You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Janan d'in wanda take masa kallon tuhuma.

Da sauri ta d'aga k'afa zata bar gurin ya rik'o hijabinta.

"Janan zan miki bayani"

Bincikewa tayi sannan ta wuce lab takai takardar ta dawo.

Ba kowa a d'akin kasancewar yau sadakar bakwai ta abokan Adnan da sukayi accident tare su Mommy suna can.

Kallon Adnan tayi ta zauna kusa da shi tana hawaye ta rik'o hannunsa tare da fad'in "dan Allah ka tashi kaji,ka tashi muyi rayuwarmu cikin aminci dan Allah Mijina"

Kanta ta d'ora a gadon tana kuka tunda aka kawoshi har yau bata tab'a ganin ya motsa koda fatar idonsa kwanansu bakwai kenan.

Tana nan zaune Jalal d'in ya shigo.

Ta d'ago idanunta ta kalleshi.

Zama yayi a gefe jikinshi a sanyaye.

"Ya jikin Adnan"

"Alhamdulillah" ta fad'a.

"Janan" ya kira sunanta da sassanyar murya.

Bata amsa ba kuma bata kalleshi ba.

Bai damu da hakan ba kawai ya fara bata labarin abinda ya faru tsakaninsu da Faisal.

Idonta cike da hawaye tace "kar kayi tunanin na zargeka a'a ko kad'an ba haka bane,kawai bana son ka shiga matsala ne"

"Kin damu dani kenan" yayi maganar a raunane.

'Dago kai tayi suka had'a ido tayi saurin sauke k'wayar idonta k'asa tace "dole in damu da kai saboda b'angare biyu kake,kana matsayin abokina wanda ya ceto rayuwata sannan kuma kai k'anin mijina ne kaga kuwa dole in damu da kai"

Shiru yayi ba tare da yace komai ba.

Su Mommy na zuwa yayi musu bayani tare suka je suka dubata yarinyar tamkar gawa.

Jinin Jalal aka d'iba aka saka mata kasancewar blood group d'insu d'aya.

Aikuwa gida ya tafi saboda jiri da ya rik'a d'ibarsa dan kwana biyu da d'aukar jininsa aka sawa Adnan yau gashi an sake d'auka.

*********

A k'ofar gidan ya tsaya kusan minti biyu bai shiga ba,wanda ya rakosa tuni ya tafi amma ya kasa shiga.

Cikin dakiya yayi sallama ya shiga,Zuhra na bakin murhu tana hura wuta Umma na kwance kan tabarma har lokacin ba'a yanke k'afar ba sai zugin azaba take mata,rashin abincin ci yafi damunsu wani lokacin sai Nura ne ke taimaka musu kud'in da Adnan ya basu kuwa tuni suka k'are a magungunan da aka d'ora Umma akai dan Allah ya jarabto mata hawan jini tamkar bazata rayu ba,Zuhra kuwa tsabar son da takewa Aliyu da kuma tausaya masa ne ya saka ta dawo garesu wani lokacin Malam yana sawa a kawo musu abinci mamanta kuwa tace wlh babu ruwanta da ita natsawar bata dawo gida ba.

"Sannunki"

Zuhra ta d'ago kai cikin rashin gane ko shi waye tace "yawwa sannu"

"Ali yana nan kuwa?"

"Eh ya shiga bayi"
Tana rufe baki sai gashi ya fito.

Butar dake hannunsa ya saki sannan ya damk'o wuyan Faisal.

"Sai na kashe ka Ashe kana raye ka kawo min annoba ka gudu wallahi sai na kasheka" duk wani k'arfinsa ya sake shi akan Faisal wanda ya kasa tab'uka komai.

Salati Zuhra keyi tare da fad'in ya sake shi dan Allah.

Ganin Aliyu na k'ok'arin yin kisan kai yasa ta fita da gudu ta kira mutane.

Da k'yar aka rabasu yana k'ara fad'in wallahi saiya kasheshi.

Da gudu Zuhra ta tafi gida ta sanarwa Malam abinda ke faruwa.

Tare suka taho ya jawosu dan sasanci.

Kuka sosai Aliyu yake yana bashi labarin abubuwan da Usman ya masa tun had'uwarsu har lokacin daya karb'i Babur d'insa ya gudu.

