You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin nan Jalal baizo yayiwa Janan gaisuwa ba itama haka.

Da yamma Zuhra tazo tare da Asabe sukayi mata ta'aziyya ta sanar da ita Aliyu ne shima a kwance babu lafiya shiyasa bata samu zuwa da wuri ba.

Hajar ma a ranar tazo tasha kuka kamar ranta zai fita dan sai da ta bawa kowa tausayi a gidan.

Amma a haka Jalal ya kutso cikin mata yace ta tashi ta bar musu gida.

"Dan Allah kayi hak'uri Jalal ka barni inyi masu ta'aziyya ko babu komai Adnan tamkar d'an uwa ne a garemu sunyi aure da yayata har da albarkar yaro"

"Ina yaron bayan ya mutu kun kasheshi wallahi Allah bazai barku ba"

"Bai mutu ba d'an Adnan yana raye domin ranar wanka ba'a b'oyon cibi"

Fizgo hijab d'in ta yayi yace "idan baki fita ba babu abinda zai hana in wulak'anta ki,ni zaki zowa da maganar banza"

Cikin kuka tace "wallahi d'an Adnan yana raye kuma zan kawo muku shi har gida"

Mari ya wanke ta dashi,mommy ta tashi ta wanke shi da mari ta nuna masa hanya tace "fita nace"

"Mommy in har zan fita sai ta fita ta bar mana gida"

"Babu inda zataje" Janan ta fad'a tare da tashi ta rik'a hannun Hajar

"Baka da imani Jalal taya zata zo ta'aziyya ka wulak'anta ta gaban mutane"

"Na wulak'anta kema baki fi k'arfin haka ba"

Zare ido tayi a tsorace ta kallesa,Raihan ta mik'e tsaye tana ma Jalal kallon mamaki dan a iya saninta duk wanda ya tab'o Janan sai yaga wulak'anci amma yau shi yake cewa haka.

"In kuma ba haka ba sai dai ki bita ku bar mana gidan"

Kallon shi ta k'arayi cike da mamaki,mutane sai magana suke masa amma yak'i kula kowa sai masifa yake.

Hannu tasa ta matse kumatunta ta na hawaye ta kalleshi tace "zan bar muku gida saboda muma muna dashi bare kayi min gori Jalal"

Kukane ya sark'eta ta saki hannunta Hajar tana shirin fita Mommy ta rik'a hannunta "ai ba gidansa bane shi kad'ai ki k'yaleni dashi Janan"

Baki ta bud'e zatayi magana kukan ya sark'eta ta rik'a jan numfashi ta bud'e baki zatayi magana taji kanta na juyawa a gurin zata zube Jalal yayi saurin rik'ota ta suma a jikinsa.

"Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un" shine abinda ya fada yana jijjigata.

"Tashi ka fita"
Kallon Mommy yayi sannan ya kalli Janan.

"Ka tashi ka fita nace ko matarka ce ta zaka rik'eta" ta fad'a cikin shouting.

Duk abin nan da ake Mameey na zaune amma ta Sadda kai k'asa bata d'ago ba har Jalal ya fita.



_Ina jiran comments d'inku._

*_Sannan duk mai littafin nan daga farko dan Allah ya turo min,Pieces ba document ba_*






_Sadeey S Adam_✍🏻
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyahπŸ‘„_*



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


57

Sati biyu da rasuwar Adnan Lubna tazo tayi ta'aziyya,itama tasha kuka sosai na rashin Adnan.


_5 Months later_

Hannunta rik'e dana Abba k'arami ta sakko zuwa falon k'asa.

Jalal ne ya fara d'agowa ya kalleta ta sauke k'wayar idonta k'asa,a gaban Mommy ta zauna k'asa kan carpet tace "Mommy dama wurinki nazo neman alfarma"

"Ina jinki Janan ko in tashi muje d'aki"

"A'a"

Shiru ta d'anyi kafin tace "dama nazo neman alfarma ina so ki barni na koma gida"

Kallonta sukayi su duka kanta na k'asa ta kasa d'agowa.

Hannu Mommy tasa ta d'ago da kan nata tace "Janan me muka yi miki kike son guduwa ki barni?"

