi hak'uri"

Rik'ota Mameey tayi tana fad'in "Janan jinin nan na meye?"

Kuka ta k'ara fashewa dashi sannan ta rungume Mameey ba tare da tace komai ba.

Mameey ta kalli Jalal tace "dan Allah Jalal ka bani minti biyar"

"Ba damuwa" ya fad'a murya a sanyaye.

Jan hannun Janan tayi sukayi bedroom.

A bakin gado ta zaunar da ita tace "ki fad'a min meya faru jinin nan daga ina? Ni mahaifiyarki ce kada ki boyemin komai Janan"

Idanunta da sukayi jajir ta d'ago ta kalleta.

"Mameey tun ranar da kika koreni a gidan nan ina nan garin ban tafi ba na kama d'akine a hotel" shiru tayi ba tare da tace komai ba.

Jin shirun yayi yawa yasa Mameey tace "to sai akayi Yaya?"

Wasu hawayen ne suka fara sauka a fuskarta tasa hannu ta goge sannan ta fara bawa Mameey labarin abinda ya faru.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ta fad'a tare da zama kan gadon ba tare da ta shirya ba.

"Janan duk wanda ya ganki a hotel bayan da iyayenki a garinnan kina tunanin wane irin kallo zai miki?"
Ta fad'a tana k'ok'arin maida hawayen dake neman fitowa daga idanunta.

"Mameey kin koreni na rasa ina zani shiyasa"

"A ina na koreki? Cewa nayi ki koma Abuja haba Janan yaushene zaki canza wannan hali naki?"

"Kiyi hak'uri Mameey na miki alk'awarin bazan sake musa duk wata maganarku ba,bazan sake Jayayya daku ba"

"Ba wannan alk'awarin kad'ai ba,ina son kiyi min alk'awarin bazaki tab'a sanar dasu ba baki da wannan ciwon na HIV"

"Meyasa Mameey?"

"Saboda bana son ki ruguza rayuwar Jalal,dan Allah Janan ki bar abin iya nan"

Kai ta d'ago tana zubda hawaye.

"Shiga kiyi wanka,bara naje gurin Jalal d'in"

"To"

Fita tayi gurin Jalal ita kuma Janan ta shiga toilet.

A tsaye ta tarar dashi ta d'anyi murmushi tace "ya na ganka a tsaye?"

Ajiyar zuciya yayi tare da fad'in "Mameey wai me yake damun Janan?meya sameta?"

Zama tayi kan kujera tare da cewa "wata ta taimaka ta kai asibiti tace it la kanta bata san meya sameta ba amma bara tayi wanka ta fito kaji ta bakinta"

"Okay" ya fad'a tare da sadda kai k'asa.

Janan na fitowa ta tsaya gaban mirrow tana k'arewa kanta kallo ta rame sosai idanuwanta sunyi zuru-zuru ga fuskarta ta fad'a sosai.

Murmushi tayi sannan ta d'auki lotion d'in Mameey ta shafa ta bud'e closet d'in Mameey ta san bazata rasa kayanta a ciki ba.

Wata doguwar riga ta janyo ta saka sannan ta d'akko night oud d'in Mameey ta feshe jikinta.

Headtie d'in ta yafa ta fita falon.

Mameey bata falon daga Jalal sai wata a gefensa wadda kanta a sunkuye yake bata shaida wacece ba.

Kallon tuhuma Jalal ke mata yayinda ita kuma take kallon matar dan ta kasa gene ko wacece da dalilin zamanta kusa dashi.

“So kike ki gane ko wacece ko?to bak'uwarki ce” tayi maganar tare da d'ago kanta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fad'a sannan taja da baya.

“Macuciya keda aure har abada bazan bari kiyi aure ba tunda kin kasa barin wannan bawan Allah ya samu kwanciyar hankali” ta nuna Jalal

Bakin Janan na karkarwa a tsorace take fad'in "a'a, a'a dan Allah"

Janan lafiyar ki kuwa,rigar Jalal ta rik'e tana fad'in "gata nan ta hana ni zaman lafiya ban san me nayi mata ba dan Allah ku fitar dani daga gidannan"

"Wai wacece?" Jalal ya sake tambaya

Da hannu Janan ta nuna ta tana fad'in "gata nan dan Allah ku fidda ta"

Kallon gurin yayi baiga komai ba
"Ni fa banga komai ba ki nutsu Janan.

" wlh tana tsaye gata nan"

A daidai lokacin Mameey ta fito ganin zuffa a goshin Janan kuma ta rik'e Jalal gam yasa tace "wai mene?"

