You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har Hisham duk idanunsu sunyo waje.

"Maganar k'anwarka gaskiya ne amma maganar soyayya ita matar aurece"

Idanunta cike da hawaye ta rasa me zata ce masa ma.

Da sauri ta ruga ta fita tana kuka shi kuma Jalal ya k'arasa gabansa ya dafa kafad'arsa.

"Kayi hak'uri kasan su mata sunada raunanniyar zuciya shiyasa"

"Kayi hak'uri wallahi sam bansan ita d'in matar aure bace"

"Karka damu ni nayi maka uzuri"

"Nagode"

'Bangaren Janan kuwa tana zuwa bakin d'akin ta goge hawayen ta yadda baza'a gane tayi kuka ba.

Koda ta shiga ta tarar da Mameey zaune kan sallaya tana lazumi Salima kuwa bacci take an saka mata drip.

Toilet ta shiga tayi alwallah ta fito ta tayar da sallah.

Kafin ta idar Jalal ya shigo ya zauna suka fara hira da Mameey, koda ta idar ranta ta k'ara had'ewa wa ba ta ko tanka masa ba.









_Sadeey_✍🏻
[3/5, 11:43 PM] β€ͺ+234 803 254 3874‬: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



*_by SaNaz deeyah_*πŸ‘„



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



62

Murmushi yake yana latsa waya yayinda taji zuciyarta tamkar ana tafasa ta.

"Mameey dama Mommy ce tace tana son idan zan tafi gobe in tafi da Janan" Ya fad'a lokacin daya sunkuya tamkar yana bara.

"A'a Mameey" Janan tayi maganar da sauri

"Oh k'arya nayi kenan?"

"Ni bance ba amma ka fad'a ba daidai ba"

"Ai dama kin dad'e a Kaduna ya kamata ki koma haka ga d'a kin bar mata"

"Amma munyi waya da Mommy nace sai next week zan koma"

"A'a kije gida ki shirya ku tafi goben in Allah ya kaimu tunda tana son ganin ki"

"Mameey kinga halin da Salima ke ciki fa kuma ace in tafi in barta"

"Amma ai ina nan,dan haka ki tattara ku tafi idan yaso duk abinda ake ciki zamuyi waya"

Zata sake yin magana Mameey ta katseta da fad'in "ki bi umarni na Janan"

Kamar zatayi kuka haka ta amsa wa Mameey.

Ranar kuwa Mameey ta kwana a asibiti su suka tafi gida,saida suka biya ta d'ebo kayanta a hotel tayi sign out sannan suka wuce gida.

_Washe gari_

Da shirin tafiya sukazo asibiti, sun d'an zauna kusan minti talatin sannan sukayi sallama suka tafi.

Suna hanya ya fara k'yalk'yalewa da dariya har yana bugun sitiyari.

Hawaye cike da idonta dan ta tsani kayi mata dariya idan ranta a b'ace yake.

"Kin d'auka zakici bulus ne?har kina tunanin fara soyayya bayan ni kin hana min zaman lafiya a gida to bari kiji matuk'ar bazaki gyara tsakanin Mommy da Amal ba tabbas kema zaki rik'a had'uwa da b'acin raina"

Cikin b'acin rai ta kalleshi tace "oh akan wannan 'yar iskar yarinya kake min haka?"

Wani wawan mari ya sakar mata ya saki sitiyarin yana k'ok'arin kai hannu jikinta yaji ana salati sannan ya tuna tuk'i yake ya cigaba da yi
"Ni kike cewa matata 'yar iska to bari muje gida sai na tabbatar miki dani tantirine"

Hannunta rik'e da kumatu tace "yo na nawa ai ka tabbatar min hakan tunda babu wuya ka kai hannunka ga kuncina to wallahi indai ina raye sai Amal ta bar gidanka bazaka zauna da ita ba dan baku dace ba,Kaine giyar so ta d'auke ka har ka kasa fahimtar ita d'in wacece"

"Oh bakinki bazaiyi shiru ba ko Janan? Bazaki daina aibunta ta ba ko?"

