You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sau biyu.

Rik'e kumatu tayi zata sake magana ya shak'ota.

"Kin manta illar da yayarki tayi min,ta sakawa d'anta dani kaina muguwar cutar da ta kwaso a yawan banzanta,ke kanki da aka yi niyyar auramin ke guduwa nayi saboda ku d'in kowa ya san kunyi gadon iskanci"

"Wallahi sai na fanshe marin da kayi min a kotu"

Da k'yar aka rabasu tare da fad'a musu bai kamata suzo asibiti suyi fad'a ba inda ake jiyya,Mommy na kuka Janan na kuka.

Da sauri Hajar ta fita,Adnan ya kalli Janan har zaiyi magana kawai ya juya da sauri ya fita,tayi saurin bin bayanshi.

"Kada ki sake ki biyoni" tsawar da yayi mata ne ya saka ta saurin tsayawa a gurin tamkar an dasata.











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```






49

"ALIYU" ta furta cikin matsanancin kuka.

Jin sunan da ta ambata ne ya saka shi tsayawa cak tare da juyawa ya kalleta.

"Aliyu kike ambata a gabana?"

Sunkuyar da kanta tayi k'asa tana zubda hawaye,ya matso dab da ita ya tallabo hab'arta da yatsa d'aya "bayan janyo Hajar da kikayi shine kike ambatar Aliyu a gabana"

Janye kanta tayi sannan tace "Aliyu ya ruguza rayuwata,kai kana neman k'arasa ta da wanne zanji"

Har zaiyi magana sai kuma kawai ya fasa ya wuce da sauri ya fita,ita kuwa da sauri tabi bayanshi kamar wata jela.

Kan wasu kujeru ya zauna tayi saurin zuwa ta tsaya a gabanshi.

"Bakya kishina Janan,meyasa zaki rik'a ambarta sunan Aliyu?kina son na mutu da b'acin rai da damuwa?"

"Kaine fa,ko ka manta alk'awarin Iya?taya zan gujeka?taya zan kasa yin kishin abinda zuciyata take son ta rayu dashi,idan ka d'auke Mommy da Jalal nafi kowa sonka a duniya"

"Ina son kiyi proving,ki d'aukar min alk'awarin bazaki tab'a guduna ba nine mijinki na har abada"

Shiru ta d'anyi kusan minti 3 bata ce komai ba har ya fara zargin kodai bazata amince ba.

"Kana da buk'atar na dafa al Qur'ani?"

'Dago kai yayi ya kalleta wanda itama shi d'in take kallo.

"Bana buk'atar hakan amma ina buk'atar kiyi min alk'awarin zaki zauna dani har abada"

Idanunta cike da hawaye ta zauna gefensa tare da cewa "ni taka ce har abada Adnan,nayi alk'awarin da kai kad'ai zan rayu"

"Bana son k'ara ganinki tare da Hajar"

"Bazaka sake ganina da ita ba dama fa taimakana tayi shiyasa amma bazan so duk wanda zai wulak'anta min Salman d'ina ba"

Murmushi yayi yace "Salman d'in Iya dai"

Murmushin da tayi har saida suka bayyana hak'oranta "kasan me?"

"Sai kin fad'a"

"Sai naji dama Iya na raye taga aurenmu"

Kallonta yayi tayi saurin rufe fuskarta da hannu.

"Muga fuskar taki mana"

Da sauri ta tashi zata bar gurin yayi saurin rik'o hannunta tare da zaunar da ita inda ta tashi.
"Oh guduna zakiyi"

"Tunani nake Abba k'arami ya tashi kuma zai nemeni nasan"

"Eh hakane ashe yaronmu na kwance ba lafiya muka taho muna soyayya oyaaa tashi muje".

**********

Washe gari tana zaune kan gadon Abba k'arami yana kan cinyarta lokacin an cire masa oxygen d'in.