Da sauri Janan ta rungume Mameey tana kuka har lokacin tana kallon matar.

"Mameey kodai na haukace ne kinga fa wata matace a d'akin nan baki ganta ba?"

Juyawa tayi ta kalli ko ina sannan tace "babu kowa sai mu uku a d'akin nan ki nutsu Janan.

“ki daina b'ata lokacin ki indai nice baki gama gani na ba” ganin tayo kanta ne yasa ta k'walla k'ara daganan bata sake sanin make faruwa ba.

**************

A hankali take bud'e idanunta har zuwa lokacin da ta gama bud'esu gaba d'aya.

Kallon Mameey tayi wadda kanta yana cinyar ta, Fahad da Jalal a tsaye sai malamin da 'yar aiki a gefe.

"Malam ta tashi"

"Yawwa Alhamdulillah"

Matsowa yayi yace a samo masa ruwa mai kyau d'an kad'an a kofi.

'Yar aikinsu taje ta d'ebo ta kawo masa

Addu'a yayi a ciki sannan ya mik'a yace tasha sauran a shafe mata fuska.

"Malam kana ganin kar ayi mata ruk'iyya?" Fahad ya sake tambaya

Gyara murya malamin yayi yace "to kasan ita ruk'iyya tana bankad'o duk wani aljani dake jikin mutum,ita kuma yarinyar nan tunda kunce bata tab'a wani abu makamancin haka ba to ina ganin da kayi ruk'iyya gara ku barta haka ayi ta samo mata magani,domin su Aljanu in har aka bankad'o su zai iya zama matsala abi abin a hankali"

"To Malam kana ganin wani magani ya kamata tayi amfani da su?"

"Ku sama mata Man Zaitun,Man Habbatussauda zata rik'a shafe jikinta dasu kafin ta kwanta bacci,sai kuma garin habbat d'in shi kuma tana kwab'a d'an kad'an da madara tana sha safe da yamma,Sai Shifa'ulinnas shi kuma sha ake shima safe da yamma,ruwan kal shi kuma zata rik'a sirka murfi d'aya da ruwa tana sha,ko ta zuba d'an kad'an a abinci idan zataci"

"Amma kamar shi ruwan kal da kayi magana ai duk zamu iya amfani dashi naji kamar ance yana wankin ciki"

"Eh sosaima,yana maganin ciwon ciki ciwon mara da sauransu,amma aljannu sam basa son ruwan kal d'in dan zakiga ma yawanci idan sunzo ana shafa shi a fuska ko kai zasu tafi"

"To Malam mun gode Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen ya rabbi Allahu ya bata lafiya"

"Ameen Malam"

"Fahad kuje sai ku kaishi gida ko"

"To Mameey" ya fad'a tare da mik'ewa tsaye

Jalal ma ya tashi yana fad'in "muje daga can sai mu sayo maganin da Malam ya fad'a"

"Jalal wallahi bani da aljanu" ta fad'a tana hawaye

Har ya tsaya zai dawo dan ta bashi tausayi sosai a yadda tayi maganar sai kuma ya tuna Mameey na gurin sai kawai ya fita.

Fashewa tayi da kuka tana fad'in "Mameey ina da Aljanu dagaske?"

"Ki kwantar da hankalinki Janan kina addu'a kinji"

"Mameey idan ta san zata shiga Jikina meyasa ta taimakeni,tana son haukatani kawai"

"Ki cigaba da Addu'a muma zamu tayaki"

Tunowa da Salima na asibiti yasa ta saurin tashi tsaye

"Lafiya?"
"Na bar wata a asibiti sam na manta babu kowa a gurin"

"To ki bari mu muje idan yaso ke sai ki zauna da Talatu a gidan ko"

"A'a Mameey dan Allah ki bari naje wlh na warke ma"

"To bara su Fahad d'in su dawo sai mu tafi gaba d'aya"

Kallon Talatu tayi tace "kinga je ki zuba abinci a manyan kulolin nan ki saka komai a basket sai a tafi dashi"

"To Mameey" da sauri ta tashi tayi kitchen

"Mameey kinyi min sabbin d'inkuna?"

"Au baki gansu ba a closet d'inki?"

"Ai ban shiga d'aki na ba,to nayi miki amma materials sunfi yawa dan naga kinfi son dogayen riguna"

"Babu Riga da zane?"

"Ke d'in zan yiwa zane,k'ugu kamar muciya a ina zaki d'ora?"