"Meyasa kai haka?kasan kuwa hak'k'in wanda aka kashe gaba d'aya ya rataya akanka saboda Kaine sanadi"

Shima Usman d'in kuka yake yana fad'in "tabbas nayi kuskure kuma bansan abin zai kai har haka ba,bayan sati d'aya da faruwar abin nazo garin naji abinda ya faru shiyasa nayi shawarar yin nesa da su tun kafin 'yan sanda su gano ni su kasheni,na yanke shawarar bazan sake dawowa ba na koma can lagos kusan shekara biyar sannan na dawo kano na cigaba da harkata"

Aliyu sai k'ok'arin kai masa duka yake Malam ya hana.

"Meya dawo da kai yanzu?" Malam ya sake tambayarshi.

"Nazo ne dan in nemi gafararsu saboda na tafka Babban kuskure kuma kullum da mafarkin abin nake rayuwa shiyasa na yanke hukunci in nemi gafarsu kafin in mik'a kaina ga hukuma,damu da oganmu ne muka hadu muka yiwa Ummi fyad'e"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Umma ta fad'a tana k'ok'arin tashi amma ta kasa.

Zaginshi kawai take tare da yi musu Allah ya isa.

Cikin zafin rai Aliyu ya janyo kujera 'yar zaune yayiwa Usman fashin kwakwai.

Anan ya fad'i ya suma Umma ma tuni ta suma.

A gigice Zuhra ta fito da waya tayi wa Ja'afar text dama har yanzu yana tuntub'arsu akan case d'in.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Malam ke nanatawa.

Dukkansu aka d'ebesu akayi asibitin cikin gari dasu.

_1 hour later_

Usman ya farka amma Umma har lokacin likitoci na kanta dan sunce dole ne a yanke k'afar.

"Kayi hak'uri Aliyu nayi amfani da son zuciya na cutar daku"

"Bazamu yafe ba meyasa ka tashi meyasa baka mutu ba" ya gigice a gurin yana neman kai masa naushi aka rirrik'e shi.

A b'angaren Umma kuwa itama bori take tana fad'in ya kashe min Ummi ta shine ashe"

"Umma kiyi hak'uri"

"Yaron nan ya cucemu ya rabamu da duk wani masoyanmu,Allah ya isa ban yafe ba"

Shak'uwa ta farayi a gigice Zuhra ta kira likita,Umma ko minti biyu bata k'ara ba ta rasu.

Jin ance Umma ta rasu ne Aliyu ya janyo k'arfen da ake saka drip ya fara makawa Usman da k'yar aka fitar da shi a haukace,yana ganin gawar Umma kuwa ya fad'in ya suma a gurin.

Ja'afar kuwa da sukazo lokacin Usman baya cikin hayyacinsa dan haka suka ce likitoci su tabbatar ya rayu.

Kwanan Usman uku a asibiti sannan ya dawo hayyacinsa,bayanin komai yayiwa Ja'afar na inda suke dan haka cikin dabara sukaje da daddare lokacin sun kamo wata yarinya suna shirin lalatata 'yan sanda sukaje suka lalata komai suka kuma cafko su.

Kwana biyu case d'in na gurin 'yan sanda sannan suka mik'asu kotu.

Iyayen yara ganin anata d'aga shari'a ne yasa suka fara zanga-zanga.

A k'arshe aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga,watansu d'aya a prison suna aikin wahala anan ma sai da suka so suyi kisa Usman kuwa tuni ya tuba yana ta istigfari sannan aka kashesu duka.

Ranar da aka kashesu kuwa aka sanarwa da Aliyu cewar an kashe yasha kuka sosai babu Baffa,ba hafsatu,ba Umma ba Ummi duk sanadin Usman wani k'aramin hauka yaso yi da k'yar aka shawo kansa.

Kallon Zuhra yayi cikin kuka yace "duk abinda Janan tayi banga laifinta ba Abba na yarda baka da laifi dan da Usman ya dawo da an sakeni".

Haka dai yayi ta kuka yana fad'o abubuwan da suka faru.

Zuhra hak'uri ta rik'a bashi tana kwantar masa da hankali.

Ya rungumeta yana fad'in " ke kad'ai ce gatana a yanzu sai d'ana bayan ku bani da kowa su baba idi da baba isa ba su damu dani ba babu wani nawa da ya damu dani a yanzu"

Itama kukan take tana k'ara bashi hak'uri.