Idanunta a lumshe tace "wallahi babu komai Mommy kawai ina son komawa gidane"

Hawaye ne suka zubo kan kuncin Mommy ta sake kallon Janan tace "da ace zuwa gida zakiyi kiyi kwana biyu to bazan hanaki ba duk da idan kin tafi ina kewarki amma ace yanzu zakiyi tafiyar dindindin ki barni da kad'aici Asabe bata nan wannan sabuwar mai aikin ba shigowa b'angaren mu take ba data gama aikinta take komawa side d'in ta Jalal bai fiya zaman gida ba ni kad'ai zaku bari da kad'aci Janan,Mamanki ta bar min ke saboda ke nake gani a matsayin Adnan amma in kika tafi shikenan fa"

Tashi tayi da sauri tayi side d'in ta dan karta fashe da kuka a gabansu.

Cikin b'acin rai Jalal ya tashi yana fad'in "har lokaci yayi da Mommy zata rik'a hawaye a dalilinki,to bari kiji tana da wanda zai d'ebe mata kewa domin jibi Amal zata tare a gidan nan idan kinga dama karki sake zuwa gidan nan idan kin tafi, kiga in abin zai mana ciwo ke d'in me" key d'in motarsa ya d'auka zai fita Abba k'arami yace "daddy zan bika"
Hannu ya d'aga masa tare da cewa "Abba kaje Amminka ta nuna maka daddynka ni Uncle ne kaji"

'Daga kai yayi alamar to, shi kuma Jalal ya fice yayinda Janan tabi k'ofar da kallo cike da mamakin furucin Jalal.

Yana fita kai tsaye gidan su Amal ya wuce,tun kafin ya k'arasa ya kirata a waya ya sanar mata.

Cikin zumud'i aka had'a masa kayan ciye-ciye a babban falon bak'i.

A gurguje tayi wanka ta dawo kan dressing mirror tana cancad'a kwalliya.

Su'ada dake zaune kan gado tace "dobeki dalla sai wani rawar kai kike kamar akanshi zaki fara sanin d'a namiji"

Harararta tayi tace "ji banza karki manta fa shi mijina ne na sunnah dan an d'aura fa"

"Umm umm kaji masu mijin sunnah wai kina nufin kin bar harka?haba k'awata karki bani mamaki mana"

Sai data gama shafa janbaki sannan tayi murmushi tace "haba beb wane irin na bar harka nida harka ta nunan harka,har kusan mutuwa nayi fa ashe dalilin zamu had'u da Jalal ne saboda na k'agu nima in shiga gidan miji in raya sunnah banyi tunanin zan sameshi da wuri haka ba ke a iya tunaninki zan iya rabuwa da kamal shine hasken rayuwata fa dan dai kawai garani yake amfani kawai yake dani amma bazai iya aurena ba"

"Kuma wallahi ya dawo yaji labarin aurenki to kuwa kin kad'e"

"Hmmm naga ina harka da wasu mazan bashi kad'ai ba"

"Amma kuma ai kinfi tsoranshi dan duk inda kike yace kizo ko me kike ajjewa kike kije ko Abbu da Ummu sai haka"

"Kinga ya isa haka ki sameni sai ku gaisa ko"

Da sauri ta fita tana zuwa k'ofar d'akin ta tsaya ta d'an gyara sannan ta shiga cikin k'asaita.

Idonsa a k'asa yana danna waya k'amshin turarensa ya bugi hancinsa.

'Dagowa yayi suka sakarwa juna murmushi.

A hankali ta k'arasa gabanshi tayi hugging d'inshi tare da bashi peck a kumatu "nayi missing naka MD"

Hannunsa ta saka cikin nashi ta d'an matse sannan ta d'ora kanta a kafad'arsa

"Kayi min shiru ko?ko dai banyi kyau bane"
Murmushin gefen kumatu yayi sannan yace "ina missing d'in ki amma ni yau kad'ai kikayi nawa"

"Ko yaushe ina cikin kewarka"

"Ina son ki tabbatar"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi tare da lumshe idanunta.

Bakinta ya shafa da hannunsa tayi saurin bud'e ido.

"Anan zaki min kiss ba a kumatu ba"

Kallonshi tayi ta d'an lumshe ido ta fara k'ok'arin kai leb'enta kan nashi ya mik'e tsaye tare da fincike hannunta daga nashi.

"Lafiya?"

Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye.

"Janan" ya fad'a cikin rud'ewa

"Janan kuma?"

"Amma...."
"ki fad'awa Abbu gobe ne tarewarki idan Allah ya kaimu zan turo mota"

Da sauri ya fita ta bishi tana kiran sunansa ya k'i juyowa har ya tashi motar ya tafi da gudu tun kan ya k'arasa gate yake horn dan a bud'e masa gate.