Tunani kawai take ta hanyar da zata bak'antawa Aliyu ba tare da ta koma gidansa ba.

Ita kam a yanzu bata jin akwai wani wanda zata iya zaman Aure dashi idan ba Adnan ba uwa uba tana da cutar HIV ta san ta zama ta Adnan duk da taso ace ta koma ga Aliyu ko dan bak'anta masa amma kuma ta hak'ura dan Adnan ko sunansa baya son ji.

'Karar message daya shigo wayar ta ne ya sa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta shiga.

'Daukar wayar tayi ta bud'e sak'on ta fara karantawa.

_Assalamu Alaikum!_
_Da fatan kina nan lafiya,ya jikin prince?Allah dai yasa da sauk'i,dan Allah ki kula min dashi sosai banason inji yana rashin lafiya idan ba haka ba zan zo in d'aukeshi dan nasan bakya wani kula dashi yadda ya kamata,Allah ya bashi ingantacciyar lafiya mai d'orewa ameen._

Duk da babu suna amma ta tabbatar Jalal ne saboda number da aka yi text d'in bata 9ja bace,duk jikinta yayi sanyi sosai.

Tana zaune tana sake karanta sak'on kawai taji sallama akanta.

'Dago kai tayi ta kalleta sai kuma ta had'e rai tare da juyar da kanta gefe.

"Janan kiyi hak'uri ban san alak'arki da Yaya Adnan ba amma yadda ya nemi fad'a min magana shiyasa nima na rama"

Ganin janan bata da niyyar bata amsa yasa ta k'araso zata d'auki file d'in Abba k'arami Janan tayi saurin rik'e hannunta.

"Karki tab'a" ta k'are had'e rai.

Ajiyar zuciya tayi tare da cewa "bani da masaniya akan ciwon da Yaya bilkis ke dashi wanda har ta d'orama Yaya Adnan,duk da bamu san me yayi ajalinta ita da d'anta ba a lokacinta amma inajin ance Yaya Adnan nada HIV na tabbatar Yaya bilkis ce ta shafa masa saboda na san tana tarayya da maza kala-kala dan haka samun AIDS a jikinta ba abin mamaki bane,nima ana min kallon haka amma wallahi ni ban tab'a yawon banza ba,na dai san nid'in kawai inada yawo ban san zaman gida"

Kallonta Janan tayi tace "to na buk'aci ki bani labarin ki ne?"

"Baki buk'ata ba amma ina son kawai ki nema min gafara wajen Yaya Adnan da Mommy amma bayan an sallameku,iyayena sun wulak'antasu amma wallahi daga baya duk munyi nadama" ta d'an goge hawayen idonta wanda yasa jikin Janan ya k'ara yin la'asar.

"Kiyi hak'uri akan abinda na miki"

"Karki damu Janan duk mun samu rashin fahimta ne"

Zama tayi tana sake bata labarin rayuwarsu hakane yasa Janan ta k'ara jin tausayin Adnan da son shi har cikin ranta.

A lokacin ta sanar mata cewar Adnan yace baya son ganinsu tare,tace aikuwa da taga lokacin zuwansu yayi zata bar gurin koda itace on call.


Washe gari kuwa suka je suka karb'o result,babu wani abu dake damunsa a cikin k'ashinsa ko kayan cikinsa zuwa brain d'insa sai ciwon convulsion (figar ruwa) kad'ai dake damunsa hakan ne yasa ta d'anji sanyi kad'an a ranta.

*_3 weeks later_*

Yau ne ranar da Janan suka dawo gida an sallami Abba k'arami,ya warke sosai sai dai ya rage surutu sai rigima daya tsira ta gaira ba dalili sai yayi ta mata kuka ina daddy,tun bata jin haushi har ta fara yi masa tsawa akan ya hau jirgi ya bashi can Singapore.

Ranar nan Mameey fad'a tayi ta mata akan yadda take yiwa Abba k'arami fad'a tamkar wani babba.