***********

"Janan dan Allah kizo kiyi min wani taimako"

'Dago kai tayi ta kallesa tace "na me?"

"Yarinyar sai kuka take na rasa ya zanyi na rarrasheta"

Kallon Adnan take da yake kwance kusan wata d'aya da sati biyu amma babu abinda ya canza numfashi kawai yake tabbatar da cewar yana raye.

"Muje" ta fad'a tare da tashi tabi bayansa.

Tun daga k'ofar d'akin suke jiwo shashshek'ar kukanta.

Suna isa Janan ta k'ara sa gefen gadon tace "haba baiwar Allah meyayi zafi haka?"

Kuka ta cigaba da yi ba tare da tace komai ba.

"Kiyi mana magana mana"
Jalal ya fad'a.

"Ki fad'a mana dumuwarki kinji pls" janan ta sake yin magana.

"Na san na rasa masoyi sannan babu wanda zai k'ara yarda dani,na kasa fad'a muku waye iyayena saboda ina tsoron yadda zasu kalleni ga an kusa bikina har anyi baiko na san wanda zan aura ba zai amince ba"

"Karki damu babu wanda baisan k'addara ba"

"Wallahi ba zai aureni ba,dama baya sona yana ta wulak'antani yanzu yaji wannan abin daya sameni babu ta yadda za'ai ya aureni babu wani namiji da zai aureni a wannan yanayi shikenan na rasa masoyi meyasa ban mutu ba na rayu?idan har ban mutu aka sallameni wallahi saina kashe kaina" ta sake fashewa da kuka.


Karkice haka Amal na miki alk'awarin zan aureki in har wanda zaki aura yace ya fasa"

Kallon shi Janan tayi a d'an tsorace,shi kuma idanunsa suna kan Amal d'in.

"Ka daina fad'ar haka dan ka kwantar min hankali"

"Dagaske nake wlh"

Da sauri Janan ta juya ta bar d'akin.

Ya kalli k'ofar sannan ya zauna ya cigaba da kwantar mata da hankali.

_Anya Jalal bai samu matsalar kwakwalwa ba?Aure fa yarinyar da baima santa ba kuma yarinyar da aka illata,me ke samun Jalal?_

Rashin samun amsa ne yasa ta kwantar da kanta a kan gadon Adnan lokaci guda taji matsanancin sarawar kai.

Addu'a ta rik'ayi kafin bacci mai nauyi ya d'auketa a gun.











_Sadeey S. Adam✍_
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



53

"Yanzu ki samin number daddynki in sanar masa halin da kike ciki dan na san suna can hankalinsu a tashe"

Murmushi tayi sannan tace "ai Abbu idan ba gawa ta aka kai masa ba bazai nemeni ba Ummu ce zatayi ta tunanin ina na tafi ba dan Ummu zata shiga damuwa ba wallahi da bazan bayyana iyayena ba dan ina kunyar su ganni a haka"

"Ko da sun ganki babu abinda zai faru domin ai kowa yasan wannan k'addara ce"

"Banda iyayena domin ni sangartacciya ce ina iya barin gidanmu har na wata biyu ba tare da kowa ya damu da inda naje ba,a cewar Abbu ma ai ni 'yar hutu ce a barni inje in huta kawai,Mamana tana yin kuka dalilin rashin zamana a gida amma ina sanar da ita bazan tab'a d'ebo mata abin kunya ba shin idan taga haka me kake tunani?"
Ta fad'a tana goge hawayen daya zubo mata.

"Ina kike tafiya?mekika yi amma kin san abinda kike bai dace ba a matsayinki na 'ya mace"

Murmushi tayi mai d'auke da hawaye tace "kasan ina nake zuwa?"