Buga k'afa tayi ta turo baki tare da cije leb'e.

Jikinta a sanyaye ta koma ciki,tana shiga d'aki tayi wurgi da d'an k'aramin mayafinta tare da kwantawa a gado.

"Tofah lover girl ya aka yi ne?" Su'adah ta fad'a tana dariya

"Kin san ko ruwa bai sha ba kawai ya mik'e yana kiran wai Janan,dama ni naga yanayinsa ya canza dama"

"Wacece Janan kuma?"

"Wata banza ce,matar yayanshi daya rasu wannan ba kin ganta ba da mukaje gaisuwa"

"Ohh eh nagane ta to ko aurenta zaiyi?"

Tashi tayi zaune ta kalleta tace "cab Allah kiyaye ai daga ni babu k'ari"

"sai kinyi dagaske fa".

A b'angaren Jalal kuwa gudu yake ta shek'awa a zuciyarsa yana fad'in _Allah yasa ba wani abu ne ya faru da Janan ba._

Ana bud'e gate yana shiga yayi parking a gurin da sauri ya shiga ciki.

Babu kowa a falon dan haka ya haye sama da saurinsa.

Tana zaune tana ninke kayan Abba k'arami taji an turo k'ofar da k'arfi an shigo.

Kallon shi tayi a d'an tsorace itama yadda taga yana haki yasa ta tsorata.

Abba k'arami na kan gado yana bacci,ya k'arasa gurinsa ya shafa kansa tare da sakin ajiyar zuciya.

Har lokacin kallonsa take,ya zauna gefen gadon yana fad'in "kayi min afuwa d'ana raina ne a b'ace"

Tashi tayi da sauri ta k'arasa inda Abba k'arami yake tasa hannu zata d'auke shi ya rik'e hannunta, ta fuzge cikin b'acin rai tace "ka sakar min d'ana kada ka sake tab'ashi"

"Dan Allah ki saurare ni Janan"

"Babu abinda zaka fada min inji na tsanek...." Da sauri yasa hannu ya rufe bakinta sai kuma yayi saurin janyewa

"Kiyi hak'uri b'acin rai ne yasa na furta haka amma kimin afuwa ki gafarceni Janan"

'Daukar Abba k'arami ta fara shirin yi yayi saurin cewa "dakata Janan, bama sai kin fita ba ni zan fita"

Da ido ta bishi lokacin yana tafiya tamkar wanda k'wai ya fashewa a ciki"

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta fashe da wani kukan.

Yana fita ya tsaya a k'ofar d'akin tare da dafa bango,wata zuciyar tace masa _meyasa baka da zuciya Jalal?yarinyar ta tsaneka kana k'ara shige mata_

Wata zuciyar tace _lokaci yayi ta zaka rabu da ita ka fita a harkarta sai kace dole_

Da sauri ya bar gurin yana fad'in da zarar Amal tazo gidannan Janan zata daina ganin 32 d'ina zan nuna mata kuskurenta sai ta gwammace gara ta koma Kaduna da zaman gidannan.

Janan kuwa tasha kukanta ta gama ta bud'e side drawer ta d'akko magungunanta gaba d'aya tayi flushing d'insu cikin kuka tace "na kusa biyoka Adnan dan bana k'aunar duniyarnan sam bata min dad'i"

Kan gadon ta koma ta fashe da matsanancin kuka,Abba k'arami dake bacci ya bud'e ido ya kalleta tayi saurin rungume shi tare da tsayar da sautin kukan nata.

Da dare da aka kira su dinner bata fita ba ta tura Abba k'arami saboda ita bata son ganin Jalal sam.

Tana zaune a tsakiyar gado ta rafka uban tagumi Mommy ta turo k'ofar ta shigo.

Stool ta janyo ta zauna ta kafe Janan da ido,shiru janan tayi dan ta san Mommy baya wuce tayi mata fad'a akan yawan kukan da take yi.

"Janan wai Jalal zai iyayin Aure kusan shekara ban sani ba"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleta kafin tayi magana Mommy ta sake cewa "tsabar wulak'anci sai dai kawai ya kira abokinsa suna bani hak'uri wai a gobe zata tare kuma har ya sanar wa iyayenta hakan"

"Mommy......" Turo k'ofar da aka yi ne ya katse mata maganar da zata yi.