"Bazan daina ba wallahi Jalal indai ina raye Amal dole ta rabu da kai dan bazamu yarda kana zama da k'azama kamarta ba"

"Ya wuce ke da muka zauna dake da cutarki har kike kiran wani k'azami"

Jin furucin ne yasa tayi shiru bakinta a sake tana hawaye,wai ita Jalal keda gori akan ciwon da a jikin yayansa yake.

Tana hawaye tace "wannan shine banbancinku da Adnan" ta goge hawayen idanunta "Allah yayiwa Adnan rahama shine masoyina na gaskiya dan kome nayi masa bazai tab'a wulak'antani ba"

Cikin b'acin rai yace "dama taya zamu zama d'aya bayan ba tare aka haifemu ba kuma ba sunanmu d'aya ba"

Shiru kawai tayi ta kwanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana hawaye.

Har suka isa Abuja babu wanda ya sake yi ma wani magana.

A falo suka tarar da Mommy da sauri Janan ta k'arasa gurinta Mommy ta rungumeta cikin jindad'in ganinta
"Kika ce sai next week"

"Eh Mameey ce tace sai na dawo yau d'in"

"To Masha Allah kije ki wanka sai kizo kici abinci,Abba k'arami ya tafi islamiyya sai six Asabe zata d'akko shi"

Da sauri ta wuce d'akin ta dan ta watsa ruwa.

Jalal kuwa yana shigowa suna gaisawa da Mommy yaga ba fuska ya wuce part d'insa.

A kwance ya tarar da Amal d'in idanunta sunyi jajir alamun taci kuka ta k'oshi tana ganin shi ta mik'e tsaye a tsorace.

"Matana lafiya?meke faruwa ne?"

Hannunsa ta rik'e gam tana fuskantarshi tace "me Mommy tace maka a kaina?"

"Babu komai kawai naga kamar ranta a b'ace shiyasa ban zauna ba na taho"

Hannunsa ta saki ta zauna gefen gadon ta dafe goshinta.
Zama yayi kusa da ita ya janyo ta jikinshi yace "me Mommy ta fad'a miki da ya sakaki kuka?"

"Tana son rabani da kaine"

"Akan me?"

"Babu dalili amma ina son ka tabbatar min da cewa kana sona"

"Ina matuk'ar k'aunarki"

"Ka tabbatar?"
"Tabbas"
"Indai haka ne ina son mu gudu mu bar Nigeria zuwa lokacin da mahaifiyarka zata fara sona ko kuma idan mun haihu sai mu dawo"

"Me?guduwa?ina bazai yuwu ba"

Tashi yayi yana k'ok'arin fita ta sha gabansa "dan Allah ka saurareni Jalal wannan itace kad'ai alfarmar da zaka min hakan zaisa in tabbatar da kana sona"


"Bazai yuwu ba Amal,Mommy na sonki sannan ni kad'ai na rage mata a duniya dan haka bazan iya yin nesa da ita ba,kinji na fad'a miki"

Da sauri ya fice ya barta anan tsaye.


Da yamma kuwa a waya Mommy ta kirashi tace ya sameta a babban falon shi da matarshi.

Amal najin sak'on Mommy gabanta ya fad'i ta rik'a addu'a Allah yasa kar Mommy ta tona mata asiri kamar yadda ta fad'a.

Suna isa falon kuwa suka zube k'asan carpet, Janan dake zaune kan kujera Mommy tace da ita "Janan mik'o min jakata akan mirrow na ajjeta"

Tashi tayi ta shiga ciki Jalal ya bita da kallo cike da jin haushinta.

Tana mik'awa Mommy jakar itama ta zauna a k'asa.