Bai samu damar bata amsa ba ta cigaba da fad'in "ina zuwa k'auyika ina taimakar mutane marasa aikin yi da taimako na gyaran makarantun k'auye da suka lalace,wani lokacin na kan zauna dasu har gona nake binsu muyo itace,muci abinci tare,gaba d'aya rayuwata na karkata ta a can ina tausayawa rayuwar mutane marasa k'arfi wanda babana bai damu da hakan ba burinshi kawai mu zamo 'yan gata'yan hutu masu ilmi baya so sam ya taimakawa talaka hasalima in har aka zo maula ko neman taimako gidanmu ranar cikin b'acin rai yake yini,babana d'an kasuwa ne yana da arzik'i sosai amma arzik'insa bana talaka bane dan haka ni kuma sai na canza akalata da taimakon talakawa,duk tafiyar da nake a tunaninsa na tafi yawan shak'atawa ne bai damu da duk dad'ewar da zanyi ba in mun dad'e bamuyi waya ba na kance masa babu network sam a inda nake,Ummu kuwa ita kawai tayi tunanin yawon shashanci nake tafiya,wannan karon satina d'aya a k'auyen kawai naji ina son dawowa gida,har na shigo cikin Abuja Motana ta lalace sai ya nemi ya taimaka min ina shiga motansa ban k'ara tsintar kaina ba sai a wani d'aki ina ji ina gani su uku suka farr mini"

Runtse ido Jalal yayi jin tsigar jikinshi na tashi.

Cikin kuka ta cigaba da fad'in "a daren suka d'aukeni suka wullar a bakin titi,da Asuba d'aya daga cikin su ya dawo ban san dalili ba ni dai na ganeshi kuma na rok'eshi daya taimakeni"

Ajiyar zuciya Jalal yayi yace "komai yanzu ya k'are tunda an kashesu zasuje su girbi abinda suka shuka su kuma sauran Allah ya toni asirinsu"

"Ameen Yaya Jalal"

Duk sai yaji wani iri yau an kirashi da Yaya.

Kallonta yayi dududu bata wuce 22years ba.

_na dad'e banga jaruma gwarzuwar mace mai kamar maza ba kamar wagga d'iya,abubuwan da ta fad'a sun bani mamaki._

Wata zuciyar tace masa _Janan ma haka halinta yake uwa uba ta zab'i zama da direban gidansu fiya da daular mahaifinta,ta zab'i zama da talaka._

"Kin gama karatu?"
"A'a yanzu nakeyi ina cikin last year d'ina"

"Wane skul?"

"Base University ina karanta gynaecology"

"Kin kyauta ma mata Allah ya taimaka amma ki daure ki bani number daddy ko"

Karb'ar wayar tayi ta sa masa number sannan ta bashi.

Sau biyu yana kiran wayar ba'ayi picking ba.
"Kayi masa text kace Amal ce ba lafiya shiyasa ka kira dan shi in bai san number ba baya picking"

"Okay"
fara rubuta text d'in yayi kamar yadda ta fad'a.

"Amma a wane area kake?" Tayi masa tambayar tana murmushi.

"Ina Garki2 Sapale street"

"Okay ni kuma a Maitama nake"

Kafin yayi magana wayarsa ta fara ringing yana ganin number babanta yayi saurin d'agawa.

Waje ya fita yayi masa bayani sannan ya dawo.

"Me Abbu yace?" ta fad'a a d'an tsorace.

"Bai ce komai sai dai hankalinsa ya tashi sosai yanzu haka yace min yana airport yanzu ya sauka k'asar amma gashinan zuwa"

"Allah sarki Abbu yana k'aunata sosai amma matar gidanmu ta tsaneni"