*********

Yau ne suka dira a Kaduna a kuma kotun da aka yi shari'ar Aliyu da Abba.

Wani sabon kuka ne ya b'alle wa Fauziyya tana ganin kamar a lokacin ake shariar.

Mameey kanta dauriya kawai take amma hoton shari'ar take gani a idanunta.

Sagir,Mommy, Adnan,sai rarrashin Fauziyya suke yayinda take jin kamar cewa suke tayi kuka.

Lokacin da suka isa sai da sukayi jira na kusan awa biyu dan alk'alin a lokacin yana gudanar da wata shari'ar.

Bayan an gama ya buk'aci da su shigo,aka yi musu iso suka shiga.

Adnan ne yayi masa bayanin abinda suke tafe dashi.

Ya kalli Alto yace "Malam ka tabbata idan muka je zaka gane inda kuka sare bishiyar"

Alto ya russuna yace "k'warai ma kuwa dan bazan manta komai na daga kafin a fara gani har zuwa gama wa dan ban tab'a ganin mutum mai adalci da mutumci kamar Alhaji Hashim ba sannan ban tab'a aikin gida da yayi min dad'i kamar nasa ba Allah ya masa rahama" ya fad'a yana goge hawaye.

"Ameen" duk suka amsa.

"Shikenan zamu tafi dani daku da ma'aikata na,za'aje ka nuna gurin a tona amma fa da sharad'i"

"Wane sharad'i fa?" Adnan ya tambaya.

"Idan har bamu ga komai ba tabbas za'a hukuntaka hukunci mai tsauri"

Jikin Janan gaba d'aya ya mutu,ta kamo hannun Abba k'arami dake rik'e dana Adnan ta damk'e sosai tana karkawa.

"Na yarda" Alto ya fad'a.

"Idan kuma aka gani zamu barku da Allah domin kunyi sanadiyyar rasuwar mahaifinmu kun samu a k'unci kunyi shari'ar zalunci da son zuciya"

Duk suka juya suka kalli Fauziyya, wani security dake tsaye ya nufota alk'alin yayi saurin dakatar dashi sannan ya kalleta yace "ni kuma nayi alk'awarin idan ba'a ga kud'in nan ba sai kinyi zaman gidan yari na tsawon shekara guda,yanzu ma sa'a kawai kika ci ba ana shari'a kika yi min tsaurin idonnan ba".

**********

Ja'afar yana zaune kan kujera,yayinda yaransa uku ke tsaye.

Daga upstairs d'in ya fara jiyo hayaniyarsu.

" fito wallahi kin bar auren Aliyu har abada 'yar matsiyata"

Trolley aka fara wurgowa tayo k'asa,kallon trolley yayi sannan ya maida hankalinsa saman.

Zuhra na gaba tana hawaye Umma na k'ara tunkud'ota Aliyu yana gefen Umma.

"Lafiya?" Shine abinda Ja'afar ya tambaya lokacin da suka k'araso falon.

"Ya saketa amma dan bak'in naci tak'i tafiya,wannan da kake gani 'yallab'ai ita ta tarwatsa rayuwar gidan nan"

"Kamar yadda kema kika tarwatsa rayuwar wasu" duk suka jiyo dan ganin wacece.

"Janan" Ja'afar,Aliyu,Zuhra duk suka furta lokaci guda.

"Janan ce, nazo d'aukar fansar mahaifina da kuka yi sanadiyyar mutuwarsa"

"Babu abinda kika isa kiyi munafuka"

"Kinci darajar ke babbace wallahi da sai na zageki"

"Janan kina da hankali kuwa?"
Kallon Ja'afar tayi har zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ta kalli k'ofa tace
"ku shigo".