Memo da pen ta fiddo ta wullawa Jalal tace "ba shawara zan baka ba umarni ne,inaso ka auri Janan ko kuma ka saki wannan matar taka,bawai saki d'aya ko biyu ba saki uku"

Duk a tsorace suka kalli Mommy ita kanta Janan batayi tunanin Mommy zata ce wai Jalal ya aureta.

"Mommy ban fahimceki ba?" Jalal ya fad'a a rud'e.

Mik'ewa Mommy tayi tsaye tana d'an tafiya tace "ka gane me nake nufi Jalal sai dai neman k'arfin bayani"

Amal kanta na k'asa tana hawaye.

"Ina nufin ka saki Amal ba saki d'aya ko biyu ba uku nake nufi ko kuma ka auri Janan bawai ka aureta ka ajjeta tamkar photo a gidan ka inaso inga jikana ta hanyarta sai ka zab'a"

"Mommy me tayi Amal tayi miki ne?tana sonki amma kin kasa fahimtar haka"

"Ni kuma bana sonta ma'ana bana son ganinta a matsayin matarka dan haka dole ku rabu"

"Mommy meyasa haka?haka fa kika sa na saki Raihan yanzu kuma kina son ki sa na saki Amal gaskiya kiyi hak'uri bazan iya ba akan me?"

"Ni kake wa wannan kalamin Jalal?"

Mommy tayi maganar tana rai a b'ace.

Da sauri Janan ta mik'e tsaye ta kalli Jalal tace "akan wannan fasik'ar kake saka mahaifiyarka kuka?"

Tashi yayi tsaye cikin b'acin rai yace "idan kika sake ce mata fasik'a na rantse da Allah saina tattakaki a gidannan"

"Na fad'a fasik'a dan bata tsoron Allah ko kad'an"

Wani wawan mari ya kai mata sannan yasa k'afa ya tad'iyeta ta fad'i

'Kara ta saki Mommy tayi saurin rik'ota,runtse ido tayi cikin azabar rad'ad'in inda ta fad'i.

"Jalal ni kayi wa haka akan zab'in dana baka ko?to kaje kai da matarka amma ka sani babu abinda zai k'ara shiga tsakanina da kai"

Tsayawa yayi cak,har Mommy ta kama Janan tana d'angyashi sukayi d'aki ya kasa motsi daga inda yake.

"Na shiga uku ni Amal ina zan saka kaina,Jalal na jawo maka matsala"

Zama yayi kan kujera ya dafe kai yana tunanin me yayi wa Mommy da take masa haka ne?.
*****
Sati guda babu abinda ke had'ashi da Mommy ko ya gaisheta ma bata amsawa,Abba k'arami kuwa sam baya zuwa inda suke gaba d'aya rayuwar tayi masa zafi.

Janan kuwa ta bugama Mameey waya akan jikin Salima Mameey ta sanar da ita cewa iyayenta sunzo sun mata cin mutumci dan haka ma sukayi baran-baran amma dai Salima ta d'an samu sauk'i dan bama ta sake sanin komai daga gareta ba,tace kuma bata son Janan ta sake neman Salima dan bata ji dad'in abinda mahaifinta yayi mata ba.
Ita kanta Janan taji babu dad'i ta bawa Mameey hak'uri sosai dan tana ganin kamar ita ta ja mata.

Yau kuwa da safe suna break fast Jalal ya shigo.

Mommy ya gaida bata amsa ba kamar yadda ta saba sharesa.

Janan ta gaidasa ya amsa mata ciki-ciki

Jan kujera d'aya yayi ya zauna "Mommy nazo muyi magana dake"

"To ai ina saurarenka"

Shiru ya d'anyi kafin yace "Mommy dan Allah me nayi miki?a cikin shekaru da basu gaza biyar ba ace na saki mata biyu?Mommy ki fad'amin laifina domin na samu damar gyarawa"

"Laifinka shine rashin bincike kafin kayi aure hakan ne yasa har yanzu bakayi dace da mace ta gari ba"

"Mommy meye laifin Amal?wallahi tana min biyayya tana k'aunarki bata tab'a sab'amin ba"

"Oh wannan shine dace?"