Bai nemi ya sani ba dan ba huruminsa bane.

```Amal ba fara bace chocolate color ce da siririyar fuska mai d'auke da kyaun halitta uwa uba dimple daya k'ara fito da kyawunta tana da diri da kyaun sura sannan kallo d'aya zaka mata ka gane ita d'in 'yar hutu ce tana da kimanin shekaru 22 a duniya,ita kad'aice a gurin iyayenta mahaifinta yana matuk'ar k'aunarta kasancewa itace 'ya d'aya tilo a gurin second wife d'inshi itama daga nan bata sake haihuwa ba haka ma matarsa ta farko bata tab'a haihuwa ba sai 'ya'yan rik'o da ta d'akko su biyu mace da namiji suma sun addabi gidan da tsiwa dan sun girmi Amal d'in sosai,Namijin shine wanda aka mata baiko dashi sam baya Sonta amma ita tana mutuwar son shi saboda akwai addini da kamun kai rashin kunya ce dai yakanyiwa Maman Amal in har ta tab'a uwar rik'onsu.```


"Bara inje in dubo Janan ina tunanin ma Mommy sunzo"

"To amma dan Allah karka dad'e dan kar suzo baka nan,bazan iya tashi ba danaje na dubashi"

"Karki damu Allah ya baku lafiya"

"Ameen"

Yana shiga yaga ana shirin fita da Adnan Mommy da Janan sai kuka suke Abba k'arami ya tsura masu ido yana kallonsu ,Adam na gefen gadon Adnan.

"Doctor meke faruwa ne?"

"Zamuje ayi scanning kai kuma ka biyoni office"

Janan kukanta dake neman fitowa fili tayi saurin rufe baki ta fita da gudu.

Kan kujera ta zauna tare da saka kanta cikin gwiwa tana jan numfashi hawaye na k'ara zubowa a idonta.

Jalal kuwa bin doctor office d'in yayi Mommy da Adam suka wuce gurin scanning.

Yana fitowa daga office d'in yaga wucewar wani Babban mutum da securities d'insa wanda jikinsa ya bashi cewar mahaifin Amal ne.

Hango Janan da yayi a zaune kanta a kife ya sashi k'arasawa gurin.

Zama yayi gefenta tare da sakin ajiyar zuciya.

'Dago kanta tayi ta kalleshi idanunta sun k'ara juyewa sun kumbura tamkar tana hararar gefe.

"Meyasa baku fad'a min Adnan ya kamu da ciwon paralysis ba? meyasa kuka b'oye min Jalal ni fa matar shi ce"

"Kiyi hak'uri Janan bama son hankalinki ya tashi"

"Wa'iyazubillah na shiga uku ni Janan,me doctor yace?"

"Ya bamu shawarar a tafi dashi India ko Egypt suna da k'wararrun likitoci saboda tunda aka kawoshi nan munfi 5weeks amma babu wani sauyi,so yanzu na kira wani friend d'ina acan Egypt dan ayi booking kafin muje in Mommy tazo zan fad'a mata sai a fara processing na tafiya Visa ce babbar matsala amma tunda abune na ciwo insha Allahu bazamu sha wahala ba"

Bata ce komai ba sai hawaye da take ta faman gogewa yana k'ara zubowa.

"Bara ina zuwa" da sauri ya tashi yayi d'akin da aka kwantar da Amal.

Yana tura k'ofar ya hangota rungume da babanta tana ta kukan shagwab'a.

Jalal ya tsugunna har k'asa ya gaidashi shi kuma ya mik'a masa hannu.

Amal ta d'ago kai ta kalli Jalal tace "Abbu wannan shine ya taimaka min"

Godiya sosai yayi masa sannan ya mik'a masa compliment card yace ka sameni a office dan kana da babbar kyauta.

Murmushi Jalal yayi yace "karka damu nayi domin Allah bana buk'atar komai"

'Daga waya Abbu yayi ya kira Ummunta ya fad'a mata halin da ake ciki.

Aikuwa babu shiri sukazo lokacin Jalal baya cikin asibitin ya fita nemo masu Visa.

Da yamma ya dawo ya fara shiga yaga jikin Adnan yana nan dai kamar da.

'Kara kwantarwa dasu Mommy hankali yayi sannan ya nufi d'akin Amal ya dubota.

Yana tura k'ofar yaji guy d'in na fad'in "wallahi na rantse Abbu bazan auri Amal ba kaima kamar uba kake a gurina domin a gidanka na tashi kayi min adalci Abbu taya zan auri macen da har namiji ba d'aya ba yayi amfani da ita"

"Ni zan Aure ta" duk suka juyo suka kalleshi,Amal kuka kawai take.

Jalal ya k'arasa gaban Abbu yace "zan Aure ta domin Allah"