Jalal ne ya shigo fuskarsa d'auke da damuwa ya durk'usa gaban Mommy yace "dan Allah kiyi hak'uri Mommy na rok'eki ki yafe min kiyi hak'uri na san nayi kuskure"

"Ba kuskure bane Jalal son zuciya ne saboda na fad'a maka tun a farko ban yarda ka auri yarinyar nan ba amma ashe ka zagaye ka tafi kayi aure ka nuna ban isa da kai ba tunda har kana da wasu iyayen bayan ni sai kaje ka sanar dasu matar da suka aura maka gobe zata tare"

"Kiyi hak'uri dan Allah Mommy"

"Ka b'ace min daga nan Jalal"

"Mommy wallahi tausayine yasa na aikata haka bada saninki ba"

"Me kake so in fad'awa dangina dana mahaifinku?" Ta fad'a da k'arfi cike da b'acin rai.

"Nayi musu text na basu hak'uri"

"Kiyi hak'uri Mommy" Janan ta fad'a tana sakkowa daga kan gadon

"Kema bayanshi kike bi?"

Kallon Jalal tayi tace "ka sani koda matarka tazo babu ruwana daku,ban hanaka ba ga part d'inka can,idan ma a cikin gidajenka na waje ne duk wanda kayi ya wadatar amma ka sani bani bace surukarta ban san kayi Aure ba dan haka karka tunkareni da matarka"
Da sauri ta tashi ta fita.

Duk Kansu sunyi cirko-cirko a tsaye,Jalal ya kalli Janan yace "ki taimakeni ki saka baki Janan"

Shiru tayi kawai tana kallon yanda ya rud'e cike da tsantsar tashin hankali.

"Amma..."
"Karki tsaya tone-tone Janan ki taimakeni Mommy na san zata karb'i hak'urinki.

Kai ta d'aga ta fita da sauri yabi bayanta,a falo ya zauna ya dafe kai Saif na k'ara bashi hak'uri.

Kusan awarsu uku a d'akin Mommy amma tak'i kulasu har Janan d'in,da taga sun dameta kawai taja blanket ta rufe jikinta har kai.

Tashi sukayi jiki a sanyaye suka fita.

" ki daure aje d'aukar Amarya dake pls" wuce wa yayi side d'insa a zuciyarta tace _gaskiya Jalal ya raina min wayo_.


*_Washe gari_*

Tunda ta fara jera kayan break fast a dining take kallon side d'in Jalal amma bata ga fitowarsa ba,kawai ji tayi tana son ganinsa,har ta gama komai taje d'akin Mommy ta sanar mata ta gama shirya komai.

Har sun zauna sun fara karyawa Mommy na bawa Abba k'arami ruwan tea Janan taji bazata iya jurewa ba tace "Mommy ko dai Jalal baya nan"

"Oho masa waya sani" ta bata amsa ba tare da ta kalleta ba.

"Amma karfa Fushin da kike masa ne yasa ya fita bai ci komai ba"

"Kin damu da rashin karyawarsa?"

Shiru tayi saboda tambayar ta mata tsauri.

"Baki bani amsa ba Janan" Mommy ta kafeta da ido,kanta a k'asa tace "a'a Mommy bana son Fushin da kike masa kuskure ne ya aikata dan Allah kiyi masa hak'uri"

"Babban kuskure shine ya kawo ta cikin gidan nan,dan haka dole ya saketa yau d'innan"

Zare idanu Janan tayi tana mamakin kalaman Mommy.

"Mommy kiyi masa afuwa dan Allah"

"Jalal yana da tarbiyya bazan so d'ana ya auri wannan yarinyar da tagama lalacewa a waje,ina son jikokina su kasance daga uwa tagari"

"Mommy....."
"Karki b'oye min komai Janan dan na san yarinyar an fad'a min halayenta kaf,kuma kema kin sani"

"Zata iya yuwuwa sharri ne Mommy"

"Janan bazan yanke hukunci akan abinda ban sani ba,bana son na rasa Jalal kamar yadda na rasa Adnan"

Ganin hawaye a idon Mommy yasa Janan ta k'ara rud'ewa.

Itama hawayen ne suka sauka a idonta a zuciyarta tace _tabbas na cuci kaina na sakawa kaina cutar da ba wanda zaiyi k'aunar zama dani a matsayin mata,meyasa nayi watsi da magani na tabbas nayi kuskure gara in zauna da cutar in rok'arwa kaina da mijina gafara kafin in mutu amma idan na yadda saboda in mutu tabbas zan mutu kafira,zuwa asibiti ya kamani_.