Shiru yayi baice komai ba.
"Jalal ka tashi ka fita bana k'aunar jin magana indai akan matarka ne,tun farko sai da nace karka aureta amma sai da kayi auren sirri da ita yanzu nace ka saketa kak'i,to tunda hakane abin sai kaji da matarka ka k'yaleni kawai"

"Kiyi hak'uri Mommy na amince zan auri Janan amma".....

"Amma me?"

"Kin san fa halin da take ciki Mommy"

"Ka iya zama da Amal bare Janan ni dai ai zab'i na baka"

"Mommy kinfi so nima ki rasani kenan kamar yadda kika rasa d'an uwa na?"

"Jalal ba fa dole nayi maka ba dan haka ka zab'a in kuma ba wannan ya kawo ka ba to fece"

Idanuwansa cike da hawaye yace "na amince zan auri Janan"

Murmushin jindad'i Mommy tayi tace "na saka bikinku nan da kwana biyar za'a d'aura aure bayan sallar juma'a"

"Amma Mommy........."
"Kiyi min shiru Janan" ta tari numfashinta.

"Ban yarda kowa ya san da aurennan ba har sai an d'aura ina nufin kar 'yan Kaduna su sani,na fad'a muku" tashi tayi rai a b'ace ta bar dinning area.

Tsoki Jalal yayi sannan ya kalleta yace "ba dai ta nan kika b'illo ba wallahi kin tashan wahala a hannuna har sai kince da kanki zaki rabu dani" ya tafi da sauri ya bar part d'in.

Kai Janan ta dafa tana kuka.
"Zuciyata dan Allah ki fad'a min gaskiya shin dagaske Jalal ne ke min wannan furucin?shin Jalal d'in nan ne na baya da ya soni so mara misaltuwa?na kasa gaskata hakan"

Kuka sosai tayi a gurin ta tashi ta nufi d'akin ta kanta na matuk'ar sarawa haka ta kwanta akan gadon wasu zafafan hawaye suka sake zubowa "meyasa ka rasu?haba mutuwa meyasa zaki d'aukemin Salma na san bazan tab'a samun masoyi kamar shi ba gaskiya Aliyu yayi min babban tabo"

Ranar har tayi sallar isha'i tana hawaye.

Tana zaune kan Sallaya Abba k'arami ya shigo da gudu ya fad'a kanta.

"Ammi"
"Ya akayi ne babana?" Shiru yayi ya d'akko wayarta yace "Ammi game"

Kunna masa game tayi sannan tace ya hau kan gadon yayi,aikuwa yana hawa bai dad'e ba yayi bacci.

Tashi tayi ta gyara masa kwanciya taja blanket ta rufe sa.

Wayarta ta janyo ta kira Fauziyya suka sha hira sosai.

Har k'arfe sha d'aya sannan ta kwanta...

Bacci ta nema ta rasa ta rasa wata irin macece Mommy, bata san cewa bata da cutar HIV ba amma tace zata aurawa d'anta,bata gudun ya samu ciwon shima,da wannan tunanin bacci ya d'auketa.

A b'angaren Jalal kuwa raba dare yayi yana ta nafiloli Allah yasa Mommy ta hak'ura da auren da take neman lak'a ba masa.

Yau saura kwana biyu a d'aura auren Janan da Jalal, tana zaune tana goge kayan Abba k'arami Mommy ta shigo.

"Yawwa Janan ina son kije ki cewa Jalal yazo ina neman sa na kira yak'i picking kuma na san yana gidan"

"To" ta fad'a tare da kashe socket d'in.

Tana tafiya gabanta na fad'uwa har ta isa part d'insu,knocking tayi ta tsaya tana jiran a bud'e,cikin sa'a kuwa shine ya bud'e k'ofar.
"Mommy na kiranka" ta fad'a sannan ta juya ta tafi.