_*Mu had'u a next page*_😉










_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄





```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





50

Juyowa tayi sai lokacin ta kula da k'afar Mommy ninke da bandage amma dan bala'i haka ta fito da Zuhra duk da azabar da take ji.

Shigowar su Mameey ba k'aramin d'agawa Aliyu hankali yayi ba yadda ya gansu tare da 'yan sanda da alk'ali daya yanke shari'a.

Bayanin komai aka yiwa Aliyu sannan suka juya dukansu zuwa farfajiyar gidan.

Daga can tsakiya gefe ya nuna daidai rumfar da aka yi ta hutawa yace "Allah ya taimake ka nan ne inda aka sare wannan bishiya"

"Ka tabbata?"

"na tabbata yallab'ai"

Juyowa yayi ya kalli Fauziyya "karki manta idan har ba'a ga komai ba kinada shekara d'aya a prison shima sai shari'a ta hukuntashi"

"Ni kuma ina da kud'in da zan d'aukaka k'ara idan har aka sake zaluntar mu"

Duk suka juyo suka kalli Janan wanda a lokacinma hawaye take.

Ja'afar magana kawai yake son yi mata amma tsananin mamakin da take bashi ya hanashi cewa komai.

Kujera aka d'akko wa alk'alin ya zauna,yayinda duk su kuma suke tsaye.

"Janan dama zan sake ganinki a rayuwata"
Zuhra ta fad'a tare da rungumeta tana kuka.

Ja'afar ya samu k'arfin gwiwar kamo hannun Abba k'arami tare da rungumeshi.

Aliyu kallonta kawai yake ita da yaron dan ya tabbatar d'ansa ne a jinin jikinsa yake jin son yaron.

Suna tsaye aka kirawo masu hak'on rijiya dan su tona gurin.

Kusan minti talatin da fara abin Umma ta juyo ta kalli Zuhra dake tsaye a gefe "munafuka an sakeki shine kika tsaya ganin gulma" ta juya ta kalli Aliyu "ka kureta ta fice anan"

"Umma rabu da ita a gama wannan aikin tukunna"

Harara ta dallawa Janan lokacin da suka had'a ido.

Da sauri Janan ta tashi ta koma gefen Adnan ta ja kujera ta zauna.

Mommy na tare da Mameey a tsaye,Fauziyya ma suna zaune a gefe ita da mijinta da 'yarsu.

"Ba dai wannan shine babyn da kika haifo ba?" Ja'afar ya fad'a.

Murmushi tayi tace "shine,Ashe dama zamu sake had'uwa da kai d'an sanda mai basaja?"

Murmushi shima yayi yace "kece mai basaja ai,tunda kika tafi kika k'i dawowa kullum da munji sallama sai munyi tunanin kece"

"Allah sarki dan Allah kuyi min uzuri insha Allahu zanje in gaida Mammy"

"Allah yasa da gaske kike"

"Ameen"

_kenan dagaske itace Janan d'in da wannan yarinyar ta fad'a?to meye had'in Janan da wannan gida da kuma tonewar da za'ayi yanzu?tabbas zanso jin labarin chakwakiyar nan._


"Janan a ina kika san wannan kuma?"

"Shine wanda na kwana a gidansu lokacin da na taho daga Yola"

"Janan d'ita mai mutane"

Murmushi kawai tayi

Har kusan awa d'aya da wani abu sannan aka ga akwatin,duk ya mak'ale da k'asa da k'yar suka fiddo shi.

Ajiyar zuciya Janan tayi dan gani take dukiyarsu ta dawo.

"Yallab'ai gashi mun fiddo"

'Daya daga cikin masu aikin ya fad'a yana goge zuffa.

Alk'alin da kansa ya taso ya tab'a akwatin yaga da kwad'o a jiki.

Kuka da Fauziyya ta fashe dashi ne yasa duk suka juya gareta.