Jin an dafa kafad'arta ne yasa ta d'ago kai ta kalli Mommy "Janan bana son rasashi dan Allah ki tayani rok'on Jalal karya kawo mana annoba ya saketa ya samu wata ya aura na yarda".

" zanyi iya k'ok'arina Mommy "

*********

Suna zaune suna hira sama-sama suka juyo hayaniya.

Mommy ta kalli Janan tace k'ila 'yan kawo kayane dan Allah karki barsu su shigo"


Da sauri ta tashi ta fita aikuwa ta gansu duk kansu manyan matane suna tsaye suna k'arewa gidan kallo.

"Sannunku fa"

"Yawwa sannu"

"Munzo jere ne ina ne part d'in Amal"

"Wace kuma Amal?"

Kallon-kallo suka farayi sannan wata tace "ba nan bane gidan Jalal?"

"Gidansu Jalal dai" Janan ta sake basu amsa.

"Mu dai nan akace zamu zo taya za'ace ba nan bane"

"Kinga baiwar Allah ni ce fa k'anwar Jalal kuma mu ba mu san wata Amal ba"

"Wallahi nan ne gidan"

"Babu inda zaku shiga sai dai ku kira shi Jalal d'in ya baku tabbaci amma mu Jalal d'inmu baiyi wani Aure ba"

Ganin sun fara hayaniya yasa tayi saurin kiran maigadi.

"Idan bazasu shiga motarsu su fita ba,ka kira securities su fitar mana dasu"

Ai tuni suka fara zagi da hayaniya suna fad'in su ba matsiyata bane.

Komawa tayi ciki ta zaune tare dafad'in "wai jere suka zo"

"Naji hayaniyarku ai,kin sallamesu ko"

"Eh" ta fad'a tana murmushi.

Kusan minti talatin dan har sun kunna kallon kawai sukaji an turo k'ofar da k'arfi.

Dukkansu suka juya suka kalli k'ofar,Jalal ne ya shigo a fusace,yana k'arasowa ya wanke Janan da mari.
Mik'ewa tayi ita da Mommy tana shirin yin magana ya sake marinta.

A fusace Mommy ta k'araso gabanshi ta wankeshi da mari tare da ture shi da dukkan k'arfinta.

"Baka da hankali me tayi maka"

"Akan me zata hana 'yan jera har tana fad'in bata san wata Amal ba kuma dan wulak'anci ta kira maigadi ya fitar dasu"

"Ta fad'a d'in nina saka ta kuma wallahi ka sake dukanta zan d'auki mummunan hukunci akanka"

Har lokacin hannun Janan a kuncinta yake.

Hawaye a idonsa yace "haba Mommy"

"Jalal na baka umarnin ka saki yarinyar nan,in kuwa ta shigo gidannan tabbas bani ba kai sai dai ka canza uwa"

Zaiyi magana ta d'aga masa hannu alamun bata son jin abinda zai fad'a.











_Sadeey S Adam_✍🏻
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyahπŸ‘„_*



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```




58

Itama Janan idonta cike da hawaye ta rab'a ta wuce d'akin ta.

Cikin b'acin rai ya juya ya tafi yana huci.

Yana shiga mota ya kwanta bayan kujera .

"Lafiya dai?ya kukayi dasu?" Saif ya tambaya yana kallon fuskar Jalal.

"Marinta nayi"

"Wa?"

"Janan mana ai ita ta rikita komai"

"Haba Jalal kuma sai ka mareta,Janan ce fa yarinyar da har yanzu akwai soyayyarta a ranka"

Kallon Saif yayi yace "babu shi yanzu, ada na sota a yanzu babu ko d'igon Sonta a zuciyata"

"Sai dai idan ba'a fasa zuciyar taka ba amma na san tabbas akwai soyayyar Janan har yanzu a cikin ta dan dai babu yadda zakayi ne"

" Saifullah dan Allah ka daina yi min maganar ta"

"Na daina amma kasan baka kyauta ba,da d'anta fa amma har yanzu bata wuce mari a gurinka ba"

"Janan d'in nawa take?wallahi ko yanzu tayi rashin kunya zan daketa"

"Ko dan Adnan ai ka raga mata"

Jin haka ne ya saka shi yin shiru tare da dafe kanshi da yaji yana sara masa "Mommy tace wai in saki Amal idan ba haka ba babu ita babu ni,Saif na kasa tab'uka komai wallahi na rasa mafita"

"Cab akwai matsala"

"Wallahi kuwa"

Shiru sukayi na wasu lokutan sannan Saif ya buga sitiyari yace "na kamo bakin zaren"

"Ta ina kenan?"