Haj Zinaru ta tashi tace "zaka iya aura mata shi tunda ta samu masoyi amma Hafiz daya san ko ita wacece taya zai aureta duk wanda yasan halin Amal ai bazai so aurenta ba ni saboda ban tab'a haihuwa ba sai ace d'an rik'on ma za'a masa dole,zanga irin son da kakewa Amal d'in da har zaka aura mata wanda baka sani ba"

"Kimin shiru Zinaru kin nuna min ban isa daku ba ban isa da Hafiz ba shikenan zan aura mata duk wanda yazo gareta matsawar ta amince domin bana son rayuwar Amal ta lalace har yanzu yarinyar nan tana bleeding dan haka zan fitar da ita waje a mata aiki amma saina d'aura aurenta a satin nan"

Ummu dai bata ce komai ba hawaye kawai take.

"Amal kin yarda zaki Aure shi"

Kai ta d'aga alamar eh.

Kallon Hafiz yayi yace "dama na dad'e da sanin baka k'aunar Amal ni ne dai nayi tunanin ba wanda zata aura taji dad'i kamarka"

Ya kalli Jalal yace "kana da number ta ka turo waliyinka muyi magana a guest house d'ina gobe,jibi nake son a d'aura aurenta da kai sannan a shirya fita da ita saboda magani"

"Babu damuwa zan turo gobe da yardar Allah"

Tashi yayi ya fita zuwa d'akin Adnan ganinsu a zaune suna hira yasa hankalinsa ya d'an kwanta.

Zama yayi gefen gadon yace "lafiya ta samu tunda har kuke hira"

"Dole ai munga ya bud'e ido fa shiyasa hankalinmu ya d'an kwanta"

"Dagaske ya bud'e ido?"

"Wallahi ya bud'e amma dai baya cikin hayyacinsa"

"Amma naji dad'i"

Hirar ya zauna anayi dashi,a haka ya samu damar fad'awa Mommy yadda sukayi da Abbu.

"Jalal" ta kira sunanshi kanta a k'asa.

Gabanshi ba k'aramin fad'uwa yayi ba da k'yar ya amsa.

Ta d'ago kai tace "Ban san baka da hankali ba sai yanzu,kawai daga taimako sai a b'ige da Aure ko an fad'a maka aure wasa ne,idan gaskiya ne abin ya turata ayi mata aikin tare da mahaifiyarta mana sai da kai dole"

"Mommy saboda yanayin halin da ta shiga"

"K'arya ne d'an uwanta wanda suka tashi tare ma ya k'ita sai kai,ban lamunta ba kuma ban amince ba"

"Amma...." tayi saurin tarar numfashinsa da "ka fitar min a ido Jalal ka fice ka bani guri"

Ranta a b'ace shima nasa a b'ace yayi saurin fita.

Da sauri Janan ta tashi ta bishi.

A jikin bango ta tarar dashi ya d'aga kanshi sama.

"Kana da saurin yarda wallahi"

'Dago kan yayi ya kalleta ba tare da yayi magana ba.

Uhmm "mu dai bamu amince ka auri wadda bamu san tushenta ba" d'aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya tsaya,gaba d'aya idanunta sun fito waje kallonshi take cike da mamaki.

Da yatsa ya nuna ta yace "ina ruwanki,wallahi idan kika k'ara shiga sabgata sai ranki yayi mummunan b'aci ke har kin san wani tushe,ko sanin tushen ne yasa kika auri direban gidanku ke baki ma san ciwon kanki ba bare na wani,aurene babu fashi saina aureta ki bar Mommy tayi magana bake figaggiyar kaza cikon benci ba"

Har ya wuce zai tafi ya dawo ya sake cewa "sa'arki d'aya kina auren masoyina kuma yayana wallahi yau da saina sake sauke yatsuna a fuskarki kada ki sake shiga harkata na fad'a miki ba ruwanki dani"

"Bazan sake shiga ba da yardar Allah"

"In har kinada zuciyar ba" ya sake fad'a.

"Zan nuna maka ina da ita"

Kallon sama da k'asa yayi mata ya tab'e baki ya wuce.

Da ido ta bishi har sai daya b'ace sannan ta fashe da kuka.

Sai da ta share hawayenta sannan ta koma d'aki tare da alk'awarin ko magana bazata k'ara had'ata dashi ba,zata ja baya dashi.











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



54

Ya kasa zama guri d'aya ya zauna ya tashi duk abin duniya ya ishesa.

"Mommy meyasa zaki hanani yin abin alkhairi?"

Dafe kai yayi yana tunanin mafita.

Can yayi murmushi ya d'auki wayarsa yayi dialing number Saifuddeen ringing d'aya ya d'aga.

Gaisawa suka yi tare da jajen kwana biyu basu had'u ba.