Janan ta rungumeta sosai suka cigaba da kuka.

"Fauziyya kina babba bai kamace ki ba"

"Ina ma Abba na raye yaga wannan rana" Fauziyya ta fad'a tana cigaba da kuka.

"Ku b'alle akwatin" Alk'alin ya bada umarni.

Guduma suka saka suka dokeshi aikuwa ya bud'e.

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,wato da aka bud'e akwatin gara da k'wari duk sunyiwa takardun kaca-kaca sai b'urb'ushen wasu wasu kam babu ma,ga k'wari a ciki har lokacin.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Aliyu ya fad'a tare da zubewa k'asa sumamme.

"Umma dake tsaye itama jiri ke d'aukarta tana fad'in " wallahi k'aryene bazamu yarda ba,k'arya suke sharri ne"

Rugawa tayi da gudu tayi waje da k'yar aka kamota.

Ganin tana hauka tuburan ga k'afar sai jini take hakan yasa aka k'ulleta tare da yi mata allurar bacci.

"Abba na cika maka burinka,da taimakon Adnan da Jalal ya Allah kajik'an Abba ka sakawa wannan bayin naka da suka taimakamin,Abba meyasa ka mutu meyasa baka jira wannan rana ba nayi maka sanadi Abba ka yafe min"

"Janan kiyi hak'uri ki bar kukan haka" Mommy ta fad'a tare rungumeta

"Ku barni nayi kuka bazaku gane irin illar da suka min ba".

Anan ne Ja'afar yaji labarin komai ya tausaya musu k'warai.

Alk'alin yace za'a yanke shari'a da zarar sun samu sauk'i(Aliyu da Umma).

Fitowa sukayi zasu tafi Mommy tace Janan sai dai ta bita su tafi Abuja,har zata musa Mameey tace a'a taje.

Zuhra kuwa tausayin Aliyu ne yasa ta maida kayanta zata zauna har zuwa lokacin da zasu warware.

"Janan" Ja'afar ya fad'a cikin sanyin murya.

Ta d'ago idanunta da suka gama rine wa ta kalleshi.

"Dan Allah Janan ki yafewa Ummi dan lokacin da zata mutu sai da ta tabbatar ta rok'eni kan na rok'a mata yafiya gareki"

"Bazan yafe ba" abinda ta fad'a kenan tare da jingina da motar tana kuka.

"Karka damu zan lallab'ata zata yafe da iznin Allah" Adnan yayi maganar.

"Alk'awari na d'auka zan rok'ar mata"

"Nima zanyi iya k'ok'ari da kanta zata kira tace maka ta yafe"

Exchanging number sukayi sannan ya tafi.

Janan ta juyo ta sake kallon gidan ta tuno rayuwar da sukayi a baya ta k'ara fashewa da kuka tare da fad'in "So haka yake Ashe?ko dad'i ko k'unci".

Rarrashinta Mommy tayi sannan suka shiga mota suka tafi,Mameey kuma sukayi kano.

***********

Tsawon wata d'aya Mameey,Fahad da Adnan suna zarya game da dukiyar.

Basu bar Kaduna ba sai da suka tabbatar an karb'i komai na dukiyarsu.

ATM's d'insu ba'a tab'a kud'in kowa ba sai na Abba dashi Aliyun ke amfani,sai filayen Mameey da gidaje wanda Abba ya siya mata duk sun dawo hannunta.

An raba gadon Abba an bawa kowa nashi Janan nata tace Fahad ya cigaba da juyawa na Fauziyya kuma ta bawa mijinta dukiyar da suka samu ba ta wasa bace gami da filaye da ginanun gidaje duk da sun saukewa Abba nauyin bashishshikan da ake binsa suma still an kawo musu kud'ed'e da yawa da Abba ke bin mutane.