"Mommy tana da sauk'in kai da hak'uri ka jinkirta tarewar Amal a k'ara lallab'a Mommy tukun"

"A'a Saif bazai yuwu ba,bana so iyayenta su d'aukemu k'ananun mutane dan haka zata tare kuma zan cigaba da bawa Mommy hak'uri"

"Jalal da Fushin Mommy gara suyi maka kallon k'aramin mutum"

"Babu abinda zai faru da yardar Allah"

"Shikenan Allah yasa"

"Ameen"

'K'arfe 5:30pm Janan taji gud'a ta window ta lek'a taga 'yan kawo Amarya ne tare da masu jeren,rufe labulen tayi tare da zaunawa kan gadon,wani kuka ne ya kubce mata ta tuno itama da yanzu haka za'a kawota gidannan.

Cikin awa da batafi uku ba 'yan jere suka tafi kasancewar part d'in akwai komai dan haka duk kayan maidawa sukayi sai wanda ba'a rasa ba suka jera.

Har Janan tayi bacci bataji motsin Mommy ba ta san itama tana can d'aki dan yau babu abinda aka jera na dinner kowa kai masa d'aki aka yi.

_Washe gari_

Tun safe tayi wanka ta shirya Abba k'arami ma sannan suka koma bacci.

Sha d'aya ta gota ta farka taga babu Abba k'arami ta tabbatar ko yana falo ko d'akin Mommy.

Toilet ta shiga tayi brush sannan ta saka hijab ta sauka k'asa dan taji k'ofar d'akin Mommy a kulle.

Tun daga nesa ta hango Amarya da Ango zaune sunsha shadda _Sea green color_ iri d'aya.

Har zata koma kawai taga sun had'a ido da Jalal.

Sakkowa ta k'arasa yi ba tare da ta kallesu tazo zata wuce kitchen.

"Ina kwana Aunty" Amal ta gaidata cikin girmamawa.

_wai Aunty ta girmeni amma tana d'irka min girman_ ta fad'a tana kallon Amal d'in sannan ta mayar da kallonta ga Jalal ta yatsina fuska ta wuce.

Canza akala tayi kawai ta fita farfajiyar gidan.

Kallon Amal yayi yace "kada ki sake gaidata tunda ai kin girmeta ba sa'arki bace,karki yarda kiyi abinda zata rainaki"

"Amma ai matar yayanka ce shiyasa"

"To tunda bata so dole ne" tashi yayi tayi saurin sak'ala hannunta cikin nashi muryarta a sanyaye tace "ko dai basu sona da kai,bani son had'aka da family d'inka"

Zaunar da ita yayi kan kujera yace "ki barni da Janan duk ita ce ta had'a komai,minti d'aya ina zuwa"
'Daga kai tayi idanunta cike da hawaye.

Yana fita tayi k'wafa tace "wallahi indai kikace dani zaki buga tabbas zaki sha wuya nayi alk'awarin sai naga bayanki tunda ke kike son rabani da mijina Janan,kafin ki aikata hakan ni zan fara rabaki dasu"
..


Tana zaune kan plastic chair ta d'ora hannunta a goshinta ya k'araso ya zauna kan kujerar dake facing d'inta.

"Meye matsalarki?"

'Dago kai tayi ta kalleshi..
"Lokacin da ka saki Raihan ka sanar min cewa duk abinda Mommy ke so shi kuke so kuma duk abinda bata so kuma baku k'aunarshi meyasa yanzu ka canza?ka auri matar da Mommy bata so kuma har kake tunanin ni ce nake had'a komai da zama da ita gara zama da Raihan dan ta sauya hali saidai kawai yanzu tana d'akinta kuma tana k'aunar aurenta da mijinta "

"Kece kika canza ni Janan,ke kika mayar dani haka"

Sakin baki tayi tana kallon sa cike da mamaki tace "taya ya zama ni,kuma na rasa me zan mayarka sai mara jin magana"