Tana shiga ta sanarwa Mommy gashinan zuwa.
"Ki shirya zai kaiki unguwa ne"
"Unguwa kuma?"
"Eh zakuje ku had'o lefe"


"Mommy"
"Janan bana son musu"

Ranta bai so ba haka ta yafa mayafi ta zauna jiransa.

Yana zuwa Mommy ta sanar masa,bai ce mata komai ba ya tashi ya tafi
"Ka tafi baka ce komai ba"

"Ta sameni a cikin mota" ya fad'a cikin b'acin rai

"Ammi zan bi ki" Abba k'arami ya fad'a yana rik'e Janan.

"Ku tafi dashi Janan"
"To" kawai tace wannan ta tashi ta fita.

A cikin motar ta sameshi kamar ba'a tab'a halittar fara'a a fuskarshi ba.

Tana zama ya danna horn sannan ya tashi motar.

Babbar Super Market ya kaita ta zab'i duk wani abu da ya dace na cikin lefe,sai da ta sayi akwati takwas da k'atuwar Ghana must go wadda takalma da jaka za'a zuba a ciki.

Duk abinnan da ake yana cikin mota bai fita ba ATM kawai ya bata.

Wani wrist watch ta gani mai kyau na maza dan haka ta d'aukeshi da ban da niyyar zata bawa Jalal shi.

"Ammi nima" Abba k'arami ya yi maganar yana kai hannu kan wani wrist watch

"Babana lokacin kasa baiyi ba,bara na baka wannan kaji" wata Azurfa ta d'auka mai kyau ta kama hannunsa ta zura masa "wow yarona kayi kyau" murna ya fara yana tsalle.

Haka taje suka biya kud'in aka had'a kayan aka fitar dasu.

Daga mota Jalal ya fito ya kalli manya-manyan ledojin da akwatunan dake gefe yace "ke me kike nufi ne?"

"Kamarya kenan?"

"Kina nufin a cikin mota na zan tafi da duk kayan nan?"

"Eh mana,a saka wasu a booth wasu kuma a bayan seat"

"Cab lallai kin raina min hankali,su basu da mota da take kai kaya ne da zan d'ebi kayannan a motana"

Harararshi tayi duk da harara garkenta sai da ya gane hakan "oh harara ta kike?"

Banza tayi ta k'i yi masa magana ta fiddo waya "bara na kira Mommy sai ta turo driver"

"A'a,oh salon kisa tayi min fad'a?"

"Ah to ya kake so nayi idan ba haka ba"

Mtswww yayi tsoki sannan ya shiga cikin Plaza d'in.

Sai da suka jira har aka d'akko mota aka zuba kayan sannan aka bisu dasu.

A zuciyarta tace _Ashe kana da yadda zakayi amma kake raina min wayo._



Koda Mommy taga kayan ta yabawa Janan yadda ta iya had'a lefe kamar wata babba.

Haka tayi ta tsokanarta tana murmushi.

Ita ta jera komai a cikin akwatunan sannan ta ware guda uku da ban guda biyar da ban.

"Mommy wannan akwati uku dama na Amal ne na ware biyar d'in ne nawa"

"Akan wane dalili za'a bawa Amal?"

"Kayan fad'ar kishiya mana ya kamata a bata"

"Har akwati uku?"

"Eh Mommy"

"Idan za'a bata akwati uku meyasa bakiyi akwati 12 naki ba"

Murmushi tayi ta sake cewa "Mommy hakan ma yayi ai"

"Shin Addini ne yace ayi kayan fad'ar kishiya?"

"A'a"

"To baza'a kai mata ba"

"Mommy amma al'adar bahaushe ne wannan"

"Janan baza'a kai ba" ta fad'a sannan ta tashi ta shiga d'aki.