Aliyu kuwa lokacin ya tashi,Umma kuwa k'afa ta rub'e tuni aka mayar dasu kangire gidansu da suka baro,Zuhra ta tafi gidansu anyi anyi ta koma tak'i babansu yace a k'yaleta mamanta kuwa tun a lokacin ta fara dana sani Abinda tayi.

Fahad kuwa yace bazasu zauna a gidan ba sai an sake gyarashi dan haka suka koma can wani gidan Abba dake Malali.

Sannan Aliyu an bashi wata uku ya dawo da duk wani abu daya ci musu tunda babu wata dukiyarsu da aka gani.

A hakanma dan Adnan ya d'akko wani judge ne amma da wancan so yayi ya lank'wasa abin.


_*2 weeks later*_

Fitowa tayi hannunta rik'e dana Abba k'arami.

Tun daga nesa ya k'ura mata ido bai d'auke ba har sai da tazo gabanshi tare da huta masa iska a kunne.

"Ke......"

Dariya tayi tare da cewa "sarkin tunani me ake tunawa kuma?"

"Abu biyu?"

"Da wanne da wanne?"

"Rayuwar da zamuyi idan munyi Aure sai na biyu kuma wallahi bana son tafiyar nan"

"Meyasa baka so?"

"Kawai bana son ganin Aliyu sai nake ganin kamar zakice zaki koma gare shi"

Ajiyar zuciya tayi tace "kai nawa ne nima taka ce, babu abinda zai rabamu da yardar Allah, yanzun ma zuwan dole ne ta kama inje d'in"

"Amma ai an gama komai me zakije kiyi musu kuma?"

"Akwai maganganu a bakina da yawa amma sai munje zakaji"

"Allah yasa alkhairi ne"

Murmushi kawai tayi ta shiga motar,shima zagaya wa yayi ya shiga ya tada motar suka tafi.

Suna tafiya suna hira har suka isa Kangire.

A bakin k'ofar gidan ta d'an tsaya wasu zafafan hawaye suka taru a idonta,abu biyu ta tuna Jalal da rayuwar k'auyen.

Da sallama suka shiga gidan Umma na kwance a tsakar gida k'afarnan a kumbure Aliyu na gefenta.

Ganin Janan da yayi ne yasa shi saurin tashi fuskarshi d'auke da hawaye yace "Janan dama zaki waiwayeni"

Adnan da ya gani a bayanta rik'e da Abba k'arami sai duk jikinshi yayi sanyi.

"Janan d'iyata,Janan kinga yadda Allah ya mayar damu ki yafe min Janan"

"Yafiya?Umma yafiya fa kika ce?" Ta fad'a cikin kuka.

"Lokacin giyar so na d'ibata ban damu da abinda kuke min ba amma babu irin rok'o da ban muku ba kan ku yafewa Abba duk da a lokacin ban san wani irin laifi ya muku ba amma kuka take,bak'in cikinku ne ya kashe Abba bazan tab'a yafe muku ba"

"Janan...."
"Dakata Aliyu dama ni abu biyu ne ya kawo ni gidannan"

Ta janyo Abba k'arami tace "ga d'anka ka sani na sani d'anka ne amma ka shegantashi tun kafin yazo duniya hakan ne yasa na cigaba da shegantashi dan babu wanda ya san kaine ubansa,bazan tab'a sanar dashi kaine mahaifinsa har sai ya girma yayi hankali in fad'a masa yadda kukayi amfani da son zuciya da irin sigar da kuka bi kuka tarwatsa farin cikina ta yadda zai k'ara tsanarka"

Ta cigaba da hawaye tana fad'in "abu na biyu shine ko ni kad'ai na rage na yafe maka sannan ka shiga aljanna wallahi bazan tab'a yafewa ba,kun cuceni kun zalunceni Allah ya isa tsakanina daku Allah ya mana sakayya"

Da sauri taja hannun Abba k'arami ta fita,yayi sauri zai bita Adnan ya rik'oshi.
"Karka bita yanzu"