"Kai Mameey da a gaban Jalal kika fad'i haka da kin bani kunya"

"Saboda Jalal d'in sa'anki ne ba Yayanki ba"

"Mameey nifa bance haka ba amma na san dai nafi wasu"

"Su wa kika fi?"

Murmushi kawai tayi Mameey ta sake cewa "idan da wanda kika fi to sai in masa kuka,ni har mamaki nake idan naga maigida(Abba k'arami) wai ke kika haifeshi"

Kunya tasa tayi shiru ta sadda kai k'asa tace "dama Mameey saboda idan ta tashi kinga dole zatayi wanka bansan wane kaya zata saka ba kuma ta d'an fini jiki"

"To ki bari idan munje munga yadda take sai na bawa Fahad ya sayo mata ready made sai a had'o da kayan wanka"

"To Mameey amma mu tafi da kayan wanka kawai in yaso sai a sayi kayan daga baya"

"To shikenan".


Bayan su Fahad sun dawo da maganin aka shirya aka tafi asibiti.

Suna shiga ta ci karo da doctor, da sauri da k'arasa gabansa tace "doctor ya jikin nata?"

"Ke kam ina kika shiga kin tafi gashi kuma ta tashi babu kowa a gurinta"

"Yanzu dai babu wata matsala?"

"Eh zaki iya shiga amma tana buk'atar wanka da abinci,kinga dai yadda ciwon yake a kula dashi sosai"

"To mungode,,har yanzu tana Emergency?"

"A'a mun mayar da ita Amenity3 saboda tana buk'atar guri mara hayaniya,zakije ki biya kud'in d'akin"

"To nagode sosai doctor"

"Mameey ku muje tana Main Female Ward cikin Amenity"

"Okay to"

Tana zaune akan gado an jingina mata pillow da bango ta jingina dashi,idanunta a lumshe suna yin sallama ta bud'e idanunta wanda suka gama yin jajir.

Mameey ta k'ura mata idanu cike da tausayinta.

Jalal jikin k'arfen ya tsaya,yana kallon ciwon tsigar jikinsa na tashi, Fahad kuwa har k'walla yaji a idanunsa.

"Sannunki ya jikin?"
Kai ta gyad'a alamar da sauk'i,daidai lokacin Janan ta shigo.

Ido Salima ta k'ura mata kenan Janan bata tafi ba bayan ta kawota asibiti.

"Sannu sis ya jikin naki"

"Da sauk'i" ta fad'a da k'yar

Zama tayi daga gefen gadon tace "Mameey kin ganta kuma doctor yace tayi wanka sannan taci abinci,dan Allah Mameey ki taimaka mata da wankan ni kuma zanje na sayo kayan da zata sauya tunda an sayo kayan wanka da mayukan"

"To kuje sai Jalal ya kaiki ko,kafin ku dawo tayi wankan"

"To Mameey ga wannan takardar ya Fahad sai ka karb'o sauran maganin kuma ka biya kud'in d'akin"

Karb'a yayi yace "to kiyi sauri Janan kar ta zauna da jini a cikin kaya babu dad'i"

"Yanzu zamu dawo insha Allahu"

Tare suka fita kowa yayi nashi gun.

A hanyar zuwa Boutique wayar Jalal d'in ta fara ringing "

Kalla yayi yana smiling yayi picking "hello Matana ya kike?"

"Ba lafiya ba Mijina yaushe zaka dawo?"

"Ummm ina jin zuwa gobe amma wace matsala ta faru kuma?"

"Mommy mana wallahi tanata min barazanar kora,tace na korar mata Janan dan haka nima saina bar gidan,Ban san me nayiwa Mommy ba wallahi sam Mommy bata k'aunata"

"Kiyi hak'uri Amal insha Allahu komai ya kusa daidaita"

Kuka ta fara kasancewar Janan na jin duk abinda ke faruwa sai ta k'ara k'ulewa.

"Matana dan Allah kiyi hak'uri kinji dan Allah, wannan ba halin Mommy bane ban san waye ya zuga Mommy take yin haka"

"Yanzu ma fa sai kulle d'akina nayi ta kawo wuk'a ta bani tana fad'in wai in kasheta in huta tunda bazan bar mata gida ba,ni dai dan Allah ka canza min gida"

"Kinga bara na kira Mommy" da sauri ya katse wayar yayi dialing ta Mommy har sai da ta kusa katsewa sannan ta d'aga.

"Ina jinka" shine abinda ta fad'a.

"Mommy dama Janan ce zakiyi waya da ita" dan yadda ta amsa masa wayar sai yaji bazai iya maganar Amal ba

Kafin Janan tayi magana tuni ya manna mata wayar a kunne.