"Halinki ne na d'auka,saboda in nuna miki k'arfin so da ikonsa,ban tab'a ji ko furta Kalmar so ga kowa ba sai ke,na soki so mara misaltuwa amma Janan a gabana kika rik'a furta kalmar baki sona ke dama baki tab'a cewa kina sona ba, koda haka ne Janan bai kamata ki furta min ba, na danne sonki ne saboda farin cikin d'an uwana amma ba wai dan na daina sonki ba,sai yanzu dana samu son gaskiya na samu macen da nake so take sona sannan kike son rabamu,ko kuma so kike na aureki da cutar k'anjamau a jikinki ne? Kin san babu zancen maganar so tsakaninmu bayan kina tare da wannan cutar ko abinda nayi wa Abba k'arami dalilinki ne saboda kin tsaneni har kika bud'e baki kina ce masa wai ni ba daddynsa bane shi baya da uba yaron da baisan komai ba kika fad'awa haka,kika kirani maci amana kika nuna min k'iyayya k'arara Janan ko kina tunanin duk na manta ne yana nan a raina "

Mik'ewa yayi cikin b'acin rai ya nuna ta da yatsa,"ki fita daga sabgata da ta iyalina Janan idan ba haka ba wallahi zaki kwashi kashinki a hannunki domin yanzu babu wannan son da nake miki ina raga miki ne saboda har yanzu ina ganin fuskar Adnan a jikinki saboda tun a baya kince kinyi dana sanin sanina a rayuwarki karda nima kisa inyi taki" da sauri ya wuce ta fara murza ido dan ta tabbatar da ba mafarki take ba.

Yana shiga ta tashi itam ta shiga,a k'ofar falon taci karo dasu tana shirin shiga.

Handbag ta janyo ta bud'e ta saka kayanta kala uku a ciki,da sauri ta fito,maigadi ya bud'e mata k'aramar k'ofar ta fita.

Kai tsaye ta d'auki napep sukayi ciniki drop ya kaita tashar Kaduna.

A mota kuwa jan hijabi tayi ta rufe fuska tana hawaye.

Jin wayarta na ringing yasa ta d'ago ta kalli screen d'in,ganin sunan Jalal ya sakata danna switch ta kashe wayar duka.

Har aka isa Kaduna sannan ta bud'e fuskarta.

Haka ta d'auki drop har gida.

Da sallama ta shiga falon gidan Mameey da Fahad suna zaune,yadda taga ran Mameey a had'e yasa ta sha jinin jikinta.

"Mameey ina yini"

"Daga ina kike?"

"Abuja"

"Me kika zo nan kiyi kuma da iznin wa?"

Shiru tayi ba tare da tace komai ba,

"ki tashi ki koma yanzu-yanzu"

Kallonta tayi tace "Mameey........"
"Kiyi min shiru ki tashi ki koma nace"

Hawaye ne ya sauka a idanunta ta kalli Mameey tace "dan Allah ki tsaya ki saurareni"

"Mameey kiyi mata hak'urin zuwa gobe tunda tasha hanya gashi motar haya" Fahad ya fad'a yana kallon Mameey.

"Fahad nina haifi Janan ba ita ta haifeni ba dan taga duk abinda take so ana yi mata shiyasa take abinda taga dama,to idan taurin kai take ji yau zan gwada mata irin nawa taurin kan,yadda tazo a motar haya haka zata koma a cikinta babu driver da zan bawa mota ya maida ita"
Tashi tayi ta bar falon.

Janan ta k'ara fashewa da kuka.

"Sai kiyi hak'uri ki tashi ki tafi kina dai gani ranta a b'ace sosai ya kamata ki sauya janan kin zama babba fa har da d'anki kusan shekara hud'u"

Idonta ta rutse tana ji Fahad yabi ta gefen ta ya wuce.

Kusan minti talatin tana kuka a wajen babu wanda yazo inda take bare ya rarrasheta dan ko motsin 'yan aikin bata ji ba bare suzo su bata hak'uri.

Tashi tayi ta rataya jakarta ta fita.

Napep ta k'ara tara zuwa k'auyen kangire.

A daidai k'ofar gidan da tayi rayuwa mai napep ya tsaya, tayi mamaki ganin rabin gidan ya zube.

Tana saka k'afarta taji gabanta ya fad'i,innalillahi wa inna'ilaihi raji'un ta karanto sau uku sannan ta shiga ciki.

Da sallama ta shiga tsakar gidan.
Zuhra ce ta lek'o daga d'akin,ganin

Please Login or Register in order to submit comment