"Dan uwa ka ceceni wallahi na san alhakinta ne ya fara binmu,Mamata ta gujeni,ga Umma kwance ance sai an yanke k'afarta bani da kud'in yin hakan ga kud'in da akace sai na biya duk 'yan uwanmu sun gujemu abinci ma da k'yar nake samu fatana ta bani d'ana ko ganin shi ne inyi sannan ta yafe min"

"Tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere,Janan bazata yafe maka a k'ank'anin lokaci ba kadai ta yin addu'a"

Hannu yasa ya fiddo kud'i bai tsaya dubawa ba ya bashi sannan ya juya ya tafi Umma na kuka Aliyu nayi.

Yana fita yaga babu Janan,ya tsorata har yayi shirin shiga nemanta sai gata sun fito daga mak'ota.

"Wannan itace wadda ta rik'a dawainiya dani lokacin dana zauna a gidan can"

Gaisawa sukayi da Adnan shima da zasu tafi ya bata kud'i yace tayi cefane.


A hanya ne Adnan ya rage sautin wa'azi sannan ya d'an kalleta idonta na kan titi.

"Dama Abba d'an Aliyu ne"

Gabanta ya fad'i sai da ta d'an jima sannan tace "eh"

"Meyasa kuka b'oye mana?"

"Kayi hak'uri"

"Baki yarda damu ba"

"Wlh ko kad'an"

"To meye dalili?"

Labarin mafarkin Abba ta bashi.

Sai daya d'an murmusa sannan yace "mafarki ai ba gaskiya bane"

"Umm" kawai tace.

"Janan" ya kira sunan a can k'asan mak'oshinsa.

"Na'am" ta amsa a sanyaye.

"Janan ki zama mai yafiya sai kiga Allah ya kara bud'a miki"

Shiru tayi kamar bata jin me yake fad'a.

"Abinda aka yi miki ba'a kyauta ba amma ke ya kamata ki zama mai manta komai Allah ma muna masa laifi ya yafe mana,dan Allah ki yafe musu musamman Ummi da take k'asa kuma ki daina sheganta d'anki kinji"

Nan ma shiru tayi ta cigaba da yin game a wayarta Abba k'arami kuwa tuni yayi bacci.

"Magana nake miki fa Janan"

Kuka ta fashe dashi tamkar k'aramar yarinyar ganin haka ne yasa shi bata hak'uri.

Har suka isa gida bata daina kuka ba,nan ma Mommy ta shiga aikin rarrashinta.

Adnan kuwa hatta Jalal da baya k'asar sai da ya kira ya sanar masa cewa Abba k'arami na da uba,dariya yayi tayi yana cewa shi dama ya san halin Janan lallai a gaida Janan.

Kwanci dashi bikinsu sai matsowa kusa yake,kullum sai yayi mata maganar yafiya kuma sai tayi kukannan amma bai fasa ba dan yasan wata ran zata yafe kuma burinsa shine ta yafe d'in.

Da kanshi ya kaita asibiti aka d'orata akan magungunan masu cutar HIV sannan aka fad'a mata ranakun da zata na zuwa lectures da kuma yadda zata bi k'a'idojin maganin.

Ana saura sati biyu biki Mameey ta rok'i Mommy alfarmar d'aukar Janan saboda suyi bikin acan ga danginta duk zasu zo.

Mommy kam bata musa ba amma tace sai dai abar Abba k'arami a gurinta.

Hakan kuwa aka yi Janan ta koma kaduna ta sake sabon shirye-shirye da Mameey ke mata tamkar auren fari.

********

Rana bata k'arya sai da uwar d'iya taji kunya,yau ne............





_*bikin Adnan da Janan dole a gwangwaje ku biyoni a shafi na gaba*_











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




51