Babu wani jinkira ya bashi labarin komai.

Daga d'ayan b'angaren Saifuddeen yayi murmushi yace "haba kai kuwa meye na d'aga hankalinka bayan akwai iyayen bogi kawai su za'a biya suje"

"Amma Saif kasan babu wanda baisan Mahaifina ba"

"Kuma babu wanda bai san ya rasu ba kawai ka sakasu a matsayin uncles d'in ka ne"

"To kana ganin har nawa za'a basu?"

"Bari yanzu zan fita idan na nemosu aka yi ciniki sai na kira ka ka tura ta account kaga goben sai muzo Abuja tare dan nima jiya na dawo Kaduna"

"Okay ba matsala nagode"

Katse wayar yayi ya zauna gefen gado tare da dafe kai a zuciyar sa yace _Amma nayiwa Mommy adalci kuwa?ta hanani yin abu nayi,ko dan na san Mommy nada fahimta idan komai ya lafa suka dawo da Amal daga can muma lokacin mun dawo daga Egypt na san Mommy baza tace komai ba dan tana da hak'uri._

_Janan fa shin ka mata adalci wulak'ancin da kai mata d'azu?_ wata zuciyar ta sake hangod'o masa question.

Ajiyar zuciya yayi a fili yace "gaskiya ban kyauta amma itama ai bai kamata tamin wannan furucin ba"

Wani irin ba dad'i yaji jikinsa a sanyaye ya tashi ya figi motarsa zuwa asibitin.

**********

Kallonta tayi rai a b'ace tace "dalla malama in zaki saki ranki ki saki haba Najwa kefa ba yarinya bace,shikenan d'an abu k'ank'ani ya d'aga miki hankali"

Kallonta Najwa tayi tace "lallai Preety kece kike ganin abin kamar wasa amma banga laifinki ba tunda baki san zafin so ba"

Dariya sosai Saudat tayi tace "ina zansan zafin so tunda ban d'orawa kaina wahala ba,ni samarin ma wasi nake dasu in naga dama"

"Ke kika d'auki so a matsayin wahala saboda ke baki san so ba baki tab'a yin soyayya ba"

"Kina nufin duk tarin samarin da nake dasu ba sonsu nake ba kuma suma basa sona?"

"Ba haka nake nufi ba ina nufin har yanzu ke da samarin naki wasa kuke ko kuma yaudarar juna,so d'aya ne kuma Jalal nakewa nawa idan har bazaki taimaka min ba to ki daina rab'ata"

Dafata tayi tace "me yayi zagi haka,kiyi hak'uri k'awata kinsan wannan shine abinda ya kawo ni gidannan saboda Mommy tace ta kasa gane kanki kullum cikin damuwa kike kin daina ko fitowa falo kuma tasan baki da wata aminiya da ta wuce ni"

Uhmm "Saudat ina cikin mawuyacin hali wallahi so na neman haukata ni ina zanga Jalal,Jalal ya gujeni Saudat numbers d'insa sun daina shiga sau biyu ina zuwa gidan su Abbas baya nan na rasa mafita"

"Gidan su Abbas meye zakije gidan su Abbas kuma?"

"Abbas ne abokinsa dan ko lokacin da yazo garinnan a gidansu ya zauna zan tambaya da ya bani new number Jalal"

Saudat ta had'e gira tace "haba k'awata don me zakije gidansu ai sai a raina ki wallahi"

"Ni banga raini ba na kirashi ban samu ba kuma shi kad'ai nasan zai fad'an inda Jalal yake"

Uhm "kinyi nisa Najwa na san yadda kika damu dashi k'ila tuni ya manta dake ma watanshi nawa bai nemeki ba.

" ke kike gani haka amma na san Jalal bai mantani ba"

"Idan bai mantaki ba meyasa bai nemeki ba ai ya san hanyar katsina kuma yasan gidanku ko"

"Nima idan har baizo ba zanje Abuja nemansa"

"Lallai kin cika babbar mara hankali"

"A soyayya dama ai bani da hankali Indai akan Jalal ne"

"Yanzu dai me zan cewa Mommy ince Jalal ne ya hanaki sukuni?"

Da sauri ta rufe mata baki "ki rufan asiri kawai zan daure in saki raina amma zan fara shirye-shiryen zuwa Abuja"

"Cab wallahi bada ni ba gad'a a kabari kuma Allah in kikace haka zakiyi sai na fad'awa Mommy"

"Shikenan na fasa'yar bak'in ciki"

"Koma me zakice kice".

*********

Kamar yadda Abbu ya tsara yau aka d'aura auren Jalal da Amal a Babban masallacin Jumma'a.

Ya kawo waliyyi da mutane biyar a matsayin 'yan uwa shaidu

Please Login or Register in order to submit comment