Shiru tayi ta kasa magana itama Mommy tayi shiru.

Ganin shirun yayi yawa yasa tace "Mommy ina yini"

"Hmm Janan Ashe kina nan"

"Mommy kiyi hak'uri dan Allah"

"Idan kinaso inyi hak'uri to ki dawo mu zauna bana son kiyi nesa dani,ga Abba k'arami kullum sai ya tambaya ina Ammi"

"Zan dawo k'arshen watannan insha Allahu"

"Meyasa bazaki dawo tare da Jalal ba?"

Kallon Jalal d'in tayi sannan tace "bani da lafiya ne kuma ina karb'ar allura kullum"

"Tofah meya sameki?"

"Ina fama da ciwon kai amma da sauk'i ma"

"Amma meyasa kika kashe wayarki?"

Shiru ta d'anyi,Mommy tace "to shikenan Allah ya k'ara sauk'i ki gaida Mameey idan zaki dawo ki kirani saina turo direba ya d'aukeki"

"To shikenan nagode"

Ta mik'awa Jalal wayar.

**********

Da yamma misalin k'arfe 5 na yamma Janan na zaune a d'akin daga ita sai Salima dake kwance a kan gado,Mameey taje gida ta dawo,Jalal da Fahad kuwa basu san inda suka tafi ba.

"Janan" Salima ta kira sunanta a hankali.

'Dan k'ara matsawa tayi jikin gadon tace "na'am kodai jikin ne?"

"A'a ina son dai kije gidanmu ki gani halin da Yayana ke ciki,idan kuma yana cell dan Allah ki kira Ya Abbas ki sanar masa"

"Abbas" ta fad'i sunan.

Kai Salima ta gyad'a alamar eh.

"To bara naje d'in ki bani address na gidanku"

Cikin k'arfin hali ta mata kwatance amma tace dan Allah kar ta fad'a musu inda take.

"Zan jira Mameey ta dawo sai naje"

"A'a dan Allah kije yanzu kar dare yayi"

Ganin ta damu yasa Janan ta tashi ta fita.

Ta d'an dad'e a tsaye bata samu Napep ba sai daga baya.

"Dan Allah kar ka d'auki kowa kayi min balance duka zan biyaka"

"To ba damuwa Hajiya"

Har k'ofar gidan ya kaita ta fidda dubu uku ta bashi.

Godiya sosai yayi mata sannan ya tafi.

Tana shiga farfajiyar gidan yayi daidai da fitowar Hisham yana k'ok'arin bud'e mota.

Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamakin ganinta a gidan.

"Janan"

Bud'e baki tayi tana k'ok'arin yin magana amma ta kasa.

"Dama kin san gidanmu?"

"Eh na sani yanzu mana,dama lafiyarka lau amma baka tambayi kasan halin da 'yar uwarka ke ciki ba"

"Wa kenan?"

"Kafi kowa sanin wa nake nufi"

"Salima ba"

"Itafa"

"Ki rabu da wannan yarinyar sam bata da hali mai kyau"

"Haba kai kuwa ita kuwa ta damu da sanin halin da kake ciki meyasa zaka ce haka?wallahi da ka san halin da Salima ke ciki da ka tausaya mata"

"Duk halin da take ciki ita ta jawa kanta,bani da wani gata sai ita amma ta zubar mana da mutumci"

"Kar kace haka Salima na k'aunarka tana shan fama akan in soka,bata da wani farin ciki sai ganin ni da kai mun zama d'aya"

"Taya zaku zama masoya bayan kinada aurenki"

Da sauri ta juyo ta kalli bayan ta dan ganin mai maganar.

"Jalal,ya akai ka san nazo nan?"

"Saboda sanin darajarki,kuma ina k'ara bibiyarki dan insan halin da kike ciki"

"Amma Jal......"
"Shhhh" yayi saurin tsayar da ita tare da matsawa kusa da Hisham

"Ita in bata da hankali meyasa kai zaka biye mata?"

"Kamarya kenan?" Hisham ya tambaya.

"Jalal me kake k'ok'arin yi haka?"

"K'watowa kaina 'yanci" ya fad'a rai a b'ace.

"Naji tana maka maganar soyayya to ka sani duk abinda tazo maka dashi k'arya take yaudararka take son yi,inaso ka rabu da zantukanta babu gaskiya a ciki,ka ganta nan matata ce mun samu tsab'ani ne sai ta gudo nan Kaduna ta kama d'aki a hotel"

Daga Janan

Please Login or Register in order to submit comment