Anyi komai na shagalin biki tamkar na budurwa,Kamu,dinner, gala,da duk sauran occasions da ba'ayi ba lokacin bikinta da Aliyu sai da aka yi yanzu,duk da bata da wasu k'awaye a Kaduna amma 'ya'yan 'yan uwa da abokan Fauzah duk sun zo,Humaira da Zee kuma suna a gaba,Momma dama da ita aka fara biki Muhasin sai ranar d'aurin Aure zaizo,Mammy ma cewa tayi ranar d'aurin Aure zata zo Ja'afar zai kawota sai su Kausar Jidda da laila ne sukazo ,Raihan bata zo ba amma Lubna da ita aka yi komai dama tun wancan zuwan bata koma ba,Umman Lubna kuwa bata hanata komai ba dan itama tana zuwa ayi aiki anan ne take fad'awa Janan d'in cewa daddyn Lubna na tayasu murna da fatan alkhairi dan bazai samu zuwa ba yana jin nauyin iyalan Abba.

Haka Maman Raihan ma tazo amma bata fad'i dalilin rashin zuwan Raihan ba itama kuma Janan d'in bata tambaya ba.

Gidan dai cike yake da bak'i kala-kala.

Yau ma a gajiye ta dawo tana shiga d'aki ta cire kaya ta saka na bacci sannan ta zube kan gado tare da lumshe ido.

Lubna ta d'aleta "Lallai yarinyar nan me kike nufi?"

Ta d'an bud'e ido d'aya tace "ke wallahi bacci nake ji na gaji"

"Allah tashi zakiyi mu fita mu kama wani aikin gobe fa d'aurin aure"

Rufe idon nata tayi tace "babu inda zani wallahi a gajiye nake ga wayata nan Adnan ma ce masa nayi kada ya kira sai sun sauka saboda bacci yayi min yawa a ido idan ya kira ki tasheni"

"Cab kin raina min hankali fa wato ni zan jire miki kiran Adnan ba?"

"Haba kawata kinsan nifa Amarya ce sai da lallab'a"

"Lallai kam,sannu amarya ke d'in zan lallab'a?zaki bushe kuwa"

"Ni dai komai zaki ce baccina zanyi" ta juya mata baya.

Lubna tayi dariya ta fita kawai.

Kamar daga sama taji wayarta na ringing ta lalubo da hannu ta d'aga sannan ta kara a kunne.

"Har kun isa?"

"Itace sallamar?"

"Oh salamu alaikum da fatan kunje gida lafiya ya gajiyan dinner?"

Murmushi yayi tamkar tana gabansa yace "Alhamdulillah kinga yanzu muka sauka ko fita daga mota banyi ba nace sai na kira gimbiyata naji ya take"

Hamma tayi tare da yin mik'a sannan tace "wallahi har na fara bacci"

"Tun yanzu"

"Eh wallahi kasan tunda aka fara biki ban samu nayi baccin cikakken awa biyu fa"

"Meyasa?"

"Hayaniya mana ga kasan dai taro dole sai an gama ake samun nutsuwa"

"Hakane kam ai bayan biki a gaba zan sakaki ki rik'a yin bacci har sai na tabbatar kin huta kin rama baccin ki"

Dariya tayi cikin jindad'i tace "office d'in fa?"

"Ai hutu zan d'auka na wata uku inci amarcina dani dake babu mai takura mana in riritaki tamkar kwai"

Dariya ta sake yi tare da fad'in "wow kace na zama 'yar gatan Adnan"

"Sosaima"

"To yanzu kasan abinda za'ayi?"

"Sai kin fad'a"

"Kaje kayi wanka kaci abinci sannan ka kwanta kayi bacci dan ka huta kafa kashe wayarka kada ma Adam(amininsa) ya damar min kai da kira,ka kular min da kanka"

"Karki damu gimbiyata angama duk abinda kikace ai shi za'ayi"

"Yawwa na manta ban fad'i wani abu ba?"

"To ina jinki"

"Kayi mafarkina kaji,ina Sonka sosai" bata jira me zai ce ba ta katse wayar ta kasheta gaba d'aya saboda kunya taji, murmushin jindad'i tayi ta fara tunanin irin soyayyar da zata

Please Login or Register in order to submit comment