Da sauri Janan ta bita ta rik'a bita,
"Janan"
"na'am"
"Kenan kin bada goyon bayan Amal ta cigaba da zama a gidannan?"

"Mommy ina so ki kwantar da hankalinki dan Allah shima Jalal a sannu zai fahimci abinda ke b'oye,amma Mommy ina so ki barshi ya auri wata bani ba saboda ciwon dake jikina"

Murmushi tayi na tsawon 15 seconds sannan tace "Janan kenan,kinyi tunanin Mameey bata sanar dani komai ba?to na gano cewa baki da wata cuta sannan na kira doctor ya sanar min cewar 3 seconds ne ke amfani a jikin abinda mai Aids ya yanke dashi daga zarar ya wuce wannan seconds d'in to tabbas ciwon ya gushe a jikin abin,so lokacin da mukaje doctor yace mana 15mnts shiyasa muka rud'e kuma kin san bamu sake zuwa gwaji ba kawai kika fara amfani da maganin masu ciwon shiyasa hakan ta faru dake,amma ina son rayuwa da mace kamarki a matsayin suruka shiyasa na zab'i ki auri Jalal duk da Mameey tace tafi so ki auri wani bashi ba saboda bata so a shiga rayuwarshi dan tana ganin kamar kin cuceshi a baya"

Hawaye gaba d'aya sun b'ata mata fuska babu abinda take sai sharesu suna dad'a zubowa.

"Janan bana so Jalal ya gano hakan har sai ya gane kurensa karki sanar masa kinji"

"To Mommy amma nima ina neman alfarma a gurinki"

"Ki fad'i ko mene"

"Inaso ki bari akaiwa Amal kayan nan sannan kimin iznin zuwa gidan Hajar"

"Kano fa?"

"Eh"

"Ki bari sai bayan aurenki ki tambayi mijinki idan ya bari sai kiyi idan bai bari ba ki hak'ura"

"Ina son sanin cewa shin dagaske ne d'an gidan Adnan yana raye?"

Hmmm "ba gaskiya bane k'arya take,ai Jalal yaje har gidan nasu,sun bashi hak'uri sosai sannan sunzo nan neman gafarar abinda ya faru,kinga kuwa d'an Adnan tabbas ya rasu,sai dai kiyi ta Addu'a Allah yajik'ansu da rahama"

"Ameen" ta fad'a tana shashshek'ar kuka.

Asabe ta kira ta taya ta suka ja akwatin zuwa part d'in Amal.

Janan bata shiga ba tace Asaben ta kai tace inji Jalal.

************

Tana zaune kan kujera ta saka hannunta duka biyu a hab'a,da sallama ya shigo ta amsa tare da binshi da ido .

"Ya dai?ko na canza miki kamanni ne kike bina da ido babu ko oyoyo"

"Jalal ina tsoro gaskiya"

Yadda tayi maganar ya saka shi saurin kallonta k'arasawa gabanta yayi ya saka hannuwansa bisa kafad'unta yace "me kuma ya sake faruwa?"

"Ina ganin indai Janan ta shigo gidannan tabbas zamana dakai ya k'are saboda Mommy na matuk'ar k'aunarta kuma nima ina tsoron ta goga maka k'anjamau nima ka saka min" ta k'arasa maganar tana kuka

Sakinta yayi ya jingina da wardrobe tare da hard'e hannayensa "Janan sai ta bar gidannan da k'afarta kina tunanin zan zauna da ita a matsayin mata ne?kawai dai zan bi umarnin Mommy ne"

"Ga akwatuna an kawo min wai injika na fad'ar kishiya"

"Wa ya kawo?"

"Asabe ce"

A fusace ya juya zai fita ta rik'o hannunsa "a'a dan Allah karka je"

"Ki barni naje naji dalilin yin k'arya da sunana"

"A'a ni zaka jawowa fa bana son shiga wata matsalar ai dama ni na san ba kai bane dan Allah kayi hak'uri"

"Amal hak'urin da kike shine ke k'ara ja mana raini a idon Janan"

"Dan Allah ka zauna ka sanyawa zuciyarka Salama"

Zama yayi yana ta tsaki,da sauri ta d'akko ruwa a fridge mai sanyi ta siyaya a kofi ta bashi.

Gaba d'aya ya shanye ya dire kofin.

Ranar haka ya kwana cikin b'acin rai ita kuwa dama ta dad'e da daina baccin dad'i.

********

Yau aka d'aura auren Jalal da Janan wanda bayan waliyyanta da Mommy ce tasa aka samo mata malamai sai k'alilan mutane da suka halarci masallacin sune suka shaida auren,ba 'yan uwa Jalal ko d'aya bare na Janan.

Dubu goma ya bada a matsayin sadaki duk dan ya bak'anta mata amma ita murna tayi tace ai sadaki kad'an yafi albarka.

Part d'in ta da ban Jalal yace ta zauna Mommy kuwa tace sam bata yarda ba dole su zauna part d'aya,in yaso ko wacce ta zab'i bedrooms biyu.

Haka kuwa akayi,Jalal ji yayi tamkar zai had'iyi zuciya saboda b'acin rai.

Da zai fita daga part d'in Mommy kuwa cewa tayi "idan baka kwana a d'akin Janan ba ban yafe maka ba"

Ya tsorata sosai da jin furucin Mommy, yana fita ta rufe part d'in nata ta d'auki Abba k'arami ta kai bedroom sannan ta kira Mameey ta sanar da ita abinda ke faruwa.

Fad'a sosai tayi akan abinda Mommy tayi,a Daren kuwa ta kira 'yan uwa ta rik'a sanar musu tare da basu hak'uri haka Mommy ma tayi.

Jalal na shiga part d'insa ya tarar da Amal a tsaye a falo.

Daf ta ita ya tsaya ransa a b'ace yace "bana son kowa ya san nayi Aure"

Hawayene kwance a fuskarta yasa hannu ya goge mata yana fad'in "Mommy ta bani iznin kwana a d'akin Janan sannan tace in har ban aikata hakan ba to bata yafe min ba"

"Hakan na nufin........" Da sauri ya toshe bakinta ya girgiza kai.

"A'a babu abinda zai faru karki yarda ki saka zargi a ranki"

Da k'yar ya lallab'ata har sai da tayi bacci kusan k'arfe d'aya ya shiga d'akin Janan.

Bacci ma take abinta yaja pillow sannan ya kwanta akan sofa.

Tsakinshi da yayi yawa ya saka ta farka,a hankali take murza idanunta hatta ware su duka.

Ganin ya kunna light bai kashe ba ya saka tace "wai mene haka Jalal? Kafa san babu kyau kwana da gaske pls ka kashe mana gaskiya"

A fusace ya mik'e yace "bazan kashe ba ai ba d'akinki bane"

Dariya tayi tace "oh abin harda gori to bari kaji nan d'akina ne kuma alfarma ta yasa har zaka kwana cikinsa"

"Alfarmar mai k'anjamau?Allah ya kiyaye wallahi k'arya kike kece kike cin alfarma ta,kin rasa wanda zai aureki Mommy ta lik'amin ke, nayi dana sanin saninki a rayuwa"

Kalamansa sun mata zafi dan haka ta k'yaleshi ta kwanta kawai.

_A week later_

Wulak'anci dad'a k'aruwa yake tsakanin ta da Jalal tun abin na bata dariya har ya fara sakata kuka.

Bata fad'awa Mommy kuma bata nuna mata komai ba,gashi babu Abba k'arami dake d'auke mata kewa tunda su Mameey sukazo Fauziyya ta d'aukeshi tace zata kaishi gurin babanshi yayi sati biyu sannan yayi wata a gurinta kafin ta maidoshi Mommy kuwa bata hanasu ba tace dama ya dace a rik'a kaishi gurin babanshi tunda shi kad'ai ya mallaka a duniya.






_Sadeey_✍🏻
[3/5, 11:43 PM] β€ͺ+234 803 254 3874‬: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



*_by SaNaz deeyahπŸ‘„_*



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



63πŸ”š

Yau tana zaune a falo kan kujera tana chatting kawai taga an turo mata text kamar haka

_Yau d'in nan Amal zata fita gurin saurayinta,zasu had'u a wani babban hotel dake wajen garin Abuja zan turo miki sunan hotel d'in da number d'akin._

_wai ke duk ina kike sanin wannan details d'in?_

_hmmm ita d'in k'awata ce wadda bata iya b'oyemin sirrinta_

_meyasa kike tona mata?_

_Saboda nima ta tona nawa ana gaf da bikina ta sanarwa da wanda zan aura cewar ni lalatacciya ce,da yak'i yarda sai tace zata nuna masa zahir,sai da ta bari munje hotel bankwana da saurayina kawai ta kirashi yazo ya ganni haka ya fasa aurena kuma har yau ban k'ara samun wanda yace zai aure ba sai dai kawai ayi harka a wuce gurin shiyasa nima nakeson mijinta yaga irin cin amanar da take masa dan inda nice na auri namiji kamar Jalal bazan tab'a kula wani ba_

_Amma kina ganin zata yarda taje gurin wani bayan tana son Jalal?_

_sosaima ai wannan jiya ya dawo daga America kuma bata tab'a tsallake buk'atarsa dan kusan zance shiya fara lalatata_

_to shikenan zan jira ki_

_okay amma dan Allah kuzo tare da Jalal dan shine nake so yaga komai_

_zanyi k'ok'arin yin hakan_

Tana kashe data ta kunna TV ta fara kallo kawai sai gani tayi an canza tasha.

Murmushi kawai tayi sannan ta tashi tayi d'akin ta.

_Yamma_

"Mommy ina son ki kirashi dan Allah ki tambayeshi ina Amal taje"

"Ki barni dashi yau zaiga k'azantar da nake son ya fitar da ita ya kasa fahimta"

Wayar tashi ta kira ta saka a handsfree tana shiga ya d'aga "hello kana ina?"

"Gani nan a hanyar dawo wa gida"

"Okay ina Amal ta tafi ne? Naga fitarta tun d'azu kuma bata zo ko tace min Mommy zan fita ba"

"Eh taje gida ne Ummu ce ta kirata zata tayata aiki"

"Okay,to kazo zaka kaini unguwa"

"To Mommy gani nan zuwa"

Kallon Janan tayi tace "kinji fa k'aryar da tayi masa"

Hmmm! kawai Janan tace sannan tace "Mommy bara naje kar yazo in sake yin laifi"

"Okay ai ga room number da Address zan gane komai dan bazan bari kije ba"

Murmushi tayi sannan tace "to Mommy"

Tashi tayi ta tafi part d'in nata ta kwanta kan kujera tana tana tunanin halin da Amal ta saka Jalal.

Kamar daga sama haka ta ganshi a gabanta yana nishi kamar wani bijimin sa.

"Ah lafiya?"
Mari ya wanka mata a gigice ta mik'e tsaye rik'e da kuncinta
"Na tsaneki na tsaneki munafuka wadda ke had'a d'a da mahaifi"

"Jalal ni kake wa wannan furucin?abin harta kaimu ga haka"

"Nayi miki makirar mace kawai wa zai fad'awa Mommy wannan maganar idan ba ke ba wa zai san Amal taje gida"

"Eh tabbas nina fad'a mata" ta fad'i tana zare idanunta da babu ko hawaye a cikinsu.

Kalle kalle ya fara yi sai kuma yayi hanyar fita,har ya kai k'ofa ta fara kuka tana fad'in "ka dawo ka sake ni shine mafita Jalal na gaji wallahi dole

Please Login or Register in order to